Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 18
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 18: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 18. Tana shiga d'akin gwaggo ta nufa lokacin tana…
4,253 words
Tana shiga d'akin gwaggo ta nufa lokacin tana cikin cin Abincin da Haulat ta zubo mata ta nufeta ta zauna ta jingina da jikinta a Shagwa6e take fad'in "shine kuka je kukai zaman ku bacin tun ran Juma'a aka d'aura Auren baku damu da kun bar ni ni kadae ba ko" dakatawa gwaggo tay tana dariya tace "to ayi hakuri auta kamawa tay nima duk na damu da rashin ki kusa amman kuma dae ai nasan ba ke kadae na bari ba ko" tura baki tay haulat dae nata dariyar yadda Fatun keta shagwa6a, yabon Abincin gwaggo ta shiga yi da yadda suka gyara gidan tace sunyi kokari sosae hakan yasa ta warware ta fara dariya cike da tsokana gwaggo tace "shiyasa bani da wani shakku akan ku in ku kai aure" turo baki Fatun tay tace "in dae tay aure" gwaggo tace "kema ai zaki yi ne ko an dingi karatun ne ba ranar gamawa?" Tace "ai kona gama ni bazan yi aure ba" da sauri gwaggo tace "ba Amin ba ban fata in ma kina cikin karatun Allah ya kawo Nagari ai aurar dake zanyi kawae Kya idasa a d'akin mijinki" shiru tay kawae cikin ranta tana ayyana da nasamu wanda nike so ma kafin in fara karatun zanyi aure na kallon haulat tay suka had'a ido tay mata Murmushi ita kuma ta tura mata baki, Bayan Magrib duk sunyi salla gwaggo ta kwala masu kira suka shigo d'akin suka zauna ta janyo wata katuwar jaka cikin kayan da suka zo dasu ta tura ma Fatun tace "ga sak'on Yayanki nan tunda bazaki tambayeshi ba da Auntyn taki Amarya, d'an kallon juna sukai ita da Haulat cikin kama kai tace "ai na tambayi ya Abbas ne fa shiyasa banyi maki Maganar ba" gyad'a kai tay Haulat ta kai hannu ta bud'e jakar wadda ta bikin ce mai d'auke da sunayensu a cikinta ma duk tarkacen souvenirs ne da aka rarraba a bikin kaya jibgi guda sai kace d'an gidansu ne yay auren ai ko d'an gidansu ne bazata samu rabin su ba ma, wata k'atuwar Calendar Haulat ta fiddo ta bud'e har bata san lokacin data furta "Wow! Gaskia sunyi matuk'ar kyau wllh" gwaggo ta amshe da fad'in "ah ai ba'a cewa komae Haulat sai Mutum ma yaje hidimar abun sai san barka wllh amman an yi matuk'ar kokari kowa yabo da fatan Alkhairi yake masu" Haulat dake murmushi tace "Allah ubangiji yasa Alkhairi ya basu zaman lafiya" gwaggo ta amsa da Amin Fatuu ma ta amsa a hankali duk jikinta yay sanyi lakwas, mik'a mata Calendar d'in Haulat tay kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa ta zuba mata ido Haisam kawae take kallo sun yi kyau iya kyau hoto ukku ne a jiki babba na sama sai biyu a k'asa gefe da gefe sunyi shiga daban daban ta Alfarma dake nuna mawadatan Mutane ne ko ina Fanan tayi dariya shi kuma d'an Murmushi yayi wuri d'aya ne yay yar dariyar da har dimple d'inshi ya lotsa da sauri ta mik'a mata Calendar din jin kwalla na niyyar taruwar mata a idanu, Haulat taci gaba da fiddo abubuwa harda jakunkunan kwali suma masu d'auke da pic dinsu gwaggo ta sake janyo wata jakar ta fiddo yan buckets masu kyau guda ukku suma dai na bikin ne tace ma Fatuu ga kuma sak'on Hajiya suma haulat ce ta bud'e marfinsu d'aya dublan ne d'aya cincin da doughnuts d'ayan kuma Alkaki ne da cake gwanin sha'awa d'an murmushi tayi ta tambayi gwaggo ita sai yaushe zata dawo tace bata sani ba amman zata d'an kwana biyu, suna haka Amadu ya shigo ya zauna hiran bikin ya shiga yi masu harda pictures da Vedios ita dae Fatuu zugudum tayi Haulat nata washe baki tana tsuma had'i da yabawa sai faman zuzuta bikin yake da gidansu ya Haisam d'in da gaba d'aya garin Abujar don sun fita da Nameer ya zaga gari dashi bama sau d'aya ba gaba d'aya jikin Fatuu yayi weak lokaci guda ta yanke tun farko sunyi kuskuren da har sukae tunanin Haisam zai so ta don kwata kwata ba ajinta bane ma, sai da akayi isha Haulat tace zata tafi gida gwaggo ta d'ibar mata abubuwan bikin tace ta kai ma Innarta ta kuma bata kud'i farko K'in amsa tay saida gwaggon tace yaushe suka fara wasa irin haka sannan ta amsa tayi godiya itama Fatuu ta d'ibar mata komae cikin nata ta rakata har gida koda innarsu taga abubuwan da aka bata sosae tay godiya har tana zolayar Fatuu tana cewa da yake fa gwaggo ta dawo gashi nan tana ta fara'a yanzu ita dae yar dariya kawae tay daga baya tay masu sallama haulat ta rakota bakin lungu ta tafi, da wuri gwaggo tay bacci ita kuma sam baccin ya k'aurace ma idanunta tay zaune saman gado ta tasa Calendar d'in tana sake kallo bata yi kuka ba saidae wata irin kewar Haisam d'in take ji k'arshe ta kwanta hannunta kan fuskarshi tana shafawa tana d'an murmushi mai ciwo tunowa da abubuwa da dama a haka dae har bacci yay awon gaba da ita.Washe gari tana cikin yin Breakfast Abbas ya kirata yace wurin 11 zai zo ya d'auketa ya d'an shiga Jami'a ne tace to sai lokacin ta tuna bata ma fad'i ma gwaggo ba dama suna tare a falon ta sanar mata godiya ta shiga yi da yima Haisam d'in Fatan Alkhairi tace tay sauri ta shirya kar lokaci ya k'ure yazo ta 6ata mashi lokaci ta amsa to ta mik'e, kafin lokacin ta gama shiryawa cikin doguwar rigar Atamfa ta d'an yi yar light make up k'arfe 11 saura yan mintuna yazo ta yafa gyalen da suka hau da kayan da takalma ta d'auki yar jakarta ta fita saida ta lek'a tace ma gwaggo sun tafi sannan ta nufi wajen, lokacin data isa bakin Motar kwankwasa glass tay ya bud'e yana sanye da jeans da t-shirt ta d'an lek'a tana murmushi tace gaba zata shiga ko baya sosae ta bashi dariya jin tambayar da tayi shima ya tambayeta a Motar ya Handsome ina take zama ta nuna mashi gaba yace to nan zata zauna sannan ta bud'e Motar ta shiga tana yar dariya ta gaidashi tay mashi ya gajiyar hanya ya amsa sannan yaja suka tafi, basu wani 6ata lokaci mai tsawo ba a Bank d'in aka gama mata komae bayan sun fito gari ya d'an zagaya da ita saida ya tabbatar ta warware sosae dama Abbas d'an barkwanci ne sosae yake ta saka ta dariya har tambayarshi tay game da Abincinta yace yayi dad'i sosae Feenah ma da Abdul sun yaba har santi sukae sosae ta washe baki can tace to in mark zai bata nawa zai bata, d'an jimm yay sai kuma yace "zan baki 95%" d'an jujjuya kai tay tace "Gaskia Ya Abbas ban yarda ba ka cike man 5 marks d'in kawae mana ba kace har santi su Aunty Feenah sukai ba" yana dariya yace "No bazan baki 100 ba da dai a gidan mijinki kika yi shi confirm kin cancanci 100%" d'an murmushi kawae tay bata ce komae ba, a wani Eatery ya tsaya yace suje suci Abinci batare data musa ba tace to suka nufi ciki ya tambayi abunda zata ci bayan sun zauna tace "Burger and ice cream" yar harara ya wurga mata kafin yace "I mean Abinci ba kayan kwad'ayi ba" tace "to ai suma Abincin ne tunda ana koshi" girgiza kai yay yace ta dai fad'i Abinci a shagwa6e tace "ni dai su nike so inna koma gida naci Abincin...." Tun kafin ta rufe baki ya fara girgiza mata kai kaman zatai kuka tace "Wayyo bafa haka Ya Haisam ke man ba dana fad'i abunda nike so yake man kuma kace Amanata aka baka fa" dariya sosae yasa yace shikenan yaja ma kanshi dama bai fad'i mata ba dariya itama take yasa akawo mata abunda take so d'in shima ya fad'i abunda za'a kawo masa, bayan duk an kawo masu suna cikin ci wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d'in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace "Latest Ango Mutanen US....." Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._
*ASM Bk2022*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.......wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d'in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace "Latest Ango Mutanen US....." Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri yaci gaba da fad'in "Mutanen Waje ya gajiyan hidima da tafiya" Haisam d'in ya amsa mashi da Alhamdulillah cigaba da fira su kae har Abbas d'in na tambayar shi lokacin da zai ci gaba da aiki yace sai Next week Abbas yace "Allah ya kaimu" amsa mashi yay da Amin ya d'an yi shiru Abbas d'in yace "gani tare da Mom Zaraah mun dawo daga bank an bud'e Account d'in amman mun tsaya Eatery muna cin Abinci" yar dariya Abbas d'in yay jin amsar da Haisam d'in ya bashi yace to, daga haka ya cire wayar Fatuu dake kallonshi lokaci guda ta yanke a ranta koma yace a batan ko bai ce ba, ita dama tasan ya daina damuwa da ita ne kawae don yayi Amarya tana cikin zancen zucin taga Abbas ya mik'o mata wayarshi yace gata, bin shi da ido tay yace "Vedio call ne zaku yi da Ya Handsome d'in ki" yay Maganar yana yar dariya jiki mace ta mik'a hannu ta amshi wayar kafin ta kalli screen d'in har saida gabanta ya d'an fad'i da suka had'a ido dashi, yana zaune kan leather sofa ya d'an kishingid'a jikinshi sanye da armless data bayyanar da suffarshi abunka da zuciya tuni Fatuu taga ya canja mata yayi mata wani irin Fresh, bin shi da ido tay ta kasa ce mashi komae Abbas dae ya ci gaba da cin Abincin shi,
"Zaraah ina wuni" ta ji cool voice d'inshi ta fad'a, d'an tura baki tay ta d'auke idonta don tasan da biyu yace haka can ta sake kallonshi taga still kallonta yake cikin shaky voice tace "..ina wuni, an je lpy" shiru yay mata ta fara yamutsa fuska ta k'ara gaidashi ya k'ara yin shiru d'an tura baki tay kaman zata sa kuka tace "to kayi hakuri" wani d'an guntun murmushi yay dama da biyu yak'i amsawa just yana son ganin reaction d'in da face d'inta zatai displaying, bin shi da ido kawae tay can yasa hannu ya shafi beard d'insa yace "ina fushi dake" da sauri tace "to mi nayi maka?"
"An d'aura man Aure but u couldn't call and rejoice wit me" d'an motsa baki tay ta sadda kai tabbas bata kirashi ta taya shi murna ba kuma har Haulat saida tace mata ta kira shi amman ta k'iya, d'agowa tay a hankali still kallonta yake duk ta kame kanta cikin rawar murya tace "to don Allah ka yi hak'uri Ya Haisam dama inata so in kira" d'an ta6e baki yay baice komae ba ta tura mashi baki fuskarta a yamutse alamar ya tanka amman yak'i cewa komae sai kallonta yake kawae sai da ya ga dama sannan ya tambaye ta ya Exams tace mashi Alhamdulillah yay mata fatan Alkhairi ta amsa sai lokacin ta tambayeshi ya Aunty Fanan yace tana lafiya daga haka yace zasu yi magana ta d'aga mashi kai ta mik'a ma Abbas wayan yana amsa yace "wai ina Amaryar ne ta barka kai kadae zaune"? Ya bashi amsa da tana Bedroom cike da jan Magana Abbas yace "d'anyen aure amman kai kana Parlor ita tana Bedroom ko har kun fara fad'a ne" yar dariya Haisam d'in yay jin wata magana ta Abbas d'in sai kace wasu k'ananun yara wai har sun fara fad'a sigh yay yace mashi tana hutawa ne bata jin dad'i, d'an buda ido Abbas yay kafin yace "Subhanallahi mi ya same ta ne naga lafiya lou ku ka tafi" bin shi da ido yay kawae Abbas d'in ya k'ara tambayar shi abunda ya same ta yasan in ba fad'i mashi yay ba bazai k'yaleshi ba hakan yasa shi ce Masha is Nausea daga tafiyan da sukai amman duk da haka saida Abbas d'in yace "amman dama tana hakan naga ta saba hawa jirgi sosae fa" ya k'are Maganar yana guntse dariya Haisam d'in yace zasu yi magana da sauri Abbas yace "No yakamata mu gaisa ai muyi mata ya jiki ga ma Mom Zarah itama zata gaidata" ya d'aga ido ya kalli Fatuu yace "Auntyn ki ce bata lafiya zaki gaidata ko?" Tura mashi baki tay yay yar dariya ya maida idon kan screen d'in yace ma Haisam Zarah zata mata sannu ya kai mata laptop d'in ya amsa da Ok kafin ya yunk'ura ya mik'e, had'add'an Bedroom ne mara hayaniya sosae komae na cikinsa fari ne tass sai d'an ratsin baki kadan a wasu wuraren, tana kwance ta kudundune cikin lallausan farin bargo ya tunkareta saida ya aje laptop d'in ta kalli can gefe kafin ya fara tada Fanan d'in a hankali ta fara motsi kafin ta yaye bargon daga fuskarta suka had'a ido, yar harara ta wurga mashi tana kokarin rufe fuskar k'asa k'asa yace Abbas ne zasu mata sannu shi da Zarah wani kallo ta wurga mashi tun kafin tace wani abu ya riga ta fad'in it's connected yay mata nuni da laptop d'in da ido, shiru tay ta fasa yin Magana ganin bata da niyyar tashi yace mata "sit up" d'an yamutsa fuska tay dama fuskar duk a harmutse take tay jajir abunka da fara ga idanunta ma sun d'an kumbura da gani dai tasha kuka gashin kanta ma duk ya harmutse haka lips d'inta ma sun d'an kumbura suma, cikin disasshiyar murya tace "but u know I can't am feeling pain al over my body" kallonta kawae yake yana tuna gumurzon da suka sha da ita wanda gaba d'aya ita taja har yay losing control yasa ta jigata sosae sam baiji dad'in hakan ba don da bakinta ta rink'a gaya mashi she hates him tunda shi mugu ne baida tausayi duk da yasan Azaba ce tasa ta fad'in hakan abun ne ma ya isheshi yay zaune a Falo har ya kira Abbas d'in a waya don su gaisa ko ya rage damuwa, matsawa yay ya kai hannu ya taimaka mata ta zauna ta jingina da heardboard sai faman fad'in ahhh take bayan ya zaunar da ita ya kai hannu can gefe ya d'aukko mata hula yasa mata duk abun nan Abbas na jin su duk da bada sauti sosae suke Maganar ba shi dama yasan ba wani ciwon tafiya dake damunta sai kace yau ta fara tafiya ai koda ma tana yin hakan to badae har abun ya kaita ga kwanciya ba ashe mazan gaske taji ya ayyana a mind d'inshi, juyo da laptop d'in yay ta kalli screen d'in suka had'a ido da Abbas dake mata murmushi itama da k'yar ta d'an yi mashi na yak'e yace "sannu Amaryarmu ashe baki ji dad'i ba yanzu yake fad'a man wai Nausea na damunki" d'aga ido tayi tay ma Haisam dake tsaye ya goya hannuwanshi a broad chest d'inshi wani kallo kafin ta kalli Abbas tay murmushi kawae bata ce komae ba yace ga Zaraah zata gaidata ta d'aga mashi kai ya mik'a ma Fatuu wayar kaman bazata amsa ba amman ba yadda ta iya ta kar6i wayar ta kalli Screen d'in suka had'a ido da Fanan kafin tace wani abu Fanan d'in tace "Zaraah how are u?" A hankali tace mata lafiya lou kafin tace ya jiki ta amsa mata da da sauki, shiru Fatun tay tana ta kallonta ita kuma sai d'an yatsine yatsine take tana sa hannu tana dafa forehead d'inta can ta kalli Fatun tace "naga baki zo biki ba gwaggo ta fad'a man kina Exams" jinjina mata kai Fatun tay tace Allah ya bada sa'a ta amsa da Amin daga haka ta mik'a ma Abbas wayar shima ya k'ara yi mata Allah ya sawake Haisam na d'auka yace mashi zasu yi magana kawae yay disconnecting don yasan halinshi yana iya mashi wata Maganar da bata kamata ba a gaban Zaraah, tun da su ka gama wayar taji komae ya fita mata a rai zuciyarta harta yanke mata Fanan d'in ciki ne da ita don tana jin k'awayenta in suna ma wad'anda zasu yi aure cikinsu da sun gama Makaranta Addu'ar Allah yasa suna zuwa first night su samu ciki wata tara su zo suna, Abbas ya lura da yanayinta da ya canza yace mata ta ida cinyewa su tafi ta d'aga mashi kai kawae haka ta rink'a turawa ba don tana jin dad'in su ba, bayan sun gama ya biya suka tafi ya maida ta gida kafin ta tafi yay mata fatan Alkhairi a jarabawarta tay mashi godiya sannan ta tambaye shi yaushe zai kawo mata Abdul wuni yace karta damu in ta gama exams in dae suka samu Hutu zai kawo shi yay mata hutun yanzu dae ta dage tayi karatu sosae Allah ya bada sa'a ta amsa da Amin daga haka suka rabu, koda ta shiga gida sosae tay yak'i da zuciyarta wurin kauda damuwa ta d'aukko littattafan da zata karanta ta fara karatu.
Washe gari Laraba Misalin k'arfe tara na safe suka shiga paper d'in practical physics sam bata yi mata wuya ba duk da lokacin da aka rink'a koya masu tana cikin damuwa sosae amman kuma ta fahimta tunda tana da brain mai kyau, kafin lokacin da za'a gama ma ita har ta gama ta taimaka ma Haulat wurin da ta kakare ko da Malaminsu ya zo Lab d'in yay going around yana ganin yadda suke yi yana zuwa kanta ya duba da murmushi yace "Weldone Sp kinyi komae daidai" d'an murmushi tay yace ta d'an taimaka ma na kusa da ita wanda basu gane ba tace to amman tana tsoron supervisors dake cikin lab d'in kar tay laifi yace ba wani abu sun yi magana dasu, aikuwa sosae ta shiga taimaka ma sauran students tana nuna masu yadda zasu yi, bayan sun fito ne kuma ta rarraba ma wasu daga cikin k'awayenta abubuwan bikin Haisam da ta kwaso, zo ka ga yadda Students suka rud'e suna yaba kyaun da sukae wasu na cewa sun ji sanarwar bikin a Radio wasu a Tv, wasu harda Addu'ar suma Allah ya basu mijin Novel yayin da wasu ke tambayarsu su d'in Matan Novel ne da zasu samu mijin Novel haka sukae ta shak'iyanci sosae suke ta Fatuu dariya wata har tana ce ma Fatun itama tasan mijin Novel zata aura tunda tana da suffar Matar Novel ita dae dariya kawae tayi yayin da cikin ranta ta ayyana na samu kuma na rasa, har Malamai duk wanda yazo wucewa yaga Calendar d'in ko wani abu mai hotonsu sai ya tsaya ya tanka har discipline master d'insu da ya gani yace yana so shima aka bashi Calendar dasu jotter, basu koma gida ba a Cikin Makarantar suka ci Abinci har Abbas ya kirata yay mata ya Exams haka gwaggo ma da Kawu Amadu, k'arfe 3:00 suka shiga next paper ta IRS wannan ai ko awa ba'ayi ba ta gama ana fara amsa duk suka bada don itama Haulat d'in ta gama cike da farinciki suka koma gida.
After 2 Months,
A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji, a yau su Fatuu na cikin tsananin farincikin da Allah ya nuna masu gama jarabawar su lafiya sai murna suke suna celebration don har anko sukae dogon skirt da yar top sai coat mai d'auke da year d'in da sukae graduation da department d'in da Mutum yay wasu sun sa himar wasu hula facing cap wasu kuma gyale sukae rolling sai d'aukar hotuna suke harda Malamai sukae d'an party, Fatuu ba tayi komae ba ta raba kaman da Jsce, gwaggo ta so yi mata abubuwa don har kud'i Haisam ma ya turo mata yace tay hidiman graduation d'in amman tace ma gwaggo duk asara ne ayi wani abun dasu kawae, tun wurin Azahar suka gama amman basu fita daga Makarantar ba sai wuraren La'asar a k'asa suka taho suna ta nishad'i ganin suna ta tafiya haulat tace mata ita dae gaskiya ta gaji amman Fatun tace aikuwa yau k'asa zasu je gida, suka ci gaba da tafiya har suka fara yin nisa sosae, suna cikin tafiya wata galleliyar Mota ta tsaya a gefensu da yake a gefen titin suke tafiya juyawa sukae a tare suka kalli Motar kafin suka juya don cigaba da tafiya kawae sai gani sukae glass d'in Motar ya fara sauka nan take sukae arba da mai tuk'a Motar wanda matashi ne zai iya kaiwa shekaru 28 haka wankan tarwad'a ne yana sanye da kananan kaya kuma da gani Hutu ya zauna mashi sosae, lek'o da fuskar shi yay da d'an murmushi yace "Barka dae yan graduation" Haulat ce ta tsaya ita kuwa Fatuu gaba tay abunta itama d'an murmushin tay tace mashi yauwa yace "I just passed sai na gan ku shine nace bari mu gaisa" tana murmushi tace sun gode d'an juya kanshi yay ya kalli Fatuu da tay gaba yace "ita friend en naki bata gaisawa da wanda bata sani bane" juyawa tay itama ta kalli Fatuu dake ta tafiyarta kafin ta maido idon kanshi tace "kusan hakane kasan ba kowa ake yadda dashi ba yanzu" yar dariya yay yace "hakane nima bai kamata in tare ku a bakin titi ba, in ba damuwa ki bani no d'in ita friend d'in taki sai in zo gida mu gaisa da ita" d'an jimm Haulat tay sai kuma ta juya ta k'ara kallon Fatun tunani ta shiga yi tasan ko ta bashi no d'in Fatuu aikin banza ne don ko ya kira ma ba saurararshi zatai ba don sam ta haramtawa kanta yin saurayi, dubara ce ta fad'o mata ta juya tace mashi "kayi hakuri ko na baka no d'in ba zatai maka wani amfani ba don ita d'in akwae sa rana a kanta dama da mun gama Makaranta za'ai bakin ta kuma gashi mun gama d'in to ba lalle ta saurare ka ba" d'an buda ido yay sai kuma yayi murmushi yace "Ok bansani ba ne amman ba wani abu Nagode sosae" tana murmushi tace to har zata juya yace su zo ya kai su subar tafiya cikin rana, juyawa tay da niyyar yi ma Fatun Magana kawai sai ta ga har ta tsaida masu Keke Napep kallon shi tay tace yayi hakuri ta riga ta tsaida masu abun hawa yace to ba matsala tace mata yana mata fatan Alkhairi Haulat d'in ta amsa da to daga haka glass din ya d'aga ita kuma ta tafi, lokacin da ta k'arasa Fatun har ta shige cikin Napep d'in itama sai ta shiga dama ita suke jira mai Napep d'in ya tambayi inda zai kaisu Haulat tace mashi Barhim sabuwar Abuja ya ja suka tafi, kallon Fatuu tay da yake mai Napep d'in ya kunna Wak'a tasan ba jin su zai ba tace "Wannan Mutumin fa don ke ya tsaya har cewa yay na bashi no d'in wayar ki sai ya kira tunda baki tsaya ba amman nasan ba lalle ki saurare shi ba shiyasa nay mashi k'aryar an kusa bikin ki" d'an ta6e baki Fatun tay tace "gwara da kika ce mashi hakan ya kama gabanshi don kuwa ba sauraran nashi zan yi ba" idon Haulat a kanta ta d'an girgiza kai tace "Wai Fatuu miyasa kike korar samari ne, da wuya mu fito ba'a samu wanda ya nuna yana son ki ba Amman sam kin k'i ki fara saurarar kowa komi kice karatu to karatu yana hana ayi saurayi ne ko kuwa zaki ta karatun ne ba ranar da zaki aure??" wani kallon gefe tay ma Haulat d'in ba tare da ta ce mata komae ba Haulat taci gaba "nasan duk Saboda Ya Haisam ne baki saurarar kowa ba wani abu ba, zuwa yanzu yakamata ki cire son shi kwata kwata a ranki kema ki tsaya ki samu wanda zaki rayu tare dashi kada kita korar Mutanen kirki ba tare da kin sani ba, ki yi hakuri in na 6ata maki rai amman gaskiya nike fad'i maki kaman yadda ya samu abokiyar rayuwa wadda yanzu na tabbatar bata rasa juna biyu kema ki fara tunanin sama ma kan ki wanda zaku rayu tare ki hak'ura da ya Haisam don matuk'ar yana ranki to fa bazaki ma kanki abunda ya dace ba shawara ce nake baki a matsayina na mai son cigaban rayuwarki" a hankali tace mata ta gode kawae don kuwa son Ya Haisam na nan a cikin ranta ta rasa ta yadda zata cire shi, suna haka wak'ar da mai Keke Napep d'in ya kunna ta k'are wata ta shiga ta Labarina baitikan wak'ar suka fara kaman haka
🎶🎶Dawo bamu gama zama ba, dama ba mu raba jini ba, wai nikam mai naiwa kauna bata mi ni wuri ba labari da kai ne dawo bamu gama zama_🎶🎶
_🎶🎶Ban gani duhu haka na kwana, yanzu ma hakan na ishi rana, damuwa ta damu da gani na gashi ta raba ni da wani na, mi nai wa kauna ne guna bata iya zama ba, yafe man in na mutu so ne bai gama salo ba...🎶🎶_