Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 29
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 29: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 29. "To ya kukai da shi ne?" Gwaggo ta tambaya shiru…
4,052 words
"To ya kukai da shi ne?" Gwaggo ta tambaya shiru ya d'an yi yana motsa baki kafin cikin rawar murya yace "ran shi ne ya 6aci yace wai ai ba wani abu bane ita tamkar Matar shi ce tunda ya biya sadaki, yanzu haka yau zuwa gobe ya bani in je in dawo da ita in ba haka ba ko bata nan za'a d'aura Auran wai sai mijin nata yaje ya d'aukko ta k'arshe ma cewa yay mu muka k'ulla komae muka sa ta gudu duk yabi mutan gidan ya fad'a masu mun sata ta gudu" wani murmushin takaici gwaggo tay ta maida idonta kan Abbas da shi ma 6acin rai ke kwance akan fuskar ta shi tace "d'ana Abbas kaji wani son zuciya ko" jinjina mata kai yay kawae gwaggon tace "to sam bazan yarda a lalata ma yarinya rayuwa ba wllh tunda shi kan shi kawae ya sani..." Maida idonta kan Baffan tay ta tambaye shi ance yaron a Jimeta yake ko yace mata eh yaron chairman ne ta kalli Abbas tace ya ci Abinci in sun huta sai suje Jimetan farko cewa yay ya k'oshi Baffan Fatuu yace don Allah ya ci sun kwaso hanya kuma yace bazai ci Abinci ba sai a lokacin gwaggo ta gabatar masu da Abbas a matsayin abokin Haisam duk sukai mashi godiya suka ce Allah ya bar zumunci, ba laifi ya ci Abincin ba kamar da yake yadikko akwae tsafta d'akin tass yake suma tsab da su bayan ya gama ne Baffan yace su je d'akin shi sai ya huta yace to suna fitowa daga falon idon Abbas ya sauka akan Mino dake zaune da k'annanta a gefe don yadikko ta hana su shiga murmushi yay ganin sak fuskar Mom Zarah ya kirata ta mik'e taje gaban shi itama tana mashi murmushi ganin yana yi mata, dafa Shoulder d'in ta yay yace ya sunanta tace mashi Ameenatu amman Mino ake ce mata ya tambayeta tana zuwa makaranta tace mashi Eh aji ukku ma take, sake tambayar ta yay yaushe itama zata zo Katsina still murmushin take tace ai tana son zuwa su Baffane suka hana wai tunda Adda Fatuu na can jinjina kai kawae yay daga haka ya wuce Baffa dake tsaye gefe yana masu d'an murmushi yay gaba suka nufi d'akin nashi, bayan tafiyar Abbas gwaggo ma cikin k'uryar d'akin ta shiga ta shiga band'aki ta watso ruwa tazo ta kwanta don ta rage gajiya saidae tunane tunane sun hanata ta hutan don in dae ba fasa auren nan akai ba to fa bazata samu kwanciyar hankali ba gashi bata san ya zasu kwashe da iyayen yaron ba. Sai da akai la'asar wurin k'arfe biyar suka shirya tafiya Jimeta lokacin da ta fito ne ta shiga gaida Yaya duk aka bita da ido yayar ta nuna mata abun zama ta zauna suka gaisa da ita da sauran Mutanan da ta taras a d'akin Yaya ta kya6e baki tace ma gwaggon ashe sai suka sa Amarya ta gudu, yar guntun murmushi kawai gwaggon tayi Yayar tace "to dae ko bata nan sai an d'aura Auren ta gama guje gujenta ta dawo" still gwaggo bata ce mata komae ba don bata son Maganar tay tsawo k'arshe ma sai ta mik'e tay masu sallama ta nufi hanyar fita sauran Mutanan duk suka ta6e baki suka bita da d'an iskan kallo bayan ta fita aka dasa tsegumi har suna cewa a Wurin gwaggon idanun Fatuu suka k'arasa k'ek'ashewa, tana fitowa waje tay ba tare da ta tsaya gaisawa da Ard'o ba don tasan shima surutan zai mata cikin sa'a kuma bai fito waje ba ta nufi Mota da tuni Abbas ya shige dasu Amadu da Kamalu da zai nuna masu hanya Baffan Fatuu dake tsaye yay masu Allah ya kiyaye yasa a dace tace Amin ta shige. Cikin 30 minutes suka isa gidan bayan Abbas yay horn maigadi ya fito suka gaisa ya tambayi daga ina suka ce su baki ne daga rugar Baffa Ard'o yana jin haka yace ko dangin Amaryar Khalid ne banza gwaggo tay sai Kamalu ne yace mashi eh kawae yana washe baki ya juya ya bud'e masu gate d'in suka shiga, har Main falo ya shigar dasu ya fara kwala ma mai aikin Hajiya kira bayan ta fito yace taje ta sanar ma Hajiya ga bak'i anyi dangin Amaryar Khalid ne tace to bayan ta gaishe dasu ta juya, bada jimawa ba sai ga Hajiyar ta Fito tana sanye da doguwar riga jallabiya ta yafa mayafinta ta nufo su fuskarta d'auke da murmushi ta zauna, gaisawa suka shiga yi a mutunce tay masu an zo lafiya gwaggo tace lafiya lau daga baya suka d'an yi shiru can tana murmushi tace "an ce man daga ruga ko?" Gwaggo tace "eh amman ba yan rugar bane daga Katsina muke" Momy tace "Allah sarki yan biki ne kenan, ya hanya an zo lafiya" gwaggo ce ta k'ara amsa mata da lafiya lou lokacin mai aikin ta kawo masu lemu da ruwa ta aje masu ganin basu da niyyar sha Momy na murmushi tace don Allah su sha ruwa lokacin gwaggo tace "dama mun zo wurin mai gidanne in yana nan sai ai mana iso" d'an jimm Momy tay kafin tace "eh yana nan bai dad'e ma da shigowa ba kuwa" gwaggo tace to don Allah a sanar mashi tace to ta mik'e lokacin su Kamalu suka bud'e bottle water d'in da aka kawo suka tsiyaya a cup suna sha ita gwaggo ma bata jin zata iya ko shan ruwan in ba anyita ta k'are ba can sai gata ta dawo bata k'araso cikin parlon ba tace masu bismilla su shigo gwaggo ce ta fara mik'ewa tace ma Amadu yaje ya shigo da Abbas ya amsa da to, parlon chairman ta kai su yana zaune shima jallabiyar ce a jikinshi da murmushi yake kallon su suna shigowa ya nuna masu Sofas alamar su zauna, bayan sun zauna su Abbas suka shigo da sallama ya amsa masu suma ya nuna masu wurin zama duk suka zazzauna, gaisawa suka fara yi cikin girmama juna daga baya shiru ta biyo baya Chairman d'in ne yace yaji ance dangin Amaryar Khalid ne daga Katsina ko gwaggo tace "Eh hakane nice kakarta dake ruk'onta" yana fara'a yace Allah sarki to sun zo lafiya tace lafiya lau Momy ma dake zauna ta k'ara fad'ad'a murmushin ta tace mata sun zo lafiya ta amsa da Alhamdulillah suka k'ara dan yin shiru, again Chairman d'inne yace yaji ance suna son ganin shi Allah yasa lafiya sauke ajiyar zuciya gwaggon tay ta juya ta kalli Amadu tace su jira su a Parlor suka amsa da to had'i da mik'ewa, saida suka fita sannan ta maida kallon ta kan chairman ta fara Magana "Alhaji nasan ba lalle in kun san abun da ke faruwa ba..." da sauri suka had'a ido da Momy kafin ya d'an gyara zama ya tambayeta Mike faruwa ne gwaggo taci gaba "game da auran yaron ku da ita yarinyar waje na, to dae zancen da nike maka ta komo gida tun shekaran jiya tace bata son auren har tayi ikirarin mutuwa zatai in ka d'aura mata aure da shi" waro ido sukae gaba d'aya a rud'e Chairman yace to mi yay zafi haka gwaggo taci ba "koma miya faru Alhaji laifin yaron ku ne shine ya k'ara cusa mata k'iyayyar auren har hakan ta faru sakamakon wasu abubuwa da basu dace ba da ya rink'a yi mata...." Nan gwaggo ta kwashe komae ta fad'a masu a razane su duka suke kallon gwaggo har ta gama kora masu bayani chairman yasa hannu ya kama ha6arshi ya kasa cewa komae ma Saboda Al'ajabi sai faman jinjina kai yake can ya kai hannu gefenshi ya d'auki wayarshi, Khalid ya kira yace komi yake ya bari yazo yanzun nan gida yana son ganin shi daga haka yay cutting kiran, ganin yadda duk fuskokin su suka nuna tsantsar damuwa yasa gwaggo tace masu sai hakuri yara ne ka haife su amman baka haifi halin su ba jinjina kai kawae sukae bada jimawa ba sai ga Khalid d'in don dama yana kan hanya ya kira shi yayi shigar complete black riga mai dogon hannu da ma6allai harda necktie sai bakin wando mahad'in rigar da gani daga wurin aiki yake, da yar sallama ya shigo parlon ya bi bak'in fuskar da ya gani da kallo kafin ya nufi gefen Momy ya zauna suma su Abbas kallon suka bi shi da shi gwaggo a ranta tana raya gashi dai in ka ganshi a ido baka cewa yana da aibu in ma da abunda za'ai mashi sharrin shi to rashin jiki ne, gaida Dad d'in shi yay kaman bazai amsa ba sai kuma k'asa k'asa ya amsa ya kalli Mom d'in shi itama ya gaida ta kafin ya k'ara bin su gwaggo da kallo Chairman ya d'an yi gyaran murya Khalid d'in ya kalle shi yace bai ga Mutane bane sai lokacin ya gaida gwaggo ta amsa mashi tun kafin ya tanka ma Abbas ya d'an d'aga mashi hannu alamar gaisuwa shiru ta sake biyo baya,
"Khalid yaushe rabon ka da wadda zaka aura?" Yaji Dad d'in shi ya jefo mashi tambaya idon shi akan shi yace tun shekaran jiya da ya maidata daga wurin gyaran jiki dad d'in yace shikenan basu k'ara had'uwa ba Khalid yace a'a jiya ya kirata yana son yaje saidae bata yi picking ba sai kuma wani uzurin ya taso mashi bai je ba amman d'azun wurin 12:00 yaje sai brother d'in ta yace bata nan sun fita, shiru dad yay yana d'an jinjina kai idanun shi akan carpet Khalid nata bin shi da ido don ya lura da canzawar da yanayin fuskar shi tay, d'agowa chairman yay a kausashe yace "miya kai ka gidan gona da ita???" Rasss gaban Khalid ya fad'i don tambaya ce da bai tsammaci jin ta ba shiru yay ya rasa amsar da zai bashi don yasan tunda yay mashi tambayar to tabbas yasan yaje da ita gidan gonar, har saida ya sake maimaita mashi sannan cikin trembling voice yace "b...ba komae just na biya ne da ita" Dad yace "ka biya da ita ka ci zarafin ta ko!" da sauri ya girgiza mashi kai yace "No Dad na kaita ta ga gidan ne" d'an murmushin takaici Dad d'in yay gwaggo ma ta kya6e baki Abbas kuwa d'an juyar da kan shi yay gefe wani irin haushi yake bashi, Dad yaci gaba "shi maganin bacci da ka saka mata a drink fa ko shima duk cikin ganin gidan ne?" Wani abu Khalid ya had'iya ya shiga motsa baki saidae ya kasa cewa komae ganin haka yasa Dad buga hannun Sofa ya daka mashi tsawa yace "Am asking my Friend!!!" runtse ido kawae Khalid yay bai taba zaton maganar zata je kunnan wani ba bare yay tunanin iyayen shi zasu sani can ya kalli Dad d'in cike da k'arfin hali yace "Dad ban bata wannan ba" duk kowa kallon shi yake Dad d'in ya yamutsa baki yace Ok bari ya d'aukko mashi Al'qur'ani sai ya rantse mashi, ganin yana kokarin tashi yasa da sauri Khalid d'in ya dakatar da shi ta hanyar fad'in "No Dad ba sai ka d'aukko ba it's true na saka mata saidae bada niyya bane sharrin shaidan ne kuma ban cutar da ita ba" komawa yay ya zauna cike da takaici yace "ka bata maganin bacci ka gane mata jiki har ka ta6ata shine baka cutar da ita ba! Idan aka ma k'anwarka Sadeeya haka zaka ji dad'i???" cije lower lip d'in shi yay remorsefully yace "am so sorry dad wllh sharrin zuciya ne tasa naga ai ni zan Aureta amman nasan nayi kuskure don Allah ka yafe man" banza Dad d'in yay mashi ya juya ya kalli Mom d'in shi da ido tay mashi alamar ya duk'a ya bashi hakuri slowly ya sauka on his knees ya shiga bashi hakuri can ya d'ago idanun shi sun yi ja yace ba shi zai ba hakuri ba ga dangin ta nan su suka cancanci ya ba hakuri don su yay ma laifi har suka tako suka zo garin Saboda hakan, juyawa yay ya kalli Gwaggo ya fara bata hak'uri yana yasan yayi ba daidai ba don Allah su yafe mashi Abbas dae sadda kan shi yay yana jinjina shi gwaggo ma rasa abun cewa tay can taji muryar Dad yana fad'in "Don Allah Hajiya ku yi hakuri kaman yadda kika ce yaro ne ka haife shi baka haifi halin shi ba amman ina mai tabbatar maki zan d'auki kwakkwaran mataki kan abun da ya aikata ai man Alfarmar hakan" yana rufe baki Mom ma ta d'auka ta hau bata Hakuri can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Hakuri ya zama dole Alhaji tunda aikin gama ya riga da ya gama" gaba d'ayansu murmushi suka saki suna mata godiya ta sake cewa "Amman Alhaji nima ina son in rok'e ka wata Alfarmar kuma ina fatan za'a yi man" jinjina kai Dad yay yace in sha Allahu ta fad'i yana ji, gyara zama gwaggo tay taci gaba "Ina son ka dubi girman Allah ka janye batun auren nan....." Zaro ido sukae shi kam Khalid wani kallo ya bita dashi cikin yar in ina Dad yace "a... amma Hajiya yanzun nan kika ce fa kin hak'ura kuma na fad'a maki zan d'auki mataki to miya kawo Maganar a janye batun auren kuma ko baki hakuran bane?" Girgiza kai tay har idanun ta sun ciko da k'walla tace "dalili na na son a fasa auren shine saboda ba auran had'i bane auren dole ne za'a ma ita yarinyar kuma nasan duk kun san illolin da auren dole ke haifarwa ba kamar yanzu da ita yarinyar ta tsani auren har tana ikirarin mutuwa zatayi in aka mata" dakatawa tay tana goge kwallan da suka fara zubo mata gaba d'aya kan su ya gama d'aurewa ganin tana kuka yasa Chairman cewa "Hajiya ai abun duk bai kai na haka ba kuma ni nasan tun tsawon shekaru ukku na nemi auren ita yarinyar don da bakinta ta fad'a man lokacin tana aji ukku na matuk'ar yabawa da komae nata shiyasa nayi sha'awar ta shigo Family na saidae a lokacin tayi k'arama kuma sai ya kasance shima yaron nawa lokacin yana k'asar waje bai ida gama karatun shi ba shiyasa sai nace a bari ta k'arasa Secondary d'inta ala bashshi in sukae Auren sai taci gaba aka kuma amince man" yana rufe baki gwaggo ta d'auka "to mudai bamu san da Maganar an bada itan ba sai sati biyu zuwa ukku da suka wuce kawae aka kira mu wai za'a zo d'aukar yarinya an bayar da ita, wllh Alhaji bazan 6oye maka ba rabon da in shiga tashin hankali irin na jin wannan batun tun rasa Mahaifiyarta da nai bawai ina k'in ai mata aure bane saidae abu ne da ban ta6a zato ba don nayi tsammanin an bani ita kuma ko za'a raba ni da ita bai kamata a nuna man fin k'arfi ba, ban ta6a samun sa6anin da har nay fushi da ita ba sai akan auren nan, na zubar da kwalla har bansan adadin ta ba ba kuma don komai ba sai Saboda amincewa da tayi wanda ita kanta don bata da yadda zatayi ne Mahaifinta ya kira yana kuka ya sanar mata cewa shima bai son a mata auren amman mahaifin shi Ard'o yace in har bai amince ba zai yafe shi ne kuma dole ya bar mashi gida........." Nan gwaggo ta kwashe duk yadda akai har Fatuu ta taho don amata auren da niyyarta na k'in zuwa biki Saboda bacin ran da take ciki har halin ciwon da take ciki, lokacin da ta gama rufe fuskarta tay tana ta kuka, sam Chairman bai ji dad'in jin abubuwan da suka faru ba don shi ya d'auka tuni sun san da Maganar, sai lokacin Abbas ya fara Magana cikin natsuwa da nuna shi mai ilimi ne ya shiga kwatanta ma Alhajin illar da yin auren zai iya haifarwa tunda har yarinyar ta gudu yanzu to in aka matsa mata za'a iya ganin ba daidai ba don yanzu kwata kwata abun ya fitar mata a rai a k'arshe ya tabbatar ma da Chairman d'in tana da wanda take so kuma shima yana sonta bai k'asar don haka shi abunda yake gani a k'yale ta ta auri wanda take so kawae kar a mata dole don ko addininmu ba'a ce ai ma yarinya dole ba a aure, shiru Chairman yay hannunshi ruk'e da ha6arshi har Abbas ya gama cike da gamsuwa ya shiga jinjina kai kafin ya fara Magana "Duk na fahimci bayanan ku kuma har ga Allah ni dama ba wai son zuciya ne yasa zan had'a auren su ba kawae don yarinyar ta kwanta man ne kuma wllh da ina da wani yaron ba Khalid ba to da shi zan nema ma auren ta, amman yanzu daga abunda ya aikata mata na fahimci sam basu dace da juna ba sannan Hajiya ki sani duk abunda bazan so ya faru da yata ba to bazan so ya faru da yar wani ba tunda d'a ai na kowa ne kuma ta cika yar halak da har ta sadaukar da farin cikinta don mahaifinta ta k'ara burge ni sosae ta cancanci itama a faranta mata Saboda haka zan maki Alfarma kamar yadda kika buk'ata matuk'ar hakan zai saka ki farinciki, Hajiya a yanzu na Janye maganar auren su a barta ta auri wanda take so Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi" ido waje Khalid ke kallon mahaifin nashi har ya rufe baki ita kuwa Hajiya Rabi'atu girgiza kai kawai take sam bata so hakan ya faru ba don tasan wata matsalar ce zata kunno kai tsakanin Khalid da Mahaifin na shi saidae har cikin ranta Gwaggon da Fatuu sun bata tausayi.................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
*ASM Bk2034*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*Wannan page kyauta ne a gareki Mommy Kubra ki yadda kika ga dama dashi🤩 Allah ubangiji ya bar mana zumunci Amin🤝😍*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
..........cike da farinciki gwaggo ta hau yi mashi godiya had'i da Addu'oi yana jinjina mata kai yana fad'in ba komae haka ma Abbas godiyar yay mashi daga baya gwaggo tace kar dai ya gaji don Allah tana k'ara neman Alfarmar yaje suyi Magana da Ard'o yace ba komae yanzu dae yamma tayi amman zuwa da safe yana nan zuwa karta damu duk abunda ya kamata za'a yi sosae suka k'ara yi mashi godiya suka Mik'e zasu tafi Mom ma ta mik'e jikinta duk ya mutu a sanyaye tace su bari su ci Abinci mana Gwaggo tace sun gode wllh saida suka ci Abinci suka taho, ita ta rakosu bayan fitar su Khalid ma ya mik'e zai tafi Dad ya ce bai sallame shi ba ya koma ya zauna, bayan tafiyarsu d'aki Momy ta koma duk ta rasa mi ke mata dad'i ta d'auki wayarta ta kira su Sadeeya suna can suna shirin Bridal shower da zasu yi gobe ta sanar mata da su dakata da komai su dawo gida matsa mata tay da tambayar abunda ya faru nan ta kwashe komae ta fad'i mata ba k'aramin tashi hankalin Sadeeya yay ba Mom na jiyo yadda take ta sakin salati. Tsitt kake ji sai Ac da tv dake ta aiki Chairman nata d'an jinjina kai da k'afa Khalid kuma ya sadda kan shi k'asa sai da aka d'an d'auki lokaci sannan Dad yay ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ya fara fad'in "Ka kyauta mun Khalid ka nuna man irin muhimmancin da nike dashi a wurin ka....,amman ka sani ba ni kai mawa ba kan ka kai mawa, kanka ka zubar ma da k'ima da daraja koda yake dama baka da su don duk mai su bazai rungumi sa6on Allah ba....." Dakatawa yay har saida Khalid d'in ya d'an d'ago ya kalle shi kafin yaci gaba "Allah ne shaida ta na fita hakkin ka a matsayi na na uba duk wani hakki na sauke kuma nasan ban yi maka tarbiyar da zata sa ka rink'a sa6a ma Allah ba hasali ma har Al'qur'ani ka sauke ba sau d'aya ba sannan kuma ka haddace wasu bangarori nashi masu yawa amman duk da haka ka za6i take sanin da ke gare ka kake aikata manyan laifukan da Allah ne shaida ta ban aikata su balle in ce abun da nike yi ne nima ake man...." Kwalla ne suka ciko idanun shi ya sa hannu yana gogewa sosae hankalin Khalid ya tashi sai zare ido yake kallonshi Dad yay yace "Khalid ka rasa abun da zaka rink'a aikatawa sai Zina!! duk da ka sani ka karanta kasan illolinta k'asan hukuncin mai aikata ta, mina rage ka dashi ne a rayuwar nan? Duk wata ni'ima Allah ubangiji yayi maka ita ya baka lafiya ya wadata ka ta yadda idan mata hud'u kake so ka aura a rana guda zaka iya amman shine ka za6i sa6a ma wanda yay maka wannan baiwar, Ya Allah! d'ana na ciki na shi ke neman mata shi ke shaye shaye....." Muryar shi ce ta karye ya fashe da kuka a gigice Khalid ya saukko ya durk'ushe a gaban shi ya fara fad'in "billahi Dad kaji na rantse maka na daina tun last Maganar da mukae da kai akan yarinyar nan Danejo ban k'ara aikata hakan da kowa ba, Yes nasan in na 6oye maka bazan 6oye ma Mahallici na ba ina ta6a mata kuma nasan hakan baida kyau kawae son zuciya ne amman nayi maka alk'awarin na daina daga yau Dad kuma ko shaye shaye da kace shima nasan ina yi amman wllh na rage kaji na rantse, don Allah Dad ka daina man kuka kar abun ya k'ara man yawa" dakatawa yay yana goge k'wallan dake zubo mashi duk wannan abun akan idon Mom da tun d'azun ta shigo tana tsaye gefe itama kukan take jin sheshshekar ta yasa Khalid juyowa ya hau rokonta kan ta taya shi rok'on Dad kar ya k'ara yin fushi da shi girgiza kai kawae take dama dalilin auren Fatuu suka k'ulla yarjejeniya har ya amince yasa suka shirya da Mahaifin nashi yanzu kuma ga wannan, matsawa Mom tay itama ta duk'a suka taru suna ta bashi hak'uri, sosae fasa Auren ya ta6a mashi zuciya don yarinyar ta shiga ran shi kuma yana tunanin ta silar ta Khalid d'in zai natsu to amman duk da da laifin Khalid d'in yasan haka Allah ya k'addara yarinyar ba Matar shi bace, can ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya d'ago ya kalle su d'an murmushin takaici yay yace ma Khalid "Ka tashi kaje komi kai don kan ka kuma kowa yay da kyau zaiga da kyau sannan ka sani kayi ma kanka don ban tunanin zaka k'ara samun nagartacciyar Matar aure kaman Yarinyar nan kuma ba baki nay maka ba wllh I assure u sai kayi da na sani u should mark my words" daga haka ya mik'e yay hanyar Bedroom d'in shi ya shige, yana shigewa Mom ma ta mik'e ta bi bayan shi idon Khalid a kan ta, ya rage saura shi kadae tunanin rayuwarshi ya shiga yi tabbas yasan bai kyauta ma kan shi ba abubuwan da yake yi daga zuwa karatu ya biye ma gur6atattun abokai ya canza daga halayar shi mai kyau zuwa maras kyau tabbas yasan ya cuci kan shi, a hankali tunanin shi ya gangaro kan Maganar Dad d'in shi ta k'arshe da ya ce sai yay dana sanin rashin Auren Fatuu ko bai fad'a mashi ba shi yasan yayi asarar mace har mace yarinya ce mai tarin baiwa lokaci guda suffarta ta fara mashi gizo ya dingi tariyo lukkuttan da suka kasance a tare yanzu shikenan ya rasata! Wani Sarawa kan shi yay mashi da k'yar ya yunk'ura ya mik'e hannunshi guda dafe da gaban kan shi ya nufi hanyar fita daga parlon, Uhmmmm dama ance rashin hakuri na rana guda kan iya ja ma mutum dana sani na har Abada Bature kuma yace Once Opportunity lost would never be regain, Allah ya kiyashe mu aikin dana sani ya k'ara shirya mu ya shirya mana zuri'a Amin ya hayyu ya kayyum.