Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 45
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 45: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 45. tun bayan da ta koma sai ciwon ya k'ara dawowa…
5,011 words
tun bayan da ta koma sai ciwon ya k'ara dawowa sosae ga yawan amai da take yi kusan kullum sai tayi amai a class wani lokaci in Malam na ciki ko kuma da break haka a Hostel ma in ya taso mata ta window take zura kanta tai tayi ga magani tana ta sha amman abun yak'i lafawa har fuskarta ta d'an rame tayi wani fayau da ita ranar laraba Fauzy tace mata kodae ta rakata gida amman sai tace tunda har anzo ranar ta bari Friday ta je tace to kodae ta saka mata drip ko taji k'arfin jikinta Fatun tace eh, da kanta ta fita taje ta siyo drip d'in bayan ta dawo ta saka mata shi lokacin daya k'are sosae ta samu k'arfin jikinta washe gari Alhamis taje class lpy lou har aka tashi, da yamma Fauzy taje siyo abu a shop bayan ta dawo ta nufo Hostel hannunta ruk'e da leda taji ana k'wala mata kira ta bayanta ta tsaya da ta juya sai taga wata yar class d'in su ce mai suna Zainab Muhammadu wadda ake ce ma suda (sarkin labari) tana ta sauri ta k'araso ta tsaya gaban Fauzy tace "dama tambayar ki nike son yi ya jikin Fatima Ard'o?" Wani kallo Fauzy tay mata tace bata ganta bane yau a class da sauri tace ta ganta taga ma duk ta rame Fauzy tace eh ai ciwo take ko daga haka ta fara kokarin wucewa Zainab d'in tace "wai kinsan abunda ake fad'a kuwa game da ciwon da take?" Cakk Fauzy ta tsaya tana kallonta tace mi ake fad'an yar in ina ta fara tace "j....ji nayi ana cewa wai kamar ciki ne da ita don ciwon da take yayi kama da laulayin ciki" rassss gaban Fauzy ya fad'i ta zaro ido waje gaba d'aya hannunta guda dafe da bakinta can ta cire cikin bacin rai tace "uban wa yace ciki gareta dama mara aure na samun ciki ne ko kuwa ana sha a ruwa ne ban sani ba???" Yarfa hannu Zainab d'in tay tace "nima fa bani nace ba abunda aketa fad'a ne nagaya maki don ku sani" daga haka ta wuce tay tafiyarta Fauzy tabi bayanta da kallo fuska a matuk'ar d'aure can ta wuce fuuu itama ta shige cikin hostel d'in idonta har rufewa yake Saboda tsabar bacin rai da bibbiyu ta rink'a hawa staircases d'in ta nufi d'akin su, lokacin data shiga Fatuu na kwance saman gado tana jiranta ta kawo mata Fanta gado ta nufa ta aje ledar hannunta gefe ta zauna fuska a d'aure ta kumbura baki ganin yanayinta yasa Fatuu yunk'urawa ta tashi zaune ta fara tambayarta lafiya bin ta da ido kawae tay kaman bazata tanka ba can cikin bacin rai tace "wllh magulmaci bai ji dad'i ba yaji haushin asara!!" A d'an rud'e Fatuu ta hau cewa ta fad'i mata gulamar mi akayi don Allah tace "wai shikenan mutum bazai yi ciwon Allah da Annabi ba sai an ja mashi sharri yanzun nan da zan shigo wai Zainab Muhammadu ta tsaida ni take fad'a man maganar da ake tayi game da ciwon ki.." a rud'e Fatuu tace mi ciwon nata yayi kaman bazata fad'i mata ba ganin yadda take mata Magiya yasa tace "ke wai ciwon da kike wai kaman ciki gare ki don ciwon yayi kama da laulayi Kiji jan sharri don Allah kawae don aja maki, ta ina zaki samu ciki tunda ba aure gare ki ba!!" Zaro ido waje Fatuu tay tasa hannu guda ta dafe kirjinta a kidi'me ta maimaita "ciki kuma!" Wani uban tsoki Fauzy taja jikin Fatuu har ya fara rawa kaman zata yi kuka tace "ni a ina zan samu ciki bacin kowa yasan ba aure gare ni ba!" Wani tsokin Fauzy taja tace "dalla rabu dasu magulmantan banza kawae an fad'a ne tunda kika ji Zainab Muhammadu ta fad'a don in dae tace abu to tabbas an yi ne ki k'yale su ta Allah ba tasu ba duk mai neman ki da sharri saidae ya koma mashi wllh" tana k'arasa Maganar ta fiddo mata Fanta d'in ta mik'a mata hannun Fatuu sai rawa yake ta amsa sai ta aje ta a gefenta kawae tsananin tsoro da fargaba ne suka kamata jin abunda zuciyarta ke ayyana mata na kada ace daga abunda Ya Haisam yayi mata ta samu ciki sosae kirjinta ke bugawa tunanin yaushe yakamata tayi period ta shiga yi a lissafin ta gobe Juma'a wata guda kenan da abun ya faru kuma tayi wanka da kwana d'aya hakan ta faru kenan yanzu kusan kwananta talatin da yin wanccan tasan kuma bayan kwana ishirin da d'aya wato sati ukku koda biyu take yin sabon period yanzu kenan lokacin ya wuce kuma ko alamun zata yi bata fara ji ba wani abu ta had'iya Kutt lokaci guda zufa ta fara tsattsafo mata ta koma tamkar an dasa ta a wurin ko kwakkwaran motsi ta kasa yi kallonta Fauzy tay ganin halin da take ciki da alama ta rude yasa tace mata wllh kada ta sake ta wani damu da zancen munafurcin su tunda ita dae ai tasan ba shi gare ta ba ko, zuru da ido kawae tay ma Fauzy k'arshe Fanta d'in ma kasa sha tay don ko kallonta ma bata k'ara yi ba Fauzy ta hau lallashin ta tana don Allah ta d'auka tasha kada ta tada hankalin ta a banza ita data san haka zata shiga damuwa da bata fad'a mata bama, a wannan daren yadda Fatuu taga rana haka ta ganshi sam bacci ya k'aurace ma idanunta sai juyi take tana zullumin kada ace da gaske ciki ne da ita don duk alamu sun nuna kaman laulayi take yin da gaske yin wannan tunanin har saida tasa hannu ta rufe bakinta, akan kunnanta aka kira sallar Asuba da k'yar ta iya yin salla tana gamawa ko Addu'a kasa yi tay ta koma gado ta kudundune lokacin da gari ya waye Fauzy ta d'an bubbuga ta tace ta tashi ta shirya kada su makara tana a kudundunen tace mata ta shirya ta tafi ita bazata je ba jin hakan yasa Fauzy zama a gefen gadon da take tace "kamar ya bazaki class ba kuma, ko don Maganar jiya to ke miye abun wai damuwa har haka ne tunda kin san kina da gaskiya ki tashi kawae ki shirya mu tafi in mutum ya isa ya tunkare mu yayi mana Maganar mu mana" duk yadda tayi da ita ta kafe kan bazata je class ba har ran Fauzyn ya 6aci tace "to ko dae Zarah da gaske cikin ne da ke???" shiru Fatun tay bata bud'e fuskarta ba kirjinta na wani irin bugu can Fauzy ta kai hannu ta yakice bargon data lullu6a Fatun ta kalleta da sauri suka zuba ma juna ido baiwar Allah duk ta firgice sai numfashi take da k'arfi wani irin kallon tuhuma Fauzy ta fara yi mata ganin haka yasa Fatun sunkuyar da kai cikin d'aurewar kai Fauzy tace "Zarah na tambaye ki baki ban amsa ba ki fad'a man gaskiya ko dae Maganar da ake gaskiya ce??" Girgiza kai ta fara yi da k'yar ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da Kwalla tace "Fauzy ya zaki fad'i hakan kema bacin kin fi kowa sanin wacece ni kuma kin san ba aure ke gare ni ba" sauke Ajiyar zuciya tay tace "to don mi zaki k'i zuwa class??" Cikin rawar murya tace "h.... hakanan kawae, hankali na ya tashi sosae da jin Maganar ban so inje class haka su k'ara tabbatar da Maganar su gara in tafi gida kawae in fad'i ma gwaggo halin ciwon da nike ciki a nema man maganin hausa" da k'yar ta kai Maganar, shiru Fauzy tay tana nazarin Maganar can tace mata shikenan ta fahimta amman ta bari a tashi sai ta rakata gidan tace mata to kawai, saida ta matsa mata sosae sannan ta d'an sha ruwan tea da yar wainar kwae, tun bayan da Fauzy ta shirya ta tafi class take ta faman kai da kawowa a cikin d'akin gaba d'aya ta gama firgicewa kanta ko kallabi babu ta rasa tunanin da zata yi tsoron ta ace da gaske tana da ciki duk in tayi wannan tunanin sai yan hanjinta sun juya can wata Zuciyar ta raya mata taje ta siyo Pt strip ta auna in shine tun wuri ta d'auki matakin daya dace, yin wannan tunanin yasa da sauri ta nufi kayan su ta d'auki hijab ta bud'e jakarta ta d'auki kud'i har zata fita tay tunanin ta saka nikab d'in Fauzy ta tafi dashi ta juya ta d'aukko shi ko sakawa daidai bata yi ba a haka ta tafi.......
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2048*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
...........Tafiya take bata san inda take wurga k'afafunta ba don sam bata cikin hayyacin ta a haka har Allah yasa ta fito cikin Asibitin tasan in taje pharmacy d'in asibitin ba za'a bata ba tunda ba Doctor ya turo ba hakan yasa ta yanke zuwa d'aya daga cikin pharmacies d'in dake wajen Asibitin tana ta tafiya gani take tafiyar ma bata sauri tamkar maidota baya ake hakan yasa ta yanke hawa Napep duk da ba wani nesa bane tama kusa isa, bayan ta tsaida ta fad'i mashi inda zai kaita shima mai Napep d'in har saida ya d'anyi mamaki yace mata nan wajen gate tace eh amman zai jira zata siyo abu ne sai ya maido ta makaranta yace nan school of nursing tace mashi eh yace to ta hau, bayan sun tsaya ta nufi cikin pharmacy d'in gabanta sai fad'uwa yake har ta kusa rubzawa k'atuwar kwalbatin dake wurin batare da ta ankare da slab din ya fashe ba mai Napep d'in ne ya d'an d'aga murya yace tabi a hankali don ya lura duk a firgice take ta d'aga mashi kai kawae, bayan ta shiga ta fad'i abunda za'a bata ba 6ata lokaci aka d'aukko mata ta je wurin biya ta bada d'ari biyar ta juyo saida cashier d'in yace mata canjin ta fa sannan ta juya ya bata ta amsa ta fito bayan ta hau Napep d'in suka komo Asibitin, a bakin gate ya aje ta ta mik'a mashi duka sauran canjin dake hannunta ta juya, ganin a rud'e take yasa yay tunanin ko bata san nawa ta bashi ba ya tsaidata yace kud'in sun yi yawa tazo ta amshi canji hannu kawae ta d'an girgiza mashi alamar ya bassu ta nufi ciki yana ta kallonta gashi dai baisan wacece ba don ta rufe face d'inta amman dae ta bashi tausayi don tabbas da gani akwai abunda ke damunta k'arshe yay mata Addu'a yaja napep din ya tafi, nan da nan ta iso d'akin su ta shige bayan ta cire nik'ab d'in zaune tay a gefen gado tana ta zare ido wani irin tashin hankali take ciki tsoronta ta gwada taga cikin ne can wata Zuciyar ta bata shawarar ta daure ta gwadan in ma shine tunda wuri ba sai taje ta siyo allurar zubda ciki ba tay ma kanta, sosae hakan yay mata ba tare da tayi tunanin wata matsala ba ta mik'e saida ta samu wani d'an murfi sannan ta fita zuwa toilet d'in su bada jimawa ba ta fito ko kallabi babu a kanta haka taje tayo fitsarin, a bakin windown d'akin ta tsaya ta d'aura robar fitsarin ta koma bakin gado ta d'aukko ledar pt d'in ta dawo, tsaye tay cike da fargaba take kallon fitsarin ba don komai sai Allah ya k'addara ba da iya tashin hankalin da take ciki ya isa yasa in ma cikin ne ya zube, can zuciyarta ta raya mata time fa na tafiya gashi yau Friday tayi abunda yakamata da sauri tasa hannu ta cizge ledan hannu na rawa ta fiddo tsinken gwajin ta tsoma shi a cikin fitsarin kaman yadda ake yi bayan ta fiddo ta aje ledar data fiddo shi a ciki ta d'aura tsinken flat hannunta nata k'akkarwa, a hankali ya fara washewa idonta akan shi tun ma kafin ya gama ta fara girgiza kai had'i da gumtse baki a haka har ya gama jajayen layuka biyu suka bayyana daro daro alamar akwae cikin, kwata kwata ta kasa yin kuka sai faman girgiza kai take tana fitar da numfashi da k'arfi da karfi ga jikinta dake ta kerma da k'yar ta kai jikin bango kusa da window d'in ta jingina bayanta sai lokacin kwalla suka fara zubo mata masu d'umi cikin wata irin murya ta fara fad'in "ciki ne da ni! Ciki....Na shiga ukku na lalace na bani! Mi maye ni Fatuu na mutu, Ya Haisam ka cuce ni, kaci amanata na shiga ukkuna in gwaggo taji wannan Maganar nasan mutuwa zatayi wllh..." tana Maganar tana Jujjuya kai, tana cikin wannan halin taji motsin kaman ana tunkaro d'akin bata gama gasgatawa ba taji muryar wata tana fad'in "Fauzy kema kin dawo kenan" Fauzyn ta bata amsa da "Eh wllh Maryam toilet ya koro ni" ta k'arasa Maganar tana dariya jin muryar Fauzy yasa a firgice Fatuu ta kai hannu ta rarumi ledar strip d'in da tsinken gwajin ta nufi gado a sukwane taja bargo ta lullu6e har kan ta, tana gama rufe jikin Fauzy na shigowa ta bita da ido sam bata kawo idonta biyu ba ta duk'a ta d'aukko bucket ta fita don flushing d'in su bai yi saidae mutum ya cika bucket da ruwa ya shek'a, tana jin lokacin data fita amman bata bud'e jikinta ba don tasan da ta ga fuskarta zata zargi wani abu tay lamo tafin hannunta toshe da bakinta, after some minutes saiga Fauzyn ta dawo ta maida bucket d'in k'ark'ashin bed tana kokarin mik'ewa kwatsam idanunta suka sauka akan pt strip d'in dake yashe a k'asa wanda sam Fatuu bata san ya fad'i ba iya ledar ce a hannunta, slowly Fauzy ta kai hannu ta d'aukko shi ganin abunda ke a jikin shi yasa ba shiri ta mik'e idanunta still na akan shi tana kallo da tsananin Al'ajabi had'i da mamaki ta d'an gyad'a kai cikin ranta ta ayyana pt strip kuma a d'akinsu mai nuna akwae ciki to waya kawo shi??? A wani irin slow ta d'ago ta kalli Fatuu dake kudundune lokaci guda kirjinta ya buga jin zuciyarta na raya mata kodae itace tunda ai ba kowa a d'akin sai ita kuma duk sauran students na Class hannu ta kai ta rufe bakinta gabanta na cigaba da fad'uwa can kuma ta cire hannun murya na rawa ta kira sunan Fatun amman bata amsa ba bata kuma nuna idonta biyu ba hakan yasa ta k'ara kiran sunan da k'arfi nan ma still bata amsa ba nan take Fauzy ta shiga girgiza kai cikin murya mai nuni da tashin hankali tace "Zarah I know u'r not asleep idonki biyu to ki tashi don na riga nasan abunda kike 6oyewa gashi ma a hannuna!!" runtse ido Fatuu tay sosae ta kasa gane mi Fauzy ke magana akai tana haka taji Muryata tana fad'in "Ki tashi Zarah ina son sanin wannan abun na waye!" Jin haka yasa a kidi'me ta yaye bargon tana juyowa idanunta suka sauka akan abunda Fauzy ta d'aga tana nuna mata wani abu Fatuu ta had'iye Kutt sai zare idanunta da sukae jawur take yanayin fuskar ta kadae ya tabbatar ma da Fauzy abunda take zargi, ganin irin kallon da take mata ne yasa cikin rawar murya Fatuu tace "m....miye wannan d'in...?" Wani d'an murmushin takaici Fauzy tay kafin tace "abun ki ne da kikai amfani dashi, yanzu ashe da gaske ciki ne da ke Zarah!!" A razane Fatuu ta hau girgiza mata kai tana fad'in ita fa bata san mi take magana ba akai ya za'ai wannan ya zama nata ita da tasan ba aure ne da ita ba, Fauzy tace "Yes Zarah ba aure ne dake ba amman kina da ciki ai ba dole sai ta aure ake samun shi ba ko" Fatuu na jin haka ta saka mata kuka tana fad'in sharri zata ja mata ita data san halinta ko samari bata saurara, duk yadda Fauzy ta so ta fad'a mata gaskiya abun yaci tura k'arshe ma sai cewa tay ta sani ko sharri ake son ja mata tunda dama anata fad'in ciki ne da ita jin wannan Maganar yasa Fauzy ta d'an sauko ta fara tunanin zai iya yuwuwa hakan ne to amman abun da d'aure kai mi ta tsare ma wani da har za'a mata sharri irin wannan ita da take zaune da kowa lafiya sannan kuma ana k'aruwa da ita sosae Saboda k'ok'arin ta, kan Fauzy ya gama d'aurewa ta rasa tunanin da zatai sai kallon Fatuu da ta duk'e kanta tana kuka take can ta juya gefe idanunta suka sauka akan hijab da nikab d'in da Fatuu ta ajiye slowly ta nufe su tasa hannu ta d'aga nikab d'in wanda nata ne kuma a cikin Akwatin kayanta tasan ta ajiye shi to miya fiddo shi? bata kaiga ba kanta amsa ba idanunta suka sake sauka a kan robar fitsarin da Fatuu tay amfani da shi harda sauran fitsarin ganin shi ya tabbatar ma da Fauzy gaskiyar Al'amari cike da tashin hankali ta juyo tana kallon Fatuu yayin da acikin ranta ta furta innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un! Kiran sunan Fatuu tay ta d'ago da jajayen idanunta ta kalleta jiki a mace ta nuna mata robar fitsarin tace itama kawo ta akai? Wani abu Fatuu ta had'iya cikin kuka ta hau rantse rantsen itafa ba ita tay amfani dasu ba k'ilan tana cikin bacci wata ta shigo d'akin don kar a kamata tayi amfani dasu anan still Fauzy tay tana kallonta kawae jin wata magana ta rashin hankali duk wuraren dake da akwae a Hostel d'in sai wata tazo d'akinsu duk da ga Fatun kwance tay hakan, ta lura in ba da gaske tay ma Fatuu ba bazata fad'i mata gaskiya ba duk da ta riga ta gama yarda itace tay amfani dasu kawae tana son taji daga bakinta ne, sauke nannauyar ajiyar zuciya tay tace "Ok fine tunda kince bake kika yi amfani dashi ba kin k'i ki fad'a man gaskiya I know what to do" tana gama Maganar ta juya zata fita da sauri Fatuu ta mik'e ta sha gabanta fuskarta jage jage cikin rawar murya tace mi zatayi d'an murmushi Fauzy tay tace ina ruwanta ta bata hanya, k'in kaucewa Fatun tay duk tay zuru zuru sai motsa baki take ta rasa abunda zata ce ganin haka yasa Fauzy cewa "tunda kina son ki sani to bari in fad'a maki, daga nan in na fita gidan ku zan wuce zan je in kai ma gwaggo wannan pt strip d'in in mata bayanin komae harda ciwon da kike tayi ba tare da saninta ba kin fake da baki son hankalinta ya tashi alhali ba haka bane sai yanzu na gano dalili" tana k'arasawa ta fara kokarin ra6awa ta gefen Fatun ta wuce da sauri ta kamata tana girgiza mata kai cikin kuka tace "Fauzy don't do dis to me na fad'a maki bani nayi amfani dashi ba nan fa Hostel room ne kowa zai iya shigowa kuma ai bani kad'ai ce a d'akin ba ko" ita kanta Fatun bata san mi take fad'a ba, d'an murmushin takaici Fauzy tay tace "Yess Zarah u'r not d only one a cikin d'akin ni dake ne so in kina tunanin ko sharri zan maki duk abun mai sauk'i ne yanzu ki sako Hijab d'in ki mu fara zuwa gidan Aunty Mareeya akai mata pt strip d'in sannan mu wuce gidan ku akai ma gwaggo kin ga duk sai a taru a tuhume mu baki d'aya" zuru Fatuu tay tana ta motsa baki cikin d'aure Fuska Fauzy tace taje ta sako Hijab d'in su tafi mana, yarfa hannu Fatuu ta fara yi ta shiga fad'in ta shiga ukku ta lalace karta yi mata haka don Allah ganin zata 6ata mata lokaci yasa Fauzy tureta gefe ta wuce har ta kai kopa taji muryar Fatun tace "ki dawo zan fad'a maki gaskiya to" cakk Fauzy ta tsaya ta runtse ido wani irin tashi hankalinta ya k'ara yi jiki a mace ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye bayanta tana ta kuka cike da Al'ajabi tace "so it's true Zarah u'r pregnant?" Jinjina mata kai tay alamar eh wani irin jiri ne ya kwashi Fauzy da sauri ta dafe kanta tana salati kafin da k'yar ta nufi gadonta ta zaune idonta akan Fatuu dake tsaye can itama ta lalla6a ta koma gefen nata gadon ta zauna suna facing juna, sun d'an d'auki lokaci a haka kwata kwata Fauzy ta kasa magana Saboda tsabar rud'ewa baki bud'e take kallon Fatuu abun ya matuk'ar tada mata hankali wai Zarah data sani bata ko kula samari bare ayi zancen soyayya ko aure itace da ciki, how on earth?" Fatuu dae sai kuka take ta sadda kai can Fauzy ta sauke ajiyar zuciya rai a 6ace ta kira sunan Fatun ta d'ago ta kalleta a kausashe tace "am highly disappointed in you Zarah, ina hankalin ki da na sani ina tunanin ki ya tafi, duk irin kamun kan ki da na sani har kika iya ba wani dama ya ku sance ki ba tare da kinyi tunanin girman zunubin hakan ba, to ko dama kina aikatawa mu kika lullu6e...." Da sauri Fatuu tace "Don girman Allah Fauzy ki daina fad'in hakan wallahi tallahi billahillazi ba hali na bane yadda kika d'auke ni haka nike, Fauzy k'addara ce ta fad'a man nima ba da son rai na ba hakan ta faru wllh fyad'e aka man" zaro ido Fauzy tay baki bud'e ta maimaita fyade aka mata da sauri Fatuu ta d'aga mata kai alamar eh salati Fauzy ta shiga yi hannunta dafe da goshinta can ta cire tace "amman ke ya akai har kika bari hakan ta faru ina kika je har aka maki hakan kuma waye yay raping en ki??" yarfa hannu Fatuu tay ta langa6ar da kai tace "Don Allah Fauzy kada ki man wannan tambayar nasan kin yarda dani to ki yadda wllh raping ne bada son raina bane" jinjina kai Fauzy tay tace "tabbas na yarda dake Zarah amman taya daga kin fad'i man rape in ki akai sai in kama bacin baki fad'i man yadda akai ba" Magiya Fatuu ta shiga yi mata kan ba sai taji yadda akai ba kawae ta taimaka mata ta san yadda zata rabu da shi amman fir Fauzy ta k'i amincewa tace lallae fa sai ta fad'i mata yadda akai har a kai raping inta in ba haka ba to da son ranta a kai kuma ba makawa sai taje gidan su ta fad'a, kuka wiwi Fatuu ta ke yi hakanan bata son ta fad'i mata wanda yay mata hakan don duk da haushin shi da take ji sai taji bata son Mutuncin shi ya zube a idon mutane gwara ta rufa mashi Asiri, k'arshe da Fauzy taga ta kafe tak'i fad'i sai ran ta ya 6aci sosae ta mik'e Fatuu na ganin haka itama ta mik'e da sauri ta nufeta ta kama hannunta guda tana kuka tana mata Magiya a fusace Fauzy tace "Wllh tllh Zarah ko kukan jini zaki indae baki fad'i man wanda yay maki hakan ba Allah a yau d'innan sai gwaggo tasan halin da ake ciki wato shi baiji komae ba yay maki hakan sai kece zaki kare shi da alama dae magana ta na akan hanya da son ran ki komae ya faru" tana rufe baki ta fara k'ok'arin k'wace hannunta daga ruk'on da Fatun tay mata cikin k'araji Fatuu ta fara fad'in "to don Allah Fauzy ki tsaya zan fad'i maki" bin ta tay da wani kallo kafin tace to ta sakar mata hannu bayan ta saki ta koma gadonta ta zauna itama ta zauna a bakin nata ganin yadda Fauzy ta kafeta da ido yasa ta fara motsa baki tana d'an nishin kuka ta rasa ta ina ma zata fara Fauzy dake kallonta tace "am listening Zarah, tell me who impregnated u??" Ba alamar wasa a fuskarta tay Maganar saida Fatuu ta had'iyi wani wahalallan yawu kafin da k'yar ta bud'e baki tace "zan fad'a maki Fauzy amman don Allah don son Annabi ki man alk'awarin bazaki fad'a ma kowa ba koda gwaggo ce kuma zaki taimaka man" kai Fauzy ta d'aga mata alamar eh hakanan taji gabanta ya fara fad'uwa tun bata ji wanene ba don ta gane Fatun na jin nauyin ta fad'i ko waye, ce mata tay ta fad'i tayi alk'awarin da bakinta Fauzyn ta bud'e baki tace tayi mata alk'awarin hakan suka zuba ma juna ido da k'yar murya na rawa Fatuu tace "Y....YA HAISAM NE!!!" Kaman saukan aradu haka Fauzy taji Maganar gaba d'aya ta zaro ido waje baki bud'e k'irjinta ya fara wani irin bugu k'arshe ta mik'e da sauri ta nufi kopar d'akin ta d'aga labulan ta d'an lek'a wajen ta tabbatar ba kowa sannan ta maido kan ta ciki tasa hannu ta tura kopar cikin tashin Hankali ta dawo ta zauna inda ta tashi a kidi'me tace "Zarah kina da hankali kuwa? have u gone mad! Saboda na matsa maki sai kin fad'a mani wanda yay maki hakan shine zaki raina man hankali don ki kare kan ki, mi Ya Haisam yay maki da ya cancanci wannan bak'in k'azafi daga gare ki???" Jujjuya kai Fatuu ta shiga yi ita dama tasan zai yi wuya duk wanda yaji Maganar nan ya yarda da ita tana sheshsheka tace "Wllh Fauzy da gaske nike shine yay rapi...." Tun kan ta k'arasa Fauzy tay mata yar tsawa tace "Enough Zarah, enough pls wannan Maganar taki ba abu bane da hankali zai d'auka wllh haba how on earth ace mutum kaman ya Haisam wai shine yay raping d'in ki, kawae na gane kina mashi sharri ne don ai saurin barin Maganar amman wllh kin ban mamaki mi ya Haisam yay maki da zaki mashi bak'in k'azafi?" Cikin kuka tace "Fauzy akan wane dalili zan mashi k'azafi miya man tunda nike dashi in ba Alkhairi ba ba abunda yake shiga tsakanin mu sai yanzu da yay man wannan mummunan abun shiyasa tun farko kika ga na kasa fad'i maki wanda yay man d'in Wallahi tallahi kinji na rantse shine kuma in zaki lura ke kan ki rannan ba sai da kika tambaye ni wai lafiya kika ga ban ciki Maganar shi ba yanzu kuma ko waya baki ganin muna yi kaman da har nace maki hankalin shi ne ba kwance ba tunda jinyar mahaifin shi yake to kawae na fad'a maki ne don abar Maganar wllh" da alama mutuwar zaune Fauzy tay ko idonta bai motsi ba k'aramar razana tay da jin zancen ba k'irjinta kai kace ana mata daka a wurin, ba wai bata yarda da zancen Fatun bane kawae ta kasa believing Haisam zai iya aikata wannan d'anyen aikin ga wata ma ba Fatuu ba, ta d'auki lokaci bata ce uffan ba sai da aka d'an jima sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Fatuu tace ta fad'a mata ya akai hakan ta faru nan Fatun ta shiga bata labari tiryan tiryan bata 6oye mata komae ba har yadda ta kasa hanashi da farko da kuma yadda har ya aikata mata hakan tana gamawa ta fashe da matsanancin kuka tana Fad'in ya cuceta ya gama da rayuwarta gashi yanzu yaja mata abun kunya, itama Fauzy kuka ta saka suka taru sukai tayi aka rasa mai rarrashin wani da k'yar Fauzy ta mik'e ya nufi gadon Fatun ta hau ta jawota jikinta ta shiga rarrashinta tana cewa ta daina fad'in abunda take fad'i akan shi daga jin yadda abun ya faru bada niyya bane kawae kaddara ce da sharrin shaid'an jin hakan yasa Fatuu d'agowa cikin kuka tace "duk da hakan harda son zuciya Fauzy dama yanzu na fahimci yana man wasu abubuwa da bai saba ba rannan fa a parlorn shi kama shi nay yana kallon man boobs ena gashi yay ta yawan ta6a ni bai jin komae ranar da zai koma wancan zuwan da yayi harda hugging ena fa yayi kawae na fahimci ya fara sha'awata ne shiyasa ya kasa daurewa duk da magiyar da na rink'a mashi amman saida ya cutar da ni" shiru Fauzy tay kaman tana nazarin wani abu Fatun ta maida kanta jikinta don wani irin Sara mata yake can bayan wani lokaci Fauzy tace "Yanzu miye abun yi don ni wllh kaina ya riga ya k'ulle saboda wannan ba k'aramin Al'amari bane ba kowace zuciya zata iya d'auka ba" da sauri Fatuu ta d'ago ta kama hannuwanta cikin muryar kuka tace "mu zubar da shi kawae Fauzy ba tare da kowa ya ji ba" waro ido Fauzy tay a razane tace "abortion kuma keda kan ki kike fad'ar hakan sai kace baki san tarin illolin shi ba......" Katseta Fatuu tay "Eh nasani Fauzy amman shi kadae ne mafita wllh in ba haka ba ba k'aramar matsala cikin nan zai jawo ba na farko kinga da an sani za'a kore ni daga school d'in nan kuma bazan k'ara samun damar yin karatu anan ba ga suna na da zai 6aci, duk ba ma wannan ba gwaggo nafi ji wllh taji zancen nan zuciyarta na iya bugawa ta mutu kinga Saboda fa wanda za'a aura man d'in nan ba shiryayye bane yana neman mata ta kasa natsuwa har da su ciwo to ina ga yanzu in taji ina d'auke da cikin shege...." tana kai k'arshen Maganar ta fad'a jikin Fauzy tana cigaba da yin kukan, shiru Fauzy tay ita dae har ga Allah tsoron abortion take can tace "ni gaskiya Zarah ban goyon bayan ki abortion Saboda abunda kan iya faruwa duk da ba fata ake ba za'a iya samun matsalar da asirin mu kuma zai zo ya tonu kinga anyi ba ai ba kenan ga laifin kisan kai kuma a wurin Ubangiji gaskiya dae muyi tunanin wata mafitar ba wannan ba",