Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 47
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 47: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 47. Yanata zaune can ya yanke yabi bayanta ya mik'e…
4,340 words
Yanata zaune can ya yanke yabi bayanta ya mik'e da sauri ya nufi cikin Corridor bada Jimawa ba ya fito ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt bayan ya d'auki wayar shi da car key ya fice da sauri, parking space ya nufa ya bud'e Motar da zai hau ya shiga bayan yayi mata key ya fito ya tunkari gate yana sakin horn da k'arfi tuni su Officer suka mik'e aka zuge mashi Gate d'in ya fice ko ta kan d'aga mashi hannun da suke bai bi ba, bayan wanda ya bud'e gate d'in ya rufe ya dawo yace ma abokin aikin ka lura da yadda ya fita kaman akwae abunda ke faruwa yace mashi eh shima ya lura kuma yana tunanin game da yarinyar nan ne da ta zo tunda ya kira yana a tsaidata d'ayan ya d'an jinjina kai yace Allah ya kyauta to ya amsa mashi da Amin, Har ya fito daga Unguwar bai ganta ba dama bai yi tunanin zai gantan ba tunda ance a Napep take tunanin inda yakamata ya nufa ya shiga yi ganin ranar Juma'a ce yasan tana komawa gida Weekend yasa ya yanke zuwa can,
Suna zuwa gab da Asibitin tace ma mai Keke Napep d'in ya d'an tsaya wanccan Pharmacy d'in zata amshi abu yace to ta ciro gyalen jallabiyar ta ta nad'a shi kaman nikab ta yadda ba za'a gane face d'in ta ba bayan ta gama ta bud'e purse ta fiddo yar takardar data rubuta sunan allurar da zata siyan dama tun kafin ta fito ta rubuta ko Fauzy bata sani ba, nufar cikin pharmacy d'in tay mai Keke Napep d'in nata kallonta cikin d'aurewar kai ganin tayi basaja wanda da ba haka take ba, bayan ta shiga ta mik'a ma d'aya daga cikin yan shagon takardar tace ita take so in akwae ya amsa yana dubawa can ya d'ago ya kalleta yace akwae amman basu yi ma Mutane da sauri tace Owk dama ba yi mata za'ai ba ya juya bayan ya d'aukko yace taje ta biya ta nufi cashier d'in ta biya aka bata receipt ta dawo ta amshi allurar ta juya yana ta kallonta har ta fice k'arshe ya d'an girgiza kai kawae, bayan ta koma cikin Napep d'in yaja suka nufi cikin asibitin, a daidai gate d'in School d'in su ya tsaya bayan ta fito ta bud'e purse d'inta ta fiddo 1500 ta mik'a mashi ya amsa ya duba da mamaki ya kalleta ganin kud'in sunyi yawa tun kafin yace wani abu tace yasha lemun da bata d'aukko mashi ba da sauran ta juya ta nufi ciki yana ta washe baki yana mata godiya, tana shigewa tasa hannu ta kwance gyalen ta nufi Hostel. Sosae yay gudu nan da nan ya iso kopar gidan su bayan ya parker ya bud'e ya fito lokacin Amadu na cikin shago yana hango shi da sauri ya bud'e ya fito ya nufo shi suka had'e ya gaishe dashi bayan ya amsa mashi yace "Zaraah na ciki?" d'an shiru Amadu yay alamar tunani can yace "gaskiya kaman bata nan don tunda na dawo daga school ban ganta ba kuma da ina cikin shago ban ga ta zo ba, shiru Haisam d'in yayi Amadu ya lura yanayin shi ya canza hakan yasa yace mashi bari dae yaje ya tambaya ko ta dawo da bai nan ta fita kai kawae Haisam ya d'aga mashi ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, d'akin gwaggo ya nufa lokacin tana kwance kan gado tana bacci tayi wankan juma'a wurin kanta ya tsaya ya fara kiran sunanta a hankali ta ware idonta akan shi tana ganin shi ta yunk'ura ta tashi zaune tace mashi lafiya tambayarta yay Fatuu ta dawo ne tace "a'a lafiya?" Yace "dama Ya Haisam ne yazo yana tambayarta yana waje" tace "ba ta kaiga dawowa ba har yanzu kace mashi tana Makaranta k'ilan zuwa zai ya d'aukko ta" d'an shiru Amadu yay sai kuma yace mata k'ilan to daga haka ya juya yana fad'in bari ya fad'i mashi, bayan ya fito ya sanar dashi har yanzu bata dawo ba kai kawae ya d'aga mashi ya juya ya koma Motar bayan ya juyata ya koma ta hanyar da ya biyo da gudu.
Lokacin da ta shiga d'akin nasu Fauzy na kwance tana bacci ta yi wanka tasa kaya a bakin gadon da take Fatuu ta zauna ji tay kamar karta tasheta ta bari sai ta tashi amman kuma bata iya hakuri don ta k'osa ai komae a gama hannu ta kai ta fara dan bubbuga jikinta a hankali ta fara motsawa kafin ta bud'e idonta tana ganin Fatuu da sauri ta yunk'ura tana murza ido ta jingina da bango cikin muryar wanda ya tashi daga bacci tace "kin dawo Zarah" kai Fatuu ta d'aga mata d'an shiru Fauzy tay tana ta kallonta can tace "kin gan shi?" nan ma kan ta sake daga mata ta k'ara cewa "to ya ku kai dashi?" d'an ta6e baki tay yanayin fuskar ta ya canza cikin bacin rai tace "bai ce komai ba sai faman bi na da ido kawae, ni dama nasan fa ba abunda zai iya cewa shi kanshi daga yanayin fuskar shi na fahimce ya rud'e da jin zancen cikin ba kamar dana nuna mashi pt strip d'in" shiru Fauzy tay saidae a ranta ta matuk'ar yin mamakin jin wai bai ce komae ba can tace "to da ya ji Maganar zaki zubar da shi miya ce??" tace "dana fad'a mashi shima tsaye yay man yana bina da ido har na baro mashi d'akin saida ina kan hanya ne naga ya kira ni ni kuma ban d'aga ba" Fauzy tace "to Saboda mi Zarah ba sai Kiji mi zai ce ba" yamutsa fuska ta fara yi idanunta suka ciko da k'walla cikin rawar murya tace "Fauzy da akwae abunda zai fad'a man tun ina can da ya fad'i man kawai nasan bai wuce yace kar in zubar ba zai handling komae kuma wllh wannan ba yar k'aramar matsala zai jawo ba ni gwaggota nafi ji Fauzy tun ina k'arama take bani labarin wata d'iyar yar wajen aikin su da tay cikin shege a koda yaushe tana man misali da ita in tana gargad'i na koda na fara period saida tay ta gargade ni akan kada na bari wani ko hannuna ya kama in ba haka ba zan samu ciki Fauzy ki taimake ni ko don ita da karatu na da kuma kallon da za'a koma yi man ba kamar dangin mu har ma dashi Ya Haisam d'in gara mu kawo k'arshen komai ba tare da kowa ya sani ba" ta k'arasa hawaye na zuba daga idanunta had'i da kai hannu ta kamo hannun Fauzy shiru tay tana bin ta da ido wani irin fad'uwa gabanta ke yi hakanan ita dae bata son a zubar da cikin ga fargabar mi zai iya zuwa ya dawo magiya Fatuu taci gaba da yi mata can ta ja dogon numfashi cikin karyayyar murya tace "Zarah tsoro nike wllh kada wani abu ya faru sakamakon yin allurar nan kinsan tana da illa fa" da sauri Fatuu tace "in sha Allahu ba abunda zai faru raina na bani hakan kuma nayi maki Alk'awarin koda wani abun ma ya faru bazan mentioning d'in ki ba zan d'aura ma kaina alhakin duk abunda zai faru pls k'awata wadda bata son damuwata ki taimaka man" hannu Fauzy ta kai baki ta d'an cije yatsun ta tana nazari Fatun na cigaba da kallon ta a marairaice can ta cire hannun cikin disashewar murya tace mata ta had'a allurar nan da nan Fatuu tay d'an murmushin farin ciki ta fara kokarin had'a allurar.........
Sosae yake gudu yana driving d'in yana kai hannu bakin shi ya d'an ciza had'i da d'an bugun steering d'in cikin lokaci kankani ya iso bakin gate d'in Makarantar su ya Parker sai lokacin ya fara tunanin yadda za'ai ya samu ganinta in ma tana a cikin school d'in hannu ya kai gefe ya d'auki phone d'in shi ya fara kiranta sai dae har ta katse bata d'aga ba haka saida ya kira sau biyar amman bata d'aga ba cikin tashin hankali ya kai hannu ya d'aki steering d'in da k'arfi ya furta "ZARAH....!!!" shiru yay yana numfashi da sauri da sauri kan shi ya gama k'ullewa bai san taya zai gan ta ba gashi bai san number d'in Fauzy ba balle ya kirata zuciyarshi ce ta raya mashi the more yake 6ata lokaci the more rayuwar ta ke shiga hadari he has to do something quickly hannu ya kai da sauri ya tashi Motar bayan ya juya ta ya jata da gudu ya tafi, yana ta sak'e sak'en abunda yakamata yayi a ranshi k'arshe zuciyar shi ta yanke mashi kawae yaje ya sanar ma Hajiya, bai d'au tsawon lokaci ba duk da da yar tazara ya iso Unguwar taso tun da ya karya kwanar gate ya fara latsa horn wani na bin wani Officer na jin hakan ya tashi da sauri ya zuge mashi Gate d'in ya shige fuuu bai nufi parking space ba ya wuce da Motar har kusa da part d'in Hajiya sannan ya parker ta ya fito ko rufe kopar bai yi ba ya wuce ciki, lokacin da ya shiga Parlon kwalam ba kowa da sauri ya nufi Bedroom d'in Hajiya yana shiga nan ma ya ga ba kowa har toilet ya nufa yay knocking tsit bai ji anyi alamun da mutum ba hakan yasa ya juyo da sauri ya fito Parlor ya nufi hanyar fita har ya kusa kaiwa k'opar fitan yaji motsi a bayan shi ya juya da sauri Amarya Saude ce don an d'aura mata aure da Officer tarewa ce kawai ta rage, daga kopar baya ta shigo hannunta ruk'e da yar roba mai fad'i Haisam na ganinta ya tunkare ta yana tambayarta Hajiya ko amsa gaisuwar da take mashi bai yi ba da hannu tay mashi nuni da inda ta fito tace mashi tana baya wurin su d'awisu ya amsa da Ok ya nufi kopar ita kaita saida tay mamakin ganin yanayin shi, yana fita bayan ya hango ta can a zaune akan kujera a gefen wurin Aku da alama fira suke hannunta d'aya ruk'e da sandar ta ta alfarma da take amfani da ita yanzu wurin yin tafiya, tun kan ya isa Aku yace ma Hajiya wai ga d'an ta nan jin haka yasa ta juya ta kalli Haisam dake tunkaro ta kafin ta juyo tana dariya tace ma Akun bata fad'a mashi jikan ta bane ba d'anta ba Akun ya dae yi shiru tamkar bai fahimci mi take nufi ba lokacin Haisam ya iso ya tsaya gefenta ta d'aga kai ta kalle shi sai yama kasa ko gaida ita sai d'an motsa baki yake lokaci guda ta gane akwai abunda ke damun shi tace mashi miya faru d'an shiru yay har saida ta maimaita sannan yace yana son yin Magana da ita ne tace to ta taso ne ko anan zasu yi yace suje Parlor tace Ok ta fara kokarin mik'ewa Aku na fad'in sai kin dawo Hajiyata tace to ya jirata suka nufi parlon tana gaba Haisam na bin ta a baya, bayan sun iso wurin kujeru akan 3 seater ta zauna shima ya zauna daga can gefenta idanunta akan shi yay shiru yana kallon carpet ganin haka yasa tace mashi shi take sauraro ya akai, shirun dae yaci gaba da yi ya rasa ta ina ma zai fara tunda yake bai ta6a jin fargabar gaya ma wani magana ba irin yau saida Hajiya ta k'ara tambayar shi da d'an k'arfi tace "miye wai ka fad'a in wani abu ya faru kayi man shiru zaka tada man hankali!" Sauke ajiyar zuciya yay ya d'an kalleta idanun shi har sun canza sai kuma ya maida su yana kallon gefe cikin raunanniyar murya ya fara cewa "...I want to tell u dat Zarah is pregnant and a.....am responsible for it" daga haka ya dakata wani kallo Hajiya ke bin shi dashi baki bud'e cikin rashin fahimta tace "Fanan nada ciki shine abun damuwa kai da zaka yi farinciki kiran ka tay ta sanar maka?" Tayi tambayar tana murmushi ya fahimci bata fahimci sunan da ya fad'i ba gashi ta kafe shi da ido alamar tana jiran amsa juyawa yay yayi facing d'in ta sosae cike da k'arfin hali yace "I said Zarah Not Fanan" lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta tsuketa cikin d'aurewar kai tace "Wace zarar?" Jimm yay sosae yake jin fargaba can dae ya dake yace "Zarah our neighbor I impregnated her yanzu haka tana d'auke da ciki na a jikinta" da alama mutuwar zaune Hajiya tay baki bud'e take kallon shi shima kallon nata yake sun dan d'auki lokaci a haka kafin ta kai hannu ta gyara zaman gilashin ta wai taga in shi ne da kyau a rud'e tace "Haisam kana da hankali kuwa kasan mi kake fad'a kuwa dama ashe ciwon da kake ba wani abu bane shaye shaye ka koya wurin turawan shine yanzu ka shawo abunda ya fi k'arfin ka kazo kana man zancen hauka to Allah ubangiji ya tsare mu da irin wannan abun kunyan ka bari muji dana shaye shayen da ka fara, yanzu kai Haisam duk yadda muke d'aukar ka mai hankali kowa na yaba halin ka nagari shine har ka bari turawa sukai galaba a kan ka wannan wane irin abun kunya ne ni Hauwa!" tana k'arasawa ta kai hannu ta ruk'e ha6a tay mashi zugudum tana mashi kallon bak'on mutum ba Haisam ba still yana ta kallon ta yasan dama bazata fahimta ba cikin sauk'i d'an matsawa yay kusa da ita yace "ni fa ba wani abu da nake sha ko kuma na sha yafi k'arfi na what am telling u is true Zarah da kika sani tana da ciki 1 month and nawa ne yanzu taje G.r.a ta sanar mani don nima ban san tana dashi ba...." Nan ya kwashe yadda sukai da Fatuu data same shi yanzu harda K'in d'aukar wayar shi da tayi da neman ta daya zo da kuma makarantar su da ya je duk ya fad'a mata, tana ta kallon shi har ya gama mata bayani tay shiru kawae, zuciyarta ta fara gasgata mata zancen shi Saboda yanayin da ta ga Fatun a d'azun tabbas yanayin ta ya nuna kaman na mai d'auke da yaron ciki iya girgiza Hajiya ta girgiza cikin tsananin tashin hankali murya na rawa tace "K.. kenan kana nufin raping d'in yar mutane kai???" d'an cije lips d'in shi yay ya d'aga mata kai alamar eh ta zabga uban salati tana tafa hannuwa ta shiga fad'in ".....Wannan wace irin musiba ce Haisam ya jawo mana, duk yadda nike Addu'ar Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani ashe kai ne zaka jawo hakan Haisam, miya faru da kai ne ka aikata ma Yarinyar Mutane wannan d'anyen aikin yarinyar da take tamkar k'anwa a gare ka, mika sha ne ka aikata mata hakan, ka fad'a man ko don ance matar ka nada matsala shi ne kai tunanin samun d'a ta wannan hanyar kasan mi ka aikata kuwa???" Sigh yay ya kai hannu ya dafa goshin shi kafin ya cire yace "I ave told you ba wani abu dana sha fa abunda ya faru wasn't intentionally kema kin san bazan aikata hakan da wani niyya ba ko don wai Fanan na da matsala nasan nayi kuskure na biye ma son zuciya wannan dalilin ne ma yasa na kasa natsuwa har na dawo nan ban wuce Us ba" kallon dae kawai take bin shi dashi tsananin tashin hankali yasa ko kuka ta kasa yi ganin shi take a matsayin wanda ba daidai yake ba don kuwa da alama ya manta girman laifin da ya akaita da wadda ya aikata mawa, cigaba yay "Yanzu dae isn't the right time da zamu cigaba da Maganan ya kamata ai stopping nata daga aikata abunda tace zata yi u know abortion nada matsala and nayi k'ok'arin in tsaidata but she refused to pick my calls kuma kinsan tunda karatun ta ne zata iya aikatawa pls do something in ya kama ko gidansu ne muje sai a fad'a ma Grandma d'inta" wannan karon kallon mahaukaci Hajiya ta koma yi mashi mahaukacin ma mai hauka tuburan don Maganar k'arshe da yayi a wurinta ta mara hankali ko miskala zarratin ce kaman yasan mi take ayyanawa yasa shi fad'in "nasan abun nada tashin hankali but bai kai na in aka samu Matsala ba don she may lose her life fa in hakan ya faru kuma ya tashin hankalin zai kasance so is better a sanar mata ta dakatar da ita and I will take responsible of everything" bakin Hajiya dai ya gama mutuwa sai ido kawae can ta yunk'ura ta mik'e shima ya mik'e ta nufi kopar fita daga parlon ganin zata fita haka yasa shi cewa veil d'in ta fa banza tay mashi tana dogara sandar ta har ta fice daga parlon shima haka...........
*ASM Bk2050*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
..........tana fitowa ta nufi hanyar gate shi kuma Haisam ya nufi Motar shi dake a bakin part d'in dama a bud'e ya barta ya shige yay reverse kafin ya juyata ya nufi hanyar gate d'in a daidai saitin Hajiya ya tsaya ya sauke glass yace mata ta shigo, banza tay mashi tana cigaba da dogara sandar ta ganin haka yasa shi bud'e Motar ya fito ya sha gabanta tay mashi wani kallo kafin tace ya jaye ya bata wuri kawae sai ya kama hannunta ya nufi Motar da ita tana ya k'yaleta amman yak'i sakin ta har saida ya bud'e kopar baya ta shiga sannan ya koma gaban ya shige tuni Officer ya zuge mashi gate ya fice yabi Motar da kallo a ran shi yana tunanin ko lafiya, A daidai gaban gidan su ya parker da sauri ya fito ya bud'e ma Hajiya kopar bayan ta zuro sandar ta kafin ta fito ya maida duka kopopin ya rufe suka nufi gidan tana gaba yana biye da ita Amadu dake cikin shago yana ganin su ya bud'e ya fito yazo gaban Hajiya ya gaishe da ita ta amsa mashi kafin ta tambaye shi Dijen na ciki yace eh ta wuce ya k'ara gaishe da Haisam ya jinjina mashi kai kawae, bin su da ido Amadu yay lokaci guda hankalin shi ya tashi don ya fahimci akwae abunda ke faruwa tun ma d'azun da Haisam d'in ya zo neman Fatuu Addu'ar Allah yasa dae lafiya yay kafin jiki a sanyaye ya koma cikin shagon, suna shiga zauren gidan Haisam yaja ya tsaya Hajiya har ta shiga ciki ta juyo ganin bai shigo ba yasa ta tamke fuska tace "Wato ka d'auke ni mutuniyar banza ko ni ce zan shiga in sanar da aika aikar da kayi?" Yana kallonta yace "No just to ask for permission first" wata uwar harara ta zabga mashi tace "kai a tunanin ka yanzu kana da wata kamala ne wanda ya aikata abunda ka aikata ai bai buk'atar a bashi izinin shiga gidan mutane ba kamar Mutanen da ya za6i zubar ma da Mutunci ka shigo muje" wani kallo yake mata ya d'an girgiza kai yay mata alamar suje da hannu ta juya lokacin ta fara yin sallama saida tayi sau biyu sannan gwaggon ta amsa ta lek'o don ganin waye koda ta gansu da sauri ta k'arasa fitowa tana washe baki jikinta sanye da riga umbrella da zani na atamfa ta d'aura kallabi nufo su tay tana masu maraba Hajiya dake bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki yasa nan da nan tausayinta ya mamaye zuciyar ta don ta tabbatar da ta san abun da ke tafe da su to tabbas manta yadda ake dariya ma zata yi balle har tayi, gaida Hajiyar tay ta amsa mata tana kokarin daidaita natsuwar ta ta kalli Haisam still da fara'a tace "d'ana Haisam barka da juma'a ya k'arfin jikin?" Slowly ya amsa mata da Alhamdulillah Hajiya ta kya6e baki tana girgiza kai gwaggon tace su shigo cikin parlor, bayan sun shiga a kan one seater Haisam ya zauna Hajiya ta nufi 3 seater gwaggo kuma ta zauna akan 2 seater ta shiga k'ara gaida Hajiyar tana mata barka da juma'a ta amsa fuska a kwa6e shi kam Haisam tunda ya zauna ya sadda kan shi k'asa, shiru duk suka yi gwaggo sai d'an murmushi take sai dae a cikin ranta ta lura kaman akwae abunda ke faruwa ba kamar Hajiya data gani ba ko mayafi saida aka d'an d'auki lokaci sannan Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Gwaggo ta fara magana "Dije gamu mun zo saidae ba irin zuwan da aka saba bane zuwa ne mara dad'i mun zo maki da Al'amari wanda ban tunanin ya ta6a faruwa a kaf dangin ku...." Dakatawa tay sakamakon kukan da ya taho mata nan fa hankalin gwaggo ya tashi haik'am ba kamar da ta ga Hajiyar na kuka ga Haisam ya sadda kai baida alamar d'agowa bare tasa ran jin bayani daga gare shi a rud'e ta hau ba Hajiya hak'ura tana had'ata da Allah ta daina kuka k'arshe ma sai ta tashi ta koma kusa da ita tasa hannu tana goge mata kwallan tana cigaba da bata hakurin can ta shanye kukan tace "Dije nasan ki ke mace ce mai tsananin k'arfin hali ba k'aramin abu bane ke ta6a maki zuciya don Allah ina rok'on ki da ki k'ara kan wanda ke gare ki don Al'amarin da muka zo da shi zai iya tarwatsa maki zuciya wllh ni kaina da nake maki Maganar nan tuni zuciyar tawa ta tarwatsa Allah ne kawae ke bani iko nake yin komae" tuni jikin gwaggo ya fara rawa duk ta bi ta rud'e a kidi'me ta hau ce ma Hajiyar to tana ji in sha Allahu ba abunda zai faru da ita ta sanar mata abunda ke faruwa cigaba Hajiya tay "Dije kin san duk inda ake zaman lafiya Shaid'an bai da sukuni har sai yaga ya tarwatsa ni dake zumunci ne mai k'arfi a tsakanin mu tsawon lokaci Saboda dage wa da Addu'oi da su Azkhar yasa tsawon lokaci bai yi nasara akan mu ba sai yanzu, dije sai yanzu....." Share k'walla taci gaba da yi hankalin gwaggo in yayi dubu ya gama tashi a lokacin ta rasa ma hasashen da zata yi kan abunda ke faruwa ganin Hajiyan tak'i fad'a mata abunda ke faruwa yasa ta juya kan Haisam tace "d'ana Haisam don Allah ka sanar dani abunda ke faruwa in sha Allahu zan fahimta ai ni musulma ce...." Tun kan ta k'arasa Hajiya ta katse ta da Fad'in "k'yale wannan Dije dashi shaid'an yay amfani yayi galaba yake son ganin ya tarwatsa mana farinciki zan sanar maki abunda ke faruwa amman ina rok'on ki da girman Allah ki fahimce ni" da sauri gwaggo ta hau jinjina mata kai alamar zata fahimtan Hajiya tace mata ina Fateema gwaggon tace mata bata kai ga dawowa ba har yanzu amman dae yau zata dawo Hajiyar tace mata ta kirata a waya yanzu ta ce mata duk abunda take ta bari ta taho gida da sauri baiwar Allah gwaggo ta mik'e ta nufi hanyar fita tana Fad'in bari ta d'aukko wayar to, bada jimawa ba ta dawo hannunta ruk'e da wayar ta fara kiran Fatuu ba tare da ta koma ta zauna ba saidai har ta yanke bata d'aga ba wasa wasa sai da ta kirata sau kusan goma amman ba'a d'aga ba Hajiya dake ta kallonta tace "halan tak'i d'agawa?" Kai gwaggo ta d'aga mata ta girgiza kai tace "dole ta k'i d'agawa don itama tana cikin tashin hankali" a razane gwaggo dake kallon ta tace "kodae wani abu ya faru da Fatun ne ko tayi had'ari ne, don Allah Hajiya ki sanar man!" ganin yadda ta rud'e yasa Hajiyar kwantar da murya ta na kokarin fahimtar da ita ba abunda take tunani bane ya same ta kawai dae akwai dalilin da ya sa ba lalle ta d'aga kiran ba, ta nuna mata lalle dole sai Fatun tazo zata ji abunda ke faruwa gwaggon tace to yanzu ya za'ai gashi ta k'i ta d'aga kiran, tambayar ta Hajiya tay ko tasan d'akin da Fatun take a can Makarantar tace a'a ta dai san Hostel d'in amman bata san d'akin su ba tunda bata ta6a zuwa ba Hajiyar ta sake tambayar ta bata san wata k'awar Fatun ba ta kirata tace ta sani amman bata da lambar wayar ta don duk in zasu gaisa da wayar Fatun suke gaisawa, shiru kowa yayi gwaggo dai na tsaye k'ik'am can Hajiya tace "ina ga tashi zamu yi mu tafi Makarantar tasu kawae alabashshi sai mu nemi d'akin nasu in mun je" shiru gwaggo tay fuskarta duk ta canza an barta a duhu sai faman sak'e sak'e take a ranta can tace ma Hajiyar "ina tunanin Amadu bai rasa lambar k'awar tata bari in mashi magana" da sauri Hajiya tace to taje taji in akwai ta juya har tana yin tuntu6e wurin fita daga parlon Hajiya na ta bi a sannu, bayan fitar ta ta maida idonta akan Haisam da still kan shi na sadde ta hau jefa mashi wani mugun kallo fuska a kwa6e, Saboda tsabar rud'ewa a yadda take ba lullu6i babu itama ta fita har bakin shagon Amadu yana ganinta ya bud'e ya fito ya hau tambayar ta lafiya ba kamar yadda yaga yanayin fuskarta murya na rawa tace "ban san abunda ke faruwa ba Amadu amman dai gaskiya da matsala gashi sun k'i sanar dani abunda ke faruwa wai sai Fatuu ta zo Hajiya harda kuka fa gashi anata kiranta a waya tak'i d'agawa" zaro ido Amadu yay ba kamar daya ji tace Hajiya harda kuka yama rasa mi zai ce Gwaggon ce ta tambaye shi ko yana da lambar Fauziyya da sauri yace "eh akwae Fatuu na kira na da ita" tace to ina wayar ya d'aukko mata ita yace to had'i da juyawa da sauri ya koma cikin shagon without wasting time ya dawo ruk'e da wayar ya fara kokarin kiran Fauzy.........,