Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 49
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 49: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 49. Cikin mintuna talatin ya isa jimetan bayan ya…
3,527 words
Cikin mintuna talatin ya isa jimetan bayan ya shiga gari ya samu wani ya tambaye shi ko akwae wani Hotel mai kyau yace mashi eh yay mashi kwatance, bayan ya isa ya kama d'aki aka bashi makulli ya nufi d'akin wanda d'an madaidaici ne akwae duk abun buk'ata na cikin bedroom da yake Hotel d'in ba wani babba bane, toilet ya fara shiga ya watso ruwa daga baya ya fito daga shi sai singlet da d'an short ya aje kayan daya cire a saman gadon shima ya zauna daga gefe ya kai hannu ya d'aukko wayarshi da ya aje lokacin da ya shigo ya shiga kiran Haisam saidae duk iya kokarin da yayi layin nashi yak'i shiga har mik'ewa yay ya d'an zagaye d'akin ko ya samu kiran ya shiga amman da yay dialing sai ya yanke k'arshe dole ya dawo bakin gadon ya zauna had'i da cillar da wayar asaman gadon ya had'e hannuwan shi ya d'aura ha6ar shi abun duniya duk ya dame shi yama rasa tunanin da zai yi, maida bayan shi yay saman gadon ya kwanta yana kallon ceiling sai sak'e sak'e yake a haka bacci yay awon gaba dashi, ba shi ya farka ba sai bayan Azahar lokacin har angama salla jiki a mace ya mik'e ya nufi toilet saida ya k'ara watsa ruwa ya d'auro Alwala sannan ya fito ya zura wandon shi ya kabbara salla anan cikin d'akin, bayan ya gama ya d'aga hannu yana Addu'a aciki ya rok'i Allah daya kawo masu mafita a Al'amarin nan ya za6a abunda yafi zama Alkhairi, bayan ya gama ya mik'e ya koma kan gadon ya shiga duniyar tunani ga yunwa ya fara ji can yaji wayar shi ta fara ringing ya juya ya kai hannu ya d'aukko ta yana kallon screen d'in yaga sunan da ya saka ma Haisam ya bayyana har bai san lokacin da yay murmushin farinciki ba duk da baida tabbacin za'a samu mafita a wurin shi, bayan ya d'aga suka gaisa yace mashi tun d'azun yake trying kiran shi amman yak'i shiga Haisam d'in ya tambaye shi yadda suka k'are da Mutanen cike da damuwa Abbas yace "Wllh H,Zakee bamuyi nasara ba k'arshe ma abun nema yay ya zama wani issue na daban" cikin cool voice d'in shi ya tambaye shi abunda ya faru nan Abbas ya kwashe komae ya fad'i mashi tun daga kan zuwa gidan Alhaji Lawal har zuwa zaman da akai d'azun a fadar Ard'o yace "Wllh kafaffen tsohon nan ya kafe kan lalle sai dae a d'aura mata auren da wanda nace suna son juna and ni na fad'i hakan thinking that za'a samu mafita ya amince kamar yadda shi Dad d'in yaron ya amince" shiru Haisam yay can yayi sigh yace "So what's d way out now?" Yarfa hannu guda Abbas yay kan lap d'in shi yace "ban sani ba H,Zakee cos am completely confused abunda nasani dae shine muddin ba wanda nace d'in to tabbas wancan guy d'in zasu aura mata wllh don tsohon ya d'auki zafi da yawa nema ma yay ya suk'e mana fa yaja aka mana caa wai in ya mutu mune and yace muddin ba'a d'aura mata da wanda aka ce tana so ba kuma ba'a bari ya aura mata wanda ya batan ba to ya yafe Dad d'inta dole ya bar mashi gida a yau d'in nan sosae ya shiga tashin hankali abun ba dad'i but he's in serious dilemma har ma da ita Zarah wllh, ni tsorona ma aje a aura mata shi ba fata ake ba wani abun mara dad'i yazo ya faru tunda ta nuna bata son shi ta tsane shi so everything can happen" shiru Haisam kaman ba zai ce komae ba saida ya d'an d'auki lokaci har Abbas d'in na fad'in "H,Zakee are u there?" Yay sigh yace mashi "yeah" Abbas d'in yaci gaba da fad'in "da akwae wanda take so sai a aura Matan kawae ba wani abu bane karatu ko a d'akinta ne sai tayi wannan ba wani problem bane har haihuwa in suna so zasu iya dakatar wa har ta gama karatunta to ni ta fad'a man ba wani wanda take so gaskiya Saboda karatu ta saka a gaba" still shirun Haisam yay can Abbas yaji yace "I think u should just marry her Abbas" har saida Abbas ya d'an zaro ido jin Maganar Haisam d'in yay d'an guntun murmushi a ranshi ya ayyana da ace ba wani a zuciyar ta tabbas da zai yadda ya aureta to amman yanzu ba zai iya auren ta ba gaskiya don yasan zuciyarta na wurin wani har saida Haisam ya k'ara mashi magana sannan yace "ba wai bazan iya auren ta ba H,Zakee saidae gaskiya itama ba lalle ta amince ba Saboda akwae shakuwa mai k'arfi tsakanin ta da Feenah hakan zai jawo babbar matsala azo a kasa samun kwanciyar hankali kuma" shiru Haisam yay yana nazarin Maganar shi can yaji yace to ko Yayi ma Najeeb magana yasan zai amince tunda yana sonta dama, yanayin fuskar Abbas d'in ne ya sauya da sauri yace "haba H,Zakee ban tunanin zaka yi wannan Maganar ba duk don mi ake gudun wannan d'in da za'a aura mata ba Saboda halin shi ba to miye marabar shi da Najeeb d'in duk abunda yake Najeeb ma nayi k'ilan ma ya take shi" sai lokacin ma shi Haisam d'in ya tuna da wannan yace "gashi Saleem was already engaged da sai in mashi magana" wani d'an guntun murmushi Abbas yay jin yadda Haisam d'in keta kawo mutane can yay ajiyar zuciya yace "H,Zakee kai why not ka aureta kawae dama kaga ance wanda take so bai K'asar kaga kenan kai ka dace matsayin wanda za'a aura mata" wani d'a murmushin gefen baki yay yama rasa wace amsa zai ba Abbas d'in har saida ya sake mashi magana kan abunda ya fad'a sannan yace "I thought k'arfi kowa sanin yaushe nay aure zaka k'ara man Maganar wani auren and Maganar shakuwa da kai itama Fanan d'in ai sun shak'u" Abbas yace "amman ai hakan ban tunanin zai hana ka aureta matuk'ar kana so ko don ka taimake ta duba da irin shak'uwar da ke tsakanin ku....." Tun kan ya k'arasa Haisam d'in ya girgiza kai tamkar yana ganin shi yace "isn't possible Abbas bansan yadda zan kawo wannan issue d'in ba just 3 months da yin aure na so let think of another solution" Abbas yace "H,Zakee Maganar aure fa ba magana bace mai sauk'i da kawae za'ai tunanin da anyi ma wani magana zai amince kuma yakamata ka rink'a tuna dalilin son fasa wannan auren nata, ni ina ganin in dae zaka amince ba wani abu bane zaka iya auranta ba tare da kowa ya sani ba just to help her ya zamana iya mu nan muka sani ko ita ba sai an sanar da ita ba kaga bayan an d'aura maku auran zaka iya rabuwa da ita ba tare da idda ta hau kanta ba" Haisam d'in yace "but baka tunanin still sunanta zai canza?" Da sauri Abbas jin kaman ya fara yin nasara yace "No, ai kaga yanzu su nan dama an sanar dasu wanda take son bai K'asar to in aka d'aura auran daga baya in tayi nisa a karatun ta sai a sanar masu ka warware auren don ba yanzu zaka dawo ba ita kuma kar tay ta zama da aure a kanta ba miji" wani kalan murmushi Haisam yay yace "what if suka maido Maganar auren wanccan din?" Abbas yace "ban tunanin hakan ai ba wai daka raba auren za'a sanar masu ba sai an samu kaman 2 years haka lokacin kuma nasan yayi auren shi tunda ba yaro bane kuma nasan ko don ya shirya da Dad d'in shi zai yi sauri yay aure in ma lokacin sun kawo zancen yi mata wani auren nasan k'ila bata rasa wanda take so then" shiru Haisam yay yana nazarin Maganar Abbas sai Addu'ar Allah yasa ya amince yake a cikin ranshi don yana da tabbacin ba lalle ya saketa ba in ya aureta don ya fahimci kamar shima yana son Zarah d'in kawae bai gane bane bayan wani d'an lokaci yace mashi shikenan in yana ganin hakan za'a samu mafita ba tare da wata matsala ba ayi hakan Abbas ya washe bakin farin ciki yace in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu Haisam d'in yana murmushi yace shi zai zaman mashi Waliyyi kenan yace eh yana dariya ya tambaye shi nawa za'a bada sadaki Abbas yace ko nawa yadda yaga yayi mashi yace zai turo mashi 1 million ya bada 500k sadakin sauran 500k d'in ai abunda yakamata sosae Abbas yay mamaki jin sadakin daidai da na Fanan ya bada hakan ya k'ara tabbatar mashi da zargin shi na yana son Fatuu kawae ya kasa ganewa ne nan take ya d'auki aniyar sai ya yi yadda yay auren ya d'ore in sha Allah, suna gama wayar sai ga kud'in ya turo mashi murna a wurin Abbas har saida ya d'an taka rawa kafin ya d'aga hannu yay ma Allah godiya ya rok'i yasa hakan yazama Alkhairi, ba 6ata lokaci ya saka kayan shi ya d'auki wayarshi ya fice, ko ta kan ya nemi Abinci bai bi ba ya hau Motar shi bayan ya fito ya nufi komawa rugar akan hanyar shi zuciyar shi ta raya mashi yakamata yaje ya sanar ma da Alhaji Lawal don ya zame masu shaida sosae hakan yay mashi ya nufi hanyar zuwa gidan cikin sa'a ya gane kuma ya same shi yana gida, bayan ya shiga Parlon shi suka gaisa Abbas ya tambayi ko ya gane shi yana fara'a yace ya gane shi mana ba duka d'azun suka rabu ba shima Abbas murmushi yake kafin ya sanar dashi yazo rok'on Alfarma ne yace to Allah yasa zai iya nan ya sanar dashi wanda take son ya amince a d'aura masu auren har ma ya turo da sadaki shine yake son don Allah ya shige masu gaba, sosae yaji dad'i yace ya taya Fatuu murna anan ya tambaye shi game da Haisam d'in Abbas ya sanar dashi sunan shi da kuma waye Mahaifin shi sosae Alhaji Lawal yay mamakin jin d'an Senator Alee Adamu Zakee ne wanda ba 6oyayyen d'an siyasa bane kusan ko ina an san shi ba kamar daya kasance shine Senator d'in daya fi kowane Senator kud'i a Arewa ba 6ata lokaci yace ya tsaya ayi sallar la'asar sai su koma rugar tare a shirya yadda za'a d'aura masu auren Abbas yace to nan Yasa aka kawo mashi Abinci yaci ya k'oshi daga baya yace zai d'an je cikin gari ya dawo yace to, kud'i yaje ya fiddo ana gama sallar la'asar ya dawo ba 6ata lokaci bayan Chairman ya dawo daga Masallaci suka tafi rugar Abbas na a Motar shi shima yana a Jeep d'in shi driver na tuk'a shi, lokacin da suka isa Ard'on na a kopar gida zaune da mutane suka nufi wurin su bayan sun zauna aka shiga gaisawa Ardon yace su shiga cikin fada Alhaji Lawal yace a'a nan ma lafiya lau tunda dama abunda ke tafe dasu ana son mutane su shaida nan Abbas yay ma Ard'on bayani game da amincewar da Haisam yay ya fiddo kud'i 500k ya aje a gaban shi yace ga sadakin ta sannan ya k'ara fiddo 200k yace wannan kuma na su ne su raba inji Angon jama'a zo kuga idanu baki bud'e kowa ke kallon kud'in Alhaji Lawal dae sai murmushi yake a rud'e Ardo ya hau tambayar wai waye wanda zai aure tan ko dai d'an yankan kai ne wannan iyayen kud'i a sadaki Alhaji Lawal ne yay masu bayanin ko wanene Angon Ardo daya gama rud'ewa harda cewa da tana da saurayi irin wannan tuntuni bata kawo shi an d'aura masu aure ba, Kamalu da Amadu da tunda suka ga isowarsu suka taso suka zo gefe don jin abunda zasu tattauna ai suna jin zancen Haisam ne za'a d'aura dashi suka nufi cikin gida da hanzari har rige rigen shiga d'akin suke lokacin su gwaggo duk suna a parlon tun bayan da suka gama sallar la'asar har saida su gwaggon suka tsorata ganin yadda suka fad'o masu Amadu na washe baki ya hau yi mata bayanin abunda ke faruwa a waje cikin d'aurewar kai ta maimaita sunan Haisam matsayin wanda za'a d'aura aure dashi yace mata eh wllh har sadaki ma an kawo Naira 500k zaro ido gwaggo tay tama kasa cewa komae Yadikko ko bata san lokacin data fara sakin murmushi ba Kamalu ne ya juya da sauri ya nufi d'akin baffan su ya sanar mashi lokacin yana kwance ya kasa fita Saboda damuwa ai yana jin zancen ya mik'e ba shiri ya nufi wajen anan aka shirya d'aura auren gobe Juma'a a Masallacin Juma'a dake Jimeta bayan gama Sallar juma'a Lokacin da Alhaji Lawal zai tafi har kud'i Abbas ya basu don su sha mai amman yak'i amsa yace da Haisam da Fatuu duk ya'yan shi ne k'arshe saidae yay ma driver d'in shi Alheri suka tafi kan sai goben, sam gwaggo ta rasa farin ciki zatai komi gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa ta yadda akai Al'amarin ya kasance haka, sai bayan sallar isha sannan duk suka hallara a parlon Yadikko harda Abbas cike da damuwa gwaggo tace "d'ana Abbas ya akai hakan ta faru Saboda mi zaku takura kan ku har haka shi Haisam bai ganin bai dad'e da yin aure ba zai k'ara wani wanda nasan ba don yana so bane kawae k'arfin hali ne irin nashi shiyasa ya za6i cire mu a matsala shi kuma ya jefa kan shi a matsalar aure ba ba k'aramin abu bane, gaskiya ni ban goyon bayan auren nan kwata kwata shima nasan bai yi nazari yadda ya kamata ba kafin ya amince, gaskiya ban amince ba kawae a k'yaleta ta auri wanda suke so hakan zai fi nima hankali na zai fi kwanciya fiye da ace Haisam ta aura" ganin yadda duk ta damu yasa Abbas warware mata komae yace shi yana ganin hakan zai fi kan ta auri wanccan da bata so kuma shima Haisam d'in hakan yayi mashi tunda ba takura shi yay ba ta bari kawae ayi yadda suka tsaran Allah yasa haka yafi zama Alkhairi" Yadikko itama tace "nima ina ganin hakan zai fi kawai ai dama Addu'ar abunda yafi zama Alkhairi duk muke tayi to hakan shi yafi Alkhairin" Baffan Fatuu dae ya rasa ta cewa su Amadu da Kamalu ma duk suka goyi bayan yadda aka tsaran gwaggo dae tay shiru fuskarta d'auke da damuwa duk da ta ragu sakamakon jin ba auren dundundun bane nan Abbas yaba gwaggo sauran 300k d'in yace ayi abunda yakamata tace yaba Baffan dama an bashi sadakin Fatun amman saida Ardo yasa aka bashi wani abu a ciki wai ai sun riga sun gama mata komae, Yadikko ta zubo ma kowa Abinci bayan an gama ci duk akai sallama kowa ya nufi wurin kwanciya Amadu har ya fita ya dawo yace ma gwaggo yana son magana da ita ta mik'e ta fito wajen jiki sukuku acan gefe suka ke6e ganin yadda duk ta damu ya shiga kwantar mata da hankali yace shi yana jin hakan wata hikima ce ta Ubangiji nan ya kwashe komae game da son da Fatuu kema Haisam d'in har ciwon da tayi acan baya suka zata na Aljanun ta ne tsananin mamaki ne ya kama gwaggo har saida tasa hannu ta ruk'e ha6arta baki bud'e ta shiga fad'in yanzu dama duk wannan halin data shiga Saboda Haisam ne Amadun yace mata tabbas don da bakinta ta fadi mashi ya bata labarin lokacin d'aya isketa cikin mawuyacin hali tana amai a d'aki har ta sanar mashi hakan tafa hannu gwaggo ta shiga yi tana salati Amadun yace don haka ta bi su da Addu'a kawae k'ilan Allah ne ya cika mata burinta, a daren ranar kasa runtsawa gwaggo tay sosae tausayin Fatuu ya mamaye mata zuciya biri yayi kama da Mutum ashe shiyasa tak'i sake ma Fanan duk da hakan ji take ba yadda za'ai auren ya dore abunda za'ai iya su ba tare da sanin dangin shi ba ita kanta bazata so Fanan taji zancen auren nan ba Saboda yadda ta d'auke su gani take hakan zai zama tamkar cin Amana ne, Washe gari Juma'a aka fara shirye shiryen d'aurin aure tunda safe Abbas da Baffan Fatuu suka tafi kasuwa suka yo siyayyar kayan Abincin da za'ai harda tunkiya da za'a yanka bayan sun dawo dole gwaggo ta washe suka fara hidiman Abinci da soyen nama bayan sallar Juma'a Mutane masu yawa suka shaida d'aurin auren Haisam da Fatuu sosae Alhaji Lawal yay kokari don kuwa shi ya kawo take aways na abinciccikan da aka raba ma Mutane, bayan sun koma gida aka ci gaba da hidiman biki saidae yawanci yaran gidan ba kowa ne yasan da Maganar auren ba sun dae ga anyi Abinci ga nama kuma an soya Yaya ranar wuni tay a d'aki tana ciwon bakin ciki tun bayan da taji da wanda aka d'aura ma Fatuu aure to ai dama ita Hassada ga mai rabo taki ce, Washe gari ana gama sallar Asuba suka kamo hanya harda su Yadikko aka taho Katsina..........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2052*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
............. Lokacin da suka iso Katsina wannan dalilin ne yasa lokacin da Fatuu ta tambayi Abbas da gaske an fasa auranta yace mata eh amman an d'aura da shi haka da zata bi su Mino lokacin da Abbas yazo kai su suga gari ta saka fitted gown Yadikko tay magana kan rashin dacewar ta fita da rigar da d'an k'aramin gyale har gwaggo ta saka baki k'arshe dai saidae ta canza kaya haka lokacin da Haisam ya kirata vedio call da tace fushi take dashi har bacci ya kwashe ta ya kai hannu yana zagaye lips d'in ta saman screen lokacin duk matar shi ce ita, bayan an samu natsuwa su Yadikko sun koma aka fara shirin cigaba da karatun Fatuu lokacin gwaggo ta nemi Abbas yazo suka zauna a parlor bayan sun gaisa ne ta fad'i mashi dalilin kiran nashi dama kan Maganar sakin Fatuu ne don suna shirin cigaba da karatun ta kuma ga aure akan ta shiyasa take so ya tuntu6i Haisam da Maganar dama sadakin shi na nan a wurin Baffan ta za'a maido mashi amman sai yace shi yana ganin ba sai an yi mashi magana ba tunda ai yasan da auren shi a Kanta kuma dole zata cigaba da karatu don haka a k'yale shi taci gaba kawae cike da damuwa gwaggo tace "amman baka ganin akwae had'ari ace ta tafi wani gari karatu da auren da bata san dashi ba a kanta ni ina ganin d'ana Abbas gara ai mashi Magana ya saki kaman yadda aka tsaran" Abbas d'in ya nuna mata shi fatan da yake dama auren ya d'ore ba wai su rabu ba gwaggo ta hau girgiza kai tace "gaskiya ni bana son hakan duk da zan yi matuk'ar farin ciki in ta samu miji kamar shi to amman ana barin halak ai ko don kunya yanzu in matar shi tasan da Maganar auren da wane ido zan kalleta ita kanta zata ga an ci Amanar ta ba kamar yadda ta d'auke ni tamkar itama ni kakarta ce" cikin kwantar da murya Abbas yace "gwaggon mu wannan duk ba abun damuwa bane in dae Allah ya kaddaro dama zasu kasance miji da mata ai mu bamu isa mu hana ba kuma duk abunda zamu yi yanzu wllh bamu isa mu raba ba don haka mu bar ma Allah komae shi zai shige mana gaba kiga komae yazo da sauk'i" ba don taso ba tace mashi shikenan amman dae gaskiya bai kamata ta tafi wani gari karatu da aure a kanta ba shine ya kawo mata shawarar Fatuu ta fara yin School of Nursing tunda an kusa fara yin Medicine anan ko bayan ta gama ne sai tayi k'arshe gwaggon ta amince ta kuma rok'e shi kan ya taimaka mata wurin kula da Fatun yace in sha Allahu, tun daga wannan lokacin duk abu in ya shafi Fatuu sai gwaggo ta tuntu6i Abbas ko lokacin da zasu bikin Haulat Nijar sai da tay mashi magana shi kuma ya kira Haisam don neman izini lokacin yace mashi duk inda zasu suje ba sai an rink'a tambayar shi ba ya bada izini haka lokacin da taso zama a Hostel farko gwaggo tak'i amincewa tace saidae in ya kama ko zasu yi wani abun kaman yadda ta fad'a mata daga baya ta tuntu6i Abbas da Maganar yay ma Haisam Maganar shi da kan shi yace abarta in dae tana so ta zauna shiyasa gwaggon ta k'yaleta take zama saidae duk da haka tana saka ido sosae a kanta kaman wurin sa kaya da kuma tabbatar da tana a Makarantar duk da ta yarda da ita sosae.
***** ****** *****