Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 53
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 53: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 53. Saida Amadu yaga fitar Mama sannan ya koma cikin…
4,333 words
Saida Amadu yaga fitar Mama sannan ya koma cikin d'akin yana niyyar komawa bakin gadon Gwaggo ta mik'e tace yazo ya zauna bari ta had'a mashi breakfast d'in yaci yanzu in ba haka ba ba lalle ya samu damar ci ba d'an anjima mutane zasu iya fara zuwa yace to, bayan ya fara ci Fatuu dake gefen shi ta tambaye shi ko yaga wayarta kafin ya bata amsa gwaggo tace gata nan cikin Aljihun ta jiya ma bayan sun koma Fauziyya ta kira ta d'aga ta fad'i mata tana Asibiti shiru Fatuu tay cikin ranta ta shiga raya da ta bi Maganar Fauzy da yanzu cikin na nan ta tabbatar ma inda tasan kiran da Haisam yay mata a waya da yawa ne harda text message bazata bari a zubar ba wani, wani irin sanyi jikinta yay nan take taji wata irin nadama tazo mata da kanta ta zubar da cikinta na halak cikin mutumin da take tsananin k'auna, gaba d'aya ji tay breakfast d'in ya fitar mata a rai ta mik'e ta tattara kayan ta nufi gefen gado dasu gwaggo na ce mata har ta k'oshi tace eh ta tashi ta bata magungunan ta, bayan ta gama sha idasa hayewa gado tayi tay lamo har gwaggo na tambayar ta ko jikin ne tace a'a bacci ne bai ishe ta ba tace ai sai taci gaba ta lumshe ido kaman baccin zatai da gaske amman tunane tunane da zancen zuci kawae take a haka baccin ya d'auketa ba, bayan Amadu ya gama yace ma gwaggo zai tafi sai anjima zai dawo tace to k'ilan ta kira shi ya dafa Abinci ya zauna cikin shiri sukai sallama ta bashi kayan Abincin da aka gama dasu ya tafi. Wuraren k'arfe sha d'aya Fatuu ta farka taga d'akin wayam ba kowa tana kwance aka turo k'opar sai ga Fauzy ta shigo da yar sallama da sauri Fatuu ta yunk'ura ta tashi zaune tana kallonta itama Fauzy da sauri ta nufi gadon ta zaune a gefe fuskarta d'auke da matsananciyar damuwa tayi mata sannu ta d'aga mata kai d'an shiru sukai sunata kallon juna fuskar Fatuu a yamutse kaman zata saka kuka can Fauzy tace "ashe haka abu ya faru harda kwanciya Asibiti tun bayan da muka rabu inata so in kira ki zullumi da fargaba suka hana ganin har dare yayi baki kirani ba kin sanar da ni halin da ake ciki yasa nai k'arfin halin kiran ki saidae kusan sau ukku ba'a d'aga ba tsoro ya kama ni sosae na shiga tunanin to ko lpy gashi na kasa kiran ko Kawu Amadu, sai can dare wurin karfe 11 nace bari in k'ara jarabawa k'ilan ki d'aga tunda lokacin kwanciya ne ina kira sai gwaggo ta d'auka nan take sanar dani wai an kwantar dake Asibiti wayar na gida aka barta wllh sosae hankali na ya tashi bazan 6oye maki ba ko bacci ban yi ba saboda fargabar abunda ya faru har aka kwantar da ke, Aunty Mareeya har ta gane ina cikin damuwa tanata tambayata Mike damuna saidae in ce mata ban jin dad'i kawai don ban san taya zan mata bayani ba" dakatawa tay ta kai idonta kan ledar Karin jinin dake rataye cike da damuwa tace "harda k'arin jini ma akai maki kenan, cikin ne ya fita kika zubda jini sosae?" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, girgiza kai Fauzy tay "Sannu, wllh irin abunda nake ta gudu kenan kinga ko a Makarantar hakan ta faru sai an san dalili, to yanzu da su gwaggon suka sani miya faru?" Shiru kaman bazata ce komae idanunta suka ciko da k'walla a hankali suka fara gangaro mata cikin muryar kuka tace "Fauzy na aikata babban kuskure wllh ashe cikin nan na halak ne ba yadda na zata ba" waro ido Fauzy tay with mouth agape a rud'e tace "cikin halak! Kenan kina son kice man Ya Haisam Mijin ki ne???" Cikin kuka ta d'aga mata kai k'ara zaro idon tay ta kai hannu ta rufe baki kafin ta cire cike da Al'ajabi ta tambayeta yadda hakan ta faru nan ta shiga fad'i mata komae da ya faru bayan ta dawo gidan har zuwa yanzu, salati Fauzy ta shiga yi tana yi tana kai hannu tana dafa gaban kanta da kuma bakin ta cikin tsananin tashin hankali ta hau fad'in "ni wllh dama raina saida ya bani anya ba wani abu a k'asa kwata kwata na kasa yadda Ya Haisam zai aikata maki hakan Saboda son zuciya kawae dai bani da wata hujja ne, innalillahi abu dae bai yi dad'i ba wllh aka ce rashin sani yafi dare duhu" sosae ta shiga damuwa har fuskar ta ta nuna idanun ta sun sauya kwalla ta kwanta cikin su sosae Fatuu ke kuka tana fad'in "nayi danasani Fauzy duk da na d'aga wayar Ya Haisam bayan dana je na sanar mashi da hakan bata faru ba, saida yay ta kira na harda message ya turo man yace kar in yi komae in picking kiran nashi amman na k'iya k'in Fad'a maki nay don kar ki hana a zubar na nuna maki sau d'aya ya kira, wllh ban yi zaton na halak bane tunda ni bansan komae ba ai gashi naga kaman ma yayi fushi Saboda hakan " itama Fauzy k'wallan ne suka fara zubo mata suna cikin haka suka ji karar bud'e kopa duk suka kai idon su kan kopar toilet sai ga gwaggo ta fito idon ta a kan su suma suka bita da ido cike da rashin gaskiya...............
*ASM Bk2055*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
......Kauda idon ta tay daga kallon su ta nufo cikin d'akin cikin kame kai Fauzy ta gaishe da ita ta amsa tare da d'an kallon ta tay mata ya mai jiki nan ma ta amsa kafin ta nufi kujera, a jikinta ta janyo Hijab d'inta ta nufi hanyar fita daga d'akin tana kokarin sakawa, bayan ta fita Fauzy ta kalli Fatuu da yar damuwa tace "ta san kin yi wani abu ne don zubar da cikin?" d'an shiru Fatun tay fuskar ta duk hawaye tace bata sani ba ko likita ya gane ya sanar masu tunda ta dad'e bata farfad'o ba amman in ma ta sanin to bata nuna mata ba, ajiyar zuciya Fauzy tay tace "to k'ilan bata sani ba amman yanzu kaman ma taji abunda muke cewa" shiru kawae Fatun tay idon Fauzy akan ta wani irin tausayin ta ne ya kamata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa yadda take son Ya Haisam bazata ji dad'i ba ace ta samu cikin shi na halak kuma ta zubar da hannun ta gashi tace yayi Fushi, hannu Fauzy ta kai ta kamo nata ta fara lallashin ta "ki kwantar da hankalin ki Zarah nasan dole Kiji ba dad'i amman kada kisa damuwa a ranki ki d'auka komae rubutacce ne dama haka Allah ya k'addaro kuma shima Ya Haisam d'in na tabbatar zai fahimce ki kawae dae dama dole ne ya nuna maki 6acin ran shi Saboda zai ga kin k'i jin Maganar shine har hakan ta faru wanda nasan bai yi zaton hakan daga wurin ki ba a yadda kuke da shi amman dae komai zai daidaita in sha Allahu, ki daina damuwa ko don halin da kike ciki kada ki samu wata matsalar kuma" tana kai Maganar ta kai hannu tana goge mata kwalla daga baya tace bari ta sanar ma Aunty Mareeya, bayan ta kirata ta sanar mata zancen kwantar da Fatun Asibiti salati ta saka hankali a tashe ta hau tambayar Fauzy abunda ya samu Zarah nan ta kwashe komai ta fad'i mata tana jin yadda take zabga salati a rud'e tace tana nan zuwa wane Asibitin take ta sanar mata, bayan sun gama wayar yar hira Fauzy ta shiga yima Fatun duk don ta daina damuwa harda zancen irin shagalin da zasu yi in komae ya daidaita da kalar su ankon da za'ai daga baya kuma yanayin fuskar ta ne ya canza tace tasan ma d'auke Fatun zai yi su bar K'asar amman dae gaskiya a bari sai sun gama karatu lokacin tasan ta k'ara samun wani cikin harma ta haihu, harda Addu'ar Allah yasa next cikin da zata samu na twins ne, tun dai Fatuu na d'an murmushi sai gata harda su dariya, Bayan sallar Azahar sai ga su Feenah Abbas ya kawo su lokacin da suka shigo su Fatun na Zaune akan gadon Fauzy na gefen ta Abdul na hango ta ya nufi gadon da gudu ya fara k'ok'arin hawa Fauzy ta taimaka mashi yana hayewa ya fad'a jikin ta Feenah na fad'in bai ganin mara lpy ce, a gefen gadon Feenah ta tsaya bayan ta aje basket d'in kayan Abincin data shigo da shi tana sanye da doguwar rigar Atamfa tayi d'aurin kallabi mai steps ga gyale mahad'in kayan ta yafa a kafad'a hannun ta na dama ruk'e da hannun Nasreen da itama tasha yan kanti, da alamun damuwa Abdul dake kallon face d'in Fatuu yace "Aunty Fatuu ashe baki lpy" itama kallon shi take da d'an murmushi ta d'aga mashi kai alamar eh ya juya ya kalli ledar K'arin jini fuskar shi kaman zai kuka idanun shi har sun kawo kwalla yace mata sannu ta rungume shi ta gefe Feenah ma tayi mata ya jiki ta amsa mata kafin ta gaishe da ita Nasreen ta fara rigimar itama a d'aurata kan gadon Feenah tace ya duk zasu haye gadon mara lafiya Fatuu ta mik'o hannu tace ba wani abu ta d'auro ta Fauzy ta kai hannu ta d'aukko ta, ganin Feenah nata tsayuwa yasa Fatuu ce mata "Aunty Feenah ga kujera can ki zauna" d'an murmushi tay tace "bari in gama ganin ki to, ashe abu kuma haka ya faru jiya Dear ke fad'a man banji dad'i ba wllh nace da an sani ai da an tari abun da wuri duk da hakan bai faru ba, shima yace man bai san abunda ke faruwa ba sai jiyan" idanun Fatuu ne suka ciko da k'walla bata dae ce komae ba sai kikkafta idanu take don kada su zubo suna haka Abbas ya shigo dama yana waje wurin gwaggo suna gaisawa, bakin gadon shima ya tsaya Fauzy ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya karatu ya maida kallon kan Fatuu cike da kulawa yace "Mom Zarah ya jikin?" Kallon shi tay a sanyaye tace da Sauk'i,
"Allah ya baki lafiya ashe haka abu kuma ya faru?" Aikuwa kaman tana jira ta fashe masu da kuka dama daurewa kawae take, girgiza kai Abbas ya shiga yi cike da tausayi Feenah ma Fuskarta kaman zata sa kukan Fauzy kuwa tuni kwalla sun ciko mata, sosae Abdul ya rud'e ya d'ago yana fad'in "Aunty Fatuu don Allah kibar kuka zaki samu lafiya in baki yi shiru ba nima zan yi kukan" k'ok'arin shanye kukan ta fara tana girgiza ma Abdul kai alamar kada yayi ya kai hannu yana goge mata kowa jikin shi yayi sanyi Abbas ne yace "Kiyi hakuri Mom Zarah nasan an maki ba daidai ba don da kin sani hakan ba zai faru ba to amman komai ki ka ga ya faru dama rubutacce ne" kallon shi tay cikin muryar kuka tace "Amman Ya Abbas Saboda mi aka 6oye man ko kai ba sai ka fad'i man ba tunda ni ban 6oye maka komai" da alamun Damuwa kan face d'in shi yace "kiyi hak'uri don Allah haka aka tsara ne ba za'a sanar maki ba shiyasa..." Katse shi tay "to Saboda mi?" Shiru yay don bai son yace mata auran tsarawa akai don a taimake ta ba don ya d'ore ba, ba kamar kuma yanzu da abu ya shiga tsakanin su, Feenah ta fahimci Abbas bai son sanar da ita game da auren hakan yasa ta kai hannu tana share mata hawayen dake zubowa tana fad'in "Haba Mom Zarah d'in mu kefa nasan mai k'arfin hali ce kiyi hak'uri komae ya wuce ko ma samu ki warke da wuri a k'ara samo mana cikin wani Baby d'in in sha Allahu ma twins za'a maida mana tunda da yawa wani rabon ke kore wani" d'an murmushi Fauzy tay ta sadda kan ta haka ma Fatuu d'an juyar da fuskar ta tay Abdul kuwa k'ura ma Feenah da tayi Maganar ido yay can ya kasa jurewa ya d'ago daga jikin Fatuu yace "Momy Aunty Fatuu tayi aure ne?"
D'an shiru tay sai kuma tace mashi "Mi yasa ka tambaya?" yace "naji kin ce ta Warke ta haifo babies?" shiru Feenah tay sham ta manta dashi a wurin tay Maganar tasan shi bai ji ya k'yale Abbas kuwa d'an d'age gira yay yana kallon Feenah da murmushi alamar jiran yaji amsar da zata ba Abdul don ya kafeta da ido can ta d'aga mashi kai tace eh tayi aure, waro ido yay alamun mamaki ya juya ya kalli Fatun ya sake juyowa ya kalli Mom d'in tashi yace "Yaushe tay auren ni ban sani ba kuma waye ta aura?" ta biyun ta amsa mashi tana d'an murmushi tace "Baban ka Zakee" har saida yay wata yar zabura ya tsuke fuska cikin fushi yace "Kamm shine sukai auran ban sani ba kuma bani nace ma ya aure ta ba" a hak'ik'an ce yay Maganar sai bin su yake da kallo ya kumburo baki sigh Abbas yay yace mashi "ai ba'a yi bikin ba tukun an dai d'aura masu aure ne....." Katse shi yay kaman zai kuka "to ni miyasa ba'a je dani d'aurin auren ba ba inada babban riga ba" har saida ya basu dariya su duka Fatun ma saida tay d'an murmushi wato shi a tunanin shi saida babban riga ake zuwa d'aurin aure, kafin wani ya bashi amsa aka turo k'opar da yar sallama k'asa k'asa ya shigo, Wow Tubarkallah Angon Fatuu shine abunda na fad'a, wankan bak'in Voile yay ana d'an hango hasken vest d'in shi kad'an hannun shi d'aure da Agogo ta bak'ar fata haka k'afafun shi dakakkun half cover ne masu kyau da tsada Sumar nan tasha gyara ta k'ara bak'i sai salk'i take, sosae yay kyau tun ma kafin ya k'arasa shigowa k'amshin turaren shi ya baza d'akin kai kace shi kadai kamfanonin turaren suke ma irin nashi don koda yaushe k'amshin shi na daban ne, tunda Fatuu tay arba da Fuskar shi gaban ta ya fara wani irin bugu gaba d'ayan su idanun su na akan shi yayin da Fauzy acikin ranta ta hau fad'in Tubarkallah sam bata ganin laifin Fatuu da take son shi ita a yadda take ji ma da itace abu ya shiga tsakanin su har ta samu ciki wllh bazata zubar da shi ba bari zatai har ta haife tunda tasan bazai ta6a wofintar da ita ba duk surutun da za'ai aje ai ta yi, Abdul na ganin shi ya saukko daga kan gadon ya nufe shi da sauri lokacin har ya zo tsakiyar d'akin a gaban shi ya tsaya yana kallon shi fuska a d'aure hakan yasa Haisam d'in tsayawa yana kallon shi Fuska a sake su Abbas nata murmushi daga inda yake yace ma Haisam "Baba Zakee yau fa ka ta6o d'an gidan ka kay mashi laifi" d'an kallon Abbas da yay Maganar yay sai kuma ya maido idon kan Abdul daya kumbura kamar zai fashe cikin cool voice d'in shi yace "What's happening?" Ya kai hannu zai dafa kan Abdul d'in da sauri ya janye kan yasa hannuwan shi duka ya ruk'e k'ugun shi alamar dai abun yau baram baram za'ai Abbas kau mi zai yi in ba dariya ba haka ma su Fauzy still Haisam murmushi yake calmly ya furta "kaga dariya suke mana tell me laifin mi nayi?" Yana tura baki yace "ashe dana ce ka auri Aunty Fatuu ka aureta ban sani ba kuma ko d'aurin auren ba'a je dani ba!" Abbas ya amshe da fad'in "kuma dae yana da babban riga ato" duk sukai dariya shima Haisam d'in yar dariyar yay ya kamo hannun shi yana fad'in yayi hak'uri to ya fara bubbuga k'afa k'arshe Haisam d'in ya sunkuce shi ya d'aura shi a bayan shi sai k'unk'uni yake cike da shagwaba, yana zuwa bakin gadon Fatuu ta sunkuyar da kanta Fauzy dake kallon shi ta gaida shi ya amsa tay mashi ya mai jiki haka Feenah ma duk ya amsa Fauzy ta sauka daga kan gadon ta nufi Kujera Feenah ma ta bi bayan ta ya rage daga shi sai Abbas tsaye a bakin gadon, kai idon shi yay kan ta kaman ance ta d'ago suka had'a ido Slowly ya furta "Ya jiki?" a sanyaye tace da Sauk'i ya jinjina kai kawae still da canjin da take gani akan Fuskar tashi, mai da kallon yay kan Abbas dake mashi wani kallo irin na wanda yay abu ba daidai ba shi kuma ya maida mashi martani da nashi mai kaman harara suna haka Dr Habeeb ya shigo cikin d'akin da sallama su Feenah suka amsa had'i da gaishe dashi yay masu ya mai jiki ya nufi su Abbas, hannu ya basu suka gaisa gaba d'aya ya kalli Haisam yay mashi ya mai jiki k'asa k'asa yace da Sauk'i kafin ya d'an matsa gaban gadon da murmushi yace ma Fatuu ya jiki tace da Sauk'i ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay tana jin wani ciwo ko a marar ta haka tace a'a bata jin komae ya k'ara tambayar yanayin jinin da ke zuba da yanayin yawan shi a kunyance take bashi amsa tana yi tana d'an sadda kai don duk su Abbas na ji,
"To ya kike jin yanayin jikin ki?" tace "kawae ba k'arfi ne sosae" jinjina kai yay "Ok sai a hankali k'arfin zai dawo zuwa anjima sai a ida saka maki sauran jinin" kai ta d'aga ya juya kan Haisam yace "Yanzu ina ganin muje ai mata Scanning d'in mu ga" kai Haisam ya d'aga ya juya ya kalleta suka had'a ido sai taga kaman ma harararta yake da sauri ta sunkuyar da kan ta, Abbas ya yi ma Feenah magana kan tazo ta taimaka mata suje wurin scanning tace to ta mik'e su kuma suka wuce tare da Dr d'in, bayan ta saukko daga kan gadon Fauzy ma ta taso lokacin gwaggo ta shigo tazo wurin su tana fad'in bari a bata abunda zata yafa ta wuce wurin jaka ta ciro mata d'an gyalen ta dama kan ta da hula suka tafi Feenah ta tallabo Shoulders d'in ta, a kan hanyar su ne Fauzy ke yin Addu'ar Allah yasa aga cikin na nan Feenah tace ai gaskiya da wuya ne Saboda Dear ya fad'a mata ta zubar da jini sosae gashi cikin dama d'an k'arami ne zai wuya ya tsaya kuma already Dr ma yace masu ya fita, lokacin da suka isa a bakin wurin suka iske su Haisam tunda ta kalle shi sau d'aya ta kauda idon ta Abbas ne yace mata ta shiga Dr d'in na ciki ta d'aga kai ta shiga suma su Feenah suka tsaya a bakin kopar don su jirata daga baya Dr ya fito yace ma su Abbas suje Office, sai bayan wasu mintuna Fatun ta fito Feenah ta tambayi an gama tace mata eh ance za'a tura ma Dr tace Ok ta k'ara kamata suka tafi, Suna zaune a Office suna yar hira aka turo result d'in ya fad'a masu gashi an turo ya fara dubawa bayan wani lokaci ya d'ago ya kalli Haisam yace "ya nuna ba sauran wani abu mahaifar ta is empty so ina ganin kawae taci gaba da shan magungunan tunda tace jinin ma ba mai yawa bane ke zuba yanzu a hankali zai d'auke, in kuma kun fi so ayi mata D&C d'in to wani lokacin yana taimakawa wurin k'ara conceiving da wuri amman dama ciki k'asa da 10 weeks ba dole sai an yi ba indai ba wata matsala haka" Wani kallo Abbas yay ma Haisam cike da shak'iyanci yace "H,Zakee ina ganin ayi matan ko Saboda ai saurin k'ara samun wanin" banza yay ma shi cikin cool voice d'in shi yace ma Dr shikenan ba sai anyi ba ya gode yana fad'in hakan ya mik'e Abbas ma ya tashi yana mashi dariyar iskanci shima Dr Habeeb d'in mik'ewa yay yana yin dariyar don daga baya Abbas yay mashi bayani game da auran da yadda aka samu cikin, saida ya rako su bakin Office d'in yace tayi duk abunda zata yi bada jimawa ba zai zo ya sa mata jinin Haisam ya amsa da Ok kafin suka tafi, Bayan su Fatuu sun koma kan kujera Feenah tasa ta zauna don taci Abinci cikin wanda ta kawo mata ta zubo mata tace ma Fauzy itama ta zuba tana murmushi tace to, tasa Fatuu gaba tay wai sai ta ci shi sosae Abdul ma na gefen ta yana fad'in taci ta k'oshi ta warke su tafi gida tare tay yar dariya suna haka Hajiya ta shigo harda Saude ruk'e da k'aton Basket din kayan Abinci da kuma Tk, Feenah ta mik'e taba Hajiyar wuri don ta zauna, bayan ta zauna idon ta akan Fatuu ta kai hannu ta dafa kafad'ar ta tace "Sannu Fateema kin ji an ja maki jinyar dole" d'an murmushi kawai Fatuu tay ta gaisheta bayan ta amsa taci gaba "an gode ma Allah daya tashi kafad'un ki, jiyan nan ai hankali na ya tashi sosae wllh yarinya tamkar ba rai ga uban jini da kika zubda, to ya jikin naki yanzu?" tana d'an murmushi tace da Sauk'i sosae Hajiya tace "to Alhamdulillah Allah ya k'aro sauk'in, su Dije sun auna Arziki don da wani abu ya same ki duk sai nayi k'arar su an bi maki hakk'in ki wllh duk da haka ba k'yale su zan ba" kowa yay murmushi su Sauden sukai mata ya jiki ta amsa masu ana haka gwaggo ta shigo cikin d'akin d'auke da plastic chairs guda biyu ta aje tace ma Saude su zauna, bayan sun zauna duk suka gaishe da ita Sukae mata ya mai jiki ta amsa masu dama ta gaisa da Hajiya tun a waje tana ta tura baki ta amsa mata, lokacin Abbas da Haisam suka shigo Hajiya ta bisu da wani wani kallo fuska a tsuke Abbas ne kawae ya gaishe da ita ta amsa mashi ba yabo ba fallasa ya kalli gwaggo yay mata bayanin da Dr yayi game da scanning d'in yace ba sai anyi Mata wankin cikin ba taci gaba da shan magani gwaggon tace to in sha Allah Hajiya tace "ai gwara dae kada ayi matan a kyaleta da wahalan da aka d'ora mata ba sai an k'ara mata wata Azabar ba" kowa dae murmushi kawae yake banda Haisam dake tsaye can ya juya zai fita Abbas yabi bayan shi,
Sai da akayi la'asar Abbas ya kira Feenah ta fito su tafi lokacin an k'ara sama Fatuu jinin Abdul yasa rigimar bazai tafi ba shi anan zai tsaya dama da yaga za'a saka mata jinin harda kukan shi da kyar gwaggo ta lalla6a shi tace Asibitin ba'a barin yara su zauna da an ganshi za'a zo a tafi dashi ya bari in suka koma gida sai yazo ya zauna har ta warke gaba d'aya yace to yaushe zasu koma gidan tace bada dad'ewa ba da an sallame su zata kira daddy d'in shi ta gaya mashi sannan ya yarda suka tafi Fauzy tay masu rakiya har bakin Mota, tana niyyar dawowa ciki sai ga Aunty Mareeya mai Keke Napep ya tsaya da ita Fauzy ta nufe su tana murmushi tay mata sannu da zuwa ta amsa tace ta d'aukko basket a ciki tace to, bayan ta d'aukko ta sallami mai Napep d'in suka nufi cikin Asibitin, lokacin da suka shiga d'akin Aunty Mareeya ta gaida su Hajiya da Gwaggo tay masu ya mai jiki suka amsa sannan ta nufi gadon Fatuu na kwance jinin nata shiga ta kalli Aunty Mareeyar da d'an murmushi ta gaishe da ita saida ta zauna a bakin gadon da alamun damuwa tay mata sannu da jiki Fatun ta amsa bayan Fauzy ta aje basket d'in tazo daga d'ayan gefen itama ta zauna Aunty Mareeya ta kalleta k'asa k'asa da murya tace "d'azun kina gaya man abun Al'ajabi ashe duk abunan mutumin nan mijin Zarah ne" gyad'a kai Fauzy tay kawae ta sake cewa "amman dai ni kun yi man rashin hankali wllh haba kaman baku san halin shi ba ai bai kamata kuyi saurin zubar da shi ba" cike da damuwa Fauzy tace "wllh nima Aunty ban so akayi saurin zubar dashi ba..." Nan ta fad'i mata yadda sukai da Fatuu kan zubar da cikin gaba d'aya k'asa k'asa suke Maganar yadda baza'a ji su ba, bayan ta gama fad'i mata ta kalli Fatuu tace "na fahimci dalilin ki Zarah haka Allah ya k'addara amman dae da kin bashi dama kin ji abunda zai ce wllh tunda mutumin nan kin fi kowa sanin halin shi bai kamata ki k'i saurarar shi ba koda ace babu auran yayi maki haka na tabbatar zai yi abunda ya dace ya samar maku mafita bazai ta6a bari ki wulakanta ba nasan k'arshe ma cewa zai ya aure ki kuma ai mu abunda muke so kenan" shiru kawae Fatuu tay ita kanta yanzu dana sani kawae take ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri amman tasan Saboda son da take mashi ne shi kuma sai taga kaman ya fara sha'awarta ne can taji muryar Aunty Mareeya tana fad'in "ni wllh dana san da Maganar bazan bari a zubar ba, ni in nice ma wllh bazan yi tunanin zubar dashi ba yaushe ma ai ko shi yace a zubar bazan yarda ba adai nemi mafita kawae" hannu Fauzy tasa ta gumtse Dariya ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tace "to uwar gulma ai don kar a akaita laifi biyu na fad'i hakan" cire hannun Fauzy tay tana ta dariya Fatuu ma saida ta d'an yi, Sai bayan Magrib duk suka tafi har da Fauzy tace nan zata kwana gwaggo tace a'a taje gida ta huta tunda ta wuni, a daren Abinci saidae gwaggo ta ba wasu don yayi yawa sosae,