Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 74
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 74: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 74. Bayan ta koma part d'in nasu kitchen ta wuce ta…
4,257 words
Bayan ta koma part d'in nasu kitchen ta wuce ta zubo Abincin a plate ta dawo parlor ta d'aura akan c-table ta fara ci, bata dad'e sosae da fara ci ba taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta, Farha ce ta shigo har saida gaban Fatun ya Fad'i ta dakata da cin Abincin tana kallon ta, nufo cikin falon tay tana tafiya cike da isa ta tsaya daga gaban Fatun suka fara kallon kallo ta wani kalan had'e rai can ta ja wani dogon tsoki ta nuna Fatuu da yatsa a fusace tace "You bastard! how dare u married my sister's Husband!!!" Shiru Fatuu tay tana kallonta, a hasale ta matsa ta kai duka hannuwanta jikin c-table d'in ta d'ago shi ta kifa ma Fatun shi Abincin ya 6aro a jikinta da sauri ta mik'e don yana da d'an zafi ga c-table d'in ya dakar mata gwuiwa, hannu ta kai ta maida table d'in ta d'ago tana kallon Farhar tana fitar da numfashi da sauri da sauri ita kuma Farhar sai huci take, a zafafe taci gaba "U must leave dis house tunda ba gidan uban ki bane, wllh sai kin bar shi talakan banza talakan wofi a gold digger" tsoki ta k'ara ja ta juya har tayi d'an taku ta juya tana nuna Fatun tace "in na k'ara ganin kin je d'aukar Abinci sai na saka maki poison kin mutu kuma ba abunda za'ai man na kashe Banzaaa" tana fad'in hakan ta juya ta tafi, tsaye Fatuu tay a wurin tamkar an dasa ta zuciyarta sai harbawa take da k'arfi k'afafuwanta na d'an yin rawa, ta d'auki lokaci a hana kafin jiki a mace ta zauna kan kujera, sosae Maganar Farhar ta k'arshe tay tasiri a kanta don yadda take nuna mata tsana tasan zata iya aikata mata hakan, da k'yar ta mik'e gwuiwowinta a sanyaye ta nufi Kitchen don ta d'aukko abunda zata gyara wurin, bayan ta gama gyarawa Bedroom ta shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay tsuru, in tace taji dad'in zuwan Farha tayi k'arya don tasan yanzu kwanciyar hankalinta ya k'are ba kamar data gane dalilin zuwan nata, k'arshe dai Abincin da bata ci ba kenan. Da daddare bata je part d'in ba balle taci Abinci sai kawae ta yanke ta dafa indomie taci, bayan ta gama dafawar bedroom ta wuce da ita, sam tama kasa sakin jiki taci indomie d'in don har bakinta ba dad'i take jin shi, yar kad'an taci ta mik'e ta maida ta kitchen, komawa tay Bedroom ta haye gado ta zauna ta shiga duniyar tunani, a ranta take raya ita bata ga amfanin wannan auren ba dama su rabu kawai ta huta don ba komai a cikin shi sai tashin hankali gashi wanda take zaune don shi ya yi tafiyar shi ya barta ko damuwa bai yi da ita ba, daga tafiyar shi zuwa yanzu zata iya k'irga sau nawa suka yi waya itama ba wani Magana mai tsawo ba iyaka ya tambayi yadda take ko chat basu yi, idanunta ne suka ciko da k'walla saidai bata bari sun zubo ba don itama yanzu har ta gaji da yin kuka, tana haka Mino ta shigo ta k'ak'alo murmushi tayi mata ta nufo ta itama tana murmushin, a bakin gadon ta zauna ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata gwaggo na gaishe da ita ta d'aga kai, tambayar ta tay ko bata lafiya ne ko wani abu na damunta taga kaman fuskarta ta canza tana murmushi tace mata lafiyar ta lau ta tambayi taci Abinci tace eh bata dad'e data gama ci ba, ce mata tay akwae sauran indomie data rage a Kitchen in zata ci, mik'ewa tay tace to bari ta d'aukko. Bayan sun gama shirin kwanciya Mino ta kwanta ita kuma ta d'aukko jakar ta don tayi karatun test da suke cikin yi Saboda exam d'in su ta matso, tana zaune a kan gadon tana karatun aka turo kopar ta kai idon ta da sauri don bata tsammaci wani ba a lokacin mantawa ma tayi bata kulle kopar ba, Farha ce ta shigo tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta sanye da hula, nufo cikin d'akin tay cikin d'acin rai ta tsaya bakin gadon tana masu kallon rashin Arzik'i, nuna Mino tay a wulakance tace "Who is she?" shiru Fatuu tay kaman bazata tanka mata ba sai kuma ta bata amsa da kanwarta ce, tafa hannuwa Farhar ta shiga yi da alamun mamaki tace wato har talakawan yan'uwanta ke zuwa kwakwa suma kenan" banza Fatuu tay mata tay k'wafa a fili ta furta duk zata yi maganin su, ce mata tay anan zata kwana don haka ta tasheta ta bata wuri, Fatuu dake kallon ta tace mata ai ga wuri nan sosae ba sai ta kwanta ba, yamutsa Fuska tay ta furta "God forbid! ni zan kwanta da pauper kina son ta goga man talauci ne" ta d'age ma Fatun gira tana kallon ta shek'ek'e, tasan fitina take nemanta da ita hakan yasa ta kai hannu ta fara tada Mino d'in, bayan ta farka tace mata ta saukko daga kan gadon, tambayar ta tayi lafiya tace mata eh kawai, saukkowa tayi ta tsaya sai lokacin ta lura da Farha dake mata kallon k'ask'anci, ganin yanayin fuskar ta yasa bata ce mata komai ba, wardrobe Fatuu ta bud'e ta fiddo bargo tazo ta shimfid'a ma Mino a saman Carpet ta d'aukko mata filo, bayan ta gama tace mata ta kwanta anan, da alamun rashin fahimta tace mata miya faru bazata kwanta a gadon ba kafin ta bata amsa a fusace Farha tace daga gidan uban su aka kawo shi ne, waro ido Mino tayi baki a d'an bud'e take kallonta ba tare data ce komai ba dama ita bata da rigima Fatuu ce mai rigimar yanzu kuma tayi sanyi lakwas, kwantawa Mino tayi itama Fatuun ta zauna a gefenta taci gaba da karatun, bata dad'e da zama ba taji Farhar ta watso mata zanin gadon dake shimfid'e a kan gadon da duvet harda pillows, hannu ta kai ta cire bedsheet d'in daya rufe mata fuska rai a 6ace tace mata ba gadon take so a bar mata ba kuma gashi nan an bar mata miyasa zata watso mata kaya tana yatsina tace ta d'aukko mata wasu wad'annan an goga masu talauci, sosae ran Fatuu ya 6aci bata dai ce mata komai ba kaman bazata d'aukko ba sai kuma ta mik'e taje ta fiddo wasu ta kawo mata ta aje akan gadon ganin zata juya tace mata bazata shimfid'a mata ba ko banda gadon rashin Arzik'i harda gadon rashin iya tarbar bak'o tayi, bata ce mata komai ba ta shiga shimfid'a mata, bayan ta gama ta koma ta kwashe wanda ta watso ta linke su ta kai Wardrobe, gaba d'aya Fatuu ta kasa yin karatun don tun bayan data kwanta ta fara kunna wak'ok'i gashi ta k'ure volume, k'arshe mik'ewa tay ta d'auki books da jakar tata ta fita daga d'akin ta koma parlor, bata dad'e sosae da komawa ba sai ga Mino ta fito a gigice tana kuka jikinta sharkaf da ruwa sai kerma take ta nufo cikin parlon, da sauri Fatuu ta mik'e ta tarbeta tun kafin ta tambaye ta abunda ya faru ta shaida, rai 6ace ta tambayi mi tayi mata ta watsa mata ruwa tace itama bata sani ba kawai tana cikin bacci taji ta watsa mata su da yawa, duk yadda Fatuu ta so kar tayi kuka ta kasa jurewa sosae Mino ta bata tausayi, zaunar da ita tayi kan kujera tace tana zuwa, Bedroom ta nufa saida ta tsaya a bakin k'opa ta goge Fuskar ta sosae sannan ta shiga, tsayawa tay daga bakin gado rai 6ace take kallon Farha dake latsa waya tace "mi tayi maki kika watsa mata ruwa haka!" banza ta mata sai kace bada ita take ba, k'ara maimaita tambayar Fatuu tayi saida ta mula sannan ta d'ago ido cike da isa tace snoring take mata daga haka ta maida idon kan waya, shiru Fatuu tay tana mata wani kallo jin sharrin data ja ma Mino na wai munshari take mata ita tasan bata yin shi tunda tare suke kwana, tunowa da ta baro Minon a jik'e yasa ta juya ta nufi wardrobe, kayan da zata canza ta d'aukko da su bedsheet d'in da Farha ta watso ta kinkima ta fita, bayan ta bata kayan ta canza tayi mata shimfid'a akan Carpet d'in parlon tace ta kwanta, kallon Fatun tayi ta tambaye ta wacece Farha nan ta bata labarin ta harda dalilin daya sa take mata hakan,
"to ki fad'a ma Hajiya abunda take mana" shiru Fatuu tay tana nazari can tace mata suyi hak'uri kawai yanzu in ta fad'i ma Hajiya ta d'auki mataki akanta Mamar ta itama tana iya yi mata wani abun, kamar Mino zata yi kuka tace to yanzu haka zasu cigaba da zama tana masu haka, shiru Fatuu tay gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i can tasa Kuka bak'in cikinta wanda duk ake mata haka Saboda shi baima damu da ita ba ganin tana kukan yasa Mino d'in ma cigaba da yi, daina yin kukan Fatuu tayi tace itama ta daina komai zai wuce bada dad'ewa ba, rok'onta tayi akan Kada ta fad'i ma gwaggo tace to tace ta kwanta, zaune Fatuu tayi ta kasa cigaba da yin karatun ma idon ta akan Mino dake kwance ta lullube, wani irin tausayin ta take ji tunani take ko tace ta daina zuwa kwanan saidae tasan dole gwaggo zata tambayi dalili, haka tay zaune tsawon lokaci sai can dare ya nitsa sannan ta kwanta,
Washe gari da wuri Fatuu tace ma Mino taje gida sai ta k'ara yin baccin acan tace to baiwar Allah harda ce mata to tazo suje tare tunda ba Makaranta itama tayi baccin tace mata a'a ko taje gwaggo korota zata yi, kaman bazata tafi ba tsoronta kada ta tafi Farhar tayi ma Fatun wani abu haka dai ta tafi, bayan tafiyarta Fatuu ta kwashe kayan shimfid'ar ta maida d'aki Farha na kwance baje baje ko salla bata tashi tayi ba, dawowa parlor Fatuu tay ta zauna tama rasa mi yakamata tayi, tsawon lokaci tana anan saiga Saude tazo kawo mata breakfast, akan c-table ta d'aura suka gaisa ganin yadda Fatun tayi tsuru yasa ta zauna tana tambayar ta miya faru a sanyaye tace mata ba komai, tana shirin k'ara yi mata magana sai ga Farhar ta fito duk suka kalleta ta wurga masu wata uwar harara ta wuce, bayan ta fita da alamun mamaki Aunty Saude ta kalli Fatuu tace mata mi tazo yi nan ne taga ta fito daga Bedroom, shiru Fatuu tay ta sunkuyar da kanta nan take Aunty Saude ta gane da wani abu dama gashi ta isketa tsuru a parlor, matsa mata tayi kan ta fad'i mata Fatun ta fara fad'i mata duk abunda tayi masu da cewar da tayi zata saka mata poison a Abinci tana yi tana goge kwalla, ran Saude ne ya 6aci tace aikuwa yanzu zata je ta fad'i ma Hajiya dama ita tasan ba abun Arziki ya kawo ta ba, rik'eta Fatuu tay ta hau yi mata Magiya kan karta fad'i na Hajiya tunda tasan ba dundundun ta zo ba ta k'yaleta tayi ta gama yanzu in aka fad'i ma Hajiya tana iya cewa ta koma gida kuma Hajiya Maryam zata ga an korar mata D'iya Saboda ita koma bata yi niyyar yi mata wani abu ba hakan na iya sawa ta cutar da ita tunda dama gani take suma kamar asiri sukai ma Hajiyar, shiru Aunty Saude tayi tana nazarin Maganar, da damuwa tace to yanzu haka zata k'yaleta tay ta mata rashin mutunci, d'an murmushi mai cin rai Fatuu tay tace mata ba komai kawae dai tana son ta taimaka mata zata daina zuwa cin Abinci bata son Hajiya ta gane koda tayi mata Magana tace tana zuwa amsa ala bashshi sai ta rink'a dafawa kawai, cewa Saude tay ta bari zata rink'a kawo mata tasan yadda zatayi Hajiyar bazata tuhumi dalilin daina zuwan nata ba Fatun tace ta barshi kawae tunda akwae kayan Abincin tace amman ya za'ai ace sai ta dawo daga Makaranta sannan ta dafa kawai zata cigaba da kawo matan in yaso randa ba Makarantar sai ta dafa tayi mata godiya.
A daddafe tayi Weekend d'in nan, Ranar Monday tunda taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta tana cikin damuwa don har fad'awa fuskarta tayi, bayan anyi break ne ta tambaye ta abunda ke damunta nan ta kwashe game da abubuwan da Farha take mata ta fad'i mata, tun kafin ta gama yanayin fuskar Fauzy ya canza bayan ta gama fad'i mata rai a matuk'ar 6ace tace "inta fasa kashe ki bata haihu K'wara ba don ubanta! ke kika k'yaleta wllh" yamutsa Fuska Fatuu tay tace to ya zatayi, a hasale Fauzy tace "wane ya zaki yi, ba ita take neman ki da rigima ba, kamata zaki ki lakad'a mata shegen duka kinsan dama irin haka sai kun had'a jiki mutum yaji a jikinshi sannan yake shiga taitayin shi" sakin baki Fatuu tay tana kallonta Fauzyn tace "ko tafi k'arfin ki ne? In tafi k'arfin ki ni ki bari in zo mu had'u mu had'a mata jini da mijina wllh zaki ga ta kiyaye ki" da sauri Fatuu ta hau girgiza mata kai tace ba zasu yi haka ba a kyaleta kawai, a hasale Fauzy tace "Wato kin fi son tay ta cusa maki bak'in ciki ko har wani ciwon yazo ya kamaki ga jarabawa a gaban mu" watsa hannu Fatun tay ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tace "Fauzy ko mi zatai man tayi ba kowa yaja man ba face Ya Haisam, duk abunda ake man Saboda shi ne kuma shi bai damu dani ba ya tafi ya barni Saboda bai sona, na tabbatar da yana sona ba yadda za'ai ya tafi tsawon wata guda da rabi ba tare da ya waiwaye ni ba tunda yana da halin ko duk sati yaso zuwa nan hakan ba wani abu bane a wurin shi, ni na rasa gane kan wannan Auren namu da yasan haka zai man da tun farko bai amince yaci gaba da zama dani ba, in don abunda ya faru ne naje na bashi hakuri kuma yace ya hak'ura to miyasa ya canza man, miyasa bai damu dani ba...., miyasa son shi yak'i barina kwata kwata, miyasa nike tunanin shi tunda shi bai damu dani ba....miyasa ba zai sake ni ba kawai in San ban tare dashi ko na cire shi daga cikin zuciya ta....." tana Maganar k'walla na zubo mata har tazo ga6ar da ta saki kukan mai cin rai ta fad'a jikin Fauzy da itama kwallan ne suka fara zubo mata, wani irin tausayin ta da bata ta6a ji ba ya kamata ta shiga d'an bubbuga bayanta tana rarrashin ta, ita kanta ta fara kokonton anya Ya Haisam na son Zarah kaman yadda suke hasashe kuwa, zuciyar ta ce ta fara raya mata aikata wani abu......
Kafin a tashi tace ma Fauzy zata rink'a bin ta Hostel sai yamma ta koma gidan don gaba d'aya bata jin dad'in gidan tace to Hajiya fa ba matsala taga bata komawa da wuri tace zata fad'i mata suna tsayawa karatun jarabawa ne tasan zata fahimta tace to, kiran Tk tayi ta sanar dashi kada yazo d'aukar ta ya d'aukko Mino kawai ita sai yamma zata dawo kuma ba sai yayi wahalar zuwa d'aukarta ba zata hau Keke Napep, bayan an tashi suka nufi Hostel, suna zuwa salla suka fara yi bayan sun gama Fauzy ta had'a mata Madara da biscuit tace ta fara sha bari ta dafa masu Abinci, tana gama sha lokacin Fauzy na cikin dafa masu Abincin ta mik'e tace bari taje ta watso ruwa har Fauzy nace mata zata iya shiga toilet d'in su kuwa tana yar dariya tace mi zai hana, cire kayanta tayi ta d'aura towel Fauzy ta kalleta tace mata wllh duk tayi d'an wuya tay murmushi kawai, bayan fitar ta Fauzy ta mik'e ta nufi inda ta tashi ta zauna ta kai hannu ta d'auki wayarta, zurfin tunanin anya Ya kamata tayi abunda take tunanin yi kuwa ta shiga, fargaba ce tay mata yawa ta maida wayar ta aje ta bar wurin, bayan Fatun ta fito tace ma Fauzy ta bata yar riga mara nauyi tasha iska kafin ta tashi tafiya ta d'aukko mata, bayan ta gama saka rigar hayewa tay saman gado ta kwanta suna d'an yin hira da Fauzy, a hankali ta fara lumshe ido Fauzy na fad'in kada tayi bacci bata ci Abincin ba tace ai ba yunwa take ji ba in ma tayi sai ta ci in ta tashi, baccin ne ya dauketa Fauzy ta zuba mata ido tana ta wasi wasin abunda take son yi acikin zuciyar ta can ta mik'e ta nufi gadon da take ta kai hannu ta d'aukko wayarta ta dawo ta haye saman gadon zuciyarta nata harbawa hannuwanta har d'an kerma suke ta shiga daddana ta......."
____________________
Fanan zaune asaman doguwar kujerar dake a cikin parlon su ta haye saman ta gaba d'aya tana sanye da yar fingilar riga da iyakarta tsakiyar cinyoyinta hannun ta kuma irin na vest kaman dai rigar bacci ce ta d'an rankwafa tana lallatsa computer d'in dake gabanta hakan yaba brown gashin ta damar zubowa ta gefe da gefen fuskar ta, daga gefen ta kuma takardu ne lokacin su can dare ne don har anyi sallar isha, tun bayan da Haisam ya aje wayar shi ya tafi had'o masu Coffee take ta damun ta da k'arar notifications, dakatawa tay ta kai hannu ta d'aukko wayar don ta kashe Wi-fi d'in wayar ko sakonnin sun daina shigowa, tana latsa power haske ya kawo jikin Screen d'in idon ta ya sauka akan sunan da tasan ya saka ma Fatuu alamar ta turo mashi sako, d'an murmushi Fanan d'in tayi a ranta ta raya wato da ita ne ta daina zumunci kenan, bayan ta kashe ta maida wayar ta aje, har taci gaba da abunda take kawai taji tana son ganin sak'on miye Zarah ta turo mashi, hannu ta kai ta d'aukko wayar ta sake kunna hasken ta bud'e, kan sakonnin WhatsApp ta danna ta shiga ciki, sak'on Fatuu ne last da aka turo hakan yasa ya kasance a sama ta kai hannu ta ta6a ya bud'e, gyara zama tayi ta fara Karantawa...................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
* ASM 071*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........A nutse ta fara karanta sak'on wanda ke bayyana sirrin zuciyar wadda ta turo wato Zarah, bayanin tun lokacin da Allah ya jarabeta da son shi da irin wahalar da ta sha hakane ma yasa ta amince ai mata Aure Saboda ta rasa shi har Allah ya juya Al'amarin ya aureta, Hak'uri ta bashi kan zargin shi da tayi ta nuna bata san akwai Aure ba a tsakanin su kuma Saboda son da take mashi ne yasa taji zafin abun sosae hakane ma yasa data samu ciki tak'i saurarar shi harta 6arar don kuma bata son girman shi ya zube a idon mutane duk don k'aunar shi da take, a k'arshe ta nuna mashi tana cikin mawuyacin hali Saboda canza mata da yayi a yanzu da burinta ya cika ta zama Matar shi, Hak'uri ta k'ara bashi tace in don cikin da ta 6arar ne yake nuna mata halin ko in kula in sha Allah zata biya shi fin shi ma amman tana a cikin matsananciyar damuwa da har tana son shafar karatun ta........., Tun Fanan na karantawa lafiya lau har ta kai yanayin Fuskar ta ya fara sauyawa, lokacin data gama karantawa d'agowa tay da yanayin d'aurewar kai ta kallo hanyar Kitchen da Haisam ke ciki, k'ara maida idonta tayi akan Screen d'in tana sake biya sak'on lokaci guda hannuwanta suka fara yin kerma ta zuro da fararen k'afafuwan ta k'asa, Slowly ta mik'e har lokacin tana cikin k'ara karanta sak'on, saida ta karanta shi sau ukku tamkar mai yin hadda, gaba d'aya ta kasa gasgata abunda take karantawa gani take kamar ba daidai take karatun ba ko kuma ba sak'on Haisam d'in bane hakan yasa sai k'ara maida idonta take tana k'ara karantawa, zuciyar ta ce ta shiga gasgata mata sak'on shi ne in ba haka ba mizai sa ta turo mashi kuma ga alamu nan a bayyane har sunanta an ambata a ciki kan ciwon da ta yi lokacin da Fanan d'in tazo......."Kenan Auran Zarah ya yi a 6oye???" ta fad'a acikin ran ta, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi mata ta fara numfashi da k'arfi har saida ta d'an bud'e baki jin numfashin na neman yi mata wuyar fitarwa, tana haka Haisam ya shigo cikin parlon yana sanye da wando 3 quarter da armless hannuwan shi duka biyun ruk'e da mug d'an tiriri na fitowa alamar abun ciki mai zafi ne, wani irin kallon tashin hankali ta shiga bin shi da shi hakan yasa shi dakatawa daga d'an gabanta yana kallon ta shima har saida gaban shi ya d'an fad'i ganin yanayinta da kuma wayar shi dake hannunta don yanayin kallon da take mashi na tuhuma ne, nufo shi tay a fujajen tana zuwa fuska a hautsine ta d'aga mashi wayar shi dake hannunta daidai kan sak'on a kid'ime tace "Don't tell me dis message is for you!!!" maida idon shi yay akan Screen d'in ya gane Zarah ce ta turo saidai bai fahimci miye akace a sak'on ba, wucewa yay yaje ya aje mugs d'in akan c-table ya juyo lokacin itama ta juyo tana kallon shi, hannu ya kai ya amshi wayar ya fara karanta message d'in a nutse har ya gama, d'agowa yay ya kalleta ta kafe shi da idanunta da ta zaro Fuskarta har ta fara yin ja alamar motsuwar jini, shiru yay kawai yana kallonta yama rasa mi zai ce mata don komai sak'on ya bayyana, girgiza kai ta shiga yi tana fitar da numfashi da k'arfi cikin d'an k'araji tace "so it's true, You married Zarah without my knowledge!" still bai ce mata komai ba aikuwa ta daka mashi tsawa a gigice tace "tell me! is she ur Wife??" d'an cize lip d'in shi yay na k'asa Slowly ya lumshe mata ido nan take ta gane mi hakan ke nufi, cikin fitar hayyaci ta fara ja da baya tana cigaba da girgiza mashi kai, bin ta ya fara yi yana ce mata "I can explain myself..." a haka har ta dangane da kujera kawai sai ta haye saman ta gudun kada ta yi ma kanta wani abu yasa shi kai hannu zai kamo ta ai kuwa ta tafi gaba d'aya ta wuntsila bayan kujerar ta fad'a saman tiles daga jin k'arar ba K'aramin bugawa tay ba, juyawa yay da sauri ya zagaya lokacin har ta mik'e tana k'ok'arin rugawa d'aki cikin zafin nama ya kamota ta fara kokowar kwacewa cikin k'araji fuskarta da idanunta sunyi jawur take fad'in "Leave me alone! Ya Haisam u'r a betrayer! u betrayed my trust, u broke the promise u have made to me! U deceived me....!" Gaba d'aya bata a cikin hayyacin ta idanunta sun jik'e da k'walla fatar k'asan idon tayi wani irin ja kamar jini, sai kiciniyar k'wace kanta take ta kansa sai rarrashinta yake yana ta tsaya zai mata bayanin yadda hakan ta faru amman ina tak'i sauraren shi fad'i take ba abunda zai fad'i mata ta san don ance tana da matsala shiyasa yayi tunanin bazata haihu ba yaje ya auri Zarah gashi nan har yayi mata ciki duk da Alk'awarin da yayi mata, abu fa ya ture gaba d'aya Fanan ta burkice mashi duk ta rud'a shi har fuskar shi ta bayyana, da dai taga ta kasa kwacewa kawae sai ta kai bakinta a jikin damtsen shi dake a bayyane ta daddage ta gartsa mashi cizo aikuwa ba Arzik'i ya saketa Saboda rad'ad'in Azabar da ya ratsa shi wurin har ya fashe nan da nan jini ya fara zubowa, ai yana sakinta ta watsa a guje hanyar Bedroom yana ganin haka shima ya bita don ya fahimci abunda take son aikatawa haka take da ranta ya 6aci sai ta ruga ta kulle kanta a cikin d'aki, ko kafin ya cimmata tuni ta shige lokacin daya kai hannu cikin zafin nama zai bud'e kopar data turo tuni har tasa Key, bugun k'opar ya fara yi da d'aga Murya yana kiran sunanta yana ta bud'e karta yi ma kanta illa, tana shiga d'akin a haukace ta nufi bango ta fara kai mashi bugu tana wani irin kuka na fitar hayyaci, har saida knuckles d'inta suka fara fitar da jini sannan ta daina ta nufi gado ta zauna dabar tana cigaba da kukan, a ranta ta fara tariyo sak'on aikuwa ta k'ara tsananta kukan ta fara sambatu tana fad'in Ya Haisam da Zarah sun ci amanarta, tunowa da Maganar ciki da ta samu tasa ta kai hannu ta fara bugun Katifar hakan bai sa ta samu sassaucin abunda take ji ba acikin zuciyarta sai ma k'ari nan fa ta mik'e ta fara wurgi da abubuwa abun har ya kai da fashe fashe, gaba d'aya hankalin Haisam ya gama tashi sai faman bugun k'opar yake da k'arfi yana kiran sunanta yana fad'in kada tayi ma kanta wani abu ta bud'e kopar, har ta kai ya fara mata Magiya ko tana jin shi ma oho ba dai alamun zata bud'e,