Kenza eBookz

Aure ko boko book 3 complete - Chapter 6

Aure ko boko book 3 complete - Chapter 6

Aure ko boko book 3 complete Chapter 6: Aure ko boko book 3 complete Chapter 6. Halimah ta sandare da waya a hannunta daga kwancen da take, ta rasa a…

3,306 words

Halimah ta sandare da waya a hannunta daga kwancen da take, ta rasa a yanayin da maganar matar ta zo mata. Daddy a gidanta? Wato Hanan sai da ta kawo shi hankalinta ya kwanta?

Ta dubi Hashim, shi kuma ya bude mata kyawawan idanunsa da suka kada cikin neman karin bayani. Kokarin sumbatar tafin kafar ta yake yi ta janye,

“Ka tashi Your Excellency, wai Daddy ya zo gidan nan. Ban san da wacce ya zo ba”. Hankalinta a matukar tashe yake don da gaske ba ta san da wacce ya zo ba. Ta san Hanan ba za ta ci amanarta ba, amma yanzu ta san tunda sun zama prominet political figure nemansu ko sanin inda suke ba zai yi wa Daddy wuya ba.

Hashim ya kama Halima da dukkan hannayensa, murmushin kwantar da hankali ya yi mata, sannan ya sumbace ta son ransa, “Go to your father Halimah… na tabbata alkhairi ne ya kawo shi. Ki karbe shi da duk wacce ya zo da ita. In ba mu kasance masu yafiya ba musamman ga iyayenmu, to hakika ba mu gode falalar Ubangiji a gare mu ba”.

Ya mikar da ita tsaye, da kansa ya canza mata rigar barcin jikinta zuwa doguwar rigar abaya, sannan shi ma ya canza. Ya dauki waya ya bada umarnin a shigo da bakin nan har falonsa.

Hannun Hashim cikin na Halimah, a lokacin da suke saukowa daga matattakalar bene. Safiyyah ba ta gidan, an kai ta wata makarantar makafi ta musamman a kasar Ingila (West of England School for the Blind, Exeter).

Daga nesa Halimah ta tsaya tana kallon mahaifinta, Prof. Zubair Numan, ya tsufa matuka, sannan ga alamu na rashin wadatar lafiya a tare da shi. Dogon wandon sa ya boye tabon kafar sa. A gefensa Hanan ce da Baffa Modibbo Hussaini.

Da gudu Hanan ta taho ta rungume Halimah, wadda ta tsaya a inda take, ta kasa cira kafa gaba, ta rasa a wane yanayi ta tsinci kan ta, Hanan kuka ta ke tana rokonta ta yafe wa Daddy, yayin da Prof. ke takowa zuwa gaban Halimah yana hawaye. A yadda ya ga Halimah da Hashim sai tsoron Allah ya kara ratsa zuciyarsa. Ba su yi aune ba suka ga Prof. ya zube gwiwoyinsa a gaban Halimah ya rike kafafun ta yana ta kuka.

Da sauri Hashim ya tsugunna ya dago Prof. Numan. Halimah ta rungume mahaifinta ta saki kuka mai tsuma rai. Shi yake neman afuwa da gafarar su, amma kukan da yake yi ya sa ko muryarsa ba ta fita sosai. Haduwar Halimah da mahaifin ta Prof. Numan bayan wucewar shekaru goma is very emotional… ya yi nadama… ya yi nadama… ya yi nadama! Ya ga ishara iya ishara.

Daga Hashim har Halimah babu wanda bai tausaya wa Daddy ba, suka kuma yafe masa da kyakkyawar zuciya.

Tun a satin suka tafi da shi asibiti a Egypt don a binciki lafiyarsa ciki da bai, cututtuka kala-kala likitoci suka gano a jikin Prof. Numan, sukari (diabet), hawan jini sannan kodarsa ta tabu.

Hashim da Halimah suka tsaya tsayin daka a kan lafiyar Prof. Numan, har ya warware. Tun a Egypt da Hanan ta gayawa Hashim abinda ya faru da Daddy da gidan su na Abuja yake wani shiri ba tareda sun sani ba. A karshe ya taho ya baro su tare da mahaifin su a kasar Egypt, yace su huta sosai, sai ya ce su dawo sannan su dawo.

Wannan zama da sukayi a kasar Egypt tareda Daddyn su a daki guda ya farfado da soyayyar su ta tun fil azal. Suna ta kula da shan magungunan sa. Motsi kadan yace “Halimah….Allah yayi miki albarka”. Hanan ta ce cikin shagwaba “ni ban da ni?” “Har dake autar Daddy, amma ta Halima special ce, kamar yadda take special a gareni”. Hanan ta ji kishi tasa kukan shagwaba, sai ya jawota jikin sa yana lallashi yace “a ko’ina akwai auta, kuma Hanan ita kadai ce autar Daddy, shalelen Daddy”.. duk suka fashe da dariya.

Yaji labarin Safeeyah iri-iri a bakin Hanan, Daddy sai da ya kara yin kuka. Ya tuna bakin da yayiwa Halimah da tsohon ciki. Yayi ta istigfari yana rokon gafarar Halimah. Halimah tace “Daddy, nifa ban yarda bakin ka ne ya kama Safeeya ba, Ubangiji na yin halittar sa ne yadda ya so, da baki ko ba baki. Don haka don Allah kada ka kara tunanin kai ne silah”.

Ya dauki baby Zarah yana mata wasa yace “amaryata Zahra’u duk kyan nan naki makauniyar nake so a matsayin uwargida, don Allah ku kaini in ganta”. Halima tace lokacin hutun su ya kusa, zata dawo gida maybe kafin mu koma ma”.

Hashim yayi musu waya cewa su taho, kuma su sauka ta Abuja. Hakan kuwa aka yi.

Halima da Hashim kwance a bayan mota ‘Rolls-Royce’ data dauko su daga filin jirgin saman Nmadi Azikwe hannun Halimah cikin na Hashim yana murzawa a hankali, cewa yake “me kike shafawa hannun naki haka Leemah? Laushin ya isa, kamshin ya isa, kada ki haukata ni daren yau, na sha wahala wata guda fa, Allah kadai yasan yadda akai na kawo yau inda nake”. Halima sai dariya take masa da fararen hakoranta. Tana kara shigewa jikinsa. Hanan da Salim mota daban suka shigo tare da Daddy.

Sai gani tayi direba ya dauke kan motar zuwa unguwar su, unguwar data yi duk wata dabdalar kuruciyar ta zuwa girmanta wato Asokoro. An kuma doshi get din gidan su.

Seun, ya bude tangamemen get din, da Halima ya fara tozali da mijin ta kwance a bayan mota, dadi da farin ciki suka rufe shi. Yace “H for Halimah H for Hanan”. Bakin sa kawai Halima ta kalla ta gane abinda ya ce. Murmushi tayi tana daga masa hannu. A lokacin ne Halima ta daga ido ta hango wani ‘cute mansion’ wanda yafi gidan su na baya tsari da kawatuwa. Da sauri ta juya ta dubi Hashim, shi kuma ya lumshe mata ido, yace.

“Safeeyah da Zarah sun gyarawa angon su gida ne. Suna neman albarkar sa…”. Halimah ta fada kirjin Hashim da karfi ta saka kuka.

Shikuwa Prof. Hawaye yake yi yana shiwa Hashim da Halimah albarka. Yana cewa cikin ransa;

“Watakila har ya mutu baza’a daina nuna masa ishara ba…..”.

****

Sun tafi sun bar Daddy a sabon gidan sa karkashin kulawar su Seun, Minister Usman Baban Salim shi ya tsaya wajen ganin Daddy yayi (court affidavit) na takardun kadarorin sa da suka kone, don ganin cewa ya sake mallakar su.

Itama Zarah Datti, ta kira Halimah a wannan daren tace gata a kasar Mexico musamman don ta sake karbawa Halima takardun karatun ta ta biyo maigidanta Mexico wani aiki da ya kawo shi. Tace Halima tayi affidavit na takardun ta ta tura mata online ba sai ta je ba. A karo na farko da Halimah ta ji sabon ‘hope’ akan ilmin da ta sha wahala ta yi. A da, ta dauka ta baiwa takardun nan baya kenan bazata kara waiwayar su ba har abada. Amma tunda ta karbi Daddy, ai dole ta karbi takardun ta. Kaddara ce Allah ya rubuta musu kuma ta riga ta faru, an jarrabesu sun kuma cinye jarrabawar su, dole yanzu su karbi kyakkyawan sakamakon da Ubangiji yake ta yi musu. In har sun kasance masu godiya a gare shi.

Ta je aka yi mata affidavit, ta rubuta application ta yi scan ta turawa Zarah. Kafin sati sai ga gabadayan takardun Halima sun dawo mata. Ta yi kuka ta yi kuka ta godewa Allah. Ta yi musu kyakkyawan adani tare da takardun Hashim.

Duk da haka bata da wani buri da su bayan ajiyewa. Ta riga ta sadaukar da rayuwar ta da lokacin ta da ilmin nata ga maigidanta da iyalin ta. Tunda ba abinda ta nema ta rasa daga mijin ta abin kaunar ta, Hashim. Gagara-gasa a cikin maza, mijin marainiya, namiji dan goyo (inji Halimah).

An saka daurin auren Daddy da Addah Saddiqa a Numan sati mai zuwa, don haka a gabadayan satin nan shirye-shirye suke yi da shirin tafiya Numan ranar alhamis, kasancewar Juma’ah bayan masallaci za’a daura auren.

Hanan ta kira Yayarta Halimah cikin raha tace “Sis Leemah, ya kamata mu hadawa Daddy lefe fa na gani na fada”. Dariya Halimah tayi ta ce “kin kawo shawara mai kyau, yanzunnan zan sa Sa’adatu ta hado komai tunda sana’ar ta kenan”.

Hashim da Halimah sun dade da baiwa Sa’adatu kanwar Hashim jari mai tsoka tana zuwa Dubai tana shigo da kayan sanyawa na mata, lesussuka, dogayen riguna da takalma da jaka na mata, ta bude kayataccen shagon ta a kantin kwari, international business take ba kama hannun yaro kuma Allah yasa mata nasibi a ciki. Dr. Rabi’ah kuwa duk da ba wani mugun shiri ne tsakanin ta da Halimah ba kamar Sa’adatun itama basu barta haka ba, a baya a Legal take koyarwa amma yanzu Hashim ya maida ta jami’ar Abuja (Gwagwalada). Sannan ya bata jari kwatankwacin na Sa’adatu. Ta karba, amma tace ita bata ra’ayin kasuwancin aikin ta ya wadace ta.

Kulawar da take baiwa Halimah yanzu, ko itace Inna sai haka, duk da a cikin ranta tana fadin Halima ta cikawa Hashim gida da ‘ya’ya mata da makauniyar da bazata moru ba, saidai ta zame masa liability, amma a wajen Halima Dr. Rabiah ta riga ta baro gini tun ran zane, ba wani abu da zata yi mata na nuna kauna a yanzu da zai wanke dattin ta riga ta yaba mata a zuciyarta acan baya.

To dama babu yadda za’ayi ace mace ta rayu babu irin wannan daga dangin miji, koda ba dukkansu ba, musamman Hashim da ya daukaki Halima a idon duniya bakidaya, baya zartar da komai sai yayi shawara da ita saboda ya yarda da intellectual positive thinking din ta. Ana rade-radin ma baya daukar shawarar mashawartan sa sai ta Engnr. Halima Numan (Mrs. Engnr. Hashim Yakasai). Akwai lokacin da Dr. Rabiah ta yi masa wannan shaguben; cikin raha; da kai da Halima bamu san wanene gwamnan Kano ba. Hashim sai yayi murmushi kawai ya girgiza kai.

Abinda ya sani shine; idan ana bada kujerar bakidayan ta zai iya baiwa Halimah Numan, karewar daukar shawarwarin ta, wadanda duk na ilmi ne da taimaka masa ga kaiwa ga nasara cikin siyasar sa. Kai sai ka dauka akan ‘Political Science’ tayi dukkan karatun ta. Nan kuwa ba komai bane tsabar bincike ne, bincike take yi ba dare ba rana akan ‘political theories and tactics’ tana dora mijin ta bisa turbar shahararrun political scholars irin su John Situart Mills, Adam Smith, Max Weber, Thomas Hobbes, Anthony Giddens, Karl Max da sauran su wadanda sune suka kirkiro ilmin siyasa a zamanance.

Babu son zuciya ko fariya a cikin shawarwarin Halima, sannan bata almubazzaranci da dukiyar al’ummah duk da damar hakan data ke da ita inda halin ta ne. Ita kawai (Legal Adviser) ce ta Hashim bayan Alhaji Datti, kuma tana da albashinta mai tsoka akan hakan daga aljihun gwamnati.

Sa’adatu ta kammala hadawa Daddy lefe ta dauko akwatunan har set 3 ta kawowa Halimah, Halima na dubawa tana yaba komai, an zuba komai mai inganci na gani na fada tamkar Addah Saddiqan da za’a kaiwa yarinya ce budurwa, suka kwasa suka tafi Numan.

Kwana biyu da zuwan su Baffa ya daura auren Daddy da anty Saddiqah, da ta ga lefen da su Halima suka yi mata sai da ta fashe da kuka, ta kudurtawa ranta rike marayun nan da uban su tsakani da Allah da dukkan amanar da zata iya.

A wannan zuwan da su Halima suka yi Numan, duk wani jinin Malam Muhammadu dana su Modibbo Hussaini sai da ya shiga list din wadanda Hashim zai samarwa sana’a kwakkwara, ko aiki ga wadanda suka yi karatu, kowa ya san a wannan bangaren gwamnatin sa tafi bada karfi, kuma ya shigo siyasa ne solely akan hakan sabida yanada good experience da feelings din matasa marasa aikin yi. Halima ganin irin hidimar da Hashim ke yi da danginta wani tunani ya darsu a ran ta.

Bayan sun kaiwa Daddy amaryar sa Abuja sun juya gidajen su, a daren ranar Halima ta tadda Hashim a main falon sa, yanata sanya hannu a takardun kwangila da zai baiwa matasa masu (first class degree) a Kano, Halima na zuwa ta zaune masa bisa cinyoyi ta sunkuya ta sumbaci kwantaccen sajensa “time for bed Baban Safeeyah”. Wato lokacin kwanciyar su yayi.

Hashim ya ce “ki dan yi hakuri na karasa Leemah, in ban gama yanzu ba goben ba iyawa zan yi ba, inada wasu ayyukan masu tarin yawa a ofis…”. Ina! Halimah bata saurareshi ba domin sassanyar sumbar da take zuba masa, dama ta san “baya wuce tayi” kuma ba’a dauki dogon lokaci ba ta dora shi akan network yadda take so, aikin da ba’a karasa ba kenan har washegari.

Saida komai ya lafa, suna kwance cikin jikin juna tamkar a haka aka halicce su, Halimah tace “your excellency, yakamata mu je Sudan mu nemi dangin Inna”. Hashim yayi shiru, yana shafa kwantaccen gashin kanta bakikkirin. Wani tunani mai kyau da shi bai taba yi ba sabida yawan al’amuran dake kansa.

Yace “insha Allah Sweetheart, zamuje cikin wata mai kamawa, Yaya Rabia ta taba zuwa ta san adireshin su, zamu tafi gabadayanmu har yara lokacin Safeeyah ta zo hutu. Nagode da tuna min muhimmin abinda hankali na bai taba kaiwa ba. Har sauran dangin Baban mu in akwai zan nemo su duk inda suke.

Washegari ya kira Yaya Rabia ya gaya mata shawarar da Halimah ta kawo, Dr. Rabi’ah sai ta ji kunya, sun baje suna ta cin gajiyar mulkin Hashim sun manta da dangin Inna, sai Halimah ce ta tuna su. Tace “sunan garin su Inna Jazeera, yakamata mu tafi har Safeeyah su ganta”. Ya ce Safeeyah na nan zuwa hutu daga Exeter next week, har da ita zamu tafi insha Allah”.

Daga ranar Hashim ya soma yi musu shirin tafiya kasar Sudan dukkan su, cikin sati biyu komai ya kammala, Halimah ta ji dadin zuwa Sudan domin dangin Inna sun karramata, sun musu tarba ta musamman, kannen mahaifin Inna su biyu ne El-Bashir da El-Mansoor sai kanwar Inna Fadhilah tana da aure da ‘ya’ya takwas, sai kuma wata Kaka ga su Inna dattijuwa mai suna Saratu. Hashim yayi musu goma ta arziki, ya kuma yi alkawarin ziyartar su akai-akai in ya samu sarari, ko shi bai zo ba Halimah zata zo. Rashin zumuncin da aka yi a baya baza’a sake maimaitawa ba insha Allahu.

Har manyan gonaki ya sayawa El-Bashir da El-Mansoor kasancewar su Manoma ne a garin na Jazeerah.

Suka dawo gida ranar Lahadi, kowanne ya koma bakin aikin sa.

Shekaru biyu akan karagar gwamnatin Kano, Halimah Zubair, ta gama farfadowa, ta dawo ‘yar gayenta har fiye da baya sanda take shugabar NCC. Wannan duka ya faru ne da taimakon Zarah Datti, aminiyar kwarai. Halima ta saki duk wani kalubale da canjin rayuwa ya janyo mata. Kula suke da mahaifin su da matar sa sosai wadda ta kama su ta rungume da dukkan kauna da soyayya kamar ita ta haife su, dama kuma Yafendo ce a garesu.

Zarah na da shekaru uku Halima ta sake samun ciki, Allah mai girma da daukaka, wannan karon sai ga ‘yan biyu maza Allah ya baiwa Halimah.

Farin cikin da Hashim yayi ba mai misaltuwa bane, yayin sadaqah yayi kyauta har ba adadi don nuna godiyarsa ga Allah. Sai dai har gobe ko ‘yan 100 zai haifa yayi rantsuwa ga manema labarai babu kamar “Safeeyah” a zuciyar sa.

Dan sauran burbushin Halimah da Dr. Rabiah keda shi a ranta game da Halima kan cewa ta cikawa Hashim gida da ‘ya’ya mata sai ya karasa vanishing. Inda Allah ya taimaketa a zuciyar ta kawai take fadi bata taba furtawa Halima ko Hashim sun ji ba, la shakka da dan sauran kimar data ke dashi a idon Halimah ya karasa zagwanyewa.

Hashim kuwa karfin zumunci da girmansa a wurin Ubangiji yake dubawa da har ya yafewa Dr. Rabi’a abinda tayi musu ya cigaba da zumunci da ita, Halima kuma dama tun fil azal ba mai halin kullaci bace ga wanda ya saba mata. Kowa tana mashi uzuri ne, uzuri sau sab’in kafin tace yayi mata laifi.

Rainon ‘yan biyu, ba abu ne mai sauki ba ga kowacce uwa, duk da kuwa Halima na da mataimaka ‘ya’yan Baffannin ta na Numan da ‘ya’yan Aunty Habiba, dangin ta duka (paternal and maternal) sun samu kyakkyawan rufin asiri albarkacin Halima, komai su take dorawa bata fiya dora bare akan harkokin ta ba sai a inda ya kamata a ce baren ne zai yi. Balle kuma dangin Hashim da sai ta sa yayi musu sau dari kafin kowa nata.

Daga haihuwar twins wadanda Hashim ya sanyawa suna Mujahid da Mubarak, ba’a rufa watanni shidda ba sai ga sabon ciki a jikin Halimah. Hankalin Halimah yayi mugun tashi. Hashim ya fito daga wanka a ranar sai ya samu Halima zaune a gefen gado ta hada kai da gwiwa tana rasgar kuka.

Bai san sanda ya saki tawul din da yake tsane kai da shi a kasa ba, ya nufe ta da sauri ya dagota cikin rikon sa “lafiya Leemah? Me ya faru?” Halimah ta janye jikin ta ta sake komawa gefe tana cigaba da rusar kuka. Lallashin duniya Hashim yayi kafin ta iya gaya masa pt-strip ya nuna mata tana da shigar ciki.

“Mujahid da Mubarak are only 6 months Cheriè. Yaya zan yi dasu idan na kara haihuwa yanzu?”

Wata ajiyar zuciya Hashim ya saki kafin ya tarairayo Halimah ya rungume tsam-tsam.

“Zan taya ki da komai Sweetheart, inna ce komai ina nufin har nakudar, har rainon, goyon. Breast-feeding kawai zaki yi, shima don bani da shi a jiki na ne. Ko kullum zaki haifo min Da indai daga jikin ki zai fito ina matukar son sa Halimah.

Na roke ki, kada ki bari shaidan ya shiga zuciyar ki har yasa miki waswasi, ya raunata imanin ki. Haihuwa kyauta ce daga Allah da sai wanda ya ga dama yake baiwa. So ki sa a ranki Ubangiji ya san zaki iya shiyasa ya baki, tunda dai alhamdulillah muna da halin ciyar dasu da tufatar dasu, ilmantar dasu da tarbiyyantar da su. Pls Sweetheart kada ki karya min zuciya in yi tunanin kin soma gajiya da haihuwa da ni…..”. Da sauri Halimah ta toshe masa baki, ta hanyar sanya tattausan bakin ta cikin nasa. Cikin wani salo mai burgewa take sumbatar Hashim kusufa-kusufa. Al’amarin da bai yi masauki a ko’ina ba sai akan makeken gadon barcin su. Soyayya ‘yar usuli ta gaskiya wadda bata fading, sun kuma tabbatar bazata yi fading ba har ranar da suka daina numfashi.

Washegari kuma sun tashi da shirin tafiya Bauchi duba Alhaji Datti dake fama da rashin lafiya. Sun samu jikin nasa da sauki, Zaarah da yaranta ma suna gidan, nan suka hade da Zarahn Halimah sai kiriniya. Alhaji Datti yayi musu nasiha mai ratsa jiki kamar yadda ya saba ya karawa Hashim da hikimomin shugabanci kamar yadda yake masa kullum.

Da Halimah da Zarah suka kebe a dakin Maman Zarah, Halima ta kokontawa Zarah halin da take ciki na kwanikar data sameta. Amma kamar Hashim itama Zarah kwantar mata da hankali tayi, ta ce “ki godewa Allah Besty, nawa ne suke nema da kudin su basu samu ba har suke zuwa asibiti ayi musu artificial? Ba sai mun je da nisa ba akan haihuwa ko Hanan ta ishe ki ishara”.

Tun daga ranar Halima tayi wani kyakkyawan kuduri a zuciyarta wanda bata gayawa kowa ba.

Bayan sun dawo gida ta daidaici lokacin da Hashim yake cikin kyakkyawan yanayi, sai ta zo ta zauna a jikin sa, ta kwantar da kai bisa kafadarsa. Cikin wata lallausar murya take magana;

“Cheriè, ka yi min alfarma in hada kayan Zarah in kaiwa Hanan ita gobe -goben nan, amma ba hutu irin wanda take zuwa ba, na barwa Hanan ita halak-malak, amincewar ka cikin dimbin alfarmomin ka da basa karewa a gare ni nake nema”.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull