Auren huce haushi complete - Chapter 35
Auren huce haushi complete Chapter 35: Auren huce haushi complete Chapter 35. Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy…
4,129 words
Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy ta Bata ta cire ta aje a gefe sai Kuma Wanda ya sawo jiya ta cire na kitchen, kofar data gani a tufe taje tadan tura ga mamakinta a bude ta ganta shiga tayi kitchen ne modern sosai babu abinda babu a cikinsa tsayawa tayi tana nazarinsa kafin ta juya ta koma dauko Kayan. Saida ta aje komai a muhallinsa sannan ta bude freezer data gani ta kwance, nama ne dasu kifa da kayan miya a Nike cikin manyan bikitin roba, kaji biyu ta Ciro da Zuba a roba ta tarasu a famfo saboda kankarar ta saki. Filawa ta diba ta kwaba da yeast da barking powder ta rufe ta koma ta gyara Naman ta Dora a wuta. Wani ruwan ta Dora daban ta dauko Madara ta bude ta diba Mai yawa ta dama Zuba akan ruwa data Dora ta Dan zame murfin sannan ta ciro hollandia custard ta fasa ta dibi yanda take ganin zata ishesu ta dama ta aje a gefe. Plates da cups da duk abinda tasan za'a bukata ta dauko ta wanke ta aje a muhallin Daya dace. Filawar data kwaba ta dauko taga ya tashi ta ringa murzawa round sai ta Gama ta shafa Mai a frying pan ta rage wuta ta shiga gasawa tanayi tana juyawa. Biyu ta raba Naman ta dattaka rabi tayi source Rabin Kuma tayi pepper soup dashi ta dama custard din ta dafa coffee Kuma. Tun daga sama Mahmud ke jiyo wani irin kanshi girki yayi tunanin ko da wani sabon restaurant a Nan kusa dasu, Saida ya fito yana saukowa yaji kamshin ya cika gidan. Shigar kananun Kaya yayi yayi masifar kyau, yau shigar da yayi ta fito da ainihin ko waye shi Dan ba karya kana kallonsa kasan matashi ne Mai cike da Jin Dadi da wadatar arziki Dan agogon dake hannunsa kadai na millions of naira ne, shigar da ya Jima da daina yinta Nan gida Nigeria rabon da ya fito haka tun kafin ya shiga rubibi. Hannu Faruq ya shiga tafawa Yana fadin "perfect match, wallahi kun Dace Ashe haka Auntyn tawa take? Haba shi yasa baka sauraren masu yi maka rawar Kai, ya Mahmud Ashe da abinda ka taka shiyasa kayi shuru ka kyale kowa, Mai irin wannan matar mezeci da tarkace irinsu Safna, wallahi na Dade Banga ma'auratan da suka tafi da imanina kamar kai da Aunty na ba, Dan Allah ka tsaya min na auri kanwarta pls🙏". Ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo lokaci Daya faruq ya gigice masa wato yaga zahrar kenan tunda ya sauko yaji gidan ya hade da kamshin girki yasa itace a kitchen, ko ba komai yasan Allah yayi Mata baiwar iya abinci a Dan zaman da sukayi ya fashimci hakan. Shi rasa abin cewa ma yayi a Kan kalaman Faruq, Dan uwansa ne na jini, amma ya gigice da ganin matarsa, tab lallai da matsala Babba. Bai nuna Masa komai ba sai Dan murmushi da yayi Yana fadin. "Ai mata ta ita kadai ce Bata da Kani ko kanwa, nine wanta nine komai nata Sai dai ka duba ko a Ina ne Zan shige maka gaba in Sha Allah". "Dan Allah nidai ka taimaka ko cikin family dinta ne ayi min wanna alfarmar ka shige min gaba". Kyale shi yayi ya nufi kitchen din lokacin ta Gama hada komai ta juyawa kofar baya tana cire jan bayan kwakwa zatayi amfani da ita in anjima. Kamshinsa ya Fara fada Mata ya shigo gurin a hankali ta juyo, Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa ya zubawa bayanta Ido,yanda ta juyo din nan shi Kansa da take halalinasa Saida yaji wani yarrr a jikinsa Dan gani yayi gaba Daya ta canza Masa ga wani irin cikowa da kirjinta yayi sosai. Lumshe Ido yayi Yana tunanin lallai dole addinin musuluci da yayi Hani ga mutum baligi ya shiga gurin macen daba muharramarsa gaskiya. Yana can Yana tunani ya tsinkayi muryarta tana fadin "Ina kwana" batare data Kara kallon inda yake ba. Bai amsa ba ya danyi gyaran murya. "Meye Kuma Ina kwana? Na fada Miki ki iya tarairaya ta wallahi, kada garin kallon ruwa kwado yayi Miki Qafa, kina da kishiya fa kinsan idan ta fiki iya lafazi da tarairayata can Zan tare a gurinta". Warrr tayi masa da sexy eyes dinta tana Masa wani kallo. "Yes ko Baki yarda ba? yanzu na Kira Miki ita ku gaisa". Kai ta girgiza Masa alamar A'a. "Come on, zo Nan ki fada min bakya son kishiyar?" Ya bude Mata hannuwansa alamar ta shigo, kafada ta make ta aje kwakwar ta nufi famfon cikin sink ta Fara wanke hannunta. Cikin takunsa na nazantaka ya shigo ciki directly gurinta ya nufa Yana fadin "Ni gani na shigo sai nazo ki bani hot one tunda ni ba'a son nawa". Bai jira tace komai ba ya saka hannunsa ya rungumeta ta baya Yana shafa cikinta. Shiru tayi Masa kamar ruwa ya cinyeta, Jin hannun nasa ya nufi wata jihar yasa tayi saurin rike Masa hannu tasan idan ya karasa akwai damuwa sosai. "Pls Dan Allah ka Bari kaga da bako a gidan kada ya jiyo mu fa". Ta fada tana kokarin kwace kanta. "Ok saboda shi Zaki hanani na sake kenan? To Bari na sender shi inda yafi wayo". Dayan hannun ya saka ya ciro wayarsa yayi dialing din number Faruq, Sam batayi zaton kiransa zeyi ba, Saida taji Yana fadar "Faruq kaje wancen part din ka qarasa aikin gani Nan zuwa". Bai jira yaji abinda yake kokarin fada ba ya kashe wayar ya Dora a gefen cabinet din kitchen yana fadin "to saiki sake ki bani hakkina tunda sirikinki yabar gurin". Juyota yayi ya hade bakinsu ya cire rolling din, yana shafar gashin da yaji gyara ga qamshin hair spray sai tashi yakeyi ya jima Yana yamutsata kafin ya janye Dan Kansa yana Maida numfashi. Tsugunnawa yayi ya dauko Mata veil din ya rufa Mata a Kanta Yana fadin "dauko wasu flask din ki zubawa Faruq nasa ki saka a basket na Kai Masa can idan ya gama ya tattara ya tafi gurin bikin da yazo". "Me yasa? ba yace min shi qaninka bane". "Ok. Dan Yana qanena saina zauna dashi gida Daya Yana kalle min Mata ko? Ai ya tafi shine mafita Dan akanki zamu iya batawa da kowa to maganin Kar ayi kada a fara, Dan Allah ki ringa saka hijab idan munyi Bak'i ba kowa ne ze iya kawar da Kai a kanki ba Kinga kuwa yanda Faruq ya gigice min na Nemo masa sister dinki, na fada masa babu Amma ya kasa fahimta sai rokona yake na samo Masa mace ko cikin family dinku ne" Ya fada a Dan zafafe. Shiru tayi ta nufi abinda ya sakatayi Saida ta Zuba Masa komai ta saka basket din ta aje a gefe ta dauko Wanda ta zubawa Mai gadi ta aje a kusa Dana Faruq din. Malam Musa ya Kira yace yazo kofar parlourn su hadu, dauka yayi ya fice daga kitchen din yabar zahra da dogon tunanin akan abinda yace Faruq din yayi.
___
Tunda garin Allah ya waye Ammah ke faman neman number zahra abin yaci tura, a yau dai hakurinta ya Gaza Dan tun Daren jiya da zilai ta Kira Ammah tana fada Mata yanda fasalin gidan da suke yake da kuma kudin da tace an Basu dubu ashirin da safe da yamma ma an kawo musu wasu kudin dubu dari-dari ita da iya Rahane ga turamen atamfofi guda hudu hudu da lace bibiyu, Kuma ta fada Mata tunda su zahrar suka fice Bata Kara ganin giccinsu ba ga wayar ta ma a rufe. Akalar Kiran Ammah ta canza ta shiga lalubo Number Abdul Hakeem. Ringing din farko ya dauka yana Fadi "barka da Asuba Ammah, an tashi lfy?. "Alhamdulillahi, idan ka tashi ka shigo Ina son ganinka" ta fada cikin damuwa. "To in Sha Allah, gani nan shigowa".. Ta kashe wayar, ta ajiye a gefe tana fadin "kazo ka nemomin wannan yaron ya fada min waye shi Ina Kuma ya Kai min 'yata ko waya ya Hana muyi da ita inji meye dalilni Daya hana ta amfani da wayar, tunda Naga Abban ba wani Abu zeyi ba, ga wannan kinibabbiyar matar tasa da koma sai taji Masa kwakwaf". Tsaki tayi tana Jin duk Zuciyar ta ba dadi ko kadan, tana Nan zaune Abdul Hakeem din ya shigo sanye da jallabiya coffee colour a jikinsa ya gaishe da Ammah ya nemi guri ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah?". "Da sauki, Nemo min mijin Zahra a wayarka naji dalilinsa na yanke ma'amalarta Dani tunda suka bar garin Nan ban Kara Jin duriyarta ba". Shiru Abdul Hakeem din yayi kafin yace "ba haka za'ayi ba, Zan kirasa na saka handsfree sai kiji yanda zamuyi dashi idan munji da alamun rashin gaskiya sai a San abunda ya Kamata tunda ba'asan dalilinsa. Ba na hanata amfani da wayar, ke uwace kiyi hakuri babu abinda ze Samar Miki 'ya da izinin Allah, in Sha Allah sai kinyi alfahari da Auren Nan Muhmud mutumin kirki ne bashi da wata alama ta rashin gaskiya, kinsan ya fada min shi Dan Sokoto ne,.har unguwar su da iyayensa duk ya fada min lokacin da zeyi tafiyar nan, yace saboda halin Rai Koda be dawo ba na nemi Sameer ko sabon mai gadin Daya kawo a can gidansu na hayin banki, ko Binya na gidan Baba malam duk mutanensa ne. Bari na kirasa Dan hankalinki ya kwanta". Ya Fara dialing din number sa. Sun Gama break fast din kenan wayarsa ta dauki slow music daga kitchen inda ya barota tsam ya tashi ya nufi kitchen din kafin yaje Kiran ya yanke, sunan Abdul Hakeem ya gani, kafin ya Kira wani Kiran ya shigo. Saida ya zauna daf da ita ya daga kiran. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu babban yayan mu, barka da Asuba". Ya fada Yana murmushi. "Wa'alaika Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu kadai, ya iyalin?" Dariya abin ya bashi "Gasu Nan muna ta basu hakuri kasan Mata sai a hankali". Ya fada Yana Dan Jan tsunin hancinta, Batasan dawa yake wayar ba. "Wai meya samu wayarta ne Bata shiga kwata-kwata duk hankakii Ammah fa ya tashi, Jin kwana biyu shiru ba suyi magana ba idan tana kusa ka Bata suyi magana Dan hankalinta ya kwanta". "Ya salam Dan Allah ka bawa Amman mu hakuri laifi tayi min na karbe wayar, amma Zan Bata ita yau in Sha Allah, ai Zan shigo garin gobe ko jibi". Tunda ta fashinci da Ya Abdul Hakeem yake wayar taji hankalinta gaba Daya yayi gida Jin cewa zeje Azaren bada ita ba sai taji duk ta shiga tashin hankali da gaske gida take son komawa, ta dauka da Wasa yake Mata lokacin da yace ze dauko Mata Rukayya idan zasuje Azare. Wayar ya Mika Mata ya Mike ya fice daga parlourn gaba Daya. Sallama tayiwa ya Abdul Hakeem din sannan ta gaishe shi. Sannan ya dora da fadin "ga Ammah nason magana dake". "Dan Allah Ya Abdul Hakeem ka Bata hakuri wallahi saboda bansan abinda Zan fada Mata ba na kashe wayar Allah ba yaji nayi ba, kaina ne yayi zafi gurin fa buduwarsa ta turoni Asibiti ita Kuma ta shiga wulakantani, Dan Allah ka rokarmin shi ya maidoni gida wallahi na gaji Ni tsoro nakeji bakaga irin gidajen da yake kawoni ba kamar baza'a mutu ba fa". Ta ida fada tana kuka. Duk abunda ke wakana Ammah na zaune tayi tagumi tana Jin wani sanyi da tausayinta a Zuciyar ta, amman koba komai ta samu nutsuwa taji lafiyar ta sauran Kuma tasan shegantake ce kawai. Wayar Abdul Hakeem ya mikawa Ammah ya tashi ya fice shima gara ya Basu guri su tattauna. "Wai kukan Kuma na menene haka? ai kowa ya gyara ya sani kowa ya Bata ya sani, kiji tsoron Allah ki rike sirrin mijinki kinsan baqi kinsan fari keba karamar yarinya bace,saboda me Zaki tafi wani guri har ki nemi kwana bada izinin mijinki ba, haka kawai kin tashi hankakin jama'ar da suka daukeki da mutumci kin kyauta kenan? To wallahi kada na sake Jin wani Abu makamancin haka daga gareki ki nutsu ki rike aurenki kada na Kara Jin kin ambaci ya dawo dake nan, kinsan dai ba'a nan zaku dawwama ba ina cewa ya fada Miki garinsu wata Rana dole ze koma gida sai kice bazaki bishi ba? Akul na karajin magana makamanciyar wannan daga bakinki". Tunda Ammah ta Fara magana Zahra ke shashsheka a hankali. "Kiyi hakuri wallahi na daina bazan Kara ba, wallahi bansan laifin da nayi Masa ba ya dauke min wayar da passport dina har da kudi da ATM duka". Salati Ammah ta dauka tana fadin "Ni Asma'u yanzu harda passport dinki Kika dauka dole ya kwashe wato guduwa kuka shirya zakiyi kibar kasar ko?" Cikin gigita Zahra ta fashe Mata da kuka sosai tana Fadi "wallahi ba guduwa zanyi ba Daman suna cikin jakar fa". Ji tayi an zare wayar daga hannunta Batasan lokacin daya taso ta shige jikinsa ba tana fadin "Dan Allah ka fadawa Ammah abinda take zargina dashi ba haka bane". Ai Jin wannan furucin na Zahra yasa Ammah yanke Kiran cikin gaggawa. Jin alamun yanke Kiran yasa shi Kara sakata a jikinsa baya son kukanta ko misqalazarratin.
AUREN HUCE HAUSHI. (Maman Fateemah.
Page 51
🖋️ ___Dan murmushi Ammah tayi,koba ba komai ta Sami peace of mind, yanzu Bata da wata fargaba,zata Kira zilai ta fada Mata ta kwantar da hankalinta babu wata damuwa Zahra na Nan lafiya kalau ita dai tayi zamanta sai lokacin Daya bukaci su dawo sai su taho din kawai. Tashi tayi da wayar a hannunta ta wuce Ciki tana Jin wata sabuwar nutsuwa tana shigar ta. Addu'ar da takewa yarinyar Allah ya Zama gatanta a dukkan al'amura.
***
Sun Jima a yanda suke ita Bata janye ba shi Kuma be saketa ba, ajiyar zuciya kawai take saki a hankali. "Wai me kika yiwa Ammah ne haka da zafi har kike neman bayi Miki shaidar zur". Tsuntse idanu tayi sai wasu hawayen. "Ya salam! Pls bana son kuka sam, ki adana abinki Mana Yana da lokaci, ai kin gane?". Shiru tayi masa, me zata fad'a Masa tace Ammah tace Mata niyyar guduwa take yi. "Pls ki fada min Mana ko saina Kira na tambayeta laifin da kikayi Mata sannan zanji Kan maganar?" Da sauri ta shiga fadar "wai fa Dan naje gidan su bestie shine take min fadan me yasa nayi yaji, shine na fada Mata ba haka bane". Dago fuskarta yayi yaga yanda idanunta suka sauya kala daga farare zuwa ja. "Shi kenan ai komai ya wuce tunda Nina janyo akayi yajin tunda na turaki gurin Haseena, nayi zaton zuwa yanzu ta aje maganar soyayya a tsakanin mu sai zumunci kawai, kiyi Hakuri nayi Mata last warning akan shirmen da tayi". "Ni dai dan Allah ka maidani gida na gaji da garin kwata kwata". Ta fada tana turo baki. Baice Mata komai ba ya nufi one seater ya zauna ya dorata a cinyarsa suna facing din juna. "Ki cire ranki da komawa Azare Saida ganin gida daga Nan sai Sokoto birnin shehu, kina tunanin Zaki koma can ne? Ai shi yasa nace a hadoki da house maid wadda take da Amana tunda a yanda Naga takunta zatayi amanar, shine dalilin da ze kaini can na fadawa Abban mu da malam Zan koma gida tunda the game is over, na samu a binda nake nema ai saina koma ayi wadda za'ayi ko?". Ya fada yana dage Mata girarsa ta dama. Wani ruwan idanunta suka kawo alamun zatayi masa halin. Bata fuska yayi ya Zama serious din nan. "Wallahi naga digon hawayenki saina sakaki kukan gaske, kuji min yarinya sai shagwaba, ai Naga kin Fara sallah gara na cire Miki yarintar Nan ko kin nutsu ki fuskanci aurenki, dan Naga alamar har yanzu Baki yarda da igiyar aurena ba a kanki tunda na kasa banbance Miki tsakanin Aya da tsakuwa ko?". Mukus ta hadiye kukan tana qiqqifta Idanu, Jin ya b'aro magana, to a Ina yaga tana sallah har yake fada Mata hakan?. Kafin ta samu zarafin magana wayar da take jikinsa ta dauki wani kidan larabawa Mai Dadi. Dagawa yayi Yana fadin "ok gani Nan Amma ka tabbata komai ya Zama ready kafin na shigo, dan Allah kace mommy ta bani aron Rukayya ta shigo Nan Hausawa Bawo road ta Taya 'yar rigimar Nan Zama zuwa yamma, ka Bata address din gidan". Ya fada yana sauketa daga jikinsa ya Bata light kiss ya manna Mata a saman goshinta Yana fadin "Zan dauki Aron motar ki na fita da ita kinji my previous, anyi min izini? Kai ta gyada Masa tana fadin. "Allah ya tsare". Harya juya ya nufi hanyar barin parlourn ya dawo ya Mika Mata wayar hannunsa,. "Kiyi amfani da ita sabon sim ne a ciki Sameer kawai nake Kira da shi kafin a kawo Miki Taki tunda na fadawa yayan mu yau Zan Baki wayarki". Hannu ta saka ta karbi wayar iPhone 16 plus ce da sauri ta dago ta kalleshi alamar mamaki fal cike da fuskarta da kallon tuhuma Dan ba da ita tayi ways da Amma ba. "Ya akayi Kika tsareni da kallo ko batayi miki ba". Ta bude Baki zatayi magana ya daga mata hannu. "Bari na dawo saina amsa tambayoyinki a nutse ai cewa nayi Miki aro bi kyauta ba ko?". Ya fice da sauri, da alama uzurinsa Mai girma ne, tun bayan fitarasa take juya wayar a hannunta idan ba bataga daidai ba a mbc taga tallarta 1.48 million naira ne kudin ta in Nigerian Price. To wai waye shi ne Dan Allah? Duk lokacin da wani Abu irin haka ya gitta a tsakaninsu baya yarda ya tsaya yayi Mata bayanin komai. Ajeta tayi a gefen da take zaune ta Zuba uban tagumi da hannu biyu tana nazarin wasu abubuwan da take gani tun shigowar su Kano abun ya canza salo gaba Daya, ta rasa Wanda zasu tattauna da dashi Aunty Hussina ce to babu waya a hannunta ta mayar da kanta kurma. Kamar an tsikareta ta Mike ta nufi upstairs da wayar a hannunta tana fadin Bari na Kira bestie musha hurar yaushe gamo da ita". Duk yanda zahra taso ta fada Mata wani Abu Daya shafi Mahmud saita kasa fada Mata Kuma da alama Ummansu Bata fada Mata taje gidan ba koda wasa, saima wani abun mamaki da sajidar ta fadawa zahrar cewar Mahmud yace zasuzo har syprus gurinta tare Amma yace kada ta fada Mata, sun dauki lokaci suna wayar har sajidar ke tsokanar Zahra tana fad'in "ke Kullum canza layi kamar wata marar gaskiy". Dan nisawa Zahra tayi kafin tace "ki Bari bestie kawai wallahi ba laifina bane shine yake kwace min wayar Kuma idan ya tashi Kuma ba ita Ze bani ba sai dai ya bani wata, jiya fa da muka fita unguwa ya shiga sahad na Nan zoo road muka hadu da Musbahu bakiga yanda ya yi, ba Banda Allah ya Soni ba da inaga sai yayi min duka ma da Allah yasa nayi tsautsayi munyi magana dashi". Dariya sajidar tayi tana fadin Namijin duniya kenan Wanda ke kishin iyalinsa, nifa Daman harga Allah musbahun nan ba wani yi min yayi ba, kawai dai baka hana nutum abinda yakeso ne, Amma Ina hadin be hadu ba ko alama wallahi,ban qara sanin haka ba Saida sarkin yaqi ya bayyana". Ta fada tana kyalkyalewa da dariya. "Wallahi bestie Baki da kirki ki ringa Jin tsoro Allah, musbahun ne haka? Amma Ina cewa harda ke a masuyi Masa campaign a wancan lokacin".. "Manta kawai bestie ya zaman past, yanzu ta Wanda Allah ya zaba Mana mukeyi, yauwa munyi magana da Baffa yace akwai saukar Alqur'ani da ake Miki in Sha Allah babu wani Abu daze sake tasiri a cikin rayuwarki in dai sihiri ne yace kiyi ta Hakuri mijinki Mai jama'a ne". "Hummm! Bari kawai bestie nifa mutumin nan tsoro yake bani". "Tsoro kuma? Kamar Yaya?" Tsaki tayi kadan. "Ba Zaki gane ba kwata kwata ba Wanda Kika zani bane wannan wani ne daban, kinsan ya maidoni Kano daga zuwa ganin likata yace nida Azare sai ganin gida, Kuma Kinga wasu mahaukatan gidaje da yake yawo Dani a cikinsu Kamar baza'a mutu ba wallahi, Kinga wannan wayar dake hannuna yanzu wallahi iPhone 16 plus ce ya bani Wai ga aro kafin ya kawo min tawa. Allah Lamainsa Yana damuna Kuma yaki yayi min bayanin komai sai sabgar gabansa yakeyi kawai".. Tunda Zahra ta shiga bayani sajida ke murmushi Dan tasan za'ayi haka Ya Abba ya kirata dazu ya fada mata waye mijin da zahra ta aura kawai ya bada kafa ne wanda shima baisan dalilinsa na yin hakan ba. "To ke meye naki na sai kin San waye shi yanzu kiyi Hakuri Mana ai yau da gobe tafi karfin Wasa ba dai Kuna tare ba, ai wata Rana gaskiya zatayi halinta abinda nakeso kiyi kawai ki saka a ranki mijinki ba macucin da ze cutar dake bane, Kuma bata haramtacciyar hanya yake samun kudinsa ba,Kika sani ko wani mashahurin Dan kasuwa ne Allah ya Baki". "Kin jiki aikin fa NGOs fa yakeyi Dan dai wata tsohuwa ta fada min wasu maganganu Wanda ta sakani a confusing sosai". "Ki manta kawai ki fiskanci zahiri tunda gashi gaki bada labari Kuma ai ya Kare keme reality a gabanki,kawai dai ki zama Mai lura da lamarinsa da kyau, kiyi kokarin Kare Masa Sha'awarsa kada ki zama lusara mijinki yaro ne Mai jini a jika Wanda Mata irinsa suke rububi Koda aure ko Kuma ayi shashanci gaskiya sai kin dage in ba haka ba garin kallon ruwa kwado yayi Miki kafa". "Kamar Yaya?" "Au Baki gane ba to ki ringa bashi hakkinsa Dan Naga alama kamar zakiyi son jiki ta wannan fannin Ni Kuma yanda nake ganinsa ba ragon namiji bane". "Inna fatahana laka fatahan mubina! Bestie yaushe Kika Zama haka wallahi badan nayi Miki farin sani ba da cewa zanyi kina wata sabgar a bayan fage, to wallahi Ni har yanzu in nan yanda nake shi ba yanda kike tunani yake ba a Nan dai sai nace kinyi failed tunaninki ya kasa.." Wata irin dariya tayi tana fadin Dan Allah mu koma video call Naga idanunki su kadai Zan kalla na tantance maganarki"
"Ba zanyi ba sai anjima tunda kin Zama abinda Kika Zama sai neman sauki gaskiya Ya Abdul Hakeem ya gamu da gamonsa a Ido kamar saliha nasan idan Kika shiga gidan sai yayi Dan wuya tunda Naga alama kina cikin.... Allah dai ya kyauta kawai". "Kai! Sharrin da zakiyi min kenan shi kenan Zan rama". Sun dauki lokaci suna Hira har sajidar ke fada Mata Hameeda ta kirata tana kuka akan abunda tayi Mata Wai Mama da Salma ne suka sakata, Bata gane kuskuren da tayi ba Saida ta dawo gida, abinda yasa suka samu sabani da Salma kenan har ita Hameedar tayi tafiyar ta Jos Saida zasu koma Jigawa sannan ta koma gida. "Lah ki fada Mata Ni a gurina ya Dade da wucewa wayace lokacin babu a hannuna Dana kirata tuntuni Amma idan nayi waya Zan nemeta ai karo Daya masu magana sukace Koda kusa ai yi akeyi, Hameeda tawa ce". "Kiyi dai taka tsan-tsan da lamarin ta kinsan ance jini yafi ruwa kauri duk rintsi ba zataqi uwarta a kanki ba, ko Zaki Kara karbarta kisan irin zaman da zakuyi da ita, Ni garama Daya daukoki daga can yayi maganin abubuwa da yawa wata qila Kuma da abinda ya lura dashi yasa ya yanke wannan hukuncin". Shigowar su Aneesa dakin sun dawo daga lectures yasa suka canza akalar hirar sun gaisa da Zahrar suna ta korafin taji dadin aure ta manta dasu ko wayarta ba'a samu saboda tayi nitso cikin kogin soyayya, ita dai saikokarin Kare Kanta takeyi sajida na tayata. Da haka sukayi sallama. Aunty Husaina ta Kira itama tayi Mata nata fadar rashin samunta a wayar sannan ta Kara dubata da jiki tare da tambayarta yanda sukayi da Asibitin? ta fada Mata fada har yanda sukayi da doctor din, da Kuma maganin da Hajiyar makwarari ta Bata, sannan ta fada Mata abinda yake faruwa da ita a Nan kanon Bata rufe Mata komai ba, tayi mamaki kwarai sai dai tun farko Daman ta yiwa lamarin sa question mark, tun ganin irin kudin da aka narkar a kankanin lokacin gyaran gidan da aka bashi a nan Azaren. Kamar hadin Baki itama Aunty Husainar cewa tayi ta Zuba Masa Ido ta Kuma yi masa biyayya, sannan sukayi sallama. Kusan awa Daya da tafiyar Mahmud Zahra taji bell na Kara alamar anyi bako. Saukowa tayi ta nufi kofar ta bude Aunty Rukayya ta gani a tsaye da basket din abinci a hannunta dayan hannun Kuma da karamar jaka irinta matafiya.
AUREN HUCE HAUSHI.
(Maman Fateemah)
Page 52
______