Auren huce haushi complete - Chapter 37
Auren huce haushi complete Chapter 37: Auren huce haushi complete Chapter 37. Sun dauki titin da ze fitar dasu HOTORO NNPC ne wayar Mahmud tayi K'ara…
4,450 words
Sun dauki titin da ze fitar dasu HOTORO NNPC ne wayar Mahmud tayi K'ara alamar shigowar massage. Ciro ta yayi ya duba, gefen titi ya gangara yayi parking. Sannan yayi dialing din number da akayi Masa text din da ita, ba Bata lokaci daga can aka daga. "Yi min cikakken bayani". Abinda Mahmud din ya fada kenan, daga can Daya bangaren aka Fara Masa bayani sai jinjina Kai kawai take yi har ya aka gama fada masa duk abinda ya nema a fada masan. "Kana jina Zan fadawa Bilyaminu ya kawota Nan Kano can sallari za'a ajeta zanzo in Sha Allah ayi Mata duk abinda ya kamata". Ya yanke kiran, ita dai Zahra ido ne nata, wani zance yakeyi Wanda ta kasa fahimta, wacece me za'a kawota tayi shi me zeyi idan yaje gidan da yace a kaita? Nan da Nan taji faduwar gaba kada fa ko Yana harkar mata, taga ba sauki idan ya rikice, ko zuwa zeyi yayi... Da sauri ta girgaiza Kai tana runtse Ido. "Ya akayi ne 'yan Mata naga kin shiga dogon tunani?". Kankance idanu tayi tana Masa wani kallo na tuhuma. "Wa kenan za'a kawo maka". Wata dariyar rainin wayo yayi Yana kallonta kasa - kasa. "Mace Mana, tunda kin hanani ai gara na nemi mafaka inda Zan rage zafi, ko so kike na kasa amfanuwa, idan har ban samu nutsuwa ba saina kwanta gadon Asibiti, kinsan ya nakeji kuwa?". Ya wani Yi mik'a Yana kokarin janyota jikinsa. Da sauri tayi baya tana fadin. "Allah ya tsari gatari da Saran shuka,ni me Zan baka ai ban cika mace ba, Daman ni me zakayi Dani da aka k'ak'aba maka sadaka bani da wata qima ko daraja a gurinka tunda bakasan darajata ba, da bakinka fa kace an fada maka duk Wanda suka nemi aurena sai sun Gama Dani suke barina kaga kana min kallon fasiqa Mai ma'amala da maza kenan me ze Hana ka Kira a kawo maka mace a gabana, wallahi tallahi bazan zauna da fasiqi ba sai dai ka rabu dani wallahi ban taba kebancewa da wani namiji ba a duniyar nan bayan Kai, bazaka shafa min wahala ba ka gudu ka barni, tunda har gobe ba Wanda yasan daga ina kake, Kuma rayuwar garin Nan ai mun santa komai ma na haya ne, haka kawai ka cuceni ka gudu ka barni da Jangwam idan da gaskiya wa yake gudun asalinsa ai duk lalacewar gida yafi daji ka koma Mana idan ba fitsare gurin kayi ba da abin kunya ba ka gudo nan". Tana kawowa Nan sai kuka, shi ikon Allah ya tsaya Yana kallo yanda ta zage tana tsula Masa rashin kunya wato Mata ba sauki gurin kishi, Dan murmushi yayi yana ayyana 'yar daru kawai. Dauko ta yayi cak kamar 'yar baby ya kwantar da kujera ya sakata cikin jikinsa ya zagaye ta da hannunsa. Tana ta mutsu-mutsun kwacewa Amma yayi Mata kyakykyawan riko. "Mai maita min abinda kikace waye Dan iskan? Ni zaki kalli idona kina fada min abinda ranki ya Raya miki? Idan matan zanbi kin isa ki hanani ne, nace a kaita sallarin Kuma Billahillazi mace ce kuma gurinta zanje ko Zaki hana ne, an fada Miki ina sonki ne kunya da kawaici yasa na karba amma badan kinyi min ba, Kuma ki rubuta ki aje har abada bazan taba sakinki ba idan ma kinayi dan naji haushi na rabu dake ne ki sake dabara, Kuma dake zamuje can din na ajeki na shiga nayi abinda nakeso mu koma Kuma kiyi min wanka, gida Kuma eh abun kunya nayi na gudo nan, yarinya na yiwa ciki Dan haka ki shirya rike yarinyar da aka Haifa min nan gaba kadan".
,AUREN HUCE HAUSHI.
Naman Fateemah.
Page 54.
...........Sun Kai kusan minti goma a haka, tana jikinsa a haka tayi kukanta Mai isarta, baris yayi da ita Yana Jin tana ajiyar zuciya, Shima da gaske ta tunzura Masa zuciya Wai "fasiqa" kalma mafi Muni Daya tabaji daga bakinta, dole ta karbi hukunci Wanda ko Nan gaba ba zata Kara marmarin fada Masa makamanciyar irinta ba. Sauke ta yayi daga jikinsa ya gyara kujerar ya tada motar, baiko Kara kallon inda take ba ta fisgeta da wani irin mahaukaciya gudu. "Wayyo Allah Nan Dan Allah kada ka kashe mu, na shiga uku". Ta fasa masa kuka Dan da gaske ta tsorata da yanda ya saki motar. Bai tanka Mata ba amma ya sassauta gudun, shiga Nan fita can taga sun shiga wata unguwa Mai karancin gine-gine duk tayi zuru-zuru da ita kofar wani katafaren gida ya tsaya ya Danna horn da karfi da gudu aka bude gate din ba wata wata ya Danna Kai cikin gidan. A tsakiyar gidan ya Parker motar, wasu kartin maza ta gani sun nufo motar da sauri kusan su shida dukkansu majiya karfi, take jikin zahra ya dauki rawa, Yana kallonta ta gefen Ido yanda take mazari, Amma ya share ta. Kofar ya bude dai dai lokacin da suka karaso suna kwasar gaisuwa. "Sagir tana Ina?". Mahmud ya fada Yana duban Wanda ya kira da sagir. "Tana ciki yanzu ba dadewa bilya ya kawo ta". "Ok.kuna iya tafiya Amma kafin Nan ku sako min little da barbar tsakar compund din nan. Yayi gaba abinsa ya nufi wata katafariyar kofar parlour. Zahra tayi mutuwar zaune Dan gaba daya tsoro ya cika Mata zuciya ganin wannan mutanen kawai tasan ba abin arziki ake qullawa a gidan Nan ba, Wanda taga ya nufi wani guri can baya ya taho tare da wasu irin karnunka masu wani irin gashi a jikinsu bula bula dasu, wani irin kara Mai Kama da fito yayi musu suka Fara zagaye motar suna wani irin gurnani, wata mota hilux taga sun shiga sai mutum biyu suka Bari a gidan suka wuce. Zahra idanunta na ganin karnukan na zagaya motar hantar cikinta ta Kama rawa, a duniya tana tsoron Kare bare wadannan data gani masu Kama da kura ai Bata San lokacin da jib'i ya rufeta ba duk da sanyin AC dake motar, wannan wane irin wulakanci ne yayi Mata Yana can Yana aikata masha'a ya sakar Mata karnuka wadanda zasu hanata fita ko Nan da can. Daya daga cikin biyun da suka rage a gidan ne ya nufi cikin gidan ya Zama daga Zahra sai Wanda take tunanin Mai gadi ne sai Kuma masu gadinta Dan taga alama saboda ita aka kawo karnukan nan, Bata San lokacin da kuka ya kwace Mata ba tana fadin. "Wayyo Allah! Abba kazo kaga yanda ake wulakantani karnuka ke gadina Kamar wata criminal". Motsin kirki ta kasayi gani take kamar idan ta motsa zasu fasa glass din su shigo ciki, ba abin tashin hankali irin gurnanin da sukeyi.
** Cikin takunsa na mazantaka ya shigo parlourn sai da yazo tsakiya yaja ya tsaya Yana karewa gurin kallo kamar yau ya Fara shigowa, ba motsin komai, da sassarfa ya Haye steps din da ze sada shi da dakunan barcin, kofa ta farko ya bude da karfi abinda ya sakata zabura kenan ta Dora hannu a ka jikinta ya dauki karkarwa tana fadin. "Wallahi Allah sani akayi bani nake Mata wannan abun ba". "Shiii! Kept quiet!". Ya daka Mata tsawa, Yana kusanto inda ta takure a jikin katafaren gadon, kafa Daya ya Dora a Kan gadon dayar tana dire a kasa Yana Kare Mata kallo tun daga sama har kasa sai wani bashi yake tashi daga jikinta. Sadda Kai tayi kasa tana tsuma.
Cikin izza da rashin son wargi ya bude bakinsa da kyar yace Mata. "Meya hadaki da rayuwar iyalina? Meta tsare miki? Keda waye kuka saka rayuwarta gaba? Waya sakaki bibiyar lamarinta gurin kawo sakonnin mugun Abu? Waye ya sakaki jefo abinda Kika jefa a gidan ranar da Zayyan ya kamaki? Kada ki kuskura kiyi min karya duk da kin haifeni Zan nuna mini true colour din yanzun nan, sai kinyi Dana sanin sanin Wanda kikewa aiki wallahi Dan Allah sai nasa an wulakantaki". Zayyan ne ya shigo. "Sir akwai damuwa Naga hankalinta ya tashi kamar tana kuka, da alama tsoronsu takeji ko a mayar dasu ne?". Wani banzan kallo ya watso masa. "Sorry sir". Ya fada Yana sadda Kai kasa. Kuka ta fasa tana fadin "Dan Allah kayi min Rai yallabai wallahi bani nake Mata wadannan abubuwan ba, wallahi Hajiya Mama ce duk Aurenta da ake fasawa ma ita ce take yin asirin da ake fasawar saboda an fada Mata duk cikin yaran gidan Zahra tafi kowa sa'ar rayuwa,mijin da zata aura ba ita ba wani ma saiya huta a jikinta,uwa uba Kuma tafi duk yaran gidan kyau da cika irin ta Mata ga nasaba ta bangaren mahaifiyarta,ko rashin zuwan kakarta kasar Nan da hannun Hajiya mamar a ciki, abinda nakai na farko Wanda wannan ya karba, ta nuna Zayyan, Shima maganine a cikin turaren wutar Wanda akace idan ta turara ka shaki kamshin bazaka Kara Zama a Azaren ba har abada, zaka kuma manta da ita Zahrar sai dai kotu ta raba Auren, na ranar Nan Kuma wallahi bansan Kona meye ba tace daga Jos aka kawo Mata wayata ma babu caji har gida tazo ita da dureba ta aikeni naje Tasha na karbo ta fada min duk yanda zanyi ta bani duba hamsin tace ladar aikina ce, wallahi iya abinda na sani kenan, kayi min Rai wallahi na daina har abada ka rufa min asiri wallahi na baro mahaifiyata babu lafiya ni nake kula da ita, kudin da nake samu a gurinta dasu muke cin abinci na Kuma sayawa tsohuwa ta magani". Ta fada tana yarfe gumi daga fuskarta duk da sanyin AC dake ratsa dakin. Tsayuwarsa ya gyara Yana jinjina maganganunta a zuciyarsa, shi yana Jin chakwakiya kala kala Amma ta zahra ta bashi mamaki wannan wace irin kiyayya ce haka. "Kinsan abinda yasa Zan kyaleki?" Da saurinta ta girgaiza Kai. "Saboda ke 'yar aike ce, shi Kuma jakada Bai taba laifi ba sai ke kin bada gudun mawa gurin cutar da marainiyar Allah Wadda bataji ba Bata gani ba, kunyi ta kokarin kada ta cimma abinda Allah ya hukunta a Kanta Ashe Taki kuke zubawa gonarta,ku Baku isa ku Hana Allah s.w.a ciki Alkawarinsa ba a Kanta, hassada ga Mai rabo Taki ce, Kuma dare ga Mai rabo hantsi ne, duk da ta auri Almajirin malam baku saurara Mata ba dole sai ta wulakanta ko? To Allah ya nuna muku Kaidin ku ba komai bane da sannu zaku girbi abinda kuka shuka, babu abinda zanyiwa Hajiya Mama taci darajar mijinta.Amma ke gargadi na farko Kuma na karshe da Zan Miki kada naji ko labarin ki a Azare duk ranar da naji labarin an ganki saina saka an batar dake har abada, ga Bilyaminu nan ze mayar dake kutattara ku nemi wani gurin ko arear Bauchi kada naji labarin an ganki, na bashi sako ze Baki idan dan talauci ne kika Zama jakadiyar yada barna to ki nemi sana'a ki Kuma tuba ga Allah Mai gafara ne Mai jinkai".
Wani kukan ne ya kwacewa Asabe Bata taba tunanin ze Zama me rangwame a gareta ba,duba da yanda Zayyan da bilyamu suka ringa surfa Mata Mari har Saida kumatunta suka Haye kamar ta kunsa biredi a ciki. "Na gode! Nagode! Yallabai Allah ya saka maka da Alkhairi lallai ka cika mumini Mai imani ka saka sharri da Alkhairi in Sha Allah gobe zamu koma gida Zuru daman nina Kiya da innata tace mu koma mahaifarta Ina kwadayin abinda nake samu da Mama".
Bai Kara tofa ko kalma daya ba ya juya ya fice daga dakin Zayyan ya biyo shi a baya. Wani bangaren ya nufa yayin da Zayyan yayi waje, har lokacin su barbar suna nasu aikin, sagir Zayyan ya kwalawa Kira ya taso daga bakin gate ya nufo shi. "Dan Allah meyasa baka da lissafi ne Wai? Kasan wacece a motar Nan daka bawa karnukan ku umarnin nan?"
Motar ya kalla yana fadin.
"A'a ban sani ba".
Kwafa yayi to matar oga ce wallahi idan ta ganeka sai tayi maganinka, da alama wani abun tayi masa kasan boss ba sauki idan aka taba shi, kasan meye bani mamaki besa nayi bij-biji da wannan matar ba saima ma makudan kudi da ya bada a bata". Ya fada Yana tsaki.
"Kai rabu da wannan muyi magana Mai mahimmanci. Dan Allah da gaske ne da ake fadin oga yayi aure? Wallahi na dauka duk shafta ce kawai". "Matsa Nan, naka Wasa ne yanzu ka janye su salin alin ka tafi dasu gurinka yanda baze gane Kai ka janyesu sai yayi zaton sun gaji ne suka zo gurinka". "Haka za'ayi Bari ka gani".
Ya juya da sauri Yana wani irin fito a hankali, da gudu sukayo gurinsa ya nufi gate suka bishi suna kada jela. Wata ajiyar zuciya zahra ta saki Dan tayi kukan har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Bayan fitowar Zayyan Mahmud yakai minti Sha biyar sannan ya fito cikin sabuwar shiga ta wasu kananun kayan, ash colour T.shirt da black trouser Yana baza kanshinsa kamar ko yaushe. Da sauri Zayyan ya nufo shi, ganin Basu little a gurin motar yasa Mahmud din yiwa Zayyan Wani kallo, shafa Kai yayi yana fadin. "Tuba muke oga, hukuncin yayi tsauri". Be ce Masa komai ba har suka karasa gurin motar saida ya bude sannan ya dubi Zayyan din Yana Mika masa key. "Ungo bari mu koma baya kayi driving din mu na gaji bazan iya mayar damu gida ba". Ya zagaya ya bude side din zahra take zaune Yana fadin. "Precious" ya Mika Mata hannu alamar ta kama ta fito...
Tun wayewar gari Hajiya Mama ke jiran Asabe ta kawo Mata sauran magungunan da zatayi amfani dasu mahadin Wanda ta tura a jefa gidan Zahra, har akayi sallar azzahar babu labarin Asabe, la'asar shiru gashi har bayan insha'i babu ko duriyarta a gidan gashi wayarta a rufe. Ganin zaman tsammani baze yuwu ba yasa Mamar fitowa neman sahura, can inda dakunansu suke ta nufa tana tufka da warwara, tashin hankalinta Daya Bata aiwatar da abinda akace tayi tun safe ba, a daki ta samu sahura ta Bata kudin adaidaita ya kaita gurin Asabe ta fada Mata tazo tana nemanta. Labarin da sahura ta dawowa Mama dashi yayi matukar daga Mata hankali, Dan 'yan gidan abokan hayarsu sun tabbatarwa da sahura tun fitar da sukayi Hajiya Mama Bata dawo gidan ba har lokacin.
AUREN HUCE HAUSHI.
Maman Fateemah.
Page 55.
_____Zayyan Yana fitowa yaga yanda zahra ke tsuma sai yaji ba Dadi, gaskiya oga Bai kyauta ba, da alama ta hadosu ne yake horata ta wannan hanyar wato halinsa Yana Nan na rashin son wargi, itama Bata tsira ba saiya nuna Mata Hali. Gurin sagir ya nufa, Yana Jin babu Dadi a cikin ransa, ga wadda za'a hada da barbar Nan yayi kaca-kaca da banza, Amma ya wani kyaleta taci bulus sai wannan Mace Mai daraja ze hada da wadannan karnukan nasa masu kama da kuraye su tsare yarinyar mutane, shi ko tausayinta bayaji ya wani yi zamansa a ciki idan ma sumewa zatayi bashi da damuwa, Allah idan ya wuce saiya casa waccan karamar 'yar iskar dan yaga alama tsohuwar Yar duniya ce ta kware a gurin munafurci. A zaune ya samu sagir Yana jin wakar boda katsina. "Dallah kashe Mana! Kai ko imani ma baka dashi, ka sakarwa baiwar Allah karnukanku marasa mutunci kazo kana shakatawa,to Bari na fada maka, idan kayi Wasa ka kusa cin taliyar karshe a karkashin oga wallahi, dan ba kowa ka sakarwa karnuka ba sai amaryar oga, idan tayi marking dinka kana zaune za'ace ka Kara gaba". Ya fada yana Jan tsaki yayi gaba abinsa. Sororo sagir yayi yabi Zayyan da kallo sai Kuma ya tashi da sauri yabi bayansa. "Dan Allah Zayyan tsaya, fada min gaskiya wallahi na dauka irin masu kawo kansu din Nan ne yake so ya koya Mata hankali, tunda mun shaida oga baya harkar Mata, shi yasa nayi biris da lamarin su". "Yayi kyau, wallahil azim nasan hankalinsa Yana Kanta dari bisa dari kawai dai so yake ya nuna mata shi din Jan wuya ne baya daukar shirme, tun wuri kasan yanda zakayi ka mayar dasu muhallinsu kafin lokacin fitowarsu yayi su fito patrol" Fitoh daya sagir yayi musu suka nufo inda suke tsaye, gaban sagir din suka turje gaba yayi suka rufa Masa baya.
Mahmud ne ya fito sharr dashi da gani wanka yayi ya sake wata shigar kananan kayan sai zuba kanshinsa yake as usual, tsaye yayi Yana yiwa Zayyan Wani kallon tuhuma sadda Kai yayi Yana shafa sumarsa. "Sorry sir, Naga ta takura ne kamar zata shide Ni Kuma Naga kada ta Kira maka ruwa".
"Ok ka fini sanin abinda ya Dace kenan ko?" Shiru Zayyan din yayi shi dai ai yayi abinda ya dace yasan Kuma yaji Dadi nunawa ne bazeyi ba, gangarowa yayi da sassarfa ya nufi motar dai-dai sagir na dawowa daga mayar da su barbar. Kamar ze Masa magana saiya fasa. "Zo ka mayar damu gida bazan iya tukin Nan ba na gaji". Ya fada Yana satar kallon zahra wadda tayi kalar tausayi da gani ba karamin tashin hankali ta shiga ba. Key din ya Mika Masa ya zagaya inda Zahra ke zaune ya bude side din yana mika Mata hannu alamar ta Kama ta fito, dauke Kai tayi Kamar bataga abinda yayi ba, ganin yana gyara tsayuwarsa yasa tayi wuf ta fito tasan ba karamin aikinsa bane ya daukota a gaban wadannan garadan. Ta gefensa ta wuce ta shige can kurya kusa da window ita fa ji tayi Yana wani karni Maimakon kamshin da yake bazawa. Kyalen after dress dinta ta ware rolling din ta rufe fuskarta tana ci gaba da sharar hawayenta, yau Mahmud yayi Mata karshen wulakanci, wai ita ya sakarwa karnuka. Tana ji yana yiwa Wanda ya kawo Mata karnuka magana akan abincin karnukan. Sannan taji sun fita daga gidan, ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana Fadi "mugu" a cikin zuciyarta, ba Kama Nan da Nan idonta ya Kara cikowa da hawaye Wai itace mijin aurenta ya kawota gidan da yake badala da wasu matan ya ajeta da karnunka ya Gama abinda zeyi harda wanka da canza Kaya Dan ta tabbatar da abinda yayi din. Tunda ya shigo baiko kalli inda take ba, wayarsa kawai yake ta dandangwala ko kansa Bai dago ba Saida Yana lure da duk motsinta ta kasan Idonsa. Basuyi tafiya Mai nisa sosai ba idan tayi la'akari da wadda sukazo zuwa nan din taji horn alamar dake nuna anzo gidan, ko Kuna anzo wani gurin a hankali ta bude idonta gidan da sukazo jiyan ne suka dawo har kofar falo zayyan yaje da motar kamar dazu da zasu fita, da sauri ta bude ta fice Bata son yaga weaknesses dinta ko kadan. Saida Zayyan ya jide kayan cikin motar sannan ya kaita parking lot ya aje ya dawo gurin da Mahmud yake tsaye. Sakon gidan Baba malam ya tura Masa a waya ze saya gobe ya tafi dasu can Azaren. Zahra na shiga ta Haye sama direct bedroom din data mayar nata ta shige, har dishi dishi take gani saboda tsabar tashin hankali, ko a mafarki Bata taba tunanin zata Sami kanta a cikin irin wannan yanayin ba, wani sabon kukan ne ya balle mata cikin kukan ta Fara rokon Allah s.w.a. Tana fadin "Ya ubangijina ka shiga cikin lamarina da wannan bawan naka, bansan ko waye shi ba, Kaine ka hadani dashi cikin kudurarka da ikonka, ka jibinci lamurana Dan isar Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w kada ka Bari ya cutar Dani ta kowanne Janibi, Ubangiji Kaine mafi tausayin masu tausayi, mafi jinkan masu jinkai ka tausayawa maraicina kasan halin Dana shiga a baya ka rabani da dariyar makiyana, innalillahi wa innailaihi raji'un Allahumma Ajirny fiymasubati wa aklinli khairin minha". Tayi rub da ciki tana ajiyar zuciya, Nan da nan Kanta ya Sara Mata sai ciwo da gyar ta iya tashin ta canza kayan jikinta Dana barci, kwantawa tayi ta shiga tariyo rayuwarta tun farkon Fara samun matsalar ta da yanda lamuran suka dunga faruwa kamar a cikin film da haka har barci ya saceta ko Addu'oin kwanciya barci Allah besa tayi ba. Sai da Mahmud ya Gama komai sannan ya hauro saman Dan Saida ya Gama wasu aikace aikacensa sannan ya shigo dakin, yayi mamakin yanda ya tarar da ita da alama barcin shammatarta yayi, pyjamas ya saka ya dawo ya zauna kusa da ita har lokacin tana sauke ajiyar zuciya a hankali. " 'yar rigima kawai, maganinki su barbar din, da bazaki Bari na samun bakin zaren da nake son kamawa ba,me bakin tsiwa kawai" Ya dan shafa sumar Kanta wadda ta kwanta baka sidik da ita sai daukar Ido takeyi. Jakarta gani a y Kasa ya dauke mata, sannan ya juyota ga mamakinsa ruwan hawaye ya gani sun gangaro daga idanunta kamar idanunta biyu, take yaji wani rashin Dadi ya shige shi, to meyasa yayi Mata haka ne Wai?. Harshensa ya saka ya Fara dauke hawayen, Jin hucin numfashinsa a fuskarta da mayen kamshinsa yasa tayi fargigit ta bude Ido. Da sauri ta yunkura zata tashi jikinta na tsuma. "Cool down precious nine". Ya riketa Jin yanda jikin ke rawa. Cikin wani irin kuka Dan ganinsa wani bakin cikin ne ya lullubeta,daya kira sunanta ji tayi Kamar ya watsa Mata wuta,da gaske ya Gama fice Mata daga Rai Sam duk yanda yake smart din Nan ganinsa take bakikkirin kamar bayan tukunya. "Ni ka sake wallahi warin najasa kakeyi, bazan iya Zama da fasiqi ba. Allah saika mayar dani gida ka rabuda dani Kuma, tunda ba tare aka haliccemu ba, daman ance tsintacciyar mage Bata mage, shi yasa ka kawoni nan ka nuna min true colour dinka, kowa kallon mutumin kirki suke Maka ashe kura ce da fatar akuya,tun yanzu ka Fara min haka Ina ga idan zama yayi zama, ai Zina har a gadon barcin mu za'ayi ta, wanda baya Jin kunyar Mahaliccinsa wazeji kunya kuma,? Ai Manzon Allah saww yayi gaskiya daya ce kuyi abinda kukeso idan bakwajin kunya". Ikon Allah ya tsaya yana kallo da gaske ta rude masa, Bai taba zaton haka take da tijara ba, kalma mafi Muni da take fada Masa ita tafi cin zuciyarsa. "FASIQI". Janyota yayi da karfi cikin jikinsa, kokowar kwacewa ta Fara tana fadin. "Ka sakeni niba mazinaciya bace kada ka shafa min masifa wallahi warin Zina kakeyi". Shi abin nata dariya ya bashi bilhaqqi da gaske take fada Masa kalmar har zuciyarta. Girgaizata yayi da karfi Yana fadin. "Zahra ki nutsu! menene haka kikeyi, waye mazinaciya?". Ba tsoro a idanunta Wanda suka tine sukayi jawur tayi masa wani kallon banza. "Kaine Mana Wanda baya tsoron taka dokar Allah Wai ka daukeni ka Kai inda zakayi masha'arka dan bani da qima da daraja a idanunka. . Cikin zafin nama ya matseta a jikinsa, cikin kaushin murya tamkar bashi bane wanda yake ririta ta ya Fara fadin... "Mai maita min abinda Kika fada? waye Dan iskan fasiqin? Anyi fasiqancin idan da abinda Kika Isa kiyi, Kuma kin Dade bakiji Ina warin najasa ba,zakiga najasa iya ganinki 'yar rainin hankali kawai, Kuma wannan ya Zama na karshen da bakinki ze fada min irin wannan maganar wallahi idan ba haka ba Zan nuna Miki ko wayeni tunda Naga bakinki bashi da linzam ke duk abinda yazo fada kikeyi bakya taunawa, saina Baki mamaki wallahi". Ya saka yatsunsa biyu ya rike labbanta na sama Dana kasa, sannan ya kafa Mata idanunsa da suka rine da bacin rai, rufe nata idanun tayi dan wallahi gani tayi ya juye ya zamar Mata wani abun tsoro, ga labbanta sai zogin rikon da yayi musu sukeyi, nan da Nan jikinta ya dauki rawa, hannu ta saka tana kokarin banbare nasa hannun daga bakinta yayi caraf ya rike hannuwan nata mutsu mutsu ta shiga yi ga babu bakin magana sai ruwan hawaye ke bin kumatunta kawai, sai da ya tabbatar ta jigatu sannan ya saki bakin Wanda har ya Dan kumbura labban sunyi jajur. Hannunta ta saka ta rufe fuskarta tana kuka Mai sauti, a haka ya taka ya wuce abinsa baiko karabi ta Kanta ba.
******* Hajiya Mama cikin tashin hankali ta dubi sahura. "Ina kike tunanin Asabe na zuwa kije ki dubo min ita". Dan jim sahurar tayi kafin tace. "Ina na sani Mama, Daman a gidan nan na Santa ta dalilinki bansan komai a Kanta ba, gidan da suke ma ai kece Kika kwatanta mini lokacin da Zaki Fara aikena gidan gurinta". Tsaki mamar tayi, ita duk lamuran sun lalace Mata, to Ina Asabe ta shiga tun jiya? ga number ta Bata shiga tayi nemanta har ta gaji amsar Daya ce a rufe Layin yake. Number Aunty Ladi ta nema ta fada Mata ga halin da ake ciki, amma itama layin baya shiga, sallamar sahura tayi, ga abin fada amma ba Hali tunda sahura iya tsegumin cikin gida kawai ta sani bata da masaniyar badak'alar karkashin kasar da akeyi a gidan. Part din Abba ta nufa duk da ba ranar aikinta bane inda sabo ta Saba irin wannan kutsen, a tufe ta samu part din abinda ya Bata mamaki kenan, juyowa tayi tana tunanin ko wani waje ya fita, to ko bayanan ai ya kamata gurin ya Zama a bude tunda Ammah zata shiga. Haka ta koma part dinta tana zancen zuci, bayan kamar minti talatin ta sake komawa kamar dazu gurin a rufe dai yake,kiran wayarsa tayi, ta shiga Amma ba'a dauka ba, abinda ya Kara daure mata Kai kenan ta nufi part din Ammah. Parlourn ba kowa sai TV a kunne volume ta rage tayi sallama shiru ba motsin kowa, wata sallamar ta Karayi daga can kitchen Alawiyya ta amsa Mata ta fito tana gaishe da Mamar. "Ina Ammah ne na shigo naji shiru inata sallama" . Cikin girmamawa Alawiyya tace Mata "tana wancan bangaren na bayan nan". "Wanne kina nufin sabon ginin da akayi?". Kaita gyada Mata alamar eh. Mamaki ne ya cika Hajiya Mama. "kije ki fada Mata Ina son Zan ganta ne yanzu" "To ai Mama suna tare da Abba ne, kuma tace kowaye yake nemanta kada a kira ta". Jiki ba kwari ta juya ta koma part dinta, taso taga Abban kwarai sai dai ta tuna da maganar Daya fada Mata kwanaki yace kada ya sake ganin kafarata da dare Idan ba aikinta bane, kome take nema ta fada Masa kafin lokacinta ya wuce karshe ma yace Mata dole ya raba kowa ya mallaki dakinsa a part dinta,wato shine aka tashi wancan ginin saboda matar so, ita Kuma ta zauna a tsohon gurin da suka Gama dabdala su biyu, kwafa tayi tana ayyana wani abu a karkashin zuciyarta. Har karfe goma Bata samu wadanda take nema ba ga Abba ma shiru be shigo ba, be kuma biyo kiranta ba har lokacin karshe ma network din wayar gaba Daya ya dauke abinda ya tilastawa Mama hakura Dole Kenan.
**