Auren huce haushi complete - Chapter 43
Auren huce haushi complete Chapter 43: Auren huce haushi complete Chapter 43. "Uwar dakina wato lamarin yallabai Yana bani mamaki gashi dai yaro Karami…
4,158 words
"Uwar dakina wato lamarin yallabai Yana bani mamaki gashi dai yaro Karami amma fa Naga alamar kowa a Karkashinsa yake,dan oga Sameer na fuskanci a nan ne yake oga amma a waje yaron oga ne". Ta fada tana dariya. Dan yatsina fuska zahra tayi. "Nifa na aje lamarin su a gefe,ita dai ai karya ai fure take Bata 'ya'ya, ni meye nawa tunda Kika min fada a kano na sakawa Raina salama na iya kaina tunda Naga abun nasu ba Mai karewa bane, Kullum da wani sabon salon da Zaki gani a gurinsu basai mitum ya Zuba musu idanu ba Randa suka shirya magantuwa sai su magantu". "Gaskiya dai kam, Nima da farko na shiga razani lokacin da aka Kaimu Kano Amma Dana ji bayani daga bakin Iya Rahane saina fashimci duk Inda mijinki ya fito ba daga Karamin gida ya fito ba,Kuma naji kishin-kishin din bacin Rai ne ya fito dashi Dan iya ta fada min sai dai tace Bata San takamaimai menene ba itama tsintar zancen tayi mommy da oga Sameer sunayi ta shigo ta kofar kitchen ta baya, abunda nakeso dake uwar dakina duk Inda rayuwa ta kaiki ki Zama Mai takatsantsan da mutane yanda naji labarin nasa dai sai kin nutsu sosai Dan na fuskanci mijin naki ko a cikin dangain na daban ne shi gaskiya, bare yanda naji iya Rahane na fada sai Wanda ya gani, Kinga dai yanda akayi ta samun akasi akan Aurenki Kuma Billahillazi asirai ne aka dunga yi nasan Allah ne ya nunawa ko waye ma iyakarsa ya Baki miji Daya da daya, wallahi a gaban idona anyi dariya an Kara akan an aura Miki Almajir Qolo Wanda Bai aje ba Bai bada ajiya ba, ance sai aga ta taqamar kyau an Kare a Almajiri mane min tsaba". Ta fada cikin nuna bacin Rai. "Kai haba Aunty zilai meye na tuna abinda ze Bata Miki Rai, ba gashi ya Zama fast ba, Ni nasan mutum be Isa yayi min abinda babu Shi a cikin kaddarar da Allah s.w.a ya rubuta min ba. Daman haka take kaddarar sai dai a jahilci irin na mutum yaga abinda yayi ne yayi tasiri,sun manta Alkawarin Allah baya canzawa". Kai Aunty zilai ta jinjina tana fadin. "Wannan gaskiya ne Allah ya Kara Miki tawakkali da qarfin imani ya doraki a Kan mak'iya da mahassada, yasa wata Rana ki Zamar musu kadangaren bakin tulu a barka ka bara ruwa a karka a Kar tulu, Allah ka nuna min ranar da karya zata Kare gaskiya tayi halinta in Sha Allahu sai kin zamar musu ciwon Ido ba yanda za'ayi dake sai hakuri, in Sha sai munga karshe masu hassada da muna furci". "Allahumma Amin". Sun Dade suna hira kafin zahra ta nunawa Aunty zilai wani daki a cikin parlour na biyu daga cikin corridor da yake fitar da mutum waje, daki ne comfortable yaji Turkish bed Mai shegen kyau yasha ubansun bedsheet sai sanyi A/C da kamshin roomfreshner dake tashi, sallama zahra tayi Mata ta wuce nata bedroom din. Wanka tayi ta Saka sleeping dress tayi shafa'i da wutiri sannan ta kwanta, lamban tayi a gado, duk kewarsa ta dameta Amma tana Jin nauyin kiransa a wannan lokacin rabonsu da waya tunda ya kirata yace Yana Dutse, da magariba tayi ta try Bata same shi ba tasan yanayi network duk da tayi marking da wuya a Kira wayarsa Bata shiga ba. Data ta bude tana duba sakonnin da suka shigo Mata ba tunda ta mayar da master layinta Daya Bata dazu. Reply din sajida ta Fara dubawa, saina Aunty Rukayya data tura mata sallama ta fada Mata itace, sakon karin jajanta rashin lafiyar malam ta turo mata har tana tsokanar ta akan meya Hana balarabiya taje India ta Sami ruwa biyu tunda kyau ne ke dukan kyau, Emoji na rufe Ido da hannu ta tura Mata. Ba zato kawai kiransa video call ya shigo, wani Abu taji ya tsirga Mata tsikar jikinta ta tashi, data tuno moment dinsu na dazu. Dauka tayi tana lumshe sexy eyes dinta. "My previoussss.." Ya fada a hankali, Yana bin fuskarta da kallo gani yayi Kamar Kara Mata kyau akeyi matukar zeyi some hours Bai ganta ba. Cikin nata salon ta bude idanunta dake Rita Masa lissafi ta saukesu a Kan nasa. "Yesss.. meu Amorrrr..." "Ya Salammmm.." Ya furta a hankali tamkar Mai tsoron wani yaji abinda yake fada, da gaske yarinyar Nan so take nayi ta sakin layi a gabanta. "Cikin muryar data saka zahra a cikin wani yanayi yace. "Inaga na fasa tafiyar Nan har sai kin samu visa Kona tafi akwai damuwa gaskiya". Tashi zaune tana cire blanket daga jikinta tunda tana jingine da pillow ne a jikin face din gadon, rigar irin transparent din nan ce Mai siririn hannu baqa sai ta Kara haskaka fatar Qirjinta sosai Nan da Nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa. Cikin shagwabar data Fara zamar Mata jiki ta Fara fadin. "Haba dai Dan Allah me Amor... kuje kawai babu Dadi Baba malam ne fa ba Wani ba,! Idan ma kazo to me zanyi maka sai dai fa ka raba hankalinka biyu, Amma idan kuka tafi zakafi samun nutsuwar data Kamata, kaji plsss.. Dan Allah". Mak'e kafada yayi tamkar yaron goye Yana Mata wani kallon Daya sakata rufe idonta dole. "Bude idonki bana son kinibibi, Kamar ba ke bace...... Bari dai nayi shiru kada na kirawowa kaina Ruwa ko?".
Luuuu tayi da Idanu, sai Kuma ta hura Masa iskar bakinta saitin bakinsa Kamar Yana kusa da ita. "Ki jirani komai dare dole nazo na biya wannan bashin". A razane ta wartsake tana marairaice fuska, tana Dan jijjiga jikinta a hankali jikin Yana wani irin shaking a hankali". "Dan girman Allah da darajar Manzon Allah kayi zaman ka wallahi Zan nemi visa da kaina Zan biyo ka". "It's too late, kiyi Shirin tarbar bako da safinsa". Kafin ta Kara rokonsa ya kashe wayar. _AUREN HUCE HAUSHI_
08055362975 ____
My WhatsApp number 09061432330
*MAMAN FATEEMAH*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w
Allah ka jikan iyayen mu da sauran musulmin da suka rigamu gidan gaskiya.
Page 62.
_______Karfe shida dot mahmud suka shiga Malam Aminu Kano international airport shida safwan Daya kawo shi, kafin su Kai ga gyara parking motar su Baba malam ta shigo wadda zayyan ya tukosu, kafin Safwan ya fito tuni Mahmud ya bude ya fice da sauri cikin wasu hadaddun suit army green sai wani wani sanyi kamshi yake fitarwa idonsa sanye da siririn eyeglasses Mai haske sosai abinda wani be taba gani a Azare ba kenan ya fito a mahmud dinsa, cikakken Dan boko da ganinsa kasan yes ba karya. Wadannan nurses din ne tare dasu Habib suka kamo gadon daukar marasa lafiya suka fito da Baba malam din. Gurinsu ya Karasa Yana fadin. " Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". Sallamar suka amsa Masa a tare, gaban gadon ya matsa yana fadin. "Barka da Asuba Baba yaka kwana?". "Jiki da sauki cikin Rahamar Allah, sannu da kokari kaji mahmudu Allah ya baka ya saka maka da Alkhairi". "Allahumma Amin" Ya fada sannan ya amsa gausuwar dasu Abubakar ke Masa, sukayi gaba shi Kuma ya koma mota ya zauna yana Kiran wayar zahra. A Nan Sameer ya same shi tare da abincin break nasu Habib. A cikin reception bangaren vip aka shiga da Baba malam, lokacin da Mahmud ya shigo su Habib suna gurin screening, gurin Baba malam suka shiga da Sameer din ya duba shi har lokaci yaran Nan nurses suna tare dashi. Ma'aikatan jirginne suka shigo suka fita da Baba malam, Sameer ne ze koma da yaran ya sallamesu duk da tun jiyan sunji alert me nauyi a account dinsu. Har cikin jirgi Sameer ya raka Mahmud ya Kara duba Baba malam yayi Masa fatan Alkhairi tare da fada Masa Shima ze shigo Daya Gama abinda yake yi. A ciki ma vip Mahmud da Baba malam suke yayin da Abubakar da Habib suke a cikin jama'a. Tunda suka tashi Mahmud ya bude Qur'an din cikin wayarsa Yana karatu lokaci bayan lokaci Yana duba Baba malam tare da tambayarsa ko da abinda yake so? abincin da ake rabawa ma cewa yayi baze ci ba. Bangaren su Abubakar,Habib kam ba baka sai kunne domin an shayar dashi mamaki ba kadan ba, yanda ya fuskanta Mahmud dai uban gidan su oga Sameer ne harda Abubakar ma tunda a airport din Nan yaga zahiri ba Wani boye-boye a ogansa ya fito sak, hatta ma'aikatan wani irin girma suke bashi. 'yar tv jikin seat din kujerar gabansa Habib ya kunne Yana ganin location din da jirgin kebi, sun kwashe awa bakwai da minti hamsin da biyu a sama kafin suyi lending a Ethiopian, an fito da Baba malam ma ya huta yaci Abinci yayi sallah, Habib sai kallon Abubakar da Mahmud yake mamaki na neman kashe shi da ransa, rayuwarsu a Azare yake tunawa duk iya kwakwar mutum baze taba sanin da wata sanayya a tsakaninsu ba ballantana kaga wani Abu Daya danganci yaro da uban gida. Shi kuwa gogan yayi fuska Kamar be gane kallon da Habib ke Masa ba. Awarsu Daya da minti goma suka sake tashi, jirginsu sai karfe shida da minti arba'in da biyar ya Sauka a INDIRI GANDI INTERNATIONAL AIRPORT new Delhi India. Suna fitowa suka iske ambulance din Max na jiran saukarsu Dan tun tasowarsu suka Fara communication da Sameer, sai a Ethiopia ne sukayi da Mahmud, ba karamin mamaki mahmud ya bawa Habib ba a lokacin Jin yana yaran indianci tamkar harshen tsohuwarsa. Ma'aikatansu suka shigar dashi cikin, Mahmud ne ya bisu, yayin da yace Abubakar ya jira Mr Salahuddeen zezo ya tafi dasu ya Kai Habib gida ya huta. Shi dai Habib yaga abinda ya girmi nasa wayon nesa ba kusa ba. Saida motar Asibitin ta bacewa ganinsu sannan Abubakar ya Dan daki kafadar Habib kadan yana fadin. "Don't mind, in Sha Allah Baba malam da kafarsa ze dawo nan,shi yasa oga ya dage azo nan din yasan suna da qualified doctors, kada ka damu yanzu muje gida ka huta tunda baka Saba da irin wannan doguwar tafiyar ta kusan twelve hours ba". "Nifa ba wannan bane damuwata ba yanda naganku da Mahmud daga jiya zuwa yau shi yafi bani mamaki abin Kamar a Shirin film". Dariya yayi Yana fadin. " Share kawai lalura fa ta gitta ai babu maganar wani boye-boye Kuma kasan yanda oga yake son malam kuwa?".
"Na sani Mana tunda tare muke dashi, kawai dai abin ne da mamaki yanda ko kadan babu wata kafa da Wani ze fashimci hakan da kuka bada". Dariya kawai Abubakar yayi ya basar da maganar, Shima Habib shiru yayi Bai sake cewa komai ba, Basu jima a gurin ba kira ya shigo wayar Abubakar, picking yayi ya Fara magana cikin harshen turanci Yana yiwa Mai Kiran kwatancen ta Inda suke. Shi dai Habib lamarin naso ya Fara bashi tsoro, gaba Daya sun juye masa daga asalin yanda ya sansu sun koma Masa wasu na daban. Suna gurin Mr Salahuddeen ya karaso, musulmi ne mutumin Pakistan, da sauri ya fito ya rugune Abubakar Yana fadin Daman Yana Nan lafiya ya yiwa india yaji tunda boss baya zuwa Shima ya dauke kafa. Dariya sukayi Abubakar ya gabatar Masa da Habib a matsayin Dan uwan Mahmud, suka gaisa da fara'a sosai a fuskarsa, Abubakar ya gabatar da Mr salahuddeen a matsayin drivern Mahmud ne duk lokacin Daya shigo kasar Kuma kamfaninsa na jewelry a Nan kasar. Har sukaje gidan da zasu Sauka Abubakar suna Hira da Mr Salahuddeen yayin da Habib ya Zama Dan kallo.
Su Mahmud suna shiga Asibitin direct suka wuce zuwa vip ward inda Sameer yayi musu booking kenan, sai suka da gyara baba malam tsab sannan suka wuce suna fadawa Mahmud yanzu masu bashi Abinci zasuzo. Kana ganin baba malam kasan ya jigatu ba kadan ba, Mai lafiya ma Yana gajiya da Zama ballantana Wanda yake a kwance, sallah suka rama kafin masu bada Abincin suzo, Mahmud Yana addu'a masu bashi abincin suka shigo tare da wasu doctors biyu da nurses biyu suma, ba laifi yaci abincin da Dan dama tunda abincin mu na Nigeria aka cike lokacin da Sameer ya cike komai, da suka Gama bashi suka dauki jininsa za'ayi gwaji sukaci Baga da sauran bincike binciken su kafin daga karshe suka cewa Mahmud zasu shiga dashi dakin bincike na musamman sai Nan da awa arba'in da takwas.
A gadon mararsa lafiya aka gungura shi zuwa dakin da za'ayi bincken, har kofar dakin Mahmud ya raka Baba malam Yana masa Addu'ar samun lafiya, hannun Mahmud baba malam ya riko. "Mahmudu ubangiji yayi maka Albarka ya amfani nemanka ya Kara maka budi na Alkhairi yanda ka jikaina kaima Allah ya dawwama maka farin ciki, ko ban tashi ba kayi kokari ka sada Fadima da iyayenka ka basu hakuri bisa yin gaban kanmu gurin aura Maka ita". "Babu komai Baba Allah ya bada nasara, in Sha Allah sai kaje Sokoto da kafarka". Murmushi yayi. "Kayya gamu dai sai abinda Allah ya hukunta". "Alkhairi in Sha Allah". Yana tsaye suka shige dashi ciki, sai kuma yaji wata irin karaya a cikin zuciyarsa. "Ubangiji ka duba niyyata ka bawa wannan bawan naka lafiya, ka tashi kafadunsa yanda mukazo kasar Nan kasa na mayar dashi Lafiya". Sai kusan biyu da rabi na dare Mahmud ya samu taxin cikin Asibitin ya nufi gida. Lokacin Daya shiga ba kowa a parlourn, Mr Ajey ya Kira a waya kukun gidan ne, fada Masa yayi ya dafa Masa coffee ya kawo Masa daki. Yaso ya Kira precious Amma ya gaji hutu yake bukata dole ya hakura wanka yayi yasha coffeen da Mr Ajey ya kawo Masa.
Tun bayan da zahra suka Gama waya da mahmud da safe ta rasa sukuni, data san haka kewarsa zata dameta da Bata bata lallabashi ba a Kan ya hakura su tafi, Batasan wani jigo bane a rayuwarta saida yayi nesa da ita tayi missing dinsa ba kadan just in one day kawai taji tana nema gazawa, Dan ko cikin barcinta shine. Da kyar ta tashi tayi wanka ta saka rigar Atampha purple Mai manyan flowers farara da ratsin yellow simple make up tayi ta yafa karamin farin gyale ta fito parlourn farko, ba kowa an gyara shi da sai kamshi yake yi ga sanyi ko Ina ya dauka, a hankali ta ratsa parlourn tana tafiyarta a nutse tamkar tana counting steps dinta ta nufi kitchen inda take jiyo motsin Aunty zilai. Kwanukan da tayi amfani dasu take wankewa, tsayawa tayi da wanke-wanken tana fuskantar zahrar dake shigowa tare da sallama. Sallamar ta amsa tare da fadin. "Barda da Asuba uwar dakina, yanzu nake tunanin naje na duba ko lafiya Baki fito ba kada abicinki ya huce. Zama tayi a Kan kujerar kitchen din tana fadin. "Lafiya kalau wallahi kawai dai bansan meya sameni ba duk bana Jin dadin garin". Dan murmushin manya Aunty zilai tayi tana fadin. Ko canjin yanayi ne kinsan bazara tana da saka kasala, ga abincin ki nan a Kan dining ko Nan Zan kawo miki?" "A'a barshi a can kawai naje naci Wai me Kika dafa need? Allah yasa Zan iyaci ni har cikina bana Jin dadinsa tun jiya". "Allah ya saukake ko Asibiti zamuje ne?"
Dan yatsina fuska zahra tayi. "Kai haba daga dan rashin dadin ciki sai mu Kama tafiya Asibiti". "To na sani uwar dakina ko Allah ya kawo Mana abinda muke nema, ai bazamuyi Wasa ba". Rufe Baki Zahra tayi da hannu tana dariya. "Kai Aunty zilai! Ki rufa min asiri ni ai ban isa wannan sabgar ba". Itama dariyar tayi tana fadin. "Bangane Baki isa wannan sabgar ba? kina nufin kallonki yake shi yallaban?". "Gaskiya dai kam, to me Zan masa". Kafin zilan ta Fadi abinda tayi niyya sukaji Karan door Bell, da sauri zilan ta fita ta nufi kofar,zayyan ta gani lokacin data bude Yana tsaye, sannu yayi Mata tunda sun gaisa lokacin data Kai Masa break fast dinsa. "A fadawa madam ta duba wayarta oga Yana kiranta". Ya fada Yana juyawa, ya koma bakin aikinsa. "Da sauri Aunty zilai ta koma kitchen din tana fadin. "Uwar dakina kije ki duba wayarki yallabai yanata Kira bakya kusa sai mutumin can ya Kira ya fada Miki ki duba Yana Kira, Dan Allah ki ringa tahowa da ita idan Zaki fito tunda kinsan mijinki baya kusa ai Kullum ta Zama ta katararki duk lokacin Daya Kira kinya samu" . Tashi tayi tana fadin. To in Sha Allah Zan kula nagode Aunty zilaina". Ta fita ta nufi bedroom din. Tana shiga bedroom din wani Kiran Yana shigowa, video call ne tunda gidan nasu suna da Wi-Fi. A cikin wani irin shauki ta dauki wayar ta dauki Kiran. "Amincin Allah da Rahamarsa su tabbata a gareki". Ya fada yana Mata wani shu'umin kallon Daya sakata Jin wani irin Abu a ilahirin jikinta. Lummm tayi da idanunta tana Masa kallon kasa-kasa, sannan ta bude Dan bakinta Wanda yake ta walainiyar lips glow a hankali ta furta. "Tare da kai". "Nagode, meye labari? Naga alama previous ba kiyi missing dina ba dubi fa yanda Keke Kara wani fresh dake Kamar wadda..... Bari dai kada na Bata show din,me Kika dafa Mana?". "Nifa yanzu na tashi bana Jin Dadi fa tun jiya da dare cikina ne Sam bana Jin dadinsa, bana Jin Zan iya cin Abinci ma kwata-kwata". Dan tsareta yayi da idanunsa da suke sakata nutsuwar dole. "Wane irin ciwon ciki kikeyi? Irin Wanda kekeyi suk ending din month ko Kuma wani ne daban?". Dan narai-narai tayi da Ido tana Masa wani kallon Nima ban sani ba. "Please precious kada ki daga min hankali wane irin ciwo ne wannan da baya tashi sai bana nan". "Bafa shi bane babu ciwo ko kadan, kawai dai cikin ne babu Dadi". "Are you sure?". Kai ta gyada Masa tana jujjuya masa golden sexy eyes dinta. Sun Dade suna hirarsu wadda ta saka kowannensu cikin nishadi da son Jin Dan uwansa a kusa dashi, Koda zahrar ta fito Aunty zilai taga canji sosai a tare da ita, ba dai tayi magana ba. Nan cikin parlour aka kawowa zahrar abincinta na Breakfast taci. Suna zaune suna Hira aka Kira Aunty zilai a waya sunan sahura ta gani, dauka tayi tana Mata sallama. Daga can bangaren sahura ta tambayi zilan Ina ne unguwar da Zahra take Hajiya Mama ta bada sako a kawowa zahra. Dan shiru Aunty zilai tayi kafin tace
Wallahi ban San sunan unguwar ba Amma ki nemi magaji ya kawo ki tunda yazo sau biyu.
Sukayi sallama Aunty zilan ta cewa zahra "uwar dakina wai Hajiya Mama ce ta bada sako sahura ta kawo miki wai nayi Mata kwatancen gidan shine nace ta nemi magaji tace ya rakota". Shiru zahrar tayi tamkar Ruwa ya cinyeta, take gargadin mahmud ya dawo Mata a cikin kwakwalwarta. "Kada ki yarda da kowa a gidanku idan ba Ammah ba, ba ruwanki da Mama Koda shiga dakinta da gaisuwa ban amince ki mu'amalance ta ba duk abinda ta Baki kada kiyi amfani dashi ko kici" Da sauri ta Tashi ta nufi daki tana ayyana Bari ta Kira magajin tace masa kada ya kawo sahura idan ta nemi ya kawo ta yace sun koma kano, tun jiya da aka tafi da Baba malam. Ta rasa meta tsarewa Mama a gidan duniyar Nan taki jininta ba kadan ba, to ko da abinda meu Amor ya sani ne akan Mama Wanda ita Bata sani ba yake ja Mata dogon warning akan kowa Dan har Aunty zilai Saida ya shata Mata wasu layuka yace kada ta wuce su a mu'amalarta da ita. 💞 * AUREN HUCE HAUSHI *
Maman Fateemah
Page 63.
............ cikin sa'a zahra ta Sami magajin a wayar, tsokanar ta ya fara. "Dan Allah ka tsaya ka isheni da magana, kanaji Wai sahura ce zata tambaye ka Ina na koma kada ka fada Mata kace Mata bana garin kawai".
"An Gama yallabiya, kinsan bazata Fara ma tunkarata da wannan maganar ba, ba sakar Mata fuska nakeyi ba tunda na gane ita munafuka ce" Tsaki zahra tayi. "Can ta matse musu duk munafurcin mutum sai dai ya koma Kansa babu abinda ze sameni sai abinda Allah ya hukunta min, Wai sako to sakon me? har wani abun arziki Mama zata taso mutum ya kawo min wadda ko kallon arziki baya hadani da ita saboda tsabar kin jinina da tayi". "Share kawai bakin ciki ne taga Allah yayi halitta a Nan take hasaada saboda nata 'ya'yan Kamar ka yanka ka boye wukar, Ni bansan wace kaddara ta Kai Abba Aurenta ba, duk matan jihar Nan Saida ya tsallake ya dauko ta Dan ma Allah yasa Basu da yawa da ansha kwantai". Ya fada Yana wata dariyar rainin wayo. Zahra ce ta katse shi tana fadin. "Amma wallahi baka da kirki magaji 'yan uwanka nefa kake fada musu haka". "Kema dai ai kinsan gaskiya na fada duba fa ki gani, kawai dai abar kaza cikin gashinta". "Allah ya shiryeka wataran sai ka fada a gabanta, ta sauke maka ajja". Tana Gama fada Masa ta yanke Kiran tasan sai su Kai minti goma shi ba gajiya zeyi ba.
Zahra Bata koma gurin Aunty zilan ba a Nan daki ta zauna, karatun Qur'an tayi sosai Dan Saida tayi surori da yawa, sannan ta shafa Addu'a ta tashi.
* Sahura ce ta shiga dakin Mama Jiki ba kwari, ganin ta shigo yasa Mama tashi zaune tana fadin. "Meya faru Kika dawo? na dauka yanzu kinje can din?"
"Eh naje Amma gidan babu alamun da mutane a cikinsa gaskiya. Dan idan ba idona ne bega dai dai ba babu wata alama data nuna giccin mutane ma a nan kusa a cikinsa, sai na Kirawo zilai nace ta fada min suna Ina ne, sai cewa tayi Wai ita Bata San sunan unguwar da suke ba tunda ba fitowa tayi ba tunda ta shiga gidan, Dan tsabar munafurci". Ta fada tana aje kunshin kayan da za'a Kaiwa zahra. Wata shariya Mama ta lafta tana fadin. "Har yaushe raini irin wannan ya shiga tsakanina da zilai? Har ta Isa ta nuna min wuyanta ya Isa yanka, wallahi idan tayi Wasa saina yi mata sanadin barin aikin kwata-kwata, ai dama matsiyaci be iya cin arziki ba". Hakuri sahurar ta ringa ringa bawa Mama ganin Nan da Nan ta ture sai masifa takeyi bakinta har kumfa yake fitarwa saboda bala'in da take kwasa . Ita dai sahura sai abin ya daure Mata Kai, to menene najin zafi haka, dan zanyi maka Alkhairi anje ba'a sameka ba, ba sai nabar abuna ba ko na bawa wani tunda Inda nayi niyya ba rabonsu bane.
Cikin bacin Rai tace kije ko magaji ne ya rakaki Mana Zaki zo kiyi tsaye Kamar baki da wayo da dabara Dan Allah wuce a gurin". Kayan ta dauka ta nufi kofa tana fadin. "Bari naje na gani ko Yana nan din". Ta wuce ta fita. Zugum Mama tayi tana nazarin yanda abubuwa suketa lalace Mata, Wai yarinyar Nan me take takama da shine? duk abinda za'ayi da sunanta sai ya lalace,ko da tsiya-tsiya yau sai sakon Nan ya shiga gidanta duk Inda ta koma ma saina lalubo shi Dan wallahi bazanga bakin cikin da ze hanani barci ba.
Duk iya kokarin sahura na taga magaji abun ya gagara wayar zilan ma an rufe ta, ko Kuma network yaki bada hadin Kai. Wata dabara ta fadowa sahura, da sauri ta nufi gurin Bala driver tana fatan samun mafita a gurinsa saboda Bata fatan ta rasa abinda Mama ta kwadaita Mata zata Bata. Yana aikin goge mota da alama fita zasuyi da Abba, sallama tayi Masa suka gaisa sannna tace Masa. "Dan Allah malam Bala ko zaka taimaka ka kwatanta min gidan da yarinyar Nan zahra suka koma naji ance sun tashi daga Nan hayin banki,Kuma na nemi duka lambobinsu ban samu ba". Ta fada tana fatan samun abinda take so. Tunda ta fara Kora bayani malam Bala ya dakata da aikin da yakeyi Yana kallon ta Saida ta Kai aya sannan yace Mata. "Haba sahura yaushe Zan dunga bin diddigin yarinyar da take gidan mijinta, ai wannan rashin lissafi nema ma wallahi ai da kunya ki fito neman gidan Zahra a Nan gurin mu alhalin ga uwarta can a cikin gida, to ke me zakiyi a can Wanda Baki son uwarta ta sani". Cikin rashin yarda da Kai ta Fara fadin. " A'a wallahi kasan wani abun alherin idan mutum zeyi baya son a gani sai dai shi yaron ya fadawa uwar tasa daga baya". "To shiga ciki ki nemi bayani dole" Ya juya yaci gaba da aikinsa ya bawa banza ajiyar ta, it's Kuma ta koma ciki da ledarta a hannu, mita yake shi kadai. "Haba mutane sai halin tsiya, Nan gaba kadan wallahi wannan mijin nata ze shayar da mutane mamaki Dan naji Alhaji Yana wani furuci jiya bansan dai dawa yake waya ba Amma Ina ganin da bincken da yake yi akan yaron Nan Kuma jiya Wanda ya saka shi ya dawo Masa da amsa".