Kenza eBookz

Auren huce haushi complete - Chapter 52

Auren huce haushi complete - Chapter 52

Auren huce haushi complete Chapter 52: Auren huce haushi complete Chapter 52. Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa…

4,156 words

Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa ta buga masa daki tana jinsa a rufe, wanka yayi ya fito cikin yadin filtex mai laushi fari tas, a parlour ya samu Hajiyar da Aminiyarta Innoni suna hira, kusa da Hajiya Innar ya zauna yana gaishe da innonin, kama haba tayi. " kai kuma yaushe ka dawo garin namu?". Tabe baki Inna tayi "kin gashi nan saida malamai suka gama karbar nasu rabon ya mula ya Mile ya dauko jiki sinkin fakiti ya dawo, yazo kuma ya zaune min yaki ko leka kofar gidan nan, kofa gidan iyayen yaki zuwa ni naga ta kaina kasan da irin wannan ranar amma ka tsallake kayi naka guri sai yanzu zaka zo kana daddofar na kaika gidan". Wata dariyar da bai shirya ba ta kubce masa. " Amma wallahi matar nan kin gama dani ni zaki cewa ina kamun kafa fake ki kaini gida,ni kadai na fito ni kadai zan koma kuma kinyi da dan halak idan na fice sai kin shekara baki sakani a idanunki ba". Ya mike ya nufi kofa, nan da nan Hajiya inna ta rude. "Idan ka bawa Annabi daraja ka dawo wallahi wasa nake maka ga abincinka can kazo kaci". Ya tsaya Amma bai juyo ba. "A aje min idan na dawo zanci lokacin magariba ya karato masallaci zani". Yana gama fada ya bude kofa ya fice. " miskili kawai idan ba haka nayi masa ba ko gidan baze leka yau ba duk kuwa yanda yake da kawa zucin uwa". "Ai mutumin naki sai ke". Saida ya gaisa da masu gadi sannan ya shiga motar da yazo a ciki ya nufi unguwarsu tunda babu nisa daga unguwar su Hajiyar, yana shiga ana kokarin tayar da sallah da sauri ya shiga cikin masallacin gidan nasu tunda da alwalarsa. Sahun bayan su Abbie dinsa yayi sallah da aka idar masu fita suka fita shi daman a dabi'arsu yawanci basa fita sai sunyi insha'i zirillahi yaci gaba dayi Abbie din bai juyo ba shima bai matsa ba sai Babban yayansu Ibrahim da yake daga jikin ginin masallacin ta kudu yake mamakin yaushe Mahmud din ya dawo kuma uncle saminu ya dawo dazu yace Mahmud ya gudu daga India, uncle mustapha ya bazu nemansa to ga Mahmud kuma a sokoto ga uncle mustapha ya sauka a abuja ze biyo jirgin karfe bakwai na dare zuwa sokoto to me kenan hakan ke nufi? Shifa daman ya dade yana zargin uncle saminu da wasu abubuwa marasa kyau a tsakaninsu. Ana idar da insha'i Mahmud ya tashi ya fice kafin Abbie din su ya tashi, hannu kawai ya dagawa securities din ya wucesu suna faman murna dan sunsan kakarsu ta yanke saka mai yiwa dawa ruwa bare gashi a karkara,koda bayanan sakonsa yana iskesu to bare gashi ya dawo. Ya dan jima a parking lot na gurin Ammi yana Karewa harabar gidan kallo ko ina haske ne tar ga wata iska mai dadi da take busowa cikin motar tare da kamshin furanni mabanbanta, abubuwan da suka faru suka dunga dawo masa daki-daki lumshe idanu yayi baiyi aune ba yaji ruwan hawaye suna bin kumatunsa abinda baiyi ba kenan duk badaqalar da aka sha a gidan nan a lokacin, kansa ya kifa jikin sitiyarin motar baiji alamun tafiya ko wani Abu sai dai jin hannun mutum yayi a bayansa bai dago ba, bubbuga kafadarsa yaji an fara kafin ya tsinkayi muryar Abbie dinsa yana fadin. "Haba! namiji baya kuka tunda ka iya jure kwaramniyar baya baka nuna rauni ba yanzu lokacin fuskantar gaba ne taso mu shiga ciki kada kannanka suga kana kuka, su raina min kai". Da Saudi ya dago jin furucin da bai zata ba daga bakin Abbie idan yayi la'akari da lokacin da guguwar abun ta tashi tsine masa ne kawai baiyi ba Amma yayi masa wata irin tujara ta Ala tsine uwar mai karya. Jikinsa ya fada yana fadin. " wallahi Abbie ban aikata ba! Ban taba zina ba, ka bani Qur'ani zan rantse da Wanda ya halicceni idan na taba zina a rayuwata Allah yayi min abinda yaso na azaba, ka yarda dani ka fadawa Ammi banyi ba sharri ne akayi min na fada Amma Baku yarda ba...kum..." Sai jikinsa ya langabe ya saki. Da sauri Ya Ibrahim dake tsaye a gefe Wanda shima hawayen yakeyi ya zaburo yana fadin . "Suma yayi Abbie bari na samo ruwa" Ya tafi da gudu ya haura steps din part din Ammi, suna zaune ya bude kofar afujajun baiko kalli su Ammi ba da saura yaran yayi kitchen da gudu ya dauko ruwan sanyi da sauri Ammi da Aishat da Batool suka rufa masa baya Ammi na tambayarsa menene? Bai ko juyo ba yayi gaba,suma gurin daya nufa suka nufa turus sukayi ganin Abbie a tsaye rungume da mutum Ya Ibrahim yana bulbula masa ruwan sanyi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da shashsheka abinya yake fada yaci gaba da fada. Ka fadawa Ammi ni ba nazinaci bane ban aikata ba". "Pls kayi shiru mana ta sani ka kwantar da hankalinka bama zarginka kaga Amminka tana jinka fa". Da sauri ya juyo sai kuma jiri ya kwashe shi ze zubar Ya Ibrahim yayi saurin rike shi suna faman jera masa sannu, juyawa Ammi tayi idanunta fal hawayen tausayin dan nata kenan duk tsawon lokacin nan yana fama da wannan damuwar wadda sai yau ya fasata gashi zata janyo masa matsala a lafiyarsa. " Allah ka biwa yaron nan haqqinsa". "Allahumma Amin". Taji su Batool sun fada sai lokacin tasan a fili tayi addu'ar. Su zahra na tsaye tana dauke da Afnan tun shigowar Wanda ya dauki ruwa ya fita su Ammy suka bishi taji gabanta yayi wata irin faduwa, ta mike tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kuma taga an shigo da Mahmud din a rirrike yana layi kamar Wanda ya bugu da kayan maye. Ai bata San yanda akayi ba ta dira a gabansa jikinta yana wata irin tsuma cikin rufewar idanu da manta a ina ma take ne ta fara fadar " Na shiga uku meya sameka meu amor...? Me akayi maka fada min dan Allah..." Hannu Aunty Aishat da Dora a bakinta data bude tana fadin. " kai? Wonderful...! the game is over".

* AUREN HUCE HAUSHI *

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

Page 76.

.............. Aunty Aishat ce tayi sauri tazo gurin zahrar saboda kowa a gurin wutarsa daukewa tayi barema Abbie da Ya Ibrahim da Basu da masaniyar da wata bakuwar fuska a gidan, itama zahrar sai data fada ta dawo Cikin hayyacinta, wata irin kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta tsage ta shige Dan kunya, me tayi kenan shike Nan tayi abun kunyar da zata Dade Bata hada Ido da Amm bai wallahi. Kan kujerar dake kusa dasu su aje Mahmud Wanda tun dirowar Zahra gabansa yaji wata irin Rahama ta saukar Masa a zuciyarsa badan a gaban iyayensa bane saiya Bata hot kisses na nuna godiyar nauyin data sauke Masa Cikin kankanin lokaci ta isar da sakon Daya Dade Yana tunanin ta Ina ze bullo musu Sai gashi in some minutes tayi musu aikin.

Aunty Aishat na rike da hannun zahra suka shige Cikin wani parlourn har lokacin jikinta Bai dawo normal ba, Afnan Auntyn ta karbe daga hannunta suka zauna. "Ki nutsu babu fa abinda ya same shi inaga farin ciki ne ya sakashi sumewa, kinsan mutumin naki da kwakawar son iyaye kinsan kuwa haduwar ai Daman za'a iya samun irin haka". Ita dai Zahra kasa daga Ido tayi ta kalli Aunty Aishar wannan abun kunya har Ina da farawa da iyawa ranar data sauka a ranar ta baza abin fada to Wai ita meye ya shiga kanta ne ta kasa controlling kanta a gaban mutane?. Itama Aunty Aishat Bata dameta da yawan magana tasan tana Cikin Jimamin abunda tayi Wanda ya bude wwani murfin da suka kasa budewa sai gashi wadda aketa kunbi kunbiyar bayyana wacece ita tayi ta bude aiki da kanta ba tare da itama ta sani ba, ta Kara girmamawa girman Allah buwayi gagara misali Dan wani connection din idan aka hada shi sai dai kayi kallo kawai, tashi tayi fice ta koma can main parlour din. Da Ido Ya Ibrahim yabi su Aishat har suka fice daga parlourn Yana kissima abubuwa masu yawa a cikin Zuciyarsa "kafa fa a gudu ba'a tsira ba". Yayin da Ammi da Abbie suka dubi juna da alamar tambaya a fuskarsu, Ammi nayi masa wani duba na Mena fada maka?. Aishat na shigowa Hajiya Inna na shigowa atfujajan uncle Mustapha na biye da Auncle Autan Hajiya Inna. " Muhammadu Rasulullahi! Ni Hadiza Naga abunda ya isheni Ashe haka ka dunga gararamba yaron Nan a cikin kasar nan kamar marar gata? saida ubangiji ya tallafeka da mutanan kirki bayin Allah masuyi Dan Allah yanzu Nan Mustapha yazo min da wannan labarin daya jiyo gurin bawan Allahn Daya tsinceshi a yashe a kasa ko takalmi babu a kafarsa ko magana fa yace baya iya yinta a lokacin, wannan Dan taliki Ubangiji yayi Masa sakayya da gidan Aljanna, duk Kuma Wanda yake da hannu gurin neman tagayyara min rayuwar jika Allah ya wulakantashi tun anan duniya Kuma wannan yaron KAINUWA ne dashen Allah ba dashen mutane ne ba, ita Kuma sameera mun barta da Allah suje suji da abun kunyarsu munafukarkar banza da Ido kamar an rutsa mazuru a dakin tantabaru na godewa Allah da 'ya'yan da take haihuwa basa Zama da yanzu ta tafi tabar mana mugun irin". Ammi CE ta matsa kusa da Hajiya Innar tana fadin. "Ayi hakuri Hajiya ai komai ya wuce ki daina tada hankalinki saboda lalurarki Bata son yawan bacin rai". "Yo bacin rai na nawa Kuma zainab ai saidai kada a Kuma". Shi dai Abbie ya yayi shiru Yana jujjuya Lamarin a zuci. Gurin Zama Ammi ta raka Hajiya Inna ta zauna kusa da inda mahmud yake zaune idanunsa a rufe. "Kai Kuma menene haka ta wani kike Riga sharaf ka kuma Kama ido ka rufe sai qif-qif kake dasu kamar wani sabon makaho". "Trouble woman". Ya fada a zuciyarsa. Abbie ne ya matso Yana gaishe da Hajiyar Yana fadin. "Haba Mustapha saboda me zaka dauko ta da Daren Nan ku taho basai a barwa safiya ba". "A'a nice nace baze taho ya barni ba kada ku taru ku nakasa shi a banza yanzu ma zuwa nayi mu tafi ko abinci baici ba, gashi ya laimin kuwa nazo na tarar kunyi ira-ira da gani wani Abu kukayi masa. Kai bude idonka ka fada min waye yayi maka wannan dibar albarkar ya jikeka sharaf haka?". Abbie ne ya zauna daga gefenta Yana fadin. "Babu Wanda yayi Masa komai murnar yaga Amminsa ce tasa ya sume Saida aka Zuba Masa ruwa sannnan ya dawo hayyacinsa". Tabe Baki tayi tana kallon Ammi wadda ta zauna daura da kafafuwan Hajiyar tana saurarenta.

"To Daman zuwa nayi na jawa kowa layi akan rayuawar yaron nan kada naji kada Kuma na gani, anyi Daya babu Kari, Kuma na nazo Kan maganar waccen matar Mai idanu Yana gwarawa wallahi ko bayan raina ka mayar da aurenta ban yafe ba sai Allah yayi Mana hisabi akan,haka me akeyi da wannan matar Mai bakar aniya aini har abada bazan taba yafe Mata ba". Ta fada tana kallon Abbie fuskarta a hade alamar ranta a bace yake. Hakuri suka dunga Bata mahmud najinsu Kuma yayi mirsisi ya bude idanunsa. "Saika tashi mu tafi ka Gama zaman gidan nan gara ma kayi aure inga ta karyar sharri Kuma haka kawai an takura maka kowa neman lika maka 'yarsa yakeyi an mayar da Kai na mamajo, kazo muje Ina da yaran dana zabar maka har hudu idan ma duka kake so saina shige maka gaba a aura makasu Rana Daya inga ta tsiyar kawo maka rida Kuma". Su dai hakurin dai suke Bata, shi kuwa da goyan tana ambatar ya tashi su tafi yayi wani Dan murmushi a cikin Zuciyarsa. "Tab ba inda zani yanzu dai da precious ke cikin gigita Sai taji dumina na kwantar Mata da hankali Nima bana son mu zauna guri Daya matsla za'a samu gara muna Dan nesa". "Wai bazaka tashin bane kayi min kunnen uwar shegu kana wani farfar da Idanu?". Uncle Mustapha ne yace mata. "Kiyi hakuri idan ya warware zuwa safe sai ya shigo ai Daman mahmud naki ne, bakiga a gurinki yayi masauki ba daze tafi ma kece ta katshen daya gani kafin yabar gidan, kefa Dan gata har sakawa yake azo takanas a kirashi video call Yana ganinki kofa tsiren da kikace Na Maru yana badawa a kawo Miki saboda Alkawari tunda a gurinsa Mahmud yake sawo Miki Bai daina kawawa ba, da naje nasameshi ya bani bill da adadin kudin tsiren Daya kawo Miki cewa yayi Wai an turo Masa kudin tsirenki na shekara ne, Yana fadin haka nasan aikinsa ne, Dan haka tashi muje na mayar dake gida idan Allah ya kaimu gone saina kawo Miki shi har gida" . Yunkurawa tayi ta tashi sai lokacin idonta ya Kai Kan Aishat. "Ke Kuma saukar yaushe Hasana? Ko Kuma ke Kika kawo shi kasar ne?". "A'a bani na kawo shi ba arashi kawai akayi nazo shima yazo". Mahmud naji suka wuce ita da uncle Mustaphan da uncle Aliyu. Abbie da Ammi da Ya Ibrahim suka bisu a baya. Saida yaji fitarsu sannan ya bude idanu Aishat da Batool kawai ya gani a parlourn duk sauran yaran sun wuce ciki. "Sannu Ya mahmud". Batool ta fada tana Dan matsowa kusa dashi. "Yauwa Batool" ya fada Yana kallonta, Aishat din ya kalla Yana Mata inkiyar tana Ina?. 'yar dariya tayi tana fadin. "Saboda Allah ka saka yarinya ta gigice irin haka har ta saki layi irin haka nasan saina amsa tuhuma a gurin Ammi Dan Naga wani irin kallo da tayi min". Batool ce ta Kara motsowa sosai ta kwantar da murya. "Ya mahmud Wai da Allah wacece wannan? tunda na ganta naji Ina sonta ina sonta wallahi gata very wise da ita, tana da kirki gashi duk abinda zata fada a Dan zaman da mukayi dazu zakiga da hikima a cikin maganarta, hikimarta ta girmi shekarunta gaskiya, gashi Bata da Jin Kai Sam idan wata ce yanda Allah yayi halitta a gurin ai sai yanda Hali yayi kawai".

"Kice kin zurma dai batool irin wannan kodawa haka?" "Gaskiyar kenan Aunty wallahi tayi, ji nake kamar jinin mu ce ita" Lumshe ido dan gogan yayi jin yanda ake Koda Masa precious tun Bata kwana a garinba har ta Fara shiga ran kannensa haka. "Matarsa ce fa bakiga ta rude ba da aka shigo dashi a rirrke ba?"

"Yehhh... Yessss... Wallahi Ko yanzu Ya mahmud ka nuna kai jarimi ne ka dauko matar da babu irinta a dukkan Family ai gara da akayi yunwa halin kowa ya fito". Ta fada tana tsallen murna kamar Karamar yarinya. A haka su Abbie suka shigo Amma ba Ya Ibrahim ya wuce parta dinsa da yake a Cikin estate din suke shida saura yayunsa. "Ke Kuma wane irin sakarci ne wannan da tshon dare kike yiwa mutane ihu haka?". Jikin Ammi ta fada tana fadin. "Wayyo Dadi Ammi Wai ashe Aunty Zahra matar ya Mahmud ce,". Shi dai Abbie gurin mahmud ya nufa ya zauna kusa dashi ya Dan taba gefen wuyansa. "Sannu me yake damunka yanzu?". "Ba komai kawai kaina ne yake ciwon kadan". "Ok.ai na yiwa doctor Hashim waya yace gashi Nan zuwa".

Jin abinda Abbie ya fada yasa Aunty Aishar da Batool suka nufi parlourn da Zahra ke zaune Basu tarar da ita a gurin ba sama suka nufa Batool nata kakabin abin tana faman magiyar Auntyn ta fada Mata ita ce ta hada Ya mahmud da Aunty Zahrar? Amsar Daya ce dai take fada Mata yanda ta ganta itama haka ta ganta. Knocking biyu sukayi Zahra tace su shigo a kan sofa suka sameta ta Zuba tagumi tana aikin tunani Afnan ta karba daga kafadar Auntyn wadda tayi barci kwantar da ita Zahra tayi. "Kuma saiki gudo Baku gaisa da Abbie ba". Sadda Kai tayi dan ji tayi Auntyn ma kunyar hada Ido takeyi da ita. "Zamu gaisa ne ai yanzu bazan iya zuwa ba wallahi kunya nakeji, ji nake kamar nayi tsuntsuwa na gudu". "Kaji Aunty meye abun kunyar a ciki keda ba rungumarsa kiyayi ba "Dan kin nuna damuwa a Kan halin da yake ciki ai Kara kankarowa kanki mutunci kikayi su iyayensa, ai Dadi sukaji ko Basu fada ba irin wannan rudewa da antayo soyyaya a gabansu sun San idan aka shiga other room Kuma sai yanda Hali yayi kenan,gaskiya a gurinki zanyi degree harda masters ma akan soyyaya Naga alamar kina Dora Ya mahmud a network". Riqe Baki Aunty Aishat tayi tana kallon Batool. "Yaushe Kika lalace haka? Wallahi Zan sami Ammi ayi gaggawar saka Miki Rana kece Mai fadar irin wannan maganganun a gaban idanuna gara a yiwa tubkar hanci kinyi service din a gidan mijinki". "Kai Aunty Mena fada Ina ce kece ya kamata ki zaunar dani kiyi min Karatun yanda Zan Kama mijin nawa, Amma bakiyi ba sai kuma Kice Zaki hadani da Ammi Wai ayi bikin ko service banyi ba salon laulayin ciki ya hanani yinsa cikin dadin rai". "Allah ya shiryeki wannan yarinyar da Baki samu miji ba wallahi cewa zanyi Ammi ta fadawa Abbie ya badaki sadaka Naga alamar idan Kika Kara watanni za'a iya samun matsala gaskiya".

Dr Hashim Bai Bata lokaci ba yazo bedroom din dake kasa wanda mahmud din ya mayar dakinsa suka shiga Dr ya duba shi, ya auna B.p normal yace ya rage saka damuwa a zuciyarsa saboda kada ta shafi lafiyarsa a irin wannan shekarun, tea yasa Ammi ta hado Masa ya Sha yayi Masa Allura ya bashi magunguna Yasha sannan ya tafi. Ba'afi minti biyar dayi Masa allurar ba ya Fara hamma zuwa minti goma yayi barci. Karfin A/C Abbie ya rage masa sannan suka fice daga dakin. Suna fitowa Ammi taja ta tsaya tana duban General. "Kaga abinda naketa fada maka ko? Game da mafarkin wannan yarinyar wallahi itace zahiri ake nuna mini a Cikin mafarkina suna tare dashi". Hannunta ya kamo suka zauna. "Ki kwantar da hankalinki lallai Allah ya nuna Miki wani sirrine da yaso ki fara gani kafin zahiri yazo Miki, tun ranar talata Mustapha ya turo min hirarsa da malamin Daya ya rike Miki yaro lokacin da baya Cikin hayyacinsa da yanda Sukayi ta fadi tashi akan nemar Masa magani da yanda ya fada anyi Masa asirin barin garin na har abada da yanda akayi auka bashi wannan yarinyar yanzu haka dai in takaice Miki labari matatmrsa ce ta sunnan wadda marikinta yayi Mata AUREN HUCE HAUSHI, saboda itama anata samun matsaloli ne a dukkan lokacin da auernta ya tashi, shine markinta Kuma Aminin malamin ya yaba da hankalinsa ya bashi aurenta ba tare da la'akari da irin matsayinsa na bako kuma Almajiri ya bashi ita, babu irin surutun da ba'ayi Masa ba ya toshe kunnensa ana ta fadar Dan ba 'yarsa bace ya Bata marar gata. To shi malamin ne ya gamu da jarabawar matsalar Spinal cord injury shi mahmud din ya fita dashi India lokacin dashi malamin yake kokarin dawo dashi gida sai kuma ya gamu da wannan lalurar yace a bamu hakuri sunyi kuskuren yi Masa Aure Amma mu dauka haka kaddarar take a rubuce gurin Ubangiji shiya kawo aka samu matsalar da tasa mahmud ya tsallake yabar gida har hakan ta faru da ba'a samu wannan matsalar ba da ta Ina zeje Azare ya zauna har a bashi auren yarinyar? Kinga Koda matarsa ce sai dai su hadu ta wata fuskar badai wannan ba tunda Allah ya hukunta matarsa ce". Jinjina Kai kawai Ammi keyi Tana Kara girmamawa girman Allah s.w.a idan yayi wani abun sai dai bawa ya kalla da Ido kawai. "Na fashimta bazan ja da hukuncin Allah ba, duk yanda yayi da bawa shine daidai naji Dadi da Allah yasa Dan uwanka yazo da maganar nan bashi Hussein ya fada ba da kuma abinda ita yarinyar tayi yanzu a gaban Dan uwansa Dan haka saika tarasu kasa Mustaphan ya kunna musu suji da kunnensu bazan dauki abinda na dauka a baya ba, Kuma sabon biki za'ayi kamar yanda ake yiwa kowa a gidan Nan maganin tsegumi Dan haka da safe Zan Kira Ya I Ishaq ya bani aron Aunty Badi'a zata rakata har Azare ta yiwa mamanta bayanin sabon biki za'ayi kosu can Basu sake ba su hada jama'arsu za'a zo a dauketa kamar ko wace Amarya da dangin mijinta suke zuwa su daukota, zatafi kima da daraja a Cikin family fiye da a wayi gari ace wai yazo da Mata ai wani ma abin magana ze Zama ko Yaya kake gani? kasan tunanin mace da namji ba Daya bane". "A maganarki babu gyara hakan yayi Amma idan har hakan za'ayi no need a ce sai kowa ya San gaskiyar maganar kawai Mustaphan yace an daura aure ne yanzu bikin za'ayi kawai Daman suna Shirin dawo dashi gida ubangidan nasa ya samu matsala Yana asibiti a India inda aka kawo labarin ganin mahmud din Ashe jiyya sukeyi a can". "Hakan yayi Allah ya Kara sutura" "Allahumma Amin" Abbie ya fada, muje ki bani wani Abu marar nauyi naci tunda Naga Alamar murna ta hanamu yin dinner a gidan nan, ki kawo min can part dina". "Kaiiii Yallabai ayi min afuwa yau Daya dai Ina da bakuwa ai nayi entertaining dinta". "Babu wannan kizo Ina jiranki ki bar musu Nan din kinsan dai zasu iya abinda zesa ki kusa nutsewa a kasa Dan kunya kuma ma ke Ina ruwanki dasu ba tare Kika gansu ba kinsa auren nasu ya dauki watannin da yinsa?". Dan murmushi Ammin tayi. "Ni fa Banga alamar yarinyar nan an mayar da ita mace ba gaskiya budurwa ce". "Kamar yaya, yarinya da mijinta ki ringa fadar haka?" Shiru tayi masa ita dai taga abinda ta gani tun ganinta da tayi dazu kafin ta sauki daga steps ta kiduri duba abinda Hajjo ta fada Mata da yake nuna yarinya budurwa ce ko tana ma'amala da maza, da niyya taje da niyyar daukar Afnan Saida ta gani sannan taji ta Samu nutsuwa. Lokacin da Ammi ta haura saman shiru da alamar sun kwanta,Saida ta Gama duk abinda zatayi ta rufo kofarta kamar zata shiga gurin zahrar saita juya ta nufi downstairs kawai tasan idan ta shiga kinya zata Bata gara ta Bari abun ya Dan bi jiki tunnna, downstairs ta nufa tana ayyana sai ta Dan yamutsa musu lissafi ko Yaya ya ne Dan su Kara sanin darajarta itafa tana kishin mace ganin an bashi yarinyar Nan a sama saiy Zahra ta Dade tana tunanin makomar aurenta baran barama dai tariga tayi sai Kuma yanda ta yuwu Wai Dan daudu a lahira. "Koyaya jikin nasa?" Ta fada a zuciyarta, ta Jima tana sakawa da kwancewa, gashi duk yanda taso ta Kira Aunty Hasana abun ya faskara haka Ammah duk network yaki bada hadin kai. Sai wurin Daya saura tayi barci, can a Cikin barcinta taji Kamar ana tabata, kwanciyarta ta gyara ba tare data bude Ido ba sai tajita a jikin mutum da wata irin zabura ta yunkura zata Mike taji an mayar da ita Baki ta bude zata zabga ihu taji carab ya hade bakinsu sai lokaci taji kanshin turarensa a hancinta, wata ajiyar zuciya ta sauke, tayi lif a jikinsa da gaske sunyi missing din juna Saida yayi Mai isarsa sannan ya dan saurara Mata ya yanye bakinsa suna maida numfashi. "Previous kin azabtar Dani whyyy... Me nayi Miki Kika haramta min ganinki kwata-kwata? Fada min kinsan halin Dana shiga kuwa? Kikasa na kasa controlling kaina a gaban elder brother dina kin kyauta min kenan?". Ita dai mukus tayi to me zata fada masa tace labewa tayi taji shirarsu da Aunty Aishat ko tace Masa me shirun shi yafi Alkhairi. Juyin duniyar Nan taki magana dole ya kyaleta ya koma wata shirar da ban. "Wai dazu da rungumeni zakiyi a gaban su Ammi?". Saka kanta tayi a kirjinsa Cikin kunya tana gigiza Masa Kai. "Kin dauka Zan tafi na barkine ko? To muna Nan sai kin haifo Mana fine babies masu Kama dake". Ya fada Yana Kai hannu akan cikinta Yana Dan shafawa. "Ka Bari Dan Allah Ammi fa tana Nan ka tashi ka tafi Dan Allah kada wani ya ganka ka shigo yayi zaton wani Abu fa". "Kwantar da hankalinki ai kin Gama Mana aikin Dana kasa yinsa a Cikin kankanin lokaci meya rage kuma? sai mu tattara mu tafi inda mukafi wayo Nima nasan nayi aure na huta da ragaita mu fuskanci rayuwa kuma, badan nayi alkawarin kawowa Ammi ke a yarinyarki ba Aida yanzu muna Shirin tarbar babyn mu ko ba haka ba?"

Wannan furucin nasa shi ya ankarar da ita akwai fa sauran Rina a kaba, Nan da Nan wani tsoro ya kamata Nan ne fa karshen maganar, a Nan ne me afkuwa fa zata afku,tunda gata a sokoto har dakin mahaifiyarsa saura da me ya rage kuma?.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull