Auren huce haushi complete - Chapter 55
Auren huce haushi complete Chapter 55: Auren huce haushi complete Chapter 55. ........... Maganar data sauka a kunnen Ammah kenan, wani kallo Ammar ta yiwa…
4,317 words
........... Maganar data sauka a kunnen Ammah kenan, wani kallo Ammar ta yiwa Abdul Hakeem na ina tunaninka yake da lissafinka yake. "Me naji kana fada tayi bako Kuma kamar yaya?". Dawo yayi daga fitar da yayi niyya. "Ammah bafa wani bane da ban Sameer ne abokin mijinta Ina ganin sako ne ze Bata fa, ya za'ayi nazo kiranta idan bansan waye ba tubda da aurenta shima ganin na hannun Daman mijinta ne Kuma ga bayanin da Kika yi min nasan da abinda ya kawo shi girinta". "Ah to yanzu naji magana, turo min magaji ya bude Masa falon baki. "Haba basai na turosa ba bani kawai na bude masa". Gurin dinning Ammah ta nufa ta dauko Masa keys din ta bashi ya fice, Alawiyya Ammah tasa ta Zuba abinci da drinks ta Kai Masa. Sai da Zahrar ta bashi a kalla minti talatin tasa dai zuwa lokacin ya Gama komai sannan ta leqa ta fadawa Ammah zataje gurinsa. Lokacin da tayi sallama ta shiga Sameer Yana tsaye da waya a kunne Yana fadin. "Dan Allah ka koyi hakuri Mana haba kamar a kanka aka Fara Aure duk ka tashi hankalina nace maka Ina Cikin gidan abincin tarba aka kawo min kafin ita madam din ta fito.....yauwa gata Nan ta fito". Ya fada Yana mikowa Zahra wayar wadda ke fadin. "Barka da sauka oga Sameer". "Yauwa sannu amarya, ungo mijinki ya hanani sakat Saida ya tasoni daga aikin daya sakani a garin nan Wai nazo na gani da abinda yake damunki". Dan murmusawa tayi. "Ni lafiya ta kalau kawai dai baya son ka huta ne, Ina baby na?". "Baby sun dauki hanyar sokoto acan zaku hadu, harda su Rukayya da mommy da mutuniyar ki ai Rukayya na fada Mata tayi tsallen albarka tace tafiya ta tashi". Ya fada yana nufar kofa. Wayar ta duba Yana Kan layin Yana jinsu. "Karawa tayi a kunne tana fadin. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". A zuciyarsa ya amsa sallamar Amma a zahiri sai yace Mata "Haba precious kunyi min adalci kenan? me yasa Zaki yarda a maida Mana hannun agogo baya, Wai Dan kada mutane suyi surutu sai a dauke min ke? Nifa nayi zaton koma menene a iya sokoto Nan ze tsayaKema na kiraki Dan na samu relief sai kik'i daga wayar sai ace min wai kuka kikeyi wato so kike na nuna musu raunina a kanki ko? Shiru tayi ita ta rasa mema zata ce Masa Umarnin mahaifiyarsa zata tsallake, da kunnanta fa taji Yana fadar Ammi ze bawa zabi ta zabar Masa Mata, to Kuma tace ta tashi tabi yan uwanta su tafi to musu zatayi Mata tace bazata ba ko Yaya?shi me yasa ya Bata zabin tayi abinda ya dace, ita Bata kullace shi ba sai ita zega laifin ta taho wato shi yayi biyayya ita kuma ta nuna ba haka ba ace kwadayin dukiyar su take yi kenan,duk da itama a Cikin wadatar ta tashi gaba da baya Amma ai ba kowa ne ya san hakan ba. "Kinyi shiru precious". "Me kake son na fada bayan biyayya na yiwa Ammi cewa fa tayi na tashi mu tafi kawai lokacin banma San inda zamu ba Saida mukazo Kano Naga mun dauki hanyar Azare na gane Ina zamu,ai Ina ganin kawai mu hakura mu yiwa Iyayen mu biyayya kaga Nima biyayyar nayi lokacin da aka bani Kai bansan Koda waye aka daura min aure ba,Amma na hakura nayi biyyyar iyaye kaima kayi biyyyar idan Ammi bani bace zabinta muyi hakuri haka Allah ya nufa zaman takaitaccene kabi abinda takeso bazaka tabe ba in Sha Allah". Cikin tashin hankali ya Fara magana. "Me kike fada haka preciousss? Kina son heart attack ya sameni? Waya fada Miki Ammi Bata Sonki? Soyayyar tasa ta raboki da gidanta badan Bata sonki ba Kinga yanda ta kasa zaune ta kasa tsaye duk fa kunyar Dan fari Ammi ta aje a gefe hidimarta takeyi babu Kama hannun yaro, Ina gama da sakon data bawa Sameer ya kawo Miki, na Ammah Ina Jin sai gobe za'a taho dashi, ki shirya dake za'a taho min fa a Mika min kayana daga cikin daki Nima naji abinda 'yan uwan sukeji na gaji da gararamba gara na tsuguna Nima na Fara hada nawa family din, in sha Allah da biyu Zaki Fara min ko 'yar gidana". Runtse idanu tayi ita fa idan yana ambatar irin wadannan kalaman na haihuwa tuno yanda sabgar take kafin samun abun haihuwar shine damuwar ta da gasken gaske tana hasaso ranar da alama Kuma an dauki hanyar zuwanta. "Dan Allah ya mahmud ka Bari ba kyau fa irin wannan maganar" "Kam bala'in waye yayan naki Allah ki iya bakinki babu hadin Zuma da guna,ki nemi yayanki tun dare be Miki ba,Ni ki barni a your love dinki kawai ko kin manta meu amor dinki ne...? Pls Dan fada min irin tanadin da aka yiwa meu amor a wannan special day din?". "Wayyo.... Dan Allah ka rufa min asiri.. ni wallahi wannan zancen yafi karfina pls Kan bariiii..? Ta fada da sigar data yamutsa Masa jam'iyya nan da nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa. "Ya salam! Previousss Anya Zan iya hakurin kwana uku nan gaskiya tahowa zanyi na daukeki mu wuce Dubai inda a tanadar Miki Dan amarcinki alkawarin nayi azumi uku kawai bazan iya ba" Ya fada Yana Mata wani irin numfashi a kunne, da sauri ta cire wayar daga kunnenta tana fadin "nashiga Tara me kuma nayi Masa? Da sauri ta mayar da wayar tana Masa magiyar ya rufa Mata asiri kada ya jawowa mahaifiyarsa abun fada Cikin kishiyoyi. Ba Karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin ya hakura, da gaske tuburewa yayi shi baya son bidi'a ansan tun yaushe suke tare da za'a wani tarki bikin babu gaira babu dalili, tana samu ya Dan sauka tayi Masa sallama tace Ammah tana kiranta anyi Baki,yasan neman guduwa takeyi kawai Bai barta ba saida ya jaddada Mata ze Kira da dare. Lokacin data fito Sameer baya kusa tasan suna tare da ya Abdul Hakeem part dinsu ta nufa Ya imam ta gani ta tambaye shi ko su Ya Abdul Hakeem suna nan? Tabbacin hakan ya Bata Kira shi a wayar ta tace tana jiran oga Sameer. Ba jimawa suka fito ya Mika Masa wayarsa, tana fadin . "Gashi nagode". Karba yayi yana fadin.. "Bari na dauko Miki sakon Ammi Wanda ta bayar a kawo Miki".. Wata Leda Yar madaidaiciya ya Miko Mata Yana fadin. "Gashi Aunty Aishat tace zakuyi waya". "Ok Nagode, bazaka shiga ku gaisa da Ammah ba?" Yar dariya yayi. "Na nawa kuma? Na shiga mun gaisa". Dan murmushi tayi ta nufi Cikin gida. Ba zato tayi arba da Aunty Hasana da gudu ta shige jikinta tana fadin. "Aunty kin manta Dani wallahi, laifin me nayi Dan Allah". "Kuji mun yarinya ! Sai Kuma nayi ta kiranki a waya har mijinki ya Raina ni ya daina Jin 'yar kunyar tawa da yakeji ai yawan damun kani ko d'a da Kira a waya bini-bini Yana kawo raini da rashin ganin kima a tsakani gara a ringa daukar lokaci yanda duk lokacin daka Kira ya Zama ana marmarinka ku rabu ana kewarka da Jin ba'a gaji da Hira da Kai ba". "Wannan maganar taki bisa hanya take, haka ake son Babba yaja girmansa". Hajiya kaltume ta fada. "Ah to Mamma fada Mata dai so take girma ya Fadi a gurin kanin nawa yanzu kuwa Aunty sama Aunty kasa duk bayan kwana biyu saiya kirani ya gaisheni". "Aunty Ina zuwa". Zahra ta fad'a tana nufar bedroom din data yiwa kanta masauki, Bata Jima ba ta fito da abinda Ammi ta Bata ta mikawa Aunty Hasana tana fadin. "Gasu Nan na manta dasu Ammi ce ta bani jiya da zamu taho". Bata zauna ba daki ta jiya tana rike da hannun Autar Aunty. Aunty Hasana ce ta cire rapping sheet din na madaidaicin, white gold din ne yayi musu maraba, da sauri Hajiya kaltume ta matso tana fadin. "Masha Allah girma sai Dan girma wani kayan sai amale wane jaki,lallai babban goro sai magogin karfe, irin wannan kyautar girma haka, 'yan biting bude sauran muga abinda ke ciki". Wata ubansun Alkyabba ce baka da ratsin zare golden sai turarika masu azabar kamshi a ciki. Jim maganar Hajiya kaltume yasa Ammah fitowa daga daki taga menene ake dagawa murya haka? Sarkar Hajiyar ta mikawa Ammah. "Duba kiga Karamar arziki irin wannan daga uwar mahmud, Ashe dasu tazo gidan ta aje ta shiga tata sabgar, inga fa sarkar Nan ta tasamma wajen fifty millions wallahi Dan kwanaki mun siyar da wata Bata Kai wannan ba wurin forty seven milion aka sayar". Ammah rasa abin fada tayi saboda abin ya Bata mamaki to su wane irin dukiya garesu mutanen nan?. Nan suka zauna suna ta maida yanda akayi har kusan la'asar duk abinda ya kamata sunyi yi an bada aikin kayan garar da za'a Kaiwa Zahra Dana Iyayen mijin duk wata al'ada da ake a sokoton Ammah ta tambaya an fada mata, da yammaci suna zaune Abba ya shigo Yana fadin. "Asma'u ku tanadi abun tarbar Baki gobe in sha Allah bakin sokoto na Nan tafe yanzu ba dadewa Kanin Alhaji Muhammad ya kirani yake fada min zasuzo naso na hanasu duba da nisan dake tsakanin Bauchi da sokoto Amma ya nuna min a'a idan ma yafi haka zasuzo godiya ce zasu zo tunda ba aure za'a sake daurawa ba inaga ko maza ne ko kuma Mata da maza ne ban sani ba dai sai ayi dai abinda ya kamata nace Abdul Hakeem suje da magaji a debo zabi sai a Kara Dana gidan idan yaso sai a kawo sabo Naman na gida. "To Allah ya kaimu, ya Kuma maganar furniture's din da za'a tafi dasu daga nan?". Sai goben insha Allah za'a had a da kayan da kikace za'a kawo daga Bauchi Sai a tafi dasu gaba daya ai inaga hakan yayi ko?"
"Eh hakan yayi Allah ya saka da Alkhairi ya jikan mahaifa". Ameen su Hajiya da Aunty Hasana suka fada ciki ya shige Aunty Hasana ya tashi tabi bayansa. Aiki su Ammah suka Fara babu kama hannun yaro auta Ammah ta turo makota tace ya fada musu su shigo gobe za'a karbi Kaya Kuma ya fadawa mamansu mujiba idan Abbansu yana gidan ta tambaye should ta shigo zasuyi aiki. Hajiya kaltume Bata bar gidan ba sai kusan Tara na dare, taso a Kara yiwa Zahra gyara Amma Aunty Hasana tace a karba a tafar Mata dashi tunda Hasanarsa ta kaita gurin masu gyaran Amare a India a barta haka Nan tunda Abu ne a duhu ba'asan yanda abun yake ba". "Eh to kema da gaskiyar ki Naga 'yar tawa har yanzu zubin 'yan Mata gareta babu kamar cikakkiyar mace a tare da ita". Da haka suka rabu haka Nan taji Bata son a Kara Bata komai idan ba fruits ba gaskiya Bata son wannan tonon sililin duk da bata da tabbas na wani Abu be shiga tsakani ba duba da tun lokacin da akayi bikin to sai dai a yanda zilai ta fada Mata bayanin da likitar Nan tayi Mata Lamarin abun dubawa ne kwarai, ita fa tausayin Zahra takeji yanda taga anyi Mata wannan gyaran tasan sai yanda Hali yayi kawai Amma da Qura a gaba.
Washe gari da sakkon aiki suka tashi Dan tun shida Maman mujiba ta shigo ita da Aina'u makociyar itama suna gaisawa sosai da Ammah din, duk bidirin da akeyi Mama Bata fito ba ko kuma tace me akeyi babu Daya,itama Ammah ta bawa banza ajiyarta. Karfe Tara Mai kyau su Inna maimuna sun shigo gidan a Bauchi suka kwana saboda sunyi dare bana Wasa ba dole suka hakura suka kwana a can. Wasu dunkuna ne aka kawo wanda Aunty Hasana ta bayar aka dinkawa Zahra express laces ne na manyan Mata Wanda suke ji da Kansu na manyan kudi ta saya saboda yau masu kawo Kayan walau maza ne ko Mata ya Zama dai babu raini duk da babu inda makusa take ta ko ina kawai dai idan kana da kyau ka Kara da wanka ne. Karfe sha biyu ta gota wasu lafta laftan motoci suka tsaya a kofar gidan Alhaji Jafar Mai yadi wa Bata lokaci Mai gadi ya bude musu tunda Alhaji ya fada Masa za'ayi Baki a gidan to Yana ganinsu yasan bakinne. Gate baba sani ya bude musu suka Sanya Mai cikn harabar gidan.
A can Kuma Zahra ce tayi make up simple ta saka fitted gown na rigar lace sai ta fito da ainihin structure din jikinta yake. Su dai su Hajiya kaltume dasu Inna mainuna suna zaune Basu yi aune ba sukaga an Fara shigowa da Kaya, tun suna girgawa har suka zubawa sarautar Allah Saida aka zube set goma Sha biyu, sai kuma mata suka shigo bisa jagorancin magaji su kuma mazan suna gurin su Abba da jama'arsa. Sannu da zuwa aka Fara jera musu mutanen Cikin parlour din tare da Basu girin zama, Aina'u ce ta ware murya ta zankada guda uku a jere abinda ya fito da su zilai da sahura daga Ina suke zaune a gidan, Mama ma fitowa tayi da Dan sauri tana fadin. "Menene akeyi a gidan nan haka da uwar Rana ake ta rafsa guda. Part din Ammah ta nufa da sauri su zilai duna biye da ita a baya, turus tayi ganin Iyayen akwatuna a zube a parlourn,kasa daurewa tayi. "Wannan kayan fa na waye haka?" Inna Maimuna ce ta Bata Amsa "na Amarya Zahra ne kin san mijin nata ya koma gida shine iyayensa suma zasuyi nasu bikin". Taku biyu tayi sai ganin ta akayi a kasa ta fadi jikinta na wata irin karkawa Nan da Nan aka yo kanta da sauri Dan Bata taimakon gaggawa.
.*AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
08055362975
Or
09061432330
Page 80.
.....….….. Subhanallahi mutanen dake parlourn suka dauka, da sauri Ammah da Aunty Hasana suka matso gurin da Mamar ta Fadi Ammah tana fadin.. "Ikon Allah har yanzu jikin ne kenan da Baki fito ba, Hasana maza Nemo Abdul Hakeem ko Hamza aje asibiti"O. "Gaskiya dai Kam tunda abun Yana neman ya Zama wani Abu daban". Hajiya kaltume ta fada yayinda wata daga cikin bakin tace. "Anya Bata da hypertension kuwa?". "Nima abinda nake tunani kenan gaskiya". Ammah ta fad'a. Cikin kankanin lokaci Hamza da imam suka shigo yayin da a waje Abdul Hakeem ta fito da mota, zilai da sahura ne suka dauketa suka nufi waje da ita, Aunty Hasana ta rufa musu baya suka fice. Saida komai ya lafa sannan su Hajiya kaltume suka samu Damar fuskantar bakinsu,nan da nan aka Fara sauke musu ashirin ta arziki Alawiyya da magaji Wanda Bai bi Yan asibitin ba domin yasan tsabar tashin hankali ne ya haddasawa mama wannan abun ba komai ba, duk Wanda yace ruwan wani baze tafasa ba nasa ko zafi bazeyi ba. Abinci bakin waje suka ringa fita dashi, sai da bakin sukaci abinci sukayi sallah sannan Aunty Surayya ta gabatar da Kayan lefen gasu Hajiya kaltume dasu Inna maimuna wadda tun faduwar Mama taja jikinta gefe tasan mugun nufinta ne ya Fara tambayarta tunda taga duk yanda ta dunga dakile Lamarin Zahra Ubangiji ya nuna Mata shine Arrazzaqu shike daukaka bawa duk kuwa yanda makiya suka so su dankwafe mutum sai ya nuna karfin ikonsa a Kan abun, gashi an waya gari Zahra tayi musu wata irin tazara tamkar tsakanin sama da kasa haka tazarar take,abinda ko a mafarki ko a hasashe babu Wanda ya taba kawo hakan.
Sun godiya sosai, sannan Aunty Surayyar ta dauko key ta mikawa Hajiya kaltume tana fadin gashi inji Ammi tace a kawowa Ammah tana gaisheta kafin komai ya lafa tazo su gaisa ace ayi Mata godiya sosai da sosai. Duk gurin ba Wanda baiyi mamaki ba na wannan kyautar girman da aka yiwa uwar Amarya. Matan makotan da suka shigo suka Fara bude kayan ana gani ana Sanya Alkhairi a ciki. Aunty Mahafuza Matar Ya Ibrahim ce tace . "Wai ina amaryar tamu ne a rakamu mu gaisa da ita kafin a kaimana ita". Inna maimuna ce tace "tashi muje ai ba nisa tayi ba tana Cikin dakin nan". Tashi tayi tana fadin gara muyi sabo tun daga Nan na Zama ta farko da zata sani a cikin matan yayun mijinta". Inna maimuna na gaba Mahafuza na binta a baya har kofar bedroom din dasu Zahra suke ita da mujiba da Yan uwanta da sukazo dasu Inna maimunar Salima da Ibtihal, salima ce ta bude kofar su Inna maimunar suka shigo idon Mahafuzar Yana Kan Zahra wadda take zaune a Kan sofa Tasha ubansu lace Wanda ya amsa sunansa tayi wani irin fitinan nan kyau a cikinsa tana daddanna iPhone sixteen plus dinta tana daga sexy eyes dinta sukayi four eyes da Mahafuzar, ba shiri ta hadiye wani Abu Daya sille ya wuce Mata Bata shirya ba. "Tabarakallahu Ahasanul kaliqin, Masha Allah" ta fada a zuciyarta, ai ita a yanda Habibinta ya fada Mata yarinyar Daya gani a part din Ammi da yake tunanin ko budurwar mahmud din ce sai taga Bai iya bada bayanin mutum ba Sam. Da fara'arta ta shigo tana musu sallama da fara'a Suma su salima suka amsa Mata suka gaisheta, Cikin nutsuwa da Jan ajiya da nuna sanin ciwon Kai Zahra ta gaishe da Mahafuza din. Gurin Zama su mujiba suka bawa Mahafuzar suna fadin. "Ki zauna Mana ga guri Aunty". Gefen gadon ta zauna tana duban zahra a kaikaice, haka Nan yarinyar tayi Mata kwarjini sosai sai taji duk ta Raina kanta duk da itama 'yar gayu ce kuma ba laifi da nata daidai kyawun Amma ganin zahra sai taji tayi lakwas tunda da biyu ta nace akan saita biyo masu kawo lefen duk da mutum hudu kawai ake bukata Mata Saida tayi yanda tayi Dan taga kul uwar daka, tunda daga waje taji gwiwarta ta sace tasan wannan da alama tafi gaban raini, to Kuma sai gashi taga itama Zahrar zahra ce ga Jan aji da alama bazata dauki raini ba.. Ganin shirun ya yi yawa yasa Mahafuza tace Amarya zamu tafi "Ni sunana Mahafuza matar Ibrahim Dange yayan mahmud". Dan murmushi zahra tayi. "Na gode Aunty Mahafuza". Tashi tayi tana fadin. "Nima na gode Amaryar mu sai kin Karaso naso ace Ina Cikin masu kwana mu tafi tare". 'yar dariya zahra tayi wadda ta Kara fito da sirrin kyawunta. Bayan ta fita Ibtihal tayi wani tsalle tana fadin. "Yessss! Adda zahra haka nake son Kama Kai da nemawa Kai mutumci". Wayar hannunta ta aje tana fadin. "Ibtihal Baki Jin magana wallahi me Kuma nayi?". "Meye ma bakiyi ba irin wannan jam class haka kamar wata saraunya fa haka kikeyi acting". Dan murmushi zahra tayi tana tuna hudubar Hajiyar makwarari lokacin da take Mata karatun dangin mijinta da yanda zata zauna dasu da yanda zata kama kanta kada ta bada fuskar da za'a Raina ta, wato ta yarda da maganar da Hausawa ke fada na cewar duk abinda Babba ya hango yaro baze hango ba ko ya hau itace rimi sai yau ta yarda da hakan, da gani wannan da salon nata rainin hankalin ta shigo Sai kuma taga an fita iyawa. Suna Nan suna maida yanda akayi Su Aunty Surayya suka shigo Zahra ta gaishe su, Nan Aunty Mahafuza ta gabatarwa Zahra Aunty Surayya da kanwar Abbie maman ya Abbas surukar Aishat sai 'yar kanwar Hajja kakar su Mahmud ta wajen uwa, sun yaba matuka da zabin mahmud sosai, sunyi musu Addu'ar Albarkar Aure sannan suka fita. Aunty Surayya ce ta dawo ganin ta dawo yasa su salima suka fice daga dakin. Kusa da Zahra ta zauna wadda ta sadda Kai saboda wani nauyinta taji ya kamata niyyar zamewa tayi kasa Aunty Surayyar ta hanata. "Zauna magana zamuyi dake, kina jina Zaki shiga sabon guri da wasu mutane Wanda zakiyi rayuwa ta har abada dasu in Sha Allah,to ki nutsu ki fashinci kowa kada kiyi garaje a cikin tafiyar ki saka hankali sosai gurin wadanda Zaki mu'amalanta babu ruwanki da kowa babu ruwanki da 'yan matan family din Nan duk yawancinsu burinsu Kan mijinki yake kada wata ta dauko Abu ta kawo Miki da sunan kyauta naci Kona Sha kiyi amfani dashi idan Kika cire Amminsa to sai Hajiya Inna, koni idan ban Kwanta Miki ba kada kiyi amfani da abunda Zan Baki kinji ko". Kai Zahra ta gyada mata. "Naji Aunty nagode in Sha Allah Zan kula da abinda Kika fada mini".
"Yauwa Kinga pass na dinner ko? Aishat tace zakuyi waya ki bawa kawayenki na kusa wadanda Kika San zasuje tunda abune da anan ya Riga ya Dade da wucewa mu a canne yake sabo, Kuma gobe insha Allah zaku taho mu yau zamubi jirgi daga Bauchi zuwa sokoto tunda mu duka har mazan mu bakwai ne, Kuma anan zamu bar Hajiayarsu Abbas da Hajja Asiya tare dasu zaku wuce goben, ki kula ki daraja Ammi tana sonki matuka kinji". Kai ta gyada Mata sai taji matar ta burgeta sosai domin a zamanin Nan babu Mai fada maka irin wannan sai mai kaunarka. Alawiyya ce tayi knocking ta leko tace "ana jiran Aunty Surayya". Sallama ta yiwa Zahra ta fice da sauri.
***
Tun kafin aje asibitin Mama ta dawo hayyacinta abun nata kamar iska haka Nan suka karasa a A/E suka dubata, tambayoyi suka shiga Jero Mata akan wane abune ya daga Mata hankali har BP dinta ya Mai dari da tamanin kasan ya Kai dari da goma, dagewa tayi ita babu abinda ya tada Mata hankali, su dai su Aunty Hasana Ido ne nasu, Mama taso su barta su dawo gida Amma suka riketa saboda sunga karfin Hali ne kawai takeyi Amma Bata da lafiya sosai zuciyarta ma tana neman kamuwa da ciwo matukar ba'ayi controlling din jinin ba, dole ta hakura aka saka Mata magani a kasan harshe aka Kuma saka Mata Karin ruwa aka saka Allurar barci dole tanaji tana gani barci yayi awon gaba da ita, Ammah ta kirawo Aunty Hasana ya Kai sau uku tana tambayar ya jikin nata. Daga karshe Aunty Hasanar gida Abdul Hakeem ya dawo da ita ta baro su zilan a can, lokacin data dawo bakin da zasu tafi sun tafi sai mutum biyun da zasu kwana suma Sana can bangaren baki. Kayan ta tarar Makota sun shigo an bude iya Wanda za'a Iya budewa sauran kuma an tattarasu gefe guda Dan bazasu ganu a Kan kanin lokaci ba. Yawan akwatunan Aunty Hasana ta tsaya kallo, Saida ta shiga dakin Ammah ta tsinkayo zancen motar da Ammi ta aikowa da Ammah. Washe gari tun sassafe motocin Kaya biyu suka dauki hanyar sokoto. Tun dare Mama ta dawo daga asibitin, matsa musu tayi akan a sallameta dole suka sallameta duk da Abba yace ta hakura ta barsu suyi aikinsu ta matsa ita dai babu abinda yake damunta. Zahra har dakin bakinsu salima da Ibtihal suka rakata ta gaishe dasu Cikin ladabi da biyyaya, shi Albarka dai zahre ta shata. Lokacin da meyin makeup ne tazo Zahra Ido ya Raina fata da duk gani takeyi kamar wasa ne babu inda zata tafi shi dai ya dawo ya same ta kamar yanda ya Saba. Nan da Nan taji wata irin karaya da tashin hankali ya saukar Mata ai ji tayi wancen wasan yara ne yanzu ne dai za'ayi maganar gaskiya,Cikin abinda be wuce minti talatin ba aka gama komai tayi kyau kamar me, sai Zuba wani kamshi take na musamman, ita kanta Ammah dauriya kawai takeyi Dan ganin abun tayi kamar yanzu ne take bikin wancen Wasa tayi duba da yanzu yanda ake komai da dangin mijinta ba kamar wancen Karon ba da su kadai su kayi budurinsu, ga tashin Hankali Sam babu nutsuwa haka tana gidan Kullum tana zulumi akan yaron kada ya gudu da yarinya ko Kuma ya gudu ya barta da ciki ba Kuma asan asalin inda za'a nema shi ba, Amma yanzu Allah s.w.a ya gama Mata gata ya juya Lamarin 'yar marainiyar Allah ya share Mata hawayen data Dade tana zubarwa akan tozarcin da ake Mata akan aure, sai gashi Ashe wani hanin ga Allah baiwa ne, wa ya taba zaton yaron Nan wani ne ko Dan wani? Ba Karamin toshe kunnuwa Abban Yara yayi ba lokacin da ake Kan ganiyar maganar ana ta ruruta wutar ya aura Mata Almajiri Wanda ba'a San asalinsa ba Dan ba 'yarsa bace Amma ace duk yanda take da kyau da cikar halitta ta Kare a kolo fakiri marar madafa, to gashi hakuri Mai tarar da arziki yau ga Zahra ta Zama farin wata Sha kallo, ga lefen da ba'a taba kwatanta kawo Mata Koda kwata dinsa ba, yanzu haka wancen lefen suna Nan a daki to ga Kuma wannan Sha kumdum din.
Wurin Abbanta Aunty Hasana ta rakata yayi Mata Nasiha sosai ya Kara jaddada Mata mashimmancin biyayyar Aure. Kafin karfe Sha Daya gidan ya dinke da jama'a abin har yaso ya bawa Ammah mamaki to ita dai Hajiya kaltume ta dankawa I. V din da Ammi ta aiko dasu na mutanen Ammah ita dai kawai tasan ta Debi shida ta bawa maman mujiba tace ta aikwa makota Koda Wanda zasuje kada abun ya Zama na tsegumi. Zahra ma nata mujiba ta debarwa tace ta bawa kawayensu Amma kadan zata bawa ita kunya ma takeji Ace Wai za'ayi wani Abu kuma na bikinta, daga baya kenan Wai sadaka da bazawara. Ta bawa magaji ya kaiwa Amatu da Aunty safiya sai wasu Kuma ta bawa sauran malaman duk da tasan abune Mai wahala suje tunda ko a Nan basuje ba tunda sukaji labarin ance mijin Almajiri ne. Zahra na dakin Ammah su Inna suna karayi Mata nasihar zanmantakewar aure tana ta sharbar kuka, ficewa Ammah tayi Dan itama daf take da sakin nata kukan. Tun dare Ammi ta Kira Ammah ta fada Mata akwai tickets na mutum goma a Nan hannun wani a Bauchi Wanda zasu rako Zahra dakinta, Sameer Yana Nan shine ze musu komai ze shigo su wuce sauran mutanen Kuma motoci sun taho.