Auren huce haushi complete - Chapter 62
Auren huce haushi complete Chapter 62: Auren huce haushi complete Chapter 62. Suna ficewa Aishat ta karaso kusa da Zahra ta zauna wadda har lokacin…
3,933 words
Suna ficewa Aishat ta karaso kusa da Zahra ta zauna wadda har lokacin idanunta a rufe suke. "Sannu zahra, ki tashi nasan idonki biyu ga doctor tazo ta dubaki kinji". Rinannun idanunta ta bude ta kalli Auntyn Nan da Nan taji idanunta sun kicciko. "Aunty Aishat Dan Allah kirawo min Aunty Hasana". Sai hawaye sharrrr... Suka biyo kumatunta. Hannunta farare sol Aunty Aishat ta rike tana girgiza Mata Kai. "Pls ki daina kuka gashi Nan za'a dubaki". Kanta kawai ta iya gyada Mata. Tashi Aishat din tayi tana fadin "doctor Bari Naga bros". Tayi waje tare da ja musu kofar tana Jin tausayin zahra da gani Bai saurara Mata ta ko kadan. "Sannu Daughter kinji Bari na duba na gani sai asan abinda za'ayi Miki, hands glove ta saka ta umarci zahrar ta gyara ta dubata. Jikinta tsima ya Kama da kyar ta Bari doctor zainab din ta dubata cikin ikon Allah Bata karu ba sai dai gurin Kam sai a hankali, dan Allah ya taimaketa jikinta irin roba din Nan ne Wanda ko haihuwa masu irin jikin sukayi Basu fiye budewa ba, jikin ba gautsi, a cikin Mata dari da wuya ka fitar da goma masu irin wannan halittar. Ruwan zafi ta shiga ta hada Mata da kanta ta sakata tana hawaye tana komai, Saida ya canza Mata sau uku cikin ikon Allah sai taji jikin Yayi Mata Dadi fitowa doctor din tayi zahrar tayi wanka ta fito simple Riga ta Bata ta saka sannan ta leka ya fad'awa Aishat ta hado Mata tea Kofi daya ta koma a kitchen din bangaren ta hado saboda babu abinda babu a ciki. Tea me kauri sosai ta hado Mata a gefen gado ta Samu zahrar tana Zaune yayin da doctor ke hada wasu allurai. Hajiya Inna ce keta fada akan Mahmud yaki Kira Mata Abbie dinsa ya Kuma Hana Aishat ta kirawo Mata shi. "Dan Allah ki tashi ki koma Zan Sha magani kawai, nifa lafiya ta kalau kawai dai bana Jin Dadi ne". Cikin hukuncin Allah saiga kira ya shigo wayarta alamar mota data gani tasan Mustapha ne da sauri ta dauka Kota Kan sallamar da yake Mata Bata bi ba ballentana ta Sami zarafin amsawa. "Kanaji na Mustapha maza ka taho da likita gidana tunda Aliyu baya gari ya duba min Dan biyu gashi Nan Zazzabi Yayi Masa rigijib ko daga Kai baya iyawa" . Ta kashe wayar, Baki bude Mahmud yabi Hajiya Inna da kallon mamaki Wai ko Kai baya iya dagawa "ikon Allah". Can Kuma uncle Mustapha suna tare da Abbie tun bayan da aka fito masallaci suke Zaune a harabar masallacin suna hirar zumunci shine uncle Mustapha ya Kira Hajiya ta tambayeta ko akwai abinda ze taho Mata dashi Dan daga Nan can gidanta ya nufa. Yayansa ya kalla Wanda shima shi yake kallon domin wayar a speaker take. "Ikon Allah meya Kai Mahmud kuma gidanta shida ga gidansa can, ko Kuma da yaji ciwon ne ya tafi can kasan shida ita tasu Bata baci". Uncle Mustapha ya fada. "To waya sani ka Kira doctor Anka sai ku hadu a can ya duba shi". Sallama sukayi Abbie ya nufi cikin gidan Yana kokarin Kiran Ammi, yayin da uncle shima ya nufi motarsa ya shiga Yana kokarin lalubo number doctor Anka din. Allurai kusan Kashi uku ta yiwa zahra wadda Saida Aunty Aishat ta riketa akayi Mata sannan ta Bata Analgesic table ta Sha ta bawa Zahra wani tube na cream tace ta shafa a can da Kuma Kan breast dinta inda shima ya dade, ta Kuma jaddada Mata shiga ruwan zafi Kamar sau biyu kafin dare Dan yanda gurin yayi sai a hankali kawai Dan ma dai Tana cikin Wanda ubangiji Yayi musu special gift da labarin ba wannan akeyi ba. Tare da Aishat suka fito suna Nan second parlour shida Hajiya innar sallama tayi musu tana fadin "yallabai in ganka mana". "A'a babu inda zaya shima ba lafiyar ce dashi ba,ko meye Fadi Masa a gabana ai ba kunyata yakeji ba tunda ya tsallake gidansa yazo gidana ya taki matarsa ai shikenan Daman ya fada min". 'kai! Hajiya you have a lot problem wallahi, doctor muje gaskiya kina da damuwa wallahi".
Yayi gaba ya nufi parlourn farko. "Yo saika Hana na fada ba haka ka fada min ba?". Ita dai Aishat Bata tanka musu ba, tasan sunfi kusa koka shiga kaji kunya bare ita da ba inuwa daya suke Sha ba. Godiya sosai Mahmud ya yiwa doctor zainab din a Nan take fada Masa ya Dan d'agawa zahrar kafa zuwa two to three days haka Dan ma Allah yasa babu ciwo masu yawa. Key din mota ya mikawa Aishat ta Bata tana parking lot sannan yace ta bawa Aishat account number. Godiya take Masa Kamar zata zube masa a Qasa yi take tana karawa Kamar zata Ari baki, itama Aishat din ta tayata yi Masa godiyar, komawa Yayi ciki kawai shi baiga wani abun yiwa irin wannan godiyar ba. A sabuwar motarta doctor zainab ta koma murna kamar me Dan tasan wata Rahama ce ubangiji Yayi Mata, motarta tafi kwanan wata biyu tana fama da ita yanzu haka tana Kan cinikin wata motar jira kawai take a Bata adashenta ta Saida tata ta hada kudin ta tura musu a kawo Mata motar Sai gashi cikin hukuncin Allah da sanyin safiya tayi Gam da katar da motar da Nan kusa Bata tab'a tunanin mallakar mota irinta ba ta millions of naira. Direct bedroom din ya wuce ji yake kamar ya cire mata ciwon daga jikinta, lokaci bayan lokaci Yana sakin smile shi kadai, mamaki yake yi Wai Daman haka lamarin yake ya tsaya Yana cutar da kansa a banza ai da yasan haka ne da gara yayi tun tuni yayi kaffarar rantsuwar a wuce gurin, Bai samu Hajiya a parlourn ba. A ciki ya sameta tana waya a yanda ya fuskanta da Ammi take wayar Dan lafazinta na karshe Daya tsinkaya ji Yayi tana fadin "yauwa turo min da ita Badi'a din tazo da Kayan biqin amaren". "Ilahiy wa Rabbi" ya furta hankali yau ya jawowa kansa barbade Ina maganar privacy a wannan lamari kuma. Gurin zahrar ya karasa Yana Mata wani duban kasa-kasa dan ji Yayi wani Abu na sama yawo duk da Zazzabin dake nukurkusarsa, zama Yayi Yana Kai hannunsa wuyanta. "Are you okay?". Kai ta gyada Mata sexy eyes din ta Nan da Nan sukayi narai-narai da hawaye.baiya wata wata ba ya rungumo kayansa Yana fadin "pls kiyi hakuri Zaki warke na daina kinji my previous". Baiyi aune ba ya jiyo salatin Hajiya Inna a kansa fadi take tana karawa. "Muhammadu Rasulullahi me Zan gani ni Hadiza, Shatu duba min Nan Dan Allah Anya abokin tagwitakar taki ne kuwa?". Ta jefawa Aishat tambaya wadda ta shigo daga raka doctor zainab. "Wannan Kuma ai tsakanin ku ni me zance kiyi hakuri Bata da lafiya ne shi yasa Amma ai badan rashin kunya yayi ba". Kokarin kwace kanta zahrar take itama wallahi Batasan ya akayi ba ta yarda suka manne juna, Amma Yayi musursisi yaki sakinta. "To Inna ya kike son nayi kukan fa zatayi". "To wayace ka jankwalo tsiyar aida saika cigaba da saka Mata Ido tunda abinda ka zaba kenan". Runtse idanunsa Yayi dole ma Yayi hijira daga gidan Nan Ashe martch ya tarowa kansa Bai sani ba. Kiran uncle Mustapha ne ya shigo wayarta Hajiya Innar. "Yauwa ku shigo sabon gurin Nan da aka Gina Dan fariya". Ta yanke Kiran ya juyo tana fadin saika taso idan ka Gama shafe ta kana neman ka lalata yarinya ai Daman tun jiya kake Mata kyarkyara". A parlourn farko suka zauna, Mahmud na gaba Hajiyar na baya tana kananun maganganu. Hannu ya bawa su uncle suka gaisa sannan ya zauna, gaishe da Hajiyar sukayi lokacin tana Zama kusa da Mahmud din. "Likita Dan Allah duba min shi Zazzabi yakeyi duk karfin hali ne kawai yakeyi Amma jikin kamar wuta yake". "To Hajiya za'ayi abinda ya kamata in sha Allah". Zafin jikinsa ya auna tare da 'yan tambayoyi doctor Ankan yayi Masa, Allura ya bashi tare da 'yan magunguna, doctorn ya jima Yana mamkin Mahmud a yanda Allah ya hore Masa dukiya da kananun shekaru ba qaramin mamakinsa Yayi ba, ace yau shine Karon farkon saninsa da mace to Ina isalin labarin Daya dunga yaduwa game dashi?. Lokacin da uncle Mustaphan yazo rako doctor ne uncle saminu shima ya shigo gidan da tasa motar kusan wannan dabi'ar su ce duk safiya suna zuwa suga yanda tsihuwarsu ta kwana. Kusa dasu yayin parking ya fito Yana fadin . "Lafiya doctor na ganka a gidan Nan da sanyin safiya?". Dariya doctor Anka yayi Yana Mika Masa hannu sukayi musabiha sannan sukayi da Uncle Mustapha. "Jarimin kamilin danku nazo na duba" "Wa kenan?". "Mahmud Mana kasan yawanci ko namiji matukar ba mazinaci bane to duk ranar Daya Fara sanin mace sai kaga ya Samu irin su Zazzabi haka da abinda baza'a rasa ba na bakon yanayin da aka samu Kai kai a cikinsa to shima hakance ta kasance wannan shine first time Daya Fara sanin mace a rayuwarsa, gaskiya na sarawa kamewarsa Allah ya taimaki 'yan baya muma ya tsare Mana namu iyalin". "Allahumma Amin ya Rabbi". Tunda doctor ya Fara Kora bayani uncle Mustapha ke yiwa Dan uwansa wani kallo na yau dai an Kama kyafa a tarko Dan shine agent na yad'a Mahmud mazinacine shiya Kama shi da kansa harda shedar hotuna a waya. Uncle Mustapha baiyi kasa a gwiwa ba ya jefawa doctor Anka tqmbaya. "Shin doctor Dan Allah irin wannan Condition din da akan shiga ga sabon shigar Tarawa da iyali shin sau nawa ake iya samun Kai a wannan yanayin?". "Sau daya ne saboda abinda jiki Bai taba jinsa bane daga haka gaskiya ba'a qara shiga irinsa". "Ok thank you very much doctor sai munyi waya". Ya karasa gurin motarsa ya wuce da dunbun mamakin young rich Guy din Nan abinda Bai taba kawowa ko a mafarki bane ace Yana da irin wannan kamewar. Wani duban kaji kunya uncle Mustapha ya yiwa uncle saminu ya wuce ya koma bangaren Muhmud tunda acan ya baro Hajiyar.
Tunda Ammi suka Gama waya da Hajiya inna taji wani irin farin ciki ya rufeta fadi take. "Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!! Allah na gode maka ko yanzu ka wanke min yarona daga zargin Zina ga matarsa ta sunna ma ya dauke Mata Kai tsawon lokaci bare har a jefe shi da kazafin Zina harda cikin shege. Wato wannan 'ya'yan sai a kyalesu wato 'yar uwarsa ya Kira tazo ta kula Masa da matarsa. Wani murmushi tayi tana fitowa zuwa dakin dasu mummy Badi'ar suke, ta labarta mata yanda sukayi da Hajiya Inna, babu b'ata lokaci Mummy bada'ar ta shirya ta dauki duk abunda zatayi Mata amfani dashi suka nufi gidan Hajiya innar tare da Aunty Hasana duk da yau suketa shirin barin garin tunda likitoci sun tabbatar da Bazasu sallami Mama ba sai sun Gama duk abinda ya kamata Dan da gaske ciwon zuciya Yana barazanar kamata shine Mahmud ya Hana a sallameta har Abba ya Kira ya nemi izinin barinta ta warware a nan. Duk hankalin Aunty Hasanar a tashe Dan lokacin da Aishat din ta kirata kafin doctor tace Mata zahrar nata sharbar kuka. Ranar Nan dai kusan yini sukayi da ita Tasha gashin ruwan magunguna gurin mummy Badi'a Dan tsaye tayi a Kan zahra Saida taga yes ta aminta da gurin sannan ta koma,dahuwar Naman rabo Mai kayan maganin bikin amare Ammi tayo Mata da kanta. Zahra ta kirawo Ammah tana Mata kuka shagwaba Wai tace Mahmud ya dawo da ita Azare ita bazata iya Zama a Nan tare dashi ba. Dan murmushi kawai Ammar tayi tasan wasa kenan dama da baisanta ba ya dauko abinsa ya taho da ita to bare yanzu da Mai rabota da wannan garin sai Allah,itama da Dade tana mamakin halin dattako da kawaici irin na yaron. Amma saita lallabata da dadin bakin tayi hakuri zuwa gaba sai Abbanta yayi magana. *AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
09062432330
_Page 87.
_________ Sai kusan magariba sannan Aunty Hasana tayi haramar tafiya lokacin suna parlour a zauna su biyu kadai,dan zahrar taji sauki sosai sai dai tafiyar ce sai a hankali take yinta, Kara matsowa Aunty Hasanar tayi kusa da zahra ta gyara Zama tana Mata kallon Kai tsaye. "Kina jina abinda nakeso dake ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki aje duk wata shiririta ki fuskanci rayuwa,yanzu kin hau wani stage na girma ki kula da mijinki ba Kada ki bada fuskar da wata zata shiga gabanki a gurinsa ki Zama Mai yuriya a gurin biyan bukatarsa kada ki yarda ya gane Baki da juriya tanan zaku iya samun baraka Mai girma, ki tsaya ki nutsu ki fashimci a wane rukuni mijin naki yake sai kisan yanda Zaki bida kayanki, Kinga yaro ne karami yanzu ne yake Kan ganiyarsa sai kin dage da bashi kilawa sosai gaskiya". Ta Jima tana koya Mata dabarun Kama miji a hannu da yanda zata kame iyayensa, idan Auntyn ta Fadi wani abun kunya take kama zahrar sai taga Kamar ba Aunty Hasanar bace. Saida sukayi sallah sannan zahra ta raka Aunty Hasanar bangaren Hajiya Inna ta kofar baya inda suka hade da part dinta. "A'a wa nake gani kamar zahara'u?". Hajiya Inna ta fada bakinta yaki rufuwa da gani tana cikin farin cikin ganinta ta taka da kafafunta ba kamar dazu ba. Murmushi zahra tayi itama tana kawar da Kai, Dan da gaske kunyarta take ji ba kadan ba, tunda ya Gama Mata tonon silili Kuma ita meta Samu na k'ararwa.
Zahra taso ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Inna Amma ba hali dole tayi Mata me spring kawai. Sun gaisa da Aunty Hasana sannan ta fada Mata zata tafi driven Daya kawota yana hanya. "Sannu 'yan biyu kinji, Allah yabar zumunci ai naji shi mijin nata na fadin jirgin safe zakubi ko?".. "Eh haka ne in Sha Allah Dan ma jikin Mama ai da tun a washe gari zamu juya to sai lalura ta gitta dole anan zamu barta tunda yayarta tazo dazu ga Kuma Hameeda itama zata zauna tunda sunyi hutu last week". "Allah ya bada lafiya ya tsare hanya, akwai sakonki naba magajiya ta Kai can sai ki Kara tsaraba". Godiya sosai sukayi Mata suka nufi kofar fita ta gaba. Sun daf da fita hajiya Inna ta Kira sunan zahar tsayawa tayi tare da juyowa ta Fara kokarin dawowa. "A'a kuje ki rakata sai ki dawo ta Nan din". "To". Ta fada suka ida ficewa Saida suka gangare steps din a hankali sannan Zahra ta dubi Aunty Hasana. "Yanzu Ashe gobe zaku tafi Amma Baki fada min ba da saidai na wayi gari naji kun wuce". Ta fad'a tana Shirin zubar da hawaye. "A'a ai kinsan bazan bar garin Nan banzo na ganki ba,to saboda waye nazo garin Banda shirirta irin taki ai kema kinsan hakan baze yuwu ba, shi yasa na wuni a gurinki yau, kuma ai zamu dawo da Ammah taga irin daular da Allah ya kawo diyarta ciki, wlh Zahra Lamarin mijinki yafi karfin tunanina na rasa abinda ya kaishi Azare Mai irin wannan mahaukaciyar dukiyar ace ya jure Zama a shagon kofar gida, dubi wannan part din tunda uwata ta haifeni ban taba ganin gado irinsa ba wallahi, ga can gidan Aljannar duniya,Zahra ki Kara godewa Allah Dan wannan Rahamarsa ce ba tsumin mu ba ba Kuma dabararta mu ba, mu dai mun Kaiwa ubangiji kukan mu akan matsakolinki mun nemi sauki da sauyin Alkhairi a gurinsa, to babu abinda zame sai muce Alhamdulillahi Allah ya Qarawa Annabi daraja lallai dogaro ga Allah jari ne, duk Wanda ya dogara ga Allah ya isar Masa". "Haka ne Aunty Nima fa abinsa Yana bani tsoro kinsan abinda ya bawa sajeeda kuwa ranar da aka kaini iPhone ce da cheque na two millions, ko wacce kuma aka Bata waya da five hundred thousand, Dan Allah Aunty waye shi?". "Ikon Allah Wai mace ke tambayar waye mijinta a gurin wani, mu yanzu ai kece Mai bamu wannan amsar Kuma". Kafin Zahra ta Fadi wani Abu sukaga an bude gate wata hamshaqiyar mota ta shigo, suna Nan tsaye harta karaso kusa dasu Sameer ne ya fito daga seat din driver,sai kuma shi uban tafiyar ya fito daga Daya side din kananun Kaya ne a jikina sai yayi Mata wani fresh dashi, sai dai Kamar ya Dan fada kadan. Gaishe da Aunty Hassanar sukayi kafin mahmud yace wa Zahra. "Ga Sameer Nan shine ze mayar da Aunty gida bana son tukin malam salmanu da dare gaskiya ya fiye gudu sosai, Sam baya duba a cikin gari yake, Aunty Allah ya tsare sai mun shigo in Sha Allah". Oga Sameer din yace "madam an wuni lafiya? Ya bakunta kuma?". "Alhamdulillahi oga Sameer yasu d'ana sukaje gida?". "Lafiya kalau d'azu ta kirani take fada min ta Kira wayarki a rufe". "Eh wlh Zan kirata anjima" Ta fada a takaice Hannuwan Aunty Hasana Zahrar ta kama ta rike tana narke fuska. "Yanzu Aunty tafiya zakiyi ki barni a Nan ni kadai ba kowa kusa dani?". "Ikon Allah to baga zilai ba Ina cewa Ammi ta Kira Ammah ta nemi abar Miki ita, ko Kuna nawa auren Zan baro nazo na tare a gidanki? Banda lalurar Mama ma data gitta ai da mun tsufa a gida, kiyi hakuri na fada Miki kwanan Nan zamu dawo da Ammah fa". Rungume Auntyn tayi ta saki kuka cikin kukan take fadar "Dan Allah ki Kara min ko sati Daya ne bani fa da lafiya".
Mahmud ne ya Dan matso ya rabata da jikin Aunty Hasaanar Yana fadin "kuje kawai Aunty halin zatayi miki'. Dan zumboro Baki da hawaye sharaf a idanunta tayi tana Masa wani duba Wanda saura kadan yayi abun kunya a gaban suruka. Tana ganin Sun yin ribas ta fada jikinsa tana sakin Dan sirirn kukan shagwaba,cak ya dauketa ganin gurin ba kowa yayi gaba da ita, Bai sauketa a ko Ina ba sai a bedroom dinta Kan sofa Yayi musu masauki yana fadin " Guduna kikeyi ko precious?". Girgiza Kai tayi alamar a'a. "To fada min me nayi Miki kike son ki gudu daga garin Nan kibi Auntyn?". "Ba kamoi fa, Ina son Naga Ammah ne". "Kice na tattara na biki, ni Kuma yanzu ai sai yanda kikayi Dani yanda Kika bude min sabon babin rayuwar nan,Wai Daman Dan Allah haka abun Nan yake Kika kyaleni Ina ta bulayi da faman Shan magani? k'afata k'afarki duk inda Zan shiga a duniyar Nan Wallahi bazan iya twenty four hours ban jiki a jikina ba sai a samu matsala, fada min Dan Allah Wai menene sirrin yau though out ni sai a hankali fa gashi doctor tayi Mana tsakani Wai sai anyi two days bamu had'u ba". Ya Kai hannunsa Yana shafa abinda yafi tsone Masa idonu a Hankali. Hannunsa ta rike tana kara narkewa a jikinsa tare da Dan kukan kissa sabanin na rabuwa da Aunty Hasaanar. " Plsss.... meu Amor ka.....Bari da ciwo fa har yanzu zafi suke". "Ya salam! Bari na duba har can din na gani, sorry SHADI I am very sorry nayi laifi ko? Ni kaina lokacin bana gane komai Allah yayi Miki Albarka ya bamu zuri'a masu Albarka, kin Gama min komai a rayuwa kin bani abinda ban tab'a samunsa ba, kin bani farin cikin da mafarkina da hasashena Basu taba hasaso min akwai irinsa a cikin duniyar nan ba, Dan Allah fada min duk abunda kike bukata a cikin duniyar nan matukar akwai sa zan Nemo Miki In Sha Allah". Ya Gama fada Yana kokarin zuge zip din gaban rigar data saka Mai Dan balance wadda bazata ringa takuta Mata ba saboda ba karya taking jiki a kaijin Nan nata. Tana a'a Saida ya duba ya gani Nan da Nan hankalinsa ya tashi. "Previoussss! Haka gurin Nan ya kumbura gara muje muga consultant na bangaren". "Ni fa yanzu babu ciwon sosai Kuma ai kumburin ma babu a Kan dazu, Kuna ai an bani magunguna ma Kuma Ammah ma ta turowa Aunty Hassana wasu Kuma an sawo su d'azu suma na Sha kawai ka Bari basai munje ko'ina ba". Rigar ya gyara Mata duk jikinsa a sanyaye, Yana zargin kansa da nuna Mata karfin da yayi, Amma Kuma Shima abin ne ya wuce tunaninsa ya kasa controlling din kansa. Kiran insha'i da Kiran wayar Hajiya Inna lokaci Daya ya shigo kunnensu zip din rigar ya gyara Mata sannan ya daga Kiran Hajiyar. "Wai Ina zahara'un ne daga Rakiya Kuma sai naji shiru? To tazo maza yanzu nasa anyi mata irin abincin daya kamata taci Kuma taje dakina ta kwana kafin ta samu lafiya Dan Naga ba iya kawar da Kai kukeyi ba 'ya'yan zamani". Wata munafukar dariya ce ta kubce Masa Yana jinjina karfin halin Hajiyar, tab dole ya tattara su Kama gabansu so take tasa' yayi kwanan tsaye kenan ai shifa yaga guri Yana jin ko tafiya zatayi baze iya barinta tayi kwanaki ba Dan saiya zauce gaskiya. "Wai bakaji abinda na fada bane kayi kunnen uwar shegu dani". "Naji Mana ai bama gidan ne, mun wuce tun dazu mun koma sai dai idan daukoki zansa ayi ku kwana tare a Nan din". Ya fada Yana Dan Jan cheeks dinta yana kashe Mata ido daya tare da dage Mata gira Daya. "A'a Allah ya tsari gatari da Saran shuka ai shikenan Daman gata ne Zanyi muku tunda kun gano ba haka ba ki cinye junan ku ai jiki magayi ba'a kwacewa yaro garma ga gurin Nan Bari ba shegiya bace da ubanta, gashi Nan za'a kawo Mata abinda nasa akayi Mata idan kaga dama ka Bari tayi amfani dashi taci kuma abincin idan kuma ka Hana duk Daya Wai makafi sunyi dare,duk Wanda Rai ze yiwa dad'i ai ba Kamar me Shiba".kit ta kashe Kiran. "Subhanallahi! Allah ya kawo mu kiji min tsohuwa da Hana ruwa gudu, Bari naje masallaci na dawo mu wuce bazan iya da rigimarta ba gara mu Kara gaba kafin ta Kira Abbie yace nayi wani abun".
******* Cikin galabaita Salma ta dubi wadda ke tare da ita a asibiti. "Dan Allah kirowo min nurse din Nan tazo ta dubuta min maganin ciwon baya da mara wallahi ciwo suoe Kamar zasu fita". Tsaki tayi matar Mai suna Saude, tana gadin "ba dole kiji jiki ba Ina cewa da hankalinki da komai Kika biyewa wannan gantaellen yaron Nan kuka dunga badala shi namiji ai ba abin kunya gare shi ba tunda bashi da tabo mace kuwa? Ina Jin baya garin ma ya wuce warri inda yake aikin kamfani ya barki da wahal ga kin rasa martabarta ta har abada,'. Tunda matar tafara mata magana Salma ke kuka tayi Dana sani yafi cikin kwando. Ga mahaifinta da wane Ido zata kalleshi Ranar da yaji wannan.abun data aikata, ga Mama ciwo Yana can Yana ta nukurkusarta a garin mutane,sai kawai ta fashe da kuka Mai Jinyar tata Dan haushi kasa bata hakuri tayi ta wuce Abinta ta nufi Kiran nurse din tana fadin "ba dai bin maza Kika zaba ba bakiga komai ba wallahi yarinya babu abunda Kika nema Kika rasa Amma kin biyewa wani sakarai Wanda Bai San inda yake Masa ciwo ba. *_ AUREN HUCE HAUSHI_*
AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah.
09061432330 08055362975
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINQAI SALATI DA DAUKAKA DA AMINCI SU QARA TABBATA GA SHUGABAN MU FIYAYYAN HALITTA ANNABIN RAHAMA MUHAMMAD S.W.W.W DA ALAYANSA DASAHABBANSA WANDA SUKA BISHI DA SALIHAN BAYI HAR ZUWA RANAR TASHIN ALQIYAMA AMIN.
Muna rokon ubangiji s.w.a ya Dora mu Kan dai dai abinda mukayi na kuskure ubangiji ka yafe Mana Dan isar Manzon Allah s.a.w.w Domi shine Mai gafara Mai jinqai.
Page. 88