Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 19

Auren katin kasa complete - Chapter 19

Auren katin kasa complete Chapter 19: Auren katin kasa complete Chapter 19. Bin bayanta yayi da kallo harya wuce dakinshi shima, yana shiga kuwa ya soma…

4,254 words

Bin bayanta yayi da kallo harya wuce dakinshi shima, yana shiga kuwa ya soma tube komai nashi ya wuce bathroom lokacin around 6:40 saida ya dauka kusan awa yana wanke wanken shi kafin ya futo da towel a kugunshi, a tsaye ya hangota bakin kofa hannunta rike da pink leda da bai san ta menene ba tana kallon gefe daman ta shugo ne yafi sau uku don tabbatar da baya cikin toilet din don a matse take sosai, wucewa yayi gaban dresser ya soma yan feshe feshen sa ba tare da ya kalli inda tak ba ita kuwa batayi gangancin kallon saide dinshi ba don bata buqatan ganin surar jikin shi a haka babu kaya, sadaf sadaf kamar munafuka ta wuce cikin toilet din tare da danna lock ta soma tube kayanta, saida tayi wanka ta samu relief, chanza pad tayi sannan ya maida kayan ta ta gyara mashi toilet din ta futo, lokacin data futo yana kan sallaya ya idar yana azkr, giftawa tayi ta gefenshi ta fuce zuwa parlor kayan jikinta ta sauya zuwa doguwar riga yar morocco ta shan iska ta wuce kitchen, store ta ciga ta deba basmati rice data sayo kwanayi tayi blending dinshi ya koma kamr shinkafar dambu ta dora ruwa kadan akan cooker plate ta saka stemer, gefe guda ta kwaso veggies dinda sukayi mata saura ta yanka green paper bell paper, carrots, green beans da beef, tana gama yanyankawa ta wanke su tass ta soma hada shredded beef sauce, cikin kankanin lokaci ta bade gidan da kamshin abincinta dambun shinkafa da shredded beef sauce, yau gaba daya yanayin girkin da take ne a gida ya zo mata, tana gamawa ta zubwa a plate ta zauna kan island ta koma gaban freezer ta dauko ruwa kawai, ta zauna. Oga kuwa tun akan sallaya ya soma jin familiar kamshin, wanda sai a gida chan Nigeria yake jin irin kamshi, futowa yayi da jallabiyanshi ya karaso har kitchen din yak are mata kallo ba tare da yace komi ba, itama bat ace mashi tak ba saima tsayawa da tayi da cin abincin nata ta kauda idanunta gefe, bata ankare ba ta ganshi gefenta ya kwabe hannayenta daga kan spoon din, juyawa tayi da kallon mamaki ta kalleshi, harara ya watsa mata tare da hade rai ya dauka spoon din ya diba abincin ya kai bakinshi tare da lumshe idanuwansa, saida yayi spoon biyar kafin ya aje ya balle marfin ruwan nata ya shanye tass ya juyo ya kalleta rai a hade yace ''kin cika seasoning a ciki, next time ki dunga lura sosai'' Yana kaiwa nan ya wuce daki abunshi, da idanu ta bishi galala, mamaki karara a fuskanta, me Kenan haka din lallai ma y agama cinye mata kusan rabin abinci sannan kuma ya tsaya yace mata wai seasoning yayi yawa, dariya abin ya bata at the same time da haushi, tsaki kawai tayi ta dauka spoon din ta soma cinye saura, komai is perfectly fine, lallai ma raina mata hankali yayi kawai, dariya ce kwai ta kufce mat aba tare da sanin dalilin hakan ba. Shiko oga tunda ya shiga daki harda yar gatsar shi yana mamakin yanda akayi ta iya girki sosai, duk yanda akayi kila taje cooking school ne maybe don taste din abincin kamar na amah shi don kamshin ne ma yayi dragging dinshi zuwa sitting room din, sallan isha I yayi kafin ya kwanta abinshi kawai bayan yasha magani, yauma yasha wahaala sosai cikin dare don saukin da yake samu bai sameshi yau ba, safiya nayi kuwa ya shirya da wurwuri ya wuce aisibiti don daga nan aiki zai wuce, yana zuwa wajen doctor kuwa ya mashi bayanin abinda ke damunshi da relief din da yake samu a cikin kwanakin saidai jiya yasha wahala sosai, cikin kwarewa ya soma mashi bayani yanda zai fuskanta ''mr amar, like I side duk wannan abubuwan da kake experiencing side effect ne, saidai kuma idan na fahimci bayaninka da kyau ka samu mace ne a kusa dakai shiyasa kake samun sauqin so I will advice kazoo ayi un freezing the earliar the better, you need to release the remaing water you have, koba komai zaka rage duk wani sha'awa da kake dauke da ita for all this years tunda baka taba having sex ba, sannan I will advice ka daina chan maganin dana baka don naga shike saka ka futa hayyacinka gaba daya''

Shuru amar yayi yana dan nazari, so all this while duk tunaninshi mafarki yayi akanta ashe da gaske ne, hes actually having so much relief idan ya rabeta, nooo I cant do thattt'' ya fada ma kanshi Godiya kawai yayi ma doc sukayi sallama ya wuce office yana zuwa kuwa ya soma bude desktop dinshi ya shiga date din da ya soma zazzabin daren, abun mamaki tun daga ranar daya soma jin relief din kuwa ya ganta a dakinshi dukda ba wani haske sosai saidai last day dinnan da yayi grabing dinta ya bashi mamaki, da irin yanayin da suka shiga da ganinta da yayi a yanxu cikin natsuwarshi da hankalinshi, da sauri ya runtse idanuwanshi, haka ya shagalce da rewinding parts dinnan ba tare da yasan yana yiba, haka kawai yake jin dadin ganin scene din karhse dai ya hane kanshi da kallon nata a cewar maysa zai dunga kallon qanqanuwar yarinya kamar wannan ay ba girmanshi bane yafi karfin haka saidai wata zuciyar nace mashi you like what you see ne, tsaki yayi ya kashe gaba daya ma. Bangaren amra kuwa tunda ta koma office yau take fama da ciwon kai sosai, gashi aranar aka kawo ma head of health report din cewa ana buqatar mutun biyar a cikin staff da interns da za a tafi dasu training on Monday mai zuwa wanda a ciki kuwa harda ita aka saka, dukda she's excited to join saidai kuma bataji dadi ba ganin babu haifa sai mrs hafiza wanda rabonta da ita tun lokacin da take zuwa kafin ta daina kuma gaba daya.

Gaba daya satin nan yayi shi cikin wahala sosai don ya jigata ba kadan ba duk dare kam baya samun rufe idanunshi kwata kwata daman maganin yana dan helping dinshi gashi doc yace a daina sha karya jawo mashi wani matsalan daban kuma, yau Friday dakyar ya tashi daga baccin wahala da yayi don saida asuba ya samu damar runtsawa karfe 11 daidai ya tashi ya watsa hot shower ya futo ya shirya cikin shirinsa ya wuce office yau m5 bai tuqa shi ba da kanshi yakai kanshi har office yana parking ya wuce sama m5 biye dashi a baya, suna shiga cikin office din hammam na kunno kai, mamakin ganinshi amar yayi don sun dauka wajen wata basuga juna ba kuma bai nemeshi ba kamar yanda ya saba shima bai neme shi ba don yasan dukkansu suna busy koda yaushe,gaisawa sukayi kafin amar kalli m5 yace ''whats on today schedule'' Gyaran murya m5 yayi don ba komai yakeson yana fada ma oganshi ba agaban mutane koda kuwa hammam dinne a wajen, cikin sauri yace ''sir yau karshen wata, akwai blood sample da za a dauka yau'' ''okay send them in 20mins'' ''Yes sir'' hammam ya fada tare da bude kofan office din ya fuce don kiran medicals, lokacin daya kira head medical bata office saidai staff, suma akwai wanda suka tafi operation ganin babu wasu manya sosai ya sashi yanke hukuncin kiran madam din oga kawai don itace babba a interns Lokacin da kiran yazo mata bata shirya zuwa cikin headquater ba, badan son rant aba ta shirya baubuwan da zata buqata ta wuce, lokacin data karasa gaban office din nashi kamar koda yaushe saida ya dauka minutes da yawa kafin ya bada izinin shugowa lokacin har hammam ya tafi abunshi, Karasawa tayi gaban office dinshi tace ''good day sir'' Bai dagoba saidai kuma zazakar muryarta tayi mashi sallama baiyi tsammanin ganinta anan ba yace ''have a seat'' Zama tayi anan kujeran baki ta maida kanta gefe ba tare da tace uppan bay a dauka kusan awa yana danne dannen shi akan laptop din gabanshi kafin ya dago ya kalleta yanda ta maqure gefe guda, miqewa yayi ya dawo kujeran opposite dinta suna fuskantar juna ya zauna, ganin haka yasa miqewa ta tattaro abubuwan da zata buqata ta tako har gabanshi, kallonta yayi daga sama har kasa kayan yau sunfi decent sosai akan jiya don basu kamata kwata lkwata ba saidai kana iya hango surar jikinta, shuru kawai yayi don yanxu ya karanci ba daga kayan bane daga ita kanta ne surar jikinta ce a haka da duk kayanda ta saka dole saisun bayyana, kwanciya yayi da bayanshi akan kujera ya miqa hannayenshi, matsowa yayi soai dab dashi ta rasa yanda zatace mashi ya dan janye hannun rigarshi shiko tsaf ya gane me take nufi amma yayi bansa za ita, aje syringe din tayi ta masto sosai kusa dashi har yana jiyo kamshi jikinta da dumin nunfashnta, a zafafae ba tare da tunanin komai bay a fuzgota kan lap dinshi, da sauri ta waro idanunta sosai akanshi zatayi magan ya sanya yatsanshi kan bakinta yace '''just do your job am checking something'' Takurewa tayi ta rasa abinyi har saida ya mika mata syring din ta karba tare da diban jini nashi, kiciniyar tashi ta soma yi saidai ya lumshe idanun nashi kamar wanda keyi bacci duk motsinta kuwa yana sane da hakan da yanda take juyi akan laps dinshi da is driving him craxyy, ''ki natsu'' Kamar an dauke wuta kuwa tayi tsit bata kuma motsawa baa nan kan laps dinshiya dauka kusan rabin awa yana jin dadin yanayi ba tareda yayi mata komai bad an zaman da tayi kawai akan laps dinshi shuru tayi itama don at this point kuma ganin abubuwan nashi sun fara yawa don ya soma wuce gona da iri, ga tsoron mashi magan take bare ta nuna mashi ita bata son haka don kar yayi tunanin aurenshi dake kanta aure ne da zai kaisu ga irin wadannan abubuwan yarjejeniyace kawai tsakaninsu ba wani abu ba, tunawa da yarjejeniya yasa ta yin jimmm kadan, babu zato ba tsammani aka bude kofan office din wanda hammam ne da wani officer suka shugo a tare wanda ya buyo shi don neman leave din hutun kwana biyu sbd mamanshi da aka kwantar a asibitin, Daburcewa tayi tana shirin sauka amma ya hana haka don hannunshi ya sanya ya saqalo a kugunta tammm don babu amfani guduwa sannan as far as he knows ba wani abu suke ba koda suna yi ma ay matarshi ce ta sunna saidai abinda bai tuna ba shine babu wanda yasan da auren nasu anan headquater saidai cecekuce da ake yi ta bayan fage wanda shi duk wannan ba damunshi yake ba don baya tsoron kowa da komai harma da abinda zai faru wannan ba matsalarshi bace, hawaye ne suka soma zubo mata tayi saurin kauda idanuwanta gefe ta dan saitin daidai kunenshi ta soma Magana ahankali wanda hakan ya haifa mashi da wani sanyin jiki ''dan allah ka sakeni, na tafi, kar mutane su zargi wani abu,'' yanda ya hade rai ya zuba ma su hammam idanu da yake kallonshi da fuskanshi ta sauya ganinsu haka sai shima wanda ya biyo bayan hammam din shi da ya kauda fuskanshi gefe yace dasu ''will you please excuse us, as you can see im very busy right now and the next time anyone of you get into my office without knowcking will answer me okay'' Yana gama fada ya kuma janyota jikinshi da kyau ya sanya fuskanshi tsakanin wuyanta yana shaker kamshinta tare da sauke mata nunfashinsa mai kashe jiki, hammam kuwa sandarewa yayi a wajen don yayi mugun mamakin ganin wannan alamari, whats going on her fucewa yayi shima dayan gayen yabi bayanshi, azafafe ya tafi office dinshi ya daki table sai a lokacin ya soma jin zafin maganar da amar ya fada mashi da abunda ya gani lalai yayi sake gashi ya rasa ya zaiyi shine ya hada wannan abun gashi zai zamo mashi babban bazarazana amaimakon nasara, ya fara son yarinyar nan Kenan ya tambayi kanshi, shidai a iya sanin da yayi ma kanshi yasan amar bazai taba kusantar yarinyar ba don tabbas shine yasan amar ciki da bai yana da wata irin izza da girman kai, sannan baya son raini, and kananun yara basa gabanshi saidai ita kuma wannan din ta fita daban don shi kanshi sometimes yana kasa resisting dinta dukda kawar haifa ce kut da kut…. Ikon allah ni harna manta da haifa ma bari muji nata bangaren. Tun bayan an salami abu bayan kwana biyu rashin lpy shi ya dawo sabo wanda likitoci at this point sun kasa gane menene matsalanshi saidai sun gano kamar anyi poisoining dinshi da wata kwayar da an kasa gano ta,ganin haka yasa aka shirya kaishi india do abun ya shafi kanshi, bayan tafiyar su india sun kwashi watan ni kusan biyu acan wanda hakan yasa haifa bata koma aiki ba don da ita aka tafi chan india din,an samu aikin ya zama successful, amma ba a sallamesu ba sbd ana son ayi monitoring abuh sosai, cikin watannan kuwa wata ranar asabar tana zaune a apartment din da suka kama anan hydrabad ta soma trying number hammam, kamar koda yauseh saida ta mashi call kusan guda goma cikin sa a ya dauko, tsabar dadi harda kukanta, tunda ta soma magan baice mata uffan ba har saida ta gama kafin yace ''please haifa ive already end our relationship, bana buqatarki a rayuwata, and please stop calling me, im done'' Wani irin kuka ne ya kufce mata ''why hammam whay what have done wrong'' ''you've done nothing'' Meysa zaka yaudare ni maysa zaka min haka'' Haifa karmu bata ma juna lokacin, nace I don't need you anymore im done'' ''Okay naji but ka fada min dalilinka'' ''idan babanki ya tashi ki tambayeshi'' Diff ya kashe wayan, kuka ne ya kufce mata nab akin ciki da dana sanin wannan muguwar sosai, mekenan yake nufi data tambayi abuhh.. Cikin kwanakin nan haka ta koma kamar wata majinyaciya sbd damuwa gashi bata samun number amra balle ta fada mata damuwanta.

Hammams…. Aikin da baiyi ba Kenan a ranar ya futo direct ya wuce motar shi, ya fuce daga headquarters, gida ya wuce drect kawai anan ya tadda hafiza zaune akan kujera don yanxu gidansu ya zama kamar gidan ubanta, yana karasowa gabanta yace ''youre useless, bakida amfani, kina nan nace ki koma office kince kina tsoron wanchan mutumin, yanxu gashi chan plans dinmu na rugujewa, I saw them with my own eyes, I saw the intimacy''

Hankali hafiza ya mugun tashi, nan take ya mike kamar tayi hauka ''nooo noo never, nayi alqawarin indai bani na sameshi ba babu mai samunshi, sannan nayi alkwarin bazai taba samun farin ciki ba so just watch and see.. Ba bata lokaci ta danna kira tare da bada umarni akan a tura duk wani evident data tanada Kallonta hammam yayi yace what are you trying to do ''just watch and see'' Shuru yayi yana kallonta sosai anya wannan tana da hankali kuwa, she doesn't plan kawai tana abu kamar mara hankali Tsaki kawai yayi ya fuce daga gidan ma baki daya. Hafiza kuwa sawa tayi daya daga cikin masu zama a cikin apartment din da amar yake aka tura anonymous complain zuwa ga marriage counsel group cewa akwai couples din da ke zaune a apartment din da sunan aure saidai kuma auren illegal ne, harda evidents suka tura aciki kuwa harda wanda aka saka akwai physical violence a ciki.

Wani irin dadi take ji ganin komi is falling into places, yanxu ko su hammam bazata jira ba zatayi duk abunda taga yafi mata don suma kamar tsoronshi sukeji basa kokarin yin komi. 104-105 Update….

Yau Monday kamar koda yaushe tun karfe bakwai ya gama shirinsa tsaf cikin kaki yayi matuqa amsar jikinsa sosai, saida ya feshe jikinsa da nora mens black perfume, yayi matukar kyau sosai, duban gefen wajen couch yayi ganin tana baccinta hankali kwance idanunsta a lumshe zara zaran eye lashes dinta sun kwanta lub fuskanta tayi fayau so cute hijab dinta ne maqale a wuyanta kamar kullum har mamaki yake ko gajiya batayi da sakawa saidai tunawa da shi ya haneta da zama babu hijab din ya sahi yin kwafa ya kauda kanshi gefe, mamakin yanda hes into her yake dukda yaqi believing hakan yanxu ta daina kwanan sitting room don tun bayan lokacin da investigators dinnan suka zo ta daina kwana achan shima bai hanata kwanan dakin ba saidai baiyi yunkurin yi mata tayin kwanciya akan gadon shi ba don bashida plans akan wannan, zazzabinshi kam yanxu yana dan sauqi sosai ba kamar da ba dukda doc yayi warning dinshi kan idan ya bari har zazzabin ya rinjayi kwayoyin lafiyar jikinshi zaizo ya daina saidai hakan yana da risk sosai don side rffect din unfreezing din da akayi mashi ne Tunda ya mata kalo daya bai sake kallonta ba, har y agama duk abinda zaiyi kafin ya janyo wayanshi ya tako har inda take, ganin wayanta a gefenta ya sahi sanya hannu ya dauka ya fuce daga dakin, fucewa yayi cikin natsuwa har gaban inda m5 yayi parking, shigewa ciki yayi bayan m5 ya mashi gaisuwa irin tasu na sojoji, aje wayoyin yayi a gefensh kafin m5 yaja motar suka wuce, relaxing kanshi yayi a jikin kujeran motar ya rufe idanunshi kamar maijin bacci abubuwa da dama suna yawo a kanshi, abunda yafi bashi mamaki shine ya duk sanda yake zaune shi kadai sai yarinyar nan ta fado mashi arai saidai yana danganta hakan da tausayinta da yakeji da kanneta da yanxu sun saba dashi sosai don duk a tunaninsu shine abokin ya muhammd daya zama gatansu a yanxu, shima sarai ya gane cewa suna mashi kallon abokin yayansu saidai basusan cewa shine ma ya daukesu harya kawosu gidansu don yayi protecting dinsu, duk zamannnan da sabon da yayi da yaran bait aba hadata dasu ba kuma baiyi tunanin hakan ba sbd nashi kudirin, saidai yayi alqawarin watara zaiyyi reuniting dinsu lokacin daya dace.

Gaban headquarters m5 yayi parking motar oga general kafin ya bude mashi, ahankali ya sanyo kafafunshi waje ya fito cikin kamewa da isa, gaa daya y agama bade compound din da kamshinsa mai dadin gaske, takowa ya soma yi harya wuce first security entrance anata sara mashi gwanin burgewa, daga masu hannu ya dungayi kafin ya wuce kowa na yabawa da kwarjini da isa irin nashi, yana shiga reception ya wuce lift zuwa last floor na bulding din m5 biye lift din na budewa ya tako gaban wajen helicopter din da ke jere kusan guda biyar a fadin wajen, kallon freshers din yayi basuda wani yawa daman basufi su ashirin ba, sai yan medicals suma su biyar, kallonsu yayi cikin saurin m5 ya rada mashi cewa mss amra bata zo ba, girgiza kai kawai ya basu go ahead kan cewa su wuce daman yana sane da ita don dalilin dauke wayanta da yayi Kenan don yasan saida wayanta zatayi komai ciki kuwa harda requesting ride harda payment,nan take kowa ya kame aka sara mashi ganin general gaba daya, kallonsu yayi kafin ya bada umarni kowa ya shiga cikin helicopter din, guda daya ne basu shiga ba wanda ta fita daban daga sauran guda hudu, shima shigewa yayi kafin m5 ya sara mashi don bandashi za ayi tafiyan ba daman ya barshi ne ya lura da wasu abubuwan da sukeyi cikin sirri, kafin ya wuce ya kalli m5 yace ''get her a new phone and a sim I will send her passport information,'' Kamewa m5 yayi yace ''yes sir'' kafin suma nasu helicopter din ya tashi sama. Suna wucewa m5 ya soma buga calls ''the plan is going smothly'' Fucewa yayi daga cikin headquarters ya sayo sabuwar bugaggiyar iphone 14 pro max deep purple tare da sim card ya saka mata a ciki, yana gamawa yayi setting wayan ya tura ma ogan shi number ta kafin ya wuce apartment domin ya kai mata, koda ya karasa yayi knocking kamar jira take tayi saurin budewa idanunta yayi tsurtsuru don tsoron abunda zai biyo baya takeyi na qin zuwa private training da aka saka ta aciki, tana ganin m5 yayi saurin gaysheta sanin matsayinta a wajen oga kafin ya miqa mata sabuwan wayan yace ''oga yace a kawo, sannan yace zan dunga zuwa kaiki aiki from tomorrow'' Shuru ta danyi kafin ta kalli ledan da yake bata, godiya ta mashi kafin ta rufe kofar ta koma ciki, zama tayi a sitting room din tana mamaki me Kenan, saurin budewa ledan tayi ganin kwalin iphone 14 promax irin tashi saidai nashi black color ne ya sata gwalo idanunta sosai sai alokacin ta gane komai, ashe shine ya dauke yar iphone x mas dinta da take riritawa, juya wayan ta soma yi, take wani irin farin ciki ya lullubeta sosai kafin ta kunna ganin an mata setting komai yasata shiga cikin wayan tana dube dube, ganin bbu contacts dinta ya sa hankalinta tashi, number daya ne a ciki shima na kasar ne kuma tasan ba number haifa bane, aje wayan tayi a gefe ta raftaka uban tagumi tama rasa wani tunani zatayi.

Chan bangare amar kuwa suna isa suka far training babu zama, sun dauka kusan kwana biyu suna tsattauran training, mamaki yake sosai yanda suk sanda za ayi training shida hammam sukeyi saidai this time araound babu hammam babu labarinshi karshe ma dai samun leave report dinshi yay akan cewa zaije india tare da babanshi health check up, share alamarin shi yayi ya maida hankalinshi kan abunda yazo yi. Kwana biyun da sukayi sun samu wahalan network don gaba daya babu network a inda suke sai a kwana na uku ne suka samu network ya dawo, sai a lokacin ne ya samu damar yin wasu ayyukan ciki kuwa harda sakon m5 wanda ya shaida mashi komai yana tafiya daidai saidai sakon karshen ne ya bashi mamaki sosai ya sanya shi cikin zulummi, nan take ya samu kebatccen waje yazaune tare da bude laptop dinshi ya soma research, hoton susupect dinsu ne ya bazu a labaran naigeria da duniya gaba daya akan cewa babban drug dealer from nigeria, mamaki ne karara a fuskanshi da tsoron abunda zai biyo baya tunda gashi yanxu dai komai ya soma bayyana saidai duk sanda siriin empire dinan ya soma tonuwa idan ana gab da kamasu komai ke rugujewa saidai yayi alqawari wannan karon komai zai faru saiya ganosu nan take ya umarci m5 daya tura mashi gaba daya backround check da mutumin, shuru yayi ya soma karanta background din yaron ciki kuwa abubuwa dadama sun bashi mamaki nan take tunani da yawa ya fara wanzuwa akanshi background check dinma dakyar m5 ya samu don koina akayi bincike akanshi ba a samun komai, a rude ya bude wayanshi ya shiga emails dinda private investigator dinshi ya tura mashi ganin address da profile din yaron iri daya ya sashi dogon nazari, tunawa da wani abu ya sashi bude report file din suspect din nan komai ya futo daga kan time din da aka kamashi da hospital report dinshi da kalar kwayar da yake safarar ta da aka samu a cikinshi, nan take ya soma comparinsing sai kawai ya kece dariya kawai chan kuma ya tsuke fuska yana mamaki sosai, menene alakar yarannan da kwayarnan, idan bai tuna ba lokacin da kannenta ke asibiti daya daga cikinsu an gano kwayar taso ta mashi lla saidai abunda ya kasa ganewa shine ashe dama chan kwayar daga Nigeria ake yenta ne kokuwa suma zuwa tayi nan kasar ganin ya rasa amsoshinsa yasa ya dukufa da nashi binciken, bayason wani tunani daban don haka ya soma bin komai a sannu a hankali.

Bangaren amra tun bayan ya tafi ta samu sakewa sosai a gidan, kullum kuwa m5 ke zuwa ya kaita headquarters sannan lokacin tashi ma da kanshi yake daukanta cikin daya daga cikin motocin general dake penthouse dinshi, sannu a hankali zancen aurenta da general ya soma fitowa, dalilin kawota da m5 keyi a motar oga kwata kwata wato general saidai sanin girman general din yasa babu wanda ya tunkareta da maganar saidai gossip dake yaduwa kamar ruwa.

Cikin kwanakin haifa ta dawo aiki, ba karamin dadi amra taji ba saboda tayi kewanta sosai, saidai ganin yanda haifa ta chanza sosai ta rame yasa hankalinta ya tashi, saida sukayi round medical check kafin suka wuce office din haifa, zama sukayi cikin hira amra ta jefo mata tambayan dalilin chanzawanta, nan take ta mata bayanin abubuwan da suka faru tsakaninta da hammam, ba karamin tausayinta amra taji ba don ita kadai tasan yanda kawarta ke sanshi saidai abunda yafi bata mamaki shine dalilin daya rabu da ita, shawarwari amra ta bata tare da tausasa ta harta warware tayi alkawarin mantawa dashi har abada. Hira suka sha sosai inda amra ke tambayanta jikin abuh wanda ya ji sauqi sosai, karfe hudu daidai suka fito, kamar koda yaushe suna fitowa m5 yayi parking motar shi gaban entrance na shiga asibiti, nan take mutane dake wucewa tsakanin headquarters da asibiti kowa yay a zuba masu idanu,kallon amra haifa tayi don tayi mamaki sosai, murmushi haifa tayi kafin tace ''mrs general, har anyi nisa ne ban sani ba'' Kauda kai amra tayi takai zata dan bugeta tace ''hmm so much has happen, shiyasa nayi ta kewarki sosai,'' Bude jakanta tayi ta dauko wayar daya bata ta kalli haifa tace ''I lost my other phone, bani contact dinki'' Kallon wayar haifa tayi batace komi ba ta saka mata contact dinta kafin suyi sallama ta wuce cikin motar m5 ya zagaya ya bude mata ta shige.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull