Auren katin kasa complete - Chapter 21
Auren katin kasa complete Chapter 21: Auren katin kasa complete Chapter 21. ''kina buqatan wani abu ne ko zaki fara hutawa?'' ''please ko zaki nunamin…
4,436 words
''kina buqatan wani abu ne ko zaki fara hutawa?'' ''please ko zaki nunamin bathroom'' ''okay ma'' Mikewa amra tayi ta fara bin matar har suka bi hanyar da zai sadaka da stairs, staircase dinma kanshi abun kallo ne, har wani curvy yayi gashi yasha carpet mai kyau, gidan is so cozy, bin bayar matar tayi har suka hau benen farko wanda keda dakuna biyu manya manya da parlor hanyar parlor sukabi kafin matar ta bude dakin dake facing parlor, tunda suka shiga ta soma raba idanuwa, dakin yasha kayan alatu, gado ne royal Turkish bed mai kyau yasha gyara da zanin gado wanda daga gani kasan na masu kudi ne, an jere dakin da pillows masu kyau, sai tsakiyan an kawata shi da carpet mai laushi gefe guda kuma wardrop din gadonne shima babba wanda ya shanye gabada wall din wajen, matsawa gefe matar tayi kafin tace ''ga toilet nan ma'' ta fada tare da nuna mata wata kofa daga gefe chan, shigewa amra tayi ciki kafin matar ta rufo mata kofar ta fuce, takowa amra tayi ta aje jakanta da wayanta akan gadon kafin ta soma nannade mayafin abayan dake jikinta don ji take kamar shaketa yake, hanyar bathroom din da matar ta nuna mata tabi, koda ta shiga nanma toilet din ya gaji da haduwa, saida ta fara rage mararta kafin ta dauro alwala ta fito don sai a lokacin ta tuna da sallolin da ake binta, futowa tayi lokacin matar ta bude kofar itama ta shugo hannunta duke da box din data aje mata a parlor, kauda kai gefe amra tayi kafin tace ''thank you, please ina buqatan sallaya'' Da sauri matar tace ''okay ma'' Takowa tayi ta bude slide wardrop din ta fiddo da sallaya katuwa ta ta shimfida mata, godiya amra tayi mata kafin ta fuce, mayafin abayrta ta dauka ta nade wuyanta dashi kafin ta tada sallah, koda ta idar ta dade sosai kan sallaya tana addua akan lamuranta, ciki kuwa harda general da bata san a wani hali yake ciki ba saidai tana jin zafi don duk wani hali yake ciki a yanxu itace ta jefashi, wannan kadai idan ta tuna yake sata kuka sosai, ta dade akan sallaya kafin ta miqe ta raqube a gefe guda ta zauna ta doka uban tagumi. Tana nan ta janyo wayarta, tama rasa me zatayi sai hawaye, tana nan zaune akayi knocking kofar, dagowa tayi ta bada izini aka shigo, matar dazun ce sanye da uniform din aiki, ktakowa tayi kafin tadan rissina tace ''me food is ready, ko akawo maki nan'' Shuru amra tayi don yanda matar dai a grime ta girmeta amma sai rissina mata take yasa taji babu dadi tace ''nagode zan sauko naci'' Juyawa matar tayi ta rufe mata kofa kafar. Koda ta kasa kanta ne ya rabu gida biyu don bata gane inane hanyar dining dinba, saida matar ta fito ta jagorance ta har dining din shima dai ba a Magana, zama tayi idanunta kan jerin warmers din, da sauri matar ta soma bude warmer din tace ''wanne za ah saka ma'' Shuru amra tayi kafin ta dan dago fuskanta dauke da murmushi tace ''zaki iya saka ko wane ma'' Murmushi itama matar tayi kafin ta zuba mata fried rice da tasha veggies da hanta sai shredded beef sauce a gefe, tana gama zuba mata ta aje mata spoon a gefe kafin ta janyo wani bowl din ta zuba mata green salad, tana gamawa ta janyo hadadden glass jug din da yasha apple juice ta zuba mata ta aje a gefe, kallon plate din amra tayi, abuncin yayi kyau a ido ga kamshin sa daya bade dining area din gaba daya saidai gaba daya damuwan dake cikin ranta yasa batada appetite gaba daya, dagowa tayi fuskanta dauke da murmushi tace ''thank you so much'' Murmushi matar tayi matai tama don haka kawai taji amra ta shiga ranta sbd calmness dint aba kamar wasu madams din ba da kudi ke sasu jin kansu har suna wulaqanta wanda suke masu aiki, ''if you need anything ma, zaki iya kirana, sunana nadine'' Girgiza mata kai amra tayi kafin matar ta juya zuwa kitchen ita kuma ta maida chokalin cikin plate ta soma deba ahankali tana kaiwa bakinta,abuncin yayi dadi sosai saidai gaba daya tunda tayi loma daya biyu taji ta koshi, juice din kawai ta samu tasha don kishirwan da takeji sosai, tana gamawa ta dauki plate din tayi hanyar da matar tabi, tundaga bakin kofar shugowa kitchen din matar ta hangota, da sauri ta sakko daga kan kujeran da take zaune ta karaso gaban amra tace ''ma dakin barshi zan kwashe'' ''haba ba komai ay, nagode sosai'' Karba matar tayi kafin tace ''ma kije ki hut azan kula da wannan, its my job'' Godiya amra ta sake mata kafin ta juya, sama ta wuce saida ta karema parlor kallo sosai, kafin ta wuce direct dakin nan, gefen gadon ta samu ta zauna ta doka uban tagumi, hawaye ne ya soma sulalewa a fuskanta, gaba daya hankalinta a tashe yake, tana nan zaune har barci ya kwashe ta akan gadon. Bata farka ba sai wajen laasar, toilet din ta wuce tayi wanka kafn ta fito ta bude box dinta, wasu kayan ta chanza kafin ta shimfida sallaya ta soma sallah, anan zaune tana azkar aka turo kofan, karasowa Nadine tayi gabanta kafin tace ''ga sako driver ya kawo'' Karban ledar amra tayi kafin ta mata godiya ta fita, mikewa tayi ta koma gefen gadon ta bude ledar, katin sim ne na mtn, da sauri ta bude ta janyo wayarta ta cire nata na saka sabon na mtn din dama tana tunanin yanda za ayi ta samu sim card don ta manta nata achan apartment dinta, tana kunnawa kuwa taga an loda kati da yawa a ciki na kusan 20k, rasa abinyi tayi, cikin call log dinta ta shiga last call din shi ne a logs dinta cikin wasi wasin rai ta rasa me zatayi runtse idanunta tayi Ta budesu kan special contact dinshi na Chan dubai, don last call dinta dashi ne, Saina haifa dake kasa, ba tare da tunanin komi ba ta danna call din, kwata kwata wayan ma baya shiga, ba karamin tashin hankali ta shiga ba don komai ya tsaya mata Chak, ganin contact din baya shiga yasa ta danna na haifa, saida tayi kusan ringing uku kafin a dauka, haifa kuwa tana zaune hankali a tashe tana neman line din amra don gaba daya headquarters ta burkice da zancenta da general, gashi taje Har apartment dinsu bata sameta ba shima kanshi general ba asan inda yake ba, Har haifa ta dawo gida hankalinta a tashe yake don rashin sanin inda kawar ta take ba karamin tada mata hankali yayi ba don ko wani irin hali ta shiga Harda ita don ita ta kawo mata shawaran yin AUREN KATIN KASA, tana zaune a daki babu irin lallabawan da ummi batayi mata ba akan ta kwantar da hankali ta saidai fur ko abinci ta kasa ci, ringing din wayanta ne ya sata janyo wayan dake gefenta ganin number da ba ta kasar ba yasa ta aje wayan gefe,Chan kuma dai jin ringing din yaqi karewa yasa ta janyo wayan tayi picking, murya amra ne ya daki kunnnenta "haiffff… it's me amra" Da sauri haifa ta mike zaune jikinta Har tawa yake tsabar murna da furgici a tare, "Babe Ina kika shiga, kina lpy? Ina kike where are you calling from" Fashe wa da kuka amra tayi kafin ta soma magana cikin shesheka "haif na dawo Nigeria,ban samu damar kiranki ba sbd gaba daya jiya hankali na a tashe yake, babe please tell me what's going on over there"
Shuru haifa tayi don tama rasa ta inda zata fara mata bayani,wayancewa ta soma yi "Thank god tunda kin koma,gaskia I can't say taqamaiman abubuwan dake nan," Saurin Tarar nunfashin ta amra tayi tace "haif just tell me, please, what's going on over there, an gano gaskia? How about him, how's he?,Haifa bazan taba yafe Ma kaina ba idan wani abu ya sameshi because of me" Tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka, mamaki ne karara a Fuskan haifa cikin taushi murya hade da lallami tace
"Calm down babu abinda zai faru, yanxu kome zai faru a cikin headquarters za ayi don ko government baza ta iya karban wannan case dinba balle kuma wasu officials din, yanxu abunda ya kamata ki fara damuwa dashi shine karatun ki," Dakyar haifa ta lallabata kafin ta kwantar mata da hankalinta. Sukayi sallama ba tareda ta samu abunda take son ji ba daga wajen haifa din
Tana nan zaune international call ya shigo cikin wayanta cikin, da sauri ta dauka wayan ta kai kunnenta "hello ma'am" Da farko bata dago wanda yake maganar ba Sai dataji yace "m5 speaking" Bata Ma tsaya amsa gaisuwanshi tace "dan Allah kamin bayanin meke faruwa, cikin harshen turanci ya soma mata bayani
"Ma'am you need to calm down, you're safe now," Shuru tayi jin ya taqaita maganar sa ta cewa "how about sir? Is he okay" "Yea ma'am he's fine, he will join you shortly" Nunfasawa tayi kafin tace "can I speak with him please"
Kamar bazai ce komai bai Chan kuma yace "he's not in a state of speaking" Hankalinta ne ya Tashi lokaci guda hawaye ya soma mata ambaliya a fuskanta tace "dan Allah ka fadamin meke faruwa, Ina ne nan aka kawoni"
"Ma'am zaki samu Ansan da kike buqata nan gaba, if you need anything you can call this line directly" Yana kaiwa na Ya kashe wayan, wani kukan ne ya sake kubce mata saida taji kanta na Sarawa kafin ta tsagaita kukan nata. Kwanan ranar tayi shi ne a wahalce.
Bari mu leka bangaren general… Kwanan sa biyu chiff anan interrogation room kafin Ana ukun aka bashi damar futowa, tunda ya fito aka wuce meeting room inda ka ganshi bazaka ce daga interrogation room ya fito ba don kamar ma hutu aka kaishi yayi ya fito, dogon zama akayi inda kamar yanda akayi zaman farko aka sake wani zaman,saida ya Sara masu kafin ya samu waje ya zauna kallon shi sukayi kafin suka soma magana "general Muhammad taura" " yes sir yayi saurin amsawa" "Ah binciken da mukayi mun gano auren da kayi is not illegal, aurenka is legal,your suspension has been called off you can now go back to your rank seat"
Murmushi yayi da gefen bakin sa kafin ya dago ya kallensu yace "thank you sir"
Mika mashi rigar rank dinshi akayi kafin ya fuce daga wajen meeting din, Kasa ya sauka kowa na harkar gabanshi Saidai bbu wanda ya sara mashi kamar yanda akeyi a da Saima Yan kuskus da akeyi, fucewa inda m5 ya yi parking yayi kafin ya bude mashi bayan motor ya shiga suka fuce daga cikin headquarters.
Dagowa yyi ya kalli m5 yace "weldone m5, you did a great job" "Thank you sir yayi saurin amsawa" "So what's the next plan now,"
"Daga nan Zan wuce dakai gida gobe flight dinka zai Tashi by 10 na safe, kamar yanda mukayi planing yanxu kowa yana tunanin anyi suspending rank dinka, and I believe daman hakan sukeso, na Har hada duk wani arrangements tare da Nigerian army, sauran binciken daya rage saika je chan, anan kuma saika bada go ahead yanda za ayi."
Shuru yayi ya lumshe idanunshi yana son ya tambayi yanda take saidai kuma ya rasa ta yanda zai fara "How's everything going over ther in Nigeria" Sanin abunda yake nufi yasa m5 cewa " everything is going according to our plan, madam is also safe" sauke nauyayyan numfashi yyi tare da lumshe idanunshi yace "Take me to the hospital..
Maida kanshi yyi kan kujran kamar mai yin bacci. Tunanin komai ya soma dawo mashi
Asalin abunda ke faruwa….. Akwai lokacin da yaje asibiti ganin likitan shi Har yayi clashing da hafiza dake bibiyarshi harta tura mashi anonymous message,da farko bai dauka abun serious ba saidai yasa m5 yayi bunciken su na sojoji. Tashin farko M5 ya nemo mashi Duk information din unknown number da farko dayagane itace Sai ya yanke shawarar ganin me zatayi, lokacin da ya gano tana da wanda suke aiki tare suna bibiyarshi shine lokacin da suka je mall shida amra wanda yayi hakan ne shima don Ya tabbatar da abunda yake zargi, nan take kuwa ya tabbatar da hakan, hafiza na aiki da Hammam wanda abun bai bashi mamaki ba kwatakwata saidai bai nuna alamun ya gane komai ba, lokacin daya fara suspecting Hammam kuwa shine tun bayan general din daya sauka wanda daga shi aka bama Amar, a lokacin ya fara bincike akan yanda Duk yawanci masu qwazon aiki anan headquarters suke barin aiki Ko kuma a sallamesu akan wani abu da sukayi achan baya su kuwa threatening dinsu da akeyi da weakness dinsu wanda suke da kawa zuci kuwa amincewa sukeyi da buqatun waenda an Kasa gano suwaye, yana kan gabar yin wannan bunciken Hammam ya kawo mashi batun yarjejeniyar auren amra wanda ya amince da hakan ne dukda aure baya cikin tsarinshi a wannan lokacin don yayi amfani da damarshi, abunda ya Kara tabbatar mashi da cewa Hammam da hafiza suna aiki tare kuwa shine Akwai ranar da Hammam ya tambayi ko Pablo ya bashi takardar yarjejeniyar auren da sukayi, amar yayi mamakin tambayar da ya mashi saidai ya shaida mashi bazai iya tunawa ba koya bashi ko bai bashi ba, hakan yasa Hammam neman pablo don jin koya bama oganshi takardun, nan ya shaida mashi ya bashi su, tundaga lokacin Amar ya cigaba da kallo shi, daga lokacin amar ya tabbatar da abunda yake zargi na neman weakness dinshi da akeyi Ko kuma abunda zaisa ayi suspending dinshi idan yaqi amincewa da buqatun su.bayan wannan ma Akwai lokacin da yayi tafiya inda yayi kusan sati guda, da taimakon cctv Amar ya gane zuwan da Hammam ya dungayi a apartment dinshi harda abubuwan da Hammam ya yi a cikin bedroom dinshi wanda bai san da Akwai cctv a cikin bedroom dinba, na farko binciken laptop dinshi ya fara da yake yawan aje wa a daki, ganin ya Kasa samun komai don strong encrypted password ne a laptop din wanda yasan a headquarters ne kawai ake amfani da portal din kuma Duk yanda zaiyi bazai taba budewa ba hakan yasa ya soma duben duben takardun da yake aje wa cikin briefcase dinshi, nan ya samu copy din takardar yarjejeniyar aure. Lokacin da Amar yaga recorded moments din daga files din cctv camera din baiyi mamaki ba saidai ya fara nashi plans din. Kamar Amar yasan da ranar threatening dinshi zaizo hakan yasa ya shirya plans dinshi ta bayan fage, Lokacin da zancen wani dan nigeria daya shigo da kwaya kasar dubai daga nan zai wuce egypt, nan take binciken dayasa m5 yayi mashi akan background din mutumin yayi mamaki sosai take ya gane cewa wannan mutumin dai daga gidan da yaran nan daya taimaka yake wato qannen amra kuma ubanshi shine marikin su a lokacin daya kara tabbatar da komai shine lokacin da health report din Salim na kwayar da taso mashi illa tayi daidai da kwayar da aka kama wannan mutumin, lokacin ya sanyo manya manyan Nigerian army a cikin lamari cikin sirri, nan take aka gano ba dan kadai ke mingling da kwayoyinba harda ubanshi ma suke business din.
Maganar aurenshi da amra kuwa sanin dole za a zo lokacin da za ayi using auren don ayi threatening dinshi hakan yasa ya shirya nashi plans din, babu tsoro ko fargaba ya Tara evidence manya manya da shaidun aurensu tun a Nigeria tun kafin tazo kasar, ba a barin nigeria dai da curruption cikin qanqanin lokaci ya shirya komai dukda baiso yin hakan ba saidai wannan ce kawai Damar da yake dashi don cimma burinshi.
Lokacin da Hammam ya kira shi ya nuna mashi true color shi baiyi mamaki ba don daman ya tsammaci hakan, kamar yanda yace ya shirya Duk abunda zaije ya biyo baya idan ba amince masu ba na cire hannunshi daga investigation din dayake, washe gari kamar yanda yayi expecting kuwa Hammam yakai Duk wani evidence din illegal auren da yayi ciki kuwa Harda abunda baiyi expecting ba wato Har wasu papers akayi na health issues dinshi Duk don koreshi saidai kuma higest attained rank group din basu damu da wannan ba don bai shafi aikin su ba, saidai samun report din cewa the most smartest, strongest and hardworking general ne zai sanya hannu cikin illegal doings, lokacin da aka nemi gani shi na gaggawa Har akayi meeting yayi expecting hakan don sun rigada sunyi planning hakan, Alokacin da aka kaishi interrogation room hankali shi a ka ace yake don yasan abubuwan da zai biyo baya, amra kuwa yasa m5 yayi mata arrangement din tafiya zuwa Nigeria ne don ya Kara tabbatarwa da mutane cewa an gane anyi banning dinta daga shiga kasar don tabbas yasan idan Har aka gano yana da nashi plan din za a iya using dinta ko ayi hurting dinta. Hakan yasa m5 yayi mata arrangement na komawanta nigeria, da farko yaso yasa akaita gida saidai ganin bashida time din yima Ammah bayani daya dace yanda zata fahimta, hakan yasa akayi necessary arrangements a gidanshi dake karkashin company taura estate tare da nema mata house keeper da zata taya ta zama kafin ya karaso. Zuwan Shi nigeria da zaiyi shima yana cikin plans dinshi don ya gano cewa Duk yanda akayi Akwai members na empire anan kasar don empire din tana da connections ba mutun daya bane tunda safarar kwayoyi sukeyi da trafficking kuma dole ta hanyoyin da yaga abubuwan dake connecting da empire din ta hanyar zai gano kosu waye don haka ya dukufa akan binciken hammam, tashin farko bincikensa ya gano masa cewa Hammam yana yin komai ne bisa ga umarnin mahaifinshi da yayi badda kama don tantirin drug smuggler ne bayaga wannan ma yana illegal abubuwan da uae government ta haramta wanda mutanen da yake dashi ne da connections ke sashi zama so powerful da ba a taba tukararshi ko gano shi. Abunda yafi bama Amar mamaki kuwa shine, ya gano cewa Hammam ba asalinsa dan alif shuraim bane, adopting dinshi yayi wanda da hakan yake manipulating dinshi yake sakashi yi mashi abubuwa saidai kwatakwata hammam bai san abubuwan da alif keyi ba ciki harda smuggling drugs. Zurfafa bincike sosai Amar yayi nan take ya gano mahaifiyar hammam wanda akayi registering mutuwarta tana raye a wani gidan mahaukata, a iya sanin dayayi ma hammam tun farko ya gane mutunne mai qaunar mahaifiyarshi baya ga wannan bai taba ganin Hammam ya shiga wani hali ba Sai Lokacin daya riski mutuwar mahaifiyarshi. Saidai abunda yafi bashi mamaki meysa akayi declaring mutuwar mahaifiyar hammam din, waye ya Kaita gidan mahaukata shin dama Chan mahaikaciya ce? Babu wanda zai bashi wannan amsoshi dole Sai shi hammam din wannan yasa ya kira hammam din. Cigaba labari…. Tun bayan daya lumshe idanunshi a cikin motar abubuwa da dama yawo suke mashi a kanshi kallon m5 Yyi kafin yace "my phone" Da sauri m5 ya zuria hannunshi cikin gefen dashboard ya zari wayoyin ya miqa mashi Karba yayi ya Kun basu duka wayoyin Kafin ya kurama line din hammam idanu, babu wani bata lokacin ya dannan Kiran hammam lokacin da call din ya shigo wayan hammam yayi mamaki sosai saidai sanin cewa dole za a sakeshi don Duk inda akace general ya wuce gaban wasa baza ayi mashi komai ba saidai za ayi suspending dinshi silently ba tare da kowa ya sani ba Dariya hammam ya kyalkyace kafin ya daga wayan yace " ka fito kenan daga…. Hmm daman na fada maka ka cire hannunka baka saurareni ba karka ga laifina fah nayi warning dinka baka ji ba"
Nunfasawa amar yayi yace "Bazan ga laifi ka ba hammam tunda bakasan abinda kake ba, you're under manipulation, hammam can't you see, open your eyes, why are you doing this,? Why are you protecting the empires" Shuru Hammam yayi kafin yace "if protecting them means protecting my father then I'm willing to sacrifice cos that's what I promised my mother, bazan taba zama butulu ba"
Dariya amar yayi kafin yace " talking of father mana nufin mutumin da yayi adopting dinka?
Mamaki ne ya bayyana akan fuskan hammam yace "how did you…" "You mean how did I find out? Don't worry there are more that I find out sannan kace sabd mamanka kake yin haka ko to inada tabbacin bazata taba alfahari dakai ba, ya kamata ka dawo tunanin ka tun kafin lokaci ya kure, Ina fatan abunda Zan tura maka zai saka dawowa daidai ka gane hanyar da kabi gurbatacciya ce"
Yana kashewa ya tura mashi hoton video mamanshi wanda yasa m5 ya dauka a asibitin mahaukata tare address din wajen kasan kuma ya rubuta *Mandate house of old age go and see for your eyes. Yana kaiwa nan ya aje wayan a gefen ya dafe kanshi dake Sara mashi sosai
Ba karamin furgici hammam ya shiga ba ganin video da amar ya tura mashi, jijiyoyin kanshi ne suka fifito sosai idanunshi yayi jaaa kamar wuta, zarar key dinshi yayi bayan ya karanta last message din ya fuce don tabbatar ma da idanunshi, direct mandate house of old age ya karasa, yanda yayi parking kadai zai tabbatar maka da ya gama zarewa, yana zuwa reception ya nuna masu video yace yana son ganin matar, nan take suka gane wa yake nema saidai gani yanda ya zare yasa suka tambayi waye shi nan take ya shaida masu danta ne shi abunda ya bashi mamaki shine nan take matar dake reception tace saita tabbatar da hakan ta hanyar kiran guardian din matar, ganin tana neman bata mashi lokaci ya sashi zaro if card dinshi ganin shi army officer ne yasa tayi saurin aje wayan da take shirin yi ta jagoranceshi zuwa dakin, turus ya tsaya hankali tashe ganin mahaifiyarshi abar qaunar shi, nan take hawaye ya soma zuba akan idanunshi daya zuba mata su,itama shi take kallo saida ta mutsuke idanunta sosai kafin ta uwar kara nan take aka taho da sauri aka ririke ta, da sauri ya karasa gabanta yana "umiy hu hadha ant (ammi is that you)" cikin kuka ya cigaba "umiy , 'ant ealaa qayd alhaya (ummi you're alive)" sosai ya rungumeta abun mamaki itama rungume shi tayi a jikin ta tace "dana,yarona kaine" Ta fada cikin larabci Saida suka gama kokekoken su kowa mamaki yake yanda ta shafe shekaru yana hauka lokaci guda memory dinta ya dawo, Nan take ya soma mata bayani "bayan na dawo daga training abbu ya shaida min mutuwarki na shiga damuwa, amma maysa na ganki annan dama baki mutu ba" "Ban mutu ba Hammam saidai zabin da aka bani yafi min na zauna a haka don bazan taba bari ka salwanta ba, Sai gashi allah ya kawo ranarda Zan hana ka shiga hadarin da tun farko aka yaudaremu batare da saninmu ba"
"Bayan tafiyarka na gano manufar alif shuraim aka ka na amfani dakai don biyan buqatunshi, babu tsoro na tunkareshi kuma ya tabbatar min da haka saidai na nuna mashi bama buqatar taimakon nashi zamu bar bashi gidanshi, nan take yayi threatening dina akan dole na nisanceka inba haka ba zai kasheni, nan ya bani zabi biyu ta hanyar bani kwaya ko kuma ya kasheni a wajen ganin banida Mafuta na karbi kwayar tundaga lokacin bansamu kaina ba Sai yanxu, I'm so sorry son na barka cikin wannan rayuwa Kara amfani" Wani irin zafi da daci zuciyar Hammam keyi, Sai yanxu komai ya warware mashi idanunshi sun bude sosai, nan take yayi alqawarin saiya kawo karshen alif kuma zai taimaki amar, abokinshi na arzki saidai yana jin kunga da takaicin rufewar idanunshi wajen taimakon mugaye.
Nan ya barta bayan ya shaida mata komai akan abunda ke faruwa " ka tafi ka barni anan Allah yana tare daku hammam Addu'a ta Ma tana tare daku, idan Har ya gane cewa ka gani gaskia zai iya lahantaka, ya kamata mu boye komai"
Da wannan sukayi sallama kafin ya tabbatar da tana under care din nurses din wajen. Amar kuwa Yana zuwa asibiti babu wani bata lokaci yanemi ganin likitanshi, nan take ya buqata likitansa da yayi unfreezing sperm dinshi, babu wani bata lokaci suka shiga operation room cikin Yan mintuna suka gama don ba wani dadewa akeyi ba wajen unfreezing din, magunguna doctor ya rubuta mashi kafin ya soma mashi bayani "thankfully kazo anyi unfreezing don daka Kara wasu kwanaki I'm sorry to say za a samu matsala, anyway for now bazaka samu erection, don't worry Duk cikin side effect din freezing dinne, but kana samun hutu da kulawa sosai komai zai dawo daidai, normally wasu in just 2days komai yake dawowa normal wasu kuma it takes a month ma,I'm sure you're ready by now ko?" Ya tambaya yana kallon amar "Uhm" kawai ya iya ce mashi kafin doc din ya cigaba "One of the side effects also is for waenda basu taba sex ba it will be a long journey, don zai saka feelings sosai and idan ka samu mace for the first time especially virgin zaka wahala sosai don zaka Kasa controlling kanka, but anyways waennan magungunan will help out sosai"
Tunda ya Lauda kanshi gege yana sauraron doc din bai kallo shi ba har saida ya gama mashi bayani sukayi sallama ya fito. Direct apartment dinshi ya wuce don daukan laptop dinshi a hajiya yake sbd haka yana shiga bai tsaya komai ba ya dauka laptop dinshi juyawa yyi zai fita nan idanunshi suka sauka akan kayan data tube Harda bra dinga garin sauri gama manta dasu bata kwashe ba, tsungunnawa yayi ya kwashe mata su, gaban closet ya karasa zai saka a ciki, Chan kuma ya tsaya kallon bra don nata yayi yana ayyana girman albarkatun kirji da Allah ya bata, nan take yaji wani abu na taso mashi, da sauri ya aje bra don ya juya ya fuce zuwa sitting room, gaba daya sai apartment din ya mashi girma sbd rashin ta a ciki, tabe baki yayi kafin yace " fitina girl" Dan murmushi ne ya ku ce mashi kafin yasa kai ya fuce daga apartment. Direct penthouse dinshi m5 ya sauke shi kafin ya wuce sama direct bayan Pablo ya gaishesa, wanka yayi kafin yayi sallah magrib da isha'I ya sauko Kasa sanya da Riga da gajeran wando bakake na under armor, sunyi matukar amsarsa sosai, dining ya wuce bai wani ci abunci sosai ba ya koma sama wajen gaming dinshi don ya kwana biyu baiyi ba, Sai wajen karfe goma ya fito daga gym ya wuce daki ya watsa hot shower A jikinshi don yana buqata kafin yabi lafiyan gado. 108-109 Update……