Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 45

Auren katin kasa complete - Chapter 45

Auren katin kasa complete Chapter 45: Auren katin kasa complete Chapter 45. Bangaren su amar tun bayan tafiyar amra kowannensu na zaune a gaban emergency…

4,117 words

Bangaren su amar tun bayan tafiyar amra kowannensu na zaune a gaban emergency room suna cikin zullumi, gaba dayansu hankalinsu a tashe yake sallah ce kawai ke fidda su amar da aman da salim, suna nan zaune har nurse tazo ta wuce da bag of jinin da aka diba na amra, tana fitowa ta sanar dasu amra tayi passing out har an bata daki, tashin hankali biyu, ga amra ga ammah, salima dai kamar zata haukace haka take ji, gashi basuji komai daga bangaren ammah ba, haka suka dunguma itada aman suka wuce dakin da aka kwantar da amra suka bar amar da salim a emergency, da sallama salima ta bude kofar, a kwance suka taddata, fuskanta yayi pale sosai, kana ganinta kasan she's not okay kwata kwata, tausayinta duk suka fara ji gaba dayansu salima dai babu abunda take sai hawaye. Basu wani dade wajen amra ba suka koma emergency ganin tana barci, koda suka koma chan ma haka salima ta zauna ta doka uban tagumi. Suna nan zaune saiga amra ta zama wata abar tausayi, salima na hangota daga nesa tayi saurin miqewa ta taho da ita don da kyar take dingisawa, suna karasowa ta kalli su aman tace ''yaya ya jikin nata? An gama operation din'' ta tambaya tana kokarin zama, kallonta yayi yana jin tausayinta sosai aranshi yace ''basu fito ba tukunna how are you feeling now? Meysa kika fito ki koma karki fadi'' ''ah ah ya aman, zan zauna anan har su fito'' Tunda suka fara Magana amar bai dago ba, idanunshi a lumshe yana addua aranshi, kana ganinshi zai baka tausayi fuskanshi tayi jaa sosai. Suna nan zaune nurse ta sake futowa hankali atashe, suna ganin futowarta suka miqe gaba dayan su,tana kokarin wucewa ta hango amra, ''alhamdullah daman dakin da kike zanje, ana buqatar wani jinin saidai ina tsoron zaki iya samun matsala kema'' Saurin katse amra tayi tace ''ku diba kawai,'' Shuru nurse din tayi tana kallonta dakyau tana son sensing wani abun, don tabbas kana ganinta kaga lafiyayyiya saidai diban jini ba abu bane mai sauqi dole zataji a jikinta, Wata nurse dinta ta sake fitowa tace ''nurse t what are you waiting for, ana buqatar jini yanxu, jinin ta yayi kasa, we can lost her at any time'' Saurin runtse idanu amar yayi gabanshi na faduwa, hankali atashe amra tace ''dan allah ki diba kawai, babu abunda zai sameni,'' Wadda aka kira da nurse t tanajin haka tace ''amma…'' ''dan allah ku diba kawai nace maku im okay'' amra ta katseta Dayar nurse dince ta shiga emergency room ta debo abubuwan da zasu diba jinin dashi, anan zaune ta saka mata canula ta soma diban jinin, babu abunda amra keyi sai runtse idanu tana hawaye, yanda takeji kamar ana zare mata rai, ana diban half nurse t ta kalleta tace ''ko zaki tashi ki dunga zagayawa saboda naga baya futa sosai''

Girgiza mata kai akwai amra tayi ta mike salima dake gefenta itama ta miqe, ahankali ta daga kafarta tayi taku daya biyu harta kusa gifta inda amar yake kafin ta yanke jiki, amar da idanunshi ke rufe yayi saurin budesu ya tarota da sauri, abubuwa da daman a yawo aranshi, cikin muryanshi da baya futowa sosai yace ''ku cire mata please'' Da kyar amra ta bude idanunta ta sauke akanshi, tsantsar damuwa ne akan fuskanshi sosai,saurin runtse idanunta tayi tace ''no karku cire min dan allah, ammah needs it more'' Binta yayi da jajayen idanunshi kafin ya dauketa gaba dayanta da hannunshi ya kalli nurse din ya nufi hanyar dakin da aka bata, yana gab da shiga dakin ya dan rankwafo daidai kunenta'' why are you stubborn, youre not okay bari acire maki'' Wasu siraraen hawaye ne suka zubo mata muryanta baya futa sosai tace ''ah ah yaya, dan allah kar a cire, ammah..'' bata kaarsa ba ta sake passing out, saurin kwantar da ita yayi akan gadon ya kalli nurse din dake biye dashi yace ''ku cire mata, zanje na nemo wani ji Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin hankali atashe, har wani tangadi yakeyi kamar zai fadi, yanxu ina zaije ya nemo jini ya tambayi kanshi, wajen emergency ya koma ya dan tsaya, yanajin kamar idan ya tafi shikenan bazai sake ganin ammah ba har abada.

After 3 hours of successful operation, sai wajen karfe biyar doctors suka fito daga cikin operating room, amar dake shirin barin wajen yayi saurin tsayawa ganin green light a jikin kofar emergency din which means an gama operation Kenan, gabanshi ne ya bada dammm, shikenan babu abunda yazo ranshi sai qila ta mutu ne, saurin rintse idanunshi yayi lokacin da doctor yake ma aman bayani kan zuje office dinshi.

Doctor na juyawa aman yabi bayanshi, amar shima dai haka ya daga kafarshi da kyar yabi bayansu zuwa office din doctor, suna shiga office din suka zauna suka kafama doctor idanu kamar tv, kallonsu shima yayi ya soma Magana ''alhamdullahi, dole mu gode ma allah, we have a successful operation, saidai shes still in coma'' Wata irin ajiyar zuciya suka sauke atare suna hamdala, amar kuwa saida yayi sujudul shukur, Kallonsu doctor ya sake yi yace ''abunda ya bamu mamaki shine shes very strong shes a fighter don ko lokacin da muka shiga operating room bamu taba tunanin zata rayu ba, saboda chance din kadan ne, sannan operation din anyi shi cikin gaggawa wanda hakan ma saboda ikon allah ne muka samu komai ya daidaita,'' Kallon doc aman yayi yace ''thank you so much thank you but munason komai game da rashin lafiyar nata, meya kawo mata wannan heart damage din?'' Nunfasawa doctor yayi ya bude file din gabanshi ya tura amsu gabansu kafin ya danyi yan danne danne akan screen din desktop dake gabanshi ya juya masu screen din ya soma bayani ''wannan scan din zuciyarta ne,wannan hole din shine yake pumping blood zuwa ga zuciya, case irin nata bamu taba samu ba saboda yawanci masu heart attack da wuya ka samu wanda heart dinshi yayi blocking gaba daya daga jan jini, saboda kwayoyin hallita da suke kare lafiyar jikin dana adam,abunda yafi bamu mamaki shine kwayoyin hallitar jikinta duk sun mutu kadan suka rage wanda sune suka taimaketa har take raye saboda jinin ta nada karfi sosai, and bayan wannan a buncikena da mukayi akwai wani substance a jikinta wanda shine ya kashe mata kwayoyin haliitar kare lafiya na jikinta wanda buncike ya nuna yana bin jininta ne bayan wannan munyi buncike akan substance din and it looks like drug ne mai karfi don drug ne mai karfi ke kashe waennan kwayoyin. Acikin file dinta naga ta taba samun heart attark, shima duk ta dalilin substance dinne don ahankali ya fara cinta harya nemi hanyar toshe wucewar jinin daga zuciyarta''

Juyowa amar da aman sukayi atare suka kalli juna, abunda suke zargi ne dai ya tabbata, so all this while daddy ita yake hari, shiyasa yace suna tafun hannunshi Kenan, muryar doctor ce ta sake katse masu tunani inda yace ''bayan wannan akwai abunda ya daure mana kai, magungunan da doctor hafix ya daurata akai ya kamata ace sunyi protecting dinta don magunguna ne masu karfi sosai, bayan wannan alamu sun nuna symptom din da take samu na fidda jini ta baki da hanci ba tun yanxu ta fara yinsu ba, maysa kukayi gangancin barinta har jininta yayi kasa?, don badan jinin wannan yarinyar ba da tuni mun rasa ta gaba daya, jinin yarinyarnan shine kadai abunda ya ceceta, sai mu gode ma Allah, and by the way shes a brave girl, babu inda aka taba diban jini bag uku lokaci guda, wasu bag daya ake diba suke passing out,'' Kallon doc din aman yayi yace ''alahamdullahi thank you so much doctor zamu iya ganinta yanxu'' ''no not now, shes in coma, will advice zuwa gobe idan komai y agama regulating don yanxu haka muma dole sai mun sanya idanu sosai akanta'' Tunda amar ya sauke kanshi kasa ya kasa dagowa har doctor y agama yi masu bayani.

Godiya sukayi mashi suka fuce daga office din, gaban emergency rooms da ake ajiye patients suka tsaya suna kallon ammah dake kwance akan gadon marasa lafiya babu abunda suke hangowa sai fuskanta don gaba daya an lullubeta fuskan nata ma an saka mata oxygyn hannunta kuma jini ne da ake kara mata, tunda suka kafa mata idanu ta jikin glass door din sunkai kusan minti talatin a tsaye, gaba dayansu duk sun firgice kamar basu ba, sun sauya gaba daya duk sun galabaice, jin ana kiran sallar magrib yasa aman yace ''muje muyi sallah'' Jiki a mace amar ya wuce aman yabi bayanshi tare da salim, fadin irin kwanciyar hankali daya samu da akace bata mutu ba ma bata lokaci ne, har sukayi sallah suka dawo cikin asibitin babu wanda yasa ko ruwa a baki, suna dawowa amar ya tsaya a bakin kofar dakin ammah ya zuba mata idanu while su salim da aman suka wuce dakin da aka kwantar da amra. Da sallama suka shiga nan suka tadda amra kwance idanunta a lumshe har an sauya mata kaya zuwa na patients, salima kuma na gefe ta na sallah tana idarwa ta mike zuwa gaban aman tace ''ya jikin ammah? An gama operation din? Hope babu abunda zai sameta? Bazata mutu ba ko?'' Haka ta dunga jero mashi tambayoyi, samun kanshi yayi da janyota jikinshi ya rungumeta yace ''calm down, the operation is succeccfull'' Jin haka yasa amra ta bude idanunta don kamar a mafarki taji Kalmar, fuskanta yayi fayau sosai tayi haske saboda jinin jikinta da aka jiba, sai jijiyoyi da suka firfito mata, kallonshi amra tayi muryanta na karkarwa tace ''is she out of danger?tana lafiya? Is she okay now? '' Saurin sakin salima yayi ya kalleta yace ''alhamdulillah, it's a successful operation, but shes still in coma, yanxu we have to wait har saita tashi.'' ''alhamdulillah alhamdulillah'' amra ta furta tana hawayen farin ciki. Kallonshi salima tayi tace ''yaya muje inason naga ammah pls'' Katse ta yayi yace ''bazaki samu ganinta ba saidai ki leka'' Amra ce ta soma kokarin mikewa tace ''please zan dubata nima, wallahi hankalina bazai taba kwanciya ba inbanganta ba'' Badan yaso ba ya jagorancesu suka fito, salima na rike da hannun amra don bata iya tsayuwa saboda jirin dake dibanta, anatse suka tako har gaban dakin inda amar ke tsaye ya zuba ma dakin idanu,kallonshi aman yayi yace ''zasu dubata'' Dn waigowa yayi ganin amra a tsaye kanta a kasa, nan take yayi saurin kauda kanshi gefe, wani irin daraja da girmanta ne ya sauka a kanshi, bayan ammah babu mace a duniyannan da yake jin ta kamar amra ayanxu, ta samu wani matsayi a zuciyarshi wanda bazai taba hadata kowa ba bayan amma, yau yarinyar daya raina itace ta taimaki mahaifiyarsa, itace ta ceci mahiafiyart ayanxu da babu ita a cikin asibitin da saidai ammah ta mutu, Samun kanshi yayi da yin baya ya tsaya daga bayanta salima ta taimaka mata suka tsaya bakin kofar, shafa kofar amra tayi tana hawaye babu abunda take fada sai ''alhamdullah ya allah, allah mung ode maka, allah ya tashi kafadunki ammah, allah ya tausasa maki ya baki strength, muna buqatarki a cikin rayuwarmu gaba daya, allah ya baki lafiya''….

Amar dai kasa tsayuwa yayi ya juya ya fuce daga wajen, don shi kadai aysan abunda yake ji a cikin zuciyarshi a wannan lokacin. Sun dade sosai wajen kofar dakin ammah kafin su koma dakin amra atare.

Karfe goma aman ya kalli amar yace ''ya kamat muje gida sai mu dawo gobe'' ''no ka tattara yarannan ku koma gida kawai ni zan kwana anan,'' Aman najin haka yace ''okay ita kuma..'' ''kuje kawai zan kula dasu'' yana kaiwa nan ya koma gaban dakin ammah, aman kuma ya juya dakin amra don sanar dasu salima sa salim su fito don su wuce gida ''salima ce ta kasteshi ta hanyar cewa ''yaya, adda fah? Ku koma kaida salim ni zan zauna da ita'' Janta gefe yayi don amra nab arci karta tashi yace ''amar zai kula da ita shi yace na wuce daku gida ma'' Jiki amace salima tace ''toh muje,'' Juyawa sukayi ganin amra nab arci basu tasheta ba suka fuce daga dakin. Suna wucewa amar ya wuce dakin amra, a kwance ya taddata tana barci fukantsa ya zubama idanu, ta rame sosai lokaci guda ta zabge, wani irin tausayinta ne ya dabaibayeshi, shi kadai yasan me yake ji game da ita a wannan lokacin, ya dade sosai anan kafin ya koma wajen ammah itama ya kai kusan awa guda a wajenta kafin ya sake dawowa dakin amra, sai ya zamana kamar shifting yake yi, idan ya duba nan saiya duba chan, gaba daya tausayinsu yake ji sosai, duk wata gajiya ma baya jinta ko kadan, karfe sha biyu ya dawo dakin amra, bai dade da shigowa ba ta bude idanunta ta sauke akanshi, kasa dauke idanunshi yay akanta, yana nazari abubuwa da yawa na yawo a kwakwalwarshi akanta, saurin kauda kanta gefe tayi batace mashi qala ba haka zalika shima baice mata komai ba, chan kuma ya juya ya fuce daga dakin, abunci ya nemo mata don yasan zata buqata anan cikin kitchen din asibitin, atare da chef din ya taho suka shigo cikin daki, kallonta ya sakeyi muryanshi kamar bazai fitaba yace ''aishaaa'' dan waigowa tayi ta kalleshi jikinta duk ya zama weak, ''seat up'' ya fada kamar bashi ba, da kyar ta fara kokarin mikewa saidai kash jikinta y agama tsami don haka tana dagowa ta koma, yana ganin haka ya matso kusa da ita ya tallabota ya zauna gefenta ya kalli cheaf din yace ''bring the food here'' Katseshi tayi saurn yi tace ''bana jin yunwa'' …….. [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update Uneditedpage

Binshi da idanu amra tayi harya fuce daga cikin dakin, da cearal dinta a hannunta ta janyo hijab dinta ta zura ta bi bayanshi, tana sauka kasa kitchen ta wuce direct ta fara kiciniyar hada coffee, anatse ta gama hadawa ta daura mashi akan saucer ta fuce daga kitchen din cikin natsuwa, da sallama ta bude bedroom dinshi a zaune yake bakin gado ya nade hannayenshi akan kirjinshi, dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta karaso har gabanshi ta dan sunkuya gefen bedside ta aje mashi mug din, ''bismillah'' Kallonta ya danyi kafin ya maida idanunshi kan mug din, cikin kamewa ya miqa hannunshi wajen bedside din ya dauka mug din kafin ya fara kaiwa bakinshi, tana ganin haka ta juya zata fuce daga dakin, hankalin shi gaba daya nakan coffee din yana kokarin cire mug din daga bakinshi bayan yayi sipping ''na baki umarnin tafiya ne?'' Tana jin haka tadan tsagaita ta juyo ta mashi kallo daya kafin ta tako har inda yake zaune ta dan tsaya daga nesa, ta dauka kusan minti biyar a tsaye duk ta gama takurewa, dan leka mug din hannun nashi tayi ganin ko half baiyi ba ta dan tabe baki ta karaso gefen da yake zaune ta zare hijab din jikin nata ta zauna gefenshi ta tankwashe kafarta kan gadon ta bashi baya tare da bude pack din cereal din nata data boye a cikin hijab, da mamaki ya waigo ganin yanda gaba daya yanxu bata kunyar shi, samun kanshi yayi da gyara zama yanda zai hangota da kyau akan gado, tana jin motsin chanza position da yayi ta juyo bakinta cike da cereal, cikin sauri ya kauda kanshi ya hade rai tamm kamar ba kallonta yake ba, sake maida idanunshi yayi kanta karaf suka hada idanu tana ganin haka ta sauke mashi lausansan murmushi mai melting herat wanda yasa heart dinshi skipping lokaci guda, cikin shagwaba tace ''yaya nifa barci nake ji wallahi, ka sallameni na tafi'' Banza yayi da it aba tare da ya sake kallonta ba, itama tana ganin haka ta juya mashi baya tana turo baki tana cin cereal din harta cinye tass, wasa wasa sun dauka kusan awa guda shi baice mata ta tafi itama bat ace mashi kala ba har barci ya soma fuzgarta, time to time yake dubanta har barci ya kwasheta ta lafe akan gadon, zuba mata idanu yayi yana kallon bayanta, hakannnan yaji hes relaxed harya gama shan coffee din, yana gamawa ya miqe ya fuce da mug din zuwa kitchen, yana dawowa ya taddata ta baje ko'ina, tayi rub da ciki, bin bayanta yayi da kallo yana ayyana abubuwa sosai aranshi kafin yayai saurin kauda kanshi, anatse ya tako bakin gadon ya kwanta daga gefe ya janyo masu duvet, koda yazo lulluba mata saida yadan tsagaita yana wani tunani aranshi ''why im I doing this?'' ya tambayi kanshi, kallon innocent face dinta yayi haka kawai yaji yana tausayinta babu dalili, saurin kauda duk wani tunanin dayazo ranshi yayi ya rufa mata duvet din ya kwanta gefe yana facing ceiling tare da nade hannayenshi a kirjinshi yana tunani har barci ya fusgeshi. Cikin dare yaji mutsu mutsu a jikinshi, ahankali ya soma bude rinannaun idanunshi harya sauke su akanta, ta nadeshi gaba daya ta rungumeshi, da mamaki ya ware idanunshi da kyau don tabbatar da abunda idanunshi ke ganar mashi, ta wani kanainayeshi tayi cuddling dinshi, he can feel her bare chest a jikinshi, saurin runste idanushi yayi ya fara kokarin janyeta daga jikinshi,bai kaiga zareta ba ta zake hade jikinta da nashi ta rike shi gam kamar ta samu pillow, shiko goga take komai ya fara chanza mashi don gaba daya jinshi yayi kamar an arura mashi wutar azaba a marar shi, ''ya allah, yarinyar nan zata haukata ni'' ya fada ahankali yana fidda nunfashin wahala, rasa abunyi yayi don gaba daya babu alamun zata bari ya janyeta daga jikinshi, gashi any wrong move yayi saita kara damkoshi wanda hakan ba karamin affecting dinshi yake ba, don haka ya hakura ma ya kyaleta saidai daren ranar dai barci kaurace mashi yayi gaba daya. Akunnenshi aka kira sallar asuba, yana jin haka kuwa ya turata gefe, ganin tana shirin damkoshi ya sashi daka mata tsawa ''kee bakida hankali ne, whats the meaning of this?'' Firgigi ta bude idanunta ta sauke akanshi, idanunta sunyi mici mici,gaba daya barcin bai isarta ba don haka ta maida idanunta ta rufe yana ganin haka kuwa ya wuce bathroom azafafe rai a bace, yana shiga ya fara yin wanka, ya dade sosai a tsakiyan shower yana rage ma kanshi wahalan da yake ji, saida yaji ana neman tada sallah yayi saurin dauro alwala ya fito ya zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin. Koda aka idar da sallah tare suka fito daga masjid shida aman da salim, idan ka gansu gwanin burgewa har suka shige cikin gida kowa ya wuce part dinsh. Yana shiga bedroom dinshi ya tako har bakin gadon ganinta a kwance kamar aynda ya barta, ranshi ne yadan sosu haka kawai don haka ya soma Magana afadace ''keee aisha!!!'' Anaste ta juyo ta bude idanunta ta suka danyi jaa ta kalleshi, ''ke are you okay?what sort of rubbishness is this? Ke kafira ne ko sai ance tashi kiyi sallah'' Miqewa tayi zaune ta kura mashi idanu, saida y agama fadace fada cen shi kawai ta fashe da kuka, wiwi ta dunga kukan shagwaba, shide tsayuwa yayi yana kallon ikon allah, lallai yarinyar nan ta gama rainashi yana mata Magana tana kukan rainin hankali, ya fada aranshi, ay baisan lokacin daya daka mata tsawa ba ''shut the fuck up, are you insane?'' Ay kamar ya kara tunzirata don haka ta miqe tsaye ta janyo hijab dinta ta karaso gabanshi tace ''haba yaya, why are you treating me like this? Meysa ka tsane ni? Me nayi maka a duniyar nan,ina kokarin ganin na faranta maka kai kuma kullum cikin neman hanyar kuntata min kakeyi,why???'' Yanda ta tsaya gabanshi babu tsor babu komai tana fada mashi maganganu ya hasalashi ya kalleta daga sama har kasa ya mata wani disgusting look yace ''nace maki ina buqatar farantawar taki ne? nace maki ki shiishigemin ne? ke kika sama kanki, waye ya yama baki wannan shawarar, look idan kina tunanin wannan abubuwan da kikeyi zai chanza mind dina youre mistaken, gwara ki daina bata ma kanki lokaci, Magana daya nakeyi bana chanza Magana, so I will advice its better you stop…''' Takowa tayi gabanshi tana sheshekar kuka jikinta na rawa ta tsaya gabanshi dab dashi ta rike kugu harda dan dingilawa don ya ganta da kyau don ya fita tsayi sosai ''nooo, nooo I will not stop, this is just the beginning ma yaya, ko mai zakace min wallahi bazan taba rabuwa dakai ba, kace ina shishigi ko ina cusa kai?, ay aynxu ma na fara, kuma kyautatawa ne ba chusa kai ba'' ta karashe tana murguda mashi baki kafin ta juya mashi baya ta duka ta dauki hijab dinta data yar da gangan a kasa, saurin yin baya yayi don gab ass dinta ya gogi gabanshi, ganin abunda take shirin yi wanda idan har ya bari hakan ta faru zaiji kunya, ba karamin chaza mashi kai yarinyar nan take yi ba itako tana dukawa ta dauki hijab dinta ta mike ta zura abunta ta gifta ta gefenshi ta nufi hanya, tana gab da fita ta dan waigo tayi murmushi don taga lokacin dayayi baya data duka ''sorry my yaya ban gaisheka ba, ina kwana?hope ka tashi lafiya '' Bata jira jin amsan shi ba ta fuce tana dariya ciki ciki, ''ay yanxu wasan ya fara, wallahi zaka ga chusa kai, daman kunya nake ji shiyasa nake baya baya dakai ammah wallahi yanxu zan nuna maka cewa ba'a yima mace haka'' Tana kaiwa nan ta shige daki ta dauro alwala ta tada kabbarar sallah tana idarwa tabi lafiyar gado hankali kwance.

Tun bayan fitar amra ya kasa motsawa, he's so stunned with her new attitude, ya kasa ganema kanshi shima yanda ya kasa taka mata burki, cije lower lip dinshi yayi yana takaicin yanda ya tsaya take fada mashi maganganu ba tare da yayi maganin ta, he's so madd, yanda she looked into his eyes har tana iya cewa she won't stop, shi abunda yafi bashi haushi ma is the fact that deep down yana son yanda take chusa kanta zuwa gareshi, dukda he's trying to distance himself from her saboda neman haukatashi da takeyi with her presence, duk motsinta akan idanunshi wanda yakeyi afake ba tare da sanin yana yi da kanshi ba, bayan wannan he started to notice he cared so for her dukda ya dauka wannan a matsayin saboda ita marainiya ne kuma yanxu reponsibity dinta da kannenshi ya dawo hannunshi saboda sanin yanda suka taso cikin wahala.

Dubai uae…. Tun bayan tafiyar amra without notice hankali haifa da Nadine ya tashi sosai. Washe gari m5 ya shaida ma Nadine saboda yasan zata damu, haifa cedai babu wanda ya shaida mata, don sunyi plans din haduwa the next day ita da amra saboda zasuyi pre graduation photoshoot, haka ta wuni tana kiran line din amra baya shiga karshe dai haka ta hakura, washe gari ma haka ta dunga kiran lne din throughout switch off, ganin haka yasa ta shirya ta wuce penthouse din amar. Koda ta iso gidan nan Nadine ta shiada mata cewa ta koma Nigeria saboda wani abu daya taso urgently wanda haka m5 ya fada mata, hankalin haifa ya tashi sosai don tana jin haka babu abunda yazo ranta sai maybe ko amra ta gudu, ko kuma general ya sake maidata gidanshi saboda wani kudirin nashi daban, ganin babu wanda zai bata amsar tambayoyinta yasa ta koma gida hankali atashe. Haka ta jera kwanaki tana zuwa gidan don neman yanda zatayi connecting da amra,gashi duk zuwan da zatayi sai sunyi sabani da m5 sabod yabar zuwa gidan, daman amfanin zuwanshi saboda ya kai amra aiki ne ko idan general yana nan, yawancin zuwan nashi sai jefi jefi yake yi don duban gidan saboda ya bama general report akan abubuwan da suke gudana a gidan wanda hakan qa''idarsa ce duk sanda baya kasar sai m5 ya bashi report ,agidan kuwa Nadine ce kawai sai dayar maid din, suke kula da gidan don sir general din bai sallamesu ba haka zalika wata na karewa zai tura masu kudin aikinsu.

After 1 month… Haifa's resident… Lokaci kamar ruwa haka yake gudu, yau wata daya Kenan rabonda haifa taji daga wajen amra, cikin kwanakin nan haifa tayi su ne cikin tashin hankali da damuwar aminiyarta, amra ta zame mata wani bangare na cikin rayuwarta da bazata taba neglecting dinta ba kota manta ta da ita, acikin kwanakin har tunanin zuwa Nigeria saida tayi saidai abuh ya hanata saboda na farko that will be the first da zata shiga kasar, gashi bata san kowa ba shima abu bashida wani connection da Nigeria don baitaba zuwa ba, don haka ya bata hakuri akan ta bari daga baya after engagement dinta da hamman wanda ake shirinyi a cikin month din.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull