Auren katin kasa complete - Chapter 47
Auren katin kasa complete Chapter 47: Auren katin kasa complete Chapter 47. Shuru kake ji a dining,babu wanda yace kala sai karar spoon dake tashi. Da…
4,442 words
Shuru kake ji a dining,babu wanda yace kala sai karar spoon dake tashi. Da sallama lantana ta shugo dining din hannunta dauke da dogon cup data hadama ammah green juice aciki, saida ta gaishe da kowa kafin ta matso kusa da ammah ta aje mata kan table tace ''hajiya ga girin juice din'' Dariya salima ta danyi data kubce mata tace ''kai anty lantana, keda wannan girin din'' Murmusa duk sukayi ammah tace ''nagode lantana sarki aiki, bakya mantuwa,ni wallahi mantawa ma nakeyi da green juice din'' Murmushi kawai lantana tayi ta juya da nufin shiga kitchen, amra data kafeta da idanu tana ganin juyawarta tace ''ji mana'' Juyowa lanatana tayi ta tsaya tace ''naam anty'' Miqewa amra tayi ta tako inda ammah take zaune tana kokarin kai juice din bakinta tace ''ammah zansha'' Da mamaki ammah ta kallota, kafin ta dan murmusa tace'' gashi doctor ay bana hanaki ba,'' Karba amra tayi ta juyo gaban lantana ta kalleta tace ''anty lantana ko zaki fara sha kiji min idan da daci'' adaburce lantana ta kalleta tana yaqe tace ''ay na taba sha, akwai daci kam wallahi, anya zaki iya sha kuwa keda kike son zaqi'' Shuru amra tayi ta sake kallonta fuskanta babu wasa, tace ''yaushe nace maki inason zaqi?, kedai ki dandana min kawai'' Atsorace lantana ta sake kallonta tace ''kaii ni zawayi yake sani saidai ki bama ammah ta dandana maki'' Amar da kanshi ke kasa yana jiyo su sama sama ya dago ya kallesu, nan kowa ma ya maida kallonsu kansu, amra dai ta dage akan lantana saita dandana, ita kuwa lanata data gama tsurewa sai dojewa take karshe ma cewa tayi, ''na doraruwan zafi akan gas bari na kshe'' Kamar daga sama taji muryar amar ''stoppp there'' Ya fada a kausashe kafin ya tako har inda suke, hannu ya sanya ya janye amra gefe anatse kafin ya karbi juice din daga hannunta ya kalli lantana yace ''shaaa'' Haba waa nan take lantana ta saki futsari, gaba daya alamunta sun nuna bata da gaskia kiri kiri, Akaro na biyu ya daka mata tsawa yace ''takeeee it and drink it up'' Jiki na bari ta karba ta fara kokarin kaiwa bakinta, bata kaiga sha ba ta saki cup din a kasa wanwas ya fashe juice din ya malale, saurin miqewa duk sukayi daga kan ammah zuwa ga aman da abun shima ya daure mashi kai, Kallon cup din amar yayi zuwaga juice din dake Malala, ahankali idanunshi suka sauka kan wani yellow drug da bai gama melting ba a cikin juice din, tsugunnawa yayi ya dauka kwayar yak are mata kallo sosai, if hes not mistaken wannan molly ce wanda daddy yake safarar su ga manyan kasashe, wanda a shekara sau daya yake hadata kuma baifi mutun biyar yake sayarma ba duk duniya, kuma da ita yake amfani yake kashe mutanen da suka nemi susha gabanshi, hankali atashe amar ya dago idanunshi sun kada sunyi jaaaa, jikinshi harya soma bari barr barr, ya kalli lanta adata saki futsri, yau karyarta ta kare asirinta ya tonu, yanxu ko tace zata falfala ta gudu bazata tsira ba, ammah ce ta kaste silence din ganin amar ya furgice lokaci guda, anatse ta tako inda suke tsaye don nesa kadan suke da dining tace ''muhammad whats wrong? In tace bata son sha ku kyaleta mana'' Hanakali aatshe ammah tayi baya ganin yanda amar ya karade ya sauya, idanunshi sunyi jaaa fuskanshi ma tayi jajawur, lantana na ganin haka tayi saurin zubewa a gwiwarta ta dora hannu aka ''na shiga uku ni abida wayyo allah na, yau karshena yazo, don darajar allah ku yafe min wallahi wallahi bayin kaina bane, sharrin shaidan ne na rantse da allah'' Kallonta amma tayi don bata gane kan zancen ba ''ke lantana meke faruwa anan? Me kikayi da kike neman gafara'' ''wallahi hajiya ba laifin…'' tassss taji saukan marinda saida ya toshe mata kunnenta nan take taji wani dummmm saida ta yi baya, bata gama jin zafin marin bay a sake kwasheta da wani marin, fuskanshi yayi jaa sosai jikinshi har rawa yake,wanda yasa ammah da amra yi baya son sun tsorata da yanda suka ganshi, lantana dai ta tafi hutun wucin gadi kafin ta dawo ya sake ball da ita, aman ne yayi saurin taro shi yana kokarin kamashi ya hambare hannunshi gefe ya sake bata wani blow daya sata gangarawa har wajen parlor, dukda haka bai barta ba saida ya bita ya dunga kwallo da ita gaba daya ya fuce daga hayyacinshi, ammah na ganin zai kashe yar mutane tayi saurin bin bayanshi tana ''muhammd kaii muhammd menene haka, dukan mace kakeyi? Kome tayi maka bai chanchanci kayi mata haka ba'' Ay muhammd fa ba sauraron ta yake ba, haka su amra sukabi bayan su suma aman ma da y agama gano komai yayi saurin bin bayansu don tabbas amar zai iya kasheta anan take, don haka yayi gaggawar janyo wayarshi ya soma kiran hukuma, Ammah dake bin amar har suka fito tsakar gida yana ball da lantana tayi saurin kallon amra tace ''aisha meke faruwa ne?,'' Kasa cewa komai amra tai don itama Karin bayani take nema, saida amar yayi mata lugu lugu idanunshi sunyi jaa sosai ya janyo wayarshi daga aljihunsa baya gani ma sosai yayi dialing number asad,yana picking azafafe yace "idan ka wuce 5 minutes baka zo nan gida b azan kashe wannan wicked soul din'' yana kaiwa nan ya kashe wayar ya fara neman abunda zai dauka ya karasata, ganin wani karfe daga chan gefe yayi saurin juyawa ya dauko yayo kanta dashi, ammah na ganin haka ta dafe kirjinta tana innalillahi, Muhammad zaiyi kisa akan idanunta, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, bat agama tunani ba taji kwal ya bugama lantana a kafa daya saida kafar ta balle, daga hannu yayi zai sake buga mata amra tayi saurin tahowa inda yake ta rungumeshi ta baya ''yayaa don allah calm down, karkayi abunda zakazo kayi dana sani'' Baya ji baya gani yace ''sakeni,'' ''wallahi bazan sakeka ba yaya, bazan taba bari kayi abunda zai jefa rayuwar ka a halaka ba,'' ''aishaaaaaaaaa'' ya daka mataa tsawa, dukda ta tsorata hakan baisa ta sakeshi ba, wani irin juyi yayi ya zubar da ita a kasa, nan take ta kwala uwar kara dayasa ammah ta kalleta, kankace me cikin kankanin lokacin ammah ta zube a kasa wanwas, jini na fita daga bakinta da hancinta hankali atashe salima ta kwala kara ''ammahhhhhhhh!!!!! Wayyo allah na shiga uku'' Amra da bat agama dawowa daidai tana ganin ammah a yashe a kasa tayi saurin rarrafowa ta karaso wajen, ganin ammah a kwance hankali aatshe ta taba ammah tace ''ammah ammah'' jin shuru ya sata taba wajen zuciyar ammah, dipp komai ya tsaya chak, hankali atashe amra ta dago agigice ta kalli salima da aman da suka zagaye ammah tace ''am….mahhh..ta mutu.uu..''hannunta da bakinta duk karkarwa suke, da sauri ta miqe tsaye kamar mahaukaciya har veil dinta na faduwa ta kaarso inda amar ke bugun lantana da duk jini ya gaba malalewa a jikinta ga uban raunuka daya ji mata, amra na karasowa ta daka mashi tsawa daya sashi tsayawa babu shiri ''amarrrrrrrrrr!!!!!' idanunta sunyi jaa sosai sai sauke nunfashi takeyi Da sauri ya waigo ya kalleta ya zuba mata idanunshi, tana ganin haka ta juya ta nuna mashi ammah ''ammahhhh'… ammahhh''' Ay baisan lokacin daya saki rodin ba taku biyu uku ya iso inda ammah ke kwance kamar gawa, salima a furgece ta dago tana kuka ''ya aman wai ta mutu, ammah ta mutu, na shiga uku na wayyo allah na'' Amar daya tsaya kikam ya kasa yin komi, jikinshi na bari ya durkuso ina ammah ke kwance rai a hannun allah……… [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: UPDATE Unedited page Ba tareda ya saurare ta ba ya janyo table din da chef din ya ajiye abuncin kafin ya fuce yace ''bana son gardama eat'' Kauda kanta gefe tayi jiki amace tace ''toilet nake son shiga'' Mikewa yayi ya sungumeta gaba dayanta, arazane ta juyo ta kalleshi, gaba daya bata da wani kuzari ajikinta don hka ta lafe a jikinshi har ya shige da ita bathroom din, yana shiga ya sauketa akan wc ya fuce daga bathroom, Bayan fitarshi ta soma tube kayan jikinta tayi wanka da ruwan zafi sosai kozaji dadin jikin nata, tana gamawa ta dauro alwala jiki amace dukda tana jin jiri sosai. Tana gamawa ta maida kayan asibitin ta fito anaste,lokacin dta fito yana zaune kan kujeran dake gefen gadon asibiti, ya dafe kanshi dake sara mashi, baiji alamun fitowanta ba saida ta rufo kofar bathroom din, dago kanshi yayi ganinta tsaye tana shirin takowa harta karaso baking ado kanta akasa, tana zuwa bakin gadon ta janyo jallabiyanta datazo asibitin da ita ajikinta, kokarin komawa bathroom tayi ganin haka yasa yayi saurin ''let me excuse you'' Yana kaiwa nan ya juya ya fuce, da mamaki ta bishi da idanu kamar bashi ba,gaba daya yayi laushi sosai, tausayinshi ta soma ji lokacin data maida idanunta kan abuncin day ace taci, yanxu haka shima baici ba ta fada aranta,jiki a mace ta sauya kayan jikinta zuwa abayar nata kafin ta zauna a kan carpet ta tada sallah. Tan idarwa ta koma kan gado ta lafe jikin gadon ko kallon abuncin batayi ba don bakinta ma daci yake mata sosai.
Wajen karfe daya tana nan zaune kafin ta miqe ta gyara mayafin abayarta ta fuce daga dakin, direct emergency ward ta wuce zuwa inda aka kwantar da ammah, anatse take tafiya kamar zata fadi harta karaso wajen, batama lura dashi ba, yana zaune daga gefen kujerun reception din ya dafe kanshi dake sara mashi sosai, Gaban dakin da ammah ke ciki ta tsaya, ta jikin glass din kofar dankin take hangota hancinta maqale da oxygen dake taimaka mata waje fidda nunfashi, ba karamin tausayinta taji ba, ta kasa gane dalilin da zaisa lantana ta cutar da wannan baiwar allah, dan zaman datayi da ammah ta karanci halayyanta, macece mai tausayi da kaunar kowa, bata da ha'inci kwata kwata ga son mutane ga hakuri uwa uba ga kyauta, batada matsala kwatakwata kowa nata ne, idan kowa bai shaide ammah ba toh tabbas ita da kannenta zasuyi mata sheda mai kyau don tayi masu komai a duniya, ammah uwace ta gari a gurin kowa. Fashewa amra tayi da matsanancin kuka sosai tana wannan tunanin aranta harya dago kanshi don kwata kwata baijin motsin ta ba data karaso wajen ba sai yanxu, samun kanshi yayi da kallonta ba tare da tasan yana yi bama, kuka sosai takeyi kamar ranta tana tausayin ammah sosai, ayau koda ance ta bata zuciyarta zata iya, ba karamin tashin hankali ta shiga ba lokacin data ga lantana tana saa mata abu acikin drink, don bashine frist time da hakan ya faru ba, dukda bata kawo komai aranta daga farko ba saidai dole yanda lanata tayi acting kamar mara gaskia lokacin data shiga kitchen dinnan ya tabbatar matar mata da something is fishy, tana nan tsaye wani irin karar na'ura ta soma tashi daga dakin, ammah dake kwace ta soma jijiga, zaro idanu amra tayi kan kace me saiga nurses gaba daya sun taho hanyar dakin harda likitoci guda biyu, hankali atashe amar ya miqe yazo gaban dakin inda amra ke tsaye, nurses na ganinsu bakin kofar suka ce ''sir ku bamu waje,'' Hankali atashe amar yace ''waaa…waaas…whats going on? Meke faruwa, you guys should fucking explain whats going on'' Ba tareda sun bashi amsa ba suka wuce cikin dakin gaba dayansu harda doctors din, nurse day ace kawai ta tsaya bakin kofar tana kokarin yi masu explaining,''sir dan allah ku kwantar da hankalinku, zamuyi iya kokarinmu akanta please'' Tana kaiwa nan ta koma cikin dakin suka dukufa akan ammah da likitoci, amra dai kasa tsayuwa tayi saida ta dafe bango, amar kuwa tunda ya kafama kofar idanu yana hango yanda suke fidda wasu na'urori agaban ammah hankalinshi ya tashi, yanda likitocin ke zarya akan ammah suna kokari cetota, babu abunda amar ke fadi sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sun dauka kusan minti ashirin a gaban ammah suna kokarin daidaita bugun ziciyarta saidai kasha bun yaci tura, kafa masu idanu amar yayi ganin sun tsaya gaba dayansu, nan take gabanshi ya fadi dammm, bude kofar doctor yayi jiki a mace kanshi a kasa ya karaso inda amar ke tsaye yace ''im so sor….'' Janyo rigarshi amar yayi yace ''what do you mean by that?, why are you sorry'' ''yallabai sai hakuri, zuciyanta ya tsaya chak bata nunfashi babu abunda zamu iyayi im sor….' Doctor bai gama fadaba amar ya katseshi ya soma cewa ''innalillahi wa inna ilaihi rajiun, innalillahi wa inna ilahi rajiun'', nan take yayi baya yuuu zai fadi, cikin sauri doctor ya taroshi, mikewa amra tayi aguje ta karaso inda amar ke yashe a kasa babu numfashi yayi passing out, saurin kamo hannunshi tayi ''yaya yaya dan allah ka tashi na shiga uku'' Gaba daya ta gama susucewa kamar wadda tayi karamin hauka babu abunda take cewa sai ''yaya dan allah ka tashi, ammah bata mutu ba bazata mutu yanxu ba insha allah''
doctor ne ya kira nurses sukada janyo gado aka saka amar akai don yayi passing out gaba daya, amra dake tsaye itama kunnuwanta zun gama jiyo mata abunda doctor fada ga amar a kwance shima kamar babu rai hankalinta ya gama tashi sosai har wani dishi dishi take gani, haka aka gangara da gadon da aka kwantar da amar har zuwa wani daki amra na biye dasu duk ta gama susucewa, har aka kwantar dashi aka mashi allura don ya samu shock ne, amra dai babu abunda take sai maimaita innalillahi a zuciyanta, shikenan ammah ta mutu, innalillahi wa inna ialihi rajiun, kallon amar tayi kawai saita fashe da wani matsanan cin kuka, haka ta duga sintirya agaban gadonshi tana hawaye ga jiri na dibanta, hankalinta y agama tashi don bata san mezai faru dashi ba shima,gabanshi ta karaso ta tsaya tana kuka ta rike hannunshi da kyau ''yaya…'' tana fadin sunan shi ta sake fashewa da wani matsanancin kukan sosai, ta dauka tsawan minti talatin a kusa dashi har ya soma motsa hannunshi, da sauri ta dago ta kalleshi lokacin harya bude idanunshi da sukayi jaa sosai, zumbur ya miqe ya dafe kirjinshi dake bugu fat fat fat, amra na ganin haka ta soma toshe bakinta ta kalleshi, shi baima kalleta bay a soma juya kanshi yana cewa ''no nooo nooo innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wani irin mafarki ne haka'' ya fada yana confusing kanshi, shuru amra tayi tana kallonshi ta kasa cewa komai har nurse ta shigo don ta duba koya tashi don alluran da akayi mashi relaxing mind takeyi idan mutun ya samu shock, after 30mins kuma zai farka, don haka tana shigowa ta kaarso gabanshi zata duba yanayin bugun zuciyarshi tana karasowa ya daka mata uwar tsawa ''don't fucking touch me, get outtttttt!!!'' yanda ya fada saida ya razanar da nurse din harda amra, aguje nurse din ta fuce don idanunshi sunyi jaa sosai jijiyoyin wuyanshi duk sun mike, amra dai bata motsa ba dukda ta tsorata sosai baya ji baya gani haka ya sauko da kafafunshi kasan gadon yana kokarin fucewa daga dakin ''karya kuke wallahi, ammah na tana raye'' yana miqewa ya fara tangal tangal zai fadi, da sauri amra ta taroshi, nauyinshi ne ya rinjayeta nan take suka fadi gaba dayansu a kasa, da sauri yafusge jikin shi ya juyo da jajayen idanunshi ya kalleta, kafin ya yunkura zai sake tashi, bai kaiga daga kafarba ya sake faduwa kasa,yana ganin haka ya dafe kanshi kawai, amra na kuka matso kusa dashi da kyar ta karaso hannunta na rawa ta fara kokarin dafashi ya daka mata tsawa ''leave me alone, ki fitaaaaa'' muryanta na rawa ta dafa ''ya…ya'' ''ki futa nace, bana son ganinki'' ya fada yana sunkuyar da kanshi, idanunshi sunyi jaaa sun tara ruwa, kwata kwata hawaye suqi futa daga idanunshi, abunda yakeji kadai ya fi kuka ciwo, yau ta kasance rana mafi baqanta a cikin rayuwarshi, har lokacin ya kasa believing abunda kunenshi suka jiyo mashi, yana nan zaune ya dunqule hannunshi ya fara bugun tiles din dakin,amra na ganin haka tayi baya tana hawaye ta fara girgiza kanta ta toshe bakinta da hannunta tana, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, babu abunda ke shimfide afuskanshi sai pain,he's in so much pain, bugun hannunshi yake akan tiles din yana ''noo noo nooo ammah noooo'' Yanda yake bugun nan saida tiles din ya fashe, hannunshi ya soma fidda jini, arazane amra ta karaso gabanshi jikinta na bari fara kokari rike hannunshi nashi, kasa hanashi tayi don kamar ta rike rock har jini ya fara Malala akasan dakin, tana kuka haka ta miqe ta rungumoshi gaba daya zuwa jikinshi ta kankameshi, ''yaya dan allah ka bari, zaka jima kanka ciwo'' Baya jinta ma kwata kwata don y adage sai bugun hannunshi yake yana ''nooooo ammah na nooooo'' Rukoshi tayi da kyau ta soma karanto mashi addua a kunenshi, tana jin yanda kirjinshi ke bugu kamar zuciyarshi zata futo, har razana saida tayi saidai hakan baisa ta sake shi ba saima dagewa datayi tana mashi addua a kunneshi,ta dauka kusan minti goma tana yi har ya daina bugun hannunshi nashi ya fara sauke ajiyar zuciya, ''shikenan, ammah kin tafi abu ya tafi,kun barni ni kadai, innalillahi wa inna ilaihi rajiun,'' ya fada yana kankame amra sosai, kwata kwata ya kasa fidda hawayen dake cikin idanunshi, zuciyarshi is so tough, when it comes to ammah hes so weak, itace weakness dinshi, lokaci guda yaji kamar an toshe mashi farin cikin rayuwarsa gaba daya. Yanda yake maganganu ba karamin karya zuciyar amra yayi ba,fadin irin tausayinsa da take ji a lokacin ma bata lokaci ne, she can feel his pain don ta shiga irin yanayi daya shiga lokacin da nasu iyayen suka mutu, tana kuka shabe shabe ta soma mashi Magana anatse cikin kunnenshi ''yaya, youre not alone, you have us you have me, allah yana tare dakai yaya, dan allah ka sauke hawayen dake cikin idanunka ko zaka samu sauki,'' Gaba daya ya gama sandarewa ya zama kamar dutse, zuciyarshi ta dashe gaba daya ta sauya daga haske zuwa baki. Suna nan zaune saiga doctor ya shgo dakin…… [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update Unedited
Suna karasowa Madina tayi parking gefen da Aman yayi parking motarshi, atare Duk suka fito, amra ba gefen Madina while salima na gefen su itama sai Aman da Salim da sukayi gaba. Anatse take ta kawa kanta a kasa, Madina ta Lura da yanda tayi sanyi sosai saidai bata tambayeta dalilin hakan ba, anatse suke tafiyar Har suka karaso dakin ammah, Aman ne ya bude kofar Duk suka shigo atare, babu kowa a cikin dakin sai ammah da nurse dake tsaye a gefenta tana goge mata jiki da towel cikin wani warm towel, juyowa nurse din tayi suka gaisa daman ta gama goge ma ammah jiki don haka ta wuce bathroom ta zuba Mr da ruwan ta fuce daga dakin. Takowa Madina tayi tare da amra gefen ammah suka tsaya, kallonta suka fara yi, babu abunda ya sauya a tattare da ita sai nunfashi da take fitarwa ahanakli, kallon amra Madina tayi tace "Allah ya bata lafiya ya Tashi kafadunta," Madina ta fada fuskanta na nuni da jimamin da take yi, salima ce ta karaso inda suke tace "Ameen anty Madina mun gode" Amra dai bata ce komai ba tana tsaye ita ma gefen gadon ta kame jikinta, sanye yake da abaya baqa tayi rolling kanta, gaba daya itama she looks pale,suna nan tsaye Aman ya shugo tare da doctor, gaba daya matsawa sukayi daga gaban gadon don su basu waje, Madina ce ta fara gaishesa, bai ma kalli inda take tsaye ba kamar kullum fuskanshi a hade babu fara'a ya amsa kafin su salima suma gaishesa, amra dai na daga gefe, don koda ya shigo bata dago kai ta kalleshi ba balle ta gaishesa, gaba daya wani irin haushinsa take ji sosai, don ko muryarshi bata son jin, shima koda ya shigo bai dago ya kalli kowa ba so bai wani damu da wanda ya gaishe shi ba da wanda bai gaishesa ba,
mikewa Aman yayi ya bashi hannu shida doctor sukayi misabaha, kafin doctor ya sake duba jikin ammah, Yan gwaje gwaje yayi kafij ya waigo ya kallesu yace "Masha Allah, tana healing cikin ikon Allah, don yanxu bata buqatan oxygen sabod nunfashinta yayi stabilising,sannan rashin farfadowartaba matsala bane saboda dole daman zata dauka dan lokaci kafin ta farfado sannan alluran da mukayi mata suna dade wa kafin su saki mutun" Yana kaiwa nan ya miqa ma Amar hannu, godiya ya mashi sosai kafin ya fuce daga dakin.
Doctor na fita salima ta kalli Amar daya tsaya bakin gadon ammah ya kafa mata idanu tace "ya Muhammad ga abunci an kawo ko azuba maka" Bai waigo ba cikin kamewa yace "no" Shuru sukayi gaba dayansu babu wanda yace qala Duk suna daga tsaye, kallon amra Aman yayi yace "sister inlaw ku zauna mana bismillah" yayi masu nuni da kujeran visitors doguwa inda Salim ne zaune. Juyowa Madina tayi ta kalleshi kafin ta maida kanta kan amra tace "Ay ni wucewa ma zanyi, amma Zan dawo da daddare Insha Allah" Kallonta amra tayi jiki amace tace "Toh anty Madina muje na rakaki" Tunda amra ta fara magana ya danyi jim ya lumshe idanunshi, bai yi tunanin da ita aka zo ba don bai dago ya kalleta ba, sai alokacin yayi mamaki sosai. Sallama Madina tayi masu kafun ta nufi hanyar fita amra na biye da ita. Tun a kan hanyar futa daga reception Madina ta dan tsaya ta kalleta "amra meke damunki? Nayi sensing abu na damunki, now tell me,meysa kika rame haka? Duk jikinki yayi sanyi" Dan dagowa amra tayi tana dan qaqalo murmushi tace "babu komai anty Madina stress ne kawai na yawon asibiti, bayan wannan ma tashin hankalin da muka shiga na rashin lafiyar ammah kadai ma zaisa hakan" Shuru Madina ta sakeyi tana nazari kafin ta dubi wayarta Ganin tana lattin zuwa aiki, "Zan dawo anjima da daddare Insha Allah zamuyi magana," "Toh anty madina allah ya kaimu" amra ta fada tana lumshe idanunta alamun gajiya da tsayuwan da sukayi, "ki koma kawai na hutar dake amaryar general" Dan murmusawa Madina tayi kafin ta wuce parking lot amra kuma ta samu waje anan gefen reception ta zauna ta doka uban tagumi kamar wadda aka aikoma mutuwa, abubuwa da dama suna yawo a kwakwalwarta.
Cikin dakin ammah kuwa, Amar ne ya miqe ya kalli su salima da Aman yace "zan wuce gida yanxu, idan wani abu ya taso call me" Aman ne ya kalleshi yace "okay, zaka wuce da sister inlaw ne?" Hanyar kofa amar yabi kafin yace "no, bazan dade ba Zan dawo" Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin ya nufi hanyar reception l, anatse yake tafiya kamar basarake Har ya kusa karasowa Inda take zaune ya doka uban tagumi ta fada duniyar tunani, Har ya kusa giftata ta dago tana shirin miqewa, kallo daya tayi mashi ta kauda kanta gefe, shikam Bai dauke idanunshi akanta ba haka zalika bai tsaya ba ya wuce abun shi, itama tana Ganin haka ta juya ta nufi hanyarshi dakin ammah jiki a mace, da sallama ta shiga cikin dakin, kallonta Duk sukayi gaba dayansu kafin ta karaso Har cikin dakin ta zauna kan kujera ta dan jingina don gaba daya babu abunda ke mata dadi, Har akayi sallah zuhur Duk sukayi sallah bai dawo ba, Aman da Salim Har suka je masallaci suma suka dawo, suna dawowa salima ta zubama kowa abunci Banda amra wadda tace bata jin yunwa sai zuwa anjima, kallonta salima tayi tace "adda ko breakfast sun kirki fa bakiyi ba dazu? Ko baki jin dadi ne?" Dago da jajayen idanunta tayi don ta sauke kanta kan gwiwanta tana jin wani irin ciwon kai sosai, anatse ya soma magana "kaina ke ciwo zanci anjima" Salima naji haka ta kyale ta ta zauna gefen Aman dake zaune kan carpet ta fara cin abuncin da suka taho dashi din hankali kwance. Har suka gama salima ta tattara amra bata dago ba kanta akasa.
Bangaren Amar yana komawa gida ya watsa ruwa ya kwanta don idan sunyi switching baya barci haka zai kwana a zaune yana yima ammah addua tare da fatan farfadowarta, sai wajen karfe uku da rabi ya Tashi daga barci, ba karamin dadin barcin yaji ba don wani irin mafarki yayi mai wuyar fasaara,dukda yajin dadin mafarki don Harda amra a ciki hakan bai hanashi tabe baki ba yayi tsaki ya wuce bathroom ya sake wani Sabon wanka kafin ya futo ya shirya cikin branded kananun kaya marasa nauyi, kamshinsa ne ke Tashi ta ko'ina harya fuce daga gidan ya kullo kofar. Yana fitowa wayar asad na shugowa, kallon wayar yayi kamar bazai daga ba, Har ya shiga cikin motar ya fara warming dinta, nan take wani call din ya sake shugowa, saurin daga wayar yayi tare da sallama,daga chan bangaren asad ya amsashi kafun ya soma mashi bayani, "oga mun kama doctor hafiz tun Daren jiya, naso Na kira na maka bayani tun alokacin sai nayi tunanin hakan bai daceba saboda kana tare da Mara lafiya, jiya wajen karfe sha daya na dare kuka kamashi a nnamdi ezikiwe international airport yana kokarin gudu wa tare da iyalinshi, ayanxu haka yana cikin interrogation room ban fara interrogating dinshi ba na bari saika zo tukunna" Shuru amar yayi yana wani nazari, tabbas ya kamata ace yana tsaye akan Duk wannan interrogation din don he needs to, saidai kuka bayajin zai iya barin ammah a yanxu inhar ba Ganin ta yayi ta farfado ba, ayanxu Duk mintuna da seconds da yake fiddau nunfashi a duniya yanada mugun amfani a wajen shi saboda ya girgiza sosai da abunda suka faru a cikin kwanakin, Nunfasawa yayi kafin ya danyi gyaran murya yace "asad, banida lokacin wannan ayanxu saboda inhar ba Ganin ammah nayi ta farfado ba bazan iya yin komai ba, kayi interrogating dinshi Duk wani abu da kasan zamu buqata, yanxu lokacina nayi dedicating dinshi to mahaifiyata ne, bazan taba samun natsuwar yin wani buncike ko interrogation, but inason Duk wani abu da kasan Zan buqaci sani Ka buncika, bazansake yin sake ba akan family na ba, this should be the last Insha Allahu" "Okay yallabai ba matsala, zanyi kokarin rukesu for now sannan zanyi maka Duk wani buncike," Godiya amar yayi mashi kafin ya kashe wayar ya yo reversing motarshi ya fuce daga gidan gaba daya.
Tunda ya fara driving ya maida hankalinshi kan hanya, babu abunda ke Tashi a kofar sai karatun Qur'an na sudais, anatse yake driving harya iso asibitin, saida ya tsaye a masjid yayi sallahr asr kafin ya wuce cikin asibitin.