Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 5

Auren katin kasa complete - Chapter 5

Auren katin kasa complete Chapter 5: Auren katin kasa complete Chapter 5. Yau kam amra bama ta jira sun fito tare da haifa ba ta wuce gida, don wani jir…

4,440 words

Yau kam amra bama ta jira sun fito tare da haifa ba ta wuce gida, don wani jir jiri takeji sosai,wuraren 4 anatse haifa ta fito ta wuce wajen motor ta, ahankali ta soma kunna motor amma me, mota tace ay saiki tafi mu gani, ganin har kusan awa daya yasa ta hakura ta fito domin kiran ride, hammam wanda tun fitowarta duk a idonshi yasa yayi sauri kiranta a waya, tana ganin call din tayi maza tayi picking, ahankali ta fara kalle kallen wajen, chan ta hangoshi wajen parking space din senior officers, amsa wayan tayi sannan ya soma Magana ''babe whats up with the car, naga baki tafi ba''..nan ta shaida mashi moton ne yaqi tashi, ganin haka yasa shi cewa su hadu a waje saiya dauketa ya sauketa gida, fita ya farayi kafin ta biyo bayanshi har bakin first gate, duk ta jigata sbd nisan wajen ba kadan bane, anatse ta bude gaban motorn ta zauna sannan yaja suka wuce, saida suka tsaya a wani café suka sha hiransu ta masoya ya saya masu icecream kafin su fito su shiga moton shi, anatse ta soma mashi Magana cikin dabara ''hamma, yanxu cikin army officers akwai wanda zai iya aure with illegal action?"..jin haka yasa yayi saurin kallonta lokacin yazo daidai kofar gidansu, saida yayi parkin gefe kafin ya juyo ya kalleta yace ''tell me why you askin me that? Are you planning on getting married illegally without your parent consent or what''??..jin haka yasa hankalinta ya dan tashi tace ''never mind kawai daman wani abu ne ya fado min arai''..jin haka yasan tana cikin damuwa sosai..ahankali ya kamo hannunta yace ''habibty what's the matter??, nasan wani abu yana damunki, cos I can see it in your face''…shuru tayi tana tunanin fada mashi, ganin shine dai close person da zata iya fada mashi wannan magana kuma babu damuwa yasa ta soma Magana ''babe, amra tana cikin damuwa, and I want to help her so bad'',,tana kaiwa nan ta fashe da kuka, ahankali ya soma dabbing bayanta har ta daina kukan sannan yace ''now tell me what's the problem so I can see if I can help''…anatse ta kwaro mashi duka bayanin yanda sukayi da matar da kuma last option data basu sannan ta karashe da ''habibi please what should we do now huh??"…nunfasawa yayi ya fada tunani mai zurfi, kafin ya fara tafa hannayenshi biyu fuskarshi dauke da murmushi yace ''habibty, matsalarki ta kare indan har wannan ne, inada solution to your problem, but for now just calm down karki fada mata, inason saina tabbatar da hasashe na kafin na taimaka maku''…jin haka yasa haifa sauke nauyayyiyar nunfashi sannan sukayi sallama ta wuce cikin gida.

Shiko hammam har ya koma gida, zuciyarshi fess babu wani damuwa a tattare dashi kwata kwata..yana shiga gida ya tadda babanshi zaune kamar kullum a sitting room ana mashi tausa kamar basarake, nan take annurin fuskar hammam ta dauke ya karasa gabanshi ya gaishesa tare da tambayan ya tafiyanshi zuwa Israel da yace yayi, baima amsa mashi ba ya fara tambaynshi abubuwan dake gudana a office da kuma kunamar da yasashi sa ido akanta kafin ya cin mata, suna gama tattaunawa ya wuce sama direct dakinshi, saida yayi wanka ya chanza zuwa pjs kafin yayi sallah sannan yabi lafiyar gado.

Amra dai ta cire rai kawai, kwanan ranar bata samu ko bacci barawo yayi gaba da ita ba, ta durqufa gaban Allah, tana kai mashi kukanta da kuma kawo mata mafita daga gareshi, sai bayan subh ta samu bacci ya dauketa.

Haifa kuwa tunda sukayi maganar nan da hammam atsorace take kuma da zullumin mai zaije ya biyo baya, dukda ta yarda dashi dari bisa dari, da tunanin wannan bacci barawo ya kwashe ta. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by: QueenMarh👸🏼

Paid book 📚

62…

Washe gari kusan a tare duk suka iso cikin headquarters, amra kuwa kamar wadda aka yima mutuwa, rama ta fara fitowa a fuskarta saboda damuwa,yau ma basu da wani aiki sosai don duk an salami officer din da aka yi admitting wanda basu da lafiya.

Jawota haifa tayi suka wuce masjid domin yin sallah, bayan sun idar gefen sakon hadadden masjid din suka zauna, ganin babu mutane da yawa acikin masjid din yasa haifa ta kalleta tace ''amra, I think matsalarmu ya kusa zuwa karshe,''…kallonta amra tayi da mamaki karara a fuskarta tace ''haifa, ta ina kike tunanin matsalar tazo karshe,kin dai ji mai matar nan ta fada ko''…hannunta haifa ta kamo gam sannan tace ''ki tsaya ki saurareni amra, jiya mun hadu da hammam shi ya maidani gida sbd motor na ya mutu''..nan ta kwashe duk yanda sukayi da hamman ta fada mata, hankali tashe amra tace ''hammam kika fada ma abinda suke yaqen yinshi akai?, kinason mu shiga matsala ne,?" da kyar haifa ta lallaba ta akan su jira suji mai zai ce masu.

Bude office dinshi da akayi kai tsaye ya sa bai dago kanshi ba ya cigaba da typing a system din gaban shi don yasan babu mai yin hakan sai hammam, zama hammam yayi a kujeran guest ya fuskanceshi da kyau sannan yace ''dude duk ka fara ramewa wallahi, hope dai ba damuwan nan ne kasa aranka ba'',..bai dago ya kalleshi ba yace ''uhm''..sanin halinshi sarai idan miskilancin ya tashi ya sa hammam cewa ''na samo mana solution but bansan yanda zaka dauki abinba, but ina tabbatar maka da idan baka amshi wannan ba to fa bansan kuma ta wani hanyan zan iya taimaka maka ba don wannan ce kadai mafita''….duk wannan bayanin da hammam yake bai dago ya kalleshi ba yace ''okay so whats the solution you're talking about?...jin haka yasa hammam gyara zama yace ''na samu yarinya da ta dace, sannan kuma tana da duk wani abubuwa da kake buqata, I mean all you listed last time kan maganar culture,''…sai alokacin ya dago ya kalli hammam sannan yace ''okay so?''…jin haka yasa hammam saurin cewa ''but itama tana da nata sharadin, zata amince da duk wata buqatarka da sharadin ka, but itama nata yana da tsauri sosai don tana buqatar katin kasa ta karkashin ka''….jin haka yasa amar ture system din gabanshi ya fuskance shi da kyau yace ''hammam are you insane?, shin kasan mai kake fada kuwa, ni amatsayi na, na wanda idan yaga za ayi haka zaiyi purnishing, ni kake cewa nayi hakan, shin ka manta muqamin da nake dashi yanxu da yanda nake da enemies gaba da baya eh?, kana son na auri yarinya donta samu katin kasa wanda kasan illegal ne idan har babu soyayya mai qarfi eh?......girgiza kai hammam yayi sannan yace ''nasan duk da wannan basai ka fada min ba, kuma da sanin haka nazo wajen ka domin na shaida maka, yanxu kai amar har kana tunanin mai zai biyo baya?, bazaka tsaya ka fara tunanin mafita ba akan matsalarka wadda idan harka rasa komai shikenannnnn''….yana kaiwa nan cikin fushi ya furzar da nunfashi ya cigaba ''amar are you sure you're okay?, ospermia ake fada maa fa, wannan ba abinda za kayi jayayya da solution din abin bane, lokacin guda ya kamata ka amince kawai, idan kuma ba zaka yardaba ni zan cire hannuna cikin lamarin nan'', yana kaiwa nan ya miqe zai fuce, da sauri amar ya tsaidashi ''hold on dude, haba idan kace zakayi fushi ka cire hannunka bansan ya zanyi''..yana kaiwa nan ya dafe kanshi ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce..''okay naji na amince da zabinka, but ni kasan bana kasada, zanyi dogon bincike akan koma wacece ita, from her parents to the people she's mingling with, daga nan if I'm satisfied na amince''..jin haka yasa hammam cewa ''kama amince kawai, duk wani bincike da zakayi ya biyo baya, kai ko tunanin baka da time din wannan bakayi ba,yanxu zan sanar da ita maganar, then saimu san me zamuyi next''..yana kaiwa nan ya fuce fuu don a shake yake da amaar yana nema mashi sauki shi kuma yana faman cijewa kawai don wani banzan ego da yanxu ya kamata ya saukeshi don yayi abinda ya dace don ya taimaki kanshi amma ya kafe akan abu daya''..direct asibiti ya wuce sannan yayi booking appointment yasa a turo mashi haifa office dinshi.

Amar kuwa tun fitar hammam ya tsaya yana nazari sosai, yanxu idan ya amince da wannan shawarar hammam din is so risky, a matsayinshi na general zai iya shafan career dinshi, and on another hand kuma idan har ya bari wannan damar ta wuceshi, to fa zaiyi dana sani ne na har abada, don komai dagule mashi yakeyi sosai, karshe dai ya yanke shawarar zai amince amma abinda yafi zama so important shine dole ne fah saiyayi bincike akan koma wacece don bazaiyi tarayya da macen da baisan usulinta ba da tushen ta.

Bayan yan mintuna qalilina aka aika ma haifa kira, domin zuwa ganin hammam, jin haka yasa amra cewa zata bita, atare suka wuce har cikin headquarters zuwa office dinshi, suna zuwa daidai kofar office dinshi sukayi knocking, office ne mai kyau daidai senior officer amma kwata kwata bai kamo office din amar a haduwa da komai ba, jin an basu izinin shiga yasa suka saka kai, yana zaune ah seat din baki, ganin haifa da amra yasa shi saurin cewa ''come have a seat''..atare suka karaso suka zauna suka gaishesa professionally don office nee, ganin haka yace ''drop the formalities girls''..gyara zama haifa tayi kamar wadda take jiran haka tace ''habibi, yanxu ya ake ciki, ka barni cikin zullumi nida amra don tun dazu na fada mata komai,''..murmushi yayi wanda ya bayyanar da fararen hakwaranshi yace ''Alhamdulillah, kamar yanda na fada maki haifa, na samu solution wanda kuma zakuyi benefiting harta samu katin qasa, saidai kuma shima wanda zai aureta din yana da nashi sharadin, wanda ba yanxu zamu sanar daku ba saidaga baya, its just simply yarjejeniya ce, kowa zai amfanu da juna, ke zaki samu katin kasa shi kuma zai samu shima abinda yake buqata wanda nasan bazaku qi amincewa ba''….jin haka yasa haifa saurin cewa ''habibi mun amince, I mean ta amince, saidai kuma yanxu abin ji shine yanda abin zamu tafiyar dashi,akwai matar da ta fada mana duk yanda abubuwan suke tafiya, dukda yanxu ta daina wannan harkar amma ganin halin da amra ke ciki yasa tace zatayi kokarin nuna mana process din komai dan bin yazo da sauqi''…jin haka hammam yasan wa take nufi, don an taba kamasu har aka kullesu daga baya aka sakesu suka fara ayyukan da zai taimake su da iyalan su.

Anatse yace ''okay yanxu abinda za ayi kuyi mana fixing date don muje mu sameta, saita mana bayanin duk wani abunda ya kamata ayi da process din kafin akai ga auren nasu, sannan ke amra inason ki rubuta min duk wani abu da ya kamata mu sani game dake, just forward it to haifa then ke kuma haifa saiki tura min.''..jin haka yasa haifa cewa ''right away habibi'' cikin murna suka fito daga office dinshi wanda amra tunda taji ance itama ana buqatar abu daga wajenta hankali tashe ta shiga zulumi, ganin wannan yanxu ba shine matsalarta ba yasa tayi saurin cewa ''haifa baki tambayeshi wanene ba?''..juyawa sukayi suka koma, abakin kofa suka tsaya haifa tace ''habibi baka fada min wanene ba,kasan sha'anin rayuwa..katseta yayi da cewa ''habibty karki damu, indai kinyi trusting dina, and karku damu zanyi fixing date don ku samu ku gana da shi, anan zaku san koma wanene''..jin haka yasa suka fito, kowannen zuciyarshi qunshe da zullumin ko wanene wannan ya amince.

Suna komawa office suka kira matar, bayan sun gaisa suka shaida mata sun samu wanda zai yarda ayi auren, murna tayi masu sannan tace suyi fixing time cikin weekend don bata aiki da weekend saisu hadu ayi Magana, don tunda ta hadu dasu taji sun kwanta mata arai musamman amra kuma tayi alkawarin saita taimaketa don ta samu abin da take buqata don ta taimaki yan uwanta.

Rayuwa Kenan, babu abinda bazakayi ba idan har ya shafi jinin ka, ga dai amra bata tunanin ko wannan abun zaisa rayuwarta ta lalace, babu abinda take hange sai qannenta kawai, Allah ka bamu masu yi mana irin wannan so.Ameen ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by: QueenMarh👸🏼

Paid book 📚 63-64

Bayan amra ta tura ma haifa duk wani bayani akanta, da gidan su dake Nigeria da duk wani na jikinta sannan itakuma haifa tayi ma hammam forwarding, shiko bai ma tsaya ya karanta ba ya turama amar, lokacin da message din ya shugo wayanshi, baima tsaya ya karanta ba ya kira m-5 akan ya samu special private investigator yayi mashi dogon research akan ta da iyayenta da duk wani danginta duk ya dubo mashi komai akanta.

Ranar Friday haifa na waya da hammam ta shaida mashi sun yanke haduwa da matar washe gari Saturday a wani private loung by 2pm, sun dade suna waya kafin sukayi sallama.

Hankali atashe amra ta tashi washe gari, zuluumi ya cikata na son ganin shin waye ya amince zai aure daga cikin army officers din, don itadai batajin akwai wanda doguwar Magana ta hadashi da ita, haka dai wunin ranar tayi sukuku babu kuzari, ganin tunanin babu abinda zai tsinana mata yasa tayi saurin wucewa toilet don yin wanka, ta dauka wajen minti ashirin kafin ta fito daure da towel wanda ya sakko har santala santalan gwiwanta dake sheki, wani sanyin qamshi jikinta ke fitarwa sbd shower gels din da tayi amfani dasu wajen yin wakan masu sanyin kamshi, jikin ta sulup kamar wadda tayi dilke babu digon gashi ko kadan akowane lungu da sako na jikin ta, anatse ta kara sa gaban dreeser ta feshe ko ina najikinta da turare da oils masu dadi, kallon kanta tayi tundaga gashinta dake nan har ya sauka kafadarta ya yi curly ya nannade, zuwa ga kirjinta dake nan tsam a mike kamar ta saka bra cup zuwa ga tudun hips dinta wanda towel din bai hanashi bayyana ba, kallon fuskarta tayi da kyau, babu abinda ya ragu ajikinta sai fuskarta da rama tadan fito mata, anatse ta shafa fuskarta sannan tace ''you can do this amra, Allah yana tare dake''..karar wayanta ne ya fargar da ita sannan tayi maza ta zura abayar da ta fito da ita, batama taba sawaba, gudun karsuyi mata kadan bata sawa yasa ta zaro ta, farar abyace kal, wanda tasha duwatsu masu kyalli kamar diamond suma farare tarr, ahankali ta jawo farar bra dinta da pant dinta ta saka anatse, saida ta saka rigar ta gane cewa ba karamin taimakon kanta tai ba ta dauko rigan don ya matseta sosai, ya manne da fatar jikinta, ganin kayan is too exposing yasa ta wuce wardrobe domin sauyawa, ringing da wayanta keyi ne yasa tayi saurin aje kayan da take zarowa ta wuce gaban wayan data aje kan gado, da sauri tayi picking don ya kusa katsewa, da sauri ta kara kunnenta, jin muryar haifa wadda ke cewa ''babe ki sakko mana na karaso, munyi latti fa sosai, bacci ne ya daukeni wallahi har naso na Makara, ki sakko kawai yanxu yanxun nan,''..jin haka yasa ta jawo jakanta ta maqala a hannunta sannan ta zaro flat shoes din ta suma farare kal sannan ta sa kai ta fuce bayan ta kulle kofar, tama manta da chanza rigar da taso tayi, …anatse ta karaso har gaban moton haifa, budewa tayi sannan ta shiga haifa ta jasu zuwa private loung din, tafiyan minti ashirin sukayi suka iso, tunda shuka shigo compound din gaban amra ya dunga faduwa, ahankali ta dunga karanto adduoi don she's so nervous, hannunta haifa ta jawo suka wuce ciki tana ce mata ''calm down babe, don't be nervous kinji, just put your trust in Allah komai zaizo mana da sauki,'' jin haka yasa amra dan daidaita natsuwarta sannan suka shiga ciki, wurin is so peaceful babu hayaniya kwata kwata, don wajen kamar bangare bangare ne, dukda da mutane amma ba ajin maganganun mutane saidai yan sautika kadan kadan,wajen da sukayi reserving suka shige suka zauna, nan aka kawo masu starter na chai tea mai kamshin dadi, suna nan zaune wajen minti biyar kafin suji sallamar matar, atsanake ta zauna suka gaisa cikin mutunci kafin itama a kawo nata chai din, tataunawa suka dan fara yi kafin su hammam su karaso.

Hammam ko yama manta bai sanar da amar ba da wuri, hakan yasa yayi saurin wucewa gidanshi, direct sama ya wuce cikin dakin amar, lokacin yana kwance yana bacci hankali kwance, har gaban gadon hammam ya karaso sannan yace'' kai gayen nan dan iska ne, baccinshi ma yake hankali kwance da karfe daya na rana, jin an yaye duvet dinshi ya sashi saurin bude idonshi da bacci bai gama bari ba yace ''what the hell is this hammam,''…hammam baiko tanka mashi ba yace ''get ready we're going out, yau zaka ga bride dinka''..jin haka yasa amar doka tsaki yace ''get out please zan kimtsa''..jin haka yasa hammam mikewa ya wuce wajen kofa yace ''nasan halinka yanxu saika kai wajen awa kana wanka kamar kifi, dan allah karka bata mana lokaci''..yana kaiwa nan ya fucewarshi zuwa qasa don ya jirashi ya kimtsa..ganin ya fuce yasa ya yaye sauran duvet din dake jikinshi, ya sakko da kafanshi ya sanya bathroom sleepers ya miqe tsaye, babu komi jikinshi sai wani dan mininin shorts wanda ya zaune mashi dam kamar pant na maza, kirar jikin shi ta futo sosai kamar giant, miqa yayi wadda ta fidda duk wani karfafan gabbanshi da jijiyoyin su, anatse ya wuce bathroom, wanka yayi na kusan 30mins kafin ya futo ya wuce closet room, ahankali ya zaro riga da wandonshi marasa nauyi kollon black, da shorts farare da inner vest, ahankali yake abubuwan shi kamar mace, kamar kullum yauma saida ya yi ruwan turare kafin ya sanya kayan, kayan sunyi mashi masifar kyau, ko ina zamzam, saida ya gyara sajen fuskarshi wanda ta cika sosai don bai saisaye ba a kwanakin, sai sheki suke yi baki sidikkk, ahankali ya futo bayan ya saka wani tsadadden loafters dinshi shima baki sannan ya bude glasses drawers dinshi, ahankali ya zaro wani hadadden bakin glass ya aje shi gefe sannan ya shimfida sallaya ya gabatar da sallar dhuhur saida ya idar sannan ya miqe ya dauko glasses din ya sanya a idanunshi, wayoyinshi ya jawo ya sanya a aljihunshi ya fara fitowa Har ya saukko kasa, duk wannan shirin da yayi ya dauka wajen awa daya yana yi, hammam na ganinshi ya soma cewa ''shege, wannan wankan duk saboda zakaga bride din naka ne''..amar ko baima kalleshi baya wuce hanyar fita da sauri hammam ya buyoshi sannan suka wuce a motor hamman.

Wuraren karfe uku suka isa cikin private loung din, anatse suka fito atare, gyara zaman glasses dinshi yayi sannan ya zura hannunshi daya cikin aljihun wandonshi, dayan kuma ya rike wayansa, yana dannawa,..tafiya suka soma yi har suka shiga cikin loung din, sanin inda akayi reserving yasa hamman tunkarar wurin direct shi kuma amar biye dashi abaya, anatse hammam yayi sallama, wanda haifa ne kawai ta iya amsa wa tana dagowa domin ganin waye na bayan hamman din, anatse suka kutsa kai suka zauna akan carpet din loung din, amar wanda tunda suka shigo bai ko bi ta kan kowa ba hankalinshi nakan waya. Itako haifa suman zaune tayi ba ita kadai bama harda matar dake tare dasu, amra kuwa bata san me ake ciki ba don gyagyadi ta soma, inda ta dan dafe da jinkin bangon wajen, ahankali wani sanyayan kamshi ya fara shiga cikin hancin, da kyar ta fara bude idanun ta suka sauka kan wanda ko a mafarki bata tsammanin zata taba hada wurin zama daya dashi ba, bude baki tayi galala kamar wadda ke shirin Magana, shiko oga baimasan tana yi ba, yadai san inda ya zauna yana fuskantar mutun,..haifa ce ta tattaro nata natsuwan sannan tace ''greetings to general sir''.. baiko dago ba bare ta saka rai ya amsa, ita ko amra ta kasa cewa komi ma, kallon da tayi mashi da farko ta kawar dakai bata kuma gigin yin wani ba.

Cikin tsoro matar ta gaishesu don sarai ta son su kuma tasan muqamin su,amma batayi tsammanin sune wanda suka amince da wannan abin ba, haka yasa ta kame kanta don kartayi laifi.

Hammam ne yayi gyaran murya sannan ya soma Magana ''wannan abokina ne kuma ogana amar, wanda duk nasan kun sanshi, general amar,shine wanda zakuyi yarjejeni''..ya nuna amra wadda a tsure take hankali tashe, sannan ya cigaba, "kamar yanda na fada maku last time shima yana da nashi buqatun, kamar yanda ke amra kike buqatan katin kasa wanda zai taimaka maki ki samu kema kuma zaki taimaka masa."……..

Jin abinda hammam ya fadi yasa yayi saurin dagowa don kallon hammam din, wai zata taimaka mashi, shi sam word din da yayi using bai mashi ba, akasin hakan yasa idonshi bai kaiga zuwa kan na hammam ba ya sauka akan ta, zaro ido yayi sannan yace ''who's she?'' da sauri ta dago kai ta kalleshi, ganin yanda idonshi ya cikata da kwarjini yasa tayi saurin saukewa, shiko kallonta ya tsaya yi na wajen minti goma kafin ya kalli hammam yace ''I'm asking who's she''..don harga Allah yana jin kamar ya taba ganin fuskar tata, amma ganin gwara ya samu tabbacin ita dince yasa ya sake tambayan..''she's amra, she works in headquarters with haifa, she's the lady that took your sample the other day''..jin hakan yasa ya tabbatar da ita dince din dai, wannan mai rawar kan ayanda ya maqala mata Kenan,..ganin yanda amar ya sauya lokaci guda ya sanya hammam cewa ''mrs lily can you start your job now''… anatse matar ta soma cewa ''okay sir..sannna ta zaro wata doguwar paper daga cikin jakanta sannan ta soma bayani ..''na farko dai duk yanda nayi tunanin abin zaizo da sauqi sakamakon yanda kuke da mukami babba abin zaiyi wuya, na farko dai dole kunsan marriage consent group saisun yi research akanku domin dukkan ku bayan kasarnan bane, but tunda oganku soja ne babba anan kasar wadda government ta bashi katin kasa dalilin haka, amma ita sanin itama yar kasar da yake ce dole saisunyi bincike sosai wanda ina tunanin hakan zaizo da sauqi idan har sukayi pretending suna son junan su sosai, na biyu kuma auren ne, dole yanda addini ya tanadar haka za ayi shi don auren sunna ne tunda ku musulmai ne kuma dole saida waliyy dinta wanda ku zaku nema wanda kuka yarda dashi don yayi hakan kuma ya rufa maku asiri, don for sure marriage consent group saisun buqaci wasu bayanai daga wajenshi harma binciken sirri saisunyi, na uku kamar yanda kuka sani bayan aure saikun dauka wata biyar atare kuma gida daya don marriage consent group suna yin zuwan bazata don ganin yanda zaman takewanku yake, na hudu dole saikunbi duk wani rules dana rubuta acikin paper dinnan kafin akaiga filing form din application na katin kasa, don ana daura aure za ah baku papers na application for her sbd shi… ta nuna amar, ..sbd shi aikinsa ya bashi katin kasa. Tana kaiwa nan ta miqa masu papers din, kowa ya karba banda amar wanda zuciyar shi ke tururi, haka kawai, don shi wannan abin kamar kaskantar da kanshi yake.

Idan kun shirya komai na maganar auren sai kuyi fixing date, most preferably Friday, don kamar yanda na rubuta cikin list din dole saiya zamana kansu a hade yake, don za ayi masu tambayoyi sosai idan marriage consent group sunzo game da kansu, kamar ita za a tambaye ta akanshi, idan har tayi kuskuren rashin amsa koda kuwa abincin da yafi so ne to fa zai jawo matsala babba. Matar na kaiwa nan tayi masu sallama akan idan sun yanke shawara saisu kirata don ta fara planning yanda zata hardada masu eveidence na cewa sun dade suna soyayya. Kallon haifa hammam yayi sannan shima ya zaro wata paper daga aljihunshi sanna ya mika mata da pen yace ''let her sign the contract''…miqa mata haifa tayi, ta dauka wajen minti biyar tana juya paper hankalinta baya kan rubutun ma, da kyar tayi signing hannunta na kakkarwa, tana gamawa ta miqa masu tayi excusing kanta zuwa restroom. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by: QueenMarh👸🏼

Paid book 📚 65-66

Kallon haifa hammam yayi sannan yace, I can be his walyy because I'm his only best friend, so about her I don't knw what to do, and its risky to hire someone,''…kallonshi haifa tayi sannan tace "habibi I have a solution to that, I've told abuuh about everything so I'm sure he will help us out insha ALLAH..jinjina kai yayi, suna nan zaune amar ya miqe abinshi ya wuce motor don yanxu kam sai yanda hammam yayi kawai, donshi bayajin zai iya yin wannan abu haka, baya son stress kwata kwata, bayan wannan ma yama za ayi ya hada kwanciyar aure da wannan qanqanuwar yarinyar salon ta raina shi, don kallon yar shekara 15 yake mata gaba dayanta.

Motor haifa suka shiga itada amra wadda zata fara sauke amra kafin ta wuce gida, tunda suka shiga cikin motor babu wanda yace qala tsakaninsu, ganin shurun yayi yawa yasa haifa cewa ''babe, naga tunda su hammam suka zo shida general baki ce komi ba, nasan hankalinki ya tashi game da duk wannan yarjejeniya, but babe ya zamuyi, wannan ce kawai solution, idan kinga bazaki iya ba kuma sai mu hakura a nema wata mafitar''…dago kanta tayi ta kalli haifa sannan tace ''haifa ni tsoronshi nake ji, kinajin dai yanda kowa ke fadin bashida kirki a office, ni tsoro nake ji.''…juyowa haifa tayi ta dan kalleta kafin ta maida idonta kan driving da take tace ''indai akan wannan ne amra, inason ki kwantar da hankalinki, all abinda ya kamata kiyi focusing akai yanxu shine yanda zaki samu ki karba katin kasa don ki taimaki qannenki, duk wani abu da zai biyo baya ki manta shi for now, just focus kinji babe''…jinjina kai amra tayi sannan tadan kwantar da kanta jikin window motar.

Hammam na sauke amar baima tsaya yabi ta kanshi ba don yasan idan har ya mashi Magana yanxu bazasu kare da sauki ba hakan yasa ya kira house boy din amar ya bashi papers din yarjejeniyar don ya kai mashi yayi wucewan shi gida ranshi fess, shiko goga yana wucewa cikin penthouse dinshi baima bi takan dinner ba ya wuce sama don ya samu ya watsa ruwa, koda ya fito jellabiya yasa sannan ya tada sallah, ya dade sosai akan sallaya yana rokon Allah akan abubuwa da dama kafin ya miqe ya wuce closet ya chanza kayansa zuwa na bacci, white pjs riga da wando wanda ya haska fatanshi sosai ya saka wannan yabi lafiyar gadonshi yah hau ya kwanta ya jawo duvet dinshi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull