Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 59

Auren katin kasa complete - Chapter 59

Auren katin kasa complete Chapter 59: Auren katin kasa complete Chapter 59. Bari mu Yan katsina…. Duniya ta juyama wannan family baya, yanxu taluacin da…

4,389 words

Bari mu Yan katsina…. Duniya ta juyama wannan family baya, yanxu taluacin da suke ciki haryaci uwar na da saboda da khady kawai suka dogara da take saida gwanjo itama ribar yanxu tayi kasa saboda hidiman gidan daya dawo hannunta dukda ba wani kudin arziki take fiddawa ba idan zasuyi cefane kullum, dari biyar ce safe da dare don ba a cin abuncin rana a gidan, dady kuwa tun bayan wannan targade da yayi har kayi mashi gyara a hannu da kafa, inda a hannunshi samu karaya while kafar kuwa ya samu targade, Toh da dai gyaran karayan nan baiyi ba kafarcema ya dan samu sauqi saidai hannun ne ya shanye gaba daya baya wani amfanuwa, sai kuma jan ruwa da yakeyi saboda inda ya ciwo wajen hannun ba a yi dressing ba haka gudaje da bad environment din wajen yayi affecting hannun, nan ya dunga Jan ruwa sai wani karshe dai hannun shanyewa tayi babu wani amfani. Haka kullum zai zauna a gida baya uban komai, tun kareema na jin tsoro shi lokacin daya gano tana da cikin shege har tazo ta daina tsoronsa take gasa mashi aya a hannu, zagi cin mutunci babu wanda basa yima juna agaban yayansu, yaranma Har sun saba da yanda iyayensu keyi ma junansu, ah anguwa kuwa babu wanda baisan kareema matar mustapha mai damfara nada cikin shege ba, tayi cikin shege da aurenta, wannan zance yasa ko fita bata iyayi yaranma idan sun futa da irin zagin da ake jifansu dashi kenan, khady dai ta gama zama yar tasha idan ma an fada bata wani damuwa don Har cewa take "Toh saime idan tayi cikin shegen idan uwar wani ce Tayi ku fada min badai tawa uwar bace to munji tayi ciki" Yanda ta zama yar daba daba yasa wasu idan sunso goga mata magana suke kyale ta saboda kangararren saurayin ta.

Bangaren wahab yana chan a kurkuku don asad saida ya tabbatar an yanke mashi hukunci daidai da abunda yayi, nan aka kaishi prison na shekara goma,don Akwai diyyar daya kamata ya biya wanda yayi ma yarinyar maqocinshi na chan lagos fyade inda aka tuntubi iyayenshi ko zasu iya biya don in ba a biya ba shekarun da zaiyi a prison zai karu, nan aka tuntubi Alhaji mustapha, lokacin da suka kirashi ma yana gida a zaune babu uban abunda yake sai zaman banza don haka da sukayi mashi bayani nan take yace "ku rufeshi kawai babu abunda zaku samu a waje na" Yana kaiwa nan ya kashe wayar baima tsaya sauraron su ba, da kareema ta tambayi ko da wa yake waya kai tsaye ya mata bayani, nan take ta dunga kuka tana tsine daddy kan Duk shine ya janyo masu wannan masifa Har yayanta suka wulaqanta gaba daya saboda zalumcin shi da cin amanar dan uwansa da yayi na wulaqanta yayansa. Nan suka dunga Sarfa ma junan su zagi ta uwa ta uba "kije kiji da shegen ciki wahallaiya asararriyar mata Wallahi nayi dana sanin aurenki kareema kina da kaso mai girma a cikin lalata rayuwata kece ma baqar kafar data lalata kin komai, badan kin sa an zubar da waennan yarannan ba da tuni na samu wani abun a wajen yayarsu" Kallonshi karima tayi tana takaici ace Wai mutun baiyi nadama ba ko kadan, "shiyasa zaka kare a haka a wulaqance, Har yanxu zuciyarka a mace take" Nan suka cigaba da cece kucensu dagashi Har ita aka rasa wanda zai jaa baki yayi shuru maqota na jin su.

Bangaren Muhammad kuwa yana chan Australia, yau watanshi biyar kenan, acahn yaqi dawowa don daddy's ya kirashi ya shaida mashi uwarshi tayi cikin shege don haka ya tura masu da kudi, ranar da yaji wannan baqin labari ya shiga tashin hankali sosai inda ya ko sun kirashi ma kasa daukan wayan yakeyi don yana Allah wadai da iyaye nashi, wannan yasa yaqi dawowa yayi zamansa acahn ya maida hankali wajen aikin shi inda yake taimakawa kaninshi ishaq daya dage yana masters dinshi anan Australia don bayan ya gama karatu ya dawo wajen Muhammad nan ya muyi sponsoring dinshi ya samu schorlaship nan ya fara masters.

Bangaren kakarsu salima kuwa, rana daya Allah ya dauki ranta anan kauye inda take zaune wajen dan uwanta, tayi jinya sosai inda suka dunga bata maganin gargajiya da farko kamar komai ya lafa sai daga baya kuma gadan gadan ciwon nata ya dawo Har Allah ya dauki ranta bata samu damar Ganin marayun jikokinta ba.

Bangaren labaran shima bayan noma haka ya samu yayi renting wani kanti nan kusa da inda yake yake haya, nan yayi amfani da kudin da ammah ta bashi ya zuba provision a cikin shagon don bashi da wani girma sosai, cikin wata biyu wajen ya bun kasa don haka ya hade da shagon dake kusa dan wanda yake haka, cikin ikon Allah Allah ya by kasa mashi, don Allah ya bashi wannan baiwar da zarar ya saka hannu akan abu sai Allah ya bukata mashi, kullum kuwa saiyayi mafarkin yarannan guda uku ada chan baya yana mafarkinsu baya Ganin fuskokoinsu saidai shadow dinsu kuma yana jin saurin kukansu Yanxu kuwa yakan iya ganin su a fili saidai Har yau baiga fuskokinsu ba saidai yaji su suna dariya. Bayan wannan Har yanxu zane kam yana. Yin shi, don idan ya dauka alakali yana Zane kamar wani pro nan ya gane cewa yayi ilimi don saida ilimi zaka iya zane irin wannan da ake kira da architecture. Abunda yafi daga mashi hankali kuwa shine Akwai ranar da yazo tsallaka titi bayan ya dawo daga shago, nan take wata mota taso bugeshi Allah ya rufa asiri mutumin ya Taka burki nan take flashback din wani mummunan accident yazo mashi, inda anan ya gane lokacin da yayi accident ne kenan, everything was dark don haka bai gane komai ba.

Alhaji kabiru dai Ana chan prison shima an kaishi gidan yari inda zai gama rayuwar shi acahn gaba daya, irin dukan dasu asad sukayi mashi yasa yayi loosing site dinshi daya, ya rame ya jeme ya zama kamar wani mai kanjamau, talking of kanjamau lokacin da yayi wata irin rashin lafiya anan prison aka kaishi asibiti nan akayi mashi test take kuwa aka gano yana da hiv. Haka aka sallamoshi bayan ya danji sauqi aka maidashi prison aka rufe shi, Har lokacin he can't imagine rayuwarshi zata juya ta zama haka ba, ya zama kaskantacce, ya lalace kuma naka sasshe bashida kowa bashida komai, dukiyar daya tara ta hanyar haramci bata amfaneshi da komai ba saima jefa shi cikin mawuyacin hali datayi. Aman Duk wata yana zuwa nan prison yana dubashi, wani sa'in yakan futo ya ganshi wani sa'in kuwa haka zai Karaci zamanshi daddy yaqi futowa don yanxu blaming dinshi yake yi akan cewa ya cuceshi yana matsayin ubanshi ya fallasa asirin sa.

Su lantaana da doctor ma ana chan ana serving a gidan yari, kowannensu an bashi shekara biyar for attempting murder.

Abuja Nigeria…… After 2 months… Yau wata biyu kenan da tafiyar Amar, Har ranar dai shuru babu labarinshi, at this point hankalin ammah ya gama Tashi don haka ta fara neman manyan mutane da ta sani acahn dubai en, shuru dai Har lokacin don haka ta fara tunanin zuwa dubai din saidai kuma tunawa da amra tayi nauyi yanxu yasa tayi cancelling tafiyar.

*** Ammah ce zaune a sitting room hannunta rike da charbi tana lazimi gefenta Salim ne dake ta faman yin game a wayar Salima don batama san ya dauko ba tana barci.

Ahankali ta soma saukowa tana dingisawa harta sauko daga stair tana nishi, amra ce sanye da doguwar rigar chan iska wadda ammah ta sayo mata su da yawa saboda ta dunga sakewa a cikin rigar, saurin nishin da takeyi ne yasa ammah ta kalli inda take tsaye bayan ta sauko kasan, murmushi kawai ammah takeyi harta karaso parlor, kallonta ammah tayi da yanda yake tafiya, cikinta ya futo sosai kamar mai wadda zata haihu yau ko gobe, daman doctor ya fada masu cewa da zarar takai wata takwas cikin nata zai bude, yanxu kuwa cikin nata yakai 8months da sati daya, cikin ya futo sosai kuma yayi mata kyau sosai, ta Kara fresh da kyau kamar bamai ciki ba babu wannan kumburu fuska da na hanci, dass dass abunta. "Wash barka da yamma ammah" ta karashe tana zama gefen kujera mai zaman mutun biyu "Sannu daughter kina kokari, wannan babyn namu tubarkallah" Dariya amra ta danyi kafin ta kalli inda Salim yake tace "kai kuma baka daddara ba ko, saita sauko ta mammake zaka daina daukan mata wannan wayar yar gold din" Dan murmusawa ammah tayi tana kallonsu. Salima ce ta sauko rai a bace Har tana grade kafafunta daga stairs, tana karasowa parlorn tayo kan salim, "kai Ka gama rainani ko? Toh Wallahi yau Saina koya maka hankali" Tana kaiwa nan tayo kanshi, ammah ne Tayi saurin hanata "haba yarinyar kirki, yi hkui bazai sake ba kinji" "Ki barta ta bugeshi ammah tunda baya ji, haka ya lalata min yawa Yanxu kwata kwata idan an kirani baba jin kara" amra ta fada tana kallonsu "Ah ah baza ayi haka ba daughter" karban wayar ammah tayi daga hannunshi kafin ta mikama salima "ungo yarinyar kirki yaci albarkaci na" Dungure kanshi salima tayi kafin ta karbi wayar, alokacin call din Aman ya shigo don haka ta wuce sama abunta tana murmushi. Kallonta amra tayi da yanda jikinta ya dau zumudin Kira harta wuce sama, shuru ta danyi don sai a lokacin amar ya fado mata, dukda tana kokarin hana zuciyarta tunanin shi saidai hakan ya gagara don yanxu idan babyn cikin ta ya danyi motsi shine yake fadi mata arai.

Suna nan zaune wayar ammah tayi vibrating, dan waigowa ammah tayi, kamar a mafarki idanunta ya sauka akan sunan Amar, cikin sauri ta dauka wayar Har hannunta na karkarwa yau wata biyu kenan rabonta dashi, "hello hello son is that you" Cikin jin dadi da murna Amar yace "yes ammah nine" "Subhanallah!! Son in Ka shiga Ka barmu cikin damuwa, wata biyu…" "So sorry ammah na shiyasa na kira ma yanxu, ko sauka bamuyi daga jirgi ba ayanxu haka maganar da nake dake" "Ya kake are you okay babu abunda ya sameka? Kana cikin koshin lafiy…" Saurin katseta yayi "I'm fine ammah, please don be worried I'm perfectly fine okay? Hope kuma kuna nan lafiya?" "Yes son we're fine alhamdullah yaushe zaka dawo? I have something very important to tell you" "I don't know ammah, saimunyi rounding up komai anan, but inason ki kwantar da hankalinki I'm perfectly fine, Muna gama operation Zan dawo Insha Al…." Dip wayar ta dauke, amra data gyara zama tana. Kallon ammah data sauke wayar, gaba daya ta maida hankalinta kan ammah haka zalika Salim shima yana daga gefe yana kallon ammah Duk sun zama curious suji ko lafiya, "Ammah lafiya dai ko?" Dan Nunfasawa ammah tayi tace "Alhamdulillah, son ne yace yana lafiya Har yanxu basu gama operation bane" Wata ijiyar zuciya amra ta saki Har yasa ammah ta juyota. "Har hankalina ya kwanta daughter, yau wata biyu da kenan, alhamdullah ya Allah" Sauke kanta kawai tayi kasa batace komai ba, saima wasa da Yan yatsunta data fara.

Washe gari wajen karfe biyu suka fito gaba dayansu, da yake weekends ne, sunyi kyau gaba dayansu daga kan amra zuwa salima sai ammah, Duk sunsha native kaya, atare suka fito gaba sayansu suka wuce motar ammah, ammah ne ke jan motar sai salima a bayan motar, Anatse ammah ke drinving while tana dan duban amra ta jikin mirror, hira suka dan farayi a tsakanin au inda amra dai saidai tace uhm ko ah ah saidai kuma in anyi abun dariya Harda ita ake kyakyatawa.

Gaban wani katon mall suka 360 mall, mall din ya gadu sosai don yana dauke da wani babban bulding mai tsayi sosai, atare suka fito gaba dayansu inda salima ta taimakawa amra ta bata helping hand saboda yanayin ta, ahankali suka shiga cikin mall, fadin irin kyau na wurin ma bata lokaci ne, babu wani hayaniyan mutane dan few mutane ke yawo, ko Ina fess fess sai kamshi, maintainance din wajen sai ba a magana saboda ko Ina clean, cikin lift suka shiga nan ma saida salima ta taimaka mata, suna hawa second floor suka wuce wani katon shop may suna baby shark, tundaga nesa zaka san shop din kayan babies ne, ammah ce agaba suna biye da ita Har suka shige cikin shop din, mutanen wajen ne sukayi welcoming din ammah kafin su fara zagaya wajen, Katon trolling ammah tasa salima ta janyo nan suka shiga shopping, abun da suka kwasa akalla zaikai wajen miliyan uku, ammah dai sage wa tayi babu abunda bata saya ba a wajen na Abubuwan da mummy and baby zasu magana dashi don suna da kaya designer don kamar ma kayan Duk na kasar waje ne, sun kwashi wajen awa biyu Ana abu daya, amra dai data gaji zama tayi nan mutanen wajen suka kawo mata ruwa da snacks, zamanta kuwa tayi taci snacks din tana cinye wa ta buqaci a kara mata nan ammah tasa su kawo mata da yawa.

Saida su salima da ammah suka gama kwashe kwashe su Duk wani cute kayan baby saida suka dauka Harda unisex babu wanda suka bari, Harda abubuwan da amra zata buqata wajen preparing delivery bag dinta, suna gamawa ammah tayi payment, lokacin da amra taji kudin saida ta kama baki, bazata iya musama ammah ba don haka taja Bakinta tayi shuru saidai bata kam taga abunda ake kira da gata.

Daga nan saida suka tsaya ammah ta saya masu kayan ciye ciye don itama tana son kayan dadi saidai diabetes dinta dake hanata cin wasu abubuwan, Sai wajen karfe biyar na yamma suka dawo gida da kaya niki niki, daki guda ammah ta fidda anan sama aka zuba kayan a dakin.

Washe gari Kayan da ammah tayi order daga dubai da uk suka iso, suka fadin irin yawan kayan da kudin da aka kashe akansu bata lokaci ne. Su Aman ne suka dunga shugowa dasu suna hawa dasu sama shida salim, suna hawowa dashi ammah tasa suka wuce dashi dakin data ware, daki ne babba sosai don Har yafi inda amra take, empty room ne saidai yasha frames, nan suka dunga zuba komai a ciki daga kan crop zuwa strollers da baby swings. Suna gama ajiyewa ammah ta shugo dakin tare da salima sai maida din gidan, nan suka fara shirya komai suna jerawa inda nan Aman shima yazo ya tayasu harhada crip da sauran abubuwan da dole sai anyi assembling, amra dai bata shugo dakin ba don kwana biyu tana dan fama da ciwon baya ga kumburin kafa da yake fama dashi.

After 1 week… A cikin sati daya ammah ta gama komai na sayayyan baby, babu abunda bata saya ba Har wanda bazasu buqata ayanxu bama Duk ta siya. Yau last appointment din amra before delivery don haka suka wuce asibiti, a cikin satitikan nan cikin amra girma yake kullum abun Har mamaki yake bama ammah, don cikin yayi girma sosai lokaci guda babu zato, Duk wasu kayanta yanxu basa shiga ta kwata kwata, sai doguwar riga mai bubu, wadda ammah ta karo mata su da yawa tana sakawa yanxu ma rigar ce a jikinta sai mayafin rigar, ahankali take sauko tana rike bayanta, tana saukowa ta dan tsaya tasa maid ta kawo mata ice water, tana nan tsaye ammah ta sauko kasan "sorry daughter na barki tsaye ko, muje" Suna sauka saiga salima ta taho da sauri itama daga sama, "Laa ammah shine zaku tafi babu ni, dan Allah Zan biku " "Toh muje" ammah ta fada tana wucewa gaba harta karasa gaban mota, tana karasawa ta bude gidan gaba kafin ta bude ma amra baya don ta daina zaman gaba, suna shigewa gaba dayansu suka bar cikin gidan.

Suna karasowa asibiti ammah tayi parking, fitowa sukayi gaba dayansu inda salima ke rike da hannun amra tana bata helping hand, anatse suke tafiya Har suka shiga cikin asibitin, suna zuwa kuwa time din appointment dinsu na cika cif. Basu tsaya komai ba suka wuce office din doctor.

Da sallama suka shiga cikin office din ammah ce a gaba sai amra dake biye da ita tare da salima. Zama sukayi gaba dayansu baya sun gaisa da doctor din. "Sannu madam ya nauyi? Hope baby is kicking" Doctor ya fada yana kallon amra Murmusawa kawai tayi batace komai ba, maida kallonshi yayi kan ammah yace "Bari mu fara scan ko? Saimug ko edd dinta yayi gaba ko ya dawo baya" Mikewa amra tayi ta wuce inda doctor kw dubata, hawa tayi kan gadon kafin ya soma dubata, yana gamawa yayi printing scan din.

Mikamaa ammah paper yayi kafin ya soma magana "alhamdullah hajiya, ta shiga wata Tara ciff and edd dinta yana nuna in the next 7 days baby will be ready to come to the world, yanxu form now ya kamata ta dage da exercise sosai zai taimaka mata sosai" "Alhamdullah I Alhamdulillah thank you doctor Ammah ta fada tana murmushi.

*** Suna fitowa daga office din doctor motar suka shige, suna shiga ammah ta kunna motar suka bar cikin asibitin, kowannen su fuskanshi dauke da murmushin jin dadi, musamman ammah, amra dai mamaki ma ya hanata tunanin komai, she can't believe itace zata haihu, allah mai ko kenan.

Suna isowa gida amra ta wuce daki saboda wani irin ciwon baya daya riketa sosai, yau kwana biyar kenan tana fama dashi yazo ya dawo haka yake mata, abunda yasa bata fada ma doctor ba kuwa shine normallly tana yin haka tun kafin cikin ta ya tsufa so yanxu daya fara mata hakan sai tayi tunanin it's normal.

Karfe Tara nayi ammah ta shugo dakinta da sallama, a zaune ta taddata tana rike bayanta, "daughter Yadai" Ammah ta fada tana zama gefenta don yanxu bata wuce minti talatin bata leko ta ba, "ba komai ammah, na gaji ne kawai da zaman" "Toh ki miek ki zagaya gidan zai saki Insha Allah" "Tohm ammah" Tana kaiwa nan ta mike ta nufi hanyar futa daga dakin, kasa ta sauka ta zagaye parlor kafin ta hau sama, tana haurowa ammah na fitowa daga dakinta, "daughter Ina zuwa, Ay kin gama kwanan dakinki yanxu, wuce muje part dina" Kanta a kasa tace "Toh ammah" Part din ammah suka wuce inda ammah ta bata gadon ta gaba daya tace ta kwanta abunta, kwanciya amra tayi har barci ya kwashe ta,

Mikewa ammah tayi ta luluba mata duvet kafin ta wuce bathroom ta dauro alwala don kusan karfe goma na dare, alwala ammah tayi tana dauro wa ta fito daga toilet din ta shimfida sallaya ta fuskanshi kibla, ta dade sosai tana addau Har barci ya kwashe anan zaune.

Karfe uku daidai kuwa Tayi saurin bude idanunta don jin wani abu daya taho mata daga mararta lokaci guda, da kyar ta zauna akan gadon tana cije lebe ta, Ta dade sosai a zaune tana danne abun da takeji, abun dai gaba gaba yakeyi don haka yana turnikota ta kwala uwar kara "innalillahi wayyo bayana" Cikin sauri ammah dake shirin sallame sallar daren da takeyi tana sallama ta mike cikin sauri ta karaso inda amra ke kwance, tana zuwa inda take taga ruwa na fita daga kasa ta don tayi sharkaf "subhanallah, daughter abun yazo gadan gadan" Cikin sauri amra ta dago ta kalli ammah "wayyo ammah bayana marana Zan mutu" "Shii babu abunda zai faru my dear Ina zuwa" Mikewa ammah tayi ta dauka wayarta kan dresser ta fara dialing number Aman. Aman dake barci karar wayarshi ta karade dakin, cikin sauri ya dauka wayar ya Kara a kunnenshi Ganin sunan ammah baima tsaya ya gama jin abunda take fada ba ya kashe wayar ya mike tsaye ya zari keys dinshi ya futo daga dakin, yana fitowa saiga ammah ta futo da amra, mayafin daga lulluba mata ma ya koma gefe, kasa suka sauko ahanakli inda amra ke kururu tana wayyo Zan mutu, babu abunda ammah keyi mata sai addua "Kai Aman zo riketa bari na dauko delivery bag" Da sauri ya karaso ya rike amra dake faman dafe ciki. Ammah na saukowa suka ta amshi amra kafin ya fuce ya fidda motarshi daga parking space.

Da taimakon Aman ammah ta saka amra a cikin motar, kusan karfe hudu kenan, suna shiga motar aman ya fushi mairam aguje suka bar compound din. Yanda yake mugun gudu yasa suka iso in few minutes, suna zuwa Aman ya wuce reception ya fada masu akwai emergency nan zauka fito a gado Har wajen mota aka fidda amra aka saka ta Har lokacin hannunta na cikin na ammah "wayyo ammah Zan mutu" kawo take fada "Bazaki mutu ba daughter, Allah ya sauke ki lafiya" Agaggauce aka shige da amra cikin delivery room inda ammah da Aman suka kasa sukuni hankali su a tashe, da kyar Aman yasamu ammah ta zauna ya dunga tausasa ta saboda ciwon zuciya ta.

Suna nan zaune Har wajen karfe biyar shuru, awa saya da rabi kenan, at that point hankalin ammah ya gama Tashi sosai, babu abunda yake sai rokon Allah ya kawo ka amra sauqi. Suna nan zaune saiga doctor ya fito tare da nurse fuskansu dauke da murmushi, mikewa ammah tayi tare da Aman sukayi saurin karasowa inda doctor yake, hannu ya miqa ma Aman don Duk a tunanin shi shine mijin amra, yana Mika mashi hannu yace "congratulations sir, ta haihu lafiya, the mummy and the babies are perfectly fine" Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke atare nan ammah tace "were she zamu iya ganinta?" "Yea zaku iya but kudan bamu minti goma a gama gyarasu, don Ana gyarata." Cikin zumudi ammah tace "Alhamdulillah alhamdullah, don ita ta amra ma take kawai don lokacin da take ce mata zata mutu ba karamin tashin hankali ta shiga ba. After like 10min saiga nurse ta fito "Ma zaku iya shugowa, mun kaita recovery ward" Nan nurse tayi masu jagora jikin ammah Har bari yakeyi tana son zuwa Ganin amra da abunda ta haifa don doctor bai fada masu ba. Nurse dince ta bude dakin ahanakli, tundaga nesa ammah ta hangota tana sanye cikin gown din marasa lafiya hannunta biyu rike da towels, nan take ammah ta soma hawaye Har tana neman faduwa kasa, nan Aman ya tallabota Har suka karaso dakin, ammah na karasowa tayi turus ta tsaya gaban gadon, gaba daya kafafunta Gaza daukanta sukayi nan take ta zube a kasa tayi sujjada tana dagowa ta daga hannu, it was a very emotional moment Aman ma kasa dauke idnaunshi yayi akan amra da babies dun dake gabanta ta rike guda biyu a hannunta sai guda daya akan gadon, dukda bak ga fuskansu ba but ya hango cute hannayen yaran farare tass, da sauri ammah ta mike ta karaso gabanta ta shafa fuska ta ta sumbace ta. Ammah na kuka amra na kukan murna, gaba dayansu aka rasa wanda zai taddashi wani "barakallah daughter Allah yayi maki albarka, Allah ya Raya mana su " abunda ammah ke fada kenan kafin ta saketa ta koma wajen babies din, takowa Aman yayi ya dauki wanda ke kwance akan gado while ammah ta rike daya amra ma ta rike daya, nan take ammah ta dunga jeroma yaran kisses tana hawayen farin ciki, suna cikin wann moment din saiga doctor ya shugo yana shugowa yayi congratulating dunsu tare da shaida masu gender na babies din, "hajiya daman kince kyautar Allah irin wannan ba a yi mashi shishigi, madam ta samu triplet 2 boys and a baby girl" "Allahu akbar" ammah tayi kabbara tana gamawa ta juyo ta kalli doctor "hajjin bana dakai za aje doctor" "Thank you so much ma thank you!!" Abund adoctor ke fada kenan, "anjima zamu sallameta Insha aallah, madam is brave, bamu taba tsammanin hakan ba," Godiya sosai ammah tayi mashi kafin ya fuce ya barsu suna kukan murna… Kallon babies sun Aman yayi yace "ammah naga suna kama dake" Dariya sukayi gaba dayansu inda ammah ta kalli babies sun for the countless times tace "gaba dayansu babu wanda yake kama dani, wannan ubansu suka dauko gaba Dayan su, kaga nan" ta fada tana nuna mashi wani dan mole din kumatunsu su duka don identical triplets ne, "kaga wannan mole din, irin na babansu ne sal hancinsu irin na mamansu skin dinsu irin na babansu, kai ni I'm jealous ma, gaba daya mazajen Nawa basu dauko mamansu da yawa ba" Dariya sukayi gaba dayansu daga ammah Har amra dake dan cije lebe don Har lokacin tana dan jin zafi a wajen donma basu yi mata stitches ba.

Nnamdi ezikiwe international airport abuja….. Karfe biyar daidai na asuba sukayi landing a international airport din abuja, Sir general Amar taura… Ahankali ya fara saukowa daga cikin jet dinshi Sanye yake da kakin sa na sojoji, yana saukowa ya shakur iskan Allah, garin yayi dan duhu don gari bai gama wayewa ba, ahankali yake tafiya majestically Duk da agajiye yake, cikin motar da aka tanadar masa anan airport ya shige nan driver ya jaa shi sai gida. Tunda yayi relaxing bayanshi a cikin motar ya lumshe idanunshi, as he promised ammah suna gama operation zai dawo gida, hakan kuwa ta kasan don suna gamawa baima koma uae ba ya taho airport ya shige jet dinshi. Ya rame sosai wanda dalilin harbinshi da akayi a kafada wajen operation din. Parking din da driver yayi ne yasa shi dawowa daga tunani daya tsunduma, bude idanunshi ya fara yi ahankli nan take gabanshi ya fadi babu dalili, ciwon dake cinshi a zuciya yana dannewa ya dawo sabo tunawa da yayi da ita, fadin irin kewarta da yayi cikin watannin nan bata lokaci ne, da ita yake kwana da ita yake Tashi kullum,

Driver ne ya bude mashi kofa don haka ya saqalo kafafunshi ya fito, yana fitowa yace "thanks" tare da wucewa cikin gidan don gari ya soma haske, yana karasawa wajen entrance baima tsaya knocking ba ya Danna pins ya bude kofar ya shige ciki, futilun kasan Duk a kashe suke don haka ya tabbatar mashi da basu Tashi ba, daman abunda yake so kenan shiyasa he wanted to surprise them, yana nan tsaye yana karema parlor kallon maid ta fito daga kitchen hannunta rike da mopper, tana karasowa inda yake dukda bata sanshi ba tace "good morning sir" "Morning" ya amsata kai tsaye kafun ya wuce bedroom dinshi, yana shiga ya watsar ruwa yayi salla yabi lafiyar gado.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull