Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 75

Auren katin kasa complete - Chapter 75

Auren katin kasa complete Chapter 75: Auren katin kasa complete Chapter 75. After like 30mins sai gashi ya futo sanye da farar riga mai gajeran hannu ta…

4,437 words

After like 30mins sai gashi ya futo sanye da farar riga mai gajeran hannu ta kamashi sai sai gajeran wando daya kai har wajen gwiwarshi, hannunshi rike da wayarshi while dayan hannun ya saka shi cikin aljihun wandon nashi, kafanshi sanye yake da wani sandals baki wanda ya fidda kyawawan yatsun kafafunshi dogaye, fuskanshi sai sheki yakeyi, he look so damn handsome, kamar ka sace shi ka gudu sai kamshi jikinsa ke fiddawa duk inda ya gifta, cikin kamewa yake tafiya harya bi hanyar stairs, walking majestically kamar basarake, fuskanshi a hade kamar koda yaushe, yana hawa sama hanyar dakinta ya wuce direct kai tsaye, yana zuwa daidai kofar nata ya sanya hannunshi kan handle din kofar ya bude, Yana budewa ta juyo arazane don harta zame towel dinta kasa tana shirin daukan doguwar rigar da zata saka, cikin saurin ta dago idanunta ta sauke akanshi, shima ita yake kallo tundaga kanta dake digar ruwa zuwa kafadarta dake sheki da sauran ruwa a jiki zuwa santatala cinyoyinta data saka wani blue lace pants, juya mashi baya tayi tana kare kirjinta ranta lokaci guda y abaci da wannan behavoiur nashi na shigowa dakin mutane babu sallama babu wani excuse kawai ya bude kofa, abunda yafi kular da ita shine yanda ya kafeta da idanu, dukda ta juya mashi ba she can feel yanda yake mata kallon kurulla, gashi babu komai a jikinta banda pant dinta, ita fatanta ma allah aysa baiyi noticing dan bumb dint aba daya fito sosai, rai abace ta jawo rigar tata ta zura abaibai kafin ta juyo ta fuskance shi, har lokacin ita yake kallo haka zalika bai rufe kofar dakin ba don yana tsaye a bakin kofar ya rike handle din kofar, ranshi a hade fuskanshi tam, dukda ya shiga wani yanayi daban ganin ta haka but bazaka taba tantance hakan ba saboda yanda fuskanshi keda wuyar fassara, ''dan allah ka dunga yin knocking in zaka shugo'' ''in naki fah?'' ya fada yana takowa inda yake bayan yayi banging kofar daya sa harta dan tsorata sosai. Takowa a soma yi ahankali har inda take tsaye dan nesa da ita har lokacin hannunshi na cikin aljihun shi, ''acikin gidana saina nema excuse kafun na shiga inda nake so? Uhmm'' Ranta e ya dan sosu da maganarshi don haka ta dago rai abace ta kalleshi ''koda kuwa a gidan naka ne, bai kamata ka shugo min haka nan ba ina saka kaya yanxu idanda tsirara nake fah?'' Kallonta yayi daga sama har kasa kafin yadan sauke wani lausassan murmushi kafin ya hade fuskan nashi, ''bakida right din fada min abunda ya kamata nayi, idan na ganki naked haramun ne?, niba mijinki bane?'' Wani irin kallo tayi mashi na kama raina min hankali kafun ta dan murmusa ''auu sai yanxu kasan ni matarka ce?, I tot kace baka buqata na a rayuwar why yanxu kuma,?' Rai a bace ya sake kallonta, ta kaishi bango sosai ita kanta dataga reaction dinshi bayan ta fada mashi hakn saida ta dan tsorata, ''anya kinje islamiyya kuwa? Let me remind you, nike da iko akanki aduk lokacin dana so, idan ina buqatarki dolenki ki mika kanki, haka zalika idan bana buqatarki baki isa kija da hakan ba,'' At this point jii tayi kamar ya chaka mata mashi a wuya, ranta ya gama baci sosai, ''niko naje islamiyya kuma ni nasan darajar mace wajen mijinta, ya muhammd bari kaji, nifa ba toy dinka bace ba da zaka dunga yi min abunda kaga dama koka fadamin abunda kaga dama, ayau idan harka buqaci rabuwa dani bazan hanaka ba but baka da right din forcing dina idan nace banayi, so ka daina cewa sai duk yanda kaga dama dani, waima tukunna inason ka fada min wani abu, what exactly do you want from me? Kace baka buqata na kace you don't accept me as a wife, what else do you want? Jikina kakeso? Indai shi kakeso yaya bazaka samu ba, saboda n agama kawo kaina inda kake, fom the moment kayi pushing dina to the wall na fita daga sabgoginka saboda ka nuna min baka buqatata kuma bazaka taba buqatata ba cikin rayuwar '' Rai abace ya damko hannunta ya juyashi bayanta ya bankarota gaba, ''washh Allah ka sakeni'' 'yanda yake huci yana turata baya idanunshi sun rufe sosai ya soma maganganu, ''idan jikin naki nake so so what are you not my wife,har yau bakisan who youre dealing with ba, baki jin kunyan fada min abunda kikaga dama, who d hell do you think you huh? Is it because kinga ammah ta tsaya mashi shiyasa you feel like saying duk abunda kikaga dama huh'' ''yaya ka sakeni zaka jimin ciwo,'' ''no bazan sakeki ba saina nuna maki inada iko dake, and I can toy with you to my satisfaction innaga dama, bakece zaki fadi yanda zanyi dake ba, you'll belong to me, only me idan naga dama,'' Hannunta daya da bai rike ba ta saka ta rike damtsen hannunshi daya rike dayan hannunta, idanunta na neman kawo ruwa ''yaya karkayi forcing dina, wallahi idan kayi haka youll regret it nan gaba, don wallahi bazan ya..'' Saurin toshe bakinta tayi jin ya turata kan gadon, gaba daya baya ji baya gani haka ya sanya hannu ya fisge rikarta ya keta rigar daga sama har kasa, kafin ya afka mata, babu irin struggling din da batayi ba akan ya saketa yaqi, saida yayi mata yaga yaga, kafin ya miqe soma sauke wandonshi daidai gwiwarshi, komawa yayi kanta, a lokacin duk ta gama galabaita, ga kuka ga gajiya daya soma tara mata, shes so weak at that point, don ko tsaya bata iya dagawa sai hawaye har lokacin bakinta bai rufe ba ''ka bari yaya,'' ''bazan bari ba, baki isa ke fada min abunda zanyi ba, saina koyama maki hankali na nuna maki nine namiji anan'' Yana kaiwa nan ya farke dan pants dinta ya dan rankwfo kadan baya ya sauke inner shorts dinshi, manhood dinshi tsaye tana haninya kamar maciji, tana gani ta runtse idanunta ta sallama mashi don tasan bazai fasa ba yanda yakai maquran nan, cikin ta ne ya soma murda mata lokaci guda gadan gadan, ''yaa ya ka bari dan allah'' Ta fada ahanakli bakinta na karkarwa, sakin boobs dinta da yake ma wani mugun matsa yayi ya dan dagata ya soma balle buttons din rigarshi, bai gama ballewa ba idanunshi ya sauka akan dan small bumbs dinta,tabbas ya dan fito kadan don yanda ya karanci jikinta aranshi zai iya zanata kuma yasanta da flat tummy sosai don shike fidda waist line dinta, bai komai aranshi ba don haka ya cigaba da abunda ya faro yana shafata daga samanta zuwa cibiyanta, dan jim yayi don alokacin ma saida ya danji mararta ta danyi tauri ta kasa kasa, gaba daya baya hayyacinshi don haka bai kawo komai bay a fara kokarin shigarta, manhood dinshi ya kama kafin ya kwanto jikinta ba tareda ya danneta bay akai bakinshi saitin kunnenta ya soma karanto addauar saduwa da iyali ahankali, yana gamawa ya daidaici hanyar shiga, ahankali ya soma kai manhood dinshi wajen, bamm yaji babu wata kofa don fatar a rufe take, kanshi ne ya dauka chargy sosai don koda yakai manhood dinshi wajen shes so wet, haka ya fara kokarin forcing kanshi ciki, tana ihu tana rokonshi baya jinta, saida ya sake komawa for the second time nan ma yaji shuru babu hanya, hankalinshi ne ya tashi don tsukewar data yi har tafi lokacin daya kusanceta, gashi yakai to the point that bazai iya hakura ba, kokarin daidaita natsuwar yayi yana kokarin kaiwa wajen ''wallahi azeem zaka kasheni, idan hark a sake kokarin shiga zaka kashemu, bakada imani ne?,'' Dagowa yayi don kalamanta sun dakeshi sosai har cikin zuciyarshi, saida ya dago yaga yanda ta galabaice ga gumi daya shafe fuskanta gaba daya, kuka take sosai harda majina idanu ta a rufe, saida taji ya tsaya ta bude idanun nata, koda ya kalli cikin idanunta saida yaga yanda yayi jaa sosai kamar agwashi, ''menayi maka meysa ka tsaneni?da kake kokarin forcing kanka a jikina,wallahi yaya bazan taba yafe maka ba idan kayi sanadiyar abunda ke tattare dani, ban taba tsammanin zaka gwada min how merciless you are ba sai yanxu'' Jikinshi ne yayi sanyi don sai a lokacin ya lura da abunda yaso yi, wanda bait aba tunanin zaiyi hakan ba a gareta dukda ita halas dinshi ce, bashida burin forcing kanshi a jikinta, ayanxun ma baisan mey ya hau kanshi ba,fushin da yayi yasa ya kasa controlling zuciyanshi, saurin mikewa yayi daga kanta jikia mace ya soma maida wandonhi, yana gamawa ya yi unbuttoning rigarshi, baima gama saka rigar ba ya kalleta ''the next time kika sake yin abunda kikayi yau bazan daga maki kafa ba,and it will be worst than this'' Ya karashe yana juya mata baya yana runtse idanu, he can't belive abunda ya fada mata bayan kuskuren dayaso tafkawa, wani irin haushi da takaicin kanshi yake ji,azafafe ya nufi hanyar kofar ya bude, ya fuce yana jin haushin kansa, bai ma tsaya ya lura da ammah dake shugowa da ledojin shopping a hannunta ba, gaba daya baya cikin natsuwarshi harya shige daki ammah na kokarin cewa ''son..mun..'' Bata karasa ba ta dubi yanda jikinshi ke karkarwa da yanda buttons din rigarshi suke a bude ya sauko daga sama a harzike, gabanta ne ya dan fadi dukda bata kawo komai aranta ba saidai gabanta daya tsananta bugu saboda tasan shid a zuciya kamar kuturu.

Yana shigewa daki ya dafe kanshi tare da fisge rigar jikinshi, ''inaliahi what was I thinking ya allah'' Wani irin zafi da haushin kanshi yakeji tunawa da yanda idanunta sukayi jaa da yanda ta soma mashi Magana a galabaice lokacin da yke kokarin forcing kanshi, runtse idanunshi yayi ya aksa gane dalilin da yasa yake treating dinta haa dukda deep down baya jin dadin hakan shima, saidai wannan banzanego din nashi bazai sashi ya zama remorseful ba, babu abunda yakeyi anan tsaye sai tsaki, ganin hakan da yakeyi bazai maidoda agogo bay aba yasa ya wuce bathroom.

Bayan shigewarshi part dinshii ammah ta bishi da idanu tana nazari kafin ta soma shigewa da abubuwan data sayo kitchen ta ajiye komai inda ya kamata na abubuwan datayi shoping dinsu kafin ta dawo parlor don daukar handbag dinta data ajiye anan parlor, su salima ne sukayi sallama ita da aman, salima ne ta fara shugowa sanye take da uniform a jikinta sai aman dake biye da ita da school bag dinta da books dinta a hannunshi tana mashi shagwaba yana bata hakuri kamar wani mijin hajiya, kallonsu ammah tayi, sun burgeta sosai yanxu ta sake tabbatar da idan aman ya auri salima zai kula da ita sosai saboda irin kaunar da yake nuna mata a fili sosai, jikinta ne ya danyi sanyi tunawa da yanda amar da amra suke zama, suda suke auren juna kwata kwata babu wani kusanci a tattare dasu ko kadan, shi miskili itama miskila, abun yana damun ammah ssoai dukda tasan amar nason amra ammah yana boyewa, bangaren amra ne ma bata tabbatar ba. ''ah ah yau kuma mai kayi mata haka ne take kunkuni'' Ammah ta fada tana kallonsu, matowa salima tayi inda ammah take don sai a lokacin suka lura da ita ''barka da yamma amah na ya zaman gida'' ''alhamdullahi daughter na ya kike ya exam, an gama lafiya? ''alhamdullah ammah, im so excited jibi grads'' Juyowa aman yayi ya kallesu yana dan murmushi yace ''barka da yamma ammah'' ''barka dai son, ya hidima da mutuniyar tata, hala kayi mata laifi ne naga tana turo baki'' ammah ta fada tana kallonta ''ammah wallahi shine wain ace zan sha icecream ya saya min wai bazai saya min ba haka kawai'' salima ta fada tana galla mashi harara Kallonshi ammah tayi, ''haba son, meysa baka saya mata ba'' ''ammah wallahi mura takeyi, da safe dana kaita school baki ganta ba she keeps on sneezing kamar hancinta zai fita'' aman ya fada yana mata gwalo ''haba daughter yafiki gaskia anan, saboda lafiyanki, yanxu ki wuce sama kiyi wanka saiki sauko kuc abunci, gobe zamuje shopping din graduation'' Cikin zumudi da murna salima tace ''yauwa ammah naa, love you so so much'' ''love you more my dear'' Juyowa salima tayi ta warci Jakarta ta wuce sama abunta tana jin dadi.

Tana wucewa shima aman ya wuce dakinshi, suna tafiya ammah ta wuce sama itama don dubo amra data bari tana barci, da sallama ta bdue dakin nata, babu kowa a cikin dakin sai karar saukn ruwa, takowa ammah tyi bakin gadon ta dan tsaya tana jiran fitiwarta, idanunta ne ya sauka kan kayan amra dake a yage a kasa sai pant dinta shima da yayi gefe, maida idanunta tayi baking ado nan take idanunta ya suaka kan beddings din daya cukwikwiye kamar anyi dambe ga dan jini akan bedsheets din kadan, hankali ammah ne ya dan soma tashi, ahankali kunnuwanta ya soma jiyo mata kukan amra dake cikin toilet, matsowa tayi da sauri hanyar bathroom din t tsaya bakin kofar tayi knocking, kunnenta ta saka ajikin kofar tana jin yanada take yan surutai ''na tsanake yaya, youre so mean, baka da Imani, I hate you'' Azafafe ammah ta donyi knocking kofar, ''daugter are you okay? Is everythingwrong,'' Amra dake tsaye gaban shower jikinta a mace tayi zaman dirshan ta mike tsaye ahanakli tana share hawayenta ''e..eh.. im fine ammah, wanka zanyi yanxu zan futo'' Komawa bakin gadon ammah tayi ta fara zarya tana son gano wani abu, don tabbas taga yanda ya sauko kasa a hargitse, ''badai muhammd forcing kanshi yayi akan yarinyar nan ba'' ta tambayi kanta, fadin irin tashi hankalin da ammah ta shiga bata lokaci ne har saida amra ta futo daga bathroom kanta a kasa, idanunta yayi jaa sosai, hannunta ammah taja suka zauna baking ado, ''daughter meya sameki, meysa idanunki sukayi jaa?'' shuru amra tayi ta sauke kanta kasa ''kaina ke ciwo'' ''karkiyi min karya daughter whats wrong? Muhammd yazo wajenki ne? meya maki?'' Kasa dagowa amra tayi haka zalika ta kasa cewa komai, ''daugter speak up, baki dauki matsayin uwa bane da kike boye min?'' Hawaye ne suka fara zarya a fuskan amra ta kasa cewa komai, ''baki dauke ni a matsayin uwa ba Kenan?'' ''ah ah ammah ba haka bane'' amra ta fada ahankali kanta a kasa tana hawaye, ''then menene? Whats wrong ki fada min komai mai ya maki?'' Cikin shehekar kuka amra ta soma Magana ''ammah bansan meysa ya tsanani ba, bayason ganina, ni na gaji da abunda yakemin, nace mashi bana so ban..'' Saurin toshe bakinta tayi ta kasa karasawa, ''innalillahi wa inna ilaihi rajiun, '' Rungumeta ammah tayi zuwa jikinta tana lallashinta, kiyi hakuri kinji, zan dauka mataki akan wannan, bazai cigaba da wulaqantaki ba idan baya sanki gwara ya rabu dake daina kukan my dear''

Saida ammah ta lalasheta kafin ta umarceta datasa kayan ta kwanta ta huta, futa ammah tayi ta bata space, saida ta sauka kasa ta dumama mata tuwo da take so sosai kafin ta hauro saman, a zaune ta taddata ta doka uban tagumi a baking ado. Kaarsowa aammah tayi ta ajiye mata abuncin a gefenta ''daughter ki daina tagumi babu kyau kinji, kici abunci ki kwanta, ki kwantar da hankalinki zan amshi iyaka dake okay?'' Grigiza mata kai tayi tare da yi mata godiya kafin ammah ta fuce daga dakin.

Dakinta ta wuce direct, koda ta shigo dakin zarya ta soma yi a dakin tana tunanin yanda zatayi da amar, dole saita koya mashi hankali, yana neman rasa yarinyar nan ba tare da saninshi ba saboda wani banzan ego dinshi.

Karfe takwas kowa ya sauko kasa, inda mazan suka wuce masallaci, suna dawowa duk suka wuce dining banda amra dake kwance a daki har lokacin bata fut ba saboda zazzabi daya riketa, tunda ya karas dining din ya gaishe da ammah yaga sauyi a fuskanta, hankalinshi ne yadan tashi don duk tunanin ko yayi mata wani abun ne batare da saninshi ba. Saida kowa ya gama cin abunci salima ta wuce da plates din kitchen, ammah ne ta miqe tsaye ta kalli inda amar yake zaune kanshi a kasa ''ka sameni a sama'' tana kaiwa nan ta wuce sama direct Gabanshi ya fadi dam tunda ta soma Magana harta wuce sama, jiki a amce ya mike yabi bayanta zuwa dakinta, da sallama ya shiga dakin a zaune ya taddata baki gado, kaarsowa yayi anaste ya zauna bakin gadon nata gefen da take zaune, ''barka da dare ammah'' Bata amsa shi ba ta soma Magana ''muhammd bansan haka ka koma very rutheless ba, bansan yanxu ka sauya ba zuwa mara tausayi da tawakkali, bayan wannan ban taba tunanin zaka take maganata ba, amma bbu komai, tunda ka kafe baka jin shawara sai abunda kaga dama kuma kake so kake shikenan zan barka kayi, saidai wallahi ian fada maka saikayi regretting nan gama, now inason ka saki yarinyar nan, zan nema mata cikakkayan namiji wanda ya fika komai na aura mata shi, kai kuma inkaga dam aka mutu a haka ma bazan kara yi maka maganar mace ba,'' Dammm yaji gabanshi ya fadi da sauri ya dago kanshi ya kalli ammah, ''ammah..'' 'shut up my dear, wallahi saika saketa tunda dama chan kace baka buqatarta baka sonta, I was so selfish dana bar yar mutane a hannun wanda baisan darajarta ba idanda nasan haka zaka wulaqantata wallahi da tun wuri na barka ka saketa taje ta auri wanda take sotunda ba sonta kake ba, yarinya son kowa qin wanda ya rasa, wallahil azeem idan yau ta fita saita dawo da namijin da ya fika komai, kyau dai allah ya bata, uwa uba halayya na gari,ga rufin asirin miji, don duk abunda kake mata bata taba futowa ta fada min ba, she cares so much for you, abuncin da zakaci inda zaka kwanta gyaran part dinka dukda batada lafiya bata tsallake duk wani abunda ya danganceka ba, ammah maita samu daga gareka? You keep on pushing her, making her feel miserable dukda na fada maka wallahi bazaka taba samun mace kamarta ba, wadda zata zauna dakai despite halin da kake ciki na rashin haihuwa, haka ta amince ta amshe ka da hannu bibiyu kai kuma baunda zaka saka mata dahsi Kenan right? Toh ka saketa kawai babu dole, allah ya hada kowa da rabonsa, kuma wallahi aurar da ita zanyi to a gentle man dazai kula da ita ya tarairayeta ya bata kulawar daka gaza bata saboda wani banzan ego naka'' ammah takai karshe tana haki kamar tayi tseren gudu. Hankali aatshe amar ke kallonta yama rasa mai zaice, kasnhi har wani juya mashi yake yi tsabar tashin hankali, ''im sorr..'' ''noo o, don't be sorry ba komai ay, wannan ne zabinka ay, kuma abunda kake so Kenan so ka saketa kawai ba damuwa nagode da nunamin da kayi ban isa dakai ba'' ''ammah dan allah kiyi hakuri wallahi ba haka bane, kin isa dani, banida kamarke a zuniyar nan, wallahi na karbeta as my wife,'' Nunfasawa ammah tayi idanunta ya rufe sosai ''ay Magana ya kare, nabaka nan da sati guda ka sakar min yarinya, bata buqatar wanda zai dunga kunsa mata bakin ciki a zuciya,'' ''ammah please…'' amar ya fada idanunshi sunyi jaa bakinshi har karkarwa yake ''don't please me, wallahi kaya yanda nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba, kuma youll regret it na fada maka, and nan da 1week ka ajiye min takardar yarinyar nan simple, now fita min adaki, I don't want to sight you anan'' Tana kaiwa nan ta nuna mashi hanyar futa, jiki a amce ya mike, duk duniya bayan ranar da ammah ta fadi bait aba shiga tashin hankali ba sai yau, gaba daya yama rasa tunanin da zaiyi harya shige cikin bedroom dinshi yana furta innalillahi a zuciyarshi , yanda yake zaarya tsakanin dakinshi da parlon shi zaka dauka ya zaunce ne, ''noo please ammah, wallahi bazan iyaba ba''

Aranar dai amar bai samu wani abu da ake kira da barci ba, don a zaune ya kwana, idanunshi yayi jaa kanshi sai sara mashi yake sosai, fadin irin tashin hankalin da yake ciki bata lokaci ne, gaba daya yama rasa irin tunanin da zaiyi game da lamarin daya bijuro mashi.

Washe gari very normal amra ta sauko kasa, don ammah da kanta tazo dakin ta ta tasota akan ta sauko kasa suyi breakfast, tana zuwa dining din ta taddasu zaune gaba dayansu, ammah na ganinta tayi mata nuni da kujerar gefenta ''zoki zauna nan daughter'' Dagowa amar yayi ya kalli inda zata zauna din, kujeran da ammah ke nuna mata ta zauna dake kusa da ammah,sauke kanshi yayi yana jin wani iri, don sai a yanxu ya fara tabbataer da abunda ammah ke fada, don akusa dashi take zama koda ayushe idan zasuci abunci a dining saidai akasin yau da ammah ta sauya mata gurin zama. Haka nan akaci abinci kowa da irin tunanin da yake, amar dai da amra baifi spoon biyu sukayi ba, shi abun duniya ya isheshi na abunda ya tunkarosa, ita kuwa shi dinne ma bata son gani kwata kata, don tana shigowa suka hada idanu nan take taji wani irin baqin ciki ya ziyarceta lokaci guda. Karfe biyu daidai kowa ya sauko kasa, salima da amra sai salim da ammah, gaba dayansu sanye suke da doguwar riga ta abaya, sunyi kyau sosai, futowa sukayi daga sitting room zuwa inda aman yayi parking don dashi zasu fita, amar dake zaune ya hango saukowansu gaba daya, saida gabanshi ya fadi lokacin dayayi arba da amra, tayi wani masifaffan kyau abayra tayi mata kyau kamar balarabiya, shape dinta ya futo sosai kamar ka sace ta ka gudu, she has this attracting look da bazaka iya resisting ba, cikin sauri ya dauke kanshi daga kanta ya hadiye wani irin miyau mai daci,saboda wani irin kallo da ammah tayi mashi, basu tsaya bin takanshi ba suka fuce yana kallonsu shima baice masu qala ba.

Wani makeken shopping mall suka shiga suka fara sayya saida suka jido abubuwa kamar babu gobe, janta gefe ammah tayi tace ''ki dunga duba wasu abubuwan na baby saboda da zarar kin shiga 8minth zamu fara sayyayn komai kinji daughter, akwai wasu ma danayi order daga dubai unisex masu kyau, sai next month zasu iso'' Sunkuyar dakai amra tayi tana murmushi, ganin haka yasa ammah cewa ''gwara ki ajiye kunyan nan fah my dear '' tana kaiwa nan ta wuce wajen da su salima suke tsaye. Sai wajen karfe biyar takwas suka dawo gida don sunyi yawo sosai inda ammah tace yau ranar salima ne saboda itace graduante,don haka suka dunga zuwa wuraren shakatawa da ciye ciye har suka kai wannan lokacin kafun su dawo.

Lokacin da suka dawo baya gidan do haka kowa ya wuce sama da abunda ya sayo, aranar dai babu maganr girki don gaba dayan su a koshe suke. Amar kuwa daya dawo yaga sauyi don ko dan coffee da amma ke ajiye mashi ranar batayi ba, gashi baiyi dinner ba, haka nan ya je kitchen ya dauka laban yasha ya koma daki ya kwanta.

Washe gari karfe takwas kowa ya futo cikin shiri, ammah sanye take da wani dakkaken lace mai shegen tsada wanda akallah zaikai dubu dari biyar, gefenta amra ce datasha atamfar super mai shegen tsada anyi mata dinkin doguwar riga A shape gown, rigar tasha stones daga sama har kasa wajen pattern din, sai salima data sha ladies suit blue, tayi masifar kyau sosai dukda batayi kwalliya ba, sai graduation gown dinta data rike a hannun tare da hular gown din, salim ma yasha riga da wando English wears yayi kyau sosai kamar bashi ba. Kasa suka sauko gaba dayansu nan suka tadda mai gayya mai aiki, yasha manyan kaya shima, ''general amar taura'' Wata dakkakkiyar shadda ya saka sky blue sai baqar hula data haskashi sosai yayi masifar kyau don koda suka hada idanu da amra saida ta sake kallonshi kafin ta tabe baki ta kauda kai, abun mamaki shine kayansu sai yazo kusan color daya, don atamfar data saka itama skyblue ce da dan ratsin black don haka ta yafa black veil, aman ne shima ya fito sanye da English wear blue kolor kayan amaryarshi suma sukayi anko, gaba daya suka futo, saida aka zo shiga motar ammah ta kallesu tace ''yanxu ya zamuyi tafiyan, mota daya bzai ishemu ba'' Salima ce tayi sauarin cewa ''ammah kizo mu shiga motar ya aman, kaima salim ka taho nan, adda ke ki shiga motar ya muhammd'' Hade rai ammah tayi har zatayi Magana aman y ace ''yes ammah kizo nan mu tafi su sais u biyomu a baya'' Amra dai babu abunda take sai tabe baki tana jinsu, saidai bata da energy din wani argument, shuru kawai ammah tayi ta wuce motar aman, salim na biye da ita, atare suka shige aman ya fuce da motar while su amra na tsaye, shine ya fara wucewa wajen motarshi yayi reverse zuwa inda take tsaye, saida ta dauka kusan minti biyu tana nazarin kodai tayi zamanta ta fasa zuwa, don bata son su kebance dagashi sai ita ko kadan,saida ya danyi horn kafin ta soma takowa anatse kamar wadda jinni baya circulating a jikinta, anatse ta bude kofar ta shige ba tare da ta kalli inda yake ba, tana shiga ta rufo kofar kafin yaja motar,tunda ya kama hanya ta kauda kanta gefe bata kalleshi ba, tsit kakeji sai karar ac, ganin shurun yayi yawa yasa ya kunna wata slow romantic music dake sanyaya zuciya, kallon gefenda take zaune yayi ganin yanda ta takure, kamar wanda ake fusga haka ya samu kanshi da dora hannunshi kan nata data ajiye akan cinyanta, da sauri ta waigo, donta furgita dataji lausassan hannunshi kan fatarta, ba zato ba tsammani taji ya fadi word in da bata taba ji daga bakinshi ba and it came out with honesty ''im..so..rry about'' Kaste shi taui saurin yi tana zame hannunta daga nashi ''ya wuce'' Yanda ta fada ya tabbatar ma da kanshi bata hakura ba, bayason takura mata don haka baice komai bay a zame hannunshi ya maida kallonshi ga hanyar da yake driving, fuskanshi na nan yanda take Har suka karaso school dinsu salima.

Wat ahaddaiyiyar makaranta ce ta manyan yayan masu kudi, fadin irin haduwar makarantar bata lokaci ne sosai, amra dai da idanu ta dunga bin wajen da kallo har yayi parking wajen parking space na guest, shine yay a fara fitowa kafin itama ta fito tana gyara zaman veil dinta, tunda suka futo mutanen dak etsaye wajen parking spec suka zuba masu idanu, babu abunda kake ji sai masha allah, perfect couple, dukda sunji abunda mutane ke fada hakan baisa amra ta saki fuskanta ba haka zalika shima har suka karasa inda su ammah ke zaune.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull