Auren katin kasa complete - Chapter 81
Auren katin kasa complete Chapter 81: Auren katin kasa complete Chapter 81. Baiwar allah abunda bata sani ba shine wannan papers din forging dinsu daddy…
4,124 words
Baiwar allah abunda bata sani ba shine wannan papers din forging dinsu daddy yayi ba sune asalin real document dinba don babu wanda yasan inda asalin paper record of the property's din yake ba harshima don koda yazo kashe dada saida yayi threating dinshi akan ya bashi real paper record din ko yanda zai kasheshi haka zai kashe amar, saidai allah bai bashi ikon samun hakan ba saboda atake dada ya mutu, alhaji kabiru kuwa yayi takaici sosai don saida ya aiwatar da kudirinsa na kashe dada saboda ya gano sirrinsa ya tuna da property record din. Saurin share hawayen fuskanta tayi bayan ta gama tunanin, anatse ta janyo locker da take aje duk wani important document ta aje aciki ta rufe. Anatse ta mike tsaye don dauro alwala, nan take taji jiri na dibanta, ahankali ta furta ''ya salam'' Da sauri tayi baya ta zauna ta dafe kanta don gaba daya kanta juyawa ya soma yi, wasa wasa bayan jiri ta soma jin throat dinta Nayin zafi sosai, wanda hakan yasa ta danyi coughing next thing saiga gudan jini ,abunda yafi tayar mata da hankali shine abunda yabiyo tarin, kallon hannunta tayi hankali atashe ta furta ''subhanallah jini kuma" Wasu irin hawaye ne ke zubowa a fuskanta babu dalili saidai tabbas tasan something is definitely going on, anaste ta soma karanto innalillahi ta yago tissue dake gefen bedside dinta ta dauki gudan jinin ta nade shi cikin tissues din, tunani ta soma yi yanda cikin kwanakin yake samun changes a jikinta wanda hakan ke bata mamaki dukda doctor ya shaida mata effect din magungunan ta ne, wanda for the mean time zata samu changes daga baya kuma zaizo ya bari idan maganin ya kare, gaba daya she's not convinced with maganar doctor don abun gaba yake yi don haka Tayi saurin janyo wayarta ta soma dialing number family doc din,yana picking suka gaisa. Tun kafin ta soma mashi bayani ya soma magana "hajiya yau ma Akwai wani chances din ne?" Tayi mamaki dajin kalamanshi don abun sounds like kamar yasan dalilin kiranshi datayi kenan, bata kawo komai aranta ba don haka tace "oh doctor harkasan complain zanyi maka kenan, anyway gaskia inaga zanzo asibitin don nayi checkup, don naga abubuwan na Kara gaba sosai, anya baza a sauya wasu magungunan ba da alamu dai wannan basu karbeni ba" ta karashe tana murmushi.
Dariya ya danyi yace "Akwai wasu chances dinne bayan wanda kika fada kwanaki hajiya?" "Eh yau na Tashi da jiri, sai kuma tari da jini" Shuru ya danyi kafin yace "okay bayan tari da jiri Akwai ciwon kirji?" Ya tambayeta kai tsaye "No gaskia babu Ay rabon da nayi ciwon kirji harna manta likita"ta bashi amsa "wannan ma yana nuna alamun Akwai ci gaba kuma maganin yana aiki saidai Ina Ganin kamar yayi maki karfi ne shiyasa kike jin jiri, amma za a iya chanza maki wasu suma dai babu guaranteed don kowani magani yana da effect substance da yake chanza organism, don wannan da na baki shine mai sauki sosai wanda bashida side effect and Duk wannan symptoms din normal ne ga masu ciwon zuciya with time zai daina Ammah najin haka tace "Toh shiknan doc ba damuwa Zan cigaba da wannan din, kasan girma idan yazo sai ah hankali" ta karashe tana murmusa daga bisani kuma tayi mashi godiya ta kashe wayar.
Wunin ranar ammah a kwance tayishi don tana miqewa sai jiri, koda su amra sukazo dubata jin shuru nan ta shaida masu da ciwon kai ta wuni. Amar ma koda ya hauro sama don ya dubata shima boye mashi tayi saboda tasan yanda zai tada hankalinshi don haka ta shaida mashi ciwon kai ne kawai ya dan rike ta, shima saida yayi mata sannu kafin ya wuce kasa zuwa part dinshi.
Tun bayan daya dawo daga dakin ammah wanka kawai yayi ya sauya kaya zuwa pjs dinshi ya zauna kan gado tare da jawo laptop dinshi ya soma yin wasu ayyukan, daman evidence ne yake tartarawa gaba daya akan mks empire da wanda dada ya tura mashi da wanda ya samu shima. Tunda ya kafa ma screen din laptop dinshi idanu ya kasa daukewa yana kallon property report dinda dada ya tura mashi cikin encrypted portal, gaba daya properties din taura sunanshi ne a jiki as the heir, haryau mamakin date din da dada yayi handing over Duk properties din yakeyi don if he can recall alokacin yana makaranta ne ko university bai gama ba, "Toh kodai tun lokacin dada ya gano sirrin daddy ne?" Ya tambayi kanshi. Ganin babu mai bashi amsa yasa ya rufe laptop din ya dubi time da agogon na rolex, almost past twelve, dan waigawa ya soma yi yana mamakin rashin zuwan ta dakin, tabe baki kawai yayi don she hakan ma yayi mashi, don he needs break from her new behaviour wanda ke sakashi yin abubuwan da ya kasa gane kanshi. Saida ya kwanta ya janyo duvet yayi addaua ya rufe idanunshi, forcefully yake son yin barci saidai tunanin da yake hana kanshi yi yagama shiga ranshi, he keeps thinking of her, tambayar kanshi kawai yake yi meysa bata zo ba? Kodai she's sick ne? Ya tambayi kanshi, da sauri ya miqe zaune zumbur ya zauna ya dafe kanshi, "goddd why do I care" ya karashe yana yar tsuka kafin ya kwanta, ko second biyu baiyi ba ya sake Tashi gama daya he's anxious, haka nan ya Tashi ya saka bathroom sleeper dinshi ya fuce daga dakin, sama ya wuce direct kamar Ana ingiza shi Har zuwa dakinta, saida ya dan tsaya yana nazari kamar ya shiga kamar karya shiga, karshe dai haka ya batse ya tura kanshi cikin dakin ba tare da yayi knocking ba, a zaune ya tadda daga ita sai singlet da shorts akan gado, ta aje dry cereal a gabanta tana ci,dan waigawa tayi tana jin alamun bude kofa, da mamaki ta kura mashi idanu don kwata kwata batayi expecting dinshi ba, shima idanun ya zuba mata Har ya shigo dakin dan nesa da ita yana mamakin Anya wannan yarinyar kalau take kuwa?, Kallonshi amra tayi Ganin yanda ya Tamke fuska kamar bai taba fara a ba don haka tace "laa Bakayi barci ba yaaya" Shuru yayi yana mamakin yanda yanzu ko irin fargabar da take yi idan zatayi mashi magana batayi, ayanxu yanda yake magana dashi sshe's talking casually. Haka ya dunga binta da idanu baice mata Kala ba Har saida ta mike tsaye ta karaso gabanshi ko kunyanshi bata jiba, tace "kana buqatan wani abu ne?"ta karashe tana mashi Farr da idanu, da ido ya dunga bin ta da kallo tundaga tsakiyan kanta don gaba daya bata da wani tsayi sosai a gabanshi zuwa cinyoyinta, cikin sauri ya kauda kanshi gefe yace "bring me coffee" Yana kaiwa nan ya fuce cikin kamewa, da idanu tabi bayanshi da kallo har ya fuce mata daga gani. [7/11, 11:18 PM] +218 92-2035171: Update Uneditedpage
Binshi da idanu amra tayi harya fuce daga cikin dakin, da cearal dinta a hannunta ta janyo hijab dinta ta zura ta bi bayanshi, tana sauka kasa kitchen ta wuce direct ta fara kiciniyar hada coffee, anatse ta gama hadawa ta daura mashi akan saucer ta fuce daga kitchen din cikin natsuwa, da sallama ta bude bedroom dinshi a zaune yake bakin gado ya nade hannayenshi akan kirjinshi, dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta karaso har gabanshi ta dan sunkuya gefen bedside ta aje mashi mug din, ''bismillah'' Kallonta ya danyi kafin ya maida idanunshi kan mug din, cikin kamewa ya miqa hannunshi wajen bedside din ya dauka mug din kafin ya fara kaiwa bakinshi, tana ganin haka ta juya zata fuce daga dakin, hankalin shi gaba daya nakan coffee din yana kokarin cire mug din daga bakinshi bayan yayi sipping ''na baki umarnin tafiya ne?'' Tana jin haka tadan tsagaita ta juyo ta mashi kallo daya kafin ta tako har inda yake zaune ta dan tsaya daga nesa, ta dauka kusan minti biyar a tsaye duk ta gama takurewa, dan leka mug din hannun nashi tayi ganin ko half baiyi ba ta dan tabe baki ta karaso gefen da yake zaune ta zare hijab din jikin nata ta zauna gefenshi ta tankwashe kafarta kan gadon ta bashi baya tare da bude pack din cereal din nata data boye a cikin hijab, da mamaki ya waigo ganin yanda gaba daya yanxu bata kunyar shi, samun kanshi yayi da gyara zama yanda zai hangota da kyau akan gado, tana jin motsin chanza position da yayi ta juyo bakinta cike da cereal, cikin sauri ya kauda kanshi ya hade rai tamm kamar ba kallonta yake ba, sake maida idanunshi yayi kanta karaf suka hada idanu tana ganin haka ta sauke mashi lausansan murmushi mai melting herat wanda yasa heart dinshi skipping lokaci guda, cikin shagwaba tace ''yaya nifa barci nake ji wallahi, ka sallameni na tafi'' Banza yayi da it aba tare da ya sake kallonta ba, itama tana ganin haka ta juya mashi baya tana turo baki tana cin cereal din harta cinye tass, wasa wasa sun dauka kusan awa guda shi baice mata ta tafi itama bat ace mashi kala ba har barci ya soma fuzgarta, time to time yake dubanta har barci ya kwasheta ta lafe akan gadon, zuba mata idanu yayi yana kallon bayanta, hakannnan yaji hes relaxed harya gama shan coffee din, yana gamawa ya miqe ya fuce da mug din zuwa kitchen, yana dawowa ya taddata ta baje ko'ina, tayi rub da ciki, bin bayanta yayi da kallo yana ayyana abubuwa sosai aranshi kafin yayai saurin kauda kanshi, anatse ya tako bakin gadon ya kwanta daga gefe ya janyo masu duvet, koda yazo lulluba mata saida yadan tsagaita yana wani tunani aranshi ''why im I doing this?'' ya tambayi kanshi, kallon innocent face dinta yayi haka kawai yaji yana tausayinta babu dalili, saurin kauda duk wani tunanin dayazo ranshi yayi ya rufa mata duvet din ya kwanta gefe yana facing ceiling tare da nade hannayenshi a kirjinshi yana tunani har barci ya fusgeshi. Cikin dare yaji mutsu mutsu a jikinshi, ahankali ya soma bude rinannaun idanunshi harya sauke su akanta, ta nadeshi gaba daya ta rungumeshi, da mamaki ya ware idanunshi da kyau don tabbatar da abunda idanunshi ke ganar mashi, ta wani kanainayeshi tayi cuddling dinshi, he can feel her bare chest a jikinshi, saurin runste idanushi yayi ya fara kokarin janyeta daga jikinshi,bai kaiga zareta ba ta zake hade jikinta da nashi ta rike shi gam kamar ta samu pillow, shiko goga take komai ya fara chanza mashi don gaba daya jinshi yayi kamar an arura mashi wutar azaba a marar shi, ''ya allah, yarinyar nan zata haukata ni'' ya fada ahankali yana fidda nunfashin wahala, rasa abunyi yayi don gaba daya babu alamun zata bari ya janyeta daga jikinshi, gashi any wrong move yayi saita kara damkoshi wanda hakan ba karamin affecting dinshi yake ba, don haka ya hakura ma ya kyaleta saidai daren ranar dai barci kaurace mashi yayi gaba daya. Akunnenshi aka kira sallar asuba, yana jin haka kuwa ya turata gefe, ganin tana shirin damkoshi ya sashi daka mata tsawa ''kee bakida hankali ne, whats the meaning of this?'' Firgigi ta bude idanunta ta sauke akanshi, idanunta sunyi mici mici,gaba daya barcin bai isarta ba don haka ta maida idanunta ta rufe yana ganin haka kuwa ya wuce bathroom azafafe rai a bace, yana shiga ya fara yin wanka, ya dade sosai a tsakiyan shower yana rage ma kanshi wahalan da yake ji, saida yaji ana neman tada sallah yayi saurin dauro alwala ya fito ya zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin. Koda aka idar da sallah tare suka fito daga masjid shida aman da salim, idan ka gansu gwanin burgewa har suka shige cikin gida kowa ya wuce part dinsh. Yana shiga bedroom dinshi ya tako har bakin gadon ganinta a kwance kamar aynda ya barta, ranshi ne yadan sosu haka kawai don haka ya soma Magana afadace ''keee aisha!!!'' Anaste ta juyo ta bude idanunta ta suka danyi jaa ta kalleshi, ''ke are you okay?what sort of rubbishness is this? Ke kafira ne ko sai ance tashi kiyi sallah'' Miqewa tayi zaune ta kura mashi idanu, saida y agama fadace fada cen shi kawai ta fashe da kuka, wiwi ta dunga kukan shagwaba, shide tsayuwa yayi yana kallon ikon allah, lallai yarinyar nan ta gama rainashi yana mata Magana tana kukan rainin hankali, ya fada aranshi, ay baisan lokacin daya daka mata tsawa ba ''shut the fuck up, are you insane?'' Ay kamar ya kara tunzirata don haka ta miqe tsaye ta janyo hijab dinta ta karaso gabanshi tace ''haba yaya, why are you treating me like this? Meysa ka tsane ni? Me nayi maka a duniyar nan,ina kokarin ganin na faranta maka kai kuma kullum cikin neman hanyar kuntata min kakeyi,why???'' Yanda ta tsaya gabanshi babu tsor babu komai tana fada mashi maganganu ya hasalashi ya kalleta daga sama har kasa ya mata wani disgusting look yace ''nace maki ina buqatar farantawar taki ne? nace maki ki shiishigemin ne? ke kika sama kanki, waye ya yama baki wannan shawarar, look idan kina tunanin wannan abubuwan da kikeyi zai chanza mind dina youre mistaken, gwara ki daina bata ma kanki lokaci, Magana daya nakeyi bana chanza Magana, so I will advice its better you stop…''' Takowa tayi gabanshi tana sheshekar kuka jikinta na rawa ta tsaya gabanshi dab dashi ta rike kugu harda dan dingilawa don ya ganta da kyau don ya fita tsayi sosai ''nooo, nooo I will not stop, this is just the beginning ma yaya, ko mai zakace min wallahi bazan taba rabuwa dakai ba, kace ina shishigi ko ina cusa kai?, ay aynxu ma na fara, kuma kyautatawa ne ba chusa kai ba'' ta karashe tana murguda mashi baki kafin ta juya mashi baya ta duka ta dauki hijab dinta data yar da gangan a kasa, saurin yin baya yayi don gab ass dinta ya gogi gabanshi, ganin abunda take shirin yi wanda idan har ya bari hakan ta faru zaiji kunya, ba karamin chaza mashi kai yarinyar nan take yi ba itako tana dukawa ta dauki hijab dinta ta mike ta zura abunta ta gifta ta gefenshi ta nufi hanya, tana gab da fita ta dan waigo tayi murmushi don taga lokacin dayayi baya data duka ''sorry my yaya ban gaisheka ba, ina kwana?hope ka tashi lafiya '' Bata jira jin amsan shi ba ta fuce tana dariya ciki ciki, ''ay yanxu wasan ya fara, wallahi zaka ga chusa kai, daman kunya nake ji shiyasa nake baya baya dakai ammah wallahi yanxu zan nuna maka cewa ba'a yima mace haka'' Tana kaiwa nan ta shige daki ta dauro alwala ta tada kabbarar sallah tana idarwa tabi lafiyar gado hankali kwance.
Tun bayan fitar amra ya kasa motsawa, he's so stunned with her new attitude, ya kasa ganema kanshi shima yanda ya kasa taka mata burki, cije lower lip dinshi yayi yana takaicin yanda ya tsaya take fada mashi maganganu ba tare da yayi maganin ta, he's so madd, yanda she looked into his eyes har tana iya cewa she won't stop, shi abunda yafi bashi haushi ma is the fact that deep down yana son yanda take chusa kanta zuwa gareshi, dukda he's trying to distance himself from her saboda neman haukatashi da takeyi with her presence, duk motsinta akan idanunshi wanda yakeyi afake ba tare da sanin yana yi da kanshi ba, bayan wannan he started to notice he cared so for her dukda ya dauka wannan a matsayin saboda ita marainiya ne kuma yanxu reponsibity dinta da kannenshi ya dawo hannunshi saboda sanin yanda suka taso cikin wahala.
Dubai uae…. Tun bayan tafiyar amra without notice hankali haifa da Nadine ya tashi sosai. Washe gari m5 ya shaida ma Nadine saboda yasan zata damu, haifa cedai babu wanda ya shaida mata, don sunyi plans din haduwa the next day ita da amra saboda zasuyi pre graduation photoshoot, haka ta wuni tana kiran line din amra baya shiga karshe dai haka ta hakura, washe gari ma haka ta dunga kiran lne din throughout switch off, ganin haka yasa ta shirya ta wuce penthouse din amar. Koda ta iso gidan nan Nadine ta shiada mata cewa ta koma Nigeria saboda wani abu daya taso urgently wanda haka m5 ya fada mata, hankalin haifa ya tashi sosai don tana jin haka babu abunda yazo ranta sai maybe ko amra ta gudu, ko kuma general ya sake maidata gidanshi saboda wani kudirin nashi daban, ganin babu wanda zai bata amsar tambayoyinta yasa ta koma gida hankali atashe. Haka ta jera kwanaki tana zuwa gidan don neman yanda zatayi connecting da amra,gashi duk zuwan da zatayi sai sunyi sabani da m5 sabod yabar zuwa gidan, daman amfanin zuwanshi saboda ya kai amra aiki ne ko idan general yana nan, yawancin zuwan nashi sai jefi jefi yake yi don duban gidan saboda ya bama general report akan abubuwan da suke gudana a gidan wanda hakan qa''idarsa ce duk sanda baya kasar sai m5 ya bashi report ,agidan kuwa Nadine ce kawai sai dayar maid din, suke kula da gidan don sir general din bai sallamesu ba haka zalika wata na karewa zai tura masu kudin aikinsu.
After 1 month… Haifa's resident… Lokaci kamar ruwa haka yake gudu, yau wata daya Kenan rabonda haifa taji daga wajen amra, cikin kwanakin nan haifa tayi su ne cikin tashin hankali da damuwar aminiyarta, amra ta zame mata wani bangare na cikin rayuwarta da bazata taba neglecting dinta ba kota manta ta da ita, acikin kwanakin har tunanin zuwa Nigeria saida tayi saidai abuh ya hanata saboda na farko that will be the first da zata shiga kasar, gashi bata san kowa ba shima abu bashida wani connection da Nigeria don baitaba zuwa ba, don haka ya bata hakuri akan ta bari daga baya after engagement dinta da hamman wanda ake shirinyi a cikin month din.
Yau gidansu haifa a cike yake tam da dangi, both dangin abuh da dangin ummi, asalin larabawa kake gani kota ina, an kawata gidansu da decoration din flowers, daga hanyar shigowa gidan anyi hanging wedding banner (welcome to haifa and hammans engagement) gaba daya anguwar ta cike da hadaddun motoci, cikin gidan kuwa shima cike yake da mata dam, anata guda, ga kamshin turaren wuta daya bade ko'ina, compound din gidan yasha lightings da decors kamar yau ne ranar bikin nasu, cikin sitting room kuwa manya manyan carpet ne shimfide da tuntu inda jiga jigan larabawa masu ji da dirhams suke zaune, duk sunsha gwala gwalai kamar competition gabansu shake da abunci kala kala, irin nasu na manya, su hammus falafel,taboule, fattoush, su mandi ne,gasassun rago da kaji a jibge, kawayen ummi da danginta da dangin abu duk kowa na zazzaune ana hira masu guda na guda masu takawa na, abun dai sai san barka,yau engagement din diya daya tilo a cikin familyn, chan na hango ummi, taci kwalliyansu na larabawa cikin traditional arab dressing na iyaye, tasha gwala gwala itama kamar babu gobe, tana saukowa daga stairs aka fara guda yiiiii yiii ko'ina, kawayenta ne suka miqe suka tarbota har zuwa cikin sitting room din. Karfe biyu daidai dangin ango suka karaso, maman hammam ce kawai sai yan uwanta na chan Iraq mutane biyar wanda duk distance relatives ne, suma sunyi kyau sosai, itama tasha gwal dinta babu laifi don shima ana gani ansan kudi ya zauna, hammam dai ya fito da mahaifiyarshi, suna karasowa aka fara guda ana gaggaiwasa, abunka da larabawa ba barsu abaya ba wajen tsegumi, dole saida aka samu waenda suka danyi tsegumin cewa ay angon is no body anan uae. Saida akaci akasha kafin aka fara shirin fitoda da amarya don ango ya iso,ummi ce dakanta ta wuce dakin haifa don dubota, da sallama ta shiga dakin, haifa dake zaune bakin dresser tasha bridal gown irin na larabawa red, tayi masifar kyau sosai tasha makeup, ta fito a asalinta na balarabiya jinin larabawa sak, she looks so beautiful sai wani irin sheki take kana ganinta kaga amarya, A zaune take bakin dresser ta kurama diamond necklace data sa akayi masu customizing ita da amra a hannunta inda a jikin necklace din aka rubuta amra bestie, idanunta ne suka kawo ruwa tunawa da alkawarin da sukyai ma juna ita da amra, she clearly recall lokacin da suka yi alakwarin having each other back, komai is moving so fast yanxu gashi har za ayi engangement dinta babu best friend dinta, babu bestie dinta a kusa da ita, alokacin da suke tare haka zasuyi ta maganar with so much excitement, tunawa da maganra amra yasa hawayen nata ya soma bullowa ''I cant wait to walk with you during your engangement, I want to be your best girl'' Jin alamun bude kofa yasa haifa bude dan box din Sarkar ta aje aciki ''I miss you so much best girl'' haifa ta fada tana goge hawayenta jin muryar ummi tana cewa ''masha allah allahumma bareek habibty masha allah'' Karasowa ummi tayi kusa da ita ganin hawaye na neman saukowa akan fuskanta, da hanzari ummi ta rike hannunta ta dagota sama ta kalleta da kyau, ''my baby why are you crying on your special day?,'' Ashagwabe haifa ta kalli ummi tace ''ummi, im so sad, todays my engangement babu amra a kusa dani, I missed her so much'' Saurin share mata fuskanta ummi tayi tace ''no dearest don't cry, im sure idan tasan kinyi kuka ranar engangment dinky saboda ita bazataji dadi ba, I'm sure she will be happy for you, and insha allah zaku sake haduwa habibty, kinga yanda kikayi kyau kuwa?'' ummi ta fada tana kamo fuskanta tayi pecking din kumatunta da goshinta, nan take emotions ya shiga, kallonta ummi tayi kmar zatayi kuka she cant believe yau engangement din diyarta, shes so happy' Saida ummi ta lallaba ta ta daina kukan kafin ta rufe mata fusknta da veil din bridal gown din ta riko hannunta suka futo.
Ataresuka fara saukowa kasan, mutane na hangosu aka fara gudaa yiii yiii yii, babu abunda ke tashi sai larabci, ''masha allah, allahumma bareek'' wasu na addua wasu nay aba kyawun amarya dukda ba a fuskanta ba, ummi na saukowa da ita ta karasa da ita gaban mahaifiyar hammam, nan ta duka ta gaisheta yanda suke traditionally, mikewa mahaifiyar hammam tayi ta rike hannunta ta rungumeta tare da kissing din kumatunta, haka ummi ta dunga zagaye da ita saida kowa ya rungumeta ya sumbaci goshin kafin a zaunar da ita a tsakiyan parlor, daman haka tradition dinsu yake, nan za a ajeta gaban kowa ango zai shigo ya sameta yayi unveiling fukanta don shi zai fara ganinta kafin afara engangement din. Karasowar ango dakin ya karade da guda, masha allah sanye yake da kundura yasha farar jellabiya, fuskanshi dauke da murmuhsi, mahaifiyarshi data shigo dashi har gaban haifa ta zaunar dashi, nan ya bude veil din haifa kafin ya sanya mata engangement ring, nan take wajen ya sake dauka da guda, anata masha allah, haifa dai kanta akasa har sukayi exchanging rings.
Nigeria taura estate… yau kwana biyu Kenan bai saka amra a idanunshi ba dukda ya damu sosai saidai ego dinshi bazaisa ya dubata ba bayan wannan ma haka ya dunga denying kanshi akan ya damu da itan dukda yana alaqanta hakan ne saboda maraicinta ne yasa ya damu badan wani abun ba, itama dai ta bangarenta tana sane dashi, don saita faki lokacin da ya futa daga gidan take shiga dakinshi ta gyara mashi ko'ina ta saka mashi turaren wuta,kyautatawa dai wadda tayi alkawarin saitayi mashi kullum tana yi abayan idanunshi, haka zata shiga closte dinshi ta gyara mashi kayanshi, bayan wannan ma ayanxu duk abunda ya shafeshi ya dawo hannunta daga kan gyaran bangarenshi bata wasa da wannan sosai zuwa ga coffee dinda ammah keyi mashi duk dare yanxu duk ita takeyi kuma idan tayi haka zata kai mashi dakinta ta aje mashi ta futo, kwata kwata bata yarda sun hadu ba don yanxu ta daina kwanan dakinshi gaba daya saboda shawarar da madina ta bata kan cewa tayi testing dinshi ta hanyar daina shishige mashi ko zai zo da kafarshi, idan har baizoba kuma dole su chanza salon yanda zasu tunkareshi. Ko wajen yin breakfast ma bata saukowa, haka zalika ammah ma bata takura mata akan dole saita sauko kasan taci dasu saboda wasu dalilai. Afili dai yana nuna bai damu ba saidai a zuci ya damu sosai don sanin kodai tana lafiya, gashi dai bazai taba iya tambayar ammah ba bayan wannan ma bazai taka har inda take ba don zata rainashi, a cikin ranshi ba karamin haushin kansa yake jib a yanda ya kasa controlling kanshi har yake saka damuwar mace aranshi wanda bait aba tsammanin zaiyi haka bag aba daya rayuwar shi.