Auren katin kasa complete - Chapter 84
Auren katin kasa complete Chapter 84: Auren katin kasa complete Chapter 84. Gefe ta matsa mashi ya bude kofar yana budewa ta shige ciki ta tsaya kikam a…
4,467 words
Gefe ta matsa mashi ya bude kofar yana budewa ta shige ciki ta tsaya kikam a sitting room kamar wata soja, don haushinsa take ji sosai, ahanakli ya karaso inda take calmly ya soma mata magana "Aisha!!" Bata motsa ba kwata kwata daga inda take harya karaso inda take tana Ganin haka Tayi saurin jaa baya, Murmushi kawai yayi don yasan halin nata zatayi shi kuma baya jin yana da lokacin wannan don haka baiyi wata wata ba ya sungumeta, babu zato ba tsammani ta jita a sama, wutsilniya ta fara yi tana san ya sauketa yaki, karshe ma dai fashe mashi tayi da kukan shagwaba, yana jinta babu abunda yakeyi sai murmushi, bai tsaya ko Ina ba kuwa sai bedroom dinshi tana nade a hannunshi, harya karaso bakin gadonshi ya ajiyeta akai,yana ajiyeta ya danyi baya yace "wait for me here karkiji ko'ina" Wata yar harara ta Galla mashi kuka ya gani saidai kawai yayi dariya aranshi yace "Zaki I kaniyanki ne yau dinnan" yana kaiwa nan ya fuce daga bedroom sun ya sauko kasa, kowani ango yana shugowa dakin Amarya ma da kaza shi kuwa general sai ganinshi nayi da flower, wata katuwar rose mai shegen kyau da tsada ya zaro daga bayan booth dinshi, yana daukowa ya rufe motarshi ya koma cikin gidan, yana shugowa ya rufe kofar mai entrance din ya wuce sama cikin izza da kamewa, Bedroom dinshi ya wuce direct har alokacin fuskanshi dauke da murmushi yana bude kofar yaga wayam,…. [7/11, 11:18 PM] +218 92-2035171: Last Update part 2 Shuru ya danyi son yasan zata iya guduwa don haka ya fuce daga bedroom din ya nufi nata dake next floor yana zuwa ya nufi hanyar bedroom din nata, Hannunshi ya fara sanya akan handle din kofar, yana danna handle din kofar yaji a rufe, shuru ya danyi yasa kunnenshi jikin kofar nan ya soma jin kukanta na Tashi a hankali, Gyara tsayuwar shi yayi kafin ya soma magana "Aisha open up let's talk" Banza tayi dashi kamar batasan yana yi ba saida ya sake maimaitawa, A taqaice sai ya dauka kusan 30mins yana karanta taki bude kofar saima Kara saurin kukanta da tayi, ranshi ya sosu sosai saidai yana kokarin dannewa saboda ayanxu dole ya lallabata, "okay shikenan ki kwanta ku huta pls ki dina kukan nan" Yana kaiwa nan ya ajiye mata yar bunch of roses din a gaban dakin ya wuce sama zuwa bedroom dinshi, yana shiga bedroom dinshi ya soma rage kayan jikinshi zuwa pjs, kafin ya kwanta ranshi Duk a dagule, dukda yaji zafin abunda tayi mashi hakan baisa yayi gushi da ita ba don yanzu ya koyi yanda zai dunga controlling anger dinshi.
Washe gari da safe amma ta aiko driver da breakfast, Haka ya sauko kasan da kanshi ya karba hasket din kafin ya wuce dining dashi, da kanshi ya koma sama zuwa bedroom dinta yayi mata knocking shuru bata bude ba, ya dauka kusan minti goma yana knocking Ganin bata da niyar budea Yasa ya kyale ta ya wuce bedroom dinshi, wanka yayi ya sauya kaya zuwa kamani kafin ya sauko kasan for the second time ya sake yi mata knocking, "Aisha!!!" Shuru babu response at that Point hankalinshi ya gama Tashi don haka yace "dan Allah say something mana? Are you okay" Daga ciki ta amsa shi da "yes I'm okay" Wata nauyyyay ijiyar zuciya ya sauke kafin ya sauka kasa yayi breakfast dinshi yana gamawa ya fuce daga gidan gaba daya don he's preparing for something.
Bai dawo gidan ba sai wajen karfe uku na rana, Yan shugowa part dinta ya wuce yana zuwa yayi knocking Har lokacin bata bude ba saima kukanta daya jiyo, at that point yakai maqura don haka yace "what's the meaning of this aisha? What is wrong with you? Nace Zan mai wani abu ne ko nayi maki wani abun ne? At least ki fito kici abunci karkiyi ma kanki illa" Shuru tayi banza dashi saima daga karshe yaji tace "ni bana jin yunwa" Shuru kawai yayi ranshi ya sosu sosai don haka ya kyaleta kawai tayi abunda yake so.
Bangaren amra kuwa ta zabi zaman dakin ne saboda bata son anything dazaiyi encountering dinta dashi, ga ciwon mara daya dan riketa ya hanata sukuni,
Duk wannan magiyar daya dunga yi mata bai sata ta bude kofar bedroom dinba tana zaune a bakin gado wani irin haushinsa takeji Har barci ya kwashe ta, washe gari haka ta lallaba tayi wanka ta sauya kaya zuwa wasu marasa nauyi dake Jere a cikin wardrobe dinta wanda tun last zuwanta suke cikin wardrobe din, tana gamawa tabi lafiyar gado abunta. Tana daga kwance ya sake yi mata knocking lokacin da aka kawo breakfast, harga Allah yunwa take ji sosai saidai taurin kanta yasa taqi futo wan balle taci abuncin. Sai wajen yamma bayan data gama galabaita ta bude kofar ta sauko ta diba abuncin ta koma daki ta sake kullle kofar.
After 2days… Haka suka dunga wasan buya ita dashi inda ya kyaleta kawai don baya son takurata saidai Duk Safiya saiya leko bakin kofar dakin nata yayi knocking ya duba lafiyarta, wani sa'in tana amsa shi wani sa'in kuwa bata kulashi haka zai tsaya inya gaji yayi tafiyarshi. A cikin kwanakin kullum amma ke aiko masu da abunci Duk Safiya da yamma.
Bayan sati guda zaman dakin ma ya gudureta da kanta ta soma futowa tana saukowa kasan tana shiga kitchen ta dafa ma kanta abunci, don yanxu saidai ya fita ya sayo takeaway ya aje mata nata don baya son ya dunga zuwa gida saboda Kar ammah tayi sensing wani abu dukda ya sayo komai na provisions da za a iya dafawa..
Bangaren su ammah, gidan is so lively, daman gida indai da yara bazai taba zama shuru ba, Salim ya koma school, salima kuwa yanxu itace kamar second mum din triplet, itace cin abuncinsu itace wankan su Dukda sometimes tare da ammah suke yi, don yawanci ma a dakin ammah suke wuni gaba daya, yara dai sai girma suke sai san barka kwata kwata basa koke koken neman uwarsu, daman inkaji yaro na kukan neman uwarshi to fah yunwa ce, su kuwa basa Shan komai sai madara da puddings.
Aranar labaran yazo gidan don amsa Kiran da ammah tayi mashi, bayan ammah ta sauko suka gaisa gaisuwar mutunci kafin ta soma magana "daman na buqaci gani Ka ne saboda inason muyi wata magana," "Toh hajiya Ina sauraronki" ya bata amsa kai tsaye "Dama maganar Salima ne da Aman," Dan Gyaran murya tayi kafin ta cigaba "Aman maraya ne , nasan kasan tarihin gidan nan basai na dago zancen ba,….Baban aisha Ina neman ma dana Aman auren yarka salima, Ina fatan zaka amince da hakan" Murmusawa labaran yayi kafin ya kalleta yace "hajiya ai kece uwarta kume kece ubanta, komai yana hannunki, Duk zabin da kikayi mata nayi naam da shi, fatan mu Allah ya sanya albarka a cikin wannan" Murmushin jin dadi ammah tayi sosai tace "Nagode Nagode da wannan karamci baban aisha, Allah ya saka da Alkhairi" "Hajiya babu godiya Ay tsakaninmu Wallahi duk abunda kikace hakan za ayi Insha Allah" …….
Saturday morning…. Anatse take saukowa daga stairs, sanye take da Riga da skirt daya kamata sosai chip chip fuskanta fayau sai dan kohl data saka a a idanu ta, anatse take saukowa zuwa kitchen, Kofar kitchen din ta bude, tana bude wa tayi turus ta tsaya Ganin tsaye yana kokarin hada tea a mug,yanda take kallonshi bai shima yake kallonta kafin ta kauda kanta gefe, ganinshi a kitchen din baisa taki karasowa ba don haka ta wuce hanyar pantry ta dauko noodles guda biyu da kwai biyu kafin ta fito, lokacin data fito yana tsaye Har lokacin ya zuba mata idanunshi yana sipping tea din hannunshi, fuskanshi tarr alamun bai dade da Tashi, kallonta ya dunga yi daga sama Har kasa Yan ajin kaunarta da shaawar ta yana double a kanshi, tayi mashi kyau sosai fatarta sai sheki takeyi don sai yanxu ya samu damar yi mata kallo kurulla sosai tundaga sama Har kasa, her body da yanda take komai a natse babu hayaniya is driving him crazy…. Gyaran murya ya danyi Har lokacin yana kallonta bayan ya sauke mug din daga bakinshi yace "good morning beautiful, Har kin gama gudun Nawa?" Dan tsayuwa tayi chak daga dauraye tukunya dake hannunta tayi bata juyo ba haka zalika bata ce mashi Tak ba, "Me zaki dafa mana" ya tambayeta yana ajiye mug din hannunshi kan granite din dake kan table din kitchen, Nan ma bata ce mashi ci kanka ba saima cigaba da abunda takeyi tayi, ganin haka ya sashi cewa "Wifey bazaki kulani ba?, Wai har yanxu hukuntanin akeyi haka? Ya kamata a yafemin haka nan mana, Wallahi nayi regretting Duk abubuwan da nayi abaya" Yana kaiwa nan ya soma takowa inda take, Lola in tana tsaye a bakin plate cooked gas tana kokarin daura pot din akan plate din, Murmushi kawai tayi don tasan daman abunda yake so kenan, yayi mata dadin baki saboda ya samu kanta cikin sauqi toh kuwa hakan bazai taba faruwa ba, Duk a tunanin ta taba ta zaiyi, abun mamaki kuwa sai taga akasin haka don yana zuwa dan da ita bai taba ta ba ya dan tsaya daga bayan nata yace "I know what you're thinking right now, inason ki san cewa bazan Kara takura ba sannan bazan fasa baki hakuri ba because I mean it, I want us to work this out, please.." Yana kaiwa nan ya wuce ya ajiye mug din kan sink kafun ya fuce daga kitchen din Yana futa amra ta tabe baki tabi bayanshi da kallo Har fuce babu abunda yake Raya wa a zuciyar ta sai "hmm tanan Ka bullo kuma, Wai ni zaiyi ma dadin baki, idan har kaga na sauko da wuri ba sunana aisha ba" Tana gama tunanin nata ta juya ta kunna gas din. Koda ta gama dafa lafiyayyiyar indomie din parlor ta dawo ta zauna ta kunna tv, sai a lokacin ta lura da nan ma an sauya komai ba dakinta kadai ba don komai dake dakinta saida aka sauya zuwa sabbi daga kan gadon zuwa carpet da sauran abubuwan dakin, nan ma parlor an sauya komai zuwa sabbin kuka wanda suka fi wanchan kyau sosai, Gyara zama tayi ta fara cin indomien saida ta cinye tass ta rage kwai daya don ta cika cikinta sosai kafin ta mike ta wuce kitchen ta wanke plate din da mug din daya sha tea kafin ta dawo kitchen din ta zauna….
Karfe sha biyu daidai ya fito daga part dinshi, ahankli yake saukowa babu abunda yake sai kamshi, hannunshi rike da wayanshi sanye yake da kananun kaya as usual kamar koda yaushe, fuskanshi na nan yanda take, Tundaga bakin stairs ya hangota a kwance akan doguwar kujera tana latsa waya hankali kwance, Karasowa yayi har inda yake bata ba lura dashi ba don waya take daga kwance "salima meysa yake kuka? Kin bata abunci kuwa" Amra ta fada Har lokacin wayan na hannunta don ta saka wayan a speaker Daga chan bangaren salima ta amsa ta "Adda Wallahi rigima ne, yanxun nan ammah ta gama bata abunci" "Kinbar ammah da hidimansu ko?" "Ah ah Wallahi, na dan shiga bathroom ne, kinsan yanxu mun koma part din ammah" "Ina hero's dina? Kai Wallahi I missed them so much, inason ganinsu Wallahi"
Amar ne yayi gyaran murya wanda yasa ta waigo ta ganshi tsaye, "kinason akawo su ne?" Ya tambayeta, banza tayi dashi kafin tayi sallama da salima ta kashe wayar. Bata kalleshi ba ta cigaba da kallon tv, Yan a Ganin haka ya dan hade rai don baya son yanda take banza dashi, idan zaiyi magana goma bazata ce mashi qala ba, "Zan futa yanxu, zaki buqaci wani abun ne? Do you need anything?" Ya tambayeta sounding very serious, Tana jin haka ta dan dago ta kalleshi , "bana buqatar komai" Tana karashe wa ta kauda kanta gefe Yana ganin haka ya girgiza kanshi kafin ya dan tako inda fuskanta yake, abunda bata taba expecting ba a wannan lokaci, sai jin lips dinshi tayi a kumatunta both sides, saurin runtse idanunta tayi sosai don kamshinsa daya bugu hancinta hade da kamshin breath dinshi da suka bugeta, "take care of your self bazan dade ba Zan dawo" yana kaiwa nan baima tsaya jin abunda zata ce ba ya fuce daga sitting room din, gaba daga amra sandarewa tayi, she can't lie wannan peck din ya shige ta sosai, Harya fuce tana jin presence dinshi da tausasan lips dinshi akan kumatunta…..
Tana nan zaune tana latsa waya tana duban hotunan da sukayi da triplets dinta lokacin birthday dinsu, babu abunda take sai murmushi musamman idan tayi playing videos dinsu, tana nan zaune saida lokacin sallah yayi ta mike ta wuce sama…
Bayan futar Amar daga larrics bai tsaya ko Ina ba sai taura estate don kusan kullum sai yazo gidan ya duba yayanshi, ya dade sosai a wajen su don sai wajen yamma likis ya futo daga gidan, yana futowa daga taura estate ya wuce shopping mall, don wunin ranar da amra yayi shi, sayyayyan kayan girke girke yayi mata ya karo wasu provisions din da yawa Duk wani abunda zata bukata Harda frozen namomi babu abunda bai sayo mata ba, Saida ya shake motar da kayyayki kafin ya wuce gida, a hanyanshi ta zuwa gidan ma saida ya tsaya ya saya masu grilled chicken kafin ya wuce gidan, lokacin daya karaso gida Har anyi Kiran sallar isha'I don haka ya bude bayan yasa securities suka shiga da kayayyakin saida suka ajiye komai kafin ya wuce masallaci. Saida aka idar ya fito ya shige cikin gidan, lokacin daya shiga sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce sama ya watsa ruwa ya sauya kaya kafin ya sauko zuwa part dinta, Knocking ya danyi fir a seconds, baiyi gangancin bude kofar ba saida ta tako da kafarta ta bude kofar, kallonta ya tsaya yi kafin ya kauda kanshi, sanye take da hijab Har kasa da alamu bata dade da idar da sallah ba. "Muje kasa na kawo provisions inason muyi sorting dinsu" Kallonshi ta danyi for a seconds fuskanta babu wani fara'a ta dan tabe baki kafin tace "Ina zuwa" Tana kaiwa nan ta rufe kofar ta shige ciki, Shima kasa ya sauko ya zauna akan kujera yana jiran saukowa ta.
Yan anan zaune saida ta duaka kusan minti ashirin kafin ta sauko, sanye take da Riga da wando na barci wanda yayi mata cif, kanta ta nade shi da hula hannunta ta rike wayanta dashi, babu abunda yake sai baza kamshi don da alamu wanka tayi kafin ta sauko tana saukowa kasan, tana karasowa Ind a yake ta tsaya kikam bata ce mashi komai ba, Already tundaga kan stairs din ya hango ta kafin ya kauda kanshi, ganin harya karaso batace mashi komai ba ya sashi mikewa ya fara duban ledojin yana shugowa dasu kitchen, tana Ganin haka itama ta soma diban ledojin tana nufa kitchen din dasu, yana hangota kuwa yayi saurin amshewa yace "just wait for me inside the kitchen let me do the job of packing it" Yana kaiwa nan ya fuce daga kitchen din, da mamaki take kallonshi, Wai Anya kuwa? Kodai he's possessed ne? Ta tambayi kanta,, tana cikin wannan nazarin sai Gashi ya dawo da wasu ledojin, haka ya dunga fita yana shugowa dasu akan idanunta saida ya gama tass ya rike kugunshi yana kallonta "Wai ashe it's not an easy task, now it's your turn, saiki fadi abunda Zan tayaki" Kauda kai amra tayi bayan ta gama sauraron nashi bata ce mashi komai ba Har lokacin fuskanta babu yabo ba fallasa, haka ta fara bude ledojin tana sorting dinsu ba tare da tace mashi komai ba, "wifey let me help you out" Kai tsaye tace "ka barshi Zan ita ni kadai" "No bazan barki kiyi ke daya ba aikin da yawa zaki gaji, let me help you please" ya karashe yana kashe mata murya wanda yasa batama san tace mashi, "okay Ka saka waennan a fridge" Murmushi kawai yayi don yanxu karantarta yake sosai yana Ganin abunda yake sosai don Ganin abunda yake so da how she react on abubuwan da yake mata. Yau saiga General guda Ana sorting abubuwa a fridge da freezer, dukda ba magana take mashi ba yaji dadin yanda suke ayyuka atare yana taimaka mata Har suka gama sorting komai, tana wanke hannunta ta fuce daga kitchen din, shima hannunshi ya wanke a gaggauce kafin ya futo, lokacin harta kai stairs yayi saurin cewa "wait… ga grilled chicken na sayo" Dan tsayuwa tayi kafin ta dan juyo tace "na koshi saidai zuwa gobe" Tana kaiwa nan ta wuce sama abunta. Ak hanata tafiya ba don haka ya juya wajen dining ya dauka kadan ya wuce dashi kitchen ya saka a cikin fridge don shima a koshen yake….
The next morning…. Da kanta ta Tashi ta wuce kitchen tayi masu breakfast, da farko cikinta kawai taso dafama sai kuma daga baya ta danji babu dadi don koba komai gidan shi take zaune don haka ta daga hardashi ta ajiye mashi a dining ta wuce sama zuwa dakinta. Amar kuwa sai wajen karfe goma sha daya ya Tashi, wanka kawai yayi ya sauya kaya zuwa na zaman gida kafun ya fuce daga bedroom din, Kamar kullum bai tsaya ko Ina ba sai kitchen ya hada tea ya fito, da mamaki idanunshi ya sauka kan dining data jera plates din abunci akai da flask sun ruwan zafi mai kyau, ahankali ya soma takowa fuskanshi dauke da murmushi ya soma bude plates din, English breakfast ne tayi pancakes da sausages sai oatmeal a cikin wnai bowl a gefe, saurin ajiye cup din tea din dake hannunshi yayi ya zauna ya fara cin breakfast din, Shida baya cin abunci sosai sai gashi ya tashi da abuncin tass bai rage komai ba, yana gamawa ya dauka plates din da bowl din ya aje a kitchen, Har zai futo yaga ko'ina clean don haka ya wanke plates sun da kanshi don baya son yana bata wahala….
**** Zaune take a bakin gado tana yanke farcenta incoming call ya shugo mata, cikin hanzari ta dauka wayar Ganin sunan anty Madina, Da sallama amra ta dauka wayar tace "anty Madina……. Kun manta dani sai yau" "Sorry my dear Wallahi na shiga busy kwana biyu, na dawo fah, nazo yin wani aiki ne ammah Zan koma," "Dan Allah kin dawo? Kai ammah naji dadi sosai" amra ta amsa ta Dariya Madina tayi kafin tace "Ay dazu na kira hajiya mu gaisa, take shaida min kin tare ma, Toh Masha Allah naji dadi kinyi abun arziki kenan? Na dauka zakiyi taurin kan maki ne" Dan turo baki amra tayi kamar taba gabanta "kai anty Madina, nidai yanxu yaushe zakizo?"
"Ki tura min address din gidan Zan shugo gobe Insha Allah," Madina ta amsa ta daga chan bangaren wayar
"Toh shikenan anty Madina sai kinzo" Sallama sukayi kafin amra ta kashe wayar, ta cigaba da yankan faratan nata.
Karfe buyer na yamma ta sake saukowa kasan don dora dinner, sanye take da doguwar rigar atamfa tayi mata kyau sosai don yanxu tafi saka su sosai ba kamar da ba da take yawa saka doguwar rigar abaya, Wayanta na gefenta ta kunna wata slow music mai dadin saurare don tafi kaunar sauraron irin wannan wakokin don suna bata nishadi sosai, haka kawai saita tsinci kanta tana murmushi idan tana sauraron wakar.
Anatse take komai bayan ta fidda veggies din da zatayi amfani dashi, cikin kwarewa take Sarrafa girkin nata tana dan takawa, gaba daya ta gama shagala a cikin wakar tana miming "love me like you do love love love me like you, touch me like you do touch touch touch like you baby"
Amar dake saukowa daga sama tundaga stairs ya soma jin kamshin abunci ta daya bade duka gidan, daman da yar yunwar shi ya sauko kasan don haka bai tsaya ko Ina ba sai kitchen, lokacin daya shugo kitchen din turus yayi yana kallonta, wani irin murmushi ne ya kubce mashi akan kyakyawan fuskanshi lokaci data daga wooden spatula da take juya abunci dashi tana rausaya "love me like you do baby….oh touch me like you do baby" Kama habar bakinshi yayi yana admiring dinta Har baisan lokacin da dariya ya kubce mashi ba, a furgice ta juyo don bata san da tsayuwar shi a wajen ba, bin kykyawar fuskarshi ta soma yi da kallo, inda yake shafa sajensa yana bitting lower lip dinshi harya shigo cikin kitchen din yace "daman jin iya waqa haka? Looks like you're enjoying your moment ki cigaba da abunki please Inason gani" Wata irin kunya ce ta luluba ta saidai da yake ita din Akwai kafiya don hakan ta matse fuska ta kashe waqar gaba daya ta fara kokarin futa daga kitchen din, saida tazo dab da Ind a yake ya sanya hannushi ya rike hannunta gentle ya soma magana anatse "oh noo please, saboda nazo ne zaki gudu? Bari na futa tohm ki cigaba da abunki" yana kaiwa nan ya fuce daga cikin kitchen din. Bun bayanshi tayi da kallo harya fuce kafin ta koma bakin gas cooker ta tsaya tana wani tunani…..
Koda ta gama dafa abunci, a cikin warmer ta zuba mashi ta wuce dining ta ajiye mashi kafin ta wuce kitchen din, tana shiga ta fiddo da plates da serving spoon da cokali Harda juice mai sanyi a jug kafin ta futo ta sake jerawa a dining din, already an kira sallan son haka ta tattara kitchen din ta wuce sama, sabon wanka ta sakeyi kafin ta dauro alwala, tana futowa ta shirya a gaggauce ta zura hijab dinta ta fada kabbara, saida ta tsaya tayi sallar isha'i tana idarwa ta mike tsaye ta janyo wayarta ta fuce daga dakin, anatse take saukowa kasa harta karaso wajen dining din, Duban abunci da zai ishi cikin ta tayi tana gamawa ta nufi hanyar stairs, a daidai nan ya shugo cikin gidan anatse, daga nesa ya hangota harta wuce sama,
Shima bai hau saman ba saida ya tsaya ya ci delica dun data daga masu kafin ya wuce sama, Part dinta ya fara tsayawa yayi knocking, tana budewa ya kalleta daga Sam shar kasa, sanye take da wasu silk kayan barci pink doguwar Riga, kanta babu wani dan kwali, Skin dinta sai sheki yakeyi wanda yasa ya kasa duake idnaunshi akanta, saida ta kafe shi da ido tace "Yadai?" "Sorry uhm, Zan ita samun coffee please" Gyra tsayuwar ta tayi sai kawai wnai irin murmushi ya kubce mata kafin ta hade rai, "wato yana son yayi using trick dinshi na kai mashi coffee daki kenan? Lallai ma ya…" Katse mata tunanin nata yayi ta hanyar cewa "idan zai samu ki ajiye min akan dining Zan sauko na dauka thanks wifey, goodnight" Yana kaiwa nan ya wuce sama, da mamanki take kallon shi harya bace mata da gani, meysa Yanxu Duk abunda taje tunanin akai bashi yake yi ba? Kodai wasa yake mata da tunaninta ne? What sort of game is he playing yanxu kuma" Haka ta tsaya tana tambayar kanta ganin babu mai bata amsa yasa ta rufe dakin ta wuce cikin bedroom din, Daukan plate din data gama cin abunci tayi ta sauko kasa, within 5min ta hada mashi coffee a cikin mug, tana gamawa ta ajiye mashi akan dining kafin ta wuce daki ta rufe kofar ta ta kwanta abunta.
Amar dake tsaye a dakin sa tsawon minti goma yana zarya hoping zatayi tunanin kawo mashi daki saijin shuru yayi, Murmushi kawai yayi yana tausasa kanshi don baya son takurata don haka ya sauko kasan da kanshi, yana zuwa kuwa ya tadda ta hada mashi coffee din ta ajiye kamar yanda yace, daukan coffe sun kawai yayi ya wuce sama yana cije lebe yana murmushi,
Washe gari sunday, baije ko'ina ba yana zaune a gida, kwata kwata baima ganta ba yau da safe don bata sauko ba, yana shirin hawa saman ne saigata ta sauko kasa, sanye take da abaya yau, tayi kyau sosai don ko mayafin abayar bata saka ba, fuskanta fayau babu komai akan fuskan nata, Batama Lura dashi ba din haka ta wuce kitchen ta hada tea ta fito tana ya tsine fuska, Tana shirin hawa saman ya tako inda yake sai alokacin ta Lura dashi ma "good morning, meysa baki sauko da wuri ba yau?" Wani irin kallo ta mashi kafin tace "banyi raayin sauko wan bane" Tana karashe wa ta dan cije Bakinta saboda ciwon marar data Tashi dashi dukda yanxu ciwon ya ragu sosai ba kamar da ba, Dan shuru yayi kafin yace "are sure you're okay?" "If I'm not zaka ga na sauko ne? Waima tsaya meysa zaka damu?tun adaa baka damu ba sai yanxu ne zaka dunga nuna min Ka wani damu dani, nifa bari kaji Wallahi I hate abubuwa da kakeyi, stop pretending to be nice baya maka kyau ma, Ka koma yanda kake kawai don ni ban ganema wannan actions din naka ba"
Knocking din da akayi ne yasa ta dan jinkirta kafin ta gifta ta gefenshi ta wuce sama abunta, yana kallo ta wuce sama baice mata komai ba haka zalika Baiji haushin ta ba saima murmushi kawai yayi ta gefen baki "I never knew masu shuru shurun nan rigima ne dasu" Wani knocking sun aka sakeyi wanda yasa ya wuce wajen kofar, yana bude kofar yaga security a tsaye "morning sir, Akwai wata baquwa tace she's here to see ma'am" "What's her name?" Amar ya tambaya "Take sunanta Madina" Shuru Amar yayi don kamar ya san sunan saidai bai gane ko wacece ba don haka yace "okay let her in" Yana kaiwa nan yabar kofar a bude, nan amra ta sauko hannunta rike da cup din data hau saman dashi, kitchen ta wuce direct ba tare da ta kalleshi ba, tana futowa daga kitchen din ta nufi janye stairs, saurin tsaidata yayi "I'm sorry if na bata maki rai okay? Bakyason Ina tambayar lafiyar ki ne?" "Yes please, bana son waennan Abubuwan da kake yi, stop being nice to me tunda I didn't ask for it," Marairaice fuska yayi yace "Tohm na bari kin hakura?" Ya tambayeta yana kallonta, Gyaran murya da akayi ne yasa suka saiga gaba dayansu, Madina da tun da suka fara magana ta shugo, ta tsaya daga bakin kofa, tana kasa motsawa saboda wani irin tukukun baqin ciki daya turniketa akan abunda amra keyi, bata taba sanin amra bata da hankali ba sai yanxu, namiji na binki kina yin abunda kikaga dama Wai Harda ya daina nuna kulawar shi a gareta abunda mata da yawa suke lacking a gidajensu kenan ita kuwa da Allah ya bata shine take neman yin iskanci, babu abunda Madina keyi sai cije lebe tan takaici ta, Ganin tana shirin tafka shirme yasa Tayi saurin gyara murya,