Auren wata ukku by sameena - Chapter 24
Auren wata ukku by sameena Chapter 24: Auren wata ukku by sameena Chapter 24. Hisham ya girgiza Kai "No Haidar. Wann Abu ne da zai shafi rayuwarka. Ba…
4,472 words
Hisham ya girgiza Kai "No Haidar. Wann Abu ne da zai shafi rayuwarka. Ba rayuwar ahalinka kawai ba.." Yai maganar cikeda nuna kulawa.
"My life is already a circus Hisham." Haidar ya basa amsa Kai tsaye.
Hisham ya d'an lumshe ido had'ida girgiza Kai "No Haidar. You have no idea what you are talking about.. Haidar na taso not knowing wanene mahaifina. Ban San me ya faru a shekarun baya ba. Bansan menene tsakanin mahaifina da mahaifiyata ba.. Bansan meyasa ta b'oye min shi ba. Iyakacin abinda na sani shine ta sanar Dani ya Mutu. Ko danginsa tak'i ta nuna mun. Rashin sanin mahaifina da asalinsa yayi affecting dina Haidar. And I am the one paying the price. Rashin sanin asalina ya janyo min setback da dama a rayuwa. Ka yarda dani." Ya k'arashe cikeda kulawa. Ya d'ago yana duban Haidar sosai "Haidar bana so irin abinda ya sameni ya sameka. Please mubi komai a hankali."
Girgiza masa Kai Haidar yai "At this point ban damu ba Hisham.! I'm so tired of everything.!"
Rufe bakin Haidar keda wuya suka hangi Mommy da Anisa na fitowa daga mota.
Haidar ya kafe Mommy da ido yana jinina Kai. Lokaci guda yake fad'i ma Hisham "Don't let that woman escape. I'll be back soon." Yana ida fad'in haka ya nufi motarsa cikin sassarfa. Hisham na bin bayansa yana tambayarsa ina zai je shi amma inaa ko zarafin amsa shi Haidar bai samu ba sai ma fuzgar motar da yai ya bar wajen.
Hisham ya dawo da baya yana girgiza Kai yasan shawo kan Haidar ai abu cikin lallama ba k'aramin aiki bane.
**
A can company kuwa Daddy ya dubi Alhaji Gimba Ya kuma girgiza kai "Ni Aliyu Maitama ne zan d'auki k'afa na tafi asibiti duba yarinyar da Kwaise taima Haidar auren wasan yara da ita Gimba.? What for..?"
"Because she's family. D'anka yana aurenta.. Inaga ta cancanci muje mu dubata." Alhaji Gimba Ya basa amsa kai tsaye.
Daddy ya kuma girgiza kai "If it were up to me, ban damu Haidar yai aure ko kar yai aure ba in the first place. Dan haka ban damu da sanin halinda Haidar ka iya kasancewa ciki ba balle yarinyar da kwaise tai masa auren shiririta da ita. Iyakacin abinda yake gaba na shine my business and my company. As long as matsalolinsu bazai affecting d'aya cikin biyun nan ba. Ban damu ba Gimba.!"
Kafin Daddy ya rufe baki Sakatariyarsa ta shigo a birkice tana nuna masa tablet din dake hannunta "Sir I'm sorry but you need to see this." Ta k'arashe tana nuna masa fuskar tablet d'in yanda Daddy yaga hoton Haidar an had'a da wani hoto na amarya amma babu fuskar amaryar sai na Haidar. Saman article din an rubuta *Shahararren D'ankasuwan nan Engr Aliyu Maitama yayi auren sirri ma tilon D'ansa. Kawo wann lokaci Babu Wanda yasan wacece Amaryar ko 'yar waye. Shin Aliyu Maitama ya aura ma D'ansa 'yar d'aya daga cikin abokan adawarsa na kasuwanci ne dan ya ceci Kampaninsa?*
"Damn it.!" Daddy ya furta a hankali. Ya juyo yana duban Alhaji Gimba "Ka gani ko.! kaga abinda nake fad'a maka ko. Wann yaron brings nothing to me but trouble."
Alhaji Gimba Ya girgiza kai yana kallon labarin "Yanzu zaka yarda da batu na da nace da kai mu tafi asibitin. Rashin nuna damuwarka zai janyo hankalin press garemu. Idan son samu ne yarinyar tana warkewa ka kira koda kwaryakwaryar walima ce tsakanin business partners dinmu ka sanar da Auren D'anka."
Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad'in bazai bari Haidar Ya tarwasta shi ba. A fusce ya fice Alhaji Gimba na take masa baya.
**
A can asibiti kuwa Haidar ne ya k'araso da yan sanda har guda biyu. Hisham na ganinsa da yansanda ya mik'e yana girgiza kai "No.. This is not happening.! Haidar mai kake shirin aikatawa.?"
Duk k'ok'arin Hisham na ganin Ya dakatar da Haidar bai nasara ba har saida Haidar d'in Ya kutsa kai cikin recovery room da aka aje Ummul.
Hisham yai wani irin burki zuciyarsa na bugawa sakamakon hango mutum da yai kwance saman gado. Dukda na'urar oxygen dake saman hancinta bai hana zuciyarsa bugawa sau uku a jere ba. Ji yai Ya kasa jurewa Har saida k'afafunsa suka kaisa gaban gadon. A daidai lokacin da Anisa harma da Mommy suke duban Haidar cikin tsananin mamaki Wanda shigowarsa dakin kenan ga yansanda biye dashi.
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*
*34*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy "Kina iya sanar da D'anki zunubanki idan kinso. I'll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D'anki ku min sanadi ba ." Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice.
Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga mahaifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k'afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata "Tell me Mommy. Wacece Fannah.?"
Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D'an nata kafin ta jinina Kai "She… She was your Dad's wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu."
Haidar ya jinina Kai a hankali "So Daddy yanada wata matar a baya.?"
Mommy ta jinina Kai a hankali.
"What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.?"
Mommy ta girgiza Kai a hankali "I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba."
"Meyasa kika nemeta.?" Ya kuma jefo ma Mommy tambaya.
Ta d'ago tana dubansa "Dan na nemi yafiyarta."
Ya kuma jinjina Kai "So tell me Mommy. Mai kika aikata mata.?"
Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai "Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin… Watak'ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D'ah na." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido.
Waiwaye…
Years back..! Borno State, Maiduguri.
Hajiya Kwaise zaune saman kujera a madaidaicin parlorn ta Wanda ya tsaru iyaka tsaruwa a wancan lokacin. Kuka take sharshar da hawaye a lokacin da taji sautin wayar landline na gidan na kururuwa. Ta mik'e da kyar ta isa ta daga wayar. Daga d'aya b'angaren muryar Aliyu Maitama ta sinkayo "Kwaise an d'aura auren.. An daura auren.. An daura aurena da Fannah.." Yanda yake maganar zaka fahimci kaman Wanda aka saka shi dole haka yake maganar. Bata k'arasa sauraro ba ta saki wayar ya fad'i kasa tana mai kuma rushewa da kuka. A haka Asshe ta k'araso ta sameta. Asshe k'anwarta da tin bayan da Kwaise tai aure rik'on Asshe ta dawo hannunta dama ba wani girme mata sosai tai ba kuma su biyu iyayensu suka Haifa.
Mommy ta dago tana duban Asshe cikin rawar murya "Asshe Aliyu yayi aure.. Aliyu ya auri d'iyar leburan dake aiki k'arkashinsa Wanda block na gini ya fado ya fasa masa Kai ya rasa ransa dalilin haka. Asshe Aliyu na ya aure 'yar wann mutumin..!" Ta kuma rushewa da kuka.
Asshe ta dubeta cikeda tausayawa "Aunty Kwaise mijinki loves you. Wllhi koda ace yayi aure bazai daina sonki ba. Ni fah ban taba ganin wacce mijinta ke mata irin Son da Uncle Engr ke Miki ba. He loves you dearly. Zai komai dan farin cikin ki Aunty Kwaise. Keda kanki kin fada Aurensa da wann yarinyar Fannah k'addara ce kawai batada kowa bayan mahaifinta da ya Mutu ta dalilin aiki k'ark'ashin ma'aikatan mijinki da yake. Wllhi na tabbata dan ya taimaketa ya aureta. Ba wai dan yana So ba ko dan ya daina sonki. Idan ba so da mijinki ke Miki ba. Mutum kaman Engr Aliyu matashi mai tashen kud'i ga k'uruciya ga dama na rayuwa da ya samu ai da tuni ya cika gidan nan da mata sai yanzu da k'addarar hakan tazo. Dan Allah kar ki saka wani Abu a ranki."
Mommy ta dago tana share hawaye "Asshe bazaki taba ganewa ba. Namiji Akan mace sunansa namiji bazakiyi shaidarsa ba. Nidai bazan iya sharing Mijina da wata ba balle wann bagidajiyar 'yar lebura."
Asshe ta furzar da huci "Toh ya kike so ai yanzu.?"
Mommy bata iya bata amsa ba sai mik'ewa da tai ta shige k'uryar daki wani sabon kuka na taso mata. Haka ta yini a daki bata aikin komai sai kuka. Asshe ke Lek'ata lokaci zuwa lokaci. Ko abinci Mommy ta kasa ci ranan.
Can dare taji shigowar motar mijinta. Nan ta Mike da sauri tana lek'en window. Hangosa tai tareda Amaryar sa tana biye dashi kanta a k'asa. A haka suka shigo har parlorn gidan.
Koda Daddy ya shigo ya tadda Mommy juya masa baya tai. Ya k'araso jikinsa duk a mace "Kwaise. My love.." Sai ya kasa ci gaba da magana yayinda kukan Mommy ya karu.
A hankali ya isa ya rungumeta ta baya. Su duka biyun hawaye na gangaro masu. Cikin kwantar da hankali yake furta "Wann shine k'addarar mu Kwaise. Allah ya k'addari Fannah zata shigo cikin rayuwarmu. Yarinyar abun tausayi ce bata da kowa sai mahaifinta da ya rasu sakamakon aikin da yake k'ark'ashina.
Mommy na hawaye take girgiza Kai "Ba hurumi na bane na tuhumeka dan ka k'ara aure Aliyu. Addini ya halatta maka auren mata d'ai d'ai har hudu idan kanada hali. Kawai alfarmar da zan rok'a daga gareka shine Kai Adalci tsakaninmu."
Ya murmusa yana dubanta. Ya saka hannunsa ya share hawayen da suka gangaro mata "I love you Kwaise.. So much..! Ban tab'a son wata mace sama dake a rayuwata ba. Ki tayani addu'a Allah ya bani ikon yin Adalci tsakaninku because.. I'm not sure idan son da nake Miki zai barni na kamanta adalci.. Kwaise ba kece cikin tashin hankali ba. Ni ne cikin tashin hankali.. Because son da nake miki baida match da ko wace mace. When it comes to you wayona baida yawa Kwaise."
Mommy ta tsaresa da ido kafin ta k'ak'aro murmushi ta riko hannayensa "You can do this in sha Allah mijina. I'm here for you.. Tashi na shiryaka amarya tana jira."
Kaman rak'umi da akala haka Daddy ya Mike Mommy ta shiryawa tsaf harda su fesa turare kaman ba ita ce ta yini kuka a daki ba.
Koda suka fito suka tadda amarya ma Mommy bata nuna komai ba. Asshe taita mamakin canzawan 'Yaruwar tata. A haka rayuwa ke tafiya masu Mommy bata nuna komai ga Daddy ya saki jiki ganin hankalin Kwaise ya kwanta. Ya maida hankali kan bunk'asa k'aramin kampaninsa a nan birnin Maiduguri da Kewaye.
Watan Fannah biyu a gidan ta fara nuna alamun masu juna biyu. Kwaise da kanta ta dauketa ta kaita asibiti akai mata gwaji aka tabbata tana d'aukeda karamin ciki na tsawon watanni biyu. Sosai Mommy ta nuna marnanta har kaman tafi Fannah murna. Lokacin Daddy na cuku cukun Kai Kasuwancinsa tsakanin Abuja da wasu jihohi Mommy da kanta tai masa Albishir na cikin da amaryarsa ke dashi sanda sukai waya tinda shi a wann lokacin ya rage zaman Maiduguri. Farin ciki wajen Aliyu Maitama baya misaltuwa. A wann lokacin yai ma matan nasa kyauta ta sabuwar mota dal 'yar yayi a wancan lokacin. Ya kuma d'ebesu gaba daya suka tafi Umra suka gode ma Allah da kyautar da yai masu dan a lokacin aurensa da Kwaise kusan shekaru biyar kenan babu rabo saida Fannah ta shigo sai gashi ta samu daga shigowarta.
Bayan dawowar su daga Umra Daddy ya tafiya ta kasuwanci da zai d'aukesa kusan wata guda.
Asshe ta dubi Mommy wacce keta faman sakin murmushi tana gustiran Apple. Ta d'an girgiza Kai tace "Kenan kin yarda ta rigaki Haifa masa Magaji Aunty Kwaise.? Ni fah kirkikin da kike ma matar nan tai yawa. Ke kaman bakijin kishi irin na mata da ake fad'a."
Murmusawa Mommy tai "Asshe kenan. Sarai nasan abinda nake kuma lokaci yayi da zan executing plan dina. Trust me."
Asshe ta girgiza Kai "Toh amma Aunty Kwaise mai zakiyi yanzu.?"
"Wann cikin da Aliyu Maitama ke rawar k'afa akansa da Kansa zai sheganta sa tin a ciki kafin a haifosa. Zai ma Fannah korar wulak'anci. Wann cikin kuma Engr Aliyu Maitama bazai taba accepting dinsa ba."
Asshe ta girgiza Kai "Amma ta ya zakiyi hakan.?"
Mommy ta kuma gyara zama "Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila'ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya ganta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake aiki k'ark'ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka masa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan ance har gobe yana mutuwan sonta."
Asshe ta sauk'e ajiyan zuciya "Toh ya abin zai kasance.?"
Mommy ta kuma murmusawa "Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K'anwata."
Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta "Kaman ya kenan Anty Kwaise.? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan."
Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu Maitama zai dawo gari ya kamasa a d'akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne." Ta k'arashe tana sakin murmushi.
Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin Fannah yai ba tareda kowa ya gansa ba.
Fannah da fitowarta kenan daga band'aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet da gajeren wando. Jikinta ya d'auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had'ida toshe bakinta da k'arfin gaske. Fannah tana kuka tana k'ok'arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta.
Daddy ya dawo cikeda d'oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b'angaren ta d'aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k'ato rungume da matarsa dake d'aure da towel ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa.
Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad'in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amincewarta ba fyade yai mata.
Daddy ya shak'osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b'acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d'aure jikinta. Ta dawo ga Daddy tana fad'in "Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba."
Daddy ya dubeta da mamaki "Dama ya Saba zuwa.?!"
Mommy ta jinjina Kai kaman gaske "Ai idan Baka nan yakan zo. Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa."
Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace "A'ah.. Wann mutumin ai mak'ocin su k'awata Baana ce. Kuma ta…" Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana.
Mommy tace "Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?"
"Ta sanar dani shi d'in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu… Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!"
Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k'arfin ta "Haka ne.? Wann D'an iskan saurayinki ne.?!" Ya tambaya yana dubanta.
Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa "Ki amsa min..! Haka ne..!"
Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad'in "Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk'ar so. Kuma mahaifinta ya min alk'awarin bani ita.. Amma 'yanuwanta Sun karya wann alk'awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu'amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..!" Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b'arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka.
Daddy ya ci gaba da huci "Ga b'arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la'akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk'a sa ma shayibu yana fad'in bari yaje ya duba section d'insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d'insa na cikin gidan an kwashe kud'ad'en ciki.
Koda aka mik'a Auwalu ma 'yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud'ad'en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud'ad'en dan su gudu su bar gari.
Daddy bai saurara daga b'angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar.
Sosai take kuka duk'e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta "Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari." Yana ida fad'in haka ya mik'e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari. 'Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad'in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k'ila da an fara k'irga ma abinda ta haifa watanni.
Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k'ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sam bata San Daddy ya shigo ba take b'arin zance.
Daddy ya dubeta da mamaki "Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!"
Sai Mommy ta mik'e tana girgiza Kai "A'a Engr dan Allah ka saurareni."
"Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud'e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma mata..? Kece kika shirya komai..?!"
Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai "Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba.."
Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa.
Mik'ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d'inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d'aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab'akar da tai sabida halin k'unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu'amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k'unci hopping idan ta haihu zuwan D'an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa "See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d'an da zakai alfahari dashi."
Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin.
Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik'e cikin hannunta baiba balle ya karb'e sa. Sai ma mik'ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D'anta sai hidiman bunk'asa Kasuwancinsa da yake. K'unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d'awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D'anta da Daddy yai take. Ta duk'ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d'an matsayin D'a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta'allak'a ga bunk'asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad'ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab'a ganin k'ok'arin Haidar ba har kawo girman sa.
Wann kenan.
(Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan 'ya'ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da 'ya'yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa).
* Ci gaban labari..
Haidar ya share hawayen da suka zubo masa "So that's the reason why he hates me.!" Ya fad'i haka Kansa a kife.
Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata "No Haidar.. Your Dad doesn't hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That's just.. his way of punishing me.!"
"Well I don't care.!" Ya fad'i haka yana mai buga teburin gabansa da k'arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad'in "I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.!" Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake.
Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai "I'm sorry my Son.. I'm sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!"
Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d'agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa.
Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta "Serving jail sentences won't be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won't rest until I see you locked up in jail.. Koda zaki k'arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don't want to see your face ever again.!" Ya k'arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik'e ya nufi k'ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k'ofa ya fice cikin tsananin huci..
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*
*34*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy "Kina iya sanar da D'anki zunubanki idan kinso. I'll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D'anki ku min sanadi ba ." Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice.
Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga mahaifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k'afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata "Tell me Mommy. Wacece Fannah.?"
Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D'an nata kafin ta jinina Kai "She… She was your Dad's wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu."
Haidar ya jinina Kai a hankali "So Daddy yanada wata matar a baya.?"
Mommy ta jinina Kai a hankali.
"What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.?"
Mommy ta girgiza Kai a hankali "I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba."
"Meyasa kika nemeta.?" Ya kuma jefo ma Mommy tambaya.
Ta d'ago tana dubansa "Dan na nemi yafiyarta."
Ya kuma jinjina Kai "So tell me Mommy. Mai kika aikata mata.?"
Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai "Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin… Watak'ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D'ah na." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido.
Waiwaye…
Years back..! Borno State, Maiduguri.