Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 29

Auren wata ukku by sameena - Chapter 29

Auren wata ukku by sameena Chapter 29: Auren wata ukku by sameena Chapter 29. Alhaji Gimba Ya dubesa da mamaki cikin gaza b'oye farin cikinsa na decision…

4,469 words

Alhaji Gimba Ya dubesa da mamaki cikin gaza b'oye farin cikinsa na decision d'in da Engr ya dauka na tsayuwa a asibiti wajen ahalinsa. Hakan na nufin Engr ya zab'i D'ansa sama da kampaninsa da Kasuwancinsa for the first time. Cikin sauri ya soma jinjina Kai "Kar ka samu damuwa abokina.. zan je na kula da komai a can.. You stay here.. Your family needs you." Ya k'arashe cikin k'ok'arin k'arfafa ma Daddy gwiwa Wanda Sam k'arfin halinsa ya hana ya nuna tsananin damuwarsa.

Kai dubansa ga yanda su Mommy ke zaune yai bayan Alhaji Gimba ya shige. Anisa sai k'ok'arin calming d'inta take da kalamai masu kwantar da hankali cewa Haidar harma da Ummul zasu samu lafiya. Mik'ewa Anisa tai tana duban Mommy wacce har lokacin bata cewa komai sai hawaye dake gangaro mata "I'll.. bring you some water Mommy." Ta k'arashe tana mai shigewa.

Bayan Anisa ta shige k'uri Daddy yaima Mommy k'uri daga nan yanda yake tsaye. Yana kallon yanda take cazgan kuka mai tsuma zuciya. Tin bayan abinda ya faru tsakaninsa da Kwaise zai iya cewa bai sake Jin ya damu da wani damuwa da ya danganceta cikin zuciyarsa ba musamman idan abun ya shafeta ita da D'anta ne. Amma yau d'in sai yaji har k'asan zuciyarsa na jin zafin kukan da Kwaise take. Har cikin zuciyarsa yana so ya k'arasa gareta ya rungumeta cikin jikinsa amma sai yana jin bazai iya hakan ba. Lumshe idanunsa yai yana mai barin wajen cikin sauri dan Sam bai son sauraren kukan da take. It hurts him a lot.

A can waje kuwa koda Anisa ta fita sun samu sun keb'e da Hisham. Ta kuma dubansa a hasale "You know your IQ doesn't work at all. Waima how many gb akan nan naka..?"

Katseta yai kaman zai mak'ureta "Don't you dare insult me. It was your idea from the very start.. Kece kika kawo shawarin a shirya masa hatsari.. If there's someone to be blamed here that should be you."

Anisa na huci take nuna sa "Kai addu'a kar wani abu ya samu Haidar.. Dan wllhi idan wani abu ya samu Haidar sai na tona maka asiri.!"

Murmushi Hisham yake da gefen baki "If that's a threat, I suggest ki ajiye sa zuwa anjima har muji wani yanayi Ummul ke ciki. Dan na miki alk'awari idan har wani abu ya sameta.. Zakiyi d'andanasanin sanina..!" Ya k'arashe jijiyoyin fuskarsa suna mimmik'ewa.

Anisa ta zaro ido tana duban Hisham cikeda mamakin irin son da yake ma Ummul. furzar da huci tai hadida rausayar da ido dan bazata basa daman ganin gazawarra ba "Let's not waste time pointing fingers at each other.. Bazai taimakemu ba.. I thought da ka shirya hatsarin zaka d'auki Ummul ka gudu da ita.. I thought you said you wanted to be with her so badly. Maiyasa kai wasa da damarka. Maiyasa baka saceta ba kowa Ya huta.?!" Ta k'arashe tana huci.

Murmushi yake da gefen baki yana dubanta "You think I'm stupid.?" Ya kuma murmusawa yana duban Anisa "To tell you the truth, I was the anonymous person da ya k'ira company ya sanar da hatsarin nasu." Ya jinjina Kai yana ci gaba da murmushi "Ina gefe ina kallon komai har yan kwanakwana suka kawo masu dauki.. Daidai da dak'ik'a guda ban bar wajen ba. I had to make sure sun samu taimako na gaggawa right away.!"

Ya kuma murmusawa yana kallon Anisa da ta zama confused tana duban makirci da ya dama nata. Hisham yaci gaba "Alak'a mai kyau mai tsafta mai cikeda yarda nake son k'ullawa da Ummul Wanda Babu algus cikinsa. And believe me na shirya hakan. Bazan tab'a bari ta zargi soyayyar da nake mata ba.. She will come to me willingly.. And she will accept me ba tareda wani ya tilasta mata ba.. Kin fahimta.?!"

Anisa ta tsaresa da ido sai kuma ta girgiza kai "I hope it happens very soon.!" Tana ida fad'in haka tasa Kai ta shige tana huci.

A yanda ta bar Mommy nan ta sameta har lokacin matsan hawaye take cikin yanayi mai nunida tsananin tashin hankali.

Anisa tai saurin sauya fuska had'ida daura damuwa saman fuskarta. Ta isa ga Mommy jiki a sanyaye ta zauna gefenta tana mai b'alle bottle water d'in da ta shigo dashi. Ta mik'a ma Mommy a hankali tana fad'in "Mommy have some water."

Girgiza mata Kai Mommy tai cikin zuban hawaye "I can't Anisa. Bazan iya ba.. Bazan iya saka komai a bakina ba tareda sanin halinda Haidar da Ummul ke ciki ba.!"

Anisa ta maidoda hannunta baya cikin sanyin jiki. Ta d'aura hannunta guda saman na Mommy tana k'ak'alo hawaye "Mommy I know you are strong.. In fact, you are the strongest woman I know.. And you are my inspiration.. But sometimes even the strong ones feel vulnerable.. Because we are human beings…" Anisa tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sai ka rantse har cikin zuciyarta Abinda take fad'i haka ne. Taci gaba "Tada hankali da damuwa dole ne.. But what they need the most now it's our prayers.. Addu'o'in mu suke buk'ata fiyeda komai Mommy.. Especially you.. Sabida ke uwa ce.. Mommy kiyi ma Haidar Addu'a.. In sha Allah zasu samu lafiya daga shi har Ummul kinji Mommy."

Hawaye na gangaro ma Mommy sai ta rungume Anisa kuka na kuma zuwa mata. Anisa ta saki murmushin cin nasara da gefen baki. A fili kuwa fad'i take "I'm here for you Mommy.. I'm here..!"

A haka Anisa taci gaba da k'arfafa ma Mommy gwiwa Har kawo zuwa fitowan wani Dr daga hanyar da zai sadaka da ER. Yana tafe yana zame safar hannunsa.

Cikin sauri Mommy ta mik'e Anisa na biyeda ita suka nufi Likitan.

Daddy Wanda shima yaga fitowan Likitan zai nufesa kenan yaga Mommy ta rigasa. Sai yaja Ya dakata Ya tsaya daga bayansu.

"Dr how's my son and his wife..? How are they doing..? Can I see them now.. Can I see my son now.. Please tell me.." Ta k'arashe cikin tsananin kid'imewa.

Dr ya dan girgiza Kai yana duban yanda ta rikice sosai. Ga mutum mai shekaru da Ya d'an soma ja is not good for their health.

Karaf Likitan ya had'a ido da Daddy dake daga gefe. A hankali Daddy ya girgiza masa kai had'ida masa alama da ido alamun kar Ya fad'i wani abinda zai k'ara mata tashin hankali.

Dr ya dan murmusa yace "Kar ki samu damuwa Hajiya.. D'anki harma da matarsa na Miki alk'awari suna samu kyakkyawan kulawa. And fortunately matarsa ta riga ta farka tana d'akin hutu. Shima munada yak'inin in a couple of hours zamu turasa d'akin hutu cikin yardar Ubangiji. There's nothing to be worried about."

Relief ya nuna saman fuskarsa Mommy. Ta soma jinjina kai "Da gaske Dr. Yarana are out of danger.. Zasu samu lafiya.. Ta dubi Anisa dake sakar mata murmushin nuna jin dadi "Zasu samu lafiya in sha Allah."

Ta juyo ta dubi Likitan dake nan tsaye gabansu "Zamu iya ganin Ummul."

Dr ya jinjina mata kai a hankali "Of course you can.. This way please." Ya k'arashe yana nuna mata hanya.

Mommy ta jinjina kai tana mai shigewa Anisa na biyeda ita.

Bayan Sun shige Dr da Daddy suka keb'e a ofishin Likitan.

Dr ya dubi Daddy yace "To be honest, I couldn't tell your wife the real condition of your son."

Daddy ya zuba masa ido. Sai Ya girgiza kai kad'an "Tell me his condition, Dr."

Dr ya jinjina Kai kad'an "He's lost a lot of blood.. But.. Zamu iya cewa he's responding well. That's why we moved him to the ICU… Amma.." Sai ya d'anyi shiru yana duban Daddy kafin ya girgiza Kai kad'an yaci gaba "Komai zai iya faruwa.. Because the first 24hrs is critical.. Let's just pray he wakes up before then. Otherwise, we don't know what might happen." Ya k'arashe yana duban Daddy hadida girgiza Kai alamun hope d'in kad'an ne.

Daddy yai shiru cikin tsananin sanyin jiki tamkar Wanda yai nisa cikin duniyar tunani. Muryar Dr ya sinkayo yana fad'in "Muna buk'akan jini da za'a k'ara masa cikin gaggawa."

Daddy ya dubi Likitan jiki a mace sai Ya jinjina kai "Go ahead Dr.. Just do your job.."

Likita ya girgiza Kai kad'an "Unfortunately bamuda irin jininsa a nan. Mun samu shortage na jinin due its high demand. Ba don muna buk'ata cikin gaggawa ba da zamu iya jira tinda jini da baida wahalan samu. A halinda ake ciki any delay zai iya janyo matsala."

Daddy ya furzar da huci kad'an. Dan shi dai Haidar D'ansa ne amma bai tab'a sanin lafiyarsa rashin lafiyarsa balle wani blood type d'insa. Ya dan girgiza Kai kad'an yace "Dr.. What's his blood type then.?"

Dr ya sanar da Daddy blood group din Haidar.

Shiru Daddy yai kaman mai tunani. Dr zai kuma magana Daddy ya dubesa had'ida katsesa cikin sauri "I have same blood type with him.. I hope zaku iya d'iban nawa."

Dr ya jinjina Kai yana mai sanar da Daddy su k'arasa lab dan suyi aune aune.

A can d'akin da Ummul take kaw. Shigowar Mommy yai daidai da bud'e idonta.

Ta soma k'ok'arin Ware idanunta da suka mata nauyi. Tsaf ta sauk'esu akan Mommy dake karasowa gaban gadon nata.

"Mommy..!" Ummul ta furta cikin murya irinta marassa lafiya.

Mommy ta sakar mata murmushi ta k'araso tana dafa kanta daga nan yanda Ummul d'in ke kwance "'Yata.. Alhamdulillah kin farka. Ya karfin jikin naki..? Mai kike ji yanzu.?"

Ummul ta dubi Mommy tana k'ok'arin tuno abinda Ya faru. Take ta tuna sansa Haidar yace birkin motarsa bata aiki. Ta tuna yayita k'ok'arin ya tsaida motar bai iya ba. Ta tuna sanda motar ta bar saman kwalta Haidar Ya mata rumfa da jikinsa cikin k'ok'arin ganin yayi saving dinta wani abu bai faru da ita ba.. Ta tuna jini da ta hango Ya wanke fuskar Haidar da ya bar saman seat d'insa yai mata rumfa cikin k'ok'arin kareta. Ga idanunsa a lumshe tamkar baya numfashi. Tinda taga Haidar a wann yanayin bata kuma sanin ina kanta yake ba sai farfadowa da ta ta ganta a gadon asibiti. Ta soma girgiza kai hawaye na gangaro mata "Mommy Haidar.. Ina Haidar yake..? Dan Allah ku fad'a mun ya samu sauki.!" Ta soma k'ok'arin mik'ewa tana fad'in "Dan Allah ku kaini wajen shi.. Dan Allah ina so naga Haidar.. Please Mommy..!"

Saurin rik'eta Mommy tai itama din hawaye take. Bata bari Ummul d'in ta bar saman gadon ba take fad'in "Haidar yana can likitoci na kula dashi Ummul. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Kema ba k'oshin lafiya ne dake ba. Look duba kiga ga bandage a goshinki da hannunki."

Cikin zuban hawaye ta katse Mommy da fad'in "A'a Mommy banjin ciwon komai.. Ni Haidar kawai nake son gani dan Allah.." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Anisa dake gefe juya ido rai cikeda takaicin Ummul. Cikin zuciyarta take fad'in ji wani iyayin banza. Sai wani neman ganin Haidar take bata ta kanta. Yaushe ma suka San juna ita Haidar d'in. Makirar banza. Ta kuma juya ido ganin Mommy ta rungume Ummul dake kuka sosai cikin k'ok'arin kwantar mata da hankali dudka Mommyn ma hawaye ke zubo mata.

A can b'angaren Daddy kaw bayan an ida d'iban jininsa an k'ara ma Haidar duban Dr Daddy yai "Doc, I want this to stay between us.. Bana so Matata ta San ni na bama Haidar jini… Ko shi Haidar d'in idan ya farka."

Dr ya jinjina cikin tabbatar ma Daddy baida matsala da hakan.

Daddy ya jinjina kai had'ida masa godiya kafin Ya k'ara da "Can I please, see him now..?"

Dr ya jinjina kai "Sure.. But it should be quick."

Daddy ya jinjina kai yayinda Dr Yai masa jagora zuwa cikin ICU bayan an basa wani rigar kariya da hula harma da nurse mask kafin ya nufo yanda Haidar ke kwance na'ura ta ko ina.

Tin daga nesa jikin Daddy yai matuk'ar sanyin yanda ya hango Haidar kwance cikin buwayar Ubangiji. Yana takowa yana tuna Haidar d'in tin haihuwarsa. Gwagwarmayar rayuwa da Ya fuskanta musamman dasu iyayensa. Ya tuna a lokutan baya sanda yake rige rigen kawo masa sakamakonsa na makaranta da kyauttukan da aka basa amma daidai da rana guda bai tab'a kalla ba balle Ya yabesa. Ya tuna banda hantara tsana da kyara babu abinda ke tsakaninsa da D'an nasa. Ya tuna irin k'ok'ari da yake a company kan duk wani aiki da aka d'aurasa ba dan komai ba sai dan ya tabbata baiyi failing mahaifinsa ba. Still nothing was enough. Ya tuna auren da Kwaise Tai masa Wanda bai saka hannunsa ba balle Ya halarta matsayinsa na tilon D'ansa dukda sanin aure wani gab'a ne mai mahimmanci a rayuwar D'an adam. Haka yaita tuna rayuwarsu na baya Har kawo tattaunawarsu da Alhaji Gimba da yanda Alhaji Gimba yace dashi yai tunani Ya gyara alak'arsa da iyalensa tun kafin Lokaci ya k'ure masa dan Lokaci baya jira. Saiga hawaye na kwararowa daga k'uncin Daddy. Yakai hannunsa dake tsananin rawa yana k'ok'arin Shafa kan Haidar.

Sosai muryarsa ke rawa sanda ya soma fad'i a fili "Aliyu..!" Ya furta a hankali yana shafa kan Haidar d'in. For the very first time da ya tab'a ambaton Haidar da sunan from his heart tin bayan da aka rad'a masa sunan. Daddy yaci gaba "My Son.!" Nan ma karo na farko da Ya ambacesa da D'ansa kai tsaye. Yaci gaba "Shin kasan a ranan da aka haifeka a lokacin da mahaifiyarka ta nuna mun kai a wann rann na samu k'arfin komawa bakin aiki.?" Ya murmusa hawaye na kuma gangaro masa "People might think kasuwanci na da Kampanina sune abinda sukai keeping dina moving.. But the truth is that you were the one that kept me going.. You brought me back my strength koda ban nuna hakan ba." Ya shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa kafin yaci gaba "Meyasa na hukunta ka cikin laifin da ba naka ba Wanda baka da masaniy akai.?" Ya dan numfasa yana kuma shafa kan Haidar d'in "I was so angry at your Mom… That I didn't even realize I wasn't only a husband who's been hurt and betrayed… I was also a father.. Na mance ni mahaifi ne da Allah Ya dank'a mun amana da kiwo Wanda zai tsaidani Ya tambayeni kan wann kiwon.. Nayi abubuwa cikin fushi.. Na d'auki tsangwama da kyara na d'aura akan ka just because you're Kwaise's Son.. Fushi yasa na mance you are also a part me.. My soul… my flesh and blood.." Ya lumshe idonsa hawaye suka kuma gangaro masa "Bai kamata na barka ka shiga cikin matsalolinmu ba. Why are You the one who's suffering the consequences... It shouldn't be this way.. If there is one thing I regret the most shine sake da damata da nai cikin shekarun da Allah Ya albarka ce ni da kai matsayin D'ah…. Forgive me son… Ka yafe mun D'ah na..!" Ya k'arashe kuka na neman cin k'arfinsa. Saida Yai masa addu'o'in samun sauk'i kafin ya baro d'akin duk jikinsa a mace.

A hanyar ficewa suka had'u da Mommy. Daddy ya bita da kallo saidai batace da shi komai ba tasa kai ta shige. Jiki babu k'wari yaja k'afarsa Ya bar wajen.

A yanda Mommy taga Haidar sosai hankalinta Ya tashi. Haka ta kwantar da kanta gefensa tana kuka tana fad'in irin k'aunar da take masa tana fad'in kar Ya tafi ya barta. Hannun Ummul taji saman k'afadarta wacce itama ta kasa hakuri har saida likitoci suka hakura suka barta ta shigo dan taga mijinta.

Ummul na k'ok'arin bama Mommy baki amma sai ta kasa sai k'unshe bakinta tai dan sosai taji kuka na zuwa mata musamman yanda taga Haidar na kwance idanunsa a lumshe ga na'ura ta hanci ta baki.

A hankali kukan Mommy ke tsagaitawa, ta sa hannu tana shafan sumarsa. Murmushi da hawaye saman fuskarta take fad'i da Ummul "Tin lokacin da yake ciki rayuwarmu ta sauya. Na shiga matsansncin damuwa.. And maybe that's why he was so tiny lokacin da na haife shi… Amma dukda haka he was strong, a fighter.." Ta kuma murmusawa tana hawaye "Sann Koda ya zama cikakken mutum mai cika ido da kyaun k'ira bai huta ba.. Tin haihuwarsa baisan wani farin ciki ba.. And that's all my fault.." Ta k'arashe tana share hawayen da suka zubo mata. Taci gaba "Meyasa nake ji kaman laifuka na yake biya..?"

Saurin girgiza mata kai Ummul tai "Kar kice haka Mommy.. Bawa baya wuce k'addararsa a rayuwa. Duk abinda ke faruwa muk'addari ne daga Allah. Wasu abubuwan suna faruwa ne cikin rayuwarmu domin su zamto mana darasi. Ubangijinmu zai jarancemu ta ko wata fuska. Muyi ma Haidar addu'a Allah Ya tashi kafad'unsa Ya basa lafiya.."

Mommy ta jinjina mata kai tana mai rik'e hannun Ummul d'in cikin nata. Ummul ta kamo hannayen Mommy sosai tana fad'in "Muje ki huta Mommy. Zan tsaya a nan na kula da Haidar.."

Mommy ta jinjina mata kai a hankali tana mai goge hawayen da suka zubo mata. Haka Ummul ta rik'o hannunta har suka fito dikda itama ga rauni jikinta. A nan k'ofa suka had'uda Anisa. Ummul ta mik'a ma Anisa hannun Mommy tana fad'in ta kula da ita tana buk'atan hutu.

Anisa ta jinina kai tana fad'in "Ummul is right.. You need to have some rest Mommy.. this isn't good for your health.. Haidar bazai so ya farka yaga kema ba lafiya ba.. Muje Mommy.." Ta k'arashe tana rik'o Mommyn wacce da gani tafiyar kawai take.

Suna shigewa Ummul ta koma cikin ICU d'in. Ta jima tana kallon Haidar dake kwance tana tuno yanda had'arin nasu Ya kasance. A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata. Ta janyo kujera ta zauna nan gaban gadon nasa. Kallonsa take tana tuna yanda aurensu Ya kasance Wanda ko sanin wanene shi balle kamanninsa batai ba farko. Ta tuna lokacin da ta shak'i poison Dr ya sanar da ita yanda Haidar Ya kula da ita. Ta tuna d'auketa da yai Ya kaita wann gidan Ya kulle.. Ta tuna yanda yai fitar da Mommy da kansa daga hannun 'yansanda Wanda a baya ya dage sai an kulleta a prison. Ta tuna tattaunawarsu kafin Had'arin Ya faru yanda yace mata bazai saceta ba kuma bazai sake rufeta ba sann zai sawwak'a mata tai tafiyarta shima zai tafi zai tafiya mai nisa far from everyone and everything. Ta tuna sanda hadarin ke faruwa yanda ya finciki seatbelt d'insa yai tsalle daga nasa kujeran yai mata rumfa cikin k'ok'arin kareta. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Bayan mahaifinta bataji akwai wani D'an adam da Ya tab'a ba ma rayuwarta mahimmanci irin haka. Ta bud'e lumsassun idanunta masu zuban ruwa tana kallonsa. A hankali ta soma k'ok'arin kai hannunta dake rawa ta d'aura saman nasa hannun. A hankali take furta "A lokacin da Umma ta shirya aurena da kai na shiga damuwa da tashin hankali na rashin sanin wanene zata aura mun." Ta kuma goge hawayen da suka gangaro mata "Ban tsammaci farin ciki ko wani rayuwa mai inganci cikin auren ba kama daga mutanen da shafin rayuwa zata had'ani dasu Har zuwa mijin." Ta k'ura masa ido hawaye na kuma gangaro mata "Shin kasan kowa gudu na yake.? Ni Ummulkhairi ban tab's tsammanin akwai wani D'anadam da zai fifita rayuwata sama da nashi ba. Koda ace akwai ban tab'a tsammani daga wajen mutum irinka ba. Wanda na tabbata ka fini a komai sau babu adadi. Sann mu biyun duniyar mu sun banbanta. Haka ne.?" Ta kuma jinjina kai tana hawaye "Dole ce tasa na danne nawa raunin gaban Mommy dan na bata k'warin gwiwa.. Amma kasan me..? Banida wani k'warin gwiwa.. Dan Allah ka tashi kaji.. Ka tashi..!" Ta k'arashe kuka na neman b'alle mata da gaske. Tai k'ok'arin saita kanta kafin ta kuma dubansa murmushi da hawaye saman fuskarta "A koda yaushe kana kiran kanka Monster.. Ni kuma ina fad'a maka kai ba mugu bane.. Mugu bazai tab'a zama mai kyakkyawan zuciya wanda ke saka damuwar wasu sama da nasa irinka ba. Yau d'in na kuma yarda da haka bayan abinda ka mun.. Watak'ila da baka zab'i ka bani kariya ba Watak'ila da ni ce zan kasance nan a kwance ba kai ba..!" Ta share hawayen da suka ziraro mata. Ta kuma daura yatsun hannunta saman nasa "Ina tareda kai.. Zaka samu lafiya cikin k'udurar Ubangiji.. Allah Ya baka lafiya…SweetMonster..!" Ta k'arashe tana mai kwantar da kanta gefensa kad'an.

**

Kano…

Hilal na Ida parking Ya juyo ya dubi Umma dake zaune bayan motar. Murmushi Ya saki kad'an "Umma mun iso.."

Umma ta sauk'e ajiyan zuciya tana dubansa "Hilal.. Na haneka kak'i ji.. Mai zai faru idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata.?"

Ya d'an girgiza kai kad'an "Ammi bazata sani ba Umma. Taimako nayi niyyan yi kaman yanda kema taimakon kikayi. Ina addu'an Allah Ya had'a mu cikin lada."

Umma ta sauk'e ajiyan zuciya kad'an tace "Ameen Hilal d'an albarka. Mu k'arasa ko."

Hilal Ya jinjina kai yana mai fitowa had'ida bud'e ma Umma k'ofa.

A daidai lokacin motan Ashshe dake biye dasu ba tareda saninsu ba ta iso wajen. Ta bama driver umarni da yai parking can gefe dasu.

Sai huci take tana ayyana gidan Uban wa Suwaiba alak'ak'ai zata kai mata D'ah.? D'aga kan da zatai taga sun nufi cikin Kotu. Asshe ta zaro ido waje tana d'ora hannaye biyu a k'irji "Na shiga uku ni Asshe mai Hilal yake a Kotu.?!"

Batasan sanda ta finciki marfin mota ba tabi bayansu a fusace.

SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!

*40*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

"Ke Suwaiba dakata.!" Ta furta da k'arfin gaske daga nan yanda take tsaye bayansu.

Gaban Umma ya yanke ya fad'i. Ta kasa juyowa sai furtawa da Tai cikin zuciyarta 'Asshe.!'

Shi kaw Hilal da tsananin mamaki Ya juyo yana dubanta "Ammi.!" Ya furta cikeda mamaki.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana huci "Baka tsammace ganina ba koh..? Nace baka tsammaci ganina ba koh..?"

Hilal Ya d'an lumshe ido kad'an ya k'araso yana k'ok'arin janye mahaifiyarsa "Ammi please don't make a scene here." A hankali yake maganar yana k'ok'arin janye ta.

Ta funcuke hannunta tana nunasa Umma da d'an yatsa "Kina jina Suwaiba kurwar zuri'ata kur..! Idan na sake ganinki kusada d'a nah.. Kinga nan." Ta nuna mata kotu dake gaba garesu "Wllhi a nan za'a rabamu.!"

Hilal yai saurin katseta "Ammi Umma bata tilasta mun zuwa wajen nan ba.. Nazo ne da rad'in kaina.."

"Rufe mun baki kai kuma kafin na Sallamaka da gaske kabi daji.!"

Umma ta k'araso cikin sauri tana girgiza kai "A'a Asshe dan Allah kar kice haka.. Wllhi Hilal yaron kirki ne mai biyayya."

Da mugun mamaki take duban Umma "Kul.! Ahir d'inki kar ki sake ki sake saka mun baki ina magana da D'ahna. Suwaiba ke har zakiyi magana akan biyayya..?!"

Umma ta sadda kai k'asa a sanyaye.

Asshe taci gaba "Kina jina idan har baki sakar mun kurwan D'ah ba wllhi sai na maidake abin kwatance a garin nan.! Ban haifo muku D'ah dan yaji da matsalolinku da gurguntaccen ahalinku ba ehe.!"

Ta dubi Hilal "Kai kuma idan ni ce na haifeka ka saka k'afarka a kotun nan.!" Tana ida fad'in haka tasa kai ta shige mota fuuu kaman zata tashi sama.

Hilal Ya dubi Umma yace "Kiyi hak'uri Umma bansan Ammi na biyedamu ba.."

Umma tai saurin girgiza masa kai alamun a'a "Kar ka damu Hilal kabi umarnin mahaifiyarka. Ni zan shiga na saurari k'aran Yaya Tani. Idan bata ganni a kotun ba zatai tunanin na kuma watsar da ita ne.. Inada yak'inin Allah zai kawo yanda za'a biya mutumin nan kudinsa Tani ta dawo gida."

Hilal Ya jinjina Kai a hankali "Umma biyan kudin bazai zama matsala ba in sha Allah.. Na Miki alk'awarin baza'a sake zaman Kotu akan wann batun ba."

Kaman daga sama suka sinkayo murya "Zaman Kotu da Tani yanzu aka fara dan sai na karb'ar ma D'anuwana hakkinsa rabon gadonsa da Tani tai yana raye. Idan banci taran Tani ba ba sunana Dije ba.!"

Tsaf Hilal ya gane Inna Dije ita ce dai Kanwar Abbansu Khulsum dake wajensa a asibiti sann koda aka sallame su Khulsum d'in ta tabbatar masa gidan Inna Dije dake Dutse zasu wuce da Abba yanda zaici gaba da jinya.

Gaisar da Inna Dije yai yana mai k'arasowa gareta "Ni zan biya taron Innah.. A kashe wutan maganar nan kowa ya huta.. Kar ki manta ku ahali ne kai juna Kotu ba naku bane musamman yanzu da Abba yake cikin wann yanayi.. Inna Idan Abba ya farfado daga jinyarsa yaga ahalinsa suna fad'a da juna irin haka mai kike tunanin zai kuma samunsa.?"

Shiru Babu Wanda yace komai daga Inna Dije har Umma. Hilal ya samu k'warin gwiwan ci gaba "Rashin lafiya irin na Abba baya buk'atan tashin hankali irin haka. Salama da kwanciyar hankali yafi buk'ata ta. Na tabbata idan Abba ya tashi yaga ahalinsa sun had'e. Suna k'aunar juna sun mance duk abinda Ya faru a baya. Sun kuma yafi juna wann kad'ai sai yafi maganin da Likita zai bashi." Ya k'arashe yana duban Inna Dije. Sai kuma ya soma saka hannu a aljihu "Zan biya ko nawa ne idan hakan zai kawo maslaha da zaman lafiya cikin ahalin."

Inna Dije na murmushi ta dakatar dashi "A'a haba.. Idan na karbi kudi hannun surki na mai na zama kuma." Tai maganar tana fad'ad'a murmushinta. Sai ta soma mutsuke ido tana janyo bakin mayafi tana share hawayen da suka soma zubo mata bagatatan "Na jima banji kalaman da suka ratsa zucuyata irinta yau ba. Tabbas Babu komai cikin k'iyayya da gaba. Tabbas D'an uwana ya farka yaga ahalinsa sun dunk'ule waje guda shine babban maganin da yake buk'ata. Laidai kam bakai halin mahaifiyarka ba. Al basa batai halin ruwa ba. Ubangiji ya maka albarka. Lallai ka cika D'ah na gari da kowa su iyaye zasuyi buri da mafarkin samu. Da ace duniyar zata cika da mutane irinka masu k'ok'arin ganin Sun wanzartar da zaman lafiya tsakanin Al'umma da rayuwa ta canza.

Haka Inna Dije taita sharb'an kuka tana fad'in ta tuba ta canza halinta. Taita saka ma Hilal albarka har ya bar wajen.

Mamaki ne ya cika Umma matuk'a da al'amarin Inna Dije dare d'aya dai kokuwa rana d'aya tak Inna Dije ta sauya. Ta ya za'a ce kalaman Hilal da basu shige a k'irga ba Sun karkata Zuciyar Dije. Kai abun da mamaki matuk'a.

Har Umma ta dawo gida mamakin wann kayan al'ajabi take.

A nan tsakargida ta yada zango ta kwab'e hijabinta ta lank'aye saman gajeren katanga dake tsakargidan.

A haka Badia da Azeema suka shigo tsakar gidan suka taddata. Duban Umma sukai a tare suka dubi juna da mamaki ganin sunata Sallama bata amsasu ba.

Suka k'araso a tare cikin sauri suka zube gabanta. Badia ta kamo hannun Umma cikin nata a dan firgice "Umma Mama ta Miki wani abin ko.? Umma saida muka fad'a Miki Mama tuban d'an muzuru tai."

Readers Also Read