Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 4

Babban goro complete novel - Chapter 4

Babban goro complete novel Chapter 4: Babban goro complete novel Chapter 4. Cikakken matashi dan shekaru ashirin da tara. Ya zama katon gaske. Kai ka ce…

1,946 words

Cikakken matashi dan shekaru ashirin da tara. Ya zama katon gaske. Kai ka ce dan shekaru talatin da biyar ne. Yana da wata irin halitta da kalar fata mai daukar hankali da fizgo zuciya zuwa gare shi. Musamman daga fitinannun matan da suka san kirar namijin duniya. Girman da ya kara ya basu mamaki dukkannin su matuka; dogo sosai, mai ginannen jikin da babu kiba, babu rama a jikinsa. Ba kamar yadda yake a da ba. A yanzun idan ka kalle shi mayuwaci ne ka bambance nationality dinsa, kasancewar Hajiya Kaltume Shuwa, yayin da mahaifinsa yake cikakken Bahaushe. A da yanada kala irin ta Alh. Aliko da mahaifinsa, amma a yanzu ya fisu haske ya su murjewa, kalar shuwa ta fito sosai a jikinsa, duk da duhun hausawan bai barshi yayi tasiri sosai ba. Sai maida shi kamar Egyptian bakaken cikin su. Kamannin Uwa da Uba ne suka cakude suka bada surar wannan giant mai sanya zuciyar diya mace cikin soyayya ta babu gaira babu dalili. Idanunshi kadai sun narkar da zuciyar Marwah, cikin wata irin masifaffiyar soyayya ba Imam din baki dayansa ba. Ita kanta Safan da ta kalle shi ta ji yayi mata kwarjini ainun, ya kuma burge ta, burgewa ba kadan ba. Irin wadannan mazan da Allah Ya hadawa komai na rayuwa, tsiraru ne a cikin al'ummah. Tace cikin ranta "ashe haka Ya Imam ke da kyau?" Sai dai hakan bai sa ta ji soyayyar shi ta aure ba, ko wani abu makamancin haka, ko kadan bata bari zuciyarta ta raya hakan ba, bata ji wani abu daban da na baya ba, wato kafin ya tafi. Tunda ta riga ta sawa ranta hakan.

Marwah ba ta taba ganin wanda hular ilmi ta yiwa kyau, ta tsaya kyam a kansa, ta dace da zubin halittarsa, ta fiddo haiba da kamalarsa, ta maida shi 'choculate-bature' irin Ya Imam ba. Da da ne, rungume su yake yi, amma a yau baki kawai ya rike cike da mamakin girmansu, yana satar kallon kwayar idon Safah, a lokacin da Daddy ya rungume shi. Fuskar Safah ba yabo ba fallasa ta ce, "Congratulations Yaya Imam!" Kwayar idon shi ta yi nauyi a cikin kallonta ya ce (idanunshi a lumshe) "Godiya nake Safahn Mami!". Marwah dake rabe a bayan Safah, tana lekensa, yana ta hira da Daddy, a lokacin da zuciyarta ke ragaita. Ragaita cikin soyayyar da ba'a san tana yi ba. Ta lalubi hannun Safah ta sanya mata wata leda da aka sunke wani abu a ciki cikin 'wrapping-sheet', (cikin abin nade kyauta) mai kyan gaske. Ta rada mata cewa ta bashi, (a zuwan ita Safahn ce ta bashi). Kallon rashin fahimta Safah ta yi mata, ta kada mata kai ta rausayar, kana ta langabar, cikin kallon lallashi, alamar kada ta watsa mata kasa a ido ta bashi. Ta gatsina baki ta ce, "Ke kin fiye fi'ili wallahi". Sannan ta mikawa Aunty Shahida dake gefensu tana waya ta ce, "Ki bawa Ya Imam in ji Marwah". Shahida sai ta dauka kunya ce da kara, don haka ta yi murmushi ta ce, "In ji ki dai". Ta murguda mata baki tace "sai kuyi kuma". Shahidah ta kama baki "ni kike zobarawa baki Safah?" Kamar tace "an zobara mikin" sai kuma tayi tafiyarta wajen su Mami ta barta anan. Abin sai ya bata dariya ta girgiza kai tace "Biyu Kyautar Allah!!!

Ta karasa inda suke shi da Daddy ta bashi. Ya jujjuya, ya yi mata kallon tambaya. Ta ce, "Sakon Safah ne!".

Bayan Daddy ya kammala duk cike-ciken takardun da suka kamata da sanya hannu (clearance), Almustapha ya karbi kwalinsa na zama cikakken 'Auto-Mobile-Engineer' (makerin motoci) da tayin aiki tare da kamfanin 'General-Motors' din Amurka, a ranar suka juyo Bournmouth. Gidan Alh. Aliko na garin Bournmouth akwai dalibai da suke zaman haya a ciki, alokacin kuma ana hutun karshen shekara kowa ya tafi hutu kasarsa, don haka gidan fes yake, kamar da mutane a ciki, 'yan share-sharen da Shahidah tayi ba masu yawa bane. Kowa ya nemi makwanci domin ya shimfide hakarkarinsa ya huta gajiyar tafiyar jirgin kasa. Bai bude sakon Safah ba sai da ya zo kwanciya. Katin gaisuwa ne mai bala'in kyau da tsada (greeting card) na fatan alheri, ga abinda tace;

"as you stribe hard 2 achiebe your goal… … here's hoping that you edcel in ebery way,… with faith in yourself and strong determination…. I strongly beliebed that success will surely come your way! A kasa ta rubuta sunanta -Safah Dan Kasa. Ya yiwa wannan kati karatu fiye da sau hamsin yana murmushi. A daren bai iya ya yi barci ba, sai karatun katin Safah. A little gift that means a lot 2 him…. Wannan ne abu na farko da ya taba fitowa daga hannun Safah zuwa gareshi da sunan kyauta ta soyayyah. Don haka muhimmancin wannan kati, yafi kyautar gida da mota a gun Imam. Ya kwana yana hasaso fuskar Safah ne, tana karanta masa wannan sakon, suna fita daga siririyar fatar bakin ta. Allah kadai ya san adadin kaunar Safah cikin zuciyarshi. Sai dai ta yi kankanta kwarai da ya tsaya yana bayyana mata dimbin soyayyar dake dankare cikin zuciyarshi a yanzu. Yana da yakinin Allah Ya halicci zuciyarshi tun fil'azal da soyayyar SAFAH, ta yadda har ba zai iya cewa ga adadinta ba. At 29, yana ganin lokaci ya zo da ya kamata ya yi aure, to amma da wace 'yar mitsilar Safahn? Da ko sakandire bata gama ba? Yana ganin har yanzu da sauran lokaci, kwata-kwata bana ne suka cika shekaru goma sha shida da haihuwa. Ba shi da damuwa, don ya san Safah zaman shi take. Iyaye da kakanni sun san da al'amarinsu tun ranar da aka haifeta. Babu macen da ke burge shi duk fadin duniyar nan sai 'yar uwarshi jinin jikinshi Safah. Ita kadai ce zai iya baiwa gurbin uwar 'ya'yansa. Mata kala-kala ya gani a rayuwarshi, daga namu na bakar fata mazauna Britain har zuwa na jajayen kunnen asali, Arab, Asians, Indians, Pakistani, Iranian, Moroccons, Portuguese, Somalis harda Jamaicans, sun so shi sun kaunace shi, da aure ne ko da gurbatacciyar mu'amala. Amma Safahn nan ita kadai ke da mulkin zuciyarshi, ta yarda har bai iya daga ido yayiwa wata mace kallon kima. Saidai ayi mu'amala kawai (dating). Mulkin Safah a zuciyar Imam, mulkine da ya tabbatar har abada babu mai ture shi. ***

Washegari misalin karfe tara na safe, ya yi wanka ya shirya cikin bakin jeans da farar riga mai ratsin baki samfurin (Calbin Klein). Ya fesa turare a gurguje ya janyo kofar falonshi ya rufe, ya shigo falon duk jama'ar gidan suna falo suna kalaci, amma babu Safah a cikin su. Marwah da Aunty Shahida suka gayar da shi, shi kuma ya gaida su Daddy, ya ja kujera gefen Hajiya Mama ya zauna. Ya ce, "Ya ya uwargida me zan samu ne?" Ta ce, "Kai tafi can, maigidan da babu awo babu cefane". Ya ce, "Ai kema kin san don bana nan ne, amma tunda gani na dawo, cefane sai kin ture, kin rasa yadda zaki yi da shi". Sannan ya yi zagaye da kwayar idanunshi masu sheki kan kowa dake bisa tebirin ya ce (yana kallon Marwah). "Ta-robar, ina ta-karfen ne?" Ta yi murmushi, wani kishi ya turniketa, amma ta sadda kanta kasa, idanunta suka kawo kwalla ta ce, "Tana dakinmu, tana da assignment ne". Ya ce, "Assignment ne zai hana cin abinci? Bari in gano ta". Babu wanda ya tanka musu. Ya mike tsam ya doshi dakin nasu. Duk suka bishi da kallo. Gabadayansu kallon tausayin yadda ya damu da murdaddiyar matar da yake so, ita bata san ma yana yi ba. Don ta kai ta kawo kowa ya fara ganewa. Zaune take a kan study-table da manya-manyan littafan sakandire a gabanta, da gilashin karatu a idonta mai kara karfin idanu ga wanda ke yawan mu'amala da takarda, tana ta rubutu. Daga bakin kofa ya tsaya yana kallon ta, duk wani motsinta a kan idanunsa. Ba ta san da tsayuwar shi ba, shi kansa bai san adadin lokutan da ya bata yana kallon nata ba. Watakila jikinta ne ya bata akwai mutum a tsaye a kanta, ta dago a hankali ta dube shi, kana ta maida kanta ta ci gaba da abinda take yi. Ya ce, "Sorry to interrupt... ki taso ki yi kalaci". Ta yamutsa fuska ta ce, "Bana jin yunwa". Ya ja kujera kusa da ita ya zauna, ya ce, "To nima ba zan ci ba, kawo rubutun in taya ki". Ba ta yi musu ba ta mika masa biro, sai ya hada komai ya rufe ya ture gefe, ya fuskance ta sosai a yayin da ta sunkuyar da kanta. Ya ce, "Na kasa gane inda kika dosa Safah, na kasa gane abinda ke karkashin zuciyarki game dani. Safah idan har yau bakisan matsayina a gareki ba sai yaushe ne?" Yayi dan shiru sannan yace "abinda kike bani a rubuce, ba shi nake gani a kan fuskarki ba. Ina so mu yi magana ta sosai, mene ne matsayin alkawarin iyayenmu a kanmu? Aure nake so Safah, ba kuma da kowa ba sai ke kanwata da na rayu shekaru masu yawa cikin son ki da kaunarki, sannan cikin dan lokaci in Allah Ya nufa, a kalla bayan kammala karatun sakandirennan, kin ga na girma har nafara tsufa. Taimakeni ki gaya min matsayin da kika bani a zuciyar ki, domin 'attitudes' (halayenki) sun fi yimin kama dana wahainiya mai canza launi a sarari" Kanta ta sunkuyar ba tare da ta ce da shi komai ba. Tana so ta ce da shi ai ba ni nake rubuta maka ba, don ni bani da lokacin ta (soyayyar). Amma kimarshi da darajar shi da take gani na Yaya agareta kuma dan uwan da babu kamarshi garesu a yanzu, ya hana. Ita har gobe kallon Imam take kawai a matsayin dan uwa na jini, amma babu birbishin soyayyah, ko kadan babu. Ita kuma bazata iya bude baki ta gaya mishi hakan ba. Ai ya zama cin fuska! Duk da bata san yaya soyayya take a zuciyar mutum ba, zata iya dorar da cewa ita kam bata jin komi sai kauna ta 'yan uwantaka akan Yaya Imam, kwatankwacin wadda take ji, a kan Marwah da aunty Shahidah. Ya yi maganar duniya ta ki ko dagowa ta dube shi, ranshi yai mugun baci, don nan duniya babu mai yi masa wulakancin da Safah take masa, bai san lokacin da ya kai hannu ya fizgo nata ba, tace "…….za ka ballani……???" Shima ya ce "zaki kashe ni ke, idan ni ban ballaki ba. Gara in ballakin, in huta da wahalar da kike baiwa zuciyata Safah". Allah Sarki! Fita ya yi kuma ya debo kayan karin kumallon da 'tea' a kankanin kofi ya kawo mata har teburinta, ya tsugunna a gaban ta, ya dora hannu akan gwiwoyinta, ya kwantar da kai a masangalin kujerar da take zaune sabida ya ga tana hawaye, hawayen da yake ganin shi ya kamata ya zubar dasu ba ita ba. Ita hawaye take don ya takura mata, da tunanin zamansa a gida yanzu wanda ke nufin a tursasa ta. Cikin murya mai rauni yace "ki sha ba don ni ba, ba don ki so ni ba, ko don na isa in saki abu ki yi, sai don damuwar da nake ciki akan ki sha din, kiyi mini wannan alfarmar, zan samu Safah?" Ta dago ta dube shi, duk sai ya bata tausayi. Amma ba ta ce da shi komai ba. Sai ta mika hannu ta dauki kofin ta kai bakinta, ya juya ya fita zuciyarshi cike da tunani mai yawa. Bai fuskanci inda ta dosa ba. Wata irin mutum ce mai wahalar karantuwa da mugun zurfin ciki. Hakan ke boyewa mutane zahirin abinda ke karkashin zuciyar ta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull