Baccin so complete by m shakur - Chapter 1
Baccin so complete by m shakur Chapter 1: Baccin so complete by m shakur Chapter 1. 💫BACCIN SO💫
4,490 words
💫BACCIN SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI!
BEFORE ANYTHING JOIN ANY OF MY COMMENTS SECTION! https://chat.whatsapp.com/Lexo516Rbc1J318UVT7a6q
https://chat.whatsapp.com/Iqo6H7ScyCu85pKADXlnsA
https://chat.whatsapp.com/K3p0bPIZP4M2RbqsDlpVzV
https://chat.whatsapp.com/FD5l1XPlv0zJjShiIL1Vyx
Cike gidan yake makil da jama'a, kana ganin yanayin tsarin ginin gidan kasan irin gidan masu dan rufin asiri ne daidai gwargwado, babban compound ne mai dan madaidacin girma dakeda wata yar kodaddiyan milk gate dayake a bude sabida jama'a dake shiga da fita. Yammata ansha makeup ansha anko, sun zagaye wata yar budurwa dakana ganinta kasan itace Amaryan sabida yanayin tufafin jikinta da gwargwaro dakuma lalle datasha a hannaye da kafafu, rawa suke sosai a tsakar gidan gaban DJ dayake buga kida yana chanza wakoki anama Amarya liki yan 50, da yan 100naira….
Duk wannan kidan da hayaniyan da ake bugawa bacci take acikin dakin dakeda dan duhu dan an sauke labulen window, kaman an tsikareta firgigita tabude idanunta tana kallon saman silin na dakin dawani irin sauri ta tashi zaune gashinta nawani irin zubowa bayanta mai tsawo baki kirin dayake a tsefe, sanye take da atampa wanda kana gani kasan sabuwa ce anko kuma dan tayi kama da na mutanen tsakar gidan yan biki, an manta dinkin doguwan riga dayamata wani irin bala'in kyau a jiki, very simple style mara nauyi kwata kwata, waige waige tashigayi kaman mai neman abu sai kawai tamike tsaye zumbur tana yarfe hannu karamin lips nata ya furta "Ammi" wanda muryanta baya fitowa, saita shiga tafiya ahankali ahankali still kalle kalle take tana shafa fuskanta da kanta tana sosa gashin data shiga hargitsawa yafara komawa wani iri kawai tabude kofan dakin, jama'a ne birjik afalon ana hayaniya, tana bude kofan kowa yadago kai yakalleta jikake falon tsit sai kuskus da aka fara, kanta tasauke kasa ahankali, saita cigaba da tafiya ahankali batare data hada ido da ko mutum daya na falon ba bakinta na furta. "Ammi, Ammi, Ammi" ba lallai ma kaji metake cewaba idan bakazo kusa da ita ba, sai gyaramata ake kowa na cire roban abincinsa daga kasa, kawai tawuce tayi kofa tafita jama'an dakin na kuskus. "Yarinya kyau iya kyau amman kan ba dadi sam, sam". "Wai ahaka aka haifeta koko jinnu ne cus kyawawan yara haka daman ance yaran jinnu ne"? "A'a wannan fa haka aka haifota da tabin hankalin ba jinnu bane, yoh yarinyar da asibitin mahaukata ma ake kaita"……… Jama'a ne cike a compound din ga rawa anayi tana fitowa kawai tafiya tashigayi har lokacin kuma kanta akasa tana magana ita kadai "Ammi, Ammi" tana tafiya tafiya irin wacce ba direction dinnan nan da nan jama'a suka fara kallonta. Amaryan dake filin rawane ta hangota taja tsaki takalli daya daga cikin yammatan wajen tace "je dan Allah ki kirawa mahaukaciyan chan mamanta kafin ta hargitsamin biki, dan wlh tabatamin biki sainaci ubanta kafin akaini gidan mijina" dasauri kawarta tace "toh bari naje" fita daga cikin filin rawan tayi tai bayan gida ta nufa inda mata ke girki dagudu tayi wajen mata mata tadan manyanta akalla zatai 46yrs haka tana sanye da same atampa da kowa yasaka tace "Ammi ga Amirah chan tsakar gida zata fara haukan" anatse Ammi tajuyo takalleta kafin tai magana matan dake kusa da Ammi tace "wai ku yaran yanzu maisa baku da tarbiya ne iyye haka ake magana Zainabu"? Turobaki tayi tace "to karya akayi? Danma nazo nafada mata ai danayi shiru abina kwashe nemanta anjima….." Ammi bata tsaya jinsu ba wucewa tayi da dan sauri tazagayo cikin compound din tanabin ko'ina da kallo tana nemanta da idanu gabanta nadan faduwa ta tare wata yar yarinya tace "kinga mini Amirah Baby?" Baby tace "tana waje tana nemanki Ammi" dasauri Ammi tasaketa tai hanyar gate tana zuwa taganta awaje tafiya take still ba takalmi akafan dasauri Ammi tasa hannu takama hannunta tace "gani nan Amirah" Ammi tai maganan tana kai dayan hannunta kan kafadarta tajuyo da ita tanadan maida ijiyan zuciya sabida kalan saurin datayi, ahankali for the first time sai yarinyar tadago kanta Ya Rabbi! Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin daya hallicci kowani bil adama, dan yarinyar nada kyau, wani irin kyau da kafin kaga mace mai kyanta sai an tona, sak Amminta tundaga white skin color din, saidai tafi Maman kyau nesa ba kusa ba, ga gashin idanu dogaye bakake sosai, ga gashin gira baki acike mai yawa kaman buzuwa, tanada dogon pointed nose, ga karamin baki pink yir exactly irin na jarirai, gefen fuskanta da goshinta duk akwai gashi kwance kaman buzuwa, chak ta tsaya tana kallon Ammi kuma babu wani reaction akan idanunta kona damuwa, kona baccin rai, kona farin ciki, Kona tsoro, kona bakin ciki, kawai fuskanta is straight, dan ijiyan zuciya Ammi ta sauke tadan sassauta murya tace "jibeki ba kallabi akanki, ba takalmi akafanki, banasha gayamiki duk sanda kika farka baki ganni ba ki zauna awajen zaki ganni zan dawoba amman bakijin maganata, wuce mutafi" Ammi takara rikewa gam tashiga tafiya, Ammi na tafiyar da ita ahankali suka shigo cikin gidan daidai wata mata datasha ado sosai tanada dan jiki kana ganinta kasan itane Maman Amarya ta tareta tana wani hura hanci tace "idan kinsan ba girkin zakiyi ba maisa kikace zakiyi tunda hankalinki nakan wannan abun" tanuna Amirah da kanta ke kasa tana dab da Ammi dake rikeda hannunta, adan natse Ammi tace "yanzu zan koma nacigaba Maman Baby" Mamababy tana wani huci tace "shidai yafi miki, kibar mahaukaciyan nan kiji da abincin jama'a" ko kadan Ammi bataso yau ranta yabaci saisa kawai takara kama hannun Amirah da kyau suka wuce bayan gidan, few matan dake wajen suka bisu da kallo ganin Ammi tadawo da yarinyar, wani plastic chair Ammi tadauka ta ijiye tadaurata akai tace "zauna bari nabaki abinci" Ammi tajuya dawani irin sauri kaman gudu Amirah ta tashi, Matan dake wajen suka bita da kallo Ammi tajuyo ta kalleta ganin taki zama takara biyota sai kawai ta kyaleta bata cemata komiba tabude katon kulan wajen tadauki plate tazuba mata white rice da stew tasaka spoon tajuya mata sannan tace "muje" Ammi tai gaba Amirah tabiyo ta abaya, Ammi takamata tasata a kujera ahankali saita debi rice a spoon tadankai bakinta jin ba zafi sosai saita debo takawo wajen bakinta dasauri tabude bakinta hakoranta farare passs, Ammi ta samata shinkafan, karba tayi duk tana kallon idanun Ammi tana taunawa ahankali, sai Ammi takama hannunta tasaka mata plate din tace "yauwa to maza cinye, bance ki tashi ba gani nan girki zanyi kinji"? Shiru tayi tana kallon Ammi tana chewing rice din, Ammi tace "kice to" da dan karamin voice nata da Ammi kadai kejinsa aduniya tace "toh Ammi" wani heart melting smile Ammi tayi ta tsaya tana kallonta sai kuma ahankali takai hannunta tashafa kumatunta tace "yauwa yar albarka na, maza cigaba da ci ingani" sauke kai tayi daga kallon Ammi ta debo abincin a spoon takai bakinta tafara ci Ammi tace "yauwa Masha Allah, kada ki tashi gani nan anan" Ammi tajuya tayi wajen murhu tana tafiya tana waigowa dantaga kota mike taganta azaune amman tanabin Ammi da idanu tanacin abinci ko kyafta idanu batayi, dan ijiyan zuciya Ammi tasauke ta tsaya kusada Rakiya tace "kuyakuri Rakiya" Rakiya tace "haba bakomi, dawainiya da yara haka ai ba karamin aiki bane, kuna nema mata maganin islamic kuwa?" Spoon na girki Ammi tadauka tana juyawa tace "babu wanda ba mayi, ba matsalan jinnu bane da itaba rashin lafiyane kawai daga Allah" dayan matan tace "gaskiya yakamata kiyi dagaske, ga sa'onninta duk sai aure, to wannan ma ai kanwartata tayi aure abarta tunda har anzo an tambayi aurenta, jibidai yau Ramla ce Amarya, gaskiya dai kuyi da gaske inba hakaba babu wanda zai auri mara lafiya"Ammi bata kara magana awajen ba sai aikin gabanta take bini bini tana dagokai ta kalli Amirah da har lokacin idanunta nakan Mamanta duk inda Ammi tayi tana binta da idanu, gama hada komi Ammi tayi tarufe pot tazo tadauki pure water tazo wurin, Ammi ta bude mata ta karbi plate din ta ijiye sannan tasaka ruwan abakinta hannuwanta tasa ahankali tadaura akan na Ammi kullum idan Ammi nabata ruwa haka takeyi tashiga sha tana kallon Ammi, Ammi tamata murmushi tace "saura kimini wasa da ruwa anan agwagwa kawai" dago kanta tayi alamun ta koshi, murya chan kasa tace "Ammi pee"Allah yasa tagama hada komi na girkin kawai tsotsewa zaiyi akwashe takalli su Rakiya tace "tunda an gama bari nakaita ciki nasa mata kallabi" dasauri Rakiya tace "karki damu tunda kingama zamu kwashe kiji da abu daya" Ammi batace komiba ta karbi plate din ta ijiye takama hannunta tace "muje toh" kankame hannun Ammi tayi suka wuce Ammi tace "duk sanda kika kara fitowa babu kallabi akanki saina saba miki mena gayamiki game da budekai ba kallabi"? Batace komiba ahaka suka shiga falon Ammi ga jama'a awajen Ammi ta gaggaisa dasu Amirah na tsaye wajen dab da Mamanta tanama wasa da yatsun Ammi ne ita kadai haka Ammi tawuce da ita bedroom duk aka bisu da kallo, ta maida kofan tarufe sannan tace "cikani kije kiyi fitsari" dan dago kanta tayi batare data saki Ammi ba sai kawai Ammi tawuce da ita bandakin tabude kofa tace "shiga" ahankali tasaki hannun Ammi, Ammi tace "yi adduan shiga bandaki" ahankali bakinta ya shiga motsi saita shiga Ammi tajuya zata wuce dasauri Amirah tace "Ammi" dan dakatawa Ammi tayi kaman zata mata fada but she knows harda mutanen dasukayi extra yawa yau agidan da hayaniyan biki yasa she's being extra clingy today, other days tana dan bata space even though duk inda zaka gan Ammi zakaga Amirah you must find her awajen, sai kawai Ammi ta tsaya tace "jekiyi to gani nan, maza kiyi alwala" gyadama Ammi kai tayi tawuce tana daga riganta Ammi na kallonta batako kyafta idanu kana ganin yanda take komi kasan mahaifiyarta tai kokari dan bata wani shirme, tashi tayi bayan tayi tsarki tamaida pant dinta sannan tai flushing zata taho Ammi tace "alwala baki salla ba" alwala tashigayi shima exactly yanda ake alwala sannan tafito Ammi da kanta ta rufe kofan bayin tadauki hijabi tabata tasaka maroon yamata bala'in kyau ta kabbarta salla tayi shima perfectly tana idarwa tajuyo takalli Ammi, Ammi dake daukan ribbon da comb tace "ba kallona nace kiyi ba tashi kizo nan nakama suman nan naki" ahankali ta tashi ta linke dadduma da hijab ta ijiye inda Ammi ke ijiye saita taho dayake abakin gado Ammi take zaune tana harhada ribons nata dasuke cikin wata yar karaman jaka daban hawa gadon tayi ta kwanta tadaura kanta kan cinyan Ammi, Ammi takalleta tace "ai yamiki kyau mage" saita dauko comb zata fara kifa kanta yayi a cikin Ammi, Ammi tace "zan kwadeki idan baki tsaya ba tunda ke baki kaunar ataba miki kan nan, kinfiso kiyita tsorata mutane dashi, bani kan nace" ahankali tafito da kan tasa akan cinyan Ammi, suka fara. Tun tana yar yarinya batason ataba kanta dambe ake sosai, itama Ammi saida tayi da gaske hakan yasa ko yanzu ma ahankali take taje mata gashin, gashinta is so silky and very black kuma bata tabasa relaxer ba, kama gashin tayi agida biyu tsaf tagama hakan yasa tajuyo da kai tana kallon Ammi, Ammi tai murmushi tace "iyye Yammata na tayi kyau Masha Allah, yimin murmushi nagani yayyy"tsayawa Amirah tayi tsuru tana kallon Ammi sosai dake murmushi kaman zata hadiye Ammi da manya manyan fararen idanunta, ahankali Ammi tajuyo dakatar da murmushin datakeyi tai shiru sai kuma idanunta suka cicciko da hawaye dasauri tadauke kanta tadanja hanci irin maison hadiye kukan nan jikinta yayi sanyi looking very sad, kama hannun Ammi Amirah tayi tashiga wasa dashi tana tattaba hannun tana wasa da fingers din Ammi tana nannade wannan da wannan, sai Ammi tajuyo da kanta ahankali kawai tazuba mata idanu tai nisa a tunani, aka bude dakin dasauri Ammi tajuyo wata yar budurwa ce tana sanye da anko itama kana ganinsu kansu daya kuma kamanninsu kusan daya kawai Amirah zata nuna mata hasken fata ne ita wannan hasken ta kaman na Ammi ne, ta ijiye jakan makaranta tace "Wayyoo Allah na Ammi ina wuni nagaji" murmushi Ammi tayi tace "andawo daga school Miemie, yaya test din" dasauri tataho wajen gadon tace "Ammi nayi kokari sosai" tai maganan duka idanununta na kan Amirah da kanta ke cinyan Ammi tana kirga yatsun Ammi kaman batasan da mutane a dakin ba, Ammi takalli Amirah tace "tashi toh ga Miemie tadawo daga school, Miemie zauna min da ita bari nakoma naduba abinci zan kawo miki shinkafa kema"
Dasauri Miemie tazauna kan gadon tana kallon Amirah tace "yau bazaki kulani ba sabida ban kawo miki tsaraba bako" Ammi tamusu dariya tace "kunfi kusa" Ammi tasa hannu tadagota ahankali tace "zauna da yaruwanki bari naje nakawo muku abinci" Ammi ta karbe hannunta tamike dasauri itama tamike, Ammi cikeda fada tanuna mata gado tace "zauna anan nace ita Maryam din bakuwan kice, tun safe banda sukuni sabida ke sai bina kike kuma kinki yarda da kowa, abin naki harda yar uwanki yau, wuce ki zauna nace" tunda Ammi tafara fada tasauke kanta kasa takai hannayenta tana sosa cinya duk saita bama Ammi da Maryam tausayi, Maryam da taji duk ba dadi dasauri ta taso takai hannu zata kamata dawani irin sauri ta matsa kusada Ammi, Ammi tace "kyaleta kawai Miemie kinsanta hayaniya da jama'a duk suna tada mata da hankali, yau rashin yardan hardake kuwuce muje" Maryam tace "kuma Ammi da bata ganki ba da nine zata mannemawa hakafa" Ammi tace "ai tunda tamiki halinta yau karki kara kawomata komi daga school" Ammi tawuce tai gaba dasauri tabi Ammi kaman bindi Allah tasa kan akwai hula yanzu, Maryam ma tabisu tana kallon yanda simple gown din yama Amirah kyau na wuce misali, backyard Ammi tayi anan taga Maman Baby awajen da ake kwashe abinci a kula tahade giran sama da kasa Ammi ta taho wajen zata wuceta Maman Baby tace "ki barshi kawai bana bukatar ki, Allah yasa inada wasu dazasu tsaya kan abinci jekiji da diyarki mara kai" dasauri Rakiya tace "mekuma yayi zafi Maman Baby kinsan yanda yara suke especially marasa lafiya kuma duk ita tahada abincin ai kafin takaita ciki" Cikeda fada Maman Baby tace "karki gayamin magana Rakiya, bakisan meke faruwa bane acikin gidan nan, bakin ciki take taga sa'an diyarta yau tana aure ga tata diyar kai duka yaran nata ma babu manemi, daya ba kan gado kan ba dadi balle ma ayi maganan aure akanta, dayan kuma sai bakin rashin kunya" Maryam ta tabe baki tana juya idanu, Maman Baby tace "shine takeso mutane su zageni kar kowa yaci abincin tunda ba yarta ke aure ba" ahankali Amirah takama bayan rigan Ammi tarike jikinta yadan fara rawa bawai tana kallon mutane bane but she understands everything that is happening around her, bataso taga ana fada da mamanta, dazaran an fara zakaga tarike ko hannu ko rigan Mamanta kanta akasa, Maman Baby tana kallon Ammi cikin idanu tace "to bari kiji wlh sama taima yaro nisa saidai yadaga fuska ya kalleta nariga namiki fincinkau Zainabu, diyata na biyu kenan danake aurar wa kekuwa kije kifara ji da mahaukaciyar nan ita kadai tazamema rayuwarki azaba da ukuba" tai maganan tana nuna Amirah, tunda ake hayaniyan nan babu abinda yabatama Ammi rai sai kalman karshe data fadi, takalli Maman Baby sosai kaman tabata amsa amman saita fasa sai kawai tasa hannu takama hannu takama Amirah dake jikinta, takalli Maryam dake huci tacika fam tace "kuwuce muje" ganin Maryam batai motsi ba Ammi tace "Maryam nace muje" zuciyanta ba dadi tajuya fuuuu, Maman Baby tadaga murya tace "dakin barta ai tarama miki yanda tasaba, ahaka zaki kare keda uwarki, Zainabu kekuma nagaya miki aniyanki akanki zai kare gadai daya nan agabanki kina gani, ke kikasan uban me kikayi Allah yabaki ita mai juyayyen kwakwalwa" mutanen wajen ne suka dinga bawa Maman Baby hakuri cus zagin yayi yawa sannna tai shiru. Kofan flat nasu Ammi tabude takalli Miemie dake huci strictly tace "wuce ciki" batai musuba tawuce ciki, Ammi tashigo da Amirah, duk an fita daga dakin, Ammi tawuce ta ita tazaunar da ita akan gado takalli Maryam dake tsaye tace "zauna kema Miemie" kaman jira take dasauri Maryam tace "Ammi wai Matarchan who did she think s….." "kul!" Ammi tafadi ahankali hakan yasa Maryam tai shiru, idanunta na ciko da hawaye jikin Ammi yayi sanyi, ahankali tace "idan baki fahimceni ba Miemie wanake dashi kuma eh? Ina zan sa raina? Ke koda zanyi fada ba abinda zaki hanani bane Maryama? Kalli yar uwanki ba lafiya, anzo neman aurenki, Babanki yace nan da wata uku, da shirya aurenki zanji koda ciwon yayarki eh Maryam? Do you think tsayawa nayi fada is wise?" Ahankali tace "Ammi ni bazanyi auren nabarku anan ba wlh" wani kallo Ammi tamata tace "ke bakida hankali ko" kawai saita fashe da kuka sosai, ahankali for the first time tunda tadawo sai Amirah tadago kanta ta kalleta, ahankali Ammi ta taho wajen Amirah na binta abaya, Ammi taduka tana kamota tace "Miemie mehaka? Meyayi zafi? Why are you crying like this? Miemie na menene"? Ammi tarungumeta cus Maryam hardly cries, cikin kuka da tsantsan zuciya tace "sai ayita kiran yaruwata mahaukaciya, Ya Amirah ba mahaukaciya bace, yar uwata ba mahaukaciya bane, she doesn't hurt me, bata cutar da kowa, Ya Amirah is kind, Ammi she takes care of me, kullum idan zani school she cleans my shoe, da farko ma da rigan jikinta take gogemin saida na nunamata da tsumma akeyi, bantaba fada mata ta gogemin takalmi ba, idan ina assignment tana zama kusadani taita kallona idan nai bacci awajen zata kwashe all books din tasamin ajakan school, she watches me and studied kome nakeyi even though she hardly talks to me, Ammi yar uwana ba mahaukaciya bane kawai Allah ya hallice ta daban ne, Amirah ba bala'i akanmu bane, my sister is special, and she's Allah's gift, I love my sister ni wlh da ita zan tafi gidan mijina idan Umar bazai yarda ba nafasa aurenshi" ganin yanda take kuka yasa Ammi kawai tadinga lallashinta ta share shirmen datake fadi na zataje gidan mijina da Amirah, da mijin zataji koda Amirah? Hmm yaro yarone!. 💫BACCIN SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣
MUTANE DAYAWA HAS BEEN ASKING ME M SHAKUR INASO KISSA CLASS, INASO NA SHIGA INTIMACY CLASS, YAUSHE ZAKI FARA😅 TO GA BABBAN ALBISHIR! ZANYI 2in1 CLASS BOTH IYA KISSA DA ILIMIN INTIMACY WATO OZA ROOM DUKA A AJI DAYA FOR A MONTH🥳😎 HAJIYA KI IYA KISSA DA KISISINA SANNAN KI IYA SARRAFA OGA AJIKINKI 🛌
NORMALLY THE CLASS SHOULD BE 10k BUT ZAN BADA 50% DISCOUNT MA READERS DINA!
PAY 5k ONLY AND JOIN KISSA/INTIMACY BOMB CLASS💃
JAMA'A DUK WANDA YA IYA YAHUTA FA KIZO KI KWASHI HAAJA MAMANA🥳 AMARE A SHIGO DA GUDU!
MAKE PAYMENT HERE AND SEND ME EVIDENCE OF PAYMENT
PAY 5k INTO 7032934950 Aishat Muhammad OPAY KO
0895672695 AISHAT MUHAMMAD GT BANK KO 6353995766 M SHAKUR WORLD MONIEPOINT
SEND EVIDENCE AND JOIN CLASS DIN🥰 wa.me/+2347012181461
Wuraren 7 akazo kai Amarya za'akai Amarya wurin Ammi danta samata albarka Maman Baby tahana tace awuce ita, itama Ammi taso fita amman gudun cin mutunci abainar jama'a yasa tai zamanta ga Amira da bata isa tai motsi batare data bitaba, ga Miemie data samu ta lallaba tahakura gwara tazauna cikin yaranta sune farin cikin rayuwanta. Tasss suka gyara falon da jama'a suka zauna sukai moping ko'ina Miemie tasa turaren wuta sannan sukai isha'i, Ammi ta kunna mata cartoon a TV a falo sabida ta yarda tazauna taje tai wanka, tace "zauna keda Miemie bari naje nai wanka, yi kallo abinki kinji diyar albarka, bari naje na watsa ruwa" Ammi bata jira amsanta ba tawuce tana kyaftama Maryam idanu alamun tariketa, bin Ammi Amirah tayi da kallo harta shiga bedroom dinta, saita janye kanta tamaida kan tv ahankali Miemie tace "mayyan Ammi, bazaki iya rayuwa babu Ammi ba Amirah" ringing taji wayanta nayi daga dakinsu dake kusadana Ammi hakan yasa tamike dasauri tace "Ya Amirah ina zuwa Ya Umar na kirana" tawuce dakinsu dakin yarage just Amirah ne ciki, kusan 10min tana zaune ita kadai tana kallon tv aka bude kofan dakin da sallama ciki ciki. "Assalamu Alaykum" wani irin tsalle Amirah tayi tasauka daga kujeran datake zaune tasauke kanta kasa dasauri, wani dattijo ne haka ya shigo yana sanye da suit, fuskanshi ahade ba rahama yama Amirah wani kallo mara dadi kafin cikeda kunci yace "ke ina uwarki"? Kan Amirah na kasa tana wasa da fingers nata tana goga hannunta awajen cinyanta tasaman riga kaman bada ita akai magana ba, dattijon yaja wani tsukin takaici. "Mtswww useless girl!" Yawuce yashiga tafiya takalmin kafansa cover shoe na kos kos kan tiles na parlor, bedroom na Ammi yabude kofan yashiga yamaida kofan yabugo da karfi yarufe dayasa Amirah tasake firgita saita dago kanta tana kallon kofan saitakai hannunta tasosa gefen fuskanta takasa komawa tazauna, hannunta sai rawa yake tana sake goga hannuwan ajikinta sosai sosai. Karan yanda aka bugo kofan yasa ahargitse Ammi tafito daga bandaki tana kokarin daura zanin wanka da kyau danta dauka Amirah tafadi ne, taga mutumin hakan yasa ta dakata tadan sauke ijiyan zuciya tace "sannu da zuwa Daddy, wlh nadauka Amirah ce tafadi bakaga yanda na tsorata ba" wani bakin kallo yamata tareda daga mata hannu yace "that's not why I'm here Madam, ubanme da me kika fadawa Asiya yau?" Ahankali Ammi tace "kaman ya?" Cikin fushi sosai Daddy yayo kanta kaman zai rufeta da duka yace "ke mesa baki da mutunci, how dare you disrespect my wife? Ba ke kikace zaki girki bakiyi ba kuma kikahau zaginta agaban jama'a on her daughter's wedding day, ke maisa bakida mutunci, you're a very very useless woman saisa kika haifi that useless, foolish, dumb headed girl dinchan!" Wlh zagin daya mata ko kadan baimata zafi ba, amman na Amirah yamata zafi da ciwo arai. Faduwa gaban Ammi yayi tadan kalli kofa cus tasan the way fada da ihu ke triggering condition din Amirah gashi daman bawai shiri suke da Babanta ba dan baya gamaciji da ita, cikeda damuwa da dan sassauta murya Ammi tace "Daddy dan Allah kayakuri kadena daga murya Amirah na falo kasan ba ishashen lafiya ne da itab…." Tasssss! Yadauke Ammi da mari mai zafi kafin Ammi ma tadawo hayyacinta yasa duka hannayenshi ya hankadata ga ruwan wanka dake kafanta jikake tasss Ammi tafadi akasa sosai, Daddy na huci sosai yace "nikike gayama maganan banza? Sabida mahaukaciyar yar da kika haifo bazanyi magana dake ba? Who do you think you're? Are you telling me how I should behave because of that dumb mental girl"? Dan bude kofan dakin kadan akayi hakan yasa Ammi dataji kaman kafanta ma ya murde tadago kanta takalli kofan shima Daddy yajuyo jin an bude kofa, Amirah ce tabude kofan dakin amman kanta akasa sai yakushin hannayenta biyu take cikeda karfin hali Ammi ta kakalo murmushi tace "Amirah banace idan ina magana da Daddyn ki kidena shigowa ba, go and watch your cartoo…." Cikeda zafin zuciya Daddy cikin tsawa yace "ubanme kikazo yi anan wuce ki koma inda kika fito ja'ira dakikiya, mahaukaciya kawai" ko motsi Amirah batayiba saima cigaba da susan hannunta datakeyi, sosai ran Daddy yabaci azuciye yajuya zaiyi kanta cikin fushi yace "badake nake magana ba kikeyi kaman badake nake ba, nace kibar wajen nan" dudda Ammi naji kaman tai targade akafa amman ganin zaiyi kan Amirah wani karfine yazo mata ta yunkuro tama kasa mikewa tsaye takai hannunta takama hannunsa arude tace "Daddy dan Allah karka tabata dan Allah kayakuri, bawai batajin maganan ka bane, ba cika gane maganan take ba dan Allah kamata afuwa, don't beat her please" wani kalan juyowa Daddy yayi sabida bakincikin yanda Ammi tarikemai kafa baiyi wata wata ba kawai ya fizge kafansa ya tokare Ammi aciki, Amirah dake yakushin hannunta tawani kalan buga kanta akofa jikinta yafara kyarma, Daddy na ihu sosai yace "maganan banza maganan wofi dani kike magana zanyi maganin ki toh agaban diyar naki nagama dake nakoma kanta tunda you're becoming bold" kawai yashiga dukan Ammi tun Ammi na daurewa bata ihu tashiga kokawa dashi tanason kwace kanta tafara ihu. Sosai Amirah tadinga buga kanta akofa cikin yar karaman muryanta tana "Ammi……Ammi…Ammi…" dukawa Daddy yayi yakaima Ammi naushi a hanci yace "zan miki jina jina yau ba nikike maidawa karamin mutum ba"wani kalan juyawa kan Amirah yafara, har rotating idanunta suke in circular motion da kanta kaman lizard, plate na tangaran da Ammi tabata abinci dazu tagani anan dakin kawai saita taho ta duka tadauka jikinta ko'ina rawa yake ta taho wajensu dukansu babu wanda ya lura da ita, batai wata wata ba tadaga plate din da duka karfin da Allah yamata na duniya kawai tabugama Daddy plate na tangaren akansa wani irin mugun mahaukacin bugu saida tray din ya tarwatse jikake ratsatsaaa!!!! ihu Daddy yayi sosai, sai jini, yashiga juyowa amman kafin ya idasa juyowa ya zube akasa a sume bayako motsi Ammi tazaro idanunta ta kankare tsabagen tsorata da mamaki, awani irin haukace Amirah ta duka tadauki a piece of broken plate din from kasa mai sharp mouth Ammi da muryanta baya fita tace "Am…..Am….mirah Amirah" Amirah was not her self tai inda Daddy ke kwance a sume zata chakamai kwalbal Ammi takama hannunta, Amirah tai wani ihu "ahhhhhhhhhhh" ta fizge kanta zatai kan Daddy Ammi batasan sanda tasa karfi tai kan Daddy ta tare sa tana bude hannuwanta ba tana goge hancinta dake jini tace "ni zaki kashe ai ba Babanki ba Amirah, maza chakamin kwalban kinji saimu mutu mubar miki duniya!" Dakatawa Amirah tayi amman har lokacin tana rike gam da kwalban jikinta na rawa sosai tana huci, taki kallon Ammi tana wani irin nishi kaman zata shide na zuciya tawani kankame kwalban dayasa jini yafara fita daga hannunta Ammi tamike da kyar tana dingishi tayi kanta, hannunta takama zata cire kwalban amman tayi tayi takasa sai numfarfashi take tana kallon Daddy har lokacin, Ammi tafashe da kuka kawai tarungumeta tana shafa kanta sosai tace "it's okay, babu abinda yasamen eh Amirah, calm down please, bagani nan ba eh, Ammin ki lafiyanta kalau!" ko kadan she wasn't calm Ammi tadago tasake kai hannunta kan nata tace "bani kwalban kinajin ciwo" amman ina Ammi takasa karbe kwalban nan daga hannunta tsabagen yanda ta kankame kwalban gam gam. EPISODE 3️⃣
Ganin tana bata lokaci akanta ga Daddy ya suma jini nabin kansa yaşa ta share fuskanta tass sai kawai ta barta tadauki hijabinta dake kan gado tasaka tadawo inda Daddy yake gabanta na faduwa tana addu'a Allah sa wani abu bai samesa ba, taduka takai hannunta ta taba wuyansa taji yana numfashi, zanin jikinta tayaga ta kulle kansa inda ke fitar da jini tadago kanta takalli Amirah dake tsaye tarike kwalban gam that's very sharp tana kallon Daddy, she's ready ta chakamai again sabida Ammi ne kawai tadakata, kan Ammi kawai ya kwance tama rasa mezatayi akwai jama'a agidan na biki, tafita yanzu taje tace gashi gashi zasu iya kashemata yarinya, Daddy ya suma ne probably sabida shekaru sunja but he won't die zai farfado, wayanta Ammi tashiga nema taganshi chan kan gado bazata iya barin Daddy tajeba.