Kenza eBookz

Baccin so complete by m shakur - Chapter 12

Baccin so complete by m shakur - Chapter 12

Baccin so complete by m shakur Chapter 12: Baccin so complete by m shakur Chapter 12. Fitowa yayi daga lungun yataho office din Marwan, instead of yayi…

4,150 words

Fitowa yayi daga lungun yataho office din Marwan, instead of yayi knocking saiya bude kofan kai tsaye idanunsa fix on Amirah da kanta ke kasa tana wasa da duka hannuwanta hulanta yadan zame baya kadan gaba gaban kitson da aka mata yafito, sai jelan kalaba daya yafito ya kwanta awuyanta har zuwa bayanta, tayi wani irin kyau kaman ka saceta ka gudu, dago kansa Marwan yayi jin an shigo office dinsa ba knocking ba sallama yaga Saleem ne he look sick but ya tsare Amirah da idanu da kaman batamasan yana wajen ba, abu yaji ya tsaya masa azuciya yanda yake kallonta, hakan yasa yamike tsaye yakalli Amirah da kanta ke kasa yace "let's go" kallonsa Saleem yayi Marwan bai kallesa ba, wlh jiyake kaman zai haukace sabida Amirah abu kaman anmai asiri, ahankali yace "can i talk to her please Doc?"Wani kallo Marwan yamai zaiyi magana amman sabida Amirah saiya kasa kawai yabude kofa daidai Nurse Nucy tazo wajen yace "take her to her room please" dasauri Nurse tace "okay Dr, let's go" takai hannu zata kama Amirah, wani ihu Amirah ta tsandara zata fada jikin Marwan yadan koma baya strictly yace "follow her nace" ahankali tajuya tabi Nurse kana ganinta kasan she's not happy saiya dawo office dinsa yamaida kofan office din yarufe, yashigo zai wuce yaje yazauna sai Saleem yakama hannunsa ahankali yace "Marwan wlh I'm serious I lov….." Marwan bai bari yakarasa maganan ba yace "menene yarjejeniyan damukayi ni da kai before I admitted you? You can just go around and be trying to talk to my patient da haka muke bari maza suyi ai da yanzu asibitin yayi loosing integrity nasa, can't you see that she's sick? Bakaga abinda tayi just now ba? What are you trying to do? Ka tsorata ta?" Asanyaye Saleem yace "amman ai zaka iyasa ta dinga yarda dani kaman yanda kasa tabi nurse din chan zaka iyasa nima ta yarda dani" wani kallo Marwan yamai zaiyi magana sai ahankali Saleem yace "I love her Marwan!!!" Wani kalan bugawa kirjin Marwan yayi, wlh takardu yake shirin dauka amman saida yazubar dasu saiya duka dasauri jikinsa yahau rawa yana daukan papers din yana kokarin controlling kansa, Saleem dabai lura da komiba yasami waje yazauna kan kujera yayi shiru cikeda damuwa yace "I know you might not believe me but wallahi wallahi I love her, you know this Marwan, Tunda nake bantaba soyayya ba, bantaba ganin wata inaso ba wlh, but this girl I saw her once shima by accident nazo wajenka a office shikenan, the moment na kulle idanuna ita nake gani, what's funny is ko sunanta ban sani ba ma, I know nothing about her, I know she's sick but I just don't care, I really, really just love her, imagine I'm in this hospital nasa ka kwantar dani just because of wacce nagani for just few seconds, I don't know what's going to happen but please Marwan help me kaji, I want to marry her, I don't care about batada lafiya or wani abu ni ko kanjamau takedashi ina sonta ahaka and I want to marry her, I want to make her my wife, please Doc Bro make her talk to me nasan this is not our agreement, I know, I just want her ko hi ne tacemin ko zuciyata taji sanyi please" yayi maganan yana kwanciya akan dogon couch din yana kallon saman dakin, Marwan da tuntuni yake aduke yamike tsaye da kyar, yanaji kaman zuciyansa zai fito daga kirjinsa sabida yanda yakeji, har wani duhu duhu idanunsa ke masa wlh, tashi zaune Saleem yayi dasauri saiya mike tsaye yazo inda Marwan yake jin baice komi ba gashi yanaji kamna zai zare, yakalli Marwan daya sauke kansa kasa yana hade haden wasu takardu a file, saiyakai hannunsa yakama hannun Marwan ahankali yakai saman kirjinsa yace "Marwan kaji yanda kirjina ke bugawa, I have no one but you, I don't have someone like Mami in my life dazan gayama matsalata take sona har zuciyanta and she will see to it nasamu solution to my problem no, nataso a hannun Matan Yaya na wacce she doesn't care about me, I have no one to tell Marwan, you're all I got, please help me, I really, really love the girl, wlh, wlh ina bala'in sonta" ahankali Marwan yadago idanunsa dasuka dan kada kadan ya kallesa amman yadake sosai bazaka taba gane halin dayake ciki ba, cikeda karfin hali yazubamai idanu, wlh saiyaji yabasa tausayi, baitaba ganin Saleem suffering and struggling like this ba plus he looks very very sick kaman harda withdrawal syndrome ma kedamunsa na alcahol, ahankali yace "why are you putting me in a very tight spot Saleem why? I'm a Dr here I'm not meant to be arranging meet and greet na patients dina suyi soyayya, soyayya can be dangerous for masu matsalan brain especially if it sour saiya kara juya kansu, to be on a safer side we don't welcome it, why Saleem? All my patients are under my care and watch why are you making me do this eh? Why me"? Ahankali Saleem da muryansa yayi rauni sosai kaman zai mai kuka , yace "sabida nasan duk duniyan nan you're the one person dazan iya kira dake sona tsakani ga Allah dudda baciki daya muka fito ba! Nasan babu abinda bazaka iyamin ba, idan is against law na asibitin muyi soyayya komu kebe I saw her parents sunzo dazu, stand for me lemme inaso naga iyayenta na nemi aurenta, I want to marry her Marwan!" Yayi maganan daidai Abba na sallama tareda knocking yana bude kofan office din dan tunda aka kwantar da Saleem baizo yadubasa ba, karaf maganan a kunnensa, ya tsaya jikin kofan yace "you want to marry wace Saleem?!". EPISODE 2️⃣3️⃣

Dukansu juyowa sukayi suka jin magana da muryan Abba, da ace any one of them zai lurada Marwan hatta yanda numfashinsa ke fita ya chanza he started breathing kaman wanda is about to faint, dukansu babu wanda ya iya magana ganin Abba, tura kofan Abba yayi yashigo office din yana gyara babban rigansa dake jikinsa dayasha aiki, yataho har zuwa wajen table din sai yasa hannunsa kawai yakama Saleem yajawo hannunsa Saleem yabiyosa dan ba karfi ajikinsa ma, cikeda so dan wlh Abba na son kanninsa ba kadan ba yace "Abubakar Saleem mekace just now"? Tsare Abba yayi da idanu still baice komiba, Abba dasauri yace "kanason kai aure naji kace?" Gyadama Abba kai yayi yana lumshe idanu yabude, Abba baisan sanda yace "Alhamdulillahi Rabbil Alameen" yasake kallonsa yace "wacece yarinyar dakake so ka aura? Yar wani gida ne"? Shiru Saleem yadanyi saiya kalli Abba muryansa ya kwanta sosai kaman batasa ba yace "Abba nima ban santaba, rannan danazo nan wajen Marwan na ganta"yadanyi shiru saiya kalli Abba yace "the only reason nazo hispital dinnan sabida na amshi katin Marwan ne dan banda kudi, ina bude office dinnan na ganta and my heart skipped for a moment" yayi shiru all memory na Amirah da abinda yafaru rannan na dawomai kaman yanzu ne akeyi, asanyaye yace "Yaya wlh itan dana gani yasa nace a kwantar dani, for the first time naji sense of responsibility, naji I want to be a better person for her, I really want to let go of my bad life and set up a good one and become responsible person for wacce nakeso" Abba dake kallonsa yace "da kyau Saleem very good"Abba yace "wacece? Nurse ce ko likita?" Dan lumshe idanu Salesem yayi yace "Yaya mara lafiya ce itama anan, i don't even know her name" Abba ya tsaresa da idanu sosai kafin yace "Saleem duk wanda ke cikin facility nan idan ba Dr ko nurse, ko wani ma'aikaci ba it only means ko yan shayeshaye kokuma mahaukata koba hakaba"? Dan ijiyan zuciya Saleem yasauke yace "Yaya ko gurguwa ce ni ita nakeso, I don't care about her condition Yaya, ita nakeso ka auramin!" Saleem yafada adan zafafe dan he's damn serious he's not even ready ya saurari duk wani wanda zaice mai mahaukaciya ce, menene menene ko matatta ce ba mahaukaciyaba yanason abinsa, Abba yadade yana kallon Saleem yana nazarinsa, Saleem is a very stubborn yaro tun yana yaro, ayanda take maganan nan idan bai masa abinda yakeso ba tsaf zaiji agari Saleem yaje yayi aure. Ahankali ya juyo yakalli Marwan dake bude bude folder yana cicciro takardu wanda ko ganin takardan bayayi da kyau tsabagen yanda kansa yadauki zafi Abba yace "Marwan" ijiye takardun Marwan yayi yace "na'am Abba" Abba yace "wacece yarinyar wani ciwo ke damunta?"Abu Marwan yaji aransa yakai kusan 20secs baice komiba chan saiyace "ahhmm bata magana ne haka Abba, rashin son mutane da sauransu" Abba yayi dan jimmm yana tunani saikuma yakalli Saleem dake kallonsa looking very serious, sai Abba yamaida kansa yakalli Marwan yace "yakake ganin za'ayi Son? Do you think with condition na yarinyar zata iya aure"? Wannan karan hannu Marwan yasa yaja kujera yazauna danji yayi kaman zai fadi saiya dauki pen yabude wani file kaman yana rubutu dan baiso yakara making eye contact dako Abba ko Saleem zasu iya gane something is going on with him, da yar karaman murya yace "I dont know Abba is her parents that can decide that" Abba yadanyi jim yana tunani yace "kuma hakane, how about kabani number mahaifinta?" Ahankali Marwan yace "bamu da number mahaifinta" Saleem saiya juyo shima ya kalli Marwan din dayake rubuce rubuce kaman da gaske, Abba yace "to zaka iya bani address na gidansu yarinyar"? Hannu yasa yadauki file na Amirah dake kan table nasa saiya mika ma Abba batare daya dago kai ba dasauri Saleem yamike yasa hannu ya karbi folder, hannunsa har rawa yake tsabagen kosawa, yabude folder Amirah, the first abu daya gani was sunan Aminatu so is that girl dayaga file nata a dakinsa rannan itace oh what a destiny.

Dasauri yawuce address din yace "ga address din Yaya ka dauka saikaje ka gayama Babanta" karba Abba yayi yana karanta address din yace "nasan layin nan sosai ai, zan nemi mahaifinta in sha Allah kam" saiya rufe folder yaba Saleem, daidai pager na Marwan na ringing dasauri yamike batare daya hada idanu dasu ba yace "Abba bari naje inada patients" Abba yace "to, to, toh kaje nima bazan wani jimaba zan tafi" Dasauri Marwan yayi kofa yabude yafita.

Juyowa Abba yayi yakalli Saleem cikeda so yace "Saleem kasan abinda kakeyi kuwa? Kasan menene auren wacce batada cikakken lafiyayyan kai kuwa? Don't just think of now? Think about your future kids da sauransu, are you sure"? Ahankali Saleem yace "Yaya nizan zauna da ita ba wani ba, yaran kuma nawane, ko gurguwace inasonta ahaka, idan kuma wannan ma bazaka tsayamin ba zan fita na nemi wayanda zasu tayani neman aurenta" Saleem yayi maganan cikeda rashin kunya da rashinji, Abba yayi shiru yana kallonsa yazaiyi maraya ne Saleem, kuma amana, dan kallon Abba Saleem yayi jin yayi shiru ganin fuskansa yanuna baiji dadi ba saiyace "I'm sorry Yaya, this days the only thin danakeyi is tunani, mesa zan kamu da son wacce ko sunanta ban sani ba banda yanzu danaga folder ta, soyayya magani ne and she can be fine, I sincerely love her and I will take care of her, Abba she's the most purest girl aduniya, she's like a dewdrop, very clean, fragile and pure" Abba yayi shiru yana kallonsa kaman ba Saleem ba ahankali yace "shikenan I will meet mahaifinta this weekend, ya jikin naka"? Ahankali yace "fine" tashi Abba yayi yace bari naje toh. Abba nafita yasake bude file din yana dubawa yana karance karance.

Marwan na fita wani Dr daya gani yaje yatayasa duba patient din yafito da sauri yawuce motansa yabude yashiga yarufo thank god motan tinted ne babu mai ganinsa, glasses yacire da sauri yana wani irin nishi kaman mai asthma kirjinshi namai zafi, Allah yasani shi baisan takamaiman meke damunshi ba, is against ethics na profession nasa wato likita ya tsaya yana soyayya da patient nasa, patient dinsa is under his care, why would he harbor love feelings towards yarinyar da bamatasan menene love ba or understand menene so. Shi baisan ko sonta yakeba that's one, menene toh numfashinsa ke nema ya tsaya sabida Saleem ya nuna yana sonta zai aureta ahaka? Why is he feeling kaman zai mutu? Is he truly in love with Amirah? How? Why? And his brother too is inlove with her! Ya runtse idanunsa, daidai wayansa yahau kuka, ciro wayan yayi yana maida glases nasa ganin Ya Ammah ce saiyaki dagawa harya katse, wayan yashiga ringing Mami ce this time hakan yasa yadauka kafin yayi magana Mami tace "kana ina Son is time for the meeting" dan jim yayi saiya kalli agogon hannunsa, murya chan kasa yace "Mami is already time for juma'a daga masallaci sainazo" ahankali Mami tace "toh shikenan Allah kaimu lokacin, meya sameka why is your voice so down"?Ahankali yace "kaine kedan ciwo" Mami tai shiru kaman bata yarda ba tace "kadawo gida kasha magani ka kwanta" daga background din yaji muryan Farida tana Mami I want to talk to Uncle M, wayan yacire yasa a speaker ya ijiye kancinyasa Mami tace "ga Farida zatai magana dakai" ahankali yace "okay" yanajin muryan Mami tana cewa fitinanniyan yarinya.

Farida tai dariya tana daukan wayan ashagwabe sosai tace "Uncle M" ahankali yace "Anty F"strictly Marwan da muryansa bata fita da kyau yace "I'm at work banson shirme so what's the matter?" Tafiya tashigayi he could feel tafiya take yaji karan tarufe kofa ahankali tace "cikina ke ciwo and I took maganin nan is not stopping" kawai saita sakin mai kuka yayi shiru, saiyasa hannu yadauki wayan yacire a speaker ya kara a kunnensa ahankali yace "ask Faiza to make tea for you I will come back soon saina miki allura okay, stop crying ki kwanta and rest" Gyadamai kai tayi tace "ohkay" katse wayan yayi kansa na sarawa, yakai 10min ahaka sannan ya kunna motan yaja nasallacin juma'a yatafi. EPISODE 2️⃣4️⃣

Yaune rana na farko dayake zaune yanajin hudba amman zuciyansa zafi yake masa kaman yayita kuka haka yakeji, sai kawai yafara kiran sunayen Allah hakan yasa yadanji natsuwa, shi baimasan sanda yafara sonta ba? Baisan mesa yakesonta ba? Amman jiyake kaman zai mutu sabida what ever is happening, ahaka akai salla aka idar sannan yafito yana tafiya ahankali yashiga motan sa yaja zuwa gida, horn yayi Musa yabude masa gate yakarasa yayi parking yana kallon motocin dake compound wanda duk na yayyinsa ne he thought by now kowacce ta tafi yanzu zasu damesa.

Bude kofan motan yayi ya fito ba labcoat ajikinsa yabarsa a mota, sai yar small Leda asibitin su wanda na alluran dazaima Farida ne a hannunsa yawuce da sallama yabude kofan falon yashiga ciki yana maida kofan yarufe all sisters dinshi suna falon saikuma wata da kallo daya yamata yadauke kai cus baisan wacece ba kuma baiga amfanin kallonta ba, Mami ta tsaresa da idanu tace "ya juma'an? Ciwon kan ya sauka"? Anutse yace "Alhamdulillah Mami, where's Farida?" Mami tace "suna dakinsu sun kwanta" ahankali yaji wata murya tace "ina yini Ya Marwan" dan tsayawa yayi saiya juyo ya kalleta still baiganeta ba gashi sai kallonsa take, gyadamata kai yayi alamun yauwa yajuya abinsa yayi staircase sai Ya Fadila tabisa yayi sama Mami na kallonsa, Ya Fadila na whispering. "Wai is this how you treat girls Doc?" Dan juyowa yayi ya kalleta looking confuse yace "wat"? Daidai sun karasa sama kamasa tayi tace "didn't you recognize that girl?" Marwan yace "which girl"? Ya Fadila takama kanta tace "Ya Allah wani kalan mutum ne kai Marwan" saita juyar da kansa tai masa pointing Ramla tace "that girl dake zaune next to kujeran Mami is she not the girl data taimaki Mami a airport, Mami asked her to come here dan muganta tana sonka da yarinyar and she's good kasan mene, she studied accounting as Major a Florida, tanada masters, and she's only 26, very young uhm Marwan" lumshe idanu yayi sannan yabude yakalleta yace "I have no business with whatever you guys are doing here, I came back for meeting idan kuma bashi zakuyi ba i have plenty patients waiting for me a hospital plus I have headache" kafin tai magana yawuce dakin Farida ransa abace abin yaba Ya Fadila mamaki hardly Marwan ke fada haka.

Su Mami suka cigaba da hira dan daman bata nunama yarinyar komiba tun jiya sukai magana itane ma tace tanaso tazo ta gaida Mami, Mami tace mata tazo yau juma'a, Mami ta lura yarinyar takamu da son Marwan and tanada hankali she just wish Marwan will see the girl.

Allura yama Farida yakalli Ya Fadila dake kansa yace "I'm hungry give me food" balla masa harara Ya Fadila tayi tace "kira Mamanka Mami mara mutunci mai masifa" dan murmushi Farida tayi ta yunkura tace "Uncle nizan kawo maka" dasauri yace "no kwanta abinki" Ya Fadila tace "au iyye hakane yarinya wato I love my uncle I don't love my Aunty zaki kirani ai ina zaman zamana for something Farida baniba" boye kanta tayi abayan Ya Marwan tana murmushi, shima Marwan yayi murmushi kadan, Ya Fadila tajuya tafita yajuyo yana kallon Faiza datai bacci yace "kema sleep" gyadamai kai tayi sai ahankali tace "Uncle you don't love that girl right?" Tsareta yayi da idanu yace "who"? The one that's with Mami downstairs, ahankali yace "do you love her"? Girgizamai kai tayi tace "no" ahankali yace "why?" Ahankali tace "cus I know she's not the type of girl you will love"tsare Farida yayi da idanu yace "what type of girl do you think I will love" murmushi tayi tace "someone like me and Faiza" tsareta yayi da idanu saiyaja hancinta baice komiba yamike yanajan bargo yarufe mata yajuya yafita daga dakin daidai Fadila na hayowa sama da abincin sa a tray ya kalleta ta ballamai harara tace "Mami tace kagama ci ka sauko katayata sauke Ramla agida kafin kawuce asibiti"baice komiba kawai ya karbi abincin yawuce dakinsa yazauna ya ijiye abincin yawuce gado ya kwanta bazaima iyacin abincin ba yasa hannunsa a switch na wutan dakin saiya kunna, saiya kashe, saiya kunna saiya kashe yana tunani, knocking kofan dakin akayi tareda budewa aka shigo Mami ce, suka hada idanu saita kalli abincin dako tabawa baiyiba, saita maida kofan tarufe ta taho wajen gadon hakan yasa cikeda karfin hali Marwan yatashi yazauna, Mami ta taho bakin gadon tazauna ta tsaresa da idanu, dauke idanu yayi da sauri dan yanzun nan saita ganosa, calmly tace "meke damunka yau"? Ahankali yace "bakomi" tsaresa da idanu Mami tayi baya kallonta yake maganan, jintai shiru saiya juyo ya kalleta, ahankali yace "Mami do you really want me to marry that girl? Idan ita kikeso na aura I can marry her for you" shiru Mami tayi tana kallonsa, ahankali tace "why will you marry wacce bakiso"? Dan ijiyan zuciya yasauke yace "sabida babu abinda zaki bukaci namiki da bazan iya miki ba" Mami na kallonsa sosai tace "nafison ka auri wacce ranka keso" gyadamata kai yayi saiyayi shiru, duk Mami na kallonsa, saita matso dab dashi tadaura hannunta akafadan sa tace "did something happen a hospital naku ne? You look very sad" lumshe idanu yayi baiso tacigaba da kallon kwayan idanunsa dan zata ganosa tsaf, murya asanyaye yace "kaine ke dan ciwo kawai nai bacci zai dena" ko kadan Ammi bata yarda ba amman batason ta takura shi, ahankali tace "koma menene I'm right here Marwan, you're not alone kaji, stop being sad, komi nufine na Allah, kwanta to" Mami ta kwantar dashi dakanta tasa kansa a pillow dataji yayi dumi, ya lumshe idanu yaki budewa ya kalleta and this is one behavior nasa tun yana yaro, idan yanada damuwa daya bude idanu Mami ta kallesa ta gane gwara ya kulle idanunsa and end up sleeping, sai Mami taja bargo tarufesa tana kallon idanunsa tacikin glass ganin kaman hawaye yafito daga eyes nasa ya tsaya a hanci, tasan is not this yarinyar nan that is making him sad, tun dazu data kira taji muryansa wani iri meke faruwa toh. EPISODE 2️⃣5️⃣

Yauma har dare su Abba basu dawoba amman Ammi tariga tagayama Yayanta yasa filinta a kasuwa agani. Bayan isha'i taji ana bude gate na gidan dasauri ta tashi tabude window taga Daddy ne da Maman Baby, hakanna jitayi she's stronger than before komawa tayi tazauna Miemie data fito daga dakinsu tace "Ammi Daddy ne?" Gyadamata kai Ammi tayi batare datai magana ba chan tace "daukomin hijabi na Miemie" dasauri Miemie tawuce bedroom na Ammi tadauko ma Ammi hijabin tafito takawo mata karba tayi tasaka sannan tace "kijirani bance ki biyoni ba" Miemie tace "toh" bude kofa Ammi tayi tafito tasaka takalmi saita wuce flat na Maman Baby Sallama tayi duk suna falon kananun yara şu biyu maza aura ta ne suka amsa sai Ammi tadaga labule tashiga tana murmushi tace "Hassan an dawo lpy" yaran suna dariya sukace lafiya lau"? Takalli Maman Baby dake kusada Abba tace "Ya hanya Maman Baby" wani banzan kallo tamata bata ansa ba Ammi takalli Abba tace "inason magana dakai" kaman jira Abba yake yace "daga zuwana bazaki barni na huta ba indai zancen mahaukaciyan nan ne zakimin wlh bazakisan inda take ba, bari kiji wallahi wallahi kinji nai rantsuwa har abada mahaukaciyan nan datakusna kasheni bazata kara shigowa gıdana ba, duk yana kumfan bakin nan Ammi kallonsa take adake sai kawai tazagayo tazauna akan kujera ta fuskanci Daddy sosai tace "ba sabida Amirah nazo ganinka ba sabida kaina nazo" Daddy saiyadanyi shiru yana kallonta hakana Maman Baby, da kyar yace "Ina jinki" dudda akwai yara awajen amman Ammi ta share tace "inaso ka sawwakamin ne!" Hakanna Daddy jiyayi gabansa yafadi dum Maman Baby tawani gyara zama tanaji har wani sanyi sanyi ajikinta, Ammi dake kallonsa sosai tace "karka damu I don't plan on collecting gidan y'ata ko motocinta ko dukiyanta dake hannunka, idan kaga dama kabamu, idan kaga dama karka bayar duk daya, sonake kasakeni nabar gidanka peacefully y'ata naruga nasan inda take a asibiti zanje na dauketa mukoma gidan yayana da zama wat I want is kasake ni, nazo ja tambayeka ne sabida karubutamin takardan kabani idan baka bani ba the first abu dazanyi gobe da safe is naje namakaka a kotu dan na gama aurenka har abada"wlh tunda yake da Ammi bata tabamai magana dakai kalan tone dinnna ba for 19yrs yanzu sai kawai yaji kirjinsa na bugawa itakuma Maman baby taji wani mugun farin ciki, baki Abba yabude zaiyi magana Maman Baby tace "dalla Sweetheart kai shashasha ne dasai ta makaka a kötü ta tona maka aşırı zaka saketa iyye? Ka saketa mana! Taje Chan şu karata wanchan diyarta ka kira dan garejin nan ka daura musu aure abar mana gidanmu oho"Daddy ya kalli Maman Baby sosai saiya kasa magana ma Ammi tace "kainake jira" Maman Baby kawai tamike tashiga wani daki tafito da takarda da biro tazo tabama Daddy tace "idan kai ba tsinanne bane shine mace zatazo ta tasaka agaba kan ka saketa ka kasa ita taci baya wlh kana rufamata ma asiri dalla ka saketa" hannu Daddy yasa yakarbi takardan saiya kalli Ammi yace "inhar na sakeki wlh ko takarda bazan siyawa Maryam takai gidan miji ba and blame it akanki ke kikaja" Ammi dake kallonsa cikin idanu tace "duk abinda kakeso kayi" ransa yaji yana baci ganin kaman so Ammi take ta kuresa tadauka bazai iya sakinta bane kodanbtaganta kyakkywa iyye saiya shiga rubuta ni Idriss na sakeki saki Maman Baby dake kansa tace "saka uku dan tasan amfaninka wlh wlh" Daddy yarubuta uku yayi signing instead of yaba Ammi saiya jefar akasa yamike tsaye fuuu afusace yabar dakin Ammi tasa hannu tadauki paper tamike tawuce tafita Maman Baby tace "idan bakibar gidan nan gobe ba wlh sai an watsar da kayan ki".

Wucewa Ammi tayi takoma flat nasu tana shiga taga Miemie a kofa Miemie tace "Ammi bai dakeki ba" girgiza mata kai tayi ahankali tazauna saitadan sauke ijiyan zuciya takalli takardan saki kawai saitaji kuka bawai she loves Daddy bane but saki is something dake taba kowace mace wlh wani iri taji saitakai hannu ta share fuskanta Miemie ta rungumetata tana shafa bayan Ammi sun dade ahaka Ammi tadago kanta tace "ba lallai aurenku yakai nan da 2month ba Babanki yace zai kirasa yadaura aurenku" zaro idanu Miemie tayi ahankali tace "Ammi" murmushi Ammi tayi tace "karki damu kome yayi zan miki kayan daki zanmiki komi daya kamata kinji Maryamana" gyadama Ammi kai tayi, ganin jikinta yayi sanyi Ammi tace "maza muje mufara hada kaya, mufara da dakinku bari muhada kayanki dana Amirah ko" Ammi tasaka takardan sakin a handbag nata sukasauke yan akwatinan su aiki suka shiga yi tass suka hada komi Miemie sleep ma daga baya Ammi ta lullubeta tawuce kitchen ta hahhada kayayyakinta tanada buhu tazauna tabude envelope na kudin da Marwan yaba Miemie bandur na yan 1k guda biyu ne that's 200k da kudin zata sami mota gobe dazai kwashe jayahta tasss sutafi gidan Yayansu bata taba sanin kudin zai taimakesu hakaba.

Readers Also Read