Kenza eBookz

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 31

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 31

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 31: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 31. "To Mama " na faɗa ,ina fitowa daga ɗakin Hajiya muka yi…

3,660 words

"To Mama " na faɗa ,ina fitowa daga ɗakin Hajiya muka yi kiciɓis da Lubna.Ta wani zo da sauri ta rungume ni tana kuka kafin ta ce "Haule na gode sosai da yadda kike ƙaunata daidai da ɗaya rana ba ki taɓa guduna ba,kuma...kuma" sai ta yi shiru.

Na ɗan ja baya kafin na ce "Lubna daga ina kike? Me ya faru da ke ne?"

Ta ce "tun da muka rabu sai Jagaba ya kai ni wani gida ya tsare ni da wuƙa sai na sanar da shi duk wani sirri da na sani dangane da farin ruhi da tawagarsa,sannan kuma na faɗa masa yadda lamurran ƙungiyar family ke tafiya.Sai dai kafin ma na yi wani yunƙuri aka ƙara sanar da shi baƙin ruhi ya suɓuce daga hannunsu shi ne ya maido ni nan gida"

"Bai dai yi miki komai ba ko?"

Ta ce "Babu abin da yayi mini"

Ina jin haka sai na ja ajiyar zuciya kafin na ce "alhamdullah! Dama dai tsorona kar ya taɓa mutumcinki"

Idonta ya kawo ƙwalla ta ce "mutumci na nawa Haule? Ai babu sauransa,tun ranar da na biyewa son zuciya na bai wa Dr David shi a ranar kuma suka zuba mini ƙwayoyin cuta ta yadda wani namiji ba zai sake mora ta ba"

Cike da tausayinta na ce "duk wata matsala ta duniya tana da magani Lubna,kin ga ki nemi man lalle mai kyau tare da ƴaƴan magarya ki yi tafasa su sai karanta duk abin da kika sani daga cikin Alkur'ani mai girma ,in sun ɗan sha iska sai ki zauna a ciki ki kunna karatun Alkur'ani kina saurare har sai ruwan sun huce sai ki fita. Sannan kuma ki samu man zaitun da na Habbatu sauda da kuma jan muski da fari ki haɗe su wuri guda ki yi karanta surori uku na ƙarshen Alkur'ani,ki haɗa da ayarul ƙursiyu da amanar rasuluh.Sai ki karanta *Waƙadimna ila ma amilu min amalin faja'alnahu haba'an mansura* sau ba adadi ki dinga shafawa da izinin Allah duk wani tsafi ko sihiri ko wata cuta da jinnu suka sakar miki duk za ta fita,ke dai kawai ki yi yaƙini ki yarda da Allah sannan kuma kar ki yi gajen haƙuri ki maida hankali "

Lubna ta yi wani murmushin da ya fi kuka ciwo kafin ta ce "da a ce tun farko na sanar da ke gaskiyar labarina da ƙila tuni na warke"

Na ce "shi yasa babu kyau ɓoye cuta a wurin da mutum yake tsammanin samun maganin warakarsa,ba kuma ko ina ne zurfin ciki yake da rana ba" "Haka ne na gode sosai,bari na je gida na ga Ummah " har ta juya za ta tafi na tsayar da ita na ce "ki yi wa Ummah godiya don ba don ita ba da tuni kin faɗa tarkon sheɗan, addu'arta ce ta zama garkuwa a gare ki"

Ta saki murmushi kafin ta fice,ni kuma sama na haura na gyara ɗakin MAHEER tsaf ina dab da na shiga wanka ya shigo fuskar nan a murtuƙe yau ya koma sak Oga Maheer.Ganin yadda yake shan ƙamshi yasa na share shi na shige wanka,bayan na fito sai na ga yana haɗa kayana waɗanda shi ne ya saya mini.

"Za ki je babban gida,wai sai sun yi biki an kuma shafa miki lalle da duk wata al'ada da ake yi" ya faɗa kamar zai fashe .Ni kuma daɗi na ji ko ba komai zan ga Innarmu,na ɓoye murnata a ciki na ce"to mene ne na fushin? In ba ka so na tafi ai kawai sai ka sanar da su"

"Na sanar da su me? Hum! Ki shirya dai ku tafi ga Mama can ita ma yadda kika san ba ita ta haife ni ba haka ta goyi bayan hakan"

Kasa riƙe dariyata na yi kawai sai na shiga ƙyalƙyatawa,yayi tsaye yana kallona kafin ya fice.Sai kuma na ji babu daɗi,a haka na kimtsa na sauka ƙasa sai da na ci abinci kafin direba ya kai mu.

Babban gida,ya ci sunansa tabbas don yana da girma sosai sannan cike yake da ahali haka aka dinga gabatar mini da kowa har na saje da su.Sai yamma lis,sannan Aliya ta zo yau ɗin ma sai da ta bani madarar nan mai magani ina dab da na sha Innarmu ta aiko kirana a dole na ajiye kofin na fita.

Ina zuwa sai na tarar da anty Aliya ita da sauran cousin sun jibgo uwar sayayyar kaya,haka na zauna ina dubawa shaf na manta da zancen wata madara sai lokacin da Hajiya ne ta zo yin sallama za su koma ita da Aliya.

"A nan za ki zauna wai?" Aliya ta tambaye ni fuskarta cike da takaici. Na ce"eh sai an saka ni lalle wai"

Ta ɗan taɓe baki kafin ta ce "kar ki bari a yi miki wanka da ruwan lalle Haule "

"Don me?" "Saboda rayuwarki na cikin matsala" "Matsalar me kuma? Wai na tambaye ki yaushe ne aurenki da Dr Muhamud?"

"Ɗaya rana za a yi da na su Dr Umar da nurse Fatee " ta bani amsa. Na ce "shikenan sai ki tafi ki bar ni ko?" Ta dube ni tsakiyar ido kafin ta ce "sai ki nemo Nadia ku zauna tare" Na tuntsire da dariya na ce "wai tana wane wuri yanzu?" "Ɓoyayyar duniya mana ina ne za ta je in ba can ba? Suna can har da Mentor " "Ɗazu Lubna ta dawo" "Na sani! Ya kamata ki haɗa aurenta da Yaya Aliyu " "Don me?" na tambaya,ta ce "hakan shi ne daidai".Na ce "kin san da ta ɓoye mana labarinta ita ɗin ba budurwa ce ba" .Aliya ta ce "shi ma ai ba saurayi ba ne, Allah kaɗai ya san iyakar ƴaƴan mutane da ya ɓata" "Haka ne!" na faɗa ina jin kuma babu daɗi,haka dai muka rabu.

★ Cikin sati guda kacal wata irin nutsuwa ta saukar mini,ina zaune luntsum cikin ahalina ina samun kulawarsu babu takura sai rarrashi ta kowanne ɓangare.An tsayar da ranar bukukuwanmu duk a rana guda, kowanne ɓangare sai shirye-shirye ake yi musamman ma dai Lubna wacce ke ta fafutukar ganin ta samu lafiya.Ta ɓangarena kuma sam na kasa gane madarar mece ce Aliya ke bani kusan kullum,amma kamar abin tsafi ko ɗigo ɗaya ban taɓa sha ba don tamkar ana nisanta ni da shan madarar da zarar ta bani ita sai wani uzuri ya gifta kuma in na dawo ban ganin kofin.Wannan al'amari ya kwashi wurin wata guda currr,yanzu ma ta kawo mini ita amma zuwan Yaya Aliyu ya hana ni na sha duk ya bi ya tayawar wa da mutane hankali yadda yake kuka kamar ƙaramin yaro yana neman gafara.Da na ji alamun ni ma kukan zan yi sai na koma can ɗakina da aka ware mini,ina buɗo ƙofar daidai lokacin ne kuma wani hannu wanda ba a gani da kyau ya ɗauke kofin madarar da Aliya ta bani.Duk yadda na so na yarda da abin da idona suka gane mini sai aka juye mini kwanya haka a dole na watsar.Kwanciyata na yi da wuri,don gobe ne za a gudanar da shafin lallen amarya da kuma wanka.Sosai na yi bacci kamar matatta,sallar asubah ma dakyar na iya yin ta.Wuraren ƙarfe tara aka soma shagalin bikin,an shafa mini lalle wanda na ji tamkar an zuba mini wani sababi yayin wanka haka kawai na daure aka gama.Sam wunin kasa cin abinci na yi har dare yayi,ina shirin kwanciya anty Aliya ta shigo hannunta riƙe da kofin madara ko kafin ta kawo gare ni kofin ya faɗi ƙasa madarar ta zube.Na lumshe ido ina kallon ɗan jinjirin macijin da ke ɗauke da siffar madara yana kallona da idonsa ƙuru-ƙuru kafin ya narke kamar ƙanƙara.

Anty Aliya ta yi saurin ɗauko abin gogewa,sai dai kafin ta dawo komai ya ɓace kamar ma babu abin da ya zuba.Da wannan mamakin ta fita yayin da ni kuma na yi kwance lamo ina tunani,kiran waya ne ya katse ni.Maheer ne,hira muka yi sama-sama wacce take cike da kewa da kuma zaƙuwar ranar da za mu tare a karo na biyu. Muna cikin wayar ne wani iska ya soma shigowa ta window tare da soma kashe mini jiki,ban san lokacin da wayar ta fita daga hannuna ta faɗi ba.Wani irin yanayi nake ji kamar wacce aka tsoma cikin ruwan ƙanƙara,kafin a hankali na soma lumshe idona aka saka ni baccin dole.

Wata tsohuwa ce ta bayyana a gabana,hannunta riƙe da tasa da kuma almakashi.Muryarta a shaƙe take ba ta fita sosai,"lokaci yayi da za ki bayar da hadiyar da kika ɗauki alƙawari" shi ne abin da ta furta kafin ta ware cinyoyina,ina jin lokacin da take saka mini almakashi tana datse jinjirin da ke kwance cikin marata a haka har ta gama ta fiddo shi duka kafin ta haɗe shi wuri guda ya zama complete jariri,sai ya soma tsala kuka yana harba ƙafafuwa a haka ta bi ta window ta fita.

Daidai nan na ji wata irin muguwar azaba ta ziyarce ni,wacce ta yi silar tashina daga bacci.Kasa jura na yi kawai na fasa ihu,ƙuguna da marata sun ƙulle ga wani irin yajin azaba da nake jin yana tsirta mini kamar ƙasana zai buɗe.

Kusan duka ahalin suka kewaya kaina,suna tambayata amma babu wanda na iya ba amsa.Ina a haka aka kira MAHEER,ya zo ya kai ni asibiti can ɗin ma babu abin da ya sauya duk wasu allurai da ake tunanin za su yi mini magani an yi amma a banza.

Daga ƙarshe Aliya ta zo,idonta sun kaɗa sun yi ja ita ce ta sanar da su da su bar ɓata lokacinsu komai za su yi mini ba zan ji dama ba har sai in alƙawarin da na ɗauko ɓoyayyar duniya ya cika. A wannan wunin ranar mutuwa ce kawai ban yi ba,amma faɗar azabar da na sha ɓarnar baki ne.Sai da rana ta kawo tsakiya kawai na samu sauƙi wanda yake tafe da yin ɓarin cikin jikina,yana gama faɗowa wata zufa ta karye mini sai na ji kamar an gafarta mini.

Gado aka bani tare da saka mini ƙarin ruwa,idon MAHEER sun kaɗa sun yi ja kamar na Aliya su duka biyun kuma sun tsure ni da ido kamar ni ce na ce cikin ya fita.

Murya ba ta fita sosai ya ce "me yasa kika bayar da jinina ga tawagar duniyar ruhaniya?" wannan tambayar tasa ita ce ta sa na fahimci taƙamaimai abin da ke faruwa. Aliya ce ta basa amsa da "saboda ta ceto taka rayuwar! Oga Maheer ka sani ko kai aka baiwa zaɓi shi ne wanda za ka ɗauka,duk ita Haule ta yi zaɓin ne ba tare da ta san wane ne ta zaɓa ba.Maitama ya ce ruhi biyu ne da ita saboda tana ɗauke da ciki,da kuma aka tambaye ta wanne ta bayar sai ta miƙa rayuwarta su kuma a waccan duniyar kusan abin da ka fi so shi suke ɗauka.Duk a tunaninsu Haule ta fi son yaronka fiye da kanta shi yasa ta bayar da kanta,in kuma hakan ta faru dole kenan sai in ta haihu in kuma ta haihu tana iya canza shawara ta bayar da wani wanda ba lallai sai jininta ba kenan an samu hadiya mai rauni .Abin da na yi ta ƙoƙarin yi kenan,na kare jinjirin cikinta har sai ta haife shi in ya so ni na mutu madadinsa,sai dai kuma kash sun san duk wani plan ɗina hakan yasa duk lokacin da na bata madara sai an ɗauke mata hankali daga shan ta"

MAHEER ya ja dogon numfashi ya ce "Allah bamu wani wanda ya fi shi"

Aliya ta amsa da Amen yayin da ni kuma na soma hawaye ina jin kewa da soyayyar yarona, MAHEER ya matso ya janye hannuna da ke kan marata ya maye gurbi da nasa haka ya dinga shafa shi yana kwantar mini da hankali.

Ba mu wani jima ba aka sallame mu,bayan komawata gida sai aka soma yi mini gyara na musamman kwacokwam aka ɗauko Mamar Yusuf likitar mata tun daga Sokoto ta zo ta dinga yi mini mahaukacin gyara wanda na san ba don MAHEER ne ya ɓare ni a leda ba to da tabbas zai ce wata budurwa ce ni.

An yi bukukuwa cikin kwanciyar hankali,sai a ranar bikin ne muka haɗu da Abba wanda jiki duk yayi masa sanyi ya kuma tuba.A kallon farko da na yi masa kuma na fahimci dukiyar da BAƘIN RUHI ya mallaka musu ta bi iska komai ya ƙare ba su da komai in banda gidan da aka gina.

Su Hassana da Goggo Lami ma sun zo,tun daren biki su da sauran ahalinmu.Har ƙasa anty Mardiyya ta durƙusa ta nemi gafarar Innarmu da kuma bani haƙuri.

Sai da aka soma zancen zuwa ɗaukar amarya ne na ji wani labari da ya kusan sumar da ni don daɗi,wai an ɗaura auren Hassana da Yaya Aliyu sai na rasa da waɗanne kalamai zan yi wa Ubangiji godiya.

Amma a haka na daure na ci kwalliya don zuwa wurin ƙawata Aliya wacce Hajiyarsu Maheer ta yi ruwa da tsaki ta yi mata duk wani abu da ya kamata a ce uwa ta yi wa ƴarta.

Maheer ne ya zo da mota ya ɗauke ni iya ni ɗaya kawai,gidan Dr Muhamud muka yi tsinke tun a hanyar tafiya yake yi mini magiya da mu wuce kawai gidanmu in mun dawo. Ina shiga muka rungume juna ni da Aliya wacce ta yi kyau sosai,ba ta da wasu ƙawaye wannan yasa na zauna mata muka yi ta hira wacce za ta kasance ta ƙarshe a tsakaninmu don kuwa ita da Dr Muhamud duniyarmu da tasu ba ɗaya ba ya zama dole su koma can inda ke daidai da su.

Sai da dare yayi sosai sannan MAHEER ya shigo shi da Dr Muhamud,muka yi musu sallama ya kai ni can babban gida saboda ƙin yarda da na yi na bi bayansa haka muka rabu yana fushi da ni.

Da na shiga cikin gida sosai aka yi ta mini faɗan dalilin da yasa na fita ba a sani ba,shiru kawai na yi na shige ɗaki.Wanka na yi na canza kaya kafin na zauna gefen Hassana wacce ta yi uban tagumi,na yi ƴar dariya don na san abin da take zullumi. Na ce "dalla Malama ki saki ranki zo mu yi hirarmu da muka saba yi lokacin da muna gida" Ta yi ɗan murmushi kafin ta ce "jan ruwa a rijiya yana ɗaya daga cikin abin da ke janyo hirarmu Haule ko kin tuna?" Na ce "ƙwaran gaske ta ya zan manta da abin da shi ne mabuɗin da ya bankaɗe duk wani sirrin gidanmu " ta ja ajiyar zuciya ta ce "Allah dai ya jiƙan ƴan uwanmu" "Amen! Gobe za a fara yi miki gyaran jiki,ƙila rana ɗaya za mu tare ni da ke" Ta ce "na ji an ce ƙawarki ce ita uwar gidan,kina ga ba ta da matsala?" "Babu ruwanta ai,kar ki wani damu" haka muka ci gaba da yin hira har bacci ya ɗauke mu.

A ɓangaren amare kuwa cikin nutsuwa Aliyu da Lubna suka gudanar da abin da suka ta ƙoƙarin aikatawa ta hanyar haramun sai ga shi yanzu za su yi shi cikin lada.Duk da babu wata soyayya a tsakaninsu amma akwai fahimtar juna,sannan kowa ya san halin kowa.Ɓangaren Dr Umar kuwa duk da ya san nurse Fatee ta yi yayin son abokinsa hakan bai sa ya rage abu ɗaya da ya yi mata tanadi ba na dangane da rayuwar aurensu, Sosai ya taka rawar gani ya goge mata harda.Su kuwa a ɓangaren su Aliya tamkar wasu romio da julliet haka suka sha romon soyayyarsu,suna gama zama abu ɗaya sai suka narke suka zama wani haske tare da tashi sama suka koma duniyarsu.

★BAYAN WATA ƊAYA

Motoci ne birjit suka zo ɗaukata,tamkar yau ne farkon zuwana wurin mijina haka na sha kuka ina riƙe Innarmu amma haka aka cire ni aka fitar da ni,kusan a tare aka ɗauke mu ni da Hassana wacce ita ma take nata kukan. Na yi tunanin gidan Hajiya ne za a kai ni,sai bayan kowa ya watse ne na lura sabon gida ne danƙarere,babu jimawa MAHEER ya shigo cak yayi tsaye muna ƴar kallon-kallon kafin yayi wani murmushi da yasa gabana bada wani irin rasss na kuma haɗiye yawun tsoronsa.

"Ƴammatana!" ya furta can ƙasan maƙoshi lokacin da ya iso gare ni ya rungume ni,ban iya cewa komai ba sai numfashi da na ja."Mu je mu yi sallah" ya furta tare da ja na muka shiga toilet muka ɗauro alwala,bayan mun gabatar da sallah muka ci muka sha muka yi wanka tare da nufar turakarsa,inda a can ne muka buɗe wani sabon shafin sabuwar rayuwa wacce ke ɗauke da sanyin kwanciyar hankali,babu motsin BAƘIN RUHI babu wata damuwa in aka cire ta kewar Aliya da nake ji kowacce safiya a kuma kowanne lokaci.Ina ji kuma har abada ba zan taɓa cire wannan kewar a raina ba saboda Aliya ta taka rawar gani wurin kai motar nasarata ga ci,so nake yi mata na jini sam ba ta da banbanci ita da anty Aliya.

Wannan kewa tata ta ci gaba da yin gini a cikin birnin zuciyata har na tsawon shekaru biyu da shuɗewarta,sai a yau na samu sauƙin mikin da rashinta ya haifar mini da na samu na haifo mata takwara.Sai bayan shekaru biyu da tarewata a gidan MAHEER kawai Allah ya bani kyautar haihuwa alhalin kaf sa'inin aurena sun haihu dukkansu,Hassana, Lubna da kuma nurse Fatee kowacce da yaronta watanni ne kawai a tsakaninsu .A kullum in na tuna ni kaɗai ce ban haihu ba sai na shiga damuwa,amma da na mayar da al'amarina wurin Allah na yarda shi ne mai yi sai ga shi a safiyar yau na sauka.

"Congratulation an samu little Aliya" shi ne abin da MAHEER ya faɗa yana ɗora mini kyakkyawar babyn mai kama da ni a kan ƙirjina,na lumshe ido ina jin sanyi a raina. Na sumbaci goshinta kafin a ɗauke ta,aka kimtsa ni tare da kai ni ɗakin hutu inda dangina ke zaman jiran fitowata don tuni an kai musu Baby.

Lubna da Hassana an sha ɗinki atamfa iri ɗaya kai kace wasu ƴan biyu,sam ba su yin wannan mugun kishi.Gefe guda kuma nurse Fatee ce ke ta ƙoƙarin ganin ta nuna mini yadda zan shayar da baby.Duk barka aka shiga yi mini ina ta yin murmushi dai,na karɓi baby kenan zan soma shayar da ita na ji wani irin yanayi ya ratsa ɗakin.A hankali na ɗaga kaina na dubi jikin window,inuwar Aliya na gani a tsaye tana sakar mini murmushi kafin ta matso ta kama hannun babyn ta saka mata wani awarwaro mai masifar kyau.Da sauri na lumshe ido jin amon muryata can cikin dodon kunnena "congratulation Ummu Aliya ! Ƙanwar Aliya ! Aminiyar Aliya ! " ko da nake buɗe idona kuma komai ya dawo normal,amma awarwaron na nan dai a hannun baby. Abin da na lura dai shi ne har aka sallame mu daga asibiti babu wanda ya lura da shi,muna tafe cikin mota mun kawo wurin bada hannu wata almajira ta zo tana yin bara.Da sauri na zunguri Lubna wacce ke kusana na ce "wannan ba ƙawarki ba ce Zuly?"

Ba ta iya bani amsa ba sai hawaye da suka zubo kan kumatunta,haka motarmu ta wuce Lubna na waiwayen Zuly.Can ta ce "alhakin mutanen da ta cutar ne yake bibiyarta kamar yadda yake gasawa Momyn nurse Fatee aya a hannu,kowa yayi tagari don kansa"

Ko da muka isa gida na tarar da anty Bahijja ta zage dantse tana yi mini gyaran gida ita da masu yi mini aiki.Sosai na ji daɗin ganinta saboda a kaf cikin waɗanda BAƘIN RUHI ya fesawa gubar azaba ita ɗaya ce har yanzu muke zumunci da ita wasu kuwa tun ranar da na yi musu magani ba mu sake haɗuwa ba.Ba a yi girki ba,daga sabuwar restaurant ɗin gwamna ya mallakawa Hajiya matsayin goron nasara aka kawo mana abinci mai rai da lafiya,wanda aka rage kuma aka yi kyauta da shi.

A ranar sunan little Aliya taro ne aka yi na ban mamaki,wuraren ƙarfe biyun rana duk dangi da abokan arziki sun haɗu a wannan lokacin ne kuma wasu bushe-bushen algaita suka karaɗe gidan ba tare da an san daga ina suke fitowa ba kowa sai mamaki yake yi yayin da ni kuma na ƙurawa fuskar baby ido wacce take rikiɗe mini kamar ta aminiyata ga kuma awarwaronta sai haske yake fitarwa ,ban san me hakan ke nufi ba amma ina fatan Allah sa awarwaron hannun nan shi ne zai haɗe ruhin babyn da na Aliya ba a gaba kuma su haifar da wani sabon al'amari.

Ina ƙoƙarin cire mata shi MAHEER ya shigo ɗakin wanda babu kowa a ciki sai ni,fuskarsa cike da tsantsar farin ciki ya ɗauki babyn tare da kamo hannuna ya ja ni can bakin window ya shiga nuna mini taurari abin da ba a taɓa gani ba wai tauraro da rana tsaka.

"Babynmu ƴar baiwa ce ki yi murna da hakan,ki godewa Allah da ya baki aminiya irin Aliya don wannan gatan duk ita ce ta yi wa ƴarmu shi " shi ne abin da MAHEER ya furta,jin furucinsa yasa na ji na samu nutsuwar ruhi sai na kama hannun baby na kuma jingina ga kafaɗarsa muka ci gaba da kallon taurarin zukatanmu cike da annushuwa......

ALHAMDULLAH !!!

A nan labarin BAƘIN RUHI ya zo ƙarshe,in da akwai abin da wani yake ganin ya dace ace an rubuta sai ya yi wa kansa hasashe kamar yadda in kun lura buɗaɗen ƙarshe ne labarin ya zo da shi. Waɗanda suka biya kuɗi don bibiyar labarin nan ina matuƙar godiya da nuna soyayyarku,ƴan bati kuma masu niyya su sauke haƙi in kuma kun ƙi sai ku yi ta dakon haƙin nawa matsalarku ce.

My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ Chamsiya Laouali Rabo

Readers Also Read