Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 11

Bakar inuwa book 1 - Chapter 11

Bakar inuwa book 1 Chapter 11: Bakar inuwa book 1 Chapter 11. “Ranka ya daɗe bakace komai ba”. Fulani ta faɗa a hankali cike da ƙasaita tana duban…

4,497 words

“Ranka ya daɗe bakace komai ba”. Fulani ta faɗa a hankali cike da ƙasaita tana duban mai-martaba dake kishingiɗe a tsakkiyar falon hutawarsa da ko iyalan nasa ba kowacce keda ikon shigarsaba sai Fulani kawai. Bai motsa ba, sai dai ya saki wani murmushin ƙasaita irin na manya, masu kuma ji da girman mulki. Kafin ya ɗago idanunsa ya ɗan dubeta ya ɗauke kansa. “Wai miyasa ku mata a koda yaushe baku da hangen nesa ne? Yanzu banda dai son neman magana miya kawo zancen haɗa Aina'u da Ramadhan aure? bayan kunji Alhaji Hameed ya zaɓa masa mata...” “Humm mai-martaba kenan, ni a ganina ai hakan ba wani abu bane, ƙara danƙon zumincine, ka tuna fa Ramadhan shine jikanka na farko namiji a gidan nan, da ace shi ɗin ɗane da namiji ya haifa ba mace ba shine kamarfa magajinka a yanzun, amma sam yaron nan baya son zama cikinmu, akoda yaushe sai dangin ubansa saboda Firdausi ta gama shanyesa su kaɗai yake gani ita da mijinta, amma idan muka haɗashi aure da Aina'u ta tayamu yaƙin jawosa jikinmu ai muma ka.......” “Ya isa dan ALLAH. Yanzu nan Wasila bana hanaki irin wannan zancen ba? Yanzu miye abin asiri dan Ramadhan yafi buƙatar ya rayu a gidan su?. Karfa ki manta can ɗin shine adonsa, kuma shine tunƙahonsa, to bana son ƙara ji, hakama maganar haɗasa da Aina'u inhar ba sune suka sasanta junansu ba bana buƙatar sake jinta. Dan har abada Alhaji Hameed bazai saka doka na karya masaba koda akan ƴaƴana ne balle jikansa da yake da iko da shi tamkar yanda yake da iko akan mahaifinsa. Kuyi masa fatan alkairi kawai ku tsaya matsayinku”. Fulani ta taune lip ɗinta da ƙarfi da haƙora kamar zata hudashi, sai dai sanin halin mijin nata yasata sakin ɗan murmushin yaƙe da cewa, “To shikenan ranka ya daɗe, yanda kace ai haka za'ayi insha ALLAH anbar zancen. Dama can rashin zama nayi nazarine akan batun shiyyasa ban fahintaba.” “Haka nakeso ki kasance. ALLAH yayi muku albarka baki ɗaya”. Da ƙyar fulani ta daure ta amsa tana haɗiyar zuciya. A ranta ko abubuwa masu yawa take kitsawa gameda kowacce shegiyar yarinyace zata aure mata jika sama taka.

(Hummm Fulani kina kaka inaga gimbiya Su'adah uwar miji. To maji yaya za'a kwashe to😜🏃).

___★____★___

*_BINGO CITY_*

Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Asabe da M. Dauda lokacin da akai kici-ɓus. Dan kuwa dai doctor Shamsu da kansa ya shigo da Aunty Hannah da Asabe, shigowarsu babu jimawa kuma Bappi da su M. Dauda suka dawo ɗakin domin yin sallama da Raudha. Asabe ce ta fara janye idanunta tana jan tsaki, hakan yasa M. Dauda da jikinsa ke tsuma da sabuwar ƙaunarta matsowa kusa da ita cikin ɗan rawar jiki. “Haba Asabe nine fa Dauda ɗinki, dan ALLAH karkiyi fushi dani wlhy sharrin shaiɗanne”. Hannunsa dake neman taɓata ta buge tana faɗin “Kaine sheɗan ɗin kanka ai macuci kaw......” “Mommy Please!!.....” Raudha ta faɗa tana fashewa da kuka dan tasan komai zai iya faruwa akan iyayenta na raba hali. Asabe zata sake magana Bappi daya fahimci su ɗinne iyayen Raudha ɗin yay saurin dakatar da ita. “Inaga nan ba wajen magana bane, kamar zaifi muyi haƙuri muje daga waje ko masaukinku ko? Ko kuma mu bari zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.....” “A'a dan ALLAH ranka ya daɗe gara ayita yau ta ƙare, idan ta bar nan bazata sake yarda na gantaba, zama ta iya sace Aminar daga nan ɗin itama”. Harara Asabe ta balla masa, sai dai riƙe hannunta da aunty Hannah tayi ya sata yin shiru ta haɗiye abinda taso faɗa.

A tare suk rankaya gidansu Asabe, sai dai Bappi motar Dr Shamsu yabi yace Ramadhan ya koma gida, dan sanda suka fito barci ya samesa yanayi a cikin mota, ya sanshi da barcin wuri, dan shi ƙa'idarsa da tara na dare tayi to ya kwanta kuma. Sai dai kwana biyun nan daya tsinta kansa a NAYA hakan bai kasanceba, shiyyasa daya ɗan kaɗaice sai ya kama barci saboda tsabar buƙatarsa da yake yi. Rikicewa sosai Hajiyar Birni tayi da ganin Alhaji Hameed Harith Taura har cikin gidanta. Mutumin da bata taɓa tunanin koda ganin motar hawansa ba a hanya balle shi kansa. Babban abinda zai birgeka da shi babu wani damuwa ko tsantsamin gidan tare da shi, hasalima da aka kawo ruwa shine ya fara sha tare da godiya. Su M. Dauda dai an nutsu saboda hararar da Hajiyar Birni ke antaya musu tamkar ƙwayar idonta zai fito.

“Kuyi haƙuri da lattin zuwan gareku matsayin wanda ƴarku tai kasadar bama kariya. Da farko dai naso ace sai ta samu lafiya zanzo da kaina na kawota gareku nai muku godiya na kuma baku haƙuri. Sai dai an samu akasin hakan a dalilin zuwan waɗan nan bayin ALLAH da ayanzu na fahimci shine mhaifin *Raudhat*. Duk da dai na haɗu da ita mahaifiyarta a aaibiti tun randa abun ya faru, hakama ku da bansan matsayinku garetaba har yanzun. Zanyi amfani da wannan damar domin neman afuwarku, ku gafarceni, da nasan Raudhat zatayi wannan kasadar domin ni tabbas zan dakatar da ita, sai dai masu iya mafana kance ƙaddara ta riga fata, sai muce ALLAH ya bata lafiya ya albarkaci rayuwarta. Ku kuma kuyi haƙuri ku koma tare dan na fahimci baƙwa tare da juna, kuma Raudhat batajin daɗin hakan”. Kafin kowa yace wani abu hajiyar birni ta amshe zancen cikin washe baki. “Ai muke da godiya ranka ya daɗe, ALLAH ya saka da alkairi bisa kulawar daka nuna akan Raudha, dan bamu taɓa zaton hakan ba. ALLAH ya kara lafiya da nisan kwana. Suko babu sauran aure a tsakaninsu dan saki uku ne yallaɓai......” M. Dauda yay wata zabura tare da fashewa da kuka. “Ni wlhy ina son matata kuma a bincika ba'a cikin hayyacina na saketaba ranka ya daɗe...” “Eh wlhy wani malami yace asiri Larai ta maka ai”. M. Gambo ya amshe zancen yana matsar kwalar ƙarya shima. Dan dukansu kowa da abinda ke ransa tsakanin shi da M. Dauda ɗin. Hajiyar birni ta amshe zancen da faɗin, “ALLAH yayama wannan malami albarka tare da Larai, dan sun taimakeni da suka aikata wannan asiri matsiyaci”. Kuka M. Dauda ya sake fashewa da shi yana fyatar majina da tsohuwar babbar rigarsa tare da matsawa zai duƙa gaban hajiyar birni ta daka masa tsawa. Itama Asabe miƙewa tai cikin masifa sai dai duk Bappi yay azamar dakatar dasu dan shikam baisan hayaniya a rayuwarsa. “Inaga dan ALLAH ayi haƙuri tunda dukanmu nan ba yara baneba. Kamar wannan magana tana buƙatar nutsuwa kuma tsakaninku ne. Dama nima akwai abinda ke tafe dani game da Raudhat. Dan tayimin abinda wani mahaluki bai taɓa minba a rayuwa, bani da abinda zan sakanka mata da shi amma ina buƙatar irinta a kusa dani. Ma'ana inason ku bani aurenta dan ALLAH ko ta hanyar hakan zan samu damar kwatanta mata kwatankwacin alkairin data min nima...” Gaba ɗayansu suka waro idanu a kansa, tare da auna shekarunsa dana Raudha. Cikin rawar baki Asabe tace, “Alhaji kai da kanka?”. Karon farko ya saki ɗan murmushi domin ganin yanda duk sukai diri-diri, gasu dai a mu'amulat tamkar mutanen banza, ƴarsu kuma nutsatstsiya kamila, amma ashe sun san abinda ya cancanta, amma bara ya sake gwadasu. Numfashi yaja ya fesar da gyara zamansa. “Eh ni da kaina”. “Wlhy na baka ranka ya daɗe” M. Dauda ya faɗa cikin zallo da rawar jiki yana sake gurfana gaban Bappi tamkar mai neman gafara. Da sauri Asabe ta amshe da, “Nidai dan ALLAH ka gafarceni Alhaji ban amince ba, Raudha bazata auri tsoho sa'an kakanta ba. Son zuciyar da naso tafkawa a baya na biye maka Dauda kan alhaji Maude Dallatu ya kaimu ga zuwa wannan matsayin, yanzu ko na gane gsky mutuncin ƴaƴana da ƙyautata rayuwarsu yafiyemin komai a duniya dan sune gatan wata rana. K....” “K! Yima mutane shiru!!”. Hajiyar birni ta faɗa cikin daka tsawar data saka Bappi toshe kunne tilas. Aunty Hannah ma da illahirin jikinta ke rawa tun fara mganar Asabe saurin fincikon Asaben tai baya da faɗin, “Asabe kina da hankali kuwa? Kinsan wanene shi a ƙasar nan?”. Kuka Asabe ta fashe musu da shi. Cikin matsar kwalla tace, “Adda ni babu ruwan da koshi ɗin wanene. Ina duba rayuwar ƴaƴana ce, bana fatan su tashi a irin tamu rayuwar, fatana suyi ƙyaƙyƙyawar rayuwa bawai ta kuɗi ko son duniya ba. Dan haka ku gafarceni, ko ni akace na auresa yamin tsufa balle Raudha”. A tare suka hayayyaƙo mata har M. Dauda dake jin a yanzu baya buƙatar lallaɓa Asabe, dan zata masa ƙafar angulu ta kaisa ta barosa. Ganin suna neman harmutsa falon Bappi ya dakatar dasu cikin roƙo. Sai da suka nutsu ya fara magana cike da dattakonsa da kamun kai. “Lallai wannan baiwar ALLAH ta fiku gaskiya, dan kuwa tayi ƙyaƙyƙyawan hange da iyaye da yawa kan kasayi harma da ƴammatan wannan zamani akan auren wanda yake da manyan shekaru. Lallai ke ɗin uwace ta gari, kuma na gode da yanda kika nuna mutuncin ƴarki da farin cikinta shine gaba a ranki fiye da kuɗi ko wani matsayin da rayuwa ke bama bawa mai ƙarewa. Banzo nan dan na koma da buƙatata ba. Dan haka zan sake roƙonki a karo na biyu. Ina son ki yarje mijinki mahaifin ƴarki ya bama jikana auren ƴarku dan ALLAH badan wani matsayi namu ba ko abinda muke da shi. Domin Raudhat a yanzu tana buƙatar ta samu tsaro kodan rayuwarta dake a cikin haɗari, to zamanta anan tare daku kuma komai zai iya faruwa harya shafeku. Badan mu zamu iya kareta ko hana wani ƙaddara sauka gareta ba, domin muma bayin ALLAH ne kamar ita, kamar kuma ku. Alkairin da taiminne yasa nakejin kwaɗayin ɗaukarta ta zama ɗaya daga cikin family ɗina. Ta kuma haifamin jikoki daga tsatsonta da nake fatan suyi koyi da ƙyawawan halayenta wanda tarihi bazai taɓa gogewaba daga abinda ta aikata na alkairi a gareni”. A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, tare da zubama Asabe ido. Zukatansu har zallo suke nason jin amsar da zata bama Bappin. Taja kimanin wasu dogayen mintuna tamkar mai nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. “Amma dan ALLAH Baba miyasa bazaka duba akwai tazarar rata tsakanin jikanka da ɗiyata ba.....” “Babu wani banbanci ɗiyata, domin kuwa dukanmu ALLAH ne ya haliccemu, ya kumace mu bauta masa shi mai rahamane ga duk wanda yayi biyayya ga hakan, sannan mai azaba ne ga duk wanda ya bijire masa. Dan haka ki sani babu wanda yafi wani a gun ALLAH sai wanda yafi jin tsoronsa. Ni da ku da Raudhat duk abu gudane. Mutanene masu barci, masu kashi, masu mantuwa, masu shagala, masu... Masu.... Masu..... Da yawa.” “Hakane ranka ya daɗe. Na gamsu da bayaninka, zan kuma iya amincewa da buƙatarkane idan har Raudha ta amince da auren jikan naka”. Babu wanda baija ajiyar zuciya ba a falon, kafin suɗan ƙara tattaunawa da Bappi, daga ƙarshe yay musu sallama suka rakasa har wajen Dr Shamsu dake jiransa a mota dan shi bai shigo ba. Tare da su M. Dauda suka tafi, dan yace zai kama musu masauki tunda nan babu wajen kwana. Aiko sai murna suke tamkar su ciza uwawunsu dan daɗi😂😝.........✍ *_Typing📲_*

*_Episode 18_*

............Tun bayan wucewar su Alhaji Hameed Taura Aunty Hannah keta faman kai kawo a ɗakinta da kiran number First lady. Sai dai kuma tayi kira yakai biyar amma ba'a ɗagaba. Ta sake duban agogo ƙarfe goma da mintuna ashirin da huɗu. Tasan yanzu first lady batai barci ba, da wahala kuma ace tana tare da president, sai dai idan wayar ta bari a wani waje. Wannan tunanin ya sata canza akalar kiran ta tura mata guntun saƙo, da ga haka ta ajiye wayar ta faɗa wanka zuciyarta fal wasiwasin ta yanda zata ɓulloma Raudha da Asabe su amince da auren nan cikin sauƙi.

*_WASHE GARI_* first lady ce ta tada Aunty Hannah a barci, dan ko sallar asuba bata tashi tayi ba har kusan 7am. Da ƙyar ta lalubo wayar takai kunnenta tana faɗin, “Hello waye?”. Amsar da first lady ta bata ya sata wartsakewa babu shiri ta tashi zaune. “Ranki ya daɗe sorry barka da safiya! Wlhy barcine a idona”. Kanta ta jinjina saboda amsar da first ladyn ta bata tana faɗin, “Okay to babu damuwa gani nan zuwa yanzun nan insha ALLAH”.

Su Asabe na a falo suna karyawa aunty Hannah ta fito cikin gayu na ɗaukar hankali. Fatisa da Fatima dake sanye da Uniform ɗin wajen abincin Hajiyar Birni suka fara gaisheta da yaba ƙyan nata. Tai murmushi tare da musu alamar love da yatsunta. Kafin ta ɗauka doya guda a cikin plate ɗin Asabe. “Ƴar uwa barka da safiya”. Duk da Asabe tayi mamakin gaisuwar saita share ta amsa mata. “Barka dai Adda fita zakiyi ne?”. “Eh wlhy zan ɗanje wajen aiki ana nemana ne”. “Aiko da zakibi ta wajen asibiti ne dana biki sai na sauka dan inason yin magana da Raudha game da zancen nan na jiya karma suje su yaudareta abun yay nisa gara na sani”. Hajiya mama dake fitowa daga kicin a masife tace, “O ke Asabe wai mike damun kanki ne dan ALLAH? Ƙiri-ƙiri kina neman mana baƙin ciki da arziƙin dake tinkaromu!. Alhaji Hameed Harith Taura fa akace. kinsan wanene Taura kuwa a ƙasar nan dama Africa gaba ɗaya?”. Kafin Asabe tace wani abu aunty Hannah tai murmushi da amshe zancen tana ƙyaftama Hajiya mama babbar yayar tasu ido. “A'a Hajiya Mama karkiga laifin Asabe. Tana da gaskiya wlhy, ya kamata muji ta bakin Raudha mu kuma binciki halin yaron, dan aure ba abin wasa bane. Tunda ba kuɗin zata aura ba mai kuɗin zata aura”. “Yauwa Adda dan ALLAH ki fahimtar dasu. Dan naga su dukiyar waɗan nan mutanen kawai suke kallo har shi uban nata da dama kwaɗayayye ne. Yanzu idan ta auresa bata son sa, ko taje tana shan wahala fa? Ai kunga mun tauye mata rayuwa”. Hajiya Mama ta danne ɓacin ran maganar Asabe da ƙyar tana ƙaƙaro murmushi. “Hakane kuma Asabe yanzu na fahimceku. Ki bar Hannah kawai ta wuce maje wajen Raudha ɗin tare tunda dama jiya banje ba”. Badan Asabe taso hakan ba ta amince. Aunty Hannah tai musu sallama ta fice kusan tare da su Fatisa da zasu hau keke napep dan hajiyar Birni tuni ta jima da wucewa ita.

*_GOVERNMENT HOUSE_*

Tun tattaunawar da sukai da aunty Hannah ɗazun da safe ta kasa zaune ta kasa tsaye, dakon shigowar shugaban ƙasa kawai take gidan, amma har zuwa yanzu ƙarfe goma sha biyu na dare babu shi babu labarinsa. Duk da dai tun kusan tara na daren ya shigo gida, sai dai sun shiga meeting ne shi da su Alhaji Yaro glass, kuma har yanzu basu fitoba. Tai ɗan gajeren tsaki tana tura hular kanta baya ta faɗa saman kujerar, duk da sanyin ac dake gauraye da falon wata irin zufa takeji mai mannewa iya fata da jini. Ta zame rigar sama ta kayan barcinta dan itama nauyi take mata saboda tsabar ƙaguwa. Rashin mafita ya sata zamewa ta kwanta a kujerar, dan ta ɗau alwashin ko zai kai asuba tana nan tana jiransa. “Gimbiyata kina lafiya kuwa?”. Shugaban ƙasa da ya shigo a matuƙar gajiye ya faɗa lokacin da yake zubewa saman kujerar gefenta. Zumbur ta miƙe zane tana ware idanunta a kansa, sam bataji motsinsaba, duk da dama tasan shi bai damu da sallama ba dan zai shiga waje. “Lafiyar nan da sauƙi wlhy tun ɗazun zaman jiranka nakeyi anan excellency ”. Fuska ya sake ƙwaɓewa yana ture hularsa. Cikin tabbatar da matuƙar gajiyar dake tare da shi da barci yace, “Bushira kiyi haƙuri babu abinda nake buƙata a yanzu irin barci da wanka”. “Shiruna bazai yuwu ba, inko nayi to zai iya cutar damu baki ɗaya. Dan maganar ta shafi shugaban ƙasar da kuke son ɗorawa na wucin gadi” Bata bashi damar yin magana ba ta cigaba da tata maganar saboda ganin ya bada hankalinsa gareta. “Tunda ka sanarmin ƙudirinku akan Alhaji Hameed da jikansa daya kawo a maimakonsa naketa nawa ƙoƙarin nima. Dukanmu munsan Ramadhan a yanzu baida mata, tunda kune kukai sanadin rasa matar tasa, shiyyasa nake ganin a yanzu ma inhar kuna buƙatar mutuwarsa kamar yanda kuka tsara (wa'iyazubillah 🤦🏻) to dolene sai mun haɗa da matarsa, dan itace mafi kusanci da shi da zatai mana aiki batare da wani zargi ya shiga ba. Kaga kenan mune ya dace mu bashi mata a karo na biyu”. “To amma.....” “Karka katseni excellency ”. Ta faɗa tana murmushi. “Nasan tambayarka itace bai wuce ina zamu samu ba? To na gama da wannan matsalar, yarinyar data bama Alhaji Hameed kariya a filin idi ɗiya ce ga ƙanwar Hannah tsohuwar matar Alhaji Yaro, kuma a yanzu haka Alhaji Hameed ya buƙaci su bama Ramadhan auren yarinyar, sai dai mahaifiyarta na neman bijirewa dan tace sai idan yarinyar naso. Amma babanta ya yarda saboda shegen ƙwaɗayi, hakama hajiyar birni da su su Hannah ɗin, duk da dai ita Hannah muna tare, dan itace ma ta tabbatar min inhar Asabe ta nunama yarinyar bataso itama bazata amince ba saboda tanada kafiya da son uwar sosai......” “Bushira sorry na katseki, ni abinda ban fahimtaba anan, ribarmi zamuci na shiga maganar tunda sun gama ƙulla zancen auren? Inhar kuma yarinyar zata iya bijirema auren muma zata iya ƙin amsar buƙatarmu ai. Sannan karki manta Hannah zata iya yin komai danta rama korar kare da Alhaji Yaro yay mata. Imagine ma ace kina tare da Hannah har yanzu batare dana sani ba”. “Duk yanda kuke tunanin Hannah ba haka take ba, tana son Alhaji yaro har yanzu, kuma ta san ba laifinsa bane laifin Fanta ne. Amfanin auren yarinyar nan a garemu Hannah zata iya sakata tai mana aikinmu cikin siyasa batare da ita kanta tasan ita ta kashesa ba, kai koda ta sani ko muna tunanin zata sani itama zamu iya kashetan dan mulkin dai ya koma hannun Alhaji Yaro. Kasan kuma inhar zaka taimaka Hannah ta koma gidan Alhaji yaro zata aikata komai har mutuwar yarinyar, dan da arziƙi a garin wasu gara a naku, a garin wasunma gara a gidanku, a gidankun ma gara a ɗakinku, a ɗakinkun ma gara a kanka. So zataima kanta yaƙine itama”. Karon farko ya kwashe da dariya yana kamo hannunta. “Oh woow gimbiyata! yanzu dai na fahimci komai wlhy. Gaskiya kinada kai tawan. To amma mu yanzu wace rawa zamu taka?”. “Yauwa yanzu kai magana shugaban ƙasar NAYA. Abinda zakuyi shine ku samu mahaifin yarinyar ku jikesa da mahaukatan kuɗaɗe. A bashi gidan zama, itama uwar a jiƙeta tare da mahaifiyar su Hannah ɗin, dama duk wanda keda faɗa aji akan auren. Sannan ku samu Alhaji Hameed ku nuna masa goyon bayanku akan auren da nuna cewar yayi hallaci ya cancanci yabo, kar kuma ya yarda yarinyar ta suɓuce ga Ramadhan dan irinsu akeso ga mulki zasu taimaki talaka. So ko yarinyar ta bijire bataso bazata taɓa samun haɗin kan kowaba ita da uwar dole su amince”. Tashi yay kawai ya rungumeta, ji yake tamkar ya haɗiyeta dan daɗin wannan shawara tata. Tun a daren ya turama su Alhaji Yaro glass saƙo da ɓoyayyar number ɗinsa da su kaɗai keda a laƙa da ita akan gobe akwai mitin ƙarfe 6 na safe kafin ya fita office.

*_BAYAN KWANAKI UKU_*

Dukan shawarar da First lady ta bada su Alhaji yaro glass sun aiwatar da ita ta hanyar nuna cewa sunyine dan Alhaji Hameed Taura da kuma Ramadhan dake matsayin surukinsu a da, dama zamansa haka babu aure na damunsu. Hundred percent Alhaji Hameed Taura ya yarda. M. Dauda kam da su Hajiyar birni haukacewa sukai dan farin ciki, dan manyan kuɗaɗe da aka mallaka musu. M. Dauda, hajiyar birni. Asabe, Hajiya mama. M. Gambo. Kuɗaɗene da zasuja jari. Koda Asabe ta nuna hakan bai mataba hajiyar birni masifa ta dinga mata, harda rantsuwar inhar bata yarda Raudha ta auri Ramadhan ba wlhy sai ta tsine mata, kuma sai dai ta ɗau Raudha subar garin dan bazata zauna inuwa guda da mai mata baƙin ciki ba. Kalaman hajiyar birni yay matuƙar tada hankalin Raudha da aka sallamo daga asibiti yau, dan Alhmdllhi ƙafarta tayi sauƙi sosai saboda kula da take samu da ingantattun magunguna gashi bata da ƙan jiki. Bazataso a sanadinta a tsinema mahaifiyartaba. Sannan idan sun bar nan ina zasuje, tunda babu wanda ke garesu sama da su a yanzun. Dan haka tace ita ta amince zata auresa duk da batajin son Ramadhan a ranta ko kaɗan, sai dai a gani guda datai masa har zuwa yanzu tanajin kwarjininsa cike da idanunta, yayinda kalamansa ke zaune daram cikin ranta shiyyasa takejin matuƙar tsoro. Amincewa aurensa na nufin tabbatuwar kalamansa gareta, sai dai kuɗi ya rufe idanun iyayenta sun kasa fahimtar ni'imar da suke ganin suna ciki *_BAƘAR INUWA..._* ce, gara ranar da suke ciki da ita. Zata amince domin gujema hawan tsinuwa akan mahaifiyarta, zata kuma amince dansu samu farin ciki koda ita zata rasa nata farin cikin. Dan duk wanda ya dubeta ya dubi Ramadhan ya tabbatar shi ba tsaran aurenta bane ba, kawai dai kakansa ya kalli abinda tai masane da tunanin zai mata tukuyci da auren alhalin bazai zame mata irin inuwar da shi yake hango mata ta jin daɗi ba.

A lokacin da waccan cakwakiya ke gudana a gidan su Raudha anan fadar shugaban ƙasa shugaban jam'iyya ne ya fitar da sunan ɗan takara a yau a zaman taron da akayi yau ɗin na manyan jam'iyyar. Inda kamar dai yanda aka saba wasu suka nuna jayayya akan Ramadhan ɗin kodan ƙarancin shekarunsa, tare da kawo hujjar bai san siyasa ba, bakuma zai iya ba tunda bama zaman ƙasar yake ba, bai san komai na wahalar talaka ba. Idanu Ramadhan ya rumtse da ƙarfi saboda wani irin sarawa da kansa yake masa a dalilin hayaniyar da ɗakin taron ya kaure da shi. Dama da ƙyar Bappi ya sakashi zuwa wajen taron har sai da ya nuna ɓacin ransa shi da Anne da Pa. Koda ya shigo yaga mutanen dake wajen daga sa'an Pa sai sa'annin Bappi baiji ko ɗar ba, a lokacinne ma yaji kibiyar son yin mulkin ta soki ƙirjinsa. Dan yana ganin yakamata sumafa matasa ace anayi dasu a ƙasar NAYA dan sune ƙasar. A yanzu kuma boren nasu ya sake harzuƙa zuciyarsa dajin eh lallai zai amince ya amshi mulkin ƙasar NAYA inhar ALLAH ya saka hakan a cikin ƙaddarar rayuwarsa. Da ƙyar shugaban jam'iyya ya tsawatar akai shiru, kafin ya yanke hukunci akan gobe za'ai primary election duk da a ransa yasan dolene candidate nasu ya tsallake. Duk sun amince da hakan, daga haka kuma taron ya watse wasu ransu ɓace wasu ransu fal murna, sai dai masu murnar zukatansu sun rabu gida biyu akan dalilin murnar.

Wani meeting ɗin su Alhaji yaro glass suka sake shiga iyakarsu kaɗai akan batun, kafin kuma da yamma shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya su sakeyin wani zaman da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

*_JIHAR DILLO. HUTAWA L.G.A_*

Koya ya shiga matuƙar mamakin yanda M. Dauda ya dawo garin hutawa a jiƙe da kuɗaɗe shi da abokinsa, dan maimakon su rufe sirrinsu sai sukazo sunama jama'a fankama da kuɗi da nuna sumafa sun kai yanzun. bama shi ba abokinsa M. Gambo ma dai ajiƙen ya dawo. Nan take aka fara ƙananun magana da dangantasu da ɓarayi saboda hankalin jama'a ya tashi musamman da suka san dai ba ko sisi su M. Dauda ke magani ba, dan inhar ba sata ba ko wannan kidnapping da akeyi ba babu ta yanda za'ai daga barinsu gari na kwana uku su dawo haka. Aiko nan take manyan anguwa suka haɗa kai suka kai ƙararsu gidan hakimi, hakimi baiyi ƙasa a gwiwa ba ya aika a ka kira masa su M. Dauda daya saka innarsa da iyalansa haɗa ƴan kayansu dan so yake a gobe ya fara gyaran gidansa. A gefe kuma yana tunanin sake sabon aure da lallaso Asabe ta dawo (bayan saki uku ne tsakaninsu🙄). Hakimi da ƴan fadarsa babu kalar binciken su M. Dauda da basuyiba amma sun dage akan sufa basu kuɗin nan akayi. Ganin kamar suna son rainama fada hankaline saboda ambatar sunan manyan mutane da sukayi yasa hakimi saka ƴan sanda suje da su. Haka kuwa akayi, a ranar a police station suka kwana, washe gari hakimi kuma ya kai magana fadar mai-martaba sarkin Dillo. Bako a ɓata lokaciba wajen yayubar su M. Dauda sai cikin birnin Dillo fadar sarki. Nan ɗin ma dai amsar da suka bama hakimi ita suka bama sarki akan inda suka samo kuɗi, sai dai shima bai gamsu ba saboda sunayen da su M. Dauda ɗin suka ambata na manyan mutane. Sai ma hankalinsane daya sake tashi dan gani yake kamar su M. Dauda nason yin amfani da sunan manyan ne dan ɓata musu suna. Baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara neman waɗanda yakeda kusanci da su ciki harda Alhaji Hameed Taura da tarihi ya nuna karatu ya taɓa haɗasu a jami'a. Da ƙyar ya samu damar magana da shi a ranar ta hanyar P.A ɗinsa, bayan sun gaisa cikin mutunta juna matsayinsu na manya da ƴar tsokana ta tsoffin abokai mai-martaba yayma Bappi bayani game da su M. Dauda. Da farko sam Alhaji Hameed Taura bai gane ba saboda baiyi tunanin su M. Dauda sun koma ba, kuma shi har yanzu ma bai basu ko sisi ba su shugaban ƙasa ne sukai musu ƙyauta. Sai da aka haɗashi da M. Dauda, yana ko jin muryarsa ya gane, amma duk da haka sai yasa aka tura masa hotunansu ta email. Yana gani kuwa ya gane, dan haka yayma mai-martaba bayanin da zai iya fahimta. Jin alaƙar dake shirin faruwa tsakanin su dan babu wanda baisan abinda yaso faruwa da Alhaji Hameed ɗin ba ran salla sai shima mai-martaba ya shiga mamaki, harma yake cema Alhaji Hameed anya kuwa baya ganin tun farko dama akwai dalilin daya saka yarinyar masa garkuwa. Alhaji Hameed Harith Taura mutum ne mai sauƙin kai da tsarkake abu koda ace yazo a yanayin daya kamata a zargesa, hakan yasa shekaru aru-aru su Alhaji Yaro glass keta cutarsa yana ƙyautata musu zato dan bai taɓa damuwar zama ya zargesu ba. Cikin nutsuwa ya fahimtar da mai-martaba shi dai zaiyi ne bisa ƙyaƙyƙyawar niyya, kuma baijin yarinyar zata aikata haka dan yarinyace ƙarama kuma nutsatstsiya. Cikin ƙanƙanin lokaci mai-martaba ya yarda dan shima mutum ne mai fahimta, harko yay alƙawarin za'a dama dashi a harkar bikin shine ma uba ga Raudha tunda dai a ƙarƙashin mulkin jiharsa take. Alhaji Hameed yayi matuƙar farin ciki yayi kuma godiya.

Wannan shine ya wanke su M. Dauda wajen hakimi da sarki, sai dai ga jama'ar gari sun ƙara gaba wajen ƙananun magana musamman da akaita dawo da zancen abinda Raudha tayi da kuma dalilin rabuwar Asabe da M. Dauda ɗin da ba'a wani jima ba. Kafin kace kwabo zance yaje bakin ƴan jarida da yanar gizo harya fara yawo...........✍

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull