Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 18

Bakar inuwa book 1 - Chapter 18

Bakar inuwa book 1 Chapter 18: Bakar inuwa book 1 Chapter 18. Suna shiga Aynah na Munirah dake laɓe suka kaima bango duka. Tunda suka kira Gimbiya Su'adah…

4,170 words

Suna shiga Aynah na Munirah dake laɓe suka kaima bango duka. Tunda suka kira Gimbiya Su'adah suka sanar mata ta basu umarnin zuwa su sami likitan su masa maganar komi za'ai kar bakinsa ya faɗi cewar da safe tasha maganin nan. Ya nuna tun jiya ta sha shi da yamma kuma ba yau ne na farko data sha ɗin ba. Shine sukazo fa, suna gab da isa ga doctor Sambo da suke zaman jira tun ɗazun sai kuma ga yayansu da kansa. Hakan ya saka su ɓuya dan kar ya gansu..

“Wane issue kuka samu?”. Ramadhan ya tambaya kansa tsaye dan shi baya son ɓoye-ɓoye ko jan rai a magana”. Cikin in-ina da fargaba Dr Sambo ya fara magana. “Ranka ya daɗe zuwa yanzu dai munyi nasarar ceto rayuwarta, mun kuma tsaida jinin. Sai dai ta zubar da jini sosai a yanzu haka muna ƙoƙarin samun wanda za'a ƙara mata ne. A binciken da mukai kuma mun gano magani ta sha wanda ya wuce ƙa'ida ma shine ya kawo tsinkewar jinin kamar haka. Badan anyi azamar kawota ba ma zata iya rasa ranta saboda maganine mai ƙarfi kuma abinda aka sha dominsa ma babu shi...” “Maganin miye?”. “M...maganin abortion ne?”. “Abortion?”. Ya maimaita maganar ta sigar tambaya. “Yes sir, sai dai kuma ma babu cikin, bincike ma ya tabbatar mana mahaifanta bai taɓa ɗaukar ciki ba sam. Hasalima a cikin yanayin perio....” “Ya isa haka..” Ramadhan ya faɗa cikin ɓacin ran bayyanar kishinsa ƙuru-ƙuru daya kasa ɓoyuwa. Da ƙyar ya danne takaicin taɓa masa mata da sukai da sanin sirrin da basu dace da sani ba daga gareta ya fara magana mai kama da gargaɗi. “Wannan maganar ta tsaya iya ni da kai. A wajen kowa yazam cikinne ya zube da gaske. Kar a ƙarama matata jinin kowa a ɗiba nawa. Da ga nan zuwa gobe ina son sanin sunan ƙwayar data sha.” “Okay ranka ya daɗe insha ALLAH. Sai dai da zai yuwu zanso ganin abinda taci na ƙarshe dan kamar daga nan matsalar take”. Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi kamar mai nazari, sai kuma ya kauda idonsa yana miƙewa, “Muje ka ɗiba jinin, sauran aikin kayi magana da Chief security na gidan”. “Okay sir ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ya kareka a duk motsinka da rayuwar iyalinka baki ɗaya”. A saman laɓɓa ya amsa yana ficewa daga office ɗin.

Ba ƙaramin tashin hankali zuciyar Ramadhan ta shiga ba lokacin da yaga Raudha. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zube ta sake haske mai ban tsoro alamar dai da gaske babu jinin a jikinta. Cikin cije lip dinsa da masifar ƙarfi ya kai hannu saman kanta ya shafa gashinta lokacin da yake kaiwa zaune a kujerar da Dr Sambo ya ajiye masa. Sai kuma ya sinkuyi kanta ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbata. ALLAH sarki Raudha, inama ace idonta biyu taga wannan al'amari. Na tabbata jininta zai iya daskarewa ma baki ɗaya. Kamar yanda ya hana a saka mata jinin kowa nasa aka saka mata, dan kuwa dagewa yay sai da aka ɗiba leda biyun da suke buƙata ɗin. Sai bayan an saka mata ne su Anne suka samu damar shigowa suka dubata, zuwa lokacin har Ramadhan ya koma cikin gidan dan shima yana ɗan buƙatar kwanciya ya huta. Ya bama Chief security damar binciko duk abinda suka tattauna da Dr Sambo. Dan haka babu ɓata lokaci Chief security ya fara aikinsa akan sauran abincin breakfast da Raudha ta ci. Ba'a samu wani tangarɗa ba wajen gano Raudha tasha maganin zubda ciki ne ta hanyar ruwan shayi da yay saura a flask ɗin. Wanda a zahiri Raudha ta shanye sa tas, sai dai lokacin da Ramadhan ke sanarma Chief security aikin da zaiyine zancen ya shiga kunnen Lubnah. A firgice taje ta matsa ruwan zafi da ga dispencer ta jefa sabuwar ƙwayar magani a ciki jikinta na rawa. Batafi mintuna biyar ba kuma Chief security ya iso falon dan ALLAH yasa ma ba'a kai ga kwashe kwanikan ba saboda halin da Raudha ta shiga ya ruɗa kowa. Kuku bai farga da abinda ke faruwa ba sai da Chief security yasa aka kira masa shi. Gaba ɗaya ya rikice ya ruɗe, dan zuwa yanzu labari ya fara karaɗe gidanne first lady ɓarin ciki tayi, ana kuma zargin an saka mata wani abune ta ci a abinci.

Su kansu su Anne a rikice suke da jin wannan al'amari musamman ma aunty Hannah da tasan suna da alaƙa da kuku. hasalima yaronsu ne su yakema aiki a gidan. A gefe kuma ta shiga mamaki da ruɗanin mizaisa kuku ya zubdama Raudha ciki? Saboda koba komai suma suna buƙatar cikin matsayinsu na jinin Raudha mafi kusanci.

(To koma dai miye, wannan wata sabuwar cakwakiyace kuma🤥🚶🏻 Aunty hannaty).

★★★

Ramadhan bai sake cewa komai ba akan batun duk da yaji cewar Raudha tasha ƙwayar ne da ruwan shayi. Hakan na nufin kuku's ne da aika-aikar, a yanzu haka kuma shugaban kuku'e ɗin dake da alhakin kula da abincinsu yana hanun securitys na gidan. Bayan sallar isha'i su Anne suka wuce gida har aunty Hannah. Sai dai zuwa lokacin Ramadhan yasa an dawo da Raudha cikin gidan tana ma ɗakinta. Alhakin dubata ya koma wuyan Dr Hauwa'u a yanzun gaba ɗaya, sannan Mama Ladi aka bari a ɗakin zata cigaba da kula da ita. Ramadhan ya nunama Dr Hauwa'u yana son kowa ya cigaba da ɗaukar hakan har su Anne cewar cikinne da Raudha kuma ya zube. Batasan dalilinsa ba, amma kuma ta karɓa alfarmarsa dan ta fahimci akwai ƙulli a cikin al'amarin mai girma. Badan ma ALLAH ya taƙaita ba komai zai iya faruwa da mahaifar Raudha ɗin, a yanzu hakama basu da tabbacin komai zai iya zama normal.

★★

Washe gari da safe ya tashi babu wani damuwar jinin da aka ɗiba masa. Dan har massallaci ya fita sallar asuba. Bayan dawowarsa massallaci ya jima zaune cikin sofa yana ƙullawa da kwancewa akan al'amarin. Wajen shidda aka kawo masa tataccen haɗin shayin lemon tsami da wasu ganyayyaki na shayi da yake sha a duk safiya dan shi ba ruwansa da wani coffee. Har kukun dake kula da shayin nasa ta kammala ta fita bai motsa ba. Baima amsa ko gaisuwarta ba. Hakama bayan fitarta bai sha shayin ba dan tunaninsa ma baya tare da duniyar mutane. Bazai so ya zama silar hana wani cin abinci ba, amma dolene ya ɗauka wani mataki game da wasu ma'aikatan gidan musamman kuku's dake da alhakin basu abu suci. A hankali ya furzar da iskar daya tara a ƙirji yana miƙewa batare da yabi takan shayin ba. Ba tsoron an zuba masa wani abu yake ba, kawai dai yau bama shi da ra'ayin shan komai ne kawai. Wanka yayo yay shirin office, tamkar kullum yau ma yayi ƙyau matuƙa yana ta baza ƙamshin turarurrukansa da suka amsa sunansu turare. Koda ya fito ɗakin Raudha ya nufa, kowa bai samu ba a ɗakin ba sai dai an gyara shi yanata ƙamshi. Raudha kwance a gado cikin bargo babu alamar ta farka. Tsaye yay akanta ya tsurama cute face nata ido, ta sake haske sosai, ta kuma rame. A hankali yakai zaune bakin gadon tare riƙo hanunta dake saman cikinta ya riƙe cikin nasa. Kasa jure abinda ya ratsa sa yayi, sai kawai ya rumtse hanun da ƙyau a cikin nashi har sai da taɗan motsa. Tabbas ya yarda ita ɗin ƙyaƙyƙyawa ce, sai dai a ganinsa tayi yarinta da yawa. A zuciya yake wannan tunanin, a zahiri kam ido kawai ya tsura mata. Yanada meeting da shuwagabanin tsaro baki ɗaya, dole ta sashi miƙewa yana ƙoƙarin zare hannunsa a cikin nata sai dai ta riƙe nasa ita kuma. Tsamm ya tsaya yana kallon hanun nata yanda ta matse yatsun nasa biyu tamkar tana ido biyu. A bazata murmushi ya suɓuce masa, sai dai komai baice ba ya zare yatsun nasa yana ɗon furzar da huci.

★ Koda ya fita kafin yaje office ma wajen meeting ɗin ya fara zarcewa, dan ya makara, kuma zama ne mai matuƙar muhimmanci. Harkar tsaro da lafiya da ilimi sune sahun farko da yake burin fara shimfiɗawa al'ummarsa kafin komai. Dan haka yasa aka shirya masa zama da shuwagabanin jami'an tsaro ta kowanne ɓangare, dana lafiya takowane nangare, dana ilimi takowane ɓangare. Zai fara zama da jami'an tsaron ne kafin sauran suma. Meeting ɗin ya jasu lokaci saboda muhimmancin sa. Dan a ƙalla sun sami good 3hours. Koda ya shiga office bai iya taɓuka wasu abun arziƙi ba. Yadai gana da vice president Alhaji Yaro glass akan wasu muhimman batutuwa. Sanda suka kammala lokacin salla yayi. bayan dawowarsa massallaci ya gana da COS daga nan ya tafi hutun awanni biyu. Maimakon zaman hutun sai yay zaman yin waya da Bappi.

Ƙarfe biyar na yamma ya shigo gidan yau. Sai da ya fara zuwa ɗakinsa yay wanka ya kimtsa cikin ƙananun kaya sannan ya fito domin duba jikinta. Bai samu kowa a ɗakinba yanzu ma. Motsin ruwa da yaji ya tabbatar masa tana toilet, agogon dake a tsintacciyar hanunsa ya kalla tare da ɗan bin ɗakin da kallo. Saukar idanunsa akan hoton dake saman bed side drawer ɗinta ya sashi takawa a hankali garesa hannayensa duka cikin aljihun wandon jeans ɗin sa, hoton ya tsurama ido duk da bawani fitaccen hoto bane, hasalima ya ɗau shekaru, dan mace ce da mijinta sai yara huɗu, ɗaya jaririya a hanun mijin, sai ƴar shekara 7 da kamanin Raudha ke tare da ita tabbacin dai itace ɗin. Sai biyu da bazasu wune shakara tara ba da alama twins ne. Kiran da akaima wayarsa ne ya katse sa da ga kallon hoton, ya zarota a aljihu yana mai janye idanunsa a hoton gaba ɗaya. A kuma dai-dai lokacin Raudha ta fito da alamun wanka tayi. A hankali take takowa cikin ɗakin dan da farko bata lura da shi ba. Sai dai kuma yanda ƙamshinsa ya cika ɗakin ya sata tsarguwa harta kasa ƙarema ɗakin kallo. Sallamar da yay lokacin da yake kai wayar a kunnensa ya sata tsayawa cak daga takowar da take, gaba ɗaya jitai ta daburce, gashi ta riga da tazo kusan tsakkiyar ɗakin tasan dai ya riga ya gama ganinta kuma. Kallonsa ta ɗan sata kaɗan, ya ɗan zuba mata idanu tamkar mai shirin gano wanda ya aikata mata abun a jikinta. Da sauri ta maida idanun nata ƙasa. Shima ya janye nasa yana cigaba da sauraren masifar da gimbiya Su'adah ke masa ta cikin wayar, shi gaba ɗaya ma ya rasa dalilin faɗan nata shiyyasa saurarenta kawai yake batare daya fahimceta ba har tayi ta gama ta katse kiran bayan ta bashi umarnin ganinsa. Kansa ya ɗan girgiza kawai yana sauke numfashi, a zuciyarsa mamakin daru irin na mahaifiyarsa yake. A zahiri kam idonsa ya maida ga Raudha datai tsaye tamkar an dasata “Ƙaraso mana”. Ya faɗa a hankali tamkar baya so. Duk da bathrobe ce a jikinta gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta. Amma saita daure ta ƙarasa bakin gadon dan jiri take gani ma. Tana gab da isa jirin ya kwashe tai tamkar zata faɗi ALLAH ya taƙaita sai jinta tai jikin mutum............✍

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* ..........Ba sai an mata wani explanation ba tasan shine. Dan mayataccen ƙamshinsa tuni ya ƙara ƙarfi a ƙofofin hancinta. Kasa buɗe ido tayi ta kallesa dan kunya, ga shi bata da ƙarfin da zata ƙwace jikinta a nasa. “Kina ganin jiri ne?”. Ya faɗa a hankali yana tallafo fuskarta cikin tafin hanunsa. Bata yarda ta buɗe idanunta ba, sai ta jinjina masa kanta, zuciyarta babu abinda take sai luguden daka kamar zata fito waje, ga tsigar jikinta sai yamutsawa take. Dan wannan shine karo na farko da ya taɓa mata irin wannan riƙon a cikin jikinsa sosai kamar haka. Shi kansa danne yanayin kawai yake a zuciyarsa, yay ƙoƙarin kaita zaune a bakin gadon.... Dai-dai lokacin Mama Ladi da batai zaton samunsa a ɗakin ba ta turo ƙofar da sallama ta shigo saboda tasan Raudha ɗin ma ta barta ne tana wanka batai tsammanin ta fito ba. Shigowar tata baisa ya janye jikinsa da ga na Raudha ba, sai ma itace data ɗan dabirce har ta samu ƙarfin yin mutsu-mutsu amma sai ya shareta. A ɗan rikice Mama Ladi ta juya zata koma ya dakatar da ita “A gafarce ni ranka ya daɗe wlhy bansan kana ciki ba”. “Is ok”. Ya faɗa tamkar baya so yana matsar da jikin nasa daga na Raudha ya zaunar da ita da ƙyau ya miƙe akan ƙafafunsa, nuni yayma Mama ladi data ajiye kayan hanun nata. Cikin girmamawa ta ƙaraso ta ɗora tray ɗin saman table da alama abinci ta haɗoma mata. “Babu dai wata matsala zuwa yanzu ko?”. “Eh ranka ya daɗe Alhmdllhi. Likitama da tazo ɗazun tace komai ya dai-daita sai dai a cigaba da kula da maganinta, ta kuma dinga cin abinci sosai dan ƙarfin jikinta ya dawo”. Baice komai ba sai kallon Raudha da yayi. Sosai ta rame, ƴar ƙibar da tayi duk ta zube. Idanun ya janye yana ɗan furzar da iska. Sai kuma yace, “ALLAH ya ƙara lafiya”. Mama Ladi ta amsa da “Amin”. Raudha ma data kai kwance saboda rashin ƙarfin jiki ta amsa a laɓɓanta. Bai sake cewa komai ba ya fita a ɗakin ya barsu, dan Taura house yake son zuwa amma a ɓadda kama zai fita gidan. Ɗakinsa ya koma ya ɗaura jacket saman kayansa da p-cap ya fita, odilan ɗinsa dake jiransa dan dashi kaɗai zasuyi fitar yay saurin risinawa yana masa barka da fitowa. Kansa kawai ya jinjina masa. “Saifu muje lokaci yaja”. “Okay sir, odilan Saifudden ya faɗa da sauri yana buɗe masa back sit.

*_★★TAURA HOUSE★★_*

Gaba ɗaya ranta a ɓace yake tun jiya a gidan, tsabar bala'in dake cin ranta ko barcin kirki batayi ba da daddare. Yinin yau kuwa babu wanda zai ce yama ganta a gidan har ƴaƴanta, sai Adda Asmah data shigo da yamma ta ƙara fanfata matuƙa saboda cikin nan na Raudha ya matuƙar tsaya musu arai duk sun san ya zube kamar yanda sukaji bakin su Lubnah da Anne. Ɗazun da rana Hajiya Shuwa da Hajiya Mufida sunje har government house sun duba Raudha. Koda Anne taga babu gimbiya Su'adah batace komai ba, saboda ɗaukar hakan matsayin kawaici ga abokan zaman nata. Knocking ƙofar bedroom ɗin nata ya katse mata wayar da takeyi da Fulani. “Ammy zan kiraki inaga gashi nan ma yazo mara mutuncin”. Daga haka ta yanke kiran da miƙewa ta buɗe ƙofar dan a kulle take kasancewar bata buƙatar kowa ya shigo mata. Barin wajen tai, Ramadhan da yaga tsantsar ɓacin rai a yanayin nata ya ɗan furzar da iskar bakinsa yana ambaton sunan ALLAH a zuciyarsa. Ko ɓangaren su Anne bai shigaba ya wuto nan. Koda ya kai zaune yana gaisheta bata amsa masa ba, sai kawai ya saki ɗan murmushi da zame p-cap ɗinsa ya ajiye shima yay shiru. Tsahon mintuna uku ɗakin ya ɗauka shiru, sake ɓaci ranta yayi fiye da wanda take ciki. A zafafe ta watsa masa harara tana magana a kausashe, “Yanzu ai ka fara ganin abinda muketa nuna maka akan wannan shegen auren, matarka tayi yanda take so na zubar da ciki saboda ta fito a gidan marasa tarbiyya. Tunda ta nuna bata shirya haihuwa ba kasani ni bazan amince ba. Dan haka dole ne ka ƙara aure nan da wata ɗaya, kuma Aina'u zaka aura.....” “Maah!. Aina'u?”. “Eh ita, idan kuma ban isa ba kamar yanda ubanka da kakaninka suka isa har suka aura maka zaɓinsu ka amsa ba tare da bijirewa ba sai naji.” Iska ya furzar da ƙarfi yana ɗan rumtse ido da buɗewa lokaci guda. “Maah Please calm down. Kibar zancen wata Aina'u a beg. S.......” “Anƙi a bari ɗin, kai yanzu Ramadhan dan baka da mutunci har kana da bakin faɗamin nabar zancen ɗiyar ƴar uwata akanka? Aka saka kama auri karuwa....” (Ya ALLAH) ya faɗa a zuciyarsa yana rumtse ido da murza goshi. Cikin zafin rai gimbiya Su'adah ta cigaba da sauke masa takaicin Raudha da shi kanshi da dama take ƙullace da shi tun lokacin first night da suke tunanin ya faru tun a waccan ranar. “Ita ga ƴar iska mara mutunci, tasan bata shirya haihuwa ba miyasa ta yarda da kai dan ubanta, nama godema ALLAH data zubar ɗin kuma mahaifar tata bazata sake ɗaukar wani cikin ba. Bani da rabon haɗa zuri'a da jinin karuwai!!”. Sosai ransa a dagule yake. Amma ya daure dan mahaifiya ta wuce wasa. Babu abinda yake sai haɗiyar zuciya. Babbar matsalarsa auren Aina'u da ta ambata, koma mizai faru sai dai ya faru babu auren Aina'u a cikin tsarinsa. Yariyar daya gani da idanunsa a cikin tsakkiyar club a America ana lesbians da ita, ƴan iska na ihu suna ɗauka a waya (Wa'iyazubillah). Ta rufe fuska da mask, shiyyasa tai tunanin babu mai ganeta, sai dai tayi rashin sa'a shi ya ganetan da idonsa. Dan ya tabbatar mata ya ganeta ɗin kuma ya cire mata mask ɗin. A wannan rana baiyi barci ba dan tashin hankali, dan koba komai itaɗin jininsa ce. Da uwarta da tashi fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sannan mahaifinta shima ɗan masarautar su Maah ɗinne ɗan uwa na jini matsayin Uncle yake garesa. Amma itace yanzu Mahaifiyarsa ke tabbatar masa zai aura. Ji kawai yake ana ambaton Raudha da ɗiyar marasa tarbiyya amma shi har yanzu bai tabbatar ba tunda bai taɓa ganinta tana aikata wani fasiƙanci ba. Itako Aina'u da idonsa ya ganta ba labari ba....... “Tunda ga ƴar iska ina magana kamin shiru ko!!”. Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin dawo masa da hankalinsa gareta. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zamansa. Cikin tausasa harshe yace, “Maah Please relax. Ki bari ki huce sai muyi magana daga baya. Indai dan haihuwa ne insha ALLAH jikoki har sai kin rasa yanda zakiyi da su a gidan nan.....” “ALLAH ya tsareni samuwarsu da ga wannan jinin karuwan da talauci. Dan haka karka sake min irin wannan maganar zan ɓata maka rai”. “Ok. ok!. shike nan kiyi haƙuri Please”. Tsaki taja tana ɗauke kanta gefe. Kaje dare yayi, amma ka tabbatar ka samu kakaninka da mahaifinka da maganar Aina'u dan wlhy babu fashi saika aureta, sai dai in mutuwa kayi ko ita ta mutu”. (Oh oh, shikam yau ya zaiyi da tsohuwar nan) ya faɗa a ransa yana dafe kai.

*_GOVERNMENT HOUSE_*

Tunda ya shigo ya zube a falon upstairs ɗin ransa duk a jagule. Kansa harya fara ciwo tsabar rasa ina zai kama. Magana da yake ji ƙasa-ƙasa kamar ana raɗa ya sashi sake nutsuwa da hasashen ta ina ne. Fahimtar da ga inda sautin ke tashi ya sakashi miƙewa. Kansa tsaye ya tunkari wajen, amma tsabar shagala da Aina'u tai a wayar da take yasa sam bataji motsinsa ba balle ƙamshin turaren sa. “Amma naji daɗi Ummi da kika sake tunzurata, duk da dai wlhy a tsorace nake. Har zuciya ina son Yaya Ramadhan, amma nasan akwai matsalar da tai mana katangar danne zumuɗina. Gani nake kamar tursasawarku ma bazatasa ya amince ya aurenin ba......” Shiru tai alamar an katseta daga can. Sai kuma ta sauke numfashi. “Wlhy zan jure Ummi, nidai yanzu burina ya amince ɗin, indai na zama matar tasa komai mai sauƙi ne. Sannan ƴar iskarnan nasan da wahala ta sake ɗaukar ciki kamar yanda doctor ya sanar mana. Kinga sanadin barinta gidan yazo kenan ƴar karuwai”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi sai kuma ta dumtse bakinta tana ɗan waige irin kar ajitan nan. Hakan yasa Ramadhan sauri ɓoyewa dan karta gansan. Janye hanunta tai a baki tana cigaba da faɗin. “Nifa harma mamakin yanda akai cikin nake Ummi, wlhy kinga wancan zaman har muka bar gidan nan bamu taɓa ganin ta shiga ɗakinsa ba ko shi ya shiga nata. Hakama yanzu banda randa muka gane tana da ciki datai pretending ya ɗakkota daga falonsa bamu taɓa ganinsu tare ba. Ni anyama cikin nan bada shi tazo ba....” Shiru ta karayi na saurare. Sai kuma tace, “Wlhy Ummi komai zai iya faruwa. Ke dai ki cigaba da fanfa Maah dan ALLAH ayi-ayi nima na shigo wannan daular ta mulki a dama dani. Hhh Ummi nice nafi dacewa da first lady ba wannan ƙwailar yarinyar da ko ƙirar mata bata da shi ba”. “Ok Ummi kije wajen Abban karya jimu kin sansa. Da safe ma karasa”.

Da kallo ya bita daga inda take tsaye harta shige lungun corridor ɗin bedrooms ɗin Raudha. Babu abinda ke masa turereniya a rai sai zantukanta da ya fahimci alaƙarsu da birkicewar mahaifiyarsu a yau. Wato Addah Asmah na tunzura Maah akan matarsa dan ya auri ƴarta. Wani murmushi ya suɓuce masa a bazata ya kai hannu ya shafo ƙeyarsa. Maimakon ɗakinsa da ya kamata ya nufa sai ya wuce na Raudha kamar yanda zuciyarsa ke tunzurashi. Kansa tsaye ya murɗa ƙofar ya shigo. Mama Ladi da ke lallaɓa Raudha ta sha ko farfesu ne da shayi tai saurin kallon ƙofar tana amsa sallamar da yay a hankali. Tunkan ya karaso ta risina tana gaisheshi. Amsawa yay idonsa akan Raudha data dafe kanta saboda ɗan nauyin da yay mata. “Wani abu ya sake faruwa ne?”. “A'a ranka ya daɗe babu abinda ya faru, bayan fitarka ne ta sake komawa barci sai yanzu ta tashi. To tace tanajin yunwa ne an kawo abincin kuma tace ta ƙoshi. Shine nake lallashinta taci kodan ta samu ƙarfin jikinta kamar yanda likitar tace”. Komai baice ba, sai alama da yayma mama ladin akan taje abinta. Cikin girmamawa ta risina da faɗin, “A fito lafiya ranka ya daɗe”. Kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa. Yana tsaye hannayensa duka a aljihu har Mama Ladi ta fice ta rufo ƙofar. Raudha da har yanzu hanunta ke dafe da kanta cikin rashin ƙarfin jiki tace, “Ina yini”?. Karon farko taji ya amsa mata gaisuwarta da “Lafiya, yaya jikin naki?”. “Alhmdllhi naji sauƙi”. Nanma baice komai ba ya taka zuwa bakin gadon ya kai zaune kusa da ita gab. Hanunta data tallafe kanta da shi ya janye da faɗin, “Oya ci abinci”. Batare data yarda ta kallesa ba ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “ALLAH na ƙoshi”. “Ashe zan miki ɗura kenan ok! Bana son gardama maza ɗauka”. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan yayi kicin-kicin da fuska babu alamar wasa tattare da shi. Badan yana mata daɗi ba ko ɗanɗano ta fara tsakurar abincin, yayinda shi kuma ya ciro wayarsa a aljihu ya fara dannawa. Da wannan ƴar damar ta ɗanci tea ɗin ma kaɗan. “ALLAH na ƙoshi”. Ta faɗa a marairaice dan yaji tausayinta. Wayar ya ajiye tare da ɗagowa yana kallonta. Yanda ya ɗan tsura mata ido kamar mai nazari ya sata fara wasa da zoben hanunta...... “Yanzu mike miki ciwo?”. Kanta ta girgiza masa. “Ba ko'ina, sai dai ɗan jiri shima ba wani mai tsawwalawa bane”. “Kina sakaci da abinci ne shiyyasa shima bai tafi ba. Idan ALLAH ya kaimu gobe inada tafiya zuwa UK, zan samu kamar 4 to 5days kafin na dawo. So bayan na dawo inada sharuɗɗa na canja tsarin zaman gidan nan”. Wani irin ƙuuuu cikinta ya bayar amma batace komai ba. Shima bai damu da cewar tata ba ya cigaba da maganarsa a kausashe babu alamar wasa. “Dole ne ki koma tsayawa a kan masu girkin nan inhar zasu mana abincin da zamu ci ni da k. Zaki koma kwana ɗakina dan Maah tana buƙatar jikoki saboda tana tunanin ta rasa wani ne a yanzun......” Cak numfashin Raudha ya tsaya a aiki, cikin rashin fahimtar zancen nasa dan ƙwalwarta ma jitai ta toshe baki ɗaya ta ɗago tana kallonsa. Shima kallon nata yake cikin sarƙe idanun nata a nashi. A hankali ya kai fuskarsa gab da tata ya hure idanun nata. Saurin rumtsesu tai da ƙoƙarin jan jikinta baya amma sai ya ɗaura hanunsa a fuskar gadon kanta ya sauka akai. Jikinta ya sake matsowa a nata shima idanunsa na ƙara ƙanƙancewa. Cikin wani sautin murya da shi kansa baisan ta suɓuto da ga ƙirjinsa zuwa harshe ba yace, “Idan kaka taso ganin jikokinta laifi ne?”. Ruɗanin da Raudha ta shiga ne ya sata fara girgiza kai jikinta na tsuma. Ya kashe mata ido ɗaya da janye fuskarsa a tata ya maida saitin kunenta “To ki shirya bata madadin babyn da take tsamanin ta rasa a jiya”. Ya ƙare maganar da ɗan sumbatar gefen kuncinta ya miƙewa lokaci guda da ɗaga mata yatsunsa biyu “Good-night”. Fitsari ne kawai ya ragema Raudha ta saki dan al'ajabinsa, amma hatta da kayan cikinta sai turereniyar dunƙulewa suke waje guda. da ƙyar ta iya sake numfashin data riƙe a ƙirji lokacin daya maida ƙofar ya rufe alamar ya fita. Gaba ɗaya kalamansa sai suka saka hajijiyarta sake dawowa sabuwa dan jinin daya batan ma ƙasa ya dinga zirarewa ta cikin jijiyoyi yabi numfashi ya fice fit. Hannu takai taɗan mari fuskarta dan gani take kamar a mafarki take dai, sai dai jin tabbacin a zahiri ne komai ya faru ba mafarki ba ya sata faɗin, “Inaga bashi bane aljani ne”.

(🤣🤣saifa aljanin kam).

★★★★★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull