Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 24

Bakar inuwa book 1 - Chapter 24

Bakar inuwa book 1 Chapter 24: Bakar inuwa book 1 Chapter 24. Fuska ta yamutse alamar ƙyankyami. Ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyarnanfa ƴar…

4,491 words

Fuska ta yamutse alamar ƙyankyami. Ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyarnanfa ƴar wulaƙancice wani lokacin. Wai ƙyanƙyaminama kikeji? Koda yake hakafa kikaimin kwanaki ina mura. Har shaƙa miki murar nai amma kikaƙi ɗauka saboda ɗan banzan ƙarfin jininki”.

Yanzu kam kasa daurewa tai ta sanya dariya. “Kai Ya Ramadhan ko tausayi babu?”.

“K nifa kibar wani cemin Yaya niba Yayanki bane bamsan kalar dangi. Nasan dai akwai abota tsakaninmu sai kumaaaaa......”

Ya ɗanja ƙarshe yana kashe mata ido batare daya ƙarasa ba. Ba shiri ta miƙe zaram amma yay saurin riƙeta ya maida. “Ustaza bansan fassara irin taku ta Ustazai fa. Kijira na karasa mana kafin ki kaini inda banje ba”.

Dole ta dawo ta zauna kamar ta ɓuya a kujerar dan kunya. Ya dungure mata kai yana kai nama bakinsa da taɓe baki. “Gulmammiyar yarinya nafasan kema kin kamu. A yanzu nan duniya bayan Mommy da Abba babu wanda kike so Kamar Ramadhan...”

“Ni yaushe nace!”.

Ta faɗa cikin suɓutar baki tana taɓe fuska.

“Yo sai kin faɗa? Yanda kika kadandaneni ram ɗazu ke daɗi mijima ai ya isa shaida.”

“Innalillahi....”

Ta faɗa kamar zata fasa kuka dan kunya. Dariya ke cinsa yanda tai wuri-wuri da idanu na kunya. Ya danne da ƙyar. “Oh kice baki son nawa mana kiga in gobe banje an ɗauramin aure da ƴammata uku ba galla-galla”.

Ji Raudha tai kamar ya kwaɗa mata guduma a tsakkiyar zuciya. A take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Tai ƙasa da kai zuciyarta na mata zafi da kalamansa.....

Wani daɗi ya baibaye Ramadhan kamar ya tashi ta taka rawa. Cikin shafa sumar dake zagaye da kumatunsa yace, “Oh su Ustazah ba kunya anga sumulmulin yaro ɗan jikan Anne an maƙale. Irin wannan kishi haka Ƙawata? To indai baki so nayo kishiyoyi yau kam dole naje farautar triple koda yake kefa huɗu ma naji kina faɗa saboda tsabar haɗama keda ma ko ɗan kiss ɗin nan na zamani sau ɗaya aka taɓa mik.......”

Ai bata bari ya ƙarasa ba ta daka tsalle ta guntse masa baki da hannayenta. Wayyo dariya kamar ta kashe Ramadhan. Yasan ya riga ya gama da ƴar darunsa yau. Sai dai wani farin ciki ke dawainiya da shi ganin kishinsa ƙuru-ƙuru tattare da ita. Koba komai yaji daɗi bashi kaɗai ke wahalar banzaba akanta ashe. Jikinsa ya jawota ya rungume. Cikin raɗa yace, “Na nayi shiru tashi kici abinci”.

“Kaci kayanka, ko kaje kuci da ƴammatan naka”.

“Wayyo Ramadhana anyi kasuwa. Uhm-uhm fa Bestie ALLAH karki tsaya kallon ruwa ƙwaɗo ya miki ƙafa. BABU SO MIYA KAWO KISHI?”.

Turesa ta shigayi da faɗin, “Wama zaice yana sonka ɗin. Abotarma an fasa”.

Nanma dariya kawai yakeyi yana sake riƙota dan ya fahimci so take tai amfani da damar ta tsere. Ya jima da gane tanada wayo duk da ƙarancin shekarunta. Matseta yay da ƙyau duk yanda taso ya hanata damar dole ta nutsu saboda abinda ya raɗa mata a kunne kamar ta nutse. tanaji tana gani ya tilasta mata cin nama da kunun wanda yay mata matuƙar daɗi. Dama da ƴar sauran yunwarta ta rana. Bayan sun kammala ta tattara kwanika zata fita da su ya hanata. Acewarsa ta tayashi salla ya bata labarin faransa tunda ita bata tambaya ba. Ganin ya zama serious doleta haƙura. Sai dai ta masa complain na rashin hijjab yace abu mai sauƙi yana da shi ai....

Raudha dai dauriya kawai take amma tabbas a tsorace take. Bayan sun idar da salla ya dafa kanta yay addu'a kamar yanda musulinci ya tanada ya kuma dace ace tun randa aka kawota gidan hakan ta faru. sai dai lokacin gogan nata na bisa gajimaren hayaƙi hakan bata faru ba. Sosai Raudha tai mamakin yanda taji yana kwararo addu'oi. Sam batai zaton yanada ilimin addini kamar haka ba. Sai taji ya sake birgeta zuciyarta ta ƙara nauyi game da shi.

Bayan sun idar ma ta buƙaci son zillewa ta gudu ya sake hanata. Ƙarshe ma kayan barci da batasan daga ina ya samosu ba ya bata wai ta saka. A matuƙar kunyace ta dubesa cikin marairaicewa amma ya nuna mata babu wani ɗaga ƙafa yau anan zata kwana. Shi ya gaji da raba musu makwanci da takeyi. Daga karshe ya haɗata da kunyar data sakata bin umarninsa dole.

“Ustazah a haka za'a samo ƴan huɗun kina gabas ina yamma. Gara dai kiba marasa ɗa kunya ki haifama Maah jikan da taketa fatan gani. Gashi ma kin ƙudiri surprising ɗinta har ƴan huɗu kika shirya.”

“Kai Ya Ramadhan magana wai bata wucewa a gunka”.

“Oh ikon ALLAH na kulafa kin fara bin hanyar rainani yarinyarnan. Ni miye nawa tunda faɗa kikai naji. Ai har Anne zanma albishir gobe”.

“Na shiga tara dan ALLAH ka taimakeni”.

“Hhhh taimako ɗayane zaki samu sai kin saka kayan nan”.

Wannan kandagarki nasa ya sata shiga toilet ta canja. Sai dai ta jima tana duban kanta a mirror ɗin toilet ɗin ta kasa fitowa. Sai kallon kanta take cike da kunya da ganin ƙyawun da tayi kamar ba itaba. Sai dai gaskiya bazata iya fita da rigarba gabans....

Maƙalewa tunaninta yay jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Tai mugun diriricewa ta ruɗe. Tama rasa mizata jawo ta rufama jikinta. Ramadhan da kamar suman wucin gadi ya riska a bakin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa ya ƙaraso gareta. Sai dai a zahiri yanda yake a nutse bazaka taɓa fahimtar halin da yake a ciki ba. A bayanta ya tsaya idanunsa kafe akanta ta cikin mirror da suke fuskanta, sai dai ita ta duƙar da kai ta kuma kuɗindine jikinta da towel ɗin data sami nasarar jawowa.

Ta bayan nata ya zuro hannayensa duka biyu ya zare towel ɗin data rumtse a cikinsu. A wani irin tashin hankali taja numfashi a fisge da rumtse idanunta da ƙarfi tana ayyanawa a ranta. “Shike nan tawa ta ƙare ni Aminatu”.

Lallausan murmushi ya saki yana yaye towel ɗin a hankali saboda furicin zuci datai ya fito fili. idunsa kuma a kan cute face nata da hawaye ke silalowa a hankali. Tabbas matarsa ƙyaƙyƙyawa ce, mai kuma ƙyawun surar jiki abin buƙatar kowane irin namiji mai lafiya. Ya ja nannauyar ajiyar zuciya da kamo kafaɗunta duka ya juyo da ita tana fuskantarsa. Rawa jikinta ya farayi dan ƙafafunta bazasu iya riƙe nauyin gangar jikintaba a yau.

Tausayinta ya sake kamashi, sai kawai ya rungumota cikin jikinsa dan shi kansa ji yake jini na haura masa har saman ƙwaƙwalwar kansa. A tare suka saki kakkaurar ajiyar zuciya, sai kawai ya ɗauketa cak suka fice.

Cikin gadonsa da kullum Raudha ke ƙwaɗayin ganin an saki runmfar net dake jikinta ya nufa da ita. A hankali ya fara kai ƙafarsa ɗaya ya dire gwiwar sa akan lallausan gadon yana rankwafawa ya direta a gadon itama. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da rauni yace, “To sakeni”.

Sam bazata iyaba. Dan hanun nata ma rawa yakeyi, ta ƙara ƙanƙame wuyan nasa da hannayenta data tallafo ƙeyarsa hawaye na rige-rige sakkowa.

“Ameenatu”.

Ya kira sunanta da murya mai tsananin tsada da tsantsane.

“Uhhmyim!".

Ta faɗa a shaƙe.

“Kiyi haƙuri na tashi zan canja kaya ne”.

Da sauri ta girgiza masa kai idanunta rumtse. “Ya Ramadhan tsoro nakeji”.

Murmushi ya saki mai sanyi, a hankali ya kai bakinsa kan laɓɓanta da goshinta ya sumbata. Cikin sake raunana harshensa yace, “Nima tsoron nakeji shiyyasa na gayyatoki ki tayani kwana kar ojuju ya kamani”.

Yanda yake mata magana a kunne ya sata sake ƙanƙamesa. Ganinfa ba sakinshi zatai ba sai ya kawai ya kwanto jikinta gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa.

“Mummy zan mutu”. Ta faɗa da ƙyar jin nauyinsa na fitar hankali. Murmushi kawai yayi ya ɗagata, baice komaiba ya fito a cikin gadon. Ita kuma ta samu damar nannaɗe kanta a bargon zuciyarta na gudu kamar zata faso ƙirjinta ta fito kawai kowa ya huta. Harya koma toilet ya kammala kimtso kansa bata buɗe kanta ba. A haka ya kashe fitilar ɗakin yabar lamps kawai ya shiga net ɗin shima. Bargon data ƙudundune a ciki ya ɗaga shima ya shige..

Murmushi yayi jin yanda ta ƙanƙame waje guda lokacin daya kwanto jikinta. A hankali ya kai lips nashi ya sumbaceta ta gefen kunne, ta ƙara curewa waje guda jikinta na rawa. “Haba Ustazah, tsoro fa na ragwayen mata ne, ko kina so masu zuwa Bingon suzo kuma babu cikin ƴan huɗun uhhm?”.

Kasa cewa komai tai, sai hawayen tsoro dake mata gudu, babu abinda ke cin ran Ramadhan sai dariya. Musamman daya shafa fuskarta yaji hawaye.

“Oh ni Ramadhana, ni kuma haka ALLAH yay dani auren raguwa. Yo raguwa mana, tunkan ace kule ke kin tafi cas...”

Tsabar yanda zuciyarta taje maƙura kuka ta fashe masa da shi mai ƙarfi. Ya danne dariyarsa da ƙyar tare da mirginota ta juyo suna fuskantar juna. Sai kawai ya rungumeta yana shafa kanta murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Sai da ya tabbatar ta nutsu ya dai-daita fuskarsu waje guda, cikin ɗan hasken dake a ɗakin yake kallonta, itako idonta a rumtse gam.

“Kodai mu haƙura da farautar ƴan huɗun kawai Ustazah?”.

Da sauri ta ɗaga mata kanta.

Ya saki murmushi mai faɗi da ɗora goshinsa kan nata ya riƙo hanunta cikin nashi. “Tom naji, amma idan an haƙura minene tukuycina ni?”.

“Wlhy zan maka nama da yawa da safe”.

Raudha ta faɗa da sauri cikin rawar murya. Mi Ramadhan zai inba dariya ba. Wato yarinyar nan ta maidashi mayen nama. A fili kuwa sai ya cewa yay “Okay ALLAH ya kaimu Ƙawata ta amana”.

Daga haka ɗakin yay shiru, jin kamar ya fara barci Raudha hankalinta ya fara kwanciya, itama sai ta lumshe na idanun. Idanu ya buɗe a hankali yana kallonta da murmushi. “Yaro yarone”. Ya faɗa a hankali da jan bargo ya lulluɓesu baki ɗaya.

Can cikin barci ta tsinkayi abinda yafi ƙarfin saninta, sai dai mai girma shugaban kasa da shirinsa yake, dan cikin ƙanƙanin lokaci yay mata dabaibayin daya sakata shagala da miƙa wuya, sai da labari yay nisa ta raina kanta.......

*_Bily kama bakinki iya nan🤐🚶🏻_*

★Kallo guda zakai mata kasan taci uban kuka harta godema ALLAH. Duk da kasancewarta ba fara tas ba yanayin saida ya nuna a fuskarta. Gaba ɗaya ta jangwabe kamar ba Ustazah Raudha ta hutawa ɗiyar baba Dauda da Asabe ba. Lallai ba ƙarya daren jiya anci ƙaniyar sabada. Dan kuwa dai mai girma shugaban ƙasar Naya Ramadhan B Hameed Taura bai nuna yasan wata Raudha ƴar 18years ba balle ya bita a sannu. Babu da kalar yaren da bata roƙesa ba amma ya toshe jinsa da ganinsa ya nuna mata baya fahimtar kowanne yare saina cikar burinsa. Cizo da yakushi kuwa ya samu rabonsa gwargwadon iko har ba'a cewa komai. A ƴan gidansu babu wanda bata lissafo yazo ya taimaketa ba har maƙwafta da su Anne sun sha kira........✍

_Mace ƴar gatan ALLAH. mace ƴar gatan duniya. Mace sarauniya. Mace farin cikin duniya. Mace duniyar duniya. Mata ina miƙo gaisuwar ban girma amma banda ballagazaye wanda suka gama rabarwa a waje🙄🙄🚶🏻😏_

End of book Leave a comment

Post

Comments No Comments posted yet

Contact Us Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation Home About FAQ's Legal Privacy Policy Terms of Service Social Facebook Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io *_Typing📲_*

*_Episode 49 & 50_*

..........Da asuba daya tadata suyi salla kuka ta dinga masa sosai. Duk sai tausayinta ya lulluɓesa. Shi kansa yasan ya tsaurara mata da yawa, dan dukan fushinsa na shekarun nan babu ƙwange sai da ya sauke shi tsaf. Bata wani yarda ya taimaka mataba tace zata iya. Koda ya haɗa mata ruwa sai ya fita a toilet ɗin ya barta. Zafin ruwan ya sata harar ƙofar tana ƙunkuni ta surkeshi ya koma salaf. A haka ta gyara jikinta ta fito tana faman sinne kai. Ga dariya ga tausayi duk suna cin Ramadhan lokaci ɗaya. Amma sai ya gimtse dan karya sake tunzurata. Da ƙyar ta yarda suka sake komawa barci bayan ta idar da sallar. Acewarsa su ɗan ƙara rage barcin idonsu dan anguwa zasuje. Taura house yake son suje hutun nan na kwanaki biyar da akai, amma bai sanar mata ba. Dan kuwa bazai yarda amarcin nan ya wucesa bai ɗana gadonsa na Taura house ba.

(Mutumin nan ko😂😜)

★Tun a daren jiya dama ya sanarma ƙanensa yau zasu wuce Taura house hutu gaba ɗayansu. Dan haka da safe ya turama Bilkisu text ta haɗama Raudha abinda duk tasan zatai amfani da shi su wuce su sai zuwa anjima zasu zo. Murmushi kawai Bilyn tayi. Sai dai kafin su fita tai ƙoƙarin haɗa breakfast ta ajiye musu. Mama Ladi kuwa ta zauna gadin abincin nan dan kuwa Anne ta kirata tun sanda suka gane Raudha ce ta aika musu takarda akan saka poison a ac ta ce mata ta dinga saka ido akan kowa na gidan kar'a cutar mata da su Raudha. Duk da tasan bata isa hana zartar da ƙaddarar UBANGIJI akansu ba.

Yanzu kam Raudha ce ta fara farkawa. Ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi matuƙa. Akan fuskar gogan nata ta saukesu. Idanunsa a lumshe, ƙyaƙyƙyawar fuskarsa tayi wani fayau. Duk da haushinsa na murzar da yay mata jiya babu tausayi da takeji haka ta shagala a kallonsa. Itama kanta tasan shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne, ga yanayin jin daɗin rayuwa daya tashi a ciki, bai san wahalar komai ba sai ta karatu. Ahankali takai yatsanta saman girarsa data daɗe tana kwaɗayin taɓa tsagar wajen da zuciyarta ke bata wanzami yay masa. Sai dai me, koda ta shafa wajen sai taji santsi irin na tabon ciwo. Mamaki ya kamata, a zuciyarta tace, (Ashe ba tsaga masa akeba tabon ciwo ne) a fili kam mamaki ƙarara ya bayyana gareta da sake girmama sunan UBANGIJI, dan babu mai kallon wajen yace ciwone. Sosai tsagar ta fita da tsari kamar yimasa akai akan sani. A hankali ta sauke numfashi da maida gashin girar data yamutsa masa ta maidashi ya kwanta. Tana ƙoƙarin sake janyewa taji an riƙe hanun. Babu shiri tai saurin rumtse ido tana fisgewa amma yaƙi saki. Nasa lumsassun idanun dake cike da barci ya buɗe a hankali a kanta. Sai kuma ya sumbaci hanun nata daya riƙi ya turashi ƙasan kuncinsa yay filo da shi. Ɗayan hanunsa kuma ya ɗaura a jikinta saitin ƙugunta. “Good morning sweetheart”. Wani bala'in kunyane da yafi na ɗazun da asuba ya lulluɓeta. Tai ƙoƙarin kauda kanta yay azamar tallafosa da hanunsa dake a ƙugunta ya hanata hakan. Cikin ɗan marairaicewa yace, “Ki amsa min mana Baby luv”. Da ƙyar ta iya buɗe baki tace, “Ina kwana”. Ahankali ya shafo kanta tun daga sumar gaban goshin har zuwa ƙeya yana ɗan murmushi. “Ya jikin ki? Duk da nima dai ya kamata a tambayeni nawa kodan yaƙushi da cizon dana sha”. Ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Tai ƙoƙarin jan hanunta da yay filo da shi amma ta kasa. “Kibar wani gulma Ustazah, nasan kina son mijinki kar kiyi sake wata ta ƙwace miki ni”. Kanta tai ƙoƙarin sinnewa a jikinsa. Yay murmushi yana riƙeta ya hana hakan. “Gara na faɗa miki gaskiya matsayina na abokinki babban amininki. Bazan so a miki kishiyaba kina ƙawata ta hanun damar, dan sai na fiki kishi kilama kullum dani zaki dinga cin dabe da ita a gidan ga muna lakaɗa mata duka ko ya kikace?”. Duk yanda taso riƙe dariyarta ta kasa. Ta saki murmushi tana turesa. “Kai Ya Ramadhan....” “K nifa bana wani kalar dangi ƙannena sun isheni, inama laifi da muke abota niba yayanki bane”. “Toni ai bazan iya faɗar sunanka ba”. Tai maganar tana sake son cusa kanta a ƙirjinsa. Haɓarta ya riƙo ya ɗago fuskar tata da sumbatar laɓɓanta. Cikin sake ƙanƙan da murya yace, “To basai ki canjamin da wani ba. Amma sam bana son Yayan nan kamar wani zamanin iyaye da kakanni, bayan kuma jiya na gama turmusheki a gadon na....” Dariya ta ɗan ƙyalƙyale da shi tana kaimasa ƙaramin duka a ƙirji. Shima sai ya rungumeta yana murmushi. Zuciyarsa fes da farin ciki.

Duk yanda taso zamewa kar suyi wanka tare bai bata damarba. Amma kuma taƙi sakin jiki haka ya gama nashi ya barota a bayin. Sanda ta fito yana zaune yana waya. Dan haka tai wuff ta fice a ɗakin bayan ta saka hijjab. Ciwo take ɗanji kaɗan-kaɗan a ƙasanta amma ta daure ta shirya cikin wani material da yay mata ƙyau sosai da fiddo kalar fatarta. Tayi fayau da ita daka ganta kaga amarya, sai dai fuskar babu walwala sosai ga idonta duk wanda ya kalleta yasan taci kuka. Yunwa takeji amma batajin son cin abinci kuma. Bakinma ɗaci takeji yana mata kamar mai malaria. Tana fesa turare ya shigo, sanye yake cikin shadda ash color datai bala'in masa ƙyau. Sai maiƙo take da ɗaukar iadanun mai kallo. Ya murza hula baƙa data fiddo ainahin hasken fatarsa da ƙyallin angwanci. Duk da waya ya shigo yanayi hakan bai hana Raudha shiga jin kunya ba, ya ƙaraso inda take yana riƙe kwalban turaren da kunya tasata cigaba da fesa ƙasa-ƙasa dan karya tada mata asthma. Ajiyewa yay saman mirror ɗin ya riƙe hanunsa cikin nata idanunsa a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yakeji kamar ya haɗiyeta. Ga ɗaurin datai ya sake fiddo ƙyanta kamar dai ya haɗiyetan ya huta kawai. Ita dai kanta a ƙasa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na _Dolce & gabbana_ daya gauraya da _burberry brit_. shiko yanata wayarsa da murza yatsun hanunta. Tsawon lokaci harta fara gundura da tsaiwar kafin yay sallama da wanda yake maganar wanda ta fahimci kamar akan harkar kasuwanci ne. Saman mirror ya ɗaura wayar da kamo fuskarta cikin tafukan hanunsa ya sumbaci goshinta, sai kuma ya sakko a hankali ya sumbaci lips ɗinta dake ƙallin lips gloss. Shima ya duƙo kaɗan yana nuna mata nasa kumatunsa da goshi. “Kai Ya Ramad......” Sai kuma ta kasa karasawa saboda ɗallin daya bama bakinta. “Dole na fara hukunta wannan bakin idan yaya ɗin nan bai fita a cikinsa ba”. Hannu tasa ta rufe laɓɓanta da zafi ya maimaye idonta na cika da ƙwalla. Hannunta ya kamo ya zuba mata link ɗinsa da agogonsa _hublot_ dayay mata ƙyau sosai kalar ash. Batai musu ba, dan koba komai tasan aiki garesa lada ne. Links ɗin ta fara saka masa sannan agogon. “Thanks bestie”. Ya faɗa a hankali idonsa a kanta. Sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen mirror ɗin. “Ƙarasa mu wuce so nake na more gida sosai lokaci nata tafiya”. Duk da batasan ina zasu ba cike take da ɗokin tafiyar. Ta ɗauka hijjab da zai shiga da kayanta ta saka tare da haɗa abinda zata iya buƙata a karamar handbag. Tana duba takalmi a akwatin lefenta ya sake shigowa. Bai yi magana ba yabi duk kayan wutar ɗakin ya kashe komai. Dai-dai tana gamawa yake faɗin, “Ko breakfast bazamu tsaya yiba mayi acan kawai”. Kanta ta jinjina masa, sai dai har yanzu taƙi yarda su haɗa ido. A hankali ya matsa gefenta yay musu hoto bayan ya faɗi abinda ya sakata ɗagowa ta kallesa a ɗan tsorace. Sai hoton ya bada wani style mai ƙayatarwa kamar anyisane da shiri.

Bayan sun sallami su Mama Ladi suka fito compound inda jerarrun motocin da zasu fitan suke. Yau ce karo na farko da zasu fita tare da shi a bayyane. Sai gaisuwa ake miƙa musu cike da ɗunbin girmamawa wadda har Raudha takejin babu daɗi akanta. Dan kuwa da yawansu sun haifeta da girmarta. A motar da tafi kowace mota ƙyau da ɗaukar idanu ga tutocin ƙasar naya a jikinta suka shiga. Kafin wanda zasu musu rakkiya Taura house ciki harda cos da wasu ministers uku suma suka shiga. Ba wani tafiya mai tazara bace ba, amma ta fahimci an bama fitar muhimmanci matuƙar dan har a redion motar da driver ya kunna saiga sanarwar yau shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura zaije hutun ƙarshen shekara gidansu a karo na farko tun bayan hawansa mulki na watanni kenan. Anan aka saka zantukan mutane daban-daban daketa masa addu'a shi da iyalinsa akan yasha hutu lafiya cikin farin ciki. Sosai ya ƙara samun nutsuwa a ransa dan kuwa zuwa yanzun ayyukan daban-daban da suka faro na talakawa sun kankama matuƙa. Abinda zai matuƙar birgeka duk wani mai kwangilar gwamnati sunansa da aikin da zaiyi a bayyane yake ga al'umma. Hakan yasa yake ƙara samun addu'a ga talakawa dan kuwa babu wani ƙunshe-ƙunshe balle a cucesu a ƙiyi musu aiki kuma su rasa daga ina matsalar take. Kai hatta kuɗin da aka bama masu kwangilan da wanda sukebin bashi sai sun kammala a cika musu duk an sanar da duniya babu wani rifa-rufa. Hakan da yay ya matuƙar taimakawa da saka tsoro a zukatan masu kwangilar dan sun san kam inma basuyiba sune a ruwa tsundum. Gashi har adadin watanni ko shekarun da aikin zai ɗauka kowa ya sani a bayyane. Bashi kaɗaiba hatta da gwamnoni da ƴan majilusu, ciyamomi, kansiloli duk aikin da zakai ma ƴan yankinka a jihohin nan 41 dolene ka sanar da komai talakawa su sani.

Tarba ce ta musamman tawagar shugaban ƙasa ta samu a Taura house, dan kuwa wannan shine karo na farko da yazo gidansu a bayyane kuma da shirin kwanaki. Sosai bakin Anne da su Yafendo ke a buɗe, ganinsa ya musu wahala yanda suke buƙata tunda ya hau mulkin nan. Raudha dai gaba ɗaya a takure take. Jitake kamar kowa zai iya gabe abinda ya faru a tsakaninsu jiya. Ga anne da su Yafendo sai nan-nan suke da ita kowa na saka mata albarka. Bayan gaishe-gaishe da addu'oi Ramadhan da su Bappi suka fita salla dan tawagar datai masa rakkiya sun koma. Sai dai Taura house tako ina zagaye yake da securitys kai gaba dayama anguwar. Dole ne ka shaida shugaban ƙasa na nan koda matakan tsaron dake kewayen anguwar baki ɗaya, kai kace ko ƙuda bazasu bari ya gitta ba. Da ƙyar Raudha ta iya tsarki da ruwan sanyi tsabar zogin da wajen ke mata zuwa yanzun. Har jin kanta take kamar wadda zazzaɓi zai saukarmawa. Anne na lure da yanayin nata sai dai batace komai ba dan zuciyarta bai kai ga zargin abinda ke faruwa da Raudha ɗin ba kai tsaye. Gashi tunda suka shigo dama yanayin idanunta na wadda taci kuka ya tsayama Anne a rai. A ɗakin Anne sukai salla duk da kuwa an gyara sashen Ramadhan ɗin tsaf domin su. Bayan idar da salla gaba ɗaya gidan ƴaƴa da iyaye aka haɗu domin yin lunch a katafaren falon Bappi. Abincine mai rai da lafiya da gamsarwa a wajen iri-iri. Anyi hakanne kawai domin walimar zuwan Ramadhan ɗin da Raudha. Sai yanzu Raudha taga gimbiya Su'adah da sauran matan gidan, dan kuwa bata shiga gaishesu ba Anne tace sai zuwa yamma sun huta. Sai dai shi Ramadhan ya shiga ya gaida Gimbiya Su'adah ɗin kawai ganin bata a masu fitowa tarbarsa. Kasancewar salla zai fita yasa bayan gaisuwa babu wani abu daya shiga tsakaninsu ya fito suka fice massallaci. Har ƙasa Raudha takai tana gaishe da iyayen. Kowa ya amsa mata cike da kulawa banda gimbiya Su'adah da ko kallon inda take bataiba. Ƙasan ranta wani takaicine da baƙin ciki da kishin yanda Raudha ta kara murjewa komai na halittar jikinta ya ƙara girma sai kace ƴar 25years. Ga tsadadden material ɗin dake jikinta wanda ta tabbatar za'a iya sayen abincin watanni na gidansu Raudhan da kuɗinsa. Ita saima taga kamar yarinyar tana wani jin kanta. Oho Raudha batasan tanai ba. Ita abinda ya dametama ya isheta. Komai yinsa take cike da dauriya. Abincinma tana matuƙar bukatarsa amma ta kasa ci saboda bakinta babu daɗi. Sai juya spoon take a ciki tana ɓata fuska. Ramadhan na lure da ita. Kuma hankalinsa na kanta. Burinsa su haɗa ido amma taƙi kallon ko inda yake. yana zaune ne tsakkiyar Bappi da Pa. Sai Anne a gefensu da Yafendo da Inna. Ita kuma tana kusa da Bilkisu da Zainab ne. Su Lubnah sai faman jan tsaki suke ƙasa-ƙasa suma kamar su halaka Raudha sukeji musamman ganin suturar data sanya kosu da suka tashi gidan kuɗin basu saka ba. Tsadajjen agogon hanunta da zabba da bangles kawai duniyane. Balle ita kanta data kara wani kyau na musamman da su sam basa lura da shi sai yau duk da kuwa suna tare da ita. Da gangan Ramadhan yay kamar ya sarƙe yaja gyaran muryar data saka kowa maida hankalinsa a kansa ana rige-rigen jera masa sannu. Bappi dake shafa masa baya kamar wani ƙaramin yaro ya kai masa kofin ruwa bakinsa yana masa sannu. Kaɗan yasha yana jinjina musu kai da satar kallon Ustazahr tasa. Sai dai bata yarda ta kallesa ba tun bayan ɗagowar datai kamar yanda kowa ya ɗago lokacin daya sarƙe. Ita sanun tatama a kan laɓɓa tai masa ta tsuke bakinta. Ganin dai ba samun yanda yakeso zaiyi ba sai ya haƙura. Takaici ya cika Aynah da duk hankalinta ke akansu. Hakama Muneera da idonsu akan yayan nasu da abinda yake yawan kallo. Jin hawaye na neman zuboma Aina'u itace ta fara mikewa wai ta ƙoahi. Babu wanda yace mata komai, hakan sai ya ƙara baƙanta ranta. Dan a ganin bai kamata aƙi bata kulawaba kodan mata ta biyu da take shirin shigowa ga ɗansu kuma ɗan uwanta. Raudha da dama ba abincin take ci na kirki ba itace ta ukun tashi a wajen. Ramadhan ya ɗan bi yanda take tafiya da kallo. Hannu ya kai ya dafe goshinsa a zuciyarsa yana ayyana (Yarinyar nan zata tonamin asiri fa). Bayan sun kammala kowa ya tashi a wajen yaso janta sashensa dan ya fahimci mugunta taima kanta bata shiga ruwan zafin daya haɗa mataba da asuba, bayajin kuma da safe ta sake kula da kanta. Takaicin kansa yaji dabai tsaya akanta ya taimaka mataba duk boranta. Sai dai duk yanda yaso ya keɓe da ita ɗin hakan bata yuwuba dan su Basma na zagaye da ita a falon Anne suna hirar school duk da ba wani saka musu baki take sosai ba. Sai dai ganin Inna da Yafendo da Anne na wajen ya sashi haƙura ya shige shi acewarsa zai ɗan huta...........✍

_Ayi haƙuri da jina shiru, banda lafiya ne_.

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull