Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 26

Bakar inuwa book 1 - Chapter 26

Bakar inuwa book 1 Chapter 26: Bakar inuwa book 1 Chapter 26. *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke…

4,500 words

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa??🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*_Episode 53_*

..........*_JIHAR ƊILLO (HUTAWA)_*

A Hutawa kam kowa yaga M. Ɗan-azumi yanzu sai yay matuƙar mamaki. Dan kamar yanda ya ƙudiri ƙara sabon aure ya auro dalleliyar budurwa sabuwa dal a kwali. Kai daka ganta kasan ƴan kuɗin ta biyo. Baƙaramin tashin hankali Larai ta shiga ba, dan saika ɗauka ma wani sabon haukane ya hau kanta. Data nema birkice masa sai ya aikata gida taje ta huta. Roƙo iya roƙo ita da danginta amma ya birkice musu ƙememe dama fitinarta ta isheshi, ga baƙin cikin rabasa da masoyiyarsa Asabe da har yanzu ko ɗigon sonta baibar zuciyarsa ba. Ganin haka Baba Nafi ta ƙara kama kanta da mutuncinta a gidan, dan tun dawowar Inna da ƙaninsa da matarsa dama gidan ya sake zama sai a hankali. Gadai jin daɗi yanzu a cikinsa amma kowa zaman haƙuri yake da ɗan uwansa saboda fitinar sirikarsu dabance a rayuwa, shi kuma M. Dauda na biye mata dan duk haukarsa yana ƙaunar Innarsa. Tun auren Raudha alaƙar zuminci mai ƙarfi ke tsakaninsa da hakimi, hakama jama'ar gari sosai suke respecting nashi kowa burinsa ya zama abokin mu'amularsa (kaiko sirikin shugaban ƙasa fa ba wasa ba😝). Da wannan damar M. Dauda kan samu na hura hanci sai ya zaɓi wanda yaso ayi zumincin, shi da M. Gambo ne dai ana nan tif da taya, sai dai baisan M. Gambo nata masa zagon ƙasan ƙoƙarin kiran Asabe a wayaba kullum, wani lokacin harda mata ɗan text na soyayya dan ƴar sakandire ɗin nan dai shi da M. Dauda sunyita. Ita Asabe har zuwa yanzu batasan wanene ba. Dan tun tana sharesa da masa masifa idan ya kirata harta ɗan fara kulashi. Hakimi daya fahimci rawar kan M. Dauda bata risinaba saima giyar kuɗi dake neman ɗorasa a wani layin bayan wanda yake kai yasa shi ƙara jansa a jiki yana masa nasiha, ya kuma bashi sarautar data tilastashi kullum zuwa gidan Hakimi ayi fadanci dashi. Koda yake mugun ɗagawa da faɗi yake da sarautar, inma ka kira sunansa baka haɗa da sauratarba to kuwa kaji barbaɗin jaraba daga sama har ƙar zai zugeka yana hura hanci da kiran shi ya wuce raini ai. Surikin shugaban mai ƙasar yake baki ɗaya, Baba sama baba ƙasa yake kiransa kuma saiya risina yake gaisheshi koda a wayane balle wani ƙaton ƙawai da talauci yayma katutu. (😂🤣ALLAH ya bar mana Man Dauda). Ya sayi ƴar kwariɓar motarsa ana yanga da ita kwana biyu ta birkice, cike da masifa ya maidawa bakaniken daya saida masa yace wlhy koya dire masa kuɗinsa kokuma yasa azo daga Bingo a cukuykuyesa yasan dai uban matar shugaban ƙasa yake. Da farko makanike ya ɗau abin wasa, dan mahaukacima suka maida M. Dauda shi da yaransa. Saiko gashi ko mintuna ashirin baiyi da barin wajenba motar ƴan sanda har uku sunzo sun yayesu gaba ɗaya har yaran nashi. Dan kuwa M. Dauda yana zuwa police station d.p.o da ayanzu ya gama haddacesa shi da yaransa koda ɗunbin alkairin da suka samu a ranar auren ƴarsa da shugaban ƙasa sukai masa tarbar mutunci. Harda matsar kwallan munahinci wajen faɗa musu abinda akai masa a gareji. Rai ɓace d.p.o ya bama yaransa umarnin zuwa a kwasosu yana bama M. Dauda haƙuri. “Baba ai kun wuce ko kallon banza yanzu a ƙasarnan, kunefa iyayen masu ƙasar. Gamu nan tunda ɗanku ya hau mulki albashinmu ma ninkashi akai tsabar adalci na wannan shugaba. Ai mu babu abinda muke sai fatan alkairi a garesa, mun kuma tabbatar lallai matasa masu jini a farce ƙasar NAYA ke buƙata irinsa.. ALLAH ya ƙara masa zaman lafiya da matarsa nan da watanni asake zuwa taron suna NAYA muci musha muyi warkan. Dan muna alfahari first lady tamuce wlhy”. Daɗi kamar zai kar m. Dauda, ya dinga washe haƙwara yana sake baje babbar rigarsa dan ɗinkunan alfarma da Alhaji Hameed Taura yay masa na biki har kala goma sune suka zama na faɗi yanzu a gari. Lokacin da aka shigo dasu Gali a ɗage M. Dauda yake kallonsu da watsa hannaye gaba. “A rufeminsu har sai na manta da wanzuwarsu sannan a tunamin”. Cikin roƙo da magiya kanikawan nan ke roƙon Alhaji Dauda (dan tunifa dama gargaɗi yake abar kiransa M. Dauda😂😜). Amma ko kallonsu baiyiba. Cikin takun ƙasaita ya buga babbar rigarsa aka fice dan d.p.o ya bada motarsa a maidashi gida.

Kwanakin kanikawan nan huɗu a ofishin ƴan sanda sannan ya bari aka sakesu da sharaɗin maido masa kuɗaɗensa nanda sati guda. Hakan kuwa akai sai gasu da kuɗaɗensa cif sun kawo, ya dinga antaya musu harara yana sake baje riga da hura hanci. Bayan ya koma gida ne ya nema kuɗin ya rasa da kwana biyu shine ya yanke jiki ya faɗi har saida aka kaisa asibiti. Wannan ne dalilin zuwa su Fatisa dubashi har suka sanarma Raudha, to ayanzu haka dai ya haɗa duk yaran gidan nasa da matan ya tabbatar musu idan kuɗinsa basu dawoba nera dubu ɗari bakwai wlhy suma cell zaisa a zubasu har sai sun magantu.

(🤣😂To bara muga ta inda kuɗin Alhaji Malam Dauda surikin shugaban ƙasar NAYA zasu fito).

*_BINGO CITY (TAURA HOUSE_*

Barci sukasha sosai kamar yanda Ramadhan yaso. Ga Anne daga falo na musu gadi dan koda su Basma suka taho wai anan zasuyi breakfast korasu tai duk da tasan da wahala hayaniyarsu takai ga sashen Ramadhan ɗin. Dama tunda ya shiga ya gaisheta bayan sallar asuba yace kar ai musu breakfast da wuri. Dan haka ba'a ɗora ɗinba kuwa sai kusan sha ɗaya na safe. Zuwa sha biyu an kammala komai an kawo falon part ɗinsa an shirya bayan an gyarashi yanata ƙamshi duk da bawani datti yayi ba. A yanzu ɗinma kusan tare suka farka sai dai motsintane ya tadashi. Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan. Cikin yanayin kasalar barci ya mika hannu ga side drawer ya ɗakko agogonsa yaɗan kalla time cikin lumshe idanu da buɗewa. Har sha biyu ta gota. Agogon ya ajiye da kai lips nashi a goshin Raudha da taƙi buɗe ido ya sumbata. Kafin ya saketa ya sauka baki ɗaya batare da yayi magana ba. Bata iya motsawaba sai da taji ya rufo toilet ɗin. Ta miƙe da ƙyar itama dan barcine da bata sabayi ba ace tun sallar asuba har kusan 1. Gadon ta shiga gyarawa a ɗan gurguje, ta maida net ɗin yanda ta gansa, sosai yake birgeta dan ya sake kawata gadon da ɗakinma baki ɗaya. Har falo ta fito neman kayan shara, cikin sa'a ta samu a cikin kitchen bayan ta karema falon da kitchen ɗin kallo. komai akwai na buƙatar ɗiya mace har tana mamakin sai kace mai mata. Shara ta gama tana tsaka da mopping ya fito. Bata yarda ta kallesa ba, sai shine dake binta da kallo ya nufi mirror yana faɗin, “Waya saki wannan aikin?”. Amsa ta bashi batare data yarda ta kalla inda yakenba dai. “Ba kowa”. Komai bai sake cewaba harta kammala ta fita da kayan, taɗan jima kafin ta dawo da fatan ALLAH yasa ya saka kaya. Sai dai addu'ar tata bataci ba dan har lokacin ɗaure yake da towel tsaye a gaban Wadrobe da alama kaya yake nema. Kaita kauda cikin sauri ta faɗa toilet. Baki yaɗan taɓe dan duk yana kallonta ta gefen ido. Ta jima bata fitoba, har sai da ta leƙo taga baya ɗakin. Da sauri-saurin tai shirinta cikin atanfa datai mata ƙyau matuƙa, ga ɗinkin ya fidda jikinta tsaf kamar ka saceta ka gudu. Ɗauri tai mai sauƙi amma ya mata ƙyar ta saka ƴan kunne kawai harda yafa mayafi sannan ta fito da nufin zuwa gaida mutanen gidan duk da kunya da nauyin ƙin zuwa akan lokaci na cinta. A tunaninta Ramadhan ma nacan, sai dai tana fitowa falo taci karo da gogan nata zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon labarai a television da alama sallar azhar yaje yayo kawai ya dawo. Tsamm tayi a ƙofar ɗaki kamar bazata karaso ba. Sai kuma cikin dauriya ta cigaba da takowa har inda yake. Kanta a ƙasa tana wasa da zobon hanunta tace, “Ya Ramadhan zanje naje na gaida su Anne”. Maimakon ya amsa mata duk da idonsa ba'a kanta yakeba sai taji ya riƙota ya zaunar saman cinyarsa. Mutsu-mutsu zata fara ya dakatar da ita ta hanyar yaye veil ɗinta gaba ɗaya. “Banda ƙauyanci miye na zuwa gaban miji da veil?”. Duk da maganar ta bata haushi sai ta dake. A sanyaye tace, “Wajensu Anne fa zanje”. Wasa yake da jelan kitsonta idonsa a tv, “Sunce sun yafe yau ko ƙofar corridor ɗin can bazakije ba nayi gaisuwan da taki ai tun ɗazun”. “Kai Ya Ramadhan wlhy bai kamataba ace banje na gaishesu ba. Gashi dama lokaci ya gama shigewa ai da kunya”. Maimakon amsa mata maganar ko barinta tafiya sai ya ɗagata daga jikinsa shima ya tashi, dining ya nufa da ita dan shi ta yunwar cikinsa ma yakeyi. Dolo ta haɗiye komai dan yaci serious kamar bashi ba. Tsorone yaɗan fara kamata na gudun karfa mutumin nan ya juya mata baya bayan ya rabata da mutuncinta. Dan taga tun jiya ya koma sha mata ƙamshi irin yanda yakeyi mata a baya. Da wannan tunanin tai saving nashi komai, zata zuba nata ya hanata yay mata nuni data zauna kawai. Dole tabi umarninsa zuciyarta fal tsoron abinda ba haka bane. Shi Ramadhan yana ɗan ɗaurewa ne kawai dan gujema abinda zuciyarsa ke kwaɗaita masa game da ita. Dan tausayinta yakeji matuka. Amnah mai shekaru da suke gab da nashi duk da tanada lalura bata iya jure ɗaukarsa akoda yaushe balle ita. Dan sauda dama idan yaje gareta sai tayi kuka balle Raudha da yakema kallon jaririya. Shi kansa yasan yayi juriyaa shekarun da babu Amnah, amma ya tabbatar ɓacin rai da tashin hankaline suka girmama juriyar tasa, yanzu ko daya ɗan ɗana bayajin zai ɗaga ƙafa duk da ƙoƙarin hakan da yakeyi. Tare sukaci abincin Raudha nata sinne-sinne. Shi dai bai kulataba. Daga ƙarshema ya amshe cokalin ya koma bata da kansa. Ina ƙasa ta shige amma babu damar gardama dan ya haɗe girar sama data ƙasa........✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*_Episode 54_*

..........Koda suka kammala falon suka sake dawowa, ya kuma ɗaure fuska yanda bazata roƙesa fitar ba. Dole ta kama kanta dan kuwa koda ya zaunar da itama karshen 3seater sai ya kwanta shi ya ɗaura kansa a cinyarta. Ya kuma kamo hannayenta duk biyu ya ɗora a sumarsa sannan ya canja musu tasha. Raudha babu bakin magana, tun tana cuna baki gaba har laushin sumar da takema kallon zatai ƙarfi saboda yanayinta na irin tamu ada ya fisgeta ta tura yatsunta a ciki a hankanli. Lumshe idanu Ramadhan yayi da sauke numfashi a hankali dan hakan abune da yake matuƙar so a rayuwarsa shima. A hankali ta cigaba da wasa da yataunta cikin sumar cike da shauƙi harta shagala ta manta dawa take tare. Haka ta cigaba da wasa da sumar kansa cikin shagala tana kallon film, yayinda shi nashi idon ke'a lumshe ya lula duniyar tunani.

★Kowa bai damu da rashin ganinsu a gidan ba har yamma, sai gimbiya Su'adah ce data cika tai fam da takaici, dan har Muneera ta aiko tai mata cid ɗinsu ta koma ta sanar mata ai duk yau ma bata tunanin Raudha taga rana. Gara Ramadhan kan fita yayo salla. Dama kuma shi yaje ya gaisheta da safe ma.. Har lunch ta shirya masa da kanta da maganin da Adda Asmah ta kawo waina fidda son Raudha a ransane ya tsaneta. Har sai ya mata korar kare a government house. Sai dai abinda bata sani ba na tsananin jan ra'ayinsa da mallakar zuciyarsane akan Ayna'u, malamin daya bata ya tabbatar mata Ramadhan yaci maganin nan sai ya manta har gimbiya Su'adah ɗin ma da kaf Taura family ya koma ƙarƙashin ikon ƴarta Ayna'u, hatta da mulkin ƙasar NAYA Aynah ce zata koma mai tsarawa da zartar da yanda za'ayi. Sai dai kuma Ramadhan ya kwafsa mata baije sashen da rana ba. Washe garima babu wanda ya gansu, sai randa suka cika kwana uku yaje sashen nata shi da Raudha da rana. Hakan baisa ta gaza tanadin na dare ba a cikin gasashshiyar kazar da taji kayan haɗi na ban mamaki aka aika masa har sashen Anne da kunun madara da yasha zuma a ciki a wannan rana. Ita kanta Raudha basu ƙyaleta ba. A baki Bilkisu sukaji abinda tafi so, amma kasancewar guri ya ƙure aka haɗa mata zoɓo mai sauƙi aka barbaɗe da magani sanin Ramadhan baya shan zoɓo shi kuma. Tunda Lubnah ta nufi sashen Anne da abinci sai kuma zuciyar gimbiya Su'adah ta shiga ƙunci, rasa mike mata daɗi tayi tanata faman kaikawo a bedroom ɗinta. Gaba ɗaya zuciyarta na nuna mata ƙiyayya da abinda ta aikata akan ɗan data haifa saboda tsanar matarsa. Sai dai kiyayyar da takeji akan Raudha nata ƙoƙarin danne gaskiyar dake son bayyana kanta ga kuskuren da idonta ya rufe ta kasa fahimta...

Sam Anne bata kawo komai a ranta ba ta haɗa kayan wajen gimbiya Su'adah a cikin dinner ɗin su Ramadhan. Taya ma zatai tunanin za'ai amfani da uwa wajen cutar da ɗanta? Ita bama ta taɓa kawoma ranta wani cikin surukan nata na bin malamai koda akan Pa ba. Tama shedesu akan hakan ɗari bisa ɗari dan bata taɓa ganiba gaskiya. Ita kuma mutumce da bata yanke hukunci akan abinda bata ganiba sam. Raudha yarinyace mai tsarta, haka kawai taji gabanta na faɗuwa lokacin da sukai zaman cin abincin. ALLAH ta shiga ambato a zuciyarta, yayinda Ramadhan gashin kaza ya ruɗesa ya ɗan ɗiba da cokali mai yatsu ya kai bakinsa yana ambaton “uhhm”. Kallonsa tai kawai batare data iya cewa komai ba. Sai da zai kai lauma ta biyu ne ALLAH ya bashi ikon ambaton Bismillah. Ƙaramar ajiyar zuciya ta sauke, koda yace suci kazan catai ta ƙoshi, dan itakam idan tace zatai irin cin namansa ai matsala za'a samu. Bai wani ci da yawa ba ya tashi akan zaije wajen meeting idan an tashi yazo yaci. Amma ta tabbatar taci abinci inba hakaba ya dawo ɗura zai mata da kansa.

Gimbiya Su'adah ce ƙarshen shigowa. Ramadhan ya gaidata cike da kunyar tun safe bai koma sashenta ba. Koda yake Anne ma da suke tare sai ya fito salla take ganinsa. Ya ɗanyi mamakin yanda ta amsa masa a sake, ta kuma gaida su Anne itama. Kowa zaune yake a kujera har su Yafendo, shine kaɗai zaune ƙasan lallausan carpet ɗin falon domin girmamawa ga iyayensa. Ba Ramadhan ɗin kaɗai ba, hatta su Pa sakewar gimbiya Su'adah ya basu mamaki, duk da suna danganta hakan da abinda ta kawo take ganin zataci nasara. Su dai babu ruwansu, idan Ramadhan ya amince ya karɓa zasu tayasa so, idan baya so kam bazasu masa dole ba tunda yay musu biyayya akan Raudha kar su cika shiga hakkinsa. Bayan an buɗe taro da addu'a Bappi ya bama Gimbiya su'adah damar faɗin abinda tazo musu da shi kafin yau. Tunda ta fara bayani Ramadhan ya ɗago a rikice yana duban mahaifiyar tasa. Fara'ar fuskarsa kuwa tuni ta ɓace sai dai komai baice ba harta kammala. Bappi ya jinjina kansa da maida hankalinsa ga Ramadhan da ya maida kansa ƙasa. “Ramadhan kaji abinda mahaifiyarka tace. Tana buƙatar ka auri ɗiyar ƴar uwarta domin likita ya sanar matarka bazata sake haihuwa ba saboda ciki data zubar a kwanaki”. Ramadhan daketa jera kalmomin innalillahi a zuciya ya nisa da ƙyar. Abinda Maah bata sani ba ya daɗe da kammala bincike akan yanda Raudha tasha magani, sai dai takamaimai wanda ya bama su Muneera maganin suka zuba mata dama yake nema ruwa a jallo. Sai gashi a cikin sauƙi ta tabbatar masa da itace, domin inba itace ɗinba taya tasan mahaifar Raudha zata lalace harta gagara haihuwa....? “Ramadhan!”. Inna dake gefensa ta kira sunansa. Numfashi ya furzar da ɗago idanunsa da suka kaɗa ya kalleta. Sai kuma ya maida kansa kasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa. “Kiyi haƙuri Maah bazan bijirema umarninki dan baki isaba. Sai dai zanyi hakane tare da tabbatar miki wannan BAƘAR INUWAr da kike hangemin gwara ranar da kike gudanmin da ita. Ban musa miki wasu a dangin Ameenatu nada tabo na ƙaddarar rayuwa ba, amma ina son ki sani wlhy Ameenatu yarinyace kamila mai addini. Sannan ta kawomin mu..tuncin...ta har gida. Idan zan faɗa miki wacece wadda kikema kallon mutuniyar kirkin a yanzu zakisha mamakin hakan. Maah laifin wani baya shafar wani ko'a wajen UBANGIJI. Sannan ALLAH na fidda rayayye a cikin matacce. yana kuma fidda matacce a cikin rayayye. Hauhuwa kuwa ta ALLAH ce, amma insha ALLAH akoda yaushe zaki iya ganin zuri'ata basai na auri wata ba”. Dukkanin wata fara'a dake a fuskar gimbiya Su'adah ta ɓace ɓat, baka ganin komai sai ɗunbin ɓacin rai da azabar masifa. Gasu Pa kuwa gaba ɗaya murmushi ne kwance a fuskokinsu, bana bijirema gimbiya Su'adah da Ramadhan yayi bane. Na yabo da tabbatar da ingancin tarbiyyar Raudha da sukajine daga bakinsa. Wanda su sanin kansune Ramadhan baya iya boye abu inhar bai masa daɗi ba zai faɗa, hakama idan yayi masa zai yaba koda da murmushi ne. Koba komai hankalinsu ya sake kwanciya da yarinyar da suka jima suna kyautatama zato. Babu wanda ya sake cewa komai har ita. sai Inna ce tai musu nasiha da gaba ɗaya take nufin da gimbiya Su'adah take amma sai ta haɗa kowa da kowa a ciki. Daga haka taron ya tashi babu wani armashi. Dan ko bikin yaran gidan da sukaso tattaunawa a yau ɗin shima bai yuwu ba dole aka barsa sai wani lokacin dan ana jiran sauran gidajen angunan su kawo kuɗi ne. Ƴammata kusan shidda za'a aurar a gidan nasu Ramadhan. Ciki harda Lubnah da Bilkisu kuwa. Sai Sumayya, Rufaidah, Ai'sha da Ummita. Dukansu sunyi karatu wasunsu ma na aiki, Ummita ce kawai take kan karatun saboda manemin nata ya takurane yasa za'a haɗa da ita amma sa'ar Muneera ce ma. Koda yake ita kanta Muneera ɗin ta isa auren ai kawai dai dan akwai yayuntane.

Babu wata walwala Ramadhan ya koma wajen Raudha, dan yasan ma'anar shirun mahaifiyarsa. Tuni ita har tayima shirin barci. Tana zaune ne a kan gadon tana assignment ɗin makaranta da aka basu na cikin hutu, sai dai sanye take da hijjab a saman kayan barcin nata. A kallo guda ta fahimci ransa a ɓace yake, cikin dauriya ta masa sannu. Bai amsa ba sai dai ya kwanta a gadon tare da ɗoro kansa saman cinyarta bayan ya ture takardun gabanta gefe. “K dole kin zama ƴar boko ko?”. Ɗan murmushi tayi kawai dan yanda yay maganar kamar mai son huce haushinsa akan bokon nata ne. Cikin san kauda masa damuwarta tace, “Harka tunamin Abbanmu. Idan mukai masa laifi koya tashi baida ko sisi sai ya hana kowa zuwa makarantar boko ranar. Ya ringa faɗin, “Anma fasa bokon, daga yau bazaku sake zuwa ba, bandama shegantaka irin ta bature yabi duk ya katantane duniya ya hana kowa zaman lafiya, komai bazaka samesa yanda kake muradi ba sai kayi wani abu shege a.b.c.d kai nifa shiyyasa ma ana kaini ina tserowa a makaranta da ƙyar na haɗa sakandire ɗin ma”. A bazata dariya ta ƙwace masa. Har haƙoransa na bayyana baki ɗaya sai dai ya kai hannu yana karewa. “ALLAH na lura Abba ɗan darune?”. Ganin yanda ya karɓi zancen ya saka Raudha dake nata ƴar dariyar itama faɗin, “Tab damma baka sanshi bane. Wlhy duk randa darun Abba ya tashi gidan nan ranar kowa sai yaji a jikinsa. Ko ruwa ka cika kofi zakasha sai yace ka ƙara masa talauci kana baƙin cikin ya zama mai kuɗi”. Yanzu kam sosai yake dariya. Raudha da farin ciki ya cikata itama ta tura yatsunta duka a cikin gashinsa tana masa susa. Nan ta shiga bashi labarin M. Dauda sai dai na hankali wanda tasan mutuncinsa bazai zube a garesa ba. Cikin amincin ALLAH sai gashi ƙaunar mahaifinta ta sauka masa a rai har yanajin sassaucin takaicin halayyarsa tada da bincike yazo da ita. “Ya kamata ma muje mu gaishe da Abba Hutawa gaskiya”. Cak Raudha ta dakata da susan da take masa a cikin gashi ta tsurama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ido idanunsa a lumshe suke yayin da hannayensa duka ke harɗe a ƙirjinsa yana kwance rigingine. Yanda ya nutsu zai baka tabbacin susar da take masa cikin gashi na masa daɗi. Ya buɗe lumsassun idanunsa da suka canja launi a hankali ya zuba mata su. Gira yaɗan ɗaga mata yana sassanyan murmushi. “Yadai naji kinyi shiru Ustazah?”. Hawayen da suka ɗan cika mata ido ta haɗiye, cikin ƙaƙaro murmushin itama tace, “Nagode da karamcinka”. “Cmon johre. An gaya miki Abban nakine ke kaɗai banson iyayi”. Yay maganar yana dungure mata hanci da ƙoƙarin miƙewa zaune. Toilet ya shiga, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya da hawaye lokaci guda. Wani abu mai muhimmanci na sukar ranta. Koda ya fito wanka cayay ta kawo masa sauran namansa. Dan bacin ran daya shigo da shi ta riga ta gusar da shi. Kawo masa tai harda kunun, yako ci abinsa yay ƙat sannan ya koma bayin yayo brush, koda ya dawo assignment ɗin ta nuna masa inda bata gane ba. “Ustazah! Kibar batun Assignment ɗin nan nima inada nawa Assignment ɗin mai kawo lada ma.” “Please Ya Ramadhan dafa an koma hutu idan ALLAH ya kaimu zamuyi submitting”. Gadon ya hawo yana ɗaure igiyar rigar barcinsa. Ya zare mata hijjab ɗin jikinta sannan ya ɗauka takardar data rubuta questions ɗin da amsar data rubuta daban na wanda ta gane. “Yarinyar nan kanki fa naja”. Ya faɗa cikin ɗage mata gira. Murmushi kawai tayi da maida kanta ƙasa. Shima hankalinsa ya sake maidawa ga takardun yana faɗin, “Ai gyaran ma kaɗanne”. Bayani ya shiga mata dalla-dalla harma akan abinda bata tambayesa ba, dan shima yayi course ɗin sanda yana jami'a. Sosai taji daɗin bayaninsa har tana sake zaƙulo masa wasu tambayoyin. Sai dai taƙi sakewa da jikinta sai faman karewa take da hannu kamar mai jin sanyi. Tsaf yana lure da ita amma yay kamar bai gani ba. Zata sake jeho masa wata tambayar ya turo kayan karatun nata ƙasa da jawota jikinsa yana faɗin, “K ni na gaji da aikin bautar bature zo kiji wata magana”. Gabantane ya shiga faɗuwa. Sai dai ko saurarenta baiyiba yaja musu bargo ya matseta a jikinsa yana shinshinar wuyanta da kai mata kiss's..........✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

Chapter notes and social links

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull