Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 3

Bakar inuwa book 1 - Chapter 3

Bakar inuwa book 1 Chapter 3: Bakar inuwa book 1 Chapter 3. ..........Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka…

4,378 words

..........Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso, inda aka amshi Raudha dake a jigace har batasan inama kanta yake ba zuwa yanzun. Ko sisi Fatima bata da shi, tayi ƙarya ne kawai dan Abbansu ya bari a kawo Raudha asibiti. Tana ganin an amshi Raudha ɗin ta fito ta nufi ofishin Doctor Rufa'i, sai dai anyi rashin sa'a wai baya nan yamaje Ɗillo tun jiya. Dawowa tai inda Mommy da Abban ke tsaye a ƙofar ɗakin da aka shiga da Raudha ɗin. Zama tai itama tabi ayarin ƴan tagumi, a haka har doctor ɗin ya fito yana mai kwantar musu da hankali akan karsu damu komai zai dai-daita, dan zai rubuta musu wasu allurai da zasu sayo, da zaran anma Raudha ɗin inssa ALLAH zata samu nutsuwa. Cikin gamsuwa da rashin damuwa aljihunsa zaiyi tsuwwa ya miƙe yabi doctor ɗin, har yaje ya dawo mommy da Fatisa da Fatima bakinsu bai saɓa ba. Sai da ya dawo da takardar ya mikama Fatisa ɗinne ta ce, “Abba ya zaka bani kuma? Ba cayay a sayo ba?”. Wani shegen kallo ya watsa mata ita da Fatima fuska a ƙwaɓe. “Kunci bu*a'ubaku, ƴan bu*a'uban yara da basa ko ganin mutuncina. Ni kikema magana haka kamar kina a gaban tsohon kwarto”. Fuska Fatisa ta ƙwaɓe tana ƙunƙuni, zai sake magana Asabe ta katsesu. “Wai nikam maganin zaku sayo a cetomin yarinya ko tazubar ɗinne ya motsa muku a bainar nasi?. Kai kullum bazaka ja girmanka ga yaran nan ba balle tauna harshenka da baiko da linzami wajen sakin magana”. “Kar yayi linzamin mana. Banda shegantaka irin tata ba itace tace tanada kuɗi ba shine zata wani tsareni da idanu na rashin ta'ido. ai sai da nace ku bata ɗan libiya amma tace tanada kuɗi ko......” “Ni dai ya isa da ALLAH. Ke Fatisa anshi kije ki sayo”. “Mommy nifa wlhy banda ko sisi anan. Nace inada sune danya yarda akawota asibiti. Dan haka sai yaje ya nemo inma baida su, dansu dai likitocin nan bawai batun lamuni suka sani b.....” Hannu yakai zai kwaɗa mata mari ta tashi ta fita a guje Fatima na take mata baya. Babu ko kunya ya rufa musu baya shima duk da kuwa tsufa ta fara kamashi, ga sigari duk ta gama cinyesa a tsayee.... “Subahanalillahi! Malam ɗan-azumi lafiya kuwa?”. Cak yaja ya tsaya yana huci saboda jin an ambaci sunansa. Sai kuma duk ya diririce ganin Falalu mai shago tare da Alhaji Maude Dallatu, ya ɗan tura hularsa baya yana ƙaƙaro murmushi. “A'a Falalu kune anan? Ince dai lafiya ko?”. “Ai kai ya kamata mu tambaya ko lafiya kuwa baba?”. Cewar Alhaji Maude duk da kuwa zai iya girmar ɗan-azumin ko suyi sa'anni. Fuska ya marairaice kamar zaiyi kuka, saboda hangen damar dake garesa ta ƙarshe da mafita kenan. “Alhaji wlhy Raudha ce babu lafiya muka kawo asibiti. Shine waccan ja'irar na bata ta sayo magani take shirin min ƙyuya irin nasu na yaran zamani”. Fatisa tai saurin waro ido waje suna kallon juna ita da Fatima da gumtse bakunan su jin dariya nason kufce musu. “Ai sai dai haƙuri baba. Inga takardar”. Alhaji Maude ya sake faɗa a ladabce yana miƙa hannu ya amshi takardar hannun Abban. Kamar bazai bashi ba dai yana ɗan nannoƙewa sai kuma ya miƙa masa. Koda Alhaji Maude ya amsa bai wani tsaya dubawa ba ya kalli Falalu dake ɗauke da kaya niƙi-niƙi alamar duba wani mara lafiyan sukazo ko makamancin hakan. “Falalu ƙarasa ciki ina zuwa”. “To ranka ya daɗe, amma daka kawo ni sai naje zai fi”. “No karka damu jeka ciki kawai zanzo yanzun”. “To a shigo lafiya”. Falalu ya faɗa cikin girmamawa yana ɗan murmushi. “Baba ka jirani nan kaima ina zuwa”. Alhaji Maude ya sake faɗa yana tafiya da kallon mal. Ɗan-azumi. Kafinma yace masa wani abu har yayi nisa. Hannu ɗan-azumi ya ɗaga sama yana godema ALLAH daya kawo masa Alhaji Maude a lokacin daya dace, sai dai a ransa kuma ya ƙudira dolene kuɗin da duk zai biya na maganin sai Fatisa tayi kashinsu. Yana nan tsaye ko mintuna goma ba'aiba sai ga Alhaji ya dawo, da taimakon sa sukaje inda aka kwantar da Raudha ɗin. Babu ɓata lokaci doctor ya amsa dan dama su kawai yake jira.

Alhaji Maude na nane da su har kusan awa uku, dan sai da Raudha ta farfaɗo ta koma normal barci da allurar ta sakata sannan yace musu zaije ya dawo zuwa anjima. Godiya suka dinga masa kamar zasu gurfana ƙasa. Yana juya baya Asabe ta warce kuɗin daya mikama Baba tana faɗin. “Ɗan cin rabo, kaci naka zaka hau kan haƙƙina”. Hannu yakai zai damƙota a fusace. “A gidan wane shege akace rabonki ne? Asabe anya zakiga ANNABI kuwa?”. “Ai tare da kai zamu gagara ganinsa kwantar da hankalinka jemage maƙi jinin ƙasa sai samaniya..” Cikin takaicinsu Fatisa tace, “Asibitine fa Mommy. Yanzu dan ALLAH idan ya dawo ya jiku kuma fa? Mudai wlhy kuna zubar mana da mutuncinmu”. Baki Asabe ta ƙyaɓe. Batare data tanka ba ta zari dubu biyu ta miƙawa baba ta saƙe sauran a zane. Ƙin amsa yayi, sai dubanta da yakeyi cikin takaici da ɓacin rai. “Mikike nufi?”. “Babu abinda nake Nufi sai haƙƙinka dana baka gashi nan. Tunda ALLAH kaɗai yasan abinda kaci kaima”. Wata dariyar takaici da tafi kuka ciwo yayi ya ɗauke kansa. “Asabe kina wasa da lamarina wlhy. Ince dai nine silar haɗa auren ko? To wabilahillazi zan iya rusashi a gabanki kuma na bashi wata sai dai ki hangi arziƙin”. Duk da taji tsoron zancen nasa dan tasan zai iya sai ta balla masa harara. Zatai magana likita daya ƙaraso ya katseta. “Baba zaku iya tafiya da ita babu damuwa”. Gaba ɗayansu suka juya gareshi, kafinma suce wani abu Fatima da bata tanka musu ba tunda suka fara ta afka ɗakin da Raudhan take Fatisa biye da ita. Asabe ma ɗakin ta juya da niyyar shiga mal. Ɗan-azumi ya samu damar warce kuɗin data saƙe a cikin zani. A wani irin muguwar zabura ta juyo, sai dai kamar walƙiya ya ɓacema idanunta. Ranta yayi ƙololuwar ɓacin da har ma ta kasa bin bayansa balle yin magana har Fatisa da Fatima suka fito riƙe da Raudha. Yini guda harta sake ramewa, sai idanu zuru-zuru ga allurar da akai mata yasa barcin bai gama sakinta ba. “Mommy mike damunki?”. Raudha ta faɗa a hankali idonta akan Asabe. Ƙwafa Asaben tayi tana magana cikin ɓacin rai, “Minene kuwa zai dameni idan ba ubanku ba, wanda ƙaddarar rabonku ta zama silar haɗuwata da shi. Wlhy a wannan gaɓar kuwa lallai zan shayar da Dauda zumar mamaki. Yanda yake jinsa tantiri nima tantiriyarce ta gaske, kuma zan tabbatar masa da hakan yau basai gobe ba”. Dariya Fatima ta ɗanyi dan ita ko'a jikinta. Raudha kam hawayen da suka ciko mata idanu ne suka silalo a hankali. Hannu ta kai ta share da ɗan cije baki saboda kanta dake sara mata. A haka suka hau mashin ko sisi babu a jikinsu. Sai da sukazo gida Asabe ta shiga ta kawoma mai napep ɗin masifa fal ranta..

Har aka sha ruwa Malam ɗan-azumi bai yarda ya dawo gidansa ba, dan yasan halin Asabe sarai. Ya tabbatar yau duk da azumin dake a bakunansu sai sun tara ƴan kallo a cikin anguwa, shi kuma baya buƙatar hakan tunda yasan shine mara gaskiya, shiyyasa ya zaɓi ƙin dawowa gidan har aka sha ruwa. Yadai samu gasashen naman kazarsa da fura mai sanyi yaci yay ƙat. Ya kuma ɗora da indomie da ƙwai da shayi wajen Bello mai shayi. Sannan ya ɗan zuƙa sigarinsa kara uku. Sai wajen sha ɗaya na dare ya lallaɓo a tunaninsa kowa yayi barci. Sai dai yayi rashin sa'ar cin karo da Asabe dake zaune dakaka tana zaman jiran shigowar tasa. Yanako shigowa tai caraf da rigarsa taci kwalarsa. Tun sunayi iya su har kowa na gidan ya farka. Dama Larai na laɓe tana kallon komai tun farko tana kwasar dariya, tunda taga Asabe zaune taƙi shigewa tasan akwai wata a ƙasa dama, balle itama akwai tsiyar data harbo, dan tun maganar da taji a ɗazun game da Alhaji Maude Dallatu mai son Raudha hankalinta bai kwanta ba, suna fita a gidan itama ta fice. Rigimace sosai ta harƙume a tsakaninsu harda doke-doke. Dan sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu da ƙyar. Kuka sosai Raudha keyi tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta. Dan ko leƙe bata leƙo ba dama tunda aka fara faɗan tana ɗaki kwance. Abu kamar wasa har gabannin asuba wannan faɗa yaƙi rabuwa. Mutane har sun gaji sun koma gidajensu sun barsu. Ƴan gidan kam har yara sun farka dan kowa ya gagara barci. Duk suna a tsakar gida, Raudha ce kawai batako leƙo ba tana lafe a ɗaki tana faman dirzar kuka. Ko sahur ɗin kirki ranar babu wanda yayi a gidan. Kiran sallar asuba yasa Baba Nafi fara roƙona malam Dauda akan ya fita massallaci shi dan ALLAH ko hakan zai kawo masalaha. Shawararta yasa shi fitar yana faman huci, duk da ba yaune karon farko da suke irin wannan faɗan ba, sai yakejin zafin Asabe a yau fiye da koyaushe. Ji yake tamkar ya saketa ya hutama ransa.

Koda aka idar da salla maimakon yaƙi dawowa gidan sai shaiɗan ya dinga tunzurasa akan ya shigo yaga ƙarshen haukan Asaben. Yaran kawai ya samu suna kiciniyar alwala a tsakar gida. Dan Baba Nafi da su Fatisa sun lallaɓa Asabe da ƙyar ta shiga ɗaki itama bayan tayi alwala. Tana ɗaki zaune tana rusar kuka ya dawo, dan ko sallar ma haka tayita tana kuka. Wani irin ɗaci da zafin Malam Dauda takeji yau fiye da ko yaushe a rayuwarta. “Haba Malam mi kuma ya dawo da kai gidan nan a yanzu?”. Baba Nafi dake tattare kayan wanke-wanke ta faɗa lokacin da malam Ɗan-azumi ke shigowa gidan zuciyarsa tamkar zata kama da wuta. Zuciyar tasa dama a kusa take, dan haka cikin masifa yace, “Na dawone dan naga ƙarshen isakancin Asabe yau a gidan nan!!”.. “Kai ɗin banza daka isa kaga ƙarshen iskancina Dauda. Kaima kasan ni nafi ƙarfin kanwar lasarka, dan ina dai-dai da wandama ya fika balle kai ɗin ƙaramin shegen bariki”. Da wani irin rawar jiki malam Dauda ya cacimi taɓaryarsu ta daka yayi kan Asabe gadan-gadan. “Aiko yau zan tabbatar miki da ni babban Shege ne....!” Baba Nafi datai saurin shan gabansa ta riƙe taɓaryar da sauri. “Haba Malam waini kam mike damunku yau haka ne? Yanzu akan ƙaramin abu dabai taka kara ya karya ba zance yaƙici yaƙi cinyewa domin ALLAH!”. Hankaɗe Baba Nafi yayi, cikin matuƙar sake harzuƙa ya fisgi taɓaryar yana ƙoƙarin sake nufar Asabe da itama ta rarumo kujerarsu ƴar tsugunno ta nufosa, su Fatima suka riƙeta. Sake riƙesa Baba Nafi tayi dan taba duk ta gama cinyesa a tsaye ba wani ƙarfin kirkine da shi ba. Cikin matuƙar sake harzuƙa yake nuna Asabe da ɗan yatsa yana faɗin, *_“Kije na sakeki Asabe. Na sakeki saki biyun daya rage tsakanina da ke!!_* Bana son sake ganin fuskarki, Idan ba hakaba wlhy yau sai na kasheki a gidan nan da hannuna”. Da sauri Larai ta shige ɗaki wani irin ɗan karen daɗi na saukar mata a rai da zuciya, har ji take tamkar ta daka tsalle ta dire dan yau burinta ya cika. Itako babu abinda zatace da malam ɗan-kande sai godiya. Gashi ya mata aikin da taketa kashe kuɗi tsahon shekaru a cikin ƙanƙanin lokaci. Gwatsar wayarta da tasha ɗaurin ƙyauraye ta ɗauka ta shiga laluben ƙanwarta Haƙila danta guntsa mata wannan daddaɗan labari haka da farar safiyar nan ta juma'a.

A tsakar gida kuwa duk yanda Baba Nafi take ƙoƙarin ƙwaɓar Malam ɗan-azumi yaƙi saurarenta sai sake maimaita kalmar saki yake ga Asabe da gaba ɗaya jikinta yay sanyi kuma a lokaci guda. Dan yana ambaton ya saketa duk zafinsa da takeji kuma sai taji ya kau baki ɗaya. Da wani irin sanyin jiki ta saki kujerar hannunta jin hajijiya na neman kadata ƙasa. Riƙota su Fatisa sukayi suma jikin nasu na rawa. Raudha dake cikin ɗaki zaune tana karatun Al-qur'ani tai saurin miƙewa tana dafe ƙirji, dan kalmar sakin nan tajita tamkar sukar mashi a ƙahon zuciya. Tuni ta nema kukan da takeyi ta rasa. Da gudu ta fito tsakar gidan, taje gaban Mahaifin nasu ta zube gwiwa a ƙasa tan roƙonsa akan yayi haƙuri karya saki Mommyn su dan ALLAH. Duk hukuncin da yakejin zai mata ita yayi matashi dan ALLAH duk zafinsa zata ɗauka. Hankaɗeta yayi cikin rufewar ido yay waje yana cigaba da kunfar baki. Raudha ta miƙe da gudu ta bisa tana kuka amma ko waiwayenta baiyiba.........✍️

*_Tofa yau dai da alama auren zobe ya ɓalle? Ko asabe zata yarda tabar gidane? Duk da kuwa saki uku ne a kanta idan aka tara da guda ɗaya na baya. Shin auren Raudha da Alhaji Maude Dallatu zai yuwu kuwa?. To minenen ma ma'anar BAƘAR INUWAr? Suwaye BAƘAR INUWAr? Mizai biyo baya a gundarin labarin BAƘAR INUWA? Dukan amsoshinku na cikin Littafin BAƘAR INUWA da nakeda tabbacin ya taɓo muku inda ke muku ƙaiƙayi. Karku ɗauka a gidan su Raudha kaɗai cakwakiyar zata ƙare. Sam ba haka bane, akwai wasu rikicin da gidajen a gaba. Sanin alaƙarsu da Littafin BAƘAR INUWA sai ka mallaki naka ankai har ƙarshe da kai. Masoya ba'a fara komai ba, dan kuwa a paidpages ne kawai zaku san minene gundarin labarin BAƘAR INUWA😉⛹🏻‍♀️🥰🥰🙏🏻_*

_Ku kasance da ZAFAFA BIYAR domin karanta daɗaɗan labaransu guda biyar dake tafe da salo na musamman masu ƙayatarwa_.

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*____________________*

*_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA K'ARA MANA HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI DA MA NA IYAYENMU BAKI ƊAYA (AMIN😭🙏🏻)._*

*_____________________*

*_Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce_*

*_Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba_*

*_Ina mata ƴan ƙwalisa ma'abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa._*

*_Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma._*

*_Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener._*

_Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252_.

*Sai kunzo🤳🏻*

*________________________* *_Episode 6_*

...........Da ga Asabe har ƴaƴanta hankalinsu a matuƙar tashe yake. Hakama Baba Nafi, duk da Asabe kishiyace a gareta aurota da akai a gidan ba ƙaramin alkairi ya zame musu ba ta wani ɓangaren. Dan koba komai Asabe kansaka Malam ɗan-azumi ya sauke haƙƙoƙin su dake kansa koda baiyi niyyar hakan ba. Dan kafin ya aurota sai ya gadama yakeyi, ya gwammaci yaje yay caca ko neman mata. Sannan duk jarabarnan tata da wahala kaga tana faɗa da kishiya, wani lokacin Larai kanso suyi, amma Asabe sai taƙi kulata. Mal. Dan-azumin ne dai ita da shi kamar suna kallon hanjin juna. Hatta da sauran yaran gidan duk sun zama sukuku, musamman ma da Inna mahaifiyar malam Dauda ɗin tazo ta sake zazzaga tata masifar ga Asabe saboda Larai taje ta sanar mata ƙarya da gaskiya, duk da kuwa ba ƙaunar laran take ba. Babu wanda ya tanka mata sai larain, dan harda kawoma Innar ruwa saboda tsugudidi. Saida ta gama zazzage masifarta tsaf da gorin Asabe tabar mata gidan ɗanta sannan tabar gidan, Asabe dai na ɗaki ita da yaranta duka cikin matsananciyar damuwa. Dan har Inna tayi ta gama babu wanda ya leƙo. Gaba ɗaya wannan yini dai anyisa a gidan cikin rashin daɗin rai ga azumi. Idan ka cire Larai dakejin tamkar ta ciji sama dan farin ciki. Malam Dauda bai sake dawowa gidan ba sai dare bayan sallar isha'i. Tsabar jinsa yau a sama da sigari ya shigo gidan yana busawa, wayarsa mai shegen ƙara tana raira waƙar (marigayi Ali makaho) Galala Baba Nafi tai tana kallonsa, dan duk iskancinsa bai taɓa shigowa gidansa yana shan sigari ba tunma yanaji da ƙuruciya a iskancin. Amma abin mamaki sai gashi a yau cikin watan azumin ramadana, a kwanakin goman ƙarshe da kowa ke dagewa da ibadar ALLAH, ya shigo gidansa dake cike da ƴaƴa a wannan yanayi. Tsakar gida ya zauna akan rijiyarsu yana kaɗa ƙafa da kai yana zuƙar sigari da ƙwala kiran sunan Asabe tamkar zai tsaga bangon gidan. Ko tari bataiba ballantana ƴaƴanta, jin taƙi tankawar ya sakashi fara zazzaga ruwan masifa da jaddada mata ta bar masa gidansa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu baisan sake ganinta. Kuma ko Yasmin bai yarda ta ɗauka ba idan zata wuce, ta bar masa abarsa. Nan ma ko tari babu wanda yayi sai Larai data fito daga ɗakinta ɗauke da tire ta jero kwanika. Dan duk da bai bada kuɗin cefane ba, ba kuma aikinta ba yau kuɗinta ta saka tai girki iya ita da ƴaƴanta da shi. Wani irin washe baki yayi yana gyara zama a lokacin data kai tsugunne gabansa tana dire tray ɗin. “A'a! Larai na mina samu haka ne?”. Cikin jin daɗin sunan daya kirata da shi ta buɗe tsohuwar kular dake sama, wadda ke cike da taliya da miyar kifi, sai kunun tsamiya a kofi da ƙosai data sayo masa a ƙaramin kwano. Albarka ya shiga kwarara mata da gyara zama ko kunya babu da tunanin bashi yay cefanen ba. Baba Nafi kuwa dake kallonsu tuni zuciyarta ta harba. Dan zuwa yanzu ta fara zargin Larai akan wannan fitinar dake faruwa tsakanin mijin nasu da Asabe. Dan lallai akwai wani abu a ƙasa gaskiya. Cikin farin ciki Malam Dauda ya kwashi girki yana kwararama Larai kirari tamkar wani jikan maroƙa. Itako sai wangale baki take.

★★★

Washe gari sabuwar fitina ta sake tashi tsakanin Asabe da malam ɗan-azumi. Dan ya tabbatar mata sai ta bar masa gida a yau. Kuma bazata tafi masa da yaransa ko'ina ba. Ta bashi haƙuri sosai tana kuka amma yaƙi saurarenta, saima yi yake tamkar tana zugashi. Dan gaba ɗaya ya sake birkicewa, har mamakinsa mutane keyi musamman yanda aka san yana bala'in son Asabe, ba kuma yaune karon farko da suke irin wannan fitinarba a cikin anguwar, harma wadda tafi haka sunayi kuma su shirya. Ana tsaka da hakan kuma sai ga Inna yau ma. Komai sake rincaɓewa yayi har maƙwafta da suka taru domin bashi haƙuri akan ya maida Asabe kodan ƴaƴansa sai da ta shafesu. Dan Inna tas ta zagesu ta sake saka malam ɗan-azumi ƙarama Asaben saki ɗaya daya saura a tsakaninsu wanda ya mantama yayisa tun shekarun baya. Wannan abu yayima su Fatisa zafi matuƙa. Dan haka suka shiga haɗa kayansu masu muhimmanci dana mahaifiyarsu. Cikin ɓacin rai Fatima taje ta jawo hannun Raudha da Asabe dake gurfane suna basa haƙuri, dan itama Asaben ta zama tamkar ba itaba yau duk masifarnan babu ita. “Mommy dan girman ALLAH in har ba Abbanmu ne autan maza ba a duniya ki barsa kizo mu wuce tunda kema kina da dangi ba'a bola ya tsintoki ba, dan ALLAH idan ya tashi ya auri Innar dake zugashi ɗin...” “K! fitsararriya!!”. Inna ta faɗa a tsawace. Ko kallonta Fatima batayiba taja hannun Raudha da Asabe suka nufi ɗaki.

Abinda Fatiman tayi ya sake hargitse gidan, Malam Dan-azumi da kansa ya shiga har cikin ɗaki ya fisgo Asabe ya kaita har ƙofar gida yana faɗin tabar masa gidansa, baya son ganinta ya tsaneta. Cikar da ƙofar gidan ta sakeyi ne yasa harsu Raudha suka fito da kaya malam Dan-azumi da Inna basu lura ba. Hakama Baba Nafi. Larai kuwa sarai ta gansu dan tana gefe tanata kwasar dariyarta. Mota ƙarama suka fara samu da zata kaisu har jihar Bina shata, kafin wata makwafciyarsu da suke ƙawance da Asaben taje ta kamo hannunta ta kawota har wajen motar, dan itace ta hana su Fatisa komawa wajen gudun kar Malam Dan-azumi ya gansu ya hanasu bin Asaben. Itako bata fatan Asabe ta tafi tabar ƴaƴanta, gara duk rintsi ta tafi da abinta kafin abun yay sauƙi, dan da gani kasan malam dauda baya cikin hankalinsa sam. Tafiyar Asabe yasa akaɗan samu sauƙin hayaniyar. Sai mutane daketa yima Malam Dan-azumi ɗin ALLAH wadai da koran Asaben da yayi batare da wani ƙwaƙwƙwaran laifi ba, dan koda aka tambayesa ya rasa mi zaice tayi masa sai babbotan borin kunya yakeyi shida Inna da dama kowa yasan batan ƙaunar Asabe dama duk surukan nata sai baba nafi kawai, ita kanta wani lokacin baba Nafin baji da dadi take hannun innar ba. Na Larai da Asabe yafi zafi ne kawai dai dan ta kasa tanƙwara Malam Dauda ɗinne ya sakesu dole ta haƙura. Yanzu ko data samu dama shiyyasa tai tsayuwar daka wajen ganin ƙarshen Asaben da take kallo matsayin wani miki ga ɗan nata....

★A Bina su Asabe suka yada zango gidan yayarta Halima da take aure anan. Sai dai kuma sunyi rashin sa'a bata nan wai tana jihar Loss kusan wata guda kenan ita da ƴaƴanta duka da mijinta. Sam Asabe bataso haka ba. Dan bata buƙatar zuwa babban birinin ƙasar Bingo dasu Fatisa wajen Gwaggo (Mahaifiyarsu hajiyar birni). Saboda ta tabbata idon hajiyar birni idon su Raudha to akwai matsala. Cikin damuwa da sanyin murya Raudha ta kalli Asabe da sauran ƴan uwanta da duk suka jigata saboda azumi, ita kanta daba azumin takeba a jigace take dan babu abinda taci tun jiya da rana sai ruwa. Hawayen dake a idanunta ta share da faɗin, “Mommy nikam a ganina mizai hana mu wuce Bingo wajen su Gwaggo direct mana. Babu amfanin wani raɓe-raɓe a gareki damu a yanzu. Na tabbata Gwaggo ta canja zuwa yanzu, sannan zata amsheki hannu biyu tunda daman zamanki da Abbanmu ne bata so.” Shiru asabe batace komaiba. Tasan maganar Raudha gaskiyane, sai dai tana fargabar zuwa dasu Bingo su lalace kuma. Su Fatisa basa jin magana tabbas, amma rashin jinsu bai kai inda masu karatu ke hasashe ba, sai dai ta tabbatar kusantasu da hajiyar birni a yanzu komai zai iya faruwa, saboda masifar son kuɗinta. Suma ƴaƴanta ta ɗorasu a hanyar banza dan kawai ta samu kuɗi, balle su kuma jikoki gasu kuma yaranta dukansu masha ALLAH, ba duk namiji zai kalla ya iya kauda kai ba...... “Mommy gaskiyafa Raudha ta faɗa wlhy, gara kawai mu tafi Bingo ɗin”. Fatima ta faɗa cikin katse tunanin Asabe. Numfashi asaben taja mai nauyi, “Banƙi ta taku ba, sai dai nima akwai abinda nake lissafawa. Amma kuma banida wata mafita saita tafiya Bingo ɗin a yanzu. Matsalar kawai dai itace bamu da isassun kuɗin motar da zasu kaimu ne mu duka”. “Akwai kuɗi Mommy”. A tare duk suka dubi Raudha datai maganar cikin mamaki. Cikin rashin damuwa da kallon da suke matan ta zaro kuɗi a cikin zani sabbi ƙal ƴan ɗari biyu ta miƙama Asabe. “Mommy jiya mutumin nan da yazo dubani a asibiti ya bani su. Nayi niyyar bakine dama idan munzo gida danki fara sana'a. Amma yanzu na tabbatar insha ALLAH zasu kaimu duk inda zamuje ko?”. Hawaye ne suka ciko idon asabe. Dan bata taɓa tunanin Raudha haka ba. Ganin yanda take musu nuni dasu gyara yasa take tunanin sam Raudha bata ƙaunarta matsayin mahaifiya. Ashe ba haka bane ba. “ALLAH yayi muku albarka, ya kare min ku”. Ta faɗa gawaye na silalo mata na nadamar sakaci da tasoyi akan tarbiyyar ƴaƴanta saboda ruɗin shaiɗan da son zuciya. Hannu Yasmin dake jikinta tasa ta share mata hawayen. “Mommy ki daina kuka, banason naga kina kuka kamar irin na Aunty R”. Asabe ta rungume Yasmin tana murmushi da share sauran hawayen. “Na bari auta, itama bazata sake yin kukaba insha ALLAHU. Da ga yau zan tsaya akanku da inganta tarbiyyarku da muku addu'ar miji nagari ba irin mahaifinku ba da ni.” Ba Raudha da ɗabi'ar iyayensu ke damunta a rai ba, hatta su Fatisa yau duk sai jikinsu yay sanyi ƙalau. Bayan asabe ta kira ƙawarta dake hutuwa sukai magana sai suka ɗunguma tasha duk da yamma tayi liƙis. Basu damuba dan tafiyar daren ma sai tafi musu kwanciyar hankali. Anan tasha sukasha ruwa dayin sallar magriba. Kafin motarsu ta tashi zuwa birnin Bingo. (Babban birnin ƙasar NAYA kenan. Dan yanzu hajiyar birni tana nan da zama ta baro jihar loss).

★★★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull