Bakin ruhi complt by mrs sadauki - Chapter 17
Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 17: Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 17. Da sauri na ƙara jan ido na kulle,ina jin yadda bayan hannunsa ke…
4,469 words
Da sauri na ƙara jan ido na kulle,ina jin yadda bayan hannunsa ke yawo kan fuskata yana goge hawayen amma kamar ma sake tunzura ni haka na ci gaba da yin wasu sabbi. Iskan bakinsa na soma jin yana hura min ,na san don na buɗe ido ne amma na ƙi. "Queen?" na ji ya furta can ƙasan maƙoshi kafin kuma na sake jin lips ɗinsa kan nawa,sai a lokacin na motsa da niyyar ture shi amma ya riƙe min dukkan hannuwan nawa tare kuma da yi min mugunta ya cije min leɓena na ƙasa sai kuma ya ɗan ture ni da sauri na buɗe ido, ya watso min wani kallo cike da shaƙiyanci ya ce "ita maitar taki har da ta sarrafa tunanin mutum kike da? Wato kambu Maita ne kika jefa min don na sumbace ki,to ai shikenan tun da kin samu abin da kike so sai ki je ki yi wanka" yana gama faɗar haka ya fice ya bar ni ƙumshe da takaici.
Da na rasa abin da zan yi kawai na yi zaune dirshen na fasa kuka,wato ni ce ma ke son haka? Shi bai ma ga rashin dacewar abin da yayi min ba tuhumata ma yake akan zunubin da shi ne ya aikata.
Sai da na ci kuka na gaji kafin na tashi na koma can ɗaki,cikin ikon Allah sai na tarar da anty Bahijja da kuma Yasmine duk sun samu bacci.Toilet na shiga,sosai na ji takaicin ganin abin da ban saba gani ba in ba a cikin mafarki na samu dalilin fitar da shi ba .Nan ɗin ma kuka na yi kafin na yi wanka na fito,ina tsaka da saka kaya Aliya ta shigo da dukkan alamu kuma cikin murna take.
Ba ta yi ƙasa da gwiwa ba ta soma surutunta da ta saba"kin ga gwamna ya saki challenge ɗin nuna gasar restaurant ɗin da suka fi iya girki,sannan kuma za a duba iya adadin mutanen da suka saya don a bai wa shugaba kyaututtuka na musamman ita da ma'aikatanta " tana maganar ne tana kallon wata takardar tana murmushi.
Duk da ban cikin yanayi haka na karɓi takardar ina dubawa,Aliya ta ci gaba da cewa "Hajiya ma ta shiga tsarin,kin ga za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin lashe wannan gasar mu fito da ƙimar Hajiya kin ga ta silar haka za ta ƙara mana albashi "
"Haka ne! Amma fa akwai jan aiki don akwai manyan restaurant fa " na faɗa .
"Ya na ji muryarki wani iri?" Aliya ta jefo min tambayar,sai a lokacin na ɗago kai muka haɗa ido ta saki ɗan murmushi tare da ƙumshe dariyarta sai kuma ta ce "za mu yi ƙoƙari don ganin mun ci gasar,kin ga har da fa babbar restaurant yayi alƙawarin zai buɗe ga gwarzuwa "
"To Allah bamu sa'a,me ya maido da ke gida?"
"Mun tashi mana! Hajiya ta wuce can kasuwa,ni ma na tawo gida kuma wallahi ban ida wanke sauran kwanuka ba kin ga karɓi key ki je ki ƙarasa" ta faɗa tare da bani key ɗin gidan abincinmu,sai kuma ta kalli anty Bahijja ta kuma maido dubanta gare ni.Na kawar da kai kawai sannan na ɗauki hijabina na fice,a ƙafa na tafi ina tafe ina tunani har na isa. Da na buɗe haka na shiga gyaran ko ina na wanke kuma kwanuka sai na zo nan inda ake cin abinci na ja kujera na zauna,abin da Maheer ne yayi min ya dinga dawo min a kwanya sai kuma na ji hakan ɗin ma na sake saka ni ni cikin wani yanayi,duk yadda na so na ture tunanin kuma na kasa.
"Almajira na yi muku bara" na ji muryar wata tsohuwa daga can bakin ƙofa,ba tare da na juyo ba na ce "ki yi haƙuri!" ban sake jin ta ce komai ba,na yi tunanin ta tafi ne sai zuwa can kuma na ji muryarta.
"Rashin sanin darajar mutane bai kamace ki ba jikata " da sauri na juyo muka haɗa ido ina kallonta sake da baki jin wani zance sai ka ce na zage ta .
"Me yasa za ki cewa na yi haƙuri alhalin kina da abin da za ki bayar da shi sadaka?" ta jefo mini tambaya tare da kafe ni da ido .
Cikin sanyi murya bayan na sauke ajiyar zuciya na ce "banda komai Kaka,ki yi haƙuri duk abinci ya ida"
Sai ta saki murmushi ta ce "a'a kina da shi,wannan ƙuncin da damuwar da ke ƙumshe a zuciyarki ita nake so ki bani"
Da na ji abin da ta ce sai na ɗan saki murmushi,ita ma ta mayar mini da martani kafin ta ce "ko ke fa! Dubi yadda fuskarki take da kyawu in kina fara'a .Faɗa mini kina sonsa irin sosai ne?"
Ƙuri na yi mata ina kallo,sai na fahimci ita fa wannan ba mutum ba ce kamar kowa.Kujera ta jawo ta zauna da kanta ba tare da na bata damar yin haka ba,sai ta tallabo fuskata da dukkan tafukan hannunta waɗanda suke da datti kafin ta ce "shi so wani abu ne da ba ya ɓoyuwa jikata,ki sani zuciyoyi suna kamu da ƙaunar junansu tun kafin masu mallakarsu su san da haka.Soyayyar mace ba ta ɓoyuwa rauni da ita kamar yadda ita ma ɗin take da rauni,yayin da shi kuma namiji yake da dakiya da ƙarfin halin ɓoye sirrin zuciyarsa sai dai kuma yake da rauni ta ɓangaren saurin bayyanar da kishinsa.Ina baki shawara,ki tsayar da zuciyarki wuri guda amma kuma ki yi abin da zai sa shi ya tunzura har ki raunata wannan ƙarfin nasa da dakiya da izza.A wannan gaɓar zai furta miki kalmar so"
Na kai hannuwana na ɗora kan nata kafin na ce "amma Kaka ban fahimci abin da kike son faɗa mini ba"
Da sauri ta janye hannuwanta kafin ta ce "je ki kawo min ruwa na sha "sai ta soma yin tari,da sauri na tashi na shiga ciki na samu kofi mai kyau na zubo mata ruwa sai dai ina fitowa wayam ban ganta ba.
Na leƙa waje ko inuwarta ban hango ba ballantana mai kama da ita,kuma ba ta isa yin nisa ba.Ni ma rufe gurin na yi na kama hanyar komawa gida.
★ A ɓangaren Maheer kuwa tun bayan da ya je bikin jana'izar Dr David ya kamu da ciwon kai mai tsanani saboda kiɗe-kiɗen manyan ganguna da kuma waƙoƙin kiristoci da ake a wurin.Wannan dalilin yasa ya ji bai iya driving kawai ya ce wa Dr Muhamud ya zo ya sauke shi gida,motarsa ma a can ya bar ta.Tun da suka shiga ciki ya lura kamar Dr Muhamud ya ji haushin yadda suka ƙure juna da ido shi da Haule amma ya basar,har ya kwanta kan kujera sai kuma ya sauko ƙasa don haɗa tea sai kuma ya ci karo da Haulen.
Sai da ya ƙarewa bayanta kallo na wani ɗan daƙiƙu kafin ya shiga ya rungume ta har ya sumbace ta,a duniya a jikin mace yana son ƙugu yana bala'in tayar masa da hankali.Sai kuma yau ne ya lura sosai Queen ɗinsa nada su sosai wannan yasa ya dire hannunsa a can .
Tun da ya ɗanɗanin zaƙin yawunta,ya ji ƙusoshin kansa sun kwance.Yau ne karon farko da ya soma yin kiss,ya so a ce kalaman ƙauna ne ya feso mata amma baƙar aƙidarsa ita ke ƙaran fankama ego ɗinsa wurin cewa bai son Haule kawai dai abokiyar cika aikinsa na duniyar Ruhaniya ce ita.Dakyar ya maida kansa sama,yana zuwa ya zube kan kujera yana jan numfashi.Dr Mahmud kuwa kallo ɗaya ya yi wa Maheer kafin ya fice ransa na masa ƙuna.
Maheer ya bi bayansa da muguwar harara kafin ya danne cikinsa da ke yi masa ciwo.Ya ja dogon tsuki a bayyane yana jin tamkar ya ɗauko Haule ya sauke girman abin da yake ji na shekara da shekaru.
In ya tuna kuma yadda ya ga duk jikinta yayi sanyi liƙis akan sumbata kawai sai ya shiga yi mata dariya yana jin cewa to ina ya gama da romance da kuma yi mata mai kankat? Dariyar shaƙiyanci yayi a fili kuma ya furta " suma za ta yi don daɗi" sai kuma ya yamutsa fuska ya miƙe a dadafe ya shiga toilet yayi wanka.
Bayan ya fito ya buɗe drower yana kallon dutsen sirrinsu wanda ke ɗauke da ɓoyayyen abu a ciki,kuma iya shi da ita ne kawai za su iya tarwatsa dutsen ya buɗe har su ga mene ne a ciki.
Rufewa yayi,ya kuma buɗe wani ɓangare ya ciro kayansa ya shirya cikin jallabiya H color.Bayan ya fesa turare sai yayi kwanciyarsa kan bed,ido ya lumshe yana son lalubo tunanin Haule duk da bai yi nasara ba amma yana jin motsin Yabobo a kusa da ita.Da sauri ya ware idonsa yana mai cewa "Uwa Yabobo a wannan duniyar ? To me ta zo yi? Kar dai a ce ta shaidawa Haule da aurena kanta in shiga uku" sai kuma ya miƙe da mugun sauri ya fito,direba yasa ya tuƙa shi zuwa can gidansu Dr David bayan ya ɗauki motarsa sai ya wuce can rijiyar sirri.
Yana kallon ruwan da ke ciki ya ja ajiyar zuciya kafin ya soma yin formula na kiranta zuwa gare shi.Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba Yabobo ta fito fuskarta ɗauke da murmushi,Maheer ya kafe ta da ido kafin ya ce "na ji kin kai mata ziyara"
"Wace ce ?"
Ya ɗan turo baki gaba ya ce "wannan yarinyar mana"
Uwa Yabobo ta kawar da kai gefe kafin ta ce,"ni ban taɓa zuwa duniyar bil'adama ba akan yara"
Ya saki murmushi mai sauti kafin ya ce "ina nufi Queen H"
"Ita ta faɗa ma na je?"
"A'a ni na gano da kaina"
"Eh haka ne"
"To amma mene ne kika ce mata?" Maheer yayi tambayar cikin sauri ,hakan ya saka Uwa Yabobo juyowa tana kallonsa tana mai cewa "tsoron me kake ji?"
Ya ɗan yamutsa fuska ya ce "ni me zan ji wa tsoro?"
"To mene ne abun damuwa?"
"Kawai ni dai ban so ta sani"
"Tsoronta kake kenan?"
"A'a kin san halinta da rawar kai , wallahi har fyaɗe tana iya yi min muddin ta san sirrin cikar ƙarfin ikonmu ya ta'allaka ne da zama abu ɗaya ni da ita"
Sai da uwa Yabobo ta ci dariya kafin ta ce "kuma fa tsaf za ta iya in dai Queen Haulat ce,amma to kai me yasa ba ka son ku zama abu ɗaya?"
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "dalilan nada yawa Uwa Yabobo ".Da sauri ta ce "bani guda uku"
Ya yi ƙasa da idonsa sannan ya ce "na farko dai har yanzu yarinya ce ita,sannan magana ba ta kwana bakinta shegen surutu ne da ita kamar Aku,a ƙarshe kuma ni dai ba zan iya bayyanar da jikina a gare ta ba"
"Shirmen banza! Babu ƙwaƙwaran dalili ko ɗaya a nan,kawai ka ce shegen taurin kanka ne ba zai bar ka wurin gudanar da abin da ke naƙarƙasar zuciyarka ba ne.Sannan ina mai baka shawara ka yi tattara don in ka cika sanyi hali da yi yuwar a canzawa Queen jarumi ɗan jagora" wani irin kallo yake bin uwa Yabobo da shi yana jin zuciyarsa na zafi,dakyar ya haɗiye yawun takaici "a canza mata wani yayi mata me?"
"Abin da ka kasa yi mata mana"
"Amma uwa Yabobo ba ki ganin ta yi ƙanƙanta,ko murfin shekara ashirin da biyar fa ba ta rufe ba.Kuma na faɗa miki tsorona take,na san ba ta shirya zuwana gare ta ba"
"Yanzu dai sai an jima akwai aikin da zan yi,ka tabbatar kuma ka tsaya tsayin daka har komai ya tafi daidai.Ita kuma Yasmine da ka yi biris ka ƙi kula da ita sai yaushe ne za ka yi mata maganin?"
Ya ja wani dogon numfashi kafin ya ce "to ai mutumniyarki ma ta sake komawa ta jajiɓo uwar Yasmine ɗin.Kin fi kowa sanin kuma macijin ciki ne babbar matsarta,na kashe shi ma bata kariya na cikinta kuma da buƙatar a fasa cikin"
"A'a bai kai ku fasa cikin ba,ka zauna ku tattauna da Queen ita ce za ta sanar da kai yadda za ku yi .Kar a kashe macijin a barsa da ransa don zai yi amfani a gaba" tana gama faɗar haka ta yi ƙasa ta koma can ƙasan rijiya.Da sauri Maheer ya bar wurin tare da zuwa ya shiga motarsa ya nufi can asibiti.
★
Ko da na isa gida na tarar da Lubna ma ta zo,suna zaune suna cin abinci ita da Aliya da kuma anty Bahijja wacce na ga babu wani laifi ta ɗan saki jikinta. Bayan mun gaisa na zauna ni ma na saka hannuna kafin na dubi inda Yasmine ke kwance tana ta bacci abinta,na ce "har yanzu ba ta farka ba? Kun ajiye mata abincin ne?"
Aliya ta ce "kin san fa ita cin abincinta ba wani ba ne,kawai dai shegen macijinta ne ke da matsala dole sai ya sha jini sannan a zauna ƙalau ba"
Shiru na ɗan yi kafin na ce "kar a sake bata shi,kawai ta ci abinci daidai wanda zai ishe ta ita ɗaya"
"Wai kin ga abin da ta yi kuwa?Amma kuma ban san dalilinki na faɗar haka ba" cewar Aliya ,ban sake yin magana ba har muka ida na fita don kawo ruwan sanyi sai na yi kiciɓis da Hajiya wacce dawowarta kenan .
A mutumce na gaishe ta amma ba ta amsa ba ta jefo min tambaya" a ina kika tafi jiya? Wato yawon gantali za ki fara Haule don kin ga na kasa ɗaukar mataki a kanki? "
"Ki yi haƙuri Hajiya " na furta cikin sanyin murya amma tamkar na watsa mata ruwan zafi haka ta soma yi min masifa tana rantse-rantse akan ba za a yi yawon ta zubar ba a gidanta.Su Aliya duk sai suka fito,sai kuma Hajiya ta koma kan anty Bahijja "ita kuma wannan wace ce? A ina kuka jajiɓo ta?"
"Ina wuni Hajiya ? Dama Maheer ne ya ce na zo sai na dinga yi miki aikin tuwo-tuwo" anty Bahijja ta faɗa murya na ɗan rawa. Hajiya ba ta sake cewa komai ba ta yi gaba,yayin da mu kuma muka je muka taya masu aikin gidanta kwaso kayan da ta sayo.
Aliya ta matso dab da ni tana mai rage murya kafin ta ce "ina ga in kuka yi auren sirri ke da Maheer akwai babbar matsala,yo in ciki ya ɓullo jikinki Haule ba ke ba hatta mu muna cikin matsala"
Na dube ta da mamaki na ce "ni kam me zai sa na aure shi? Allah kiyaye min" a nan take kuma abin da yayi min ya faɗo min a rai har sai da na ji wani yanayi ya ratsa ni.
Aliya ta yi murmushi mai sauti kawai ba tare da ta ƙara cewa komai ba,bayan mun gama kwasar kaya muka yi sallah sai Lubna ta ɗebo tafarnuwa muka fara gyarawa a nan cikin ɗakinmu.
Aliya uwar surutu ta ce "Haule ni kam ki ci gaba da bamu labarinki,ya aka yi har kika zo nan gidan Hajiya?"
Na ce "tun ranar da na samu wannan ɓoyayyen sirrin na faɗa muku ban ƙara samun sukunin ruhi ba,duk kuma wata hanya ko alama wacce za ta nunawa iyayenmu maza na san sirrinsu Innarmu ta toshe ta.A kullum cikin yi min turare take sannan tana karanta min wasu abubuwa na cikin littafinta.Sai dai duk da hakan wannan halittar ta ɓoye a ɗakin sirri ba ta bar ni shaƙat ba haka duk dare zan dinga jin tana kirana tana cewa " Haule ki zo zuwa gare ni,Haule ke ce magajiyar wannan gidan " ban ƙara gigin ƙara komawa ba a bisa tsaron Innarmu wacce ta koma yin bacci da ido ɗaya.Ban san cewa ƙin zuwan nan da nake yi babbar illa ba ce sai da ƙuraje suka fara feso min a jiki masu mugun ƙaiƙayi,ba na yin bacci haka ma mutanen gida .Ana ta nema mini magana amma shiru kamar mai cutar kuturta haka abu ke ta yin gaba,ban warke ba kuma wata cutar ta sake bayyana a gare ni ita ce ta rashin yin baccin dare .Ko angaje ban yi ,sai in an kira sallar asubah kawai.Haka nake gadin dare wanda banda abubuwan ban tsoro babu abin da ake nuna min,a wani yammaci ne aka fara yin ruwa kamar da bakin ƙwarya yayin da mutane ke nema mafaka don su ɓuya a daidai wannan lokacin ne Innarmu ta samu zane ta goya ni tare da yafa wani ƙaton bargo wanda ban taɓa ganinsa ba sai ranar.Haka ta fito da mu ,ta yi tafiyar ƙasa mai nisa kafin ta tsaya ta sauke ni sai a lokacin kuma na ga cikin jeji ne ta kawo mu.
Tamkar yadda ake wankan jego haka Innarmu ta yi min wanka da wasu ruwa tana furta wasu harufa,cikin abin da bai fi minti goma ba sai ga dukkan ciwukan jikina sun warke.
Da mamaki na ce "Inna ya aka yi kika yi haka? Duba duk na warke "
"Kar ki sake yin tambaya Haule,ina so ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurare ni.Lokacin barin gida a wurinki yayi,za ki je wani gun ki ci gaba da rayuwa.Zamanki a gida babbar illa ce a gare ki da kuma sauran al'umma,na ɗaukarwa Yayana alƙawarin cewa zan ci gaba da gadin muƙamin nan har zuwa lokacin da zan damƙa shi gare ki,Haule ke ce hasken da zai haskawa duniya wane ne BAƘIN RUHI don haka ki zama jaruma kar ki saka tsoro a tafiyarki" bayan ta gama yin wannan furicin ba ta bani damar yin magana ba ta hura min wata hoda a fuska,ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na ganni a kwance kusan wata makarantar allo.Ban san a ina ne nake ba,wacce ƙasa ce? Shi ma ban sani ba.Haka na tashi zaune ina kallon yadda almajirai ke ta yin karatu,na jima sosai a haka kafin malaminsu ya zo gare ni.
"Baiwar Allah wace ce ke?" ita ce tambayar da ya yi min bayan yayi mini sallama. Na ɗago na dube shi babban malami ne,muna haɗa ido sai na ga yayi murmushi tare da cewa "tashi ki shiga ciki kin ga gidana nan" haka na miƙe na shiga kamar yadda ya ce ɗin,sai dai a bakin ƙofa na tsaya cak ina kallon ikon Allah. Wata mata ce a zaune dirshen kan tabarma tana ciyar da ƙadangare abinci tamkar wani ɗanta.
"Ke lafiya? Wace ce ke?" ta yi min magana cikin ruɓaɓiyar hausarta da dukkan alamu ba bahaushiya ba ce.Ban kai ga amsawa ba malamin ya shigo yana cewa "Agwe ki bata abinci baƙuwarmu ce,ta ɓata ne ba ta san kowa ba"
Ta yamutsa fuska kafin ta yi min alama da hannu,dakyar na cira ƙafata na isa gare ta sai ta nuna min gefenta na zauna sai kuma a lokacin wannan ƙadangaren da na gani a kallon farko na ga ya koma ɗan ƙaramin yaro kyakkyawa da shi kuwa.
Ko da ganin haka sai na fahimci cewa to na ƙara shiga hannun wasu matsafan."Ungo ci gaba da basa abincin kafin na kawo miki ruwa" ta faɗa tare da turo min kwanon abinci,yaron na kalla sai na ga yayi min ƙuri yana kallo.Ƙwayar idonsa sam ba ta yi kama da ta yaro ɗan shekara biyu ba,ta fi kama da ta babban mutum amma haka na daure na ɗebo abinci na kai bakinsa amma sai ya ƙi ci sai dai aukin kallona har sai da na tsargu.
Mamarsa ta dawo ta kawo min ruwa na karɓa na sha,bayan nan ta bani abinci na ci sannan na yi wanka na mayar da kayana.A wuni guda na fahimci Agwe,mace ce mai kirki sannan Kirista ce ita akwai addini da tawakali.Na gano haka ne a bisa labarinta da ta bani cewa tun aurensu da malam take neman haihuwa ba ta samu ba sai shekaru biyun da suka gabata ta samu Jafet shi ma da taimakon shugaban Cocinsu,ni dai saurarenta kawai nake amma ni na san gaskiyar da ba ta sani ba wannan yaro ba mutum ba ne .
A hankali na ɗan juya ɓangaren da yake a shimfiɗe yana bacci,sai na ga yana kallona kamar mai son tantance wani abu ni kuwa sai na mayar da kaina doluwa na shafi kansa na ce "kyakkyawa da shi kuwa anty,kin ga ashe hatta kiristoci ma kuna yin addu'a kenan ta neman biyan buƙata?"
Ta washe baki ta ce "eh sosai gobe in zan tafi in kana so sai mu je tare"
Na ce "zan je mana"
Ni na taya ta yin girkin dare,bayan an gama muka ci sai bayan sallar isha'i kawai malam ya zauna da mu ya binciki karatuna da kuma addinina kafin ya koyar da ni abin da ba a rasa ba.
Da dare yayi sosai duk muka yi shirin kwanciya,idona a rufe suke amma ba bacci nake ba.Ji na yi ana kallona irin kallon ƙurillar nan amma ko da wasa ban buɗe idona ba don kuwa na fi tunanin aljanin yaron nan ne,ai kuwa shi ne.A hankali na ɗaga fatun idona ina satar kallonsa ta ƙasan ido,sai na ga idonsa suna bado haske tamkar na mage ban kula shi ba haka ban nuna na gane wane ne shi ba haka na soma yin tunanin gida har bacci ya ɗauke ni.
Washegari malam ya tashe ni na yi sallar asubah,sai Anty ta bani zanenta na yi ɗaurin ƙirji sai na wanke kayana ko da gari yayi haske kuwa sun bushe na yi wanka na mayar da abina.Bayan mun ci ɗumame sai muka fita zuwa Coci,sosai na yi mamakin ganin yadda Cocin ta cika maƙil da mutane.
Cikin ƙanƙanen lokaci na ƙarewa cocin kallo,komai na cikinta ja ne tun daga kujerun da mutane ke zama har wani dogo capet da ke shimfiɗe haka ma inda Fasto ɗin ke tsaye yana yi musu huɗuba shi ma ja ne,idona na sauka kan wata ƙatuwar Cross sai na ji gabana ya faɗi saboda wani tambari da na gani a tsakiya mai zanen ido.Ina shirin kawar da kai sai na ga idon na ƙyaftawa daidai kuma wannan lokacin ne Fasto ya ce "duk kowa ya lumshe ido za mu fara yin addu'a " haka kowa ya rufe ido,amma ni nawa na bar su a buɗe akwai mutane sosai amma hakan bai hana Fasto sanin cewa akwai wanda bai rufe idon ba sosai na yi mamakin haka da na ji yana cewa "kowa ya rufe ido na ce" amma na ƙi rufewar sai da na gansa a tsaye a gabana tsudum,na zabura ina kallonsa tare da mamakin ta ya aka yi duk ya ƙetare mutane har ya zo gabana? Ba ma wannan ba wurin na da girma sosai in ma zai tawo ai zan ji sawun takunsa ba da sauri na rufe ido.
Addu'o'insa waɗanda ba na komai ba ne sai na tsafi ya soma yi nan wasu suka fara faɗuwa suna ihun iskokai ,a gaban idona ƙatti majiya ƙarfi suke ɗaukar duk wanda ya faɗi suna shigar da shi wani gurin.
Cikin muryarsa ta mayaudara yake cewa "mala'iku za su sauko yanzu ,kowa yayi addu'ar da yake so"muryar Anty Agwe na ji tana addu'ar tana so ɗanta ya fara magana kamar kowanne yaro,a hankali na buɗe ido na kalli Jafet wanda ke goye a bayanta ,shi ma kallona yayi yana wani ƙanƙance ido.Muryar Fasto ta daki kunnena inda yake cewa "akwai waɗanda ba namu ba ne a wurin nan,akwai kura da fatar akuya a cikinmu" yana gama faɗar haka sai ƙamshin wani turare ya cika wurin,yayin da kuma Fasto ya soma zagayen ko ina yana magana cikin wata irin murya wacce ta saukar min da kasala nan take jikina ya ɗau kyarma kafin na farga na zube ƙasa,da sauri ƙattin nan suka zo suka ciciɓe ni suka shigar da ni inda na ga sun kai sauran a can ne na yi arba da wani sabon tashin hankali,na fahimci cewa har yanzu dai tamkar ina cikin komar iyayenmu maza...... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
27
Ɗakin da suka kai ni wani keɓaɓen wuri ne mai kamar matattarar sheɗanu,an yi zane iri-iri na fatale da doddani sannan ga wani abu da suka da farin alli a ƙasa mai kamar da'ira.A cikinsa suka jefa ni suka yi tafiyarsu,da na gwada fita sai na ji tamkar an hura wuta a wajen da'irar da nake ciki dole na zauna babu jimawa kuma shi Fasto ɗin ya shigo da maƙarabansa.Wasu suna waƙar nan ta kiristoci yayin da wata mata kuma ke kwance tana jan ciki tamkar yadda tsutsa ke yi,sai kuma na ji muryar Fasto yana amton sunana "Haule kin jima a wannan duniyar,amma ba ki ga komai ba.Yau esprit da ruhinki za su yi balaguro su zaga duniyarmu " yana gama faɗar haka sai biyu daga cikin maƙarabansa suka zo suka kamo hannuwana,ina son ƙwacewa na gudu amma tamkar wata gawa haka nake a sandare ban iya wani motsi.
Fasto ya matso kusa da ni hannunsa riƙe da wani plate mai cike da jini baƙi ƙirin,sai kuma alƙalami."Wannan gangar jikin da kuma ruhin da ke cikinsa namu ne,a yau za mu ƙaddamar da ke ki san amfanin zuwanki duniya.Za ki yi hidima ga shugaba,kafin ya dawo mamallakinki ya shiga gangar jikinki " yayi magana tare da ɗaukar alƙalamin yana dangwalo wannan baƙin jinin yana mai yi min zane a tsakiyar goshi da kuma hannuna na hagu .Yana gamawa na soma ganin wasu irin baƙaƙen inuwoyi na saukowa tamkar doddani,na yi ƙara sai dai muryata ba ta fita ba.Tuni suka fara ɗalasiman tsafi ta hanyar fasa ƙwai da kuma kunna jan kyandir,tamkar an hasa wuta a cikina haka nake jin duk illahirin jikina ya ɗau zafi,ɗaya daga cikin inuwar da ke faman saukowa ta matso dab da fuskata ta ce " bamu abin da kike da na farin ruhin da ya hana mu ƙarasa aikinmu" tana gama wannan furucin sai na soma kakarin amai tamkar ina son fitar da wani abu,ƙila abin da suke so ne.
Ina cikin wannan hali ne kwatsam sai ga wata tsohuwa ta shigo ɗakin hannunta riƙe da wani tsohon Bible tana mai karanta shi cikin muryata ta tsofi,nan take Fasto ya faɗi ƙasa yana nishin azaba haka ma maƙarabansa.
Ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na ganni a ɗakin tsohuwar nan. "Kin tashi?" ta furta,na jinjina mata kai kawai ita kuma ta ci gaba da cewa "ban san dalilinki na zuwa Cocin BAƘIN RUHI ba alhalin kina ɗauke da baiwar fararen taurari.Amma ki sani da ace ban zo ba da ƙila sun juya alƙiblarki"
Na ce "amma Kaka na ji kina karatun Bible hakan na nufin ke ma Kirista ce? Kuma dama Bible nada muhimmancin haka?"