Bakin ruhi complt by mrs sadauki - Chapter 5
Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 5: Bakin ruhi complt by mrs sadauki Chapter 5. Kiran na ɗaga,bayan mun gaisa ya tambaye ni yana son mu yi magana…
4,418 words
Kiran na ɗaga,bayan mun gaisa ya tambaye ni yana son mu yi magana amma don Allah ba ta waya ba mu haɗu ko da wani restaurant ne.A ranar nan rabon na rabu da alaƙaƙai ne yasa na yarda da gayyatar Dr David,wani abun mamaki kuma shine a restaurant ɗin Hajiya ne muka haɗu a nan ne na fara ganinki Haule haka kawai na ji kin yi min sai kuma na ga kina yawan kallona a duk lokacin da za ki kai abinci a wani teburin da aka buƙata.A tattare da ke na ga wasu abubuwan na daban sai dai ban san ya zan yi na yi miki magana ba,a nan ne kuma hankalina ya rabu biyu na yadda zan yi na samo sperm ɗin Dr David da kuma na mamakin yadda kike yin abu kamar siddabaru.
Dakyar na iya tattaro jarumtar tunkarar Dr David kan cewa ina son sperme ɗinsa saboda an ce yana gyara fuska,bai wani musa min ba don dama ya kira ni izuwa nan ne don bani haƙuri da kuma neman alfarmar mu koma soyayya.Mun yi da shi zai kawo min sperm ɗin zuwa dare,da wannan muka rabu ya sauke ni gida.Duk yadda muka yi da shi na kwashe na shaidawa Zuly ta yi murna sosai har ta kasa ɓoye farin cikinta,sai kuma na yi mamakin haka amma na ɓoye shi har lokacin da Dr David ya zo ya kawo min abin da na buƙata cikin wata ƴar kwalba.
Bayan na karɓa ya jefo min wata tambayar da ta hautsana hanjin cikina,"Lubna kin tabbata a fuskarki za ki shafa shi?" duk da a lokacin na firgita amma haka na mayar da abin tsokana na ce a'a cikin mahaifata zan ɗura shi don na samo baby mai kama da kai,nan yayi dariya muka taɓa ƴar hira kafin ya tafi.
Yana gusawa motar Zuly ta parker na shiga muka lula can gidanta,cike da zumuɗi take cewa "meeting ɗinki na Japan an ɗaga shi,yau za mu je ɗakin sirrin Boss domin gabatar da sacrifice ɗinki na farko" sam ban fahimci abin da take cewa ba,sannan kuma ban tambaya ba.
Yau ma ta cikin madubinta muka bi muka isa a ɗakin taron,abun mamaki kowa ya haɗu har da shi kansa Boss ɗin wanda idonsa ke jifana da kallon sha'awa.Ba a ɓata lokaci ba muka dugunzuma wani ɗaki mai shegen duhu ,babu abu mai haske ko ɗaya in kuka cire wani mirror .
Cikin wata irin busashiyar murya Boss ya kira sunana,hakan yasa na ɗan matsa ba tare da na amsa ba.Hannu ya miƙo min,na san za ku ce ta yaya na ga haka duk da na ce akwai duhu a ɗakin.To abin shine da zarar mutum ya kai wani lavel yana samun wani ido a tsakiyar goshinsa mai gane masa komai da ido normal ba zai gani ba.
Yana karɓar robar sperm ɗin ya buɗe ta,sannan ya dangwalo da yatsansa ya shiga yin rubutu a jikin madubin *BAƘIN RUHI* shi ne abin da ya rubuta nan take wata irin guguwa da iska mai ƙarfi suka cika ɗakin na yi tunanin duk za su yi murna sai dai fa akasin haka ne ya faru saboda kururuwa da suka soma,kafin ƙyaftawar ido wani jan maciji ya bayyana a mirror ɗin yana feshin wuta kafin kuma madubin ya tarwatse wanda turnuƙin fashewarsa ta haifar min da gushewar hankali ko da na farka a kwance na same ni kan shimfiɗa Ummah na yi min fifita.Ina ware idona sosai nan na yi arba da Alhaji wato Maheer,wani irin mugun kallo ne yake watso min yana hararena.
Ummah ta ce "kin farka Lubna?" ban amsa ba sai dai na yunƙura zan tashi sai dai na kasa saboda yadda jikina ke yi min mugun ciwo. "Ki kwanta ki huta" cewar Ummah. Shi kuwa cike da mugunta ya ce "barta za ta iya tashi,ke miƙe "
Maganarsa tamkar umarni ne a gare ni,haka na ji ba zan iya yi masa muso ba na miƙe na tashi zaune duk da kuwa uwar azabar da nake ji.Wani magani ya fiddo cikin aljihu ya miƙo min,"komai za ki ci ki dinga zuba wannan a ciki,in kuma kika kuskure daidai ɗaya rana za ki koma hannun waɗanda kika fito"
A lokacin da na ji Ummah na yi masa godiya sai na fahimci tuni ya shaida mata komai,ban yi mamakin yadda aka yi ya san komai ba don na fahimci yana da power.Sannan a cikin coma ɗin da na shiga haka aka yi min wahayin komai ta yadda aka yi ya tarwatsa komai,ashe lokacin da muke yin magana da Dr David Maheer ya shigo restaurant ɗin kuma ya ji abin da nake cewa.Sannan kuma abin da ba ki sani ba Haule sarai Maheer ya san cewa ke ma ba normal mutum ba ce,kamar yadda na dinga kallon abubuwan da kike na siddabaru to shi ma idonsa suna iya ganin duk abin da kike yi" Lubna na kawowa nan da dogon labarinta da take bamu ni da Aliya sai ta yi shiru,ni kuma numfashi na ja kafin na ce "amma ta ya aka yi ni ban san da cewa shi ma yana da power ba sai yau? "
"Saboda ƙarfinsa ya wuce yadda duk kike tunani,kin ga fa shi ne ya kuɓutar da ni daga komarsu tun lokacin ba su sake waiwayata ba.Haka ita ma Ummah ba ta yi sake kan kula da lamurrana ba kullum cikin yi min addu'o'i take,duk asubah in ta gama sallah kamar wata ƴar baby haka take dafa goshina tana yi min addu'o'i " cewar Lubna.
Na dubi Aliya wacce duk yanayinta ya canza kafin na ce "ya dai?"
"Babu komai! Amma dai a yadda na fahimta ita ma Lubna ta shiga komar BAƘIN RUHI ne kamar yadda na saba ganin gawarwakin waɗanda suka mutu ta silarsa,su ma jini yana fita ta idonsu"
Furucin Aliya ya tuno min da gawar Haidar,murya na ɗan rawa na ce "Lubna bayan an yi wa mahaifinki wanka shin jinin da ya fita ta idonsa ya wanku?"
Ta ce "wallahi ban sani ba saboda lokacin ai na faɗa muku ban cikin hayyacina kuma ko da na farka tuni an kawar da shi"
Na ce "da buƙatar mu samo amsa,babu kuma wanda zai bamu tabbacin haka sai Ummah.In dai hakan ta kasance to tabbas BAƘIN RUHI nada ƙarfi sosai ta yadda ya bazu a duniyar nan to amma wane ne shi?" na yi tambayar da ni da su babu wanda ya san amsarta.....
My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822
🔞Don Allah masu zuwa suce min complet suke so ku yi haƙuri Ni ma banda shi,yanzu nake typing in kina so ki biya na saka ki group.
*BAƘIN RUHI*🧌🐲
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
BONUS na book ɗin *BAƘIN RUHI* mai so ya tura 300 kafin na saki last free page 10 gobe in sha Allah ki tura kai tsaye ta wannan account ɗin 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBABK sai ki turo min shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Da zarar na saki last free page discount ɗin ya ƙare.
Masu sha'awar karanta tsofin Books ɗina ku zo na yi muku discount,ga wacce ta shirya ta tuntuɓe Ni kai tsaye ta WhatsApp +22795045822
09
Dare yayi sosai wannan yasa muka jingine bayar da labarin,duk da na san akwai abubuwan da Lubna ta ɓoye wanda ba ta faɗa ba amma haka na yi shiru na samu wuri na kwanta.Ido na lumshe nan take Maheer ya bayyana cikin tunanina,zaune yake a ɗakinsa ya sha wata doguwar rigar bacci ta maza fara sol da ita.Gabanta a buɗe yake,hakan ya bani damar ganin fafaɗen ƙirjinsa mai ɗauke da suma baƙa silik ta kwanta sai sheƙi take.Duk da ban taɓa saurayi ba,amma gargasar ƙirji na ɗaya da abin da nake fatan samu a wurin mijin aurena hakan yasa na kafe gurin da ido ko ƙyaftawa ban yi.
Har sai da na ji muryarsa yana cewa ,"kin ga dama kin zo" da wani mugun sauri na buɗe idona sai kuma na tashi zaune na dafe saitin zuciyata da take bugawa,sam na kasa gane shin tunaninsa ne na yi? Ko kuwa dai ban sani ba bacci ne ya ɗauke ni sai na soma mafarkinsa? Amma dai tabbas na gansa da idona sai dai irin wannan tunanin bai taɓa zuwar min ba.
Cike da tsoro na ƙara kwanciya na lumshe idona zuciyata na ci gaba da matsanancin bugawa.Wannan karon jinsa na yi dab da ni har muna jin hucin juna kai kace hatta gangar jikinmu na tare da juna ne,nan kuwa iya esprit ne.A hankali na ɗaga idona na kalle shi,yadda yayi wani tsaye ƙiƙam a gabana duk ya kere ni kamar Giwa da ɗan tsako.
"Yanzu kuma wannan mene ne da ka jawo ni cikin tunaninka?" na tambaye shi. Cike da shaƙiyanci yasa hannunsa mai sanyi ya wani matse haɓata tare da ɗago ta ya ce,"ni kike yi wa magana haka? Sa'anki ne ni? Wato ni ne ma na shiga tunaninki? Kin zata ban gane ba? Ke ce kika shigo tunanina,na lura tun da kika zo gidan nan idonki na kaina duk kin bi kin takura ni kin hana ni saƙat,faɗa min wa ya aiko ki?"
Cike da jin haushi na sa dukkan hannuwana na tura ƙirjinsa sai dai ko gezau bai yi ba,shi ma tuni ya hassala sai ya kama hannuna ya murɗe har sai da na saki ƴar ƙara na soma fizge-fizge amma ya ƙi saki na.
"Duk shegen kinibibinki ne ya jawo miki halin da kike ciki amma ko kaɗan ba ki cancanci samu wannan power ba,sam ban ga ma dalilin da yasa ƴar aike ta mallaka miki mahaɗin ƙarfin ikona b..." ban bari ya kai ƙarshen aya ba na gantsara masa cizo a ƙirji da wani mugun sauri ya sake ni tare da ja baya ,daidai nan ni kuma na tashi zaune tare da buɗe idona fayau.
Saitin hannuna na duba inda ya murɗe sai na ga yayi ja sosai tamkar a zahiri ne ya riƙe ni ɗin,ƙin komawa na yi na kwanta sai na ci gaba da zama tsakiyar su Lubna da tuni sun yi bacci.
Ina nan zaune na ji handle na motsi ,kafin kuma ƙofar ta buɗe kanta ƙiiiii sai dai ban ga kowa wanda ya shigo ba.Wani irin tsoro ne ya kama ni ,sai nake ganin kamar Maheer ɗin ne zai shigo a zahiri.
"Haule!" na ji muryar da har na koma ga Allah ba zan taɓa mantawa da ita ba ta kira sunana cikin wani irin yanayi. Na soma waige-waige kafin na ce "Husseina? Husseina ke ce? " ba ta bani amsa ba,sai jin wani abu na yi cikin iska ya kama hannuna yana jana sai kawai na sauko daga shimfiɗar na soma take mata baya duk da kuwa idona bai ganinta.
Da muka ratso falo haka ƙofarsa ita ma ta buɗe kanta,haka ma ta ƙofar gida. Muna fitowa sai Husseina ta bayyana a gare ni,tana sanye cikin farin likafaninta har izuwa yanzu kuma kukan jinin take.
Kan dakali ta ja ni muka zauna kafin ta ce "Haule sai yaushe za ki kuɓutar da mu daga cikin ƙangin da muke ? Har yanzu ba ki samo mahaɗin sirrin tarwatsa BAƘIN RUHI ba?"
Jikina banda rawa babu abin da yake yi,na ce "ta ya aka yi kika zo nan? Kuma me yasa kika fito da ni waje? Ai sai ki yi min magana a can ɗakinmu"
Ta ce "in muna cikin gidan nan idonki ba za su taɓa gani ba Haule,amma na tambaye ki wane ne kike so har haka wanda ya mantar da ke dalilin zuwanki ƙasar nan?"
"So kuma? A'a ni ban son kowa" ban ida rufe bakina ba Husseina ta ɓace ɓat,cike da mamakin ta ya za ta tafi ba ta yi min sallama ba na miƙe da niyyar shiga gida sai dai kuma na tsaya cak sakamakon ganin mutum tsaye a gabana fuskar nan tamau fiye da kullum.Wani irin mugun tsoronsa da shakkarsa ne suka yi min dirar mikiya musamman da na gansa da kayan jikin nan irin na tunanina.
"Da wa kike magana?" ya jefo min tambayar cikin tsawa kamar wani ubana.
Mayafin jarumta na aro na yafawa kaina na ce "da kai mana"
Ya waro ido kafin ya ce "ke kar ki raina min hankali da ni kuma?"
"Eh to wa ka gani a nan bayan mu biyu?"
"Me kika fito yi to?"
"Abin da ka fito yi" na basa amsa kai tsaye tare da yin gaba sai dai ƙofar a rufe take ruf.Na juyo na dube shi,sai na ga yana wani miskilin murmushi kafin ya ce "ina ce dai fatalwa ce ta fito da ke waje? To ki ce ta mayar da ke in tana da izzar zama a inda nake" yana gama faɗar haka sai ya zo yana tsayuwa ƙofar ta buɗe kanta na yi wuf zan shige amma tuni ta rufe shi kuma ya shiga ciki.
Tsoro ne ya kama ni,cikin magiya na ce "don Allah Alhaji ka buɗe min "
Banza yayi da ni duk da kuwa da ina jin alamun tsayuwarsa bai tafi ba.Hadari ne ya soma haɗa kansa haɗi da tsawa da walƙiya,nan tsorona ya ninku don kuwa duk jarumtata ban son ruwan sama su dake ni.
"Ki faɗa min da wa kike magana sai na buɗe miki " na tsinkayo muryarsa.
Cikin kukan da ya fara zuwar min na ce "ka buɗe min na yi ma alƙawari zan sanar da kai" ai kuwa ya buɗe ƙofar ina shiga na baza a guje na nufi can ƙofar da za ta sada ni da babban falo.
Cak na tsaya ina waro ido saboda wani jaririn maciji da ya sarkaye handle ɗin ƙofa,ina juyawa kuma sai na hangi Maheer yana takowa izuwa inda nake.Timmm na ji ƙarar faɗowar macijin kafin ya fara yin silululu yana tawowa,a mugun firgice na yi baya tare da rugawa na tarbo Maheer ɗin na koma bayansa tare da ƙanƙanme shi ina kuka ashe gudun gara na yi na faɗa gidan zanzaro shine mamallakin macijin.
"Sahut!" shine furucin da yayi kafin macijin yayi tsalle ya ɗale kafaɗarsa hakan ya baiwa bindinsa bugun fuskata nan take na yi luuu zan faɗi da sauri ya juyo tare da taro ni sai dai muna haɗa ido da macijin igiyar saita numfashina ta katse ban ƙara sanin abin da ke faruwa ba sai da na ji muryar Hajiya a kaina tana cewa "ka ƙi faɗin abin da ya same ta,sannan ma wai me ya kawo ta ɗakinka? Maheer me ka yi wa ƴar mutane?"
Wani irin sarawa kaina yayi jin wani batu wai ɗakin Maheer ,ban shirya ba na buɗe idona tarau ai kuwa a ɗakin nasa nake kwance kan bed ɗinsa abin da ya fi ɗaga min hankali bai fi yadda na ji duk ƙamshin jikinsa ya dabaibaye ni ba.
Muna haɗa ido da Hajiya ta yi saurin matsowa "Haule me kike yi ɗakin Alhaji?"
Shiru na yi don kuwa sam na kasa tuna komai da ya faru ciki kuwa har da zuwan Husseina,abin da na sani dai shi ne ina kwance a ɗakinmu Lubna ta gama bamu labari.
Maheer ɗin na kalla wanda shi ma ni yake kallo da idonsa da suka kaɗa suka yi ja kamar tsohon maye. Hajiya ta mangare ni cike da masifa ta ce "don ubanki ba za ki faɗa min abin da kika zo yi ɗakinsa ba?"
Shaaa hawaye suka fara yi min zuba,don sai yanzu ma ne nake ganin illar wanzuwata a nan uwa uba kuma ni kaina ban san ta ya aka yi na tsinci kaina a nan ɗin ba.
A karo na biyu na juya na dubi Maheer,Hajiya ta buɗe baki da niyyar yin wata masifar iya sunana kawai ta furta Maheer yayi wata irin busa mai ratsa dodon kunne sai ta yi shiru tana mai cewa "In Haule ta gama gyara maka ɗakin ta je ta shirya don Allah kafin su Lubna su gama saka kaya a mota" sai kuma ta fice.
Ya juyar da kai gefe ya ce "ki tashi ki koma ɓangarenku"
"Amma Alhaji me ya kawo ni nan?" na yi tambayar wasu sabbin hawaye na ƙara zubo min. "Dalla Malama saukar min daga gado,ban sani ba ki je ki tambayi fatalwar da ta kawo miki ziyara" ya faɗa a hassale.
"Fatalwa kuma?" na yi tambayar,ya zo da ƙarfi ya wani fizgo ni na faɗo daga gadon amma sai na yi saurin miƙewa ina jin tsanarsa na ƙara ninkuwa a raina.Idona har wani rufewa suke na nufi ƙofar fita,da na ratsa falonsa ne idona ya sauka da duwatsun awarwarona nan ma mamaki na yi,na duƙa zan kwashe su amma tamkar yadda iska ke ɗaga leda haka duk suka tashi sama suka yi bayana,sai na juya nan na ga ashe shi ne yayi amfani da siddabarunsa ya janye su.
Hannuna na duba na ga yayi ja alamun an yi wa wurin mugun riƙo,ban tanka shi ba na fita.Ina fara taka step na ga Lubna a tsaye tana kallon benen wanda yake ɓangaren Maheer ne,a cikin idonta nake hango wasu abubuwa da suka haɗa da zargi da kuma mugun kishi amma ban kula ta ba na wuce part ɗinmu.
Sai da zan shiga toilet ne na lura doguwar rigar baccinsa a jikina,na kwance ɗaurin na jefar da rigar amma abin mamaki sai ta ƙi taɓo ƙasa.
Ban san lokacin da na furta "matsafi kawai" sai kuma na ɗauki rigar na ajiye ta cikin jakar kayana.Bayan na shiga toilet na cire kayan jikina,ina wanka amma ƙamshinsa ne ke tashi.Bayan na gama wanka na zo na gabatar da sallar asubah wacce ta wuce ni don tuni ƙarfe bakwai ta buga.
A gaggauce na kimtsa cikin kaya masu kyau sannan na ɗauki rigar da nake ɗorawa a sama mai sunan Hajiya da kuma restaurant ɗinta.
Ko da na fito tuni an jera komai a mota,cike da ladabi na gaishe da Hajiya .Yadda na ga Lubna na kauce min yasa ban takura ta ba akan sai mun yi magana,a yau tare da Aliya za mu je a nisa umarnin Hajiya hakan yasa muka shiga mota muka wuce can.
Bayan an gama jera komai a wurinsa sai kuma na fito nan inda ke teburan cin abinci na ƙara gyarawa,babu jimawa kuwa mutane suka fara zuwa Aliya ta dinga taya ni aikin har muka samu ƙafa ta ɗan tsana sai na zuba abincin da za mu ci,sai kuma a lokacin na dube ta da kyau na ce "Aliya don Allah me ya faru a jiya a gidan Hajiya na kasa tuna komai,kawai dai na tashi na tsinci kaina a ɗakin Alhaji "
Dama tun tuni na lura ita ma da magana a bakinta,kawai dai ta yi shiru ne. Aliya ta ce "to mu dai mun tashi ba mu gan ki ba,shine Anty Lubna ta je ta sanar da Hajiya ita kuma tana shiga ɗakin Maheer don sanar da shi ta tarar da ke a gadonsa kina bacci sai ta yi kururuwa duk muka haura sama kafin kuma mu iya cewa wani abu shi Alhajin ya fito daga wanka dole muka fita waje saboda mugun kallon da watso mana.Amma ni ma ban san me ya faru ba,na dai ji Anty Lubna na cewa kin ci amanarta kin je ɗakin Alhaji alhalin kin san tana sonsa,kuma wai don kawai ta yarda da ke ne shi yasa jiya ta bamu labarin cewa sperm ɗinsa ne ta kai a madadin na Dr David "
Kaina ne na ji yayi wata irin sarawa,ɓacin rai ya ƙara dirar min.Tsakanin jin sperm ɗin Maheer ne Lubna ta yi amfani da shi,da kuma jin zargin da take min sai na rasa wane ne ya fi yi min ciwo.
Abincin na ji ya fita raina,na miƙe na wanke hannuna.Kuka nake son yi don samu salamar zuci sai dai ina fitowa idona yayi tozali da wata mai ciki tana aman jini duk ya ɓata teburin da ke gaban kujerar da take zaune,hankali tashe na nufe ta sai dai tana ɗago idonta na tsaya cak sakamakon abin da ya gigita ji da ganina.....
My book is only 500 amma na yi discount daga yanzu zuwa kafin na saki page 10 ta ƙarshen free.ki tura 300 ta wannan account 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBABK sai ki turo min da shaida biya +22795045822
🔞don Allah kawai ki saka 300 ɗin ki bani receip ba sai mun tsaya gaishe-gaishe ba🙈 Wacce ba ta shirya ba don Allah kar ta yi min magana
*BAƘIN RUHI*🧌🐲
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
Last free page 10
Fuskarta ta yi wani irin ja kamar za ta tsage jini ya zubo,ga idonta da suke baƙi ƙirin sam babu hasken nan.Bakinta kuma jini ne shaɓe-shaɓe yana mai ci gaba da ɓulɓulo mata.A kallon tsanaken da na yi mata duk ta yi gudu ba za ta haura shekara ashirin da biyar ba,sam kasa cira ƙafata na yi daga inda nake sai ita ce ta yunƙura ta taso ta zo tare da zubewa gabana.Yatsun hannunta na taɓa ƙafata na ji wani irin yanayi ya ratsa ni,yanayi ne wanda na taɓa shiga irinsa lokacin baya shi ma ba zan taɓa mata wannan mummunar ranar ba.
Yawun bakina ne na ji sun fara taruwa da kansu kafin su soma ɗiga suna sauka kanta tamkar ana zubar da ruwan pampo ko kuma ana yayyafi.Zafin hucinta da fitar numfashinta shi ya cika wurin tamkar wacce ake zarar ranta,ƙila shi ya jawo hankalin Aliya ta fito daga can ɓangaren ta zo nan.
"Ƙwayar cutar BAƘIN RUHI,Haule ki ja baya mana contact da ke yana iya haifar da tsayawar numfashinta" Aliya ta faɗa tana mai jawo ni baya,sai a lokacin na ji wani irin raɗaɗi a ƙafata daidai wurin da ta ɗora yatsun hannunta da na kai duba wurin sai na ga tamkar an zuba min acid ne tuni ya wani kumburo ga wata uwar azaba da nake ji.
Na yi baya na samu kujera na zauna,yayin da Aliya kuma ta soma juya hannunta mai ɗauke da ƙarfin iko na power nan take ya kawo haske tare da bayyanar da wani dunƙulalen haske sai ta cillawa wannan mai cikin shi sai ya zagaye ta sai a lokacin ta nufo ni ta tsuguna ta kamo ƙafata.
Hankalinta na ga duk ya tashi,ni kuma na ce "kar ki damu zan warke hakan ya taɓa faruwa da ni ai.Amma me yasa kika jefa mata wannan hasken?"
"Ɗaure ta ne na yi ta yadda ba za ta iya motsawa ba,haka shi ma dafin jikinta zai tsaya da aiki don yana dab da raba ta da rayuwarta.Yanzu dai bari na naɗe miki ƙafarki,sai mu tattauna yadda za a warkar da wannan baiwar Allah "
Wani tissu ta samu ta ɗaure min ƙafa,na tashi tsaye kan ƙafafuna ina kallon mai cikin wacce ta zama kamar gumki ta kasa motsi.
"Mene ne ke damunta Aliya?"
"Ya za a yi mu samo maganin cutarta ita ce tambayar da ya dace ki yi Haule,kar ki bari kuskuren da kika yi baya ya sake maimatuwa " ina jin furucin da Aliya ta yi sai na yi saurin dubanta,ta jinjina kai kafin ta ce "na san antynki ai,kar kuma ki tambaye ni ta yaya yanzu mafita za mu nemo kuma ke ce za ki jagoranci tafiyar"
Na ja wani gwabron numfashi kafin na ce,"dole sai na samu labarin mafarin abin da ya haifar mata da wannan cutar"
Shiru Aliya ta yi kafin ta ce "in haka ne muna da buƙatar madubi ko da ɗan guntu ne"
Ban kai ga yin magana ba aka shigo,Lubna ce da sauri na nufe ta sanin kullum tana yawo da madubi a jaka.
"Yawwa don Allah ki bamu aron madubinki" na faɗa .
Inda mai cikin take a durƙushe ta duba kafin ta zuge zip ɗin jakarta ta miƙo min,sai na je kusan Aliya na tambaye ta "ya za a yi yanzu?"
"Ki je saitin idonta ki haska madubin za ta yi magana sai mu ji" cewar Aliya . Dukka mu ukun muka yi tsaye,suka saka ni a tsakiya yayin da na daidaita madubin ita kuma Aliya ta yi amfani do powerta ta ɗago kanta sai a lokacin na yi mata magana "Wace ce ke? Mene ne dalilin shigarki wannan halin?"
"Sunana Meelat,ƴa ga masu matsakaicin hali,ba mu da kuɗi amma muna da rufin asiri.Na yi karatuna a makarantun gwamnati har Allah yasa na kai matakin University,ina shekara ta biyu yanzu haka.Tun zuwana can na ga yadda rayuwar jami'a take yadda ake challenge ɗin sutura da kuma wayoyi.To dama tun can farko ina sha'awar rayuwar luxery,ina da babban burin shiga mota ,zuwa gidajen cin abinci na manyan mutane da sauransu.Kwatsam wata rana na fito daga jami'a zan je wurin gyaran gashi wata rantsatsar mota ta parker a gabana,a hankali ya sauke madubin motarsa wanda yake baƙi ƙirin ɗin nan.Wani babban mutum ne na gani cikin shiga ta alfarma,fari ne shi tasss mai kyau mai gayu wannan yasa ban wani ja aji ba da ya nemi ya rage min hanya.Sam ban yi duba da ya haife ni ba ko kuma kusan yin jika da ni ba,abin da ke gabana kawai kuɗi.Shi ya biya kuɗin da aka gyara min gashi da aka gama min kuma na kira shi ya zo ya ɗauke ni kamar yadda ya buƙata ya bani lambar wayarsa.Kafin ya mayar da ni can jami'a sai da yayi min shopping kuma ya faɗa min ƙudirinsa na sona yake,nan fa muka fara soyayya ko sau ɗaya bai taɓa kai hannunsa jikina ba tsawon watanni uku muna tare kuma komai nake so yana yi min.Ni da ƙawayena mun mayar da shi atm ɗinmu,a takaice dai sai da muka kwashe wata biyar kafin ya gayyace ni gidansa ya ce yana yin birthday na zo mu yanka cake sai na koma sannan kuma sai na duba gidan in yayi min nan zai ajiye ni in mun yi aure .Haka na je can gidan nasa mai kamar aljannar duniya inda ake parker motoci ma kawai abin kallo sannan akwai motoci iri-,kamar baƙauya haka na yi ta kallon har muka wuce can falonsa ashe ban ga komai ba don cikin ya fi haɗuwa.Ya nuna min kujera ya ce na zauna zai yi sallah ya dawo.Duk da a lokacin bai wuce ƙarfe biyar na yamma ba amma ban tambaye shi sallar mece ce zai yi ba kawai abin da na ɗauka mutum ne mai addini.