Batuol mamman complete novel - Chapter 14
Batuol mamman complete novel Chapter 14: Batuol mamman complete novel Chapter 14. "Inda na aike kin har wani nisa ne dashi da zaki fara yi min felekenki na…
3,353 words
"Inda na aike kin har wani nisa ne dashi da zaki fara yi min felekenki na tsiya. Ko kuwa nace kije ki zauna ne?"
Zumburo baki tayi "Ummi wanka zata yi idan na gama shanya. Zaki kai mata ruwan ki ajiye mata soso da komai a kusa da ita inji miki aiken?"
Mairama tana daki ta jiyo su ta rinka shafa bango har ta fito.
"Ke!" Tace da tsawa
Radhiya ta juyo tana jira taji Mairama ta umarceta da zuwa kantin ta fada mata kai tsaye ba zuwa zata yi ba. Tunda mahaifiyarta ta makance ta kara hankali da bambance su waye masu kaunarsu da gaskiya. Malamijo ya gina gidansa da turbar nafsi nafsi kowa ta kansa yake yi. Babu wani jinkai na azo a gani saboda rashin wadata su da abubuwan da ya dace. Idan ka cire Yadikko babu wadda take leka Mairama balle ace mata yaya jiki. Dukkansu take kallo tana jin kanta daidai dasu. A duniya bata da sama da Umminta sai Emzee. Shi kuma haushinsa take ji saboda rashin magana. Gabadayansa bashi da walwala sosai yaron saboda tsangwama musamman daga Salame kafin ta bar gidan.
"Ki karba kije ki siyo mata ko ma meye idan kin dawo sai nayi wankan"
Radhiya yarinya 'yar kimanin shekara goma sha daya wadda ta gado zuciya ta mahaifiyarta, barkwanci da jarumtar mahaifinta da kuma jinkai da tausayi nasu su biyu ta kekashe idanu "Ummi ni bazani ba idan na tafi ma zubar da kudin zanyi a kwata ko na sayi danmalelen gidan Fadi. Haka kawai yau babu makaranta kowa yana nan taki aikensu sai ni saboda bata damu dake ba" ta kare maganar muryarta da alamun zata yi kuka.
Mairama ta daga hannu daga inda take tsaye kamar za ta dake ta "kizo ki karba kafin ranki ya baci"
Juya keya tayi ta mika hannu ta baya tana jira Binta ta ajiye mata kudin harda wani kada jiki. Emzee ne yazo ya karbe "ni zanje me za'a siyo miki?"
Binta ta warce kudin "bazaka je ba din, wannan fitsararriyar nake so inga uban da ya tsaya mata a cikin gidan nan. Har ni kike juyawa keya saboda baki da kunya"
Mairama daurewa kawai take yi saboda rashin ido. Itama ta sani an tsangwami 'ya'yanta an hanasu rawar gaban hantsi saboda an ga tana zaune. Amaren Malamijo Hanne da Binta sunfi kowa kaudi da takura musu. Kuncin zuciyarta ne ya taso ta tuna mijinta. Da yana raye waye duk gidan nan ya isa ya taka su? Yadda kowane uba ke kaunar 'ya'yan shima tasan zai so nasa kuma ya kyautata musu rayuwa.
"Karami janyo min hannun yayarka"
Da kanta ta karaso gaban Mairama ta kama hannunta don ta nuna mata ta iso. Hannunta ta shimfide mata a gadon baya, dukan ya shigeta amma ta dake. Mairama kanta ciwo take ji yana addabar zuciyarta "in ce kije aiken ki ce bazaki ba saboda ban isa ba? Ko saboda bani da ido sai yadda..."
Zubewa tayi a kasa tasa kuka "Ummi kiyi hakuri don Allah zanje."
Kudin ta karba daga hannun Emzee tana cewa ya mayar da Ummi daki kafin ta dawo. Rai a bace taje ta siyo yeast din naira hamsin maimakon na ashirin da aka aiketa. Da ta dawo daga bakin kofa ta tsaya ta zura hannu
"Gashi"
"Shigo ki bani" Binta tace da gadara tana fadawa yayarta "kinga fa irin jarabar da muke fama da ita. Uwa makauniya 'ya'ya marasa da'a"
"Mu ba jaraba bane" Radhiya ta maida mata da tsiwa.
Bintu bata bata lokaci ba ta kai mata lafiyayyen mari.
"Uwarki makauniyar nan ma bata isa ba wallahi"
Tana kuka baki bai mutu ba "ba dai uwata ba"
Ran Binta ya kara baci "sai ta wa?"
"Wanda ya tsargu dashi nake" Radhiya ta amsa kai tsaye. Kafin Binta ta ankara ta fice daga dakin. Da sauri ta kamo Radhiya a tsakar gidan tana shirin shiga dakinsu.
Mairama tana jinsu ta yi salati ta sake tashi "me kika sake yi kuma?"
Binta ke dukan Radhiya da zagi amma a hakan cewa take ba dai tata uwar ba. Hajjo ta taho kwatar Radhiya Binta ta sake tunzura ta daga hannu zata sake kai mata duka ga Mairama har ta soma hawaye suka ji sallama.
Amsa sallamar bakuwar suka yi Binta bata kula ba ta kuma daga hannu taji matar da ta shigo tace tayi hakuri kada ta sake dukanta yara sai da rarrashi.
Idanu a soye don itama Binta ba kunyar gareta ba tace "yau ko uban da ya haifi uwarta ne wallahi bai isa ya hanani dukanta ba"
Malamijo wanda motocin da ya gani a kofar gidansa suka saka shi tasowa daga majalisar da yake ko kallon mutanen wajen baiyi ba tunda ya ga daya ta shiga gidansa. Ya shigo kenan ya ji me Binta tace ya kuwa murtuke fuska.
"Ahhh lallai yarinya kwananki a gidana ne ya kare shiyasa kike zagina. To shiga ki kwaso tsiyarki kizo ki wuce na sakeki saki biyu"
Innawuro ta kalli Ali tana jin wani bacin rai. Wato duk tsayin shekarun nan yana nan da bakin halinsa na sakin mata. Ta sani wadda ya saka din tayi laifi amma a bainar jama'a haka ya dankara mata saki.
Shi kuwa ko a jikinsa sai ma binta da yayi da kallo yana son tuna a ina ya santa. Matan gidan da yara hankali ya koma wurin Binta da tayi dakinta tana kuka basu kula da Radhiya da take zaune a kasa ba ko bakuwar da take tsaye. Yadikko har kullum ita ce mai hankalin kuma bata gida a lokacin.
Mairama ta duka tana mika hannu neman Radhiya da ta tabbatar tana wurin tana kuka.
Cikin kuka da ta gaji da laluben tace "ina kike ne?"
Muryarta kawai Innawuro taji ta saki baki tana kallonta. Babu tantama wannan ce Mairama diyar Mairo don banda kama ta fuska hatta muryarsu tayi shige sosai.
Kafadar Radhiyan tayi sa'ar dafawa ita kuma haushin aiken tun farko ta janye jikinta tana saka kuka mai sautin da bata yi ba a gaban wadda ta daketa.
"Ba ke kika ce sai naje mata aike ba"
"Allah Ya baki hakuri to tashi muje daki"
Mairama ta mikar da Radhiya a daidai lokacin da Innawuro tace "Mairama?"
Malamijo kuma yace "Innawuro?"
Mairama ta juya duk da bata ganinta ita kuma ta juya tana kallon Malamijo ashe tun dazu yana tsaye. Hankalinta duk yayi kan Mairama tace "muna da yawa sauran suna waje. Na shigo ne sanar da zuwan namu"
Yawun bakinsa ne ya kafe, lebbansa suka bushe sai harshe yake ta fitarwa yana lashesu. Duka motocin nan bus uku da canta daya 'yan uwan Mairo ne? Ya sani da kansa ya taba nemansu saboda tausayin Mairama. Amma tuni ya watsar musamman yanzu da rayuwarta take cikin garari.
Innawuro ta dawo dashi cikin hayyacinsa da yaji tana cewa Emzee ya fita ya cewa bakin waje su shigo. Yaron ya tafi yin abinda ta saka shi ta dawo da kallonta ga Radhiya da Mairama da suke tsaye kawai a wurin.
Gani tayi har yanzu Malamijo yaki magana ta cewa Mairama "muje dakinki kinji 'yata"
Mamaki ne fal cikinta bata san ko su waye ba.
"Ke muje daki" ta ce da Radhiya
Hannunta cikin na Radhiya suka shiga dakin da komai ya kare masa yanzu sai katifa da shirgin kayansu. Rage tsayi Mairama tayi daidai kunnen Radhiya "ina bakuwar take? Kin taba ganinta?"
Innawuro tana kusa dasu kuma taji tambayoyin da tayi mata. Radhiya sai ta dago kai tayi mata murmushi tana dan jin kunya. Mairama ta matsa mata hannu
"Ki bani amsa mana, idan rigima kika sake kwaso min zaneki zanyi wannan karon"
Hayaniya ce ta cika tsakar gidan. Maza ne matasa da magidanta harda dattijai haka ma mata suka rinka tururuwar shigowa. Malamijo yayi tsamo dashi yana kallonsu zuciyarsa ta cika da firgici da ya ga cikin matasan harda masu sanduna. Sandarsu ce ta fulani da ado baya cika sai da ita, amma da yake ba gaskiya gareshi ba sai ya manta da wannan al'adar ya luluka tunanin ko dai duka zasu yi masa. Fulatanci suke ziryan baka jin komai sai sunan Mairama. To shima dai yaren gidansa kenan sai dai suna taba Hausa sosai.
Gaban Radhiya sai da ya fadi da ta hangosu q ta tabota "Ummi sun kara yawa wallahi harda sanduna."
A kidime tace "dan gidan wa kika tabo kuma?"
Harda dan guntun hawayenta na tsoro tace "ni da bana fita wa zan taba?"
"Mairama kwantar da hankalinki muje wajen don nan bazai daukemu ba. Ni da su duka dangin Mairo ne mahaifiyarki"
"Me? Da gaske?" Matsawa tayi daga jikin Radhiya hannuwanta suna neman kofa da sauri zata fita.
Innawuro jiki ya kama rawa ganin da yadda Mairama ta fita. Radhiya ta kalla hawaye suna wanke fuskarta.
"Bata gani ne?"
Radhiya tabi bayan Mairama don ta karasa da ita gabansu tana cewa "eh"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta iya fada tana kuka har wajen suna jin sautinta.
Duka idanunsu sun koma kan Mairama tana kuka take tambayar Radhiya da ta rike mata hannu su nawa ne?
Baffa Gide kamar yadda 'ya'yan 'yan uwa suke kiransa ji yayi kamar iska zata daga shi don tashin hankali da yaji me takw cewa kuma tamkar ya ga Mairo haka kamanin Mairama suke da na 'yar uwarta. Kyaunta ne yasa Malamijo zabarta da biyan bashi duk da a lokacin Innawuro ta girme mata kuma itama bata yi aure ba.
Tsakar gidan kamar gidan kallo ya koma. Ga dangin mahaifiyar Mairama ga ahalin gidan Malamijo kacokan.
Shi Baffa Habubakari kuka yake ma saboda rauninsa yafi na dan uwansa. 'Ya'yansu jiki yayi sanyi. Basu san Mairo ba don manyan ma suna kanana komai ya faru amma sun san wannan makauniyar da ta nufosu jininsu ce. Ga dai idanu a bude amma basa ganin komai.
Sai da suka zo tsakiya Radhiya taja hannunta don su gaishesu tunda ta ga akwai manya "ummi mu gaishesu"
Emzee sai ya baro gefe shima ya dawo ya durkusa tare da Umminsa da Addarsa.
"Ina wuninku, yaya hanya....Allah sarki ashe baku manta dani ba" shine abinda Mairama take cewa tana ta waige hagu da dama saboda rashin sanin a ina suke.
Su Radhiya ma gaishe su suka yi bakin Mairama kamar gonar auduga duk da bata san mutum nawa bane. Ganinsu su ukun nan ya ishi bawa tausayi. Ga uwa mai cike da kuruciya amma makauniya mai marayu biyu a gabanta. Ga kuma 'ya'yanta tamkar zakuna suna gadin farincikinsu, jigon rayuwarsu.
Sautin kuka Mairama ta fara ji daga yawancin matan da suke wurin ta rinka murmushi tana jiran taji wani cikinsu ya tabata taji dumin uwa. Kamar Innawuro ta sani ta durkusa a gabanta ta rungumeta suna sakin kuka a tare.
Ardo Barkindo ya kalli Malamijo ya fito a tsolon rakensa yace "a bamu wuri mu zauna ko"
Sai kuma ya farga ya dawo daga duniyar tunani "kai, kai ina kuke ne, ga baki a shimfada musu tabarmi daga jikin bangon can yafi inuwa."
Tabarmin aka kawo suka zazzauna ya sake dubansu "wace mai girki ne a kawo musu abinci"
Hajjo sarkin bakar magana ta tabe baki "Binta ce kuma yanzu ka dankara mata saki ko a kirawo ta ne?"
Kunya tamkar wanda aka watsawa ruwan kankara haka Malamijo yaji ya muzanta a gaban mutanen da ya taba wulakantawa yau suka taru suka yi masa kwarjini.
Allah Ya taimake shi Yadikko ta dawo yace "Uhmm, uhmmm....Yadikko fito da kwanuka aje gidan Tsahare ayi musu hadin wake da shinkafa amma da miya za'a siyo da salak. Idan akwai taliya 'yar gwamnati duka ta bada saboda ya ishesu. Sannan tasa nama a wadace do Allah"
Yau wace rana Malamijo zaiyi abin kai. Ya zura hannu zai zaro kudi yaji hankalinsa ya tashi...mutanen nan fa da yawa, anya ba duka rugarsu Gide ya kwaso ba?
Ardo ya dakatar dashi don bai manta bayanan da yaji game da Malamijo ba.
"Kaga Malam Ali ba zama zamuyi ba a kan hanya muke. Ka zauna muyi magana"
A tsorace ya zauna daga gefen Baffa Gide don kallon da yake masa kamar zai wafto shi ya shiga dukansa ne. Bangaren matan kuwa Mairama sai dai taji wannan ta rike mata hannu ko an shafa bayanta suna fadin sunayensu.
Da addua ga marigayiya Mairo Ardo ya fara bude zaman nasu sannan ya ari bakin duka dangin nasu ya baiwa Mairama hakuri akan zumunci da suka yi sakaci dashi. Daga karshe ya gabatar da bukatarsu da cewa a yau dinnan ba gobe ba suke son daukarta da 'ya'yanta zasu koma da ita wurinsu.
"Don Allah da gaske?" Mairama ta sami kanta da fada cike da farinciki. Bata sansu ba kuma bata san halayensu ba amma ko don samun nutsuwarta tana so ace gata da dangin mahaifiyarta.
Matar Baffa Habubakari tace mata "Allah Yasa ki yarda ki bimu"
Ita kuwa me zai hanata yarda idan ba rashin sanin ciwon kai ba. Ardo ya umarci yaran nasu maza da su je su shigo da kayan da suka zo dasu. Malamijo ya baza ido ya ga wane shirgin suka kawo sai kukan tumaki ya ratsa kunnensa.
Raguna hudu ne da katoto kuma kosasshen sa guda daya. Kwanduna manya manya guda biyu cike da kwan zabi, buhun shinkafa daya 'yar gwamnati mai doki sai 'yar hausa daya da kuma buhun gero shima biyu.
"Tun daga haihuwar Mairama har aurenta, haihuwar jikokinmu da rasuwar mijinta da muka sami labari babu wani abu daya da muka halarta balle mu bada gudunmawa a matsayin iyayenta. Mal Ali ga wannan kayan, ba wai sakayya bace sai dai ihsani ne daga garemu kuma muna godiya a madadin marigayiya Mairo na kula da marainiyar Allah da kayi" Baffa Gide ya ce sauran suna gyada kai.
Innawuro ta riko hannun Emzee ya zauna a gefenta "ba rabaka zamuyi da ita ba. Mairama har abada 'yarka ce. Muna so ne dai ta bimu ta sanmu muma mu santa"
Yake Malamijo yake ya rasa dalilin da yasa suka yi masa kwarjini "bama zan hanaku tafiya da ita ba"
Kasa magana Malamijo yayi sai tarin kunya kamar ya tona rami ya binne kansa. Ba Mairama ba kadai kaf 'yayansa me zai bugi kirji yace yayi musu. Hajjo sai da ta magantu taji dadi ta fake da yi musu godiya "Allah Ya saka da alkhairi mungode. Ohh Malamijo baki sun zo gari -e- gari ko ruwa ba'a basu ba sai karbar kyauta daga hannunsu. Ke Radhiya tashi muje na tayaku hada kaya yau kakarku ta yanke saka"
Cike da zumudi Radhiya ta mike tana kallon yadda Mairama take ta fara'a a tsakanin mutane. Idan ma kuruciya tasa bata gane mahimmancin zumunci ba a iya hankalinta ta sani cewa Umminta tana cikin farinciki. Wannan kuma ya isheta komai.
Yadikko bata hakura ba sai da ta dafa musu dafadukan shinkafa da wake. Babu bama dai bare kifi amma tayi nata kokarin. Abin kunya ne ace wannan bakin sun zo sun tafi basu ci komai ba ga nisan hanya. Tasan tsiyar da suka tarar a gidan ita ta kara tunzura komawarsu a ranar.
Batare da bata lokaci ba suka fito an gama shiri. Wani dan akwati da take ajiyar mahimman abubuwa kamar khakin Zayyan, wasikarsa da kuma hotuna tace Radhiya ta tabbata ta dauko. Dariya tayi don ta gama haddace komai na ciki. Hotunan yawanci na bikin iyayenta ne da na sunanta.
Karfe biyar da kwata sun gama shiga mota. Baffa Gide yana tsaye a gefen mota kusa da Malamijo suka sake yin musabaha "yanzu da muka dena yawo idan kana nemanmu mun koma Giade can asalin garinmu amma rugarmu tana daga ciki da dan tafiya daga garin. Wannan da kake gani mijin Innawuro shine Ardo na biyu bayan kafuwar rugar"
Sallama Mairama tayi da kowa daga ita har su Radhiya ko digon hawaye irin na kewa dinnan. Rabuwa da Yadikko da Hajjo da kuma sauran 'yan uwa ya dan sa sunji wani iri to amma fa ko kadan bikin Magaji bazai hana na Magajiya ba.
**********
WAIWAYE.... [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: Max, Anna da Liam sune 'ya'yan da suka tashi a hannun Mami. Suna ganin shigowarsu lawn din suka taho suna murna. Idanun Anna jazur taci kuka tun safe take abu daya.
Rungume Mami tayi "bana so ki tafi Naanaa" tace cikin yaren jamusanci.
Da yaren Mami ta maida mata "kiyi hakuri Anna, watarana zan zo ziyara ko ke kizo mana Nigeria ko"
"Zaki zo aurena next year?"
"In sha Allah"
Hawaye Anna take ta rinka sumbatar kumatun Mami ita kuwa sai dariya. Liam da Max hannuwanta suka rike suka kaita tsakiyar wurin suna nunawa jama'a Naanaa dinsu. Mai aiki ce amma wadda take a inda aka san darajar masu aiki har masu gida suke karrama su.
Ta sami kyaututtuka da yawa daga abokan aikinta da abokan arziki.
Frau Marie Schmidt ta kawo envelop da kudi a ciki ta bata sannan ta bawa Fauziyya da Zahra wasu setin dankunne da sarka 'yan ubansu wai su saka da bikinsu. Zayyana ma an bata katon teddy kusan kansu daya. Tana ta murna Mami a ranta tayi dariya kawai. 'Yan kasarmu ina muka wani san darajar teddy.
Hotunan tarihi suke dauka Major ya daga waya yana fadin inda suke. Ko minti biyu ba'ayi ba sai ga matashin saurayi kyakkyawa wankan tarwada mai cike da kwarjini da haiba ya shigo wurin sanye da uniform dinsa na matukin jirgin KLM mallakar kasar Germany. Jacket da wando ne navy blue sai farar shirt a ciki kansa sanye da hula irin ta Captain din jirgi. Mata hudu ne a gefensa hagu da dama air hostess kowacce da uniform riga da skirt sky blue suna rike da flowers masu kyau.
Shigowar tasu ta kayatar da mutanen wurin bare iyayensa. Yana shigowa kai tsaye wurin Major ya nufa ya rungume shi. Mami ta saki baki sai kuma ta daure fuska cikin wasa.
"Awwab, yau din ma?"
Sai da yayi mata dariya sannan ya rungume Maminsa a kunnenta yana cewa "sorry Mamina"
'Yan matan da suke abokan aikinsa kowacce ta mika mata flower da dan gift suna mata fatan alkhairi.
Awwab ya fiddo tickets biyar daga aljihun sa ya mikawa Major.
"Daddy ga nawa gift din...Captain M.A Mustapha shine zai ja jirginku zuwa birnin Abuja. Sai da na duba schedule dina na sayi ticket. Tafiya ta dawo nan da sati biyu. I hope it is okay"
Zayyana tayi tsalle ta dane shi tana ihun murna. Mami sai murmushi kawai na jindadi. Major kuwa tsokanarsa yake yi wai bazai shiga ba kada ya zubar dasu a teku.
An gama party lafiya suka koma gida tare dashi. Shirye shirye ya kankama inda suka hada ya nasu ya nasu sai gida Nigeria.
***********
Iyayen Zainab sun sakata a gaba kowa da abinda yake cewa tun da ta sanar musu cewa a yiwa iyayen Hadir magana akan aurensu.
"Wai shin idan kin koma soyayya zaki rinka zuba muku a kwano kuna ci? Ke ba aiki shi a zaune. Ni har yau ban gamsu da ba ke kika kashewa kanki aure ba" mamanta tace a hasale.
Babanta ne ma mai dan sauki a gareta "Zainab nasan kila ko a wurin Ibrahim kina ji cewa jikin Hadir babu wani sauki sai na musulunci. Kinje kin shafe shekaru tare da Musa kin saba da jindadi. Ta ina zaki koma gidansu?"
"Baba na fada muku ya bani gida a Kano sannan ya kara min jari akan wanda ya bani tun da nake zuwa Dubai saro kaya dashi. Alhamdulillah Allah Ya wadatani Abbansu Aisha ne sila. Ni zan cigaba da tafiya kasuwancina ne Ibrahim ya rinka kula dashi idan bana nan"
Mamanta ta kara kulewa "sannu uwar tsari, waro har kin gama tsara yadda komai zai kasance"
Allah Ya sani tana son iyayenta kuma tana girmama su. Amma wannan karon tana jin tayi girman da ya kamata a karbi uzurinta idan tazo dashi.
"Idan ba kwa so na komawa Hadir bazan koma ba. Amma wallahi bazan kara aure ba har na mutu"
Tsam ta tashi daga dakin Baban nata. Sun san Zainab da taurin kai. Anyi sa'a ma zamanta da Musa Allah Yayi da tsayin kwana. Tufka suke da warwara suna guje mata matsala a gaba. Karshe mahaifinta yace su barta Allah kadai Yasan dalilin wannan soyayya da take yi masa.