Batuol mamman complete novel - Chapter 57
Batuol mamman complete novel Chapter 57: Batuol mamman complete novel Chapter 57. Hannu kawai yasa ya janyota ta fito ya sake matso da ita jikinsa sosai…
3,370 words
Hannu kawai yasa ya janyota ta fito ya sake matso da ita jikinsa sosai yayi musu selfie.
"Akwai bil adama a bayan mota" cewar Yousuf bayan ya sami chance din kaiwa Arifah kiss a kan hancinta tana rufe idanu.
Dariya Awwab yayi wai yanzu damarsa ce sun gama nasu bai ce komai ba. Zama Radhiya tayi ya gyara mata rigarta ya rufe kofar sannan ya ja suka tafi kana leka motar taurarin soyayya sun mata kawanya.
Wani katafaren events hall suka nufa inda suke iya ganin taron motoci sun cike wurin parking din ciki an fara layi a gefen titi. Suna shiga Emzee yana fita bayan ya karbi mukullin motarsu daga hannun Ibrahim da su suka ajiye su Laila da Zayyana.
"Ina kuma zaka je kasan yanzu su Daada zasu iso a fara"
"Yanzu zan dawo Rahima zan dauko please kace bazan dade ba idan an nemeni"
"Emzee kodai-kodai?" Ibrahim yace yana daga gira.
Cike da shauki Emzee yace "fadi ka kara bros yarinyar nan ta cuceni...ko shiryawa banyi ba kawai na nemi zuciyata na rasa ashe ita ta dauka. Da tayi warning dina kasan kai zan fara sanarwa"
Duka Ibrahim ya kai masa a baya yana kyakyata dariya "shege malamin soyayya ya fada ruwa....tabdi amma har ta bani tausayi ta kwaso Emzee chewing gum"
"Me ka mayar dani?"
"Irin mazan da idan suna son mace zasu iya sadaukar da komai nasu domin kyautata mata mana"
"To kai din ba shi bane?"
Bangaren da Zayyana take Ibrahim ya kallo "I can die for her man"
"I feel you bros nima haka nake ji. Ina bukatar time da ita ne domin in san ko wacece. Na dai fi tunanin tana da alaka da gidansu Halifa maybe cousin dinsu ce tunda ina ganinta da Hibbah."
Gaban Ibrahim ne ya fadi ya soma tunanin yaya akayi Emzee bai san wace Rahima ba. Tunawa yayi da yadda ya tsani Gwaggo Salame yaji jikinsa yayi sanyi. Bai taba ganin Emzee so cheerful ba irin yanzu, gaskiya bazai iya rushe masa wannan sabon farincikin ba. Zai bari ya gano da kansa kila sanadiyar shiryawar iyayensu kenan.
"Na tafi" yaji Emzee yace.
A gurguje ya tada motar ya koma gida. Minti goma ya kaishi saboda babu nisa da gidansu. Sai yanzu ya tuna bashi da nambar wayarta to ta yaya zai kirata. Idan kuma ta tafi wurin bata jira shi ba fa. Tambayoyin da yake ta yiwa kansa kenan sai ga mai aikinsu 'yar budurwar ta fito itama a shirye fes da ita.
"Yauwa don Allah kirawo min Rahima a dakin Adda Radhiya."
"Kowa ya tafi fa muma Ummi tace yanzu dreba zai dawo daukarmu shine na fito dubawa da ka shigo"
Gwiwarsa ce tayi sanyi ya koma motar sai ya sake dawowa zuciyarsa na fada masa Rahima na jiransa "daure ki duba min nasan tana nan"
Ba musu ta shiga gidan. Dakin kasa da suke ta shiga tayi sa'ar ganin Rahima a shirye cikin nata kayan kamar kowa Ummi ta dinka mata sai dai ita dasu Zahra dankwalin kayan suka saka. Arifah da Radhiya ne kawai masu ashoke manyan amare. Mayafinta daidai da ita har ka ta lulluba shi yadda ta saba tayi kyau sosai.
"Karami ke kiranki a waje"
Da faduwar gaba ta tashi tana tunanin karfin halinta na zama don yace ta zauna. Sai dai bata jin akwai ranar da za ta yi fatan yi masa musu saboda babban matsayin da ya kwata ta karfin tsiya a zuciyarta don itama bata shirya ba.
Kayansa hatta hula sak na mahaifinsa yana tsaye a bakin kofa ta fito. Ido suka hada ya sakar mata murmushi ta janyo mayafin ta rufe rabin fuskarta.
"Hey kada ki cuceni ki hanani ganin fuskarki yau ba kawance"
Langabe kai tayi suna tafiya wurin motar "sai me?"
"Muhammad da Rahima"
Sake rufe fuska tayi komai nata yana burge shi matuka ya dora hannunsa a saitin zuciyarsa "my God, she is so adorable"
Sun kusa kaiwa motar yaji an kwala masa kira daga cikin gidan "kai Karami ku jirani wannan dreban da za'a turo ban ga ranar zuwansa ba"
Ba kowa bace illa Salame ta taho buguzum cikin wata kodaddiyar shadda wadda take yiwa kallon mai kyau har yanzu tana goye da Khadi kamar wata jaririya.
Gaban Rahima ya fadi zuciyar Emzee kuma tamkar ta fito ta baki saboda bacin rai har ta iso bakin motar ta bude gaba ta shige kwam abinta. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: A bangaren Yousuf da Arifah kwatancen hanya ta rinka yi masa a kunyace har su ka iso titin da zai sada su da gidan inda daga nan ya gane hanya. Ciki ya shiga tunda masu gadin sun gane motarta kuma tana ciki. Duk ta daburce saboda auren nasu yazo da wuri basu gama sabo sosai dashi ba. Ya san da hakan shima shiyasa yake kokarin dinki duk wata kofa kafin su fara rayuwar auren sosai.
"A love yanzu yaya zaki yi dani?"
Fasa bude kofar tayi ta waigo kadan "me ya faru?"
"Kin taho dani gashi bansan hanyar komawa ba kuma bani da ko cent a jikina da zan nemi taxi. Ga dare..." yace da wani irin yanayin da zaisa a tausaya masa.
"Kaine fa kace zaka rakoni in karbi motar. Yanzu yaya kake so ayi?"
Kwantar da kansa yayi baya ya jingina da kujerar yana kallonta "Nima ki rakani"
"Yanzu su Mom zasu dawo ace ina naje?"
Bude bangaren shi ta ga zaiyi cikin yanayin ko in kula yace "tunda haka ne muje kawai na kwana a dakinki kinga gobe sai mu shirya daga nan mu tafi zaifi sauki"
Idanu ta zaro tana kada hannu "wasa kake yi amma"
"Gadon naki karami ne? To ba sai ki kwanta a kasa ba ni ki bani gadon tunda nine bako"
Dariya ya bata ma yadda yake maganar tace "rufa min asiri...ko za ka kira Yayana yazo ya daukeka?"
"Ni bazan shiga rayuwar kanwata in hanata samun kulawa daga mijinta ba"
"Hmm Y love rigima kake ji naga alama"
"Ko daya" yace yana kamo hannunta ya rike yana murza yatsun.
"To ka dauki motar ka tafi da ita"
"In bata a hanya gobe ace ba'a ganni ba...naki"
"Bari na nemi dreba ya mayar da kai"
Bata rai yayi "bana so"
"Ya zamuyi to?" Tace tana tura baki don tsoronta daya kada iyayenta su dawo a gansu sai ace bata da kunya musamman Mom dinta. Bata san yaya akayi ba ya janyota rabin jikinta a cinyarsa ya rungumeta sosai yana shakar kamshin jikinta mai dadi. Kansa yana gefen wuyanta sai numfashinsa kawai take ji yace.
"Mhmmm mon amour" yana jin kamar su kwana a haka "...inata baki haske, inata baki haske kinki ganewa."
Yadda hausar tasa ke fita da abinda yace ne ya sakata dariyar dole "kana ta bani haske..."
"Eh mana amma baki gane ba....kowane ango yana tare da matarsa ni tawa tana nuna min halin hausawan Nigeria"
"Ban dau haske bane" tace a hankali tana kokarin zamewa sai gashi tar an hasko wata torchlight mai mugun haske sosai cikin motar ta barin da yake.
Arifah gabadaya ta gigice don kunya ta fasa guduwa sai ma kara kankame shi da tayi a kunyace bata son ko waye a tsaye ya ganta a haka. Yusouf kuwa ko a jikinsa sai ma sauke glass da yayi rabi har lokacin tana cikin jiikinsa. Security din yace da pidgin english "na Madam i dey find I never see her comot from the car"
Ko kalma daya bai fahimta ba sai ma kullewa da kansa yayi yace "pardon?" Sai kuma kawai ya dan taba kafadarta
"Ba fa na jin yaren nan ki kore shi kafin nayi masa ido daya na ganin matata"
Yadda yake bata rai ma abin dariya ne. Haka ta daure ta dago kanta kadan "Oga Sunday I dey come"
"No wahala" mutumin yace tunda ya tabbatar tana nan ya juya abinsa.
Kokarin tashi daga jikinsa ta soma yi "Y love bari na hadaka da driver please"
Sake riketa yayi ta kasa motsawa "ke kuwa ki dau haske mana A love, biyoki nayi fa don mu taya juna murnar aure"
Duk wasu dabarunsa ta gama ganewa. Ko Radhiya kanwarta ai tasan ta wuce ayi mata wannan wayon bare ita. Wace murnar aure zata yi a kofar gida. Hannunta ta mika masa na dama ya riko da nasa ta dan daga hannun sama da kasa tana jinjinawa "congratulations on your...."
"Rike kayarki tunda baki daukar haske ga abinda nake nufi" yace yana kai mata wani irin kiss da ya hanata motsawa.
Dirin motocin da suka ji daga waje ne ya tayar musu da hankali su duka ta tashi daga jikinsa da sauri.
"Yanzu ya zamuyi?"
Tashin hankali karara a fuskarsa yace "nima ban sani ba, ba gidanku bane"
A tsorace take amma dole tayi dariya don ya fita rikicewa. Shiyasa yaso ta dau haske tun dazu ya samu ya gudu saboda Yousuf mutum ne mai kunya sosai. Ko lokacin da yaso Radhiya wannan kunyar ita tayi ta cutarsa ya kasa fada da wuri ashe rabon Arifah Nasiruddeen ne. Saurin kiran Awwab yayi yace yazo ya dauke shi su tafi.
***********
Bayan fitar Radhiya daga falon da sauri ya biyo bayanta amma bai ga alamunta ba. Da gudu ta shiga cikin gidan tana ji kamar za'a gane me tayi. Awwab zai kirata kenan don shi bai ki yau ya kwana a gidan ba Yousuf ya kira.
"Ni gaskiya bazan zo ba rakiyar taka tayi kadan ni kuma yanzu na fara" yace masa yana dariya.
Yousuf ya kalli motocin su Baban Arifa "Kada muyi haka mana Awwab ni da na baka kanwata ya kamata ka kyautata min"
"Ni ba kanwar na baka ba"
Daga murya Yousuf yayi amma kana ji kasan kawai damuwa ce "kada kasa na dage bikin nan sai ta gama ècole"
"Daidai kenan, sai ayi bikin da baby dinmu mu shiga gida mu uku ko hudu" bai san me ya dami Yousuf din ba amma dadin tsokanarsa yake ji yana dariya lokacin da Raji da Bilal suka fito kowa da murmushi saman fuskokinsu.
"A love kiyi masa magana" Yousuf yace da Arifa kamar yayi kuka.
Tana karbar wayar ta soma magiya don tana iya hango kallon da Mom dinta take sakar mata bayan ta fito daga mota. Yousuf sai ji yayi wani gumi na neman saukar masa duk sanyin garin. Tare da Arifah suka matsa wurinsu suna musu barka da dawowa.
"Yousuf ba dai sawa tayi ka kawota ba ka biye mata kai kuma?" Cewar Mom tana musu kallon daidai.
Awwab na jin muryarta da hannu yayiwa su Raji alama suka shige mota yaja suna dariya yau sun sami abin tsokanarsa. Rakiyar yau bata yi ba sai dai ko gobe a sake.
Yousuf yace da Mom "na ga ta karbi motar ne ga dare. Su Awwab nake jira zamu tafi suna hanya"
"To babu damuwa bari na wuce"
Excellency da mutanensa yayi gefe suna magana yana yiwa ango da amarya murmushi yace su shiga ciki kafin Awwab din ya karaso. A ransa kuwa dariyar yadda Mom sarkin takura ta ritsa su yake yi. Tunda anyi aure ba shikenan ba, ko don tayi sa'a ba sai da safe ya dawo mata da 'yarta ba.
A cikin gidan ma kamar yana kan kaya hankalinsa bai kwanta ba saboda hawa da saukar da Mom ta rinka yi sai da Awwab ya kira shi. Da sauri ya fita daga gidan yana sauke ajiyar zuciya.
Kai daren ranar kamar yayi ihu saboda yadda su Awwab suka saka shi a gaba da tsokana. Mami tana jiyo hayaniya daga dakin Awwab inda suke kwana kamar wasu yara.
"Irin haka basarwa ake yi Yousuf" Awwab yace yana mike bayansa akan gado saboda gajiya.
"Zan rama duk kuyi ku gama. Kuma matsa min na kwanta yau nan nake so."
Ture Awwab yayi tsakiya dariya ta hana shi tabuka komai har Yousuf din ya kwanta a wurin mutum biyu don da gangan ya bude hannuwa wai baya son takura.
**********
Fauziyya da Zahra sun riga Radhiya shiga daki. Rahima da Zayyana wani dakin suke kwana a kasa yanzu saboda yayyensu dake saman a dakin Radhiya ga yara biyu.
Yadda take sauke numfashi Zahra ta tambayeta ko gudu tayi ta gyada kai.
"To dai mutum ya girma guje guje ba naki bane amaryarmu" Zahran tace mata.
"Kyaleta fa tayi abinta nan da sati biyu ko da kudi nasan da wuya ta iya daga kafa"
"Me zaisa Adda Fauzi?" Radhiya tace da iyaka gaskiyarta.
Zahra tace "Kyale wannan yayar taki kin santa sarai da tsokana"
Tawul ta dauko za ta cire kayanta ta shiga wanka Fauziyya ta fara yi mata kallon mara gaskiya saboda a takure take wanda ba halin ta bane.
"Amaryar Hamma kada kice min janbakin nan ya goge...gaskiya ina jin ba mai kyan kika saya ba. Ni fa shiyasa abu designer bai dameni ba, ance baya fita da wuri sai an goge shi amma ke lips dinki kamar baki shafa komai ba. Kalli ki gani" ta juya tana nunawa Zahra da tsokana.
Radhiya ta rasa yadda zata yi sauran abinda basu gane ba ma sun gane don ba karamar kunya taji ba, shikenan Hammanta ya janyo mata. Turo baki tayi kamar za ta yi musu kuka "to ba...ba...uhmmm tissue na saka na goge"
Fauziyya ta saki fuska "ohhh irin makeup remover dinnan ko? Please nima bani nagoge don ni sanyi nake ji bazan iya wanka ba"
"Fauziyya ki kiyayeni ko in kira Ya Bilal yazo ya kwashe mana ke kowa ya huta. Mutum yana fama da kansa amma baki baya shiru" cewar Zahra amma daga ita har Fauziyyan dariyar tsokana suke yiwa Radhiya. Yau mai balotelli an dinke mata baki.
Cikin dariya Fauziyya tace "wai ma in tambayeki, makeup remover din baya goge fuska iyakarsa baki kawai?"
Sai yanzu Radhiya ta fahimci ina suka dosa da wannan tambayar da dariyar. Aka yiwa wani ma ta rama bare an shiga gonarta. 'Yar dariya tayi tana sunkuyar da kai tace "sauran yana bakin Hammana shi ya goge min"
Idanu Fauziyya ta zaro Zahra kuwa dariya harda rike ciki. Suna son juna idan an hado kamar kar a rabu saboda irin wannan dramar.
"Kika bashi ya shanye?" Fauziyya tace fuskarta kadai sai tasa mutum dariya.
Radhiya ta gimtse dariyarta ta zauna kan gado ta dora kafa daya kan daya tana daukar wayarta. Sunan da ta saka masa Mon Chèri (my sweetheart) ta nemo tana nunawa Fauziyya "In kira shi ki tabbatar?"
"Zahra ki fadawa su Mama tun wuri kada gobe labari ya wuce goge lipstick a bashi matarsa"
"Ba tambayata kika yi ba Adda Fauzinmu" tace da shakiyanci.
"Ah to matambayi baya bata gashi nan an dora ki akan hanya yadda zaki gane" cewar Zahra har lokacin dariya take yi sosai ita da Radhiya. Katse dariyar suka yi a dole da suka ji ance
"Schatzi" daga cikin wayar hannunta.
Su duka ukun suka kalli wayar harda ita da ta kira bata sani ba kafin suka fice daga dakin a guje suna dariya sai ka rantse yara ne masu kananun shekaru. Awwab da yaji shiru sai ya kashe wayar yana tunanin kila bata san ta kira ba saboda dare yayi.
Da suka koma dakin ma suna kallon juna sai su kwashe da dariya Fauziyya na cewa dadin abin itama an goge mata nata janbakin yau da tayi kwanan tausayin kanta.
Komai nasu abin sha'awa musamman wannan hadin kan da ya samo asali daga jajircewar iyayensu.
**********
Washegari wuraren shadaya na safe a can gefe guda na katon falon gidan Zahra ce da kannen nata Fauziyya da Radhiya Rahima tana yi musu lalle iya yatsun hannu kawai banda kafa. Su na cikin yi Mami da Mama suka shigo Zayyana da tun daren jiya aka yi mata nata ta tashi da sauri tayi bakin kofa za ta karbi DK ta ga baya hannun Mama ko Mami.
Baki ta tura tana leka waje "Mama ina DK?"
Mami ta daure fuska tace "Meye haka babu gaisuwa ni matsa ki ban wuri yana wurin Ibrahim a mota"
Murmushi tayi kafin ta matsa tana gaishesu. Mama tace taje ta karbo shi kunya take tana ganin idan ta fita kowa zai gane meye tsakaninsu. Ganin Hibbah ta taso zata karbo shi yasa ta fita da sauri. Hibbah tayi dan murmushi suna hada ido da Rahima.
Fauziyya ta hararesu "gulmammu ko dai ku fasa mana kwan nan ko yau na danneku a daki ayi muku balotelli ko ya kike gani babbar yaya" ta kalli Radhiya.
Dariyarsu kadai ta isa tona asiri amma Zahra tace "ku bari ta dawo mu sakata a daki ta fada ko yau ayi taro tana gida"
Hibbah da Rahima dai sai dariya Fauziyya tace su din ma duk sai ta binciko nasu tunda Radhiya ta kauce su ne next.
Wata irin tafiya Zayyana ta rinka yi kamar bazata isa wurin motar ba saboda irin kallon da Ibrahim yake yi mata. Tana zuwa ya fito da DK a hannu yana murmushi.
"Kawo shi" tace tana mika hannu.
Kara makale shi yayi a jikinsa yana harararta "dama ba wurina kika zo ba?"
"Ni kanina nazo dauka"
Wani irin kallo ya bita dashi "Ya kina ganina amma ta wannan yaron kike yi. Tun wuri ki sani bazan yarda da wasan kanin miji ba."
Kamar gaske ya hade rai ita kuwa dariya ma take yi "Ka jira a haifi kanin mijin wannan dai twin dina ne ko ba ka ji sunansa ba...Zayyan da Zayyanatu" tayi masa gwalo.
Bata fuska Ibrahim yayi ya tale baki yadda take yi ta cigaba da dariya. Muryar kuka ya soma yi mata "idan ba kin janyo na rage masa matsayi ba tunda haka ne. Tun farko ni me yasa ba'a saka min Zayyan din ba shi a saka masa Ibrahim?"
"Saboda shi Zayyan kanina ne, shi kuma Ya Khaleel...." juya idanu tayi bata karasa ba ta kama hanya za ta gudu.
Ibrahim kamar wanda aka dora a gajimare yake yawo don dadi ya biyota ya mika mata shi. Tana karbarsa ta kai hancinta jikin nasa tana gogawa tare da yi masa murmushi "baby DK dinaaaa"
Jingina Ibrahim yayi da bango yana kallonta da jin sabuwar soyayya na dibansa "yaro kaji dadinka ko yaushe ni kuma zan sami arzikin ayi min haka wa ya sani"
Kai ta dago ya kashe mata ido bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta ji ta shige ciki ta barshi a tsaye yana ta murmushi.
Emzee ne ya shigo ta karamin gate da ledar mangaro masu kyau wanda ya sauka daga motar ya tsallaka siyowa da suna hanya kafin su shiga kwanar gidan. Yana karasowa motoci uku suka shigo manyan mata wayayyu suka rinka fitowa daga ciki. Mom Arifah kadai suka gane suka gaisa da ita da sauran matan tace Emzee ya kaisu wurin Mairama.
Yana gaba sauran duka suna bayansa da ita suka shigo. Su Radhiya suka gaishesu sannan Zayyana ta hau sama ta fadawa su Ummi. Gayyar lallen ce ta tashi dama sun saka wata leda a wurin basu bata ko ina ba suka tafi daki.
Dukkaninsu matan manya ne su takwas. Biyu matan gwamnoni, uku matan sanatoci, karamar ministan ilimi sai matar ministan ilimin wai sun zo sake yiwa Mairama murna ne zasu koma garuruwansa. Duka Mom Arifah ce ta gayyato su. Abubuwan ci da sha aka kawo musu Salame tana daga daki take jin muryoyin manya don su Yadikko bayan gidan suka tafi wurin aikin nama kafin isowar su Mama da Mami da zasu hadu ayi abinci da Tante. Ko da wasa bata hangi kanta tana taya aikin komai ba a gidan banda kwanan bakinciki da tayi jiya saboda yadda ganin Alh Salisu ya kara tada mata hankali shi da matarsa. Fitowa tayi tana hura hanci Mairama kuwa tace musu ga yayarta tana nunata.
A mutumce suke gaisawa da ita sai ta saki fuska ta samu ta zauna a kujerar da tafi kusa da Mom Arifah tana ta wangale baki.
Hannun Ummi da Mom Arifah ta gani ta yaba "gaskiya ina son lallen nan Mairama yaya zamuyi? A ina mai yi take? Yayi kyau sosai"
Dadi Ummu taji " 'yata ce tayi min sunanta Rahima"
Matar gwamnan Abia kasa hakuri tayi tana shafa hannun tare da kallon kafar gwanin sha'awa "ni dai a kirawo ta idan tana kusa tayi min inje dashi gida yarana su gani...nawa ake biyanta don basira irin wannan nasan da tsada"