Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 69

Batuol mamman complete novel - Chapter 69

Batuol mamman complete novel Chapter 69: Batuol mamman complete novel Chapter 69. Wayar Awwab ta katsesu Radhiya tayi hanzarin mayar da kayan da tazo dasu…

3,310 words

Wayar Awwab ta katsesu Radhiya tayi hanzarin mayar da kayan da tazo dasu ta dauki jakar kayanta ta sauka. Abinci aka gabatar musu wanda Arifah tasa aka shirya amma kunya ta hanasu ci. Plate Awwab ya samu ya zuba musu shi da Radhiya ya rike hannunta su ka koma wurin wasu kujera daga can gefe guda. Yousuf yace masa ya kyauta dama bashi da niyar barin Arifah ta tashi bata ci komai ba.

Yadda suka saba kama-kama da spoon daya Awwab da Radhiya suka yi a haka aka ci abincin sannan suka tafi tare da Yousuf ya sauketa a gida.

***********

Ana saura kwana biyu fara events din Jos wanda kowa zaije banda Radhiya ance itama amarya ce. Tayi magiyar har Awwab ta roka yace tayi hakuri ba yinsa bane amma idan ta shirya ya kama musu masauki shi da ita sai su tafi tare. Da jin haka tasan hakuri ya zame mata dole ta gama rigimarta da shagwaba ta sallama. Sai gashi Zayyana da Rahima suka ce mata zasu zauna da ita su ma sun fasa zuwa. Ummi kuwa tace basu isa ba ya zama dole a karrama iyalin Excellency. To karshe dai Fauziyya ce ta fake da laulayi ta zauna tunda kwana biyu ne zasu yi kuma dai ba son tafiyar take ba. An gama wannan shawarar washegari ya kama ranar da za'a mayar da Rahima asibiti. Ido ya sace kamar bashi ba amma kuma yana ta ruwa.

Ummi ta shirya zasu tafi da Emzee da Ibrahim shiru bata sauko ba Emzee ya hau sama kiranta. A falon saman ya ganta zaune akan kujera ta dafe kai tare da runtse idanu.

"Ummi..." yace a tsorace ganin tana ta runtse ido "baki da lafiya ne?"

Hannunta ta dago masa tana son ya taimaka mata ta tashi "tun dazu nake jiran wani ya hawo, taimaka ka mayar dani daki jiri ke dibata sosai"

Da taimakonsa ta karasa dakin da kyar kanta yana ta juyawa kuma ta kafe bazata bisu asibitin ba wai stress ne kawai da rashin zama.

"Kaje ka kai min yarinyata a duba mata idon nan idan kun dawo sai ku karbo sakon nan da na fada maka wanda zamu tafi dashi Jos gobe"

Ba haka yaso ba don har Daada ya kira a waya ya fada masa. Sanin halinta na kin asibiti yace su tafi da Rahiman ya kusa tasowa zai kaita da kansa.

Yana saukowa ya nemi Ibrahim ya rasa. Can ya hango shi da Zayyana suna hira an nutse a cikin soyayya. Tsaki yaja tuni ya dawo daga rakiyar 'yan mata. Zayyana ya tura ta kira Rahima su tafi Ibrahim ya kyabe baki

"Ni dai gaskiya babu inda zata je ka kira wayarta mana ko kaje ka kirata da kanka. Dawo ki zauna kinji"

Emzee ya rike haba "ashe da gaske akwai ranar da zan ga kana tale baki? Kanwata kiyi a hankali kada ya fiki iyawa a kasa gane wace Zayyana waye Ibrahim"

"Banda abinka ga Zayyanan ai" Ibrahim ya nuna kansa sannan ya nuna Zayyana yace "ga Ibrahim".

Murmushi tayi tana jin kunya ta je kiran Rahima. Dama a shirye take gudun bacin rai daga Emzee yasa tayi zamanta sai Ummi ta sauko. Lokacin da ya fadawa Radhiya Ummin bata jindadi tana daki bata sani ba. Zayyana tace bazata bisu ba saboda anyi printing takardunta na admission da ta samu a Nile University akwai wuraren da zata cike Mami zata turo dreba a karba. Ibrahim kememe yaki bin Emzee da yaji haka.

"Kuje ku dawo Zee-zee ina jiranka a nan" ya nuna inda yake zaune.

Haushi ya kama shi kuwa saboda ganin yanzu su biyu ne kadai zasu shiga motar. Gaba tayi nufin shiga tunda su kadai ne yace "koma baya".

Bayan ta zaga ta zauna abinta batare da tayi masa magana ba. Yana zama ya kula kamar mudubinsa a saitin fuskarta yake don duk motsinta yana gani maimakon ya hango titi.

"Koma gefe" ya umarceta.

Gefen ta koma ta rakube zuciyarta tana zafi. Ba komai yake damunta ba sai rashin sanin aihinin abinda tayi masa wanda ya bata masa rai har yake mata haka. A gaban mutane bama ya shiga shirginta sai ya zama dole. Idan su kadai ne kuma dalili ya janyo sai yayi mata magana to ba mai dadi yake yi ba. Ba karamin azabtuwa yake da yin hakan ba domin kuwa har yanzu ya kasa rabata da matsayin da ya bata na Rahiman Muhammad. Ga tausayinta da yake dawainiya dashi saboda ciwon idonta.

Ko tari taki yi a motar ya kunna karatun Qur'ani kira'ar Mishary Rashid Al-Afasy cikin suratul Kahf. Da kadan da kadan yake jin tashin muryarta tana bin karatun a hankali sai ya sami kansa da rage volume batare da tayi la'akari ba. Idanunta a rufe sai dai lokaci lokaci tana sanya tissue ta goge ruwan da yake fitowa kamar hawaye daga dayan idon nata. Bakinta yake bi da kallo ta mudubi can cikin zuciyarsa yace "Rahima".

Wani mugun horn yaji yayi saurin kallon gabansa tare da taka burki da karfi kadan ya rage ya dokawa motar gabansa. Rahima ta bude ido da sauri ya juyo suka hada ido sai harara yake maka mata.

"Wato ta nan kika bullo kuma? Bari mu koma gida addu'a zan ce Ummi ta rinka yi min saboda na fuskanci abin naki da gaske ne."

Bata fahimci me yake nufi ba shi kuwa bai fasa cewa zai tsananta addu'a ba wai tunda an biyo ta can asirinsu ya tono shine ake neman sake tafiyar da tunaninsa gashi daga kallonta ta mirror ya kusa yin accident. Idan ka ga yadda yake fadan abin dariya kuma ya kasa hakura da kallonta ta mirror din. Sun kusa isa asibitin yayi parking a gefen hanya saboda abin ya ishe shi yace ta dawo gaba. Ita dai bata da ta cewa sai fatan idan ma wata lalurar ya gamu da ita da ta janyo masa chanja halaye Allah Ya yaye masa. Yanzu ta dena jin haushinsa sam sai tausayi.

A asibitin tare suka shiga wurin likitan. Tambayoyi yayi mata game da yadda take jin idon ya haska ya gama bincikensa sannan yace ta rufe idon mai lafiyar ta karanto masa ABCD da aka hargitsa daga can karshen wani office inda ake gwajin ido. Zuciyar Emzee ta tsinke kuka ne kawai baiyi ba jin Rahima guda biyar kadai ta iya fada daidai sauran kuwa sai dai ta kalli Q tace O ko ta kira K da E. Abin gwanin ban tausayi sai da mutum yayi mata haka sau uku ya tabbatar abinda yake zargi ne ya sami idon. Ita kuwa ganin yana maimatawa har cewa tayi dashi tana gani fa. Sai dai sakamakon toshewar da jijiyoyi suka yi da jini aikinsu yayi matukar rauni duk da cewa an magance toshewar kumburin ya warke gabadaya. Ko idon zai yi lafiya da wahala ta sake gani sosai dashi. Yatsunsa ya shiga nuna mata yana cewa ta fadi ko nawa ne. Nan Rahima ta rikice inda bata tantance biyu da uku. Hawaye sosai ta soma yi da likitan ya soma bayani. Duk yadda Emzee yake kokarin nesanta kansa da ita ba karamin tausayinta bane hake bin ko ina a jikinsa. Wasu magungunan ya rubuta mata sannan ya auna karfin idon yace zaiyi mata glass ne su dawo nan da kwana uku.

"Babu yadda za'ayi mu samu gobe da safe saboda tafiya zamuyi a goben" cewar Emzee.

"Zaku iya samu amma sai ka kara kudi. Kayi magana da cashier din idan ka fita"

Nan suka gama komai ya biya kudi cikin wanda Ummi ta bashi. Maimakon su tafi gida wani babban shago ya wuce da ita ya sa salesgirl din tayata neman frame mai kyau. Wani round ta zaba ya dace da fuskarta babu dai me yiwa kowa magana ya biya kudin suka koma asibiti. A mota ya barta yace ya kai musu sannan suka tafi gida.

Zayyan na komawa gida ya sami Mairamansa a kwance Radhiya ta bata tea taki sha wai bacci kawai take son yi ta rabu da ita.

"Jeki abinki Alheran ajiye min tea din" yace da ita.

Tana fita ya cire rigar khakinsa ya rage singlet da godon wando ya kwanta a kusa da ita tare da janyota jikinsa.

"Fillo me yake damunki ne kwanakin nan na lura kamar baki da lafiya."

"Stress ne Sojana kuma kaima kasan dole ne tunda kun dauko mana abinda yafi karfinmu."

Dariya yayi yana shafa kwantaccen gashin kanta da yake nadewa da kansa saboda laushi. Dinner ce angwaye suka tsara abarsu Baban Arifah yazo ya chanja komai. Abokansa 'yan siyasa da manyan mutane wasu ba zuwa Jos zasuyi ba shine suke ganin kawai gara ayi wata a Abujan. Sai kuma bangaren sojoji da suke yiwa Zayyan kallon wani celebrity suma kowa yana son zuwa bikin 'yarsa. Excellency yace bai ga amfanin ayi taro gutsi-gutsi ba alhalin mutane daya ne zasu zo. Kuma dama bikin ya rabu kashi kashi ayi ta tara gajiya da barnar kudi. Hakan da yayi ya kara masa kima a idanun su Baba Hadir da Daddy domin ya nuna yasan zafin nema ba kamar yadda yake a wurin 'yan siyasarmu ba ayi sati ana biki ana barin kudi. Shiyasa su Mama kullum suna tafe ana ta shiri domin suyi taron da zai kayatar ya fitar da mazajensu kunya.

A cikin kunneta Zayyan yace "ni kuwa sai nake ganin kamar na tureki ne Fillo"

Da saurinta ta tashi zaune "rufa min asiri da abin kunya Sojana. Muna bikin 'ya ka tureni da wane ido zan kalli mutane."

"Kin fiye tsoro kamar ba matar soja ba. Ina ruwanki da mutane. Iyaka ki goya namu ta goya nasu ba shikenan ba"

"Ni dai ka dena wannan fatan" tace tana sake narke masa.

"Yanzu ma na fara, kinsan irin farincikin da zanyi kuwa idan gaske ne? Hmmm Fillo kiyi fatan Allah Ya amsa domin ki ganewa idanunki babban matsayin da zaki kara takawa a zuciyata"

"Kana nufin akwai inda ba ni bace dama?"

"Ko daya, sai dai zan kara mata fadi ne domin a haka kinyi mata yawa" yace yana kara rungumeta tare da addu'ar cikar burinsa.

A nata bangaren itama hasashen cikin take yi amma kunyar kasancewarsa take. Ina zata boye kanta ace tayi ciki bayan ta aurar da 'ya. Ga tarin fargabar yadda Zainab ta haihu.

Sai dare ta iya saukowa Emzee yayi musu bayanin abinda likita yace. Mairama taji babu dadi sosai. Wata kiyayya ta banza da Salame ta dorawa kanta ta janyo ta makanta 'yarta da bata yi mata laifin komai ba. Kuka sosai Rahima take yi Zayyan yace kowa ya fita ya barsu da ita. Daga shi sai ita da Ummi ya rinka yi mata nasiha akan hakuri da karbar kaddara. A nutse yake janta karshe ya nemi jin me take son karantawa idan ta gama makaranta tace Nursing take so. Murmushi yayi yana yabawa zabinta sai dai wani hanzari ba gudu ba shine makarantar da aka sama mata sun ce sai sunyi mata gwaji kafin ta shiga SS3. Idan bata sami result irin wanda suke bukata ba sai ta maimaita ajin.

"Daada repeting fa kenan a wayance" tace a sanyaye da guntun hawayenta.

Ummi tayi dariya "kin ganni fa tare muke tafiya da yayyenki Ibrahim da Karami. Yanzu nan da sati biyu zan koma makaranta ina level 4 suna level 4"

Murmushi tayi kafin tace "Nasan ma sai sunyi min ko don English da Maths"

Kwantar mata da hankali Daada ya cigaba da yi yace ko me ya faru kada ta damu. Ummi kuma tace za'a daukar mata lesson teacher a gida. Bayan ta koma wurin Radhiya wayar Malamijo Ummi ta kira ta fada masa.

Fada yayi kamar ya ari baki karshe yace "Mairama kinga hakkinki ko"

Hawaye ta soma yi "Malamijo ka dena fadin haka kaddararmu ce daga ni har Rahiman"

"Ai ko ban fada ba hakan ne. Salame ko kadan bata da hankali. A da bata damu da Rahima ba yanzu kuma hakkin yarinyar nan bibiyarta yake duk inda ta zauna bata da zance sai Rahima kamar wata sabon kamu. Tayi ta nunawa mutane kafarta wai ita tayi mata lalle..."

Dariya ce ta nemi kwacewa Mairama tace "Kayi hakuri ba da niyar bata maka rai na fada ba"

Albarka ya rinka saka mata yace ba da ita yake fushin ba yana dai jira ya gani ko wannan dalilin zai sa Salame ta dawo hayyacinta sosai. A yadda ya tsara Na'e da wasu ne cikin yaran zasu zo Abujan. Yadikko taje Sakkwato ita kuma Hajjo taje Nijar. Maman 'yan biyu dai banda ita a wannan yawon yaranta kananu ne ga zaman mota.

**********

Bikin kwana biyu suka halarta a Jos tare da su Tante Nasara da wasu daga Nijar da suka taho tare. Kudi dai yayi kuka to amma ba abin mamaki bane duba da cewa biki ne na 'ya daya tilo ga gwamnar jihar tasu.

Gabadaya aka dunguma suka koma Abuja wasu a mota wasu a jirgi. A hanya Ummi ta rinka amai kamar zata fitar da kayan cikinta don sosai ta galabaita. Mama tana sannu tana murmushi wanda ya janyo Ummi kai kararta wurin Mami. Hakuri Mami ta bata tana gargadin Mama da ido saboda birkici musu da Ummin tayi. Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa ciki ne duk da bata je asibiti ba hankalinta duk ya tashi ina za ta kai abin kunya a cewarta. Da su ka isa gidan Daada su duka ukun suka sauka a nan ana lallaba patient. 'Ya'yan nasu basu san me yake damunta ba sai hawa suke ana mata sannu. Sai da ya rage su hudu a dakin da Tante Nasara sannan Mama ta kasa hakuri ta soma tambayarta.

Doki ne ya isheta tana dariya "Ummin Awwab anya baki harbu ba?"

Ummi ta gama aika mata sakon harara kamar ido zai fado "kin manta bindigeni akayi"

Su duka ukun suka sa dariya ta sake hade rai lokacin da Tante tace "abar zancen wasa matar Yaya kamar fa ciki ne dake"

"Wannan ya wuce kama Nasara barka da zuwan Daada ne yake sakata amai. Sai dai muce Allah Ya inganta" cewar Mami.

"Wallahi...wallahi...." ta soma cewa sai kuma kuka sosai tana yi harda sheshsheka tace "ina zan kai wannan abin kunya don Allah. Ciki kamar wata yarinya?"

Mama ta galla mata harara "Allah Ya bamu hakuri" tana dauko DK da yake kwance akan gadon "kai taho kaji dan soyayya in yayeka in samo maka kani ko kanwa."

Fuska jajur Ummi take nunata da hannu ga hawaye yaki tsayawa "Ya isheki Zainab wannan ba abin wasa bane."

"Ni bansan ma me zan ce miki ba. Ki wayi gari bayan shekaru da dama da cikin Zayyan a jikinki abinda nasan ko a mafarki baki hangowa shine kike kuka? Mairama kyauta irin wannan ai sai sadaka da kyautata ibada. Uhmm Mami ga kanwarki nan bari na nemi Emzee ya kaini gida kada ta bata min rai" ta mike za ta fita Tante ta rikota tana cewa.

"Allah Ya shiryeku kuna abu kamar yara"

Mami ta sauke taguminta da tayi tana kallonsu suna aikin hararar juna "ni tunda nake ma na taba ganin matan da suka gagara girma kamar wadannan."

Mama tace "baki jinta ne da wani shirme wai kunya...wannan ba shine babbar shaidar Zayyan ya dawo da soyayyar Mairama ba"

Duk yadda jikin Ummi yake a mace bai hanata jifan Mama da pillow ba itama tana dariyar "Allah Ya shiryeki Zainab"

"Amin Ya shiryemu mu duka." Ta koma tana kallon Mami "saura ke fa ya kamata mu ga shaidar cewa har yau kina qalbin Major"

"Allah Ya tsareni da wannan abin kunya" tayi saurin cewa.

Ummi tace "ooooohhh da shine kuke yi min fata saboda rashin tausayi. Ni na manta yadda ake raino"

"Kin dai san yadda ake samun baby....."

Tante ta hangame baki "Haka kike Zainab?"

"Ta wuce nan Nasara ki kalleta kawai ki dauke kai" cewar Mami.

Tsokanar juna suka cigaba da yi ana cewa Ummi ta tabbatar taje asibiti duk da dai ko yanzu sun fara kirgin watanni. Babu ruwansu 'ya'ya suna shagalinsu suma suna nasu.

Washegari duk wasu masu zuwa daga wani garin sun gama isowa. Radhiya dasu Zahra da wuri suka tafi salon inda Arifah da wata cousin dinta suke jiransu. Gyaran hannu da kafa aka fara yi musu ga fatar jikinsu tana ta sheki anyi gyara har an gaji. Bayan sun gama aka zo wankin kai. Radhiya na bude gashinta Arifah ta rike baki ganin yadda kasansa yayi wani irin ja mai duhu.

"Dye kika saka?"

"Lalle ne" ta bata amsa kafin ta hau bayanin yadda ta kwana hudu tana kwana da lallen da take shafawa a a gashin kullum. Kimantawa tayi kamar daya bisa ukun gashin amma daga kasa take saka masa lallen shine yayi wannan kalar. Daga sama zuwa kafadunta baki yayin da kasan ya bada wata kala mai kyau. Ita da bata saka relaxer steaming da stretching aka yi mata ranar wuni guda a nan suka kwasheta.

Yau Laraba ranar da ake jira tayi. Karfe takwas mai lalle tazo dama jiya an yiwa kowa amarya kadai ta rage. Zama na musamman suka yi aka gama ja sannan aka dora baki. Karfe biyar Mama tayo waya don itama gidanta da baki haka na Mami. Su Hussaina, Nura da Hany wadda ta soma jin sauki sun taho. Gidan Mami tayi masauki sauran suna gidan Mummy Gambo.

A jikin katin an riga an rubuta tsarin events ciki harda zuwan baki daga bakwai da rabi tunda ana Magrib shida da rabi ne zuwa takwas da kwata lokacin da za'a rufe hall a fara event. Mutanenmu da son biki babu mai son a rufe shi a waje shiyasa duk mai zuwa shiri yake da gasken gaske.

Wanka Radhiya ta silla tare da dauro alwalar magrib. Bayan ta shafa mai tayi sallah ta zura kaya don har ita Mama kira take akan idan suka bata lokaci zata saba musu ne. Riga da skirt ne na wani irin material pink da ya amsa sunansa. Rigar daidai da jikinta amma wuyan ya rufe mata baya sai daga gaba aka bude. Hannun dogo daga kasa an bude shi sosai. Shirt din ma sai daga kasan gwiwa aka saka net domin kara masa fadi. Kafin a fara kwalliya Emzee ya kwankwasa kofar dakin yana kiranta.

Tana lekowa ya saki murmushi "my one and only Sis kinyi kyau"

Itama murmushin tayi "kai Emzee ba ayi kwalliyar ba fa."

"Duk da haka bani da ta biyunki" yace daidai fitowar Rahima ta kada kanta kawai don yanzu ta saba da halinsa. Dakin Daada ya nufa da Addarsa inda suka sami iyayensu suna jiransu. Baki yaran su ka saki suna kallon Ummi da Daada sunyi kyau kamar ranar tasu ce. Ummi lace ne baki a jikinta wanda ya amsa sunansa anyi masa wani irin adon cin baki da sky blue din zare da stones. Anyi mata kwalliya ta fito sosai tana haskawa abinka da mai yaron ciki. Mayafinta, takalmi da jaka duka sky blue ne, ga dankareriyar sarka da abin hannu. Daada kuma shaddarsa ce sky blue din aikin jikinta simple yet elegant. Yana sanye da hula zannabukar wadda ta dace da kayan. Ummi rike take da links tana kokarin balle masa a hannun rigar ta kasa. Shigowar Emzee shine ta bashi ya makala masa.

Daada yace a rufewa Radhiya ido kyauta zai bata. Emzee ne mai wannan aikin sai da Daada ya bude wata hadaddiyar sarka shigen ta Ummi sannan aka bude mata idon. Tsabar murna kuka ta saka masa ta fada jikinsa. Emzee sai ya koma gefe yana daukarsu hoto gashinta ya kwanta a bayanta. Saka mata dankunnen da sarka iyayenta suka yi tana ta musu addu'a da godiya.Kusan minti goma suna kashe selfie a tsakaninsu sannan Radhiya ta tafi aka fara zuba mata kwalliya tayi kyau karshe. Wasu kayan Fauziyya ta daukar mata a wata karamar jaka da kayan gyara kwalliya saboda idan anyi rabin taron an riga an kama musu daki da zasu chanja kaya a cikin Sheraton Hotel inda za'ayi event din.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull