Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 78

Batuol mamman complete novel - Chapter 78

Batuol mamman complete novel Chapter 78: Batuol mamman complete novel Chapter 78. Awwab ya tashi zai rabasu Baba Hadir ya hana sai zama da suka yi suna…

432 words

Awwab ya tashi zai rabasu Baba Hadir ya hana sai zama da suka yi suna kallonsu ana dariya manya na fassara lamarin.

Yana daga kwance ta danne shi yace "ni bazanyi soja ba don Allah ki dagani"

Idanunta ta ware a kansa tana sukuwa a bayansa har ta soma tara masa gajiya "to waye zai kareka idan ana fa'a"

Hantsilota yayi yana nishi "ba gaki ba idan kin zama sojan sai ki kareni"

Tayi wani murmushin bada fadi ita ga soja sai kuma ta janyo kwalar rigarsa yana shirin guduwa "idan zan kareka ni me zaka rinka bani to?"

"Boubou wuyana" ya ce ta sake shi da kyar "zan rinka siyo abinci ina kawo miki yadda Daada yake kawowa Ummi Baba kuma yake kaiwa Mama"

"Ahh irin na Abbana da Mamma kenan fa...to na yarda amma wallahi ka goyani" ta haye bayan nasa Nasr ya janyota ta fado,

Dama shima tara shi take yi ai kuwa ta juya ta ce "Haidar taron dangi"

Barin kayan wasan yayi suka hadu shi da Boubou suka danne Nasr. Baba Hadir na ganin haka ya tashi ya raba fadan ya hadasu da sweet suka tafi yana jin DK yana Boubou ki kyaleni sai ta ce idan ta zama soja ta fasa kareshi.

Awwab da Radhiya basu bi ta kan sauran yaran ba dama nan suka yi niyar barinsu suka wuce gida yana cewa yau zai kwana goge mata janbaki.

Falon ya rage Zayyan da Mairama, Mustapha da Hassana sai Hadir da Zainab su ka zauna hira suna tunowa juna wasu lokuta da suka gabata da yadda rayuwa ta sauya musu. A kowane yanayi sai dai bawa yace ALHAMDULILLAH.

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Cikin amincin Allah a yau Ya nufeni da cika alkhairina gareku na kawo muku karshen KDM. Jinjinar ban girma gareku baki daya ahalin groups dinnan. Nagode Allah Ya bar zumunci.

Abinda na rubuta mai amfani Allah Yasa ni daku mu amfana. Wanda yake na kuskure Ya kawar da hankulanmu daga kai Ya yafe min.

Ina rokonku alfarmar wannan wata mai daraja da zamu shiga duk wadda na taba yiwa ba daidai ba ku yafe min, nima na yafe muku.

Abu na karshe muna rokon Allah Ya Dubi sojojinmu Ya amintar da rayuwarsu Ya karesu a duk inda suke.

Don Allah kada mu manta a rike min amana domin na kawo muku wannan labari ne kashi na daya da na biyu a hade. Wasunku sun sani ba karamin aiki bane zaman typing da hada labari. Don Allah ba don ni ba yadda muka hadu lafiya mu rabu lafiya kada kowa ya shiga hakkin kowa.

SonSo Fisabilillah

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull