Bibiyata akeyi complete novel - Chapter 4
Bibiyata akeyi complete novel Chapter 4: Bibiyata akeyi complete novel Chapter 4. Suna shiga daki tayi sauri tasa ki sannan tajuya zuwa ga *hanna* dake…
3,372 words
Suna shiga daki tayi sauri tasa ki sannan tajuya zuwa ga *hanna* dake tsaye kaman gawa *hanna* *hanna* takirata ta jijigata Amma shiru daga hannu tayi tabata lafiyayyan mari Wanda ba shiri tadawo hayyacinta (kusan cewa Koda amakaranta kike kawarki tanemi kirakata wani waje toh kikira gida kifada kafin Dan kikan iya fadawa halaka su iyaye sunbar yaayansu akan suna makaranta) Dan gashi kusan haka tafaru da *hanna*
*Hanna* dan Allah mubar Wanda magana Dan fitowarta kamar rasa rayukanmu ne mu binneta kinji daga Mata Kai kawai tayi ammaa tasamu kanta da addu'ar Allah yasa kar suyi nasara akansa
To be continued
_Ur's_ _Z33yyb3rw3r_
BIBIYATA AKEYI
Bismillahirahmanirrahim
Writting by © _zaynab_ _bawa_ ( _z33yyb3rw3r_ )
_Asmy_ _b_ _Aliyu_ Nagode da addu'arki ki gareni Allah yabar zumunci
Page 13
*
Haka kawai ta tsinci kanta da masa addu'ar kariya daga sharrin su
Haka amira tayita kwantar Mata da hankali Dan tasan Abu kadan ke dagawa kawar tata hankali gata dasa damuwa,,,,,,,, bata barta ba sanda taga tadan sake!!!!!! ,,,,,,, Ni wallahi amira abinda yadaga mun hankali Sai kace abinda yake faruwa a film bantaba dauka yana faruwa a zahiri ba,,,,,,,, Yanzu deh mubar wannan maganan barin duba mana abinda zamuci Fita tayi zuwa kitchen Dan dafa musu indomie Dan shi yafi komai sauki,,,,,,,,
================
Ina labarin najeeb ne??????
Yana katse wayan ya nufi falo a guje Dan fadawa mahaifinsu yaje nema masa aure,,,,,,,,, Turus yayi tundaga bakin kofan falon zumudi yasa gabaki daya ya manta da babansu yayi tafiya,,,,,,
Murmushi yayi tareda sosa keyarsa yajuya Amma ya kudirta duk randa akace dad yadawo maganar da zaifara masa kenan,,,,
Haka yashare sukayi tacin soyayya awaya shida sweety dinsa duk da rashin ganinta yana damunsa Amma,,,,, yakudurta gobe saiya sata a idanunsa,,,,,,,,,
Babban abinda ke damunsa dukda a'ido tana nuna masa tana sansa Amma abaki bata taba furta masa ba Ya alakanta Hakan da kunyan da take dashi
Duk bata kasance bafula tana ba,,,,, amma tanada matukar kunya,,,,,,,,,,,,,, ita cikakkiyar bahaushiya ce Wanda kana kallonta zakaga cikar zatinta na hausawa,,,,,,, Da asalin kyawu irinna hausawa ya bayyana ajikinta
================
Wayan da take gefen sane ta dauki ruri!!!!,,,,, Koda ba'a fada ba yasan wayan da ke kiransa,,, Wani irin faduwar gaba ne yake damunsa kuma yarasa dalili,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, Hakanne yasa kallon yanayinsa captain Ahmad yafita daga office din zaiba shi privacy,,,,, Dan MG Idan yana cikin wani yanayi baya bukatar kowa kusa sanin halinsa ne yasa Idan suna tare dashi suka ganshi a wannan yanayi suke bashi waje shi kadai??????
Captain Ahmad yazo Fita ya umurceshi da ya ajiye masa phone dinsa guda biyu,, Da Wanda mahaifinsa ke samunsa da kuma Wanda yake talakawa masu complain suke samun sa,,,,,,,, Sai akayi rashin sa'a dake phones din iri daya ne ya'ajiye Wanda manyan mutane suke nemansa,,,, Ringing din da wayarsa keyi ne ya tabbatar masa da ba phone din dayace a ajiye aka ajiye bah,,,,,
Tsaki yaja sanda wayan tayi rurin ta tagaji bai dauka ba,,,,,,,,, Sai da aka sake kirane sannan cikin nutsuwa yadauki phone din tare da picking din call din Dan kiran daga mr presdent na Nigeria ne,,,,,, Gaisawa sukayi cikin mutun tawa sannan yake fada masa sunada meeting da zasuyi a Dubai a burj al_arab kuma suna gayyatarsa tareda bukatan matakan tsoro
Haka kawae ya tsinci kansa da rashin son zuwa wajen Amma zaije kodan kare lafiyar al'umma
================
Sai karfe uku sannan amira takira driver yakaisu taraka *_hanna_* gida Suka fito sannan sukayiwa Ammin su amira sallama har kofar gida suka kaita,, sannan suka juya
Bayan shigar ta gida tayita kokari ta danne damuwarta, dan ko mama bata fahimta ba Tun karfe tara najeeb yakira ta Dan hatta mance da abunda yafaru da rana hira sukasha sosai daga nan Sai kusan 10:30 sukayi sallama Dan anty hajja ta hanata wayan dare sosae.
Wayanta tasauka tahau bincike a iya bincikenta bata samu wata masaniya akan wannan mutumin da akeson kashewa ba,,, Haka bacci yadauketa da taradda din wayannan mutane
Baccine mai cike da mafarkai kala kala,,,, Akarshe ne tayi mafarkin wannan mutumi wanda awancen lokacin tayi mafarki ya harbi najeeb,,,, Ya gurfana agabanta yana kuka amma takasa jin abinda yake fada Ahaka tafarka cikin tsoro Amma hankalinta baikai na wancen karan tashi ba waigawa gefe tayi taga anty hajja nata sharar bacci itada yaranta Mata biyu Aisha (mammii) mai sunan mama Sai halima Wanda taci sunan yayar babanta Sauka tayi tanufi toilet tadauro al'wala salla taringa yi tana neman zabin Allah saikusan uku bacci yadauketa akan sallayan
Kiran sallan farko ne yatasheta tatashi takara dauro al'wala taga batar da sallah Sannan tatashi anty Dan itama ta gabatar da nata sallan,,,,,,, koma wa tayi ta kwanta nan da nan wani bacci mai dadin gaske yayi awon gaba da ita
Kamar a afarki taringa jin muryarsa a cikin bacci komadda idanuwanta takarayi tarufe can kaman Wanda tatuno wani tayi saurin mikewa tayi cikin falo aguje tana ihu,,,,,
To be continued
_Ur's_ _Z33yyb3rw3r_
BIBIYATA AKEYI
Bismillahirahmanirrahim
Writting by © _zaynab_ _bawa_ ( _z33yyb3rw3r_ )
Page 14
*
Falo tayi da gudu, tana zuwa kuma tatsaya da mamaki dauke a fuskar ta,,,,,,,,, Juyowa sukayi suka kalketa,,,,,,,, Aikaman jira takeyi takarasa dagudu ta rungumeta,,,, Cikin farinciki itama ta rungumeta,,,,,,,, Muryar sane ta daki dodon kunnu wansu,,, Oh ni tunda ba'a murnar ganina Sai in koma saurin saketa tayi ta riko hannunsa,,,,,,, Yaya ba haka bane fah,,,, rausayar da kansa yayi!!!!!!!! Toh meye Idan ba haka bah!!!!!!! Kankantar da murya tayi,,,, yaya please OK ya wuce,,,,,, Saurin sakinsa tayi tunowa da tayi bafah muharraminta bane,,,,,,!!!!! Ankuma yafada acikin zuciyar sa,,,,,,,,,,, Zama sukayi nan tadi ya barke tsakanin yan uwan da suka dade basuga juna bah,,,,,,, Hira sukeyi sosai har ma ta manta tanada lecture's Can wayan ta ta dauki ruri,,,,,, Tana kallan mai kiran saida gabanta ya fadi,,,,,, Alokacin ta tuno tanada lecture's Saurin daukan wayan tayi,,,,,,,,,,, Beb wai me kikeyi a gida ne tun 9 fa muka shiga lecture's kuma zuwa 12 zaiyi test ai batasan lokacin da taduro akan kujera ba,,,,,, Daki tawuce tashiga wanka batafi 15minute ba tafuto,,,,,, Shiryawa tayi cikin blue da red din atampha,,,,, Bakaramin kyau tayi ba sannan ta dauko ribbom tayi parking kanta,,,, duk da gashin kanta bai cika tsayi ba Amma Idan tayi kitso yakankai kafadunta, cikan da kanta ke dashi ne yakan hana kallan tsayinsa sosai,,,,,, Cikar da gashin ke dashi ne yasa da tayi parking yataso kamar Wanda tasa ribbom na acuci,,,,,,,,,,,,, Dankwali tadaura sannan tadauko khimar dinta dogo sosai ta daura,,, Sannan tafesa turare mai sanyin kamshi wanda saika matsa kusa da ita kafin kaji kamshin,,,,,,,,, Takal minta ta dauko plat dake tanada Dan tsayi yasa tayi dass dass gwanin sha'awa,,,,,,,
Futowa tayi dauke da side back dinta mai tsadan ba jebbu ba,,,,,,, Dan mama da yayunta na kokari wajen sayamata kayayyaki masu tsada,,,,, Tsugunawa tayi tasauko phone dinta da tabari akan kujera,,,,,, Juyawa tayi ta kalli kujeran da hameedah ke zaune,,,,, subhanallah wani irin kama naga sunayi da wannan yarinyar wanda bazasu wuce sa'anni ba Sai tsiran da bazaifi na months ba,,,,,
Tabbas suna kama saidai bambamcin da baza'a rasa ba,,,,,,,,, 6s muje koh,,,,,, Muje inahh???? Skull mana kinsan ai tunda kinzo toh tare zamu,,,,,, Dan bawani uzurirrikan da zandauka,,,,, Tashi tayi suka dugun zuma kitchen dan yiwa mama Sallama,,,,,, me nake gani badai wani wajen daku je ba,,,, *_Hanna_* tayi saurin karfe zancen,,,,,, Ehh mama school zamuje,,,!!!! Amma ai kyabarta tahuta yanxu fa isowarsu daga kano,,,,, Ko ruwa batshaba balle wani abinci,,,,, Zamuci a makaranta tafada tareda jan hannun hameedah,,!!!!!!
Saikusan 11 suka isa makarantar,,,,, kiran amira tayi sukaje yanda take suka sameta,,,,, Gaskiya Beb kuna kama da 6s dinki sosai,,,, Harya wuce yanda kike fada,,,, saidai tafiki kyau tafada tareda kashe Mata idoh daya dukan wasa *hanna* takai Mata kinfiye sa idoh kekam kinji jiki,,,,,, Kyaleta kawai dannasan tafada ne kawai kowa yace kinfini kyau Dan idanuwanki yafi nawa girma kuma kinfini dogon hanci Cewar hameedah!!!!!!! Dariya sukasa kede kawai kin tsorata da wayan nan idanuwan tanne amma bawani kyawun da ta fiki,,,,,
Beb bamu karya bafa,,,, lallai bakida hankali kikabar bakuwa da yunwa harara ta galla Mata wacece bakuwar,,,,,,, Ninaga alama in muka biyeki Sai munrasa test dinnan,,,,, Uhm kawai amira tace sannan suka nufi hanyan _barhakkk_ dake gefen hostels na school din danyin breakfast,,,
Sanda sukeyi ordering kafin suka zaune tadi sukeyi wanda zaka rantse amira sundade da sanin juna da hameedah!!!!!!!!!! Dan duk su ukun bbu baya wajen surutu!!!!!! Wayan *hanna* ce tadauki ruri jin kidan yasa tasan wa yake kira Dan ringing dinsa dabanne,,,,, Daukan wayan tayi,,,, sannan tajuya gefe da gefe aikuwa caraff idanuwanta ya sauka akansu,,,,,,,,,,, Saurin juyawa tayi sannan takara wayar a kunnenta,,,, Hellow°°°°sweety Na'am kina school ne????? Eh!!!!! Ina zuwa yanxu kijirani Haka kawai ta tsinci kanta da faduwar gaba!!!!!! No plx karkazo,,,,, karnazo???? Dalili????? Shiru tayi tafara kame kame '' ''''''''hmm dama nasani baki da wani abinda zakice nadade da fahimtar bakya sona nikadai nake hauka akanki,,,,,,,, Tabbas kina shirin jefani wani hali Dan har ikika gujeni mutuwa zanyi plz karki barni nizan koya Miki yanda zaki soni Amma plx karki rabu dani yafada cikin sarkewar murya,,,,,,
Wani irin tausayinsa da sansa ne suka kara ninkuwa cikin zuciyar ta!!!!! Mekaki fadi haka kasan Nima bazan iya rabuwa dakai ba To meyasa bakyason muhadu????? Kijirani agidan anty Idan nafito a lecture's zanzo,,,,,,, OK bye luv u saurin katse wayan tayi dan bazata iya bashi amsa ba,,, tadaga wayan akunnenta tana murmushi,,,,,
Zuba Mata idoh sukayi kaman wanda tayi wani abun,,,,, meye hakan da'allah kun wani tsareni da idoh kaman tsoffin mayu,,,,, ko gizau basuyi ba sukaci gaba da kallanta hameedah harda karawa da tagumi,,,,,,,, Amma cikin ranta wani dadi takeji na ganin yar uwarta tasamu masoyi,,,,,,,,,,,,,,,,, Tsaki taja sannan taci gaba dacin abincinta,,,,,,,,
Waye shii?? Cewar hameedah najeeb tabata amsa atakaice yatsine fuska amira tayi "" ""sannan tace zaiyi yabari afusace da dago bangane me kike nufii ba cikin bacin rai!!!!!!!!!!
To be continued
Ur's z33yyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
Bismillahirahmanirrahim
Writting by © _zaynab_ _bawa_ ( _z33yyb3rw3r_ )
This page is Dedicated to u___anty rash wish u success in your exams
Page 15
*
Ni na tabbata akwae wanda yarigashi kuma haka kawai zaizo yayiwa wani wucel aiba haka akeyiba Cikin bacin rai *hanna* tace toh saiki mutu Amma aure kam na auri najeeb angama saikuje kuyita haukanku keda su Tajuya gun waynnan mutanen ta maka musu harara,,,,, Jan jakarta tayi tana shirin barin wajen Saurin riketa hameedah tayi sannan takalli amira ku fahimtar dani mana har yanzu bawai nagane yanda kuka dosa bane
Juyar da kanta *hanna* tayi tarike kugu tana karkada karkada jikinta ida adole ranta ya baci Dakyar suka shawo kanta ta zauna Dan Sanda amira tabada hakuri tukunna,,,,,,,,,,,,,,,,, Labari suka fara bawa hameedah ba abinda suka boye Mata tass suka kwashe komai suka fada Mata,,,,, Ai nan da nan idanuwan ta sukayi jawur,,,,, Kai Amma wannan Ammah nan anyi tsinanniya na tabbata da umma(mamar hameeda) tasani Sai ta Mata tass tass ai tasanta Ke matar wan mahaifinki kike tsinewa,,,, ai wallahi Sai na Mata tsiya tunda ba yanxu zan tafi ba ai zata gane kuranta,,,,,,, adai Mata sassauci sukace tareda tuntsirewa da dariya,,,,,, Amma kinsan me ni Allah banga laifin amira ba Nima inaji kaman akwae wani alkairi a tattare da waynnan mutanen tafada tareda kallonsu ta kasan idoh,,,,, Harara *hanna* ta galla Mata da'allah malama rufa mana bakii!!!!! Amma kinsan me kemafa banga laifinki na zurfafa ason najeeb ba danna tabbata gayan yayi danke ko akaya baki zaben jebbu!!!!!!
Kallan wayanta tayi subhanallah ke time din test yawuce,,,, Wani test kum``````saurin rufe bakinta tayi da tafukan hannunta tunowa da tayi karyar data shirga mata dazu
Kallo mai cike da tuhuma *hanna* tayi mata,,,,,,, Sorry Beb Allah narasa yadda zanyi kizo Skull ne nadau zancen jiyannane yahanaki zuwa shiyasa,,, Dakiyi ma yafi haka,,,, ita kuwa hameedah banda dariya ba abinda take musu
Fita sukayi ta niyyar wucewa gidan anty ai kuwa acan suka sami najeeb Dan zumudin ganinta bayan sungaisa da najeeb dinne,,,,,, Suka shige suka barsu su kadai itakuwa anty murnar ganin yar uwarta hameedah yasa ta manta dasu,,,,,
Soyayya sukasha kaman bbu gobe kamar karsu rabu saidai duk wani Soyayyar su sukanyi ta cikin sanin yaka mata Dan basu taba goce hanya duk wani abinda addini yahana basa yinshi Domin albarka Soyayyar suke nema,,,,,,,,
================
Dubai
Kasar dubai aranar yau tatashi cikin wani irin cikowar mutane sakamokon taron kasa da za'ayi gobe MG kokadan baysamu lokacin kansa ba danko lokacin cin abinci bai samu ba sakamokon yadda garin yake makill da jama'a yanata kokarin yadda zaikare lafiyan al'umma Garin acike yake Dan manya manya sunfara suka duk wani waje da kuka sani nacikin Kasar Dubai acike yake Dan bakinmu na Nigeria a wani katon estate yasauke a _emarr_ _sidra_ _hills_ _eatate_ Inda sarakunan larabawa kuwa sunsha karrama ansauesu a _arabella_ _town_ _houses_ Wanda wasu da yawancin su sunje ne Dan yawan bude idoh Dan dubai kasaace Wanda taci gaba sosai afadin duniya Shirya sojojinsa kawai yakeyi inda bayaso asamu wata matsala awannan taron Bakin Nigeria sun isoh Wanda suka hada da manya manyan yan shiyasa aciki kuwa hadda wanda suke neman rayuwarsa,,,,, shikuwa yananan yana shirin kare tasu rayuwar
Sanda yaje airport yataresu yasada su da masaukin su sannan yawuce zuwa wani wajan Dan taran wasu shuwa gabannin Dan kowani shugaba burinsa daya yakaaance MG yana daya daga cikin masu taryan sa awannan lokaci
Har kusan tsakiyan dare MG baisamu hutu ba dakyar su captain Ahmad sika yakiceshi Dan yasa mu hutu,,,,,
Futa sukayi suka shirya masa motoci 9 hadu na bayansa hadu na gaban sa Sai kuma tashi atsakiya,,,,,,, Captain Ahmed ne yake tuki gefensa kuma daniel ne Wanda Shima MG ya yarda dashi sosai Dan yanada rikon gaskiya shiyasa Har yabarshi yashiga jikinsa sosai
Koda suka isa gida daniel ne yayi saurin fitiowa ya bude masa kofa fita yayi cikin takun sa nakasaita Wanda ko ba'afada ba kasan jinin sarauta ne
Kai tsaye cikin gidan yanufa,,, Kowani soldier yazauna awajan tsayuwar sa captain Ahmed da daniel ne suka rufa masa baya hannu yadaga musu alamun su tsaya sannan yacewa captain Ahmed yabiyoshi akwae sakon dayakeson bashi bbu musu daniel yatsaya shikuwa captain ahmad yabishi abaya Dan karban sakon
Bayan shigansu ne daniel ya cije libs yarasa me captain Ahmed yafishi da MG yake nuna bamban ci atsakaninsu Kuma hakan Yana matukar yimasa zafi aransa Amma ya alakanta hakan da bambam cin addini dasuke
Abinda be saniba shine duk cikin sojojin MG yafiji da Ahmed duk da yafishi agirme dakuma matsayi hakan bai hanashi zama yayi shawara da, Captain Ahmed ba
Tunda yashiga yariga da yasan ummii tayi bacci to baibi takanta ba,,,,,,,,,,, abinda baisaniba shine ko karfe nawa zekai nadare ummii,,,, saitaga dawowanshi dake iya runtsawa sake labulen dake hannun ta tayi sannan taje ta kwanta,,,, koba komai ranta yayi dadi naganinsa cikin kwanciyar hankali,,,,, bandaki yawuce ya watsa ruwa baifi mintuna kadan da kwaciya ba bacci yadaukeshi,,,,,,,,,,
Asuban fari ya farka wani irin mummunan faduwan gaba yatashi da ita Wanda yarasa dalili wanka yayi ya shirya cikin kakinsaa mai fitar da ainihin kyawunsa da cikar zatinsa
Dakin ummii yawuce yasameta tana bacci baiso tada ita ba hakan yasa yajuya yatafi Amma irin wannan taron yaso ace yafita da addu'ar mahaifiya akansa,,,, Sanda suka tsaya amasallaci musulmen cikin suka gabatar da sallah kafin suka nufi burj al'arab hotel din da za'a gabatar da taron
To be continued
Ur's Z33yyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
Bismillahirahmanirrahim
Writting by © _zaynab_ _bawa_ ( _z33yyb3rw3r_ )
_ _This_ _page_ _is_ _Dedicated_ to _u_ :: *hajja* *_ceh_* * _kece * * _mutum_ * *ta* farko _datafara_ _bani_ _kwarin_ _guiwan_ _rubutun_ _littafi_ _tanks_ _alot_ _I_ _luv_ u _so_ _much__
Page 16
*
Sai wajan karfe uku 3:00 sannan suka bar gidan anty,,,,,, Amira ta wuce gida suma suka wuce gida,,,,,,,, Bayan isansu gida sunyi sallar la'asar wani sabon hira suka dasa Kai sis wallahi najeeb ya hadu wani farr tayi da idoh duk farin ciki ya cikata anyabi abin sonta Allah koh tace,,,, eh mana kunyi bala'in da cewa Saleem ne yashigo kanin *hanna* anty hameedah wai kizo inji Ammah yafada yana kallon wayarta,,,,,,,,,, Kai meye kawani zubawa wayarta ido da'alllah fice kabawa mutane waje,,,,,, Kai sis kinfiya takura Ina ruwanki kokuma wayarki ya kallah zonan Saleem karba,,,,,, Zuwa yayi ya tsaya medakayi da phone din sosa keyarsa yayI game yafada atakaice karba katafi,,,,, itakuwa *hanna* murmushin dakisan waye Saleem tabita dashi,,,,,,,,
Ke wai ba Ammah ne kekiran kiba kikatsaya yatsine fuska tayi kyaleta kawai bawani akyaleta tashi muje,,,,,,,, Nasan wani abin take nema Sai kiji dadin bata amsa,,,,,,,,,,,,, Mikewa tayi suka nufi dakin Ammah Suna shiga suka sameta itada yaranta rabi'ah da hafsat suna zaune Afalo Sallama sukayi basusami amsawa hakan baida mesu ba suka zauna,,,,,,,,,,,, Juyowa tayi ta kallesu gidan ubanki ne nan dazaki isoh tun safe bakizo kin gaishe niba,,,,,, Maciya amana ko yanzu kuma dawani cin amana uwartaki ta aikoki,,,,,,
Ko uwarki bata isa tazonan gidan,,,,, tanuna batasan inanan ba,,,,, Balle ke karamar marar kunya,,,,,,, Iya bacin rai ransu yakai kololuwa wajan baci,,,,, Hameedah ce cikin bacin rai tabude baki zatai magana s damke hannun ta *_hanna_* tayi da karfi kallon ta tayi ta girgiza Mata kayi kawar da kanta tayi cikin takaici na hanata ramawa da *hanna* tayi
Juyawa tayi ta fuskanci Amma kingama akwai Abu me mahimmanci da mukeyi tafada hadeda wani murmushi wanda Ammah takasa tantance namiye shi,,,,,,,, Sake baki tayi Dan uwarki aibake nakira ba,,,,, Rashin kunyan ki haryakai ki Har yakai agaban idanuwamu kiyiwa mahaifiyar mu raini,,, Hafsat ce tatashi da niyyar dukanta,,, Ammah tahanata kull karki tabata kibarni da uwarta zanyi ni, Jan hannun hameedah tayi wadda ga baki daya ji take kaman ta fashe tsabar bakin ciki,,,,,,,,, Janta tayi Har sunzo bakin kofa Ammah tace shegiya mai bakin jini,,,,,, Saurin tura hameedah waje tayi tadawo cikin dakin wani kallon kaskanci tabi hafsa dashi,, Wato kece Har zaki dakeni ko tabani wallahi saina miki shegen duka,,, Sannan tajuya gun Ammah da gabaki daya al'ajabi yahanata cewa komai,,,,,, Idan Har zaki iya duban idona kice mun mai bakin jini kamata yayi ki fara aurar da nagabanki wanda duk cikinsu bbu wacce bata bani sama da shekara ba tukunna kisamo bakin gori,,,,,,,,,
Tana fadin Haka tajuya tafice tabarsu cikin jimami Samin hameedah tayi tsaye tana jiranta a bakin kofa,,, dayake taso biyota Amma takulle kofan,,
Murmushi tabita dashi saurin kawar da kanta tayi tafice fuuuuuuu Binta *hanna* tayi abaya Har suka shiga dakin mama ganinsu Ahaka yasa anty takirasu tana tambayarsu,,,,,,,
*Hanna* taso boye Mata amma hameedah takwashe komai yafada mata ran anty yabaci Amma Sai ta danne kawai Dan yanada kyau tun yanzu afara koya musu yin hakuri kafin auransu
Ahaka yaya jalal yashigo yasamesu, Kallon *hanna* yayi wai Ina kuka shiga ne kam tun safe,,,, gidan anty fa mukaje,,, shine ba gayyata yafada tareda zama kan kujera,,,,, yaya daga makaranta fa muka wuce,,,,, Haka suka zauna sukayi ta tadi Dan Har sunmanta da bakin cikin da Ammah ta durka musu
Sallar magrib ne ta tashe su sukayi sallar suka dawo akasake sabon hira,,,,,,,,,,,,,, Saikusan 9:00 najeeb yakirata suka sha soyayyarsu sanda tafara jin bacci kafin sukayi Sallama takwanta Dan hameedah ta dade da bacci,,,,,,,,,,,,, Irin mafarkin jiya data karayi ne yatashe ta,,,, Tarasa me wannan mutumi yake nema da take kallonsa gurfane agabanta,,,,,,,,
Datarasa mafita kawae ta dauro alwala tagiba dayin nafila Har bacci yadauketa,,,,,,,,,, Har ta makara a sallar asubahi Sai wajen 6:30 ta tashi tayi sallah Tunda ta farka ta tsinci kanta cikin wata irin matsanan ciyar faduwar gaba Gabaki daya Tanaji kamar akwai wani abunda ke damunta amma tayi duk iya tunanin ta tarasa dalilin damuwar tata
================
Taro yayi iya Taro Dan duk wani manyan duniyar nan sun halacci wannan Taro Amfara gudanar da taro komai na tafiya daidai Ina tawajan MG haryanzu faduwar gabansa tsananta takeyi
Duk wani tsaro daya kamata awajan antanadar Inda layin da MG yake zaune layin manyan mutane ne wayar sace tadauki ruri ganin yanda wajan yake a cike yasa yatashi dan amsa wayar, mahaifinsa ne yake kira yasa bazai iya kindauka ba
Kokarin fita daga wajan dayake yake niyyar yi soldiers suka taso Dan bin bayansa daga musu hannu yayi alamun su koma,,, Bamusu suka tsaya inda captain Ahmed yabi bayansa,,,,,,,
To be continued
Ur's Z33yyb3rw3r
*BIBIYATA AKEYI*
_Bismillahirahmanirrahim_