Kenza eBookz

Boyayyen mutun complete - Chapter 27

Boyayyen mutun complete - Chapter 27

Boyayyen mutun complete Chapter 27: Boyayyen mutun complete Chapter 27. Maida wayar tayi jaka ta tashi tsaye tadau jakanta tana kallon Nadeera da hankalin…

2,716 words

Maida wayar tayi jaka ta tashi tsaye tadau jakanta tana kallon Nadeera da hankalin ta yay nisa sosai kan duba kayan tace "Princess bari nai magana da mijinki kinji" tashi tayi tsaye tanabin handbag din data dauka da kallo tace "ina zaki Mum" tai maganan idanunta na ciccikowa da hawaye, dawowa kusa da ita Mum tayi ta zauna agefen ta ta rungumeta tareda mata kiss a forehead sanan ta dauko magungunan data kawo mata tace "ki dinga shan wanan everyday da yogurt morning and night maganin kine, make sure kinsha am coming zanje na duba jikin yayan ki ne, zan sake dawowa na dubaki kinji" girgiza ma Mum kai tayi ta rirriketa tafashe da kuka sosai tace "Mummy dan Allah kitafi dani zanbiku Canada din, Mum bansan kowa anan ba, dan Allah karki barni kinji Mummy na" tafashe da kuka sosai, hawayen datake yi Mum ta share cikin lallashi tace "Princess look kinriga kinyi aure, Abban ki yariga yamiki aure banda iko dake yanzu dole ki zauna ki rungumi mijinki kiyakuri kinji Princess" fashewa tayi sosai da kuka tace "Mummy mesa Abba yamin haka, mesa yakemin abinda yakemin menama Abba ne? Mummy am tired wlh ni nagaji da komi da kowa I hate myself I hate my life I just wanna di...." da sauri Mum ta taushe mata baki tace "ke bakida hankaline, komi daya faru kaddara ne kimanta da komi saisa nan yafi miki tayanda Abba bazaima kara ganin kiba, yanzu share hawayen ki zansa abaki waya zamu dinga waya kullum and zan dinga turomaki abubuwa kina amfani dasu" share mata hawayen tayi sanan ta tashi da sauri tai hanyar kofa da gudu Nadeera ta mike tabita tafada jikinta ta kankameta ta kurma uban ihu da saida yafito da Marwan dasu Abdallah, kara kankame Mum tayi tana kuka tace "saikin tafi dani Mummy, dan Allah kitafi dani Mum, nagaji da rayuwa baki, to naji naji kizo ki zauna dani anan karki sake tafiya ki barni I don't know them" ta nuna su Marwan da hannu dake kallonta, tafashe da kuka, sosai take neman karya zuciyar Mum da kyar ta dago jajayen idanunta ta kalli Marwan tace "please zoka kaita daki Marwan, I have to go yayan su ya farka a asibiti" wani irin kankame Mum tayi tana kuka sosai tace "inkinama Allah Mummy na kitafi dani zan biku chan Canadan, nima inaso naga Ya Muhsin din please Mummy na kitafi dani" cikin wani irin raunanniyar murya Mum tace "dan Allah kidena kuka haka Princess ke yarinya ce wai, nace zan dinga zuwa and zamu dinga waya okay, gayan uwanki nan zasu kula dake" makema Mum kafada tayi cikin kuka, ahankali Mum ta dagota daga jikinta tana share mata fuska tace "to shikenan, naji" daidai nan taji an wani irin rike mata hannu kafin ta ankara ya fizgota yasata ajikinshi ya rungumeta da karfi ta yanda ko motsin kirki bata iyayi, aiko tafashe dawani sabon kuka tana mikama Mum hannu, murmushi tamata tajuya da sauri ta sauka kasa, bin bayanta Omari dazai mayar da ita yayi zuwa kasa, wani irin fashewa tai da kuka tana kwalama Mum kira kaman zata tsaga gida. "Mummy Mummyna" jijjigata ya shiga yi kafin yabude kofan dakinsu ahankali ya shiga da ita yay kan gado da ita ya zaunar da ita yana kallon yanda take kuka ko ina na jikinta na rawa, wani irin kwantar da ita yay kan gadon yahau ya janyota kan jikinshi ya daure fuska tareda daura yatsanshi akan lips dinta ahankali yace "kimin shiru" gyadamai kai tayi kaman wata marainiya hawaye na fitowa daga idanunta, rungumeta yayi yace "kinajin yunwa?" girgiza mai kai tayi cikin kuka mara sauti da sauri yace "mekika ci?" bakinta na rawa tace "dognut and..and dambun nama" "Mum takawo miki?" yay maganan yana sharce hawayen dayake gangaro mata, gyadamai kai tayi ahankali yay murmushi yace "Nima zanyi tafiya zaki bini Oman naje dake?" girgiza mai kai tayi tana kwalla kuka nacinta sosai amma yaki bari tayi, lips dinta dake rawan kuka yama kiss mai kara ya saki yace "why? Mesa bazaki bini ba? Are you scared?" gyadamai kai tayi, shiru yayi yana kallonta son ta namai wani irin Kane Kane azuciya, ahankali yana shafa wuyanta yace "kinfison kibi Mum kihadu da dat goat, you want him to molest you again?" girgiza mai kai tayi tafashe da kuka sosai dan ya mugun tuna mata da Abba, hannu yasa akan lips dinshi idanunshi sundan chanza kala yace "kinason dat goat yay raping dinkine?" girgiza mai kai tayi hakan yasa ya taba inda ya kumbura a fuskanta yace "kin kalli Mirror yau have you seen abinda yamiki?" kasa magana tayi tana kuka hakan yasa yadan fuzar da iska yace "stop crying and sleep bakida lafiya" gyadamai kai tayi jikinta na rawa, hada goshinshi yayi da nata yana kallon fuskarta ahankali yace "is okay stop crying, maisa bakisan gidan nan?" bakinta na rawa sosai tace "s..sabida gidan daji ne" kafeta yayi da ido yana kallon yanda kirjinta kewani irin bugawa yadan fuzar da iska yace "in chanza miki gida?" gyadamai kai tayi da sauri, murya chan kasa yace "ina kikeso na maida ke?" ahankali tace "cikin gari" hanunta yakama yahada da nashi yace "okay done! Wat else kikeso?" bakinta narawa tace "and...and st.." tai shiru, lips dinta nakasa yakama yana shafa bayanta batare daya sakiba yace "and wat?" raurau tai da ido tace "stop wearing mask" shiru yayi yana kallonta saikuma yay murmushi yahau yimata wani irin kiss kaman zai cinyeta da kyar yasake ta ya kalleta yace "you've changed me Rahma" kallonshi tadanyi kafin ta lumshe ido tana breathing heavenly bakinshi ya daura a kunenta yace "am sleepy make me sleep my amarya"....

*** Ahankali Abba ke bude ido akan gadon asibiti acikin hadadden dakinshi, anamai karin ruwa ansaka plasta a kasan hancinshi inda yafashe, da kyar yakarasa bude ido yana kallon saman dakin yabude baki cikin sambatun ciwo yace "why are you stubborn mana Princess? Kimin shiru anan, oya kamamin, kinfi maman ki dadi wlh Princess, kinfi maman ki zaki da komi, wayyyooo Princess kamamin, you're bless princess" wani iri iri maganganun ke fita daga bakinshi sabida hakoran shi biyu nagaba dasuka fita, sake bude bakin yayi ahankali yace "Princ..." afirgice yawani irin yunkuro zai tashi ya ware idanun tangararas yana kallon ko ina yana dafe kirjinshi dake wani irin bugawa komi na dawo mai, daidai lokacin wani Dr ya shigo dakin da stethoscope a hanunshi, binshi Abba yay da kallo harya karaso gaban gadon, Dr yace "barka da tashi Alhaji yanzu meke maka ciwo?" cikin tsananin fushi Abba yanuna shi da yatsa da maganan shi dabata fita da kyau yace "waya kawoni nan? Wata farar mata mai suna Hajara ce takawo ni halan? Ashe dama tasan inda Princess take, ashe Hajara tamasan wanda ya dauke Princess dan ai tare na gansu, Hajara kin cuceni kin cuci kanki kuma kin tsokano tsuliyan dodo" ya dago kai ya kalli Dr cikin kunan rai yace "nawane hakorin roba? Koma nawane akawo asamin original one din wanda baya kama da hakorin roba shinake so, zo tugemin wanan karin ruwan zanje nemo yata, yauwa kiramin kwamissioner ina wayana wai?" yahau waige waige yana dube dube akan gadon, sake kallon Dr yayi ganin bai ciremai karin ruwan ba yace "nace kazo ka cire min, tafiya zanyi wani ya gudun mun da y'a, shiyamin ma wanan dukan yanaso ya kasheni yarabani da y'ata" ahankali Dr yace " calm down Alhaji bazaka iya tafiya ko inama ba, bakada karfi, an mugun dakanka a ciki, da kyar muka shawo kan matsalan amma dudda haka wall din stomach dinka are very weak, dole you need to relax and heal, am advising you not to go anyway for now, ka kwanta yanzu zan kira dietician Dr zaizo yay examining dinka saiya sa akawoma abincin daya kamata kaci, zai kuma bama kitchen time table din abinci daya kamata kaci, bazamu iya sallaman ka yanzu ba koma menene za'a kira kwamissiona saisuyi handling everything za'a ga yarka in sha Allah" yanda yake maganan calmly trying to calm the patient down ammq Abba baisan wanan ba, ihu Abba yayi yace "kace am not strong kana nufin ni tsoho ne kome?" ya nunashi da yatsa yace "kai likita, kai likita kasan wacece Princess a rayuwata kuwa, she's my baby girl, my innocent baby girl, my chubby baby girl, my one and only baby girl, I can die for that girl kai, kawomin discharge against medical advice form lemme sign bazan iyaba, bazan iya zamaba princess na hanun wani kato Allah kadai yasan meyake mata, bakaji zuciyata bane yanda take suya, rashin ganin princess da sanin inda take, da tunanin me shegen nan kemata shizai fara kasheni ba wanan ciwon ba, Dr ka sallameni and give me drugs I can manage" yay maganan yana sauke ajiyan zuciya saikuma ya nuna kanshi da hannu yace "ni, ni wani kato ya daka kan yata? Ni dinan, niya zubar ma da hakora kan yata, ai wlh idan na yarda shege nake yanzu zan nunama koma waye shegen nan wanene ni, zan nunama waye Naseeru, badai you want to bring the monster in me out ba, am out and babu abinda zai iya containing dina, zamusa kafar wando daya dakai, kamoka da ganinka kuwan saidai idan ba'a Abuja yakeba amma ko'a takashin Uwatata ya buya wlh saina nemoshi" ya buga gado da hannu yana kwafa, juyawa Dr yayi yafita daga dakin ahankali tunanin kodai harda kai ya bugu ne, dan Alhaji doesn't seems normal. [10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *Karki karanta in baki biyaba*

*Maman Abd Shakur*

*A3*

Adaidai lokacin nurse din ta shigo da gudu tana gunguro defibrillator din ta tsaya chak agaban gadon tana karanta machine din dake hade da gadon Muhsin tana kuma kallon patient din da idanunshi suka koma sama, daga kai tayi ta kalli Dr din da ahankali ya zame hanunshi daga kan kirjin Muhsin ya dagokai ya kalli nurse din tareda girgiza mata kai yakai alamun bashi kuma, hannunshi ya daura kan fuskarshi Ya Muhsin ya rufe idanunshi ahankali tareda jan farin bargon gadon yarufe shi ya juyo ya kalli Abba da Mum dake wani irin numfashi da sauri da sauri sunyi suman tsaye ko kyafta ido basayi kallon Muhsin da aka rufe suke ba kakkautawa, cikin tsananin fushi Dr ya kalli Nurse din yace "get his folder from my office time of death 4:30PM" ya kalli Abba da Mum da babu wanda ya iya wani kwawkwaran motsi cikin su yace "I hope you guys are happy now kun kashe danku" yay pointing Mum da yatsa yace "I made it clear to you ranan dakika zo office dina cewa yaron nan bayason any type of hayaniya, bayason damuwa karku, bayason tashin hankali, karku daga mai hankali kark..." bude kofar dakin akayi hakan yasa Dr yadaga kai ya kalli kofan Ahmad ne ya shigo kaman wani abu ya wurgo shi idanunshi sunyi jajir yabi su Mum da yaga fuskarta akumbure da jini da kallo kafin ahankali ya juyo da kanshi ya kalli gadon dayaga an lullube Ya Muhsin da bargo harkai.

Tsaki Dr yayi cikin bacin rai yace "da girman ku, da girman ku, manya daku xakuzo kuna dambe agaban danku mara lafiya, a hospital for dat matter, ku yarane? You guys are very very selfish my God, anyways the damage has been done already, kuzo kuyi clearing komi kokuma nan da 10min zan aiko awuce dashi mutuary" yajuya yabi ta gefen Ahmad dako motsi yakasa yana kallon Muhsin dake alullube, fita Dr yayi hakan yasa Ahmad yadaga kafa ahankali kaman mai matsala a kafa yakarasa jikin gadon ya tsaya chak kafin ya mika hannunshi dake rawa sosai ya daura akan bargon yaja kasa nan yaga fuskar Muhsin da zufa kekan goshinshi idanunshi a lumshe, wani irin faduwa yayi akan guiwowinshi kaman mara lafiya ya fashe dawani irin kuka ya daura kanshi akan gadon yace "innalillahi wa inna ilahi raji'un, Ya Muhsin! Ya Muhsin! dan Allah karka tafi ka barni ni kadai dawayanan mutanen we called our parents, Ya Muhsin you are my strength, my support system, my guardian please wake up, am sorry is my fault, is all my fault, na fita nikadai na barka tareda mutanen nan, Ya Muhsin dina!" yawani irin tashi yana jijjigashi amma ko gezau, fashewa yay dawani irin kuka yama kasa magana da kyar ya iya dago dakai ahankali hawayen dayake suna diga ajikin Ya Muhsin yaja bargon yarufe shi back yana tofamai addu'a kafin yawani irin juyowa cikin fushi yatako har zuwa gaban Abba dake kallonshi jiki asake yace "Alhaji Naseer Aluminum!" saida zuciyar Abba tawani irin girgiza sabida yanda dan cikin shi ya kira sunanshi kai tsaye haka, wani irin kuka kecin Ahmad da kyar cikin kuka ya iya yay magana. "karka, never in your life call me your son, kaiba mahaifina bane, I regret ranan danazo duniyan nan amatsayin danka, na tsanake na tsaneka sosai, I hate you, and kaje sai Allah yamana hisabi dakai kashemin dan uwana dakayi bazan taba yafema ba!" zaro ido Abba yayi yana kallonshi idanunshi sunyi jajir yarasa ta cewa, yajuya ya kalli Mum dake wani irin kuka kanta akasa yace "and you Mum, am so so disappointed in you, kome Mutumin nan zai miki saiki biye mai? I tried talking to you but kince namiki shiru nabarki kiyi magana and vent out your anger, that you are tired, so yanzu you've vented your anger kinyi son ranki danki kuma yarasu kun kasheshi da bakin cikin ku are you happy now? Are you happy Mum? Are you satisfy? Kozaki cigaba ne?" yay maganan yana kuka sosai, girgiza mai kai Mum tayi cikin kuka sosai kaman zata mutu, hannu Ahmad ya daga yana musu clapping yana hawaye yace "wow, wow, wow you guys deserve an award na kashe danku" yajuya dawani irin sauri cikin fushi yafita daga dakin dan zuwa clearing everything ya tafi da wanshi gida, da kyar cikin kuka Mum tadago kanta ta kalli Abba da shima ita yake kallo da idanunshi dasukayi kaman an jijjiga bera a buta tsabagen fitowa, atare sukai wurin gadon suka tsaya, cikin kuka sosai Mum ta kalli Abba tace "Alhaji danmu, Alhaji Muhsin, my son da gaske ya mutu Alhaji?" tai maganan kaman zararra tana janye blanket din daga fuskarshi tana wani irin kallon shi tana kuka, kallon Muhsin din Abba yayi gabaki daya kanshi ya kwance yakasa furta komi sai zaro ido dayake yi gabanshi na faduwa, bude kofan dakin akayi Ahmad da idanunshi sukai jajir ya shigo dawani abokinshi Bello dauke da makara dakuma babban tabarma, wani irin nishi Abba yafara yi yana kallon Ahmad din dako kallon inda Abban yake baiyiba suka ajiye komi akasa yazo ta gaban gadon shida abokinshi zasu dagashi da sauri Abba ya mika hannu zai dagashi Ahmad yamai wani irin kallon da idanunshi dasukai mugun jajir saida gaban Abba yafadi ahankali ya janye hanunshi ya maida kirji kaman mai shirin yin salla yana kallon Ahmad din, Ahmad da abokin nashi sukadau Ya Muhsin suka sakashi a tabarman suka sakashi a makara suka dauka suka fita daga dakin Mum nawani irin kuka tabisu da gudu Abba ma yabisu da sauri ko kallon su Ahmad baiyiba suka sakashi cikin motan ambulance din asibitin dasukai haya suka shiga kafin Mum dake kuka sosai da Abba su iso yawani irin rufe motan yacema direban su tafi suka fita daga asibitin, Mum ta tsugunna a wurin tana wani irin kuka kaman zata mutu bama tasan meke mata dadiba, Abba ya tsaya akanta yana kallonta ahankali yace "H...Ha..Hajara, tashi mutafi, kinji tashi muje" ahankali Mum tamike kaman tababba tace "a'a ina zani dakai wajen Muhsin zani shi kadai muka bari adaki" da sauri ta juya zata koma cikin hospital din Abba yarike hanunta da sauri yace "Hajara dubi, kalleni" cikin kuka sosai ta kalli Abba, Abba yace "Allah yafi nida ke son danmu, dama kuma shiya bamu shiko?" yatambayi Mum ahankali, da sauri ta girgiza mai kai hawaye na bulbulowa Abba yace "to Allah yama Muhsin rasuwa, addu'a zamumai ba kukaba kinji, yanzu zomu tafi gida naga banga motar ki a parking space ba, bakizo dashi bane" gyadamai kai Mum tayi tana wani irin kuka, juyawa yayi ahankali rike da hanunta ganin bata hayyacinta yay bakin gate da ita, yatare musu taxi suka shiga suka zauna yaciro wayarshi yafara kiraye kirayen abokan arziki da abokan business.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull