Boyayyen mutun complete - Chapter 3
Boyayyen mutun complete Chapter 3: Boyayyen mutun complete Chapter 3. 3rd floor din taje gabaki daya bangaren F din single single rooms ne, inda ake…
2,253 words
3rd floor din taje gabaki daya bangaren F din single single rooms ne, inda ake kwantar da masu kudi haka kuma irin masu matsalan brain da basuson hayaniya ko kadan ko irin wayanda akaima brain surgery dinan, babu ma hayaniya a floor din ko kadan ba'a cika barin visitors ba, wasu bodyguards tagani a passage din dazai kaika room 17F din guda biyu, dakin shi kadaine a lungun, hakan yasa tadan tabe baki aranta tai wajen batare dataji ko dar aranta ba tana kaiwa wajen ta tsaya tace "Dr ce ta aikoni" matsa mata sukayi ta wuce tai dakin bude kofan abinta tayi ta shiga tana hararan su, maida kofar tayi ta rufe ta juyo, wani Dr tagani ajikin gadon daya bata baya yana sanye da white lab coat tsaye kusa da gadon patient din hanunshi rike da alluran dayake kokarin yima drip din patient din dake kwance kan gadon, bakin abun dataga ya rufe keyanshi har zuwa side din face dinshi tabi da kallo dan kanshi sanye yake da p-cap, tsaye tayi kikam kaman gunki tacigaba da kallonshi, yana sanye da black straight trouser dayaji karin guga, sai black socks akafanshi dake cikin black Gucci cover shoe, dakin sai wani irin kamshin mayen turare mai dadi yake wanda take kyautata zato daga jikinshi ne, tsira alluran yayi a ruwan drip din da aka makalama patient din gabaki daya farin ruwan yakoma sea blue hakan yasa tabi hanunshi daya rike alluran da kallo kaman wata wawiya, ganin safan hannu akan hanunshi yasa da sauri tayo inda yake ta zagayo ta gabanshi tana magana. "Dr Mashood is it you menene a fuskark...?" kasa karasa maganan tayi ganin mutum gabaki daya fuskarshi rufe cikin mask ga bakin glass a idonshi ko lips dinshi bata gani bare hanci, wani irin kafewa tayi ta kwalalo ido heart dinta nawani irin beating tana kallonshi shima kallonta yake batare daya zaro alluran daga jikin ledan drip dinba, wani irin girgiza da patient din kan gadon yafara yasa ta kalli patient din ta wutsiyar ido batare data janye asalin idanunta daga kanshi ba jikinta yafara wani irin rawa, wani irin kumfa kumfa ne yafara fitowa daga bakin patient din hakan yasa amugun tsorace ta wangale baki zatai ihu, wani irin fizgo hanunta yayi ta taho luuu zata fado jikinshi da sauri ya matsa baya, hannu yasa abayan wandonshi yaciro bindigar dake bayan wandonshi, bindigar tabi da kallo ya daura mata akan goshi dawani irin murya dataji kirjinta yana amsawa yace "if you scream am gonna shoot you" wani irin kallon bindigar dake forehead dinta take da idanunta dataji yana jujjuya wa, numfashinta na neman daukewa idanunta na lumlumshe wa kafin dip numfashin ya dauke ta sume, luuuu tafado jikinshi asandare da sauri ya zare bindigar daga goshinta yay baya shima zai fadi dan tunda yake ko hanun mace bai taba rikewa tunda yay girma balle mace gabaki dayanta tafado jikinshi, da kyar ya iya ya dafa bango da hanunshi dake rike da bindiga, dayan hanunshi kuma akan bayanta yana kara danneta kanta na kwance a kirjinshi gudun karya saketa tafadi tai kara aji ashigo, gabaki daya jikinshi mutuwa yayi yakasa tureta yarasa yanda zaiyi ya mike baimasan mezaiyi ba first thing in history! Yayi kusan 1 minute ahaka da kyar ya tattaro dan kuzarin daya ragemai ya sanya hanunshi akan kafadunta ya fito da ita daga jikinshi ya zaunar da ita gefenshi akasan wajen, luu kanta yataho zai fada jikinshi da sauri ya mike tsaye hakan yasa ta baje a kasan tiles din, ya tsaya jikin gadon ya maida bindigarshi bayan wandonshi, sake dan kallonta yayi yanda take kwance akasan wajen saikuma ya dauke kai da sauri yana kokarin dawo da natsuwar shi, hannu yasa a aljihun lab coat din dake jikinshi yaciro wata yar karaman abu mai kama da camera, kokarin kunna ma abun yakeyi yakasa gabaki daya ya rasa natsuwar shi hanunshi sai rawa yake, ahankali yasake kallonta da sauri ya kawad dakai yace "damn it" wani irin wahalalliyar tsaki yaja jin tafiyan mutane daga ta wajen dakin, da sauri yay wurin window dakin yahaura yabi jikin pipe din bangon yay kasa ko tsoro bayaji kafin ya dirka kasa batare da kowa ya ganshi ba dan yawancin babu mutane ata back yard din hopital din, gyara zaman p-cap dinshi yayi da lab coat din ta yanda koda mutane zasu hangoshi ta window ne zasu zaci wani Dr ne, yafara tafiya kaman zaki yay wurin yar karaman kofan dake wanjen dabakowa, budewa yayi ahankali ya fice daga asibitin, wani jeep ya shiga dake pake cikin layin uban motocin da akai parking a wurin da bishiyoyin yacika, yana shiga aka tayar da motar aka bar wajen, lab coat din jikinshi yacire ya dukunkule ya yar cikin wani irin fushi da yadade baiyiba, da sauri Abdallah dake driving yace "menene Ya Marwan bakasamu kai Scanning idon nashi bane?" rungume kujeran gaba yayi kafin ya saki kujeran tareda kaima kujeran wani irin duka yawani irin mike jikinshi, jikinshi na wani irin rawa yana wani irin nishi kaman zaki, arude Abdallah yay parking abakin hanya ya fito ya zagayo ta bayan ya bude kofan ya shigo ya maida kofan ya rufe arude ya dafashi yace "Ya Marwan, Ya Marwan menene meya bata maka rai haka?" wani irin dagowa yayi wuf kaman zaki yawani irin shako wuyan Abdallah yana wani irin junjuyar dakai, arude Abdallah ya dafa hanunshi yana bubbugawa idanunshi najuyawa da kyar yace "Ya..Ya Marwan control yourself, bani bane, bani bane, is me, Abdallah ne, let me..g.." [8/25, 10:15 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳
*BOYAYYEN MUTUN* 🕳🕳🕳🕳
*Maman Abd Shakur*
5⃣
Da sauri ya sakeshi kaman wani zararre hakan yasa Abdallah yafara wani irin tari, sake dukan kujera yayi kaman zaki zuciyarshi na tafarfasa yace "I will kill her" kakkabe jikinshi yashiga yi sabida yanda yaji yake kamshinta, gabaki daya kamshin jikinta kawai yakeji ko ina a jikinshi keyi duk inda yajuya kaman zaiyi hauka haka yakeji, ihu yayi ya dunkule hannu ya daki iska yace "damn, damn, damn it! saina kasheta, ubanwa yace tai hugging dina". Dago jajayen idonshi yayi tsabagen shakan dayasha ya kalli wan nashi da sauri ya kara matsawa kusa dashi ahankali yace "calm down, calm down Ya Marwan, have you forgotten what momma told you about your anger issue eh Ya Marwan?" juyo dakai yayi ya kalli kanin nashi, shiru yayi yana kallon yanda wuyanshi yay ja abunku da fari yay shaida da sauri ya matsa kusa dashi ya taba wuyanshi ahankali yace "who did this to you?" shiru Abdallah yayi saikuma yay murmushi yace "nevermind, ai am fine" rungume kanin nashi yayi da wata irin murya datai rauni sosai yace "am sorry Abdallah i know is me, nasan ninayi ma haka please forgive me, i don't know what got into my head, Abdallah am sorry okay" dan dariya yayi yace "am fine trust me Ya Marwan but meya bata maka rai haka ne, wakake cewa u wanna kill?" sakin shi yayi yakoma gefe ya daura kanshi akan kujera yay shiru batare daya bashi amsa ba, hakan yasa Abdallah ya juya yabude motar yafita, binshi yay da kallo kafin ya juyar da kanshi dayan side din ya lumshe ido da sauri ya bude ganin fuskar yarinyar dake sanye da kayan nurses ta kwalalomai ido tana kallonshi, dukan kujera yasake yi yace "damn it, i will kill her, saina kasheta" Abdallah dake kallonshi ta madubi jiyayi kaman yama yayan nashi kuka, kafin sukai gida wani irin mugun zazzabi yarufe shi, shi arayuwan shi baitaba jin abinda yaji yauba, yasaba rayuwan shi dagashi sai kaninshi, mace dai saidai yagansu ahanya ko awani wurin suna tafiya. Sunyi tafiyan dayakai kusan 35 minutes kafin Abdallah yay horn agaban gidansu kamal ya bude musu, shiga yayi ya kashe motan ya fito ya zagayo ya bude bayan ahankali yana dafa kujera yafito daga motan ya tsaya da sauri ya dafe motan jin jiri na neman kwashe shi, da sauri kamal wanda yake abokin Abdallah daya gama kulle gate yakaraso wajen yana kallon Marwan din daya dafe mota yace "wah happen to him Friend? Why is he like this baida lpy ne?" Abdallah dake kokarin kama hanunshi yace "wlh i have no idea" tattaro karfinshi yayi ya tashi daga jikin motar yay cikin gidan yabude kofa ya shiga ciki jiri na dibanshi, upstairs yayi ya bude kofar wani daki ya shiga hadadden dakine da akai komi off white dakin kaman nawani dan president, kan lumtsatsen gadon ya fada yaja bargo yarufa ya dukunkune dan wani irin sanyi yakeji sosai.
Kamal ne ya dafa Abdallah dayay mutuwar tsaye jikinshi duk yay sanyi yanabin kofar da wan nashi yabi ya shige ciki da kallo hawaye sun taru a idonshi sosai, jijjiga kafadarshi Kamal yayi yace "dalla chill karka damu kanka he will be fine yasaba fushi haka ai" hannu yasa ya sharce dan gutun hawayen daya bullo daga idonshi ya girgiza kai har lokacin bai janye idonshi daga kofan ba yace "i don't think so, this anger is different from wanda yasaba yi, kamal i don't want anything to happen to my brother, he has suffered enough a duniyan nan, i hate, hate, hate it wen he's suffering wen he's mind is not at peace" ya karashe maganan hawaye na gangarowa daga idanunshi, "kai wai me haka dalla kadena kuka dont break my heart as well, muje mukira mai Baba maybe yafada mai wat d problem is" Kamal yay maganan yana janshi amma ko motsi baiyi ba ahankali yace "kana ganin zai fada?" yay maganan yana janye idonshi daga kofan ya kalli Kamal, gyadamai kai kamal yayi yana murmushi yace "sosai ma kasan he has alot of respect ma Baba, let's give it a try muje Baba na masallaci" gaba kamal yayi Abdallah na biye dashi, tare sukaga tsohon da akalla zaiyi kusan 70 ko 71 tareda Omari dayake biyamai karatun Al Qur'ani, saida suka jira suka kai karshen aya sanan suka fada musu Ya Marwan ba lpy, Omari ma kusan yafisu tashin hankali rufe Qur'ani yayi ya ijiye a inda ake ijiyewa yafita daga masallacin da sauri su Baba biye dashi da sauri yay sama ya bude dakin ya shiga wajen gadon yayi ya tsugunna yana kallon mask din fuskarshi, ganin yanda numfashinshi ke fita ahankali yasa yakai hanunshi ya daura kan wuyanshi da safan fuskan ya sauka har wajen zafi yaji hakan yasa yadan yayi bargon ya kamo hanunshi ya hada da nashi kafin ya daura kanshi akan gadon yay shiru yana sauke tagwayen ijiyan zuciya, dafashi Baba yayi yace "bacci yakene Omari?" gyada kai yayi batare daya dago kaiba, hakan yasa Baba yace "to Allah kara sauki katashi kaje kasiyomai magani ne inya tashi yasha kasan zazzabi batamai kyau" gyada kai yasake yi batare daya juyoba hakan yasa Baba ya juya ya kalli Kamal da Abdallah da idanunshi sunyi jajir yace "ku muje ku barshi yay baccin shi" bayanda suka iya suka juya suka fita suka rufo musu kofan, yafi 5mins ahaka kafin ya dago kanshi ya tashi tsaye idanunshi sunyi ja ya tsaya yana kallon Marwan din saikuma asanyaye ya fita daga dakin ya sauka kasa car key yadauka yawuce waje yadau wata bakar mota kirar Kia yafice.
*** Saukan ruwan sanyi dataji akan fuskarta yasa tawani irin ware ido at once kafin tasaki wani irin uban ihu tana kalle kallen dakin. "malama ki natsu" taji an mata magana, dago kanta tayi atsorace taga wani matashin police ne dabazai wuce 29 hakaba akanta rike da bottle water mai sanyi wanda tana kyautata zaton shi aka zuba mata, bayanshi wasu police ne guda biyu sai HOD dinsu dakuma consultant din data turota zuwa dakin saikuma wata mata da taci uban gayu kanta tasha attachment dake gefe tana goge idanunta dasukai ja sosai dawani farin handky, sai kuma security biyun dake bakin passage dinan, wani irin rawa taji jikinta ya dauka kanta nawani irin ciwo tana binsu da kallo daidai dai dai, farin jaka da aka jefa alluran da wanan mask man yama patient dinnan anyi zipping kan ledan police din ya nuna mata yana mata wani irin kallo yace "a ina kika samo alluran nan?" kallon alluran tayi kanta nawani irin sarawa dan har ga Allah bama ta gane alluran ba, girgiza kai tayi da bakinta daya mata nauyi sosai muryanta narawa tace "ni, ni bansan alluran nan ba" wani irin kallo inspector da aka rubuta Inspector Aliyu Alkali ajikin tag dinshi yamata kafin yamika hannu police din bayanshi yasaka mai ankwa, cije lips dinshi yayi yana kallon fuskarta yace "fine i think zaki fadi gaskiya in munkaikai station" yawani irin kamo hanunta yana handcuff din akai yana kullewa. "you are hereby arrested for injecting a patient with deadly substance, you have the right to remain silence because anything you say or do could be use against you in the court of law" arude ta kalleshi heart dinta nawani irin racing da tunda take a duniya batajin zuciyarta yataba irin gudun nanba, dagata yayi kaman wata kaya hakan yasa tai baya luuuu ta sake sumewa, watsa mata ruwan yayi a fuska yana tsaki hakan yasa tasake bude ido tanajan numfashi nunama police biyun dake gefenshi ita yayi yace "kutafi da ita mota am coming" janta sukai luu sukai waje da ita, binsu kawai take dan sosai kanta ke juyawa hankalin tama baya jikinta kalman arrested kawai ke yawo akanta, kallon Su HOD yayi bayan ya zuba hannu a aljihu yace "keep me posted akan condition din patient din" yajuya yafita daga dakin. [8/26, 7:35 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳
*BOYAYYEN MUTUN*🕳🕳🕳🕳
*Maman Abd Shakur*
6⃣