Kenza eBookz

Boyayyen mutun complete - Chapter 6

Boyayyen mutun complete - Chapter 6

Boyayyen mutun complete Chapter 6: Boyayyen mutun complete Chapter 6. Laptop din dake kan cinyarshi ne yazo zai fadi tsabagen yanda yake juyawa yana…

3,307 words

Laptop din dake kan cinyarshi ne yazo zai fadi tsabagen yanda yake juyawa yana kallonta da sauri Abdallah ya mika hannu ya dauke laptop din daga kan cinyarshi yace "Ya Marwan" dan juyowa yayi ya kalleshi kafin yakara juyawa yana kallonta tana tsaye akan titi kana ganinta kasan abin hawa take jira, dan sanyi jikin Abdallah yayi, asanyaye yace "itace yesterday nurse from St. Edward?" ahankali ya juyo ya kalli Abdallah, shima Abdallah kallonshi yake ganin ko alamun zai bashi amsa baiyiba yasa yay dan murmushi yabude kofa ya fita daga motan, kalle kallen kasan wajen ya shiga yi kaman mai neman abu, hango wani kusa yayi akasan nan kusa da motarsu kadan hakan yasa yay wurin da sauri saida yafara daga kai ya kalli titin, ganin har lokacin tana nan kan titi bata sami abin hawaba yasa ya cire takalmin kafar shi ya tsugunna ya juyar da kusan yataka nail din tareda runtse ido dan zafi saida tadan bula kafan sanan yay maza ya janye kafar data fara jini, jini na bulbulowa, zama yay akasan wajen ya kwala ihu. "wayyo Allah nurse, nurse" daidai lokacin ta tare wani keke napep tana shirin shiga bama tajishi ba hankalin ta yay nisa gida tana tunanin hala Mum ta dawo yanzu, nuna mata bayanta mai napep din yayi yace "hajiya bake wancan dayaji ciwo ke kiraba?" ahankali ta juya dan ganin mai kiranta, hakan yasa Abdallah ya nunata da hannu kaman zaiyi kuka yace "nurse nataka wani abu, wayyo Allah am bleeding karna mutu, zoo ki dubani" gyara zama tai a keke napep din ta dauke kai saikuma ta sake kallonshi tace "this is a minor injury kacika raki, kaje kai alluran tetanus a any nearby pharmacy" ta kalli mai napep tace "muje malam" kaman zaiyi kuka ya rike kafan yana kallo yace "Nurse wlh karma kifara kisa nai bleeding to death, kinyi nightingale pladge fa zakuyi best dinku for patients, dan haka my life is in your hands now, kizo ko Allah ya kamaki" murmushi tayi daya kara mata kyau, oh yau Allah yahadata da namiji mai halin Ya Ahmad, dan bazan surutu bala'i, fitowa tayi daga keken tace "malam yi tafiyar ka karna batama lokaci" sanan tajuya, karasowa tayi ahankali inda yake tana kallon kafan nashi. Marwan da gabaki daya ya kafeta da ido any step datai taking har cikin kasakasan ranshi yakeji, namomin jikinshi nawani irin amsawa, blood stream dinshi nawani irin freezing. Tsayawa tai agaban shi tana kallon kafan, ahankali ta sauke jakan bayanta ta tsugunna batare data kalli fuskarshi ba, zage zip din jakar tayi ta fito da yar karaman first aid kit din dake ciki ta ijiye a gefe, handglove tazaro daga kwalinsu tasaka a hannu hakan yasa ya kwalalo ido yace "Nurse tiyata zakimin ne wai? kai!" wlh batasan lokacin data fara dariya ba, hannu tadaura akan fuskarta ta rufe tana dariya sosai dan maganan shi ya mugun bata dariya, ahankali Marwan yay wining down tinted glass din motar kasa kadan danya kalleta da kyau, yanda take dariyan da hannayenta data daura akan fuskarta yakara mata wani irin kyau, wani irin tafiyan butterfly yaji acikin cikinshi hakan yasa ya daura hannunshi akan cikin dayaji kaman ma yana murdawa yana kallonta still. Kasa daina kallonta Abdallah yayi yace "wai bazaki dena dariyan ba sai jinin jikina yakare, jibi yanda jini ke fita daga fine kafana fa" janye hanun tayi daga fuskarta ahankali batare data kalleshi ba ta bude kit din ta ciro spirit ta bude ta kwara mai akan ciwon dake jinin, dan kara yayi yace "auuch, me wanan kikasa min? Gaskiya u are a wicked nurse ba kya petting patient" murmushi tayi batare datace komiba tadau cotton wool tana sharewa tace "kaiko kacika raki, ga surutu kaman yayana Ya Ahmad, inyaji ciwo ko haka yake kaman kai" tai maganan daidai tagama cleaning ciwon tana kokarin cire handglove din hanunta sai kallonta yake, ahankali yace "and I know inda ace my sister na nan she would've been just like you" dago manyan idanunta tayi ta kallai daidai tagama cire handglove din, shima ita yake kallo, daukan kit dinta tayi ta maida cikin jakan tace "make sure kaje an maka tetanus injection, Allah sawake" daukan jakanta tayi ta goya zata juya wani irin sanyi ne ya shiga jikinta sosai hakan yasa ta tsaya chak tareda juyowa ta kalli motar su, da sauri Marwan yay wining glass din up tun kafin ta lura, atishawa tayi tai hamdala, mikewa Abdallah yayi yace "inane asibitin ku anan zanje nai alluran" batare data juyoba tace "St. Edward teaching hospital" tai gaba da sauri tai titi daidai lokacin wani keke napep ya tsaya ta tare ta shiga.

Kakkabe jikinshi yayi yay murmushi yabude kofan motar su ya shiga ya zauna ya rufo ya leko da kanshi ya kalli yayan nashi yana murmushi yace "how was my act?" ahankali yace "kana hauka ko, inba hakaba tayaya zaka taka nail comfortably, wats wrong with you Abdallah" murmushi yayi yana murza key motar yace "because you are in love" "what!" yafada angrily, tada motar yayi yace "Allah Ya Marwan, dudda baka fadamin abinda yafaru jiyaba tace a St. Edward take aiki which was inda mukaje jiya and naga yanda kake kallonta dat wat made me do abinda nayi sabida ka kalleta da kyau, finally kaga wata kanaso, finally you've seen someone, finally kai developing feelings ma someone, finally Ya Marwan zaiyi aure, finally Ya Marwan is in luv" tsaki yayi "something is really wrong with you Abdallah, kai! are you sick upstairs?" yay maganan kaman wani dan daba dinan, tsaki yasake yi ya dau MacBook dinshi yafara danne danne amma bama ya gane komi, sake dago kai yayi ya kalli Abdallah ta madubi yace "karka karamin irin maganan nan, i hate it! am not in luv, i just don't know what is wrong with me, i guess fushi nake kan rashin concluding aikin jiya" murmushi kawai Abdallah yayi yacigaba da tukin shi batare dayace komiba. [8/28, 6:56 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳

*Maman Abd Shakur*

1⃣1⃣ - 1⃣2⃣

Shi kadai ya dinga jera uban tsaki yafi sau goma, gabaki daya fuskarta yake gani barinma lokacin data daura hannayen ta akan fuskarta tana dariya, tsaki yayi yamaida hankalinshi yacigaba da aikinshi da MacBook yana so ya natsu amma ina ya kasa a screen din MacBook dinma ganinta yayi tanamai murmushi hakan yasa yawani irin jan dogon tsaki yarufe system din da sauri yace "damn it!" sai uban huci yake kaman kumurci yana duddunkule hannu, murmushi Abdallah yayi yacigaba da tukinshi abinshi yace "ari".

Koda takai gida babu kowa duk sun tafi aiki Abba ma bayanan, mai aikinsu ce kawai agidan gaisheta tayi ta wuce daki tai wanka kaya ta chanzo har lokacin tana murmushin rakin Abdallah tafito tai kitchen tana taya yar aikin nasu aiki sukai hadadden girki ma Mum sukai arranging gidan aka share ko ina sai kamshi yake, tafito da kayan wankinta sukai backyard inda washing machine yake ya wanke su ya dauraye ta ciro ta shanya sanan ta dawo dakin lokacin an sakko daga masallacin juma'a hakan yasa tai dakinta taje tai salla, wayarta dake ringing yasa ta mike da sauri ta dauka agaban madubi, Mum data gani yasa tai wani irin tsalle ta zauna akan gado tadau wayar saikuma ta saki kuka tace "Mum tunda kika tafi baki nemeni ba kona kiraki baki dauka why Mum" dan dariya Mum tayi daga ta dayan bangaren tace "sorry my princess, busy nake sosai, meetings nakeyi wlh dawasu investors, apart from hakan ma inaso nasai share wani mutumi a burj al Arab amma sai yanga sukemin wai akwai wasu akasa, yanzu dai how are you? Abban ku told me what happen to you, sorry princess dina Allah ya kara tsaremin ke da protecting dinki kinji" gyadakai tai ahankali tace "Ameen Mum, karfe nawane zaku iso?" "ina princess?" "nan mana Mum, bayau zaki dawoba?" dan dariya Mum tayi tace "haba princess dina ke bakiso Mum dinki ta nemo kudin aurenkine? In aka tashi bikinki namiki biki, biki mai suna biki ba bikiki ba, biki da sai Nigeria da Abuja ta girgiza, kefa nake nemanma kudin nan uhm Apple of my eyes" make kafada tayi a shagwaban ce tace "Mumy ni wlh banaso, please just come back i want to hug you Mum, wlh kullum sainai mafarkin ki" takarashe maganan tana kuka, sosai zuciyar Mum ta karaya hakan yasa tace "kinga ko princess ayanzu haka danake miki magana i don't know yaushe zan dawo ma, cikin kaso goma a abubuwan danazo yi ko kashi uku ban kammalaba, but i promise you, i promise you princess, i will double my effort just for you kadai, dan kawai nagama da wuri nazo nima i miss my baby girl, my one and only baby girl, forget duk brothers dinki are kobo u are d only naira in my life, oya laugh inji" dariya tahau yi hawaye na fita, tana mugun son Mum dinta itace naira rayuwan mum, su Ya Muhsin da Ya Ahmad kobo ne su haha abinda ke kara sata jin dadi kenan, dariyan da Mum taji tanayi yasa ta sauke ajiyar zuciya hankalinta yadan kwanta sosai dan tunda Abba yay fushi yamata text din abinda yasameta dan bata kirasa back ba takasa samin natsuwa, ganin yanzu she's smiling yasa hankalinta ya kwanta sosai, ahankali tace "okay princess i will hang up now akwai inda zani i will try as much as possible nadinga kiranki kullum kinji, no matter how tight my schedules are, I love you" ahankali tace "I love you too Mum saikin dawo" "yauwa yar albarka bye" katse wayar Mum tayi hakan yasa tafada gado tana kukan bakin cikin bazata dawo yauba ahaka bacci yay awon gaba da ita sai wuraren biyar ma ta tashi da sauri ta fada bayi ta dauro alwala tazo tai sallan laa'sar sanaj ta fita ta debi fried rice kadan ta dawo palo rike da plate din ta zauna akan kujera tanaci tana kallon zee world.

Sai da aka kira magrib ta tashi plate din takai kitchen ta wanke ta ijiye sanan ta fito tana yarfe hannu ta wuce tai dakinta alwala ta dauro tasaka hijabi tahau kan dadduma tanacikin salla Abba yatura kofan ya leko ganin tana salla yasa ya wuce dakinshi, alwala yayo shima ya fice dan zuwa masallaci, tana idarwa karatu tayi dan taji fitan Abba tasan kuma sai bayan sallan Isha zasu shigo dukan su, saida aka kira sallan isha sanan ta tashi tayi tana idarwa ta linke dadduma ta cire hijabin, dan kwalin riga da zanin dake jikinta ta dauka ta daura sanan ta fice daga dakin tai falo rike da wayarta, zama tai akan kujera tana kallon film wayarta yay ringing da sauri ta dauka ganin Fauzy ce kafin ma tai magana Fauzy tace "ance wai anyi suspending dinki wlh school dinmu yan iska ne, Allah zai saka miki kinji Nadeera" murmushi tayi tace "bakomi ya kike yasu Mum da Ameer auta?" ajiyar zuciya ta sauke tace "Alhamdulillah, Ameer sunje masallaci da Abba, mum na dakinta, gobe zanzo kinanan ko?" girgixa kai tayi tace "wlh Ya Ahmad yace zamu fita" "aiko wlh kezaki zo jibin dan kiji rotten tomatoe" dan dariya tayi tace "naji to zanzo ran Sunday, amma bayan la'asar fa" kaman Fauzy zatai kuka tace "please babe tunda safe zakizo da magrib zaki koma bye banison jin komi" ta katse wayar dip hakan yasa taciro wayar daga kunne tanabin wayan da kallo. "lemme see dat phone" da sauri ta daga kai Ya Muhsin ne zaune kan daya daga cikin kujerun falon yana sanye da jallabiya brown, ahankali ta tashi takaimai wayar batare daya karba ba ya watsa mata wani irin mugun kallo yace "dawa kike waya?" ahankali tace "da Fauzy ce, Ya Muhsin dama inaso naje gidansu ran Sunday ne tunda gobe zamu fita da Ya Ahmad" hararanta yayi batare daya karbi wayan datake mikamai ba, dan murmushi tayi tace "naje please?" dauke kanshi yayi yaciro wayarshi daga aljihu yana danne danne kafin yace "fine ran Sunday na saukeki kafin nai tafiya" "ina zaka?" tai maganan kaman zatai kuka tana kallonshi, ahankali yace "Kaduna to attend one conference, will be coming back the next day dasafe" ahankali tajuya batare datace komiba takoma kan kujeran datake kai ta kwanta kaman marainiya bayan ta jefar da wayar kan center table, dago kai yayi ya kalleta yace "common tashi kibani abinci" tashi tayi tai dining din hakan yasa shima yamike yay dining din yaja kujera ya zauna, warmer ta bude ta zuba mai fried rice din a plate da chicken daidai lokacin Abba da Ya Ahmad suka shigo dining din suma suka taho ta zuba musu taje fridge ta dauko pineapple juice din dasuka hada ta zuba musu kafin ta koma gefen Abba ta zauna tai shiru, kallonta Abba yayi yace "bazaki ciba" kaman jira take tafashe da kuka hakan yasa duk suka tsaya dacin abincin suna kallonta, Abba dayafi kowa rudewa yace "wai menene kike kuka eh Princess?" share hawayen tayi da bayan hannu cikin hakin kuka tace "Abba ba Ya Muhsin bane zaiyi tafiya ba, kowa nata tafiya ana barina ni kadai a gidan" kafin Abba yay magana Ya Ahmad yay dariyan zolaya yace "nima tafiya zanyi yarinya sati daya zanyi zanje UBA seminar a lagos mainland" kara rushewa tai da kuka, Abba ya watsama Ahmad dake dariya harara ya dago kanta yana share mata hawayen yace "karki biyema Ahmad wasa yake miki, Muhsin ne kawai zaiyi tafiya kuma ai washegari da safe zai dawo sabida aikin shi, ashe ma anyi suspending dinki a makaranta baki fadamin ba, yanzu dai yayanki yasamu ya fitar dake case din ansamu glimpse of him, dan keyarshi ma aka gani ta CCTV camera kwara daya dake bayan asibitin daya kamashi, hakan kuma ya nuna abinda kika fada gaskiya ne yanxu dai ance bayan sati biyu ki dawo" murmushi tayi sosai ta kalli Ya Muhsin dake cin abinci shi tace "thank you Ya" gyada mata kai yayi Abba kuma yacigaba dacin abincin shi, ana gamawa duk sukai falo ita kuma ta kwashe kwanukan takai kitchen ta wanke ta gyara dining kafin tadawo falon ta zauna gefen Abba tanajin hiran dasuke na labarai, daganan kuma bacci yay awon gaba da ita wuraren shadaya, tadata Abba yayi ta mike ta wuce dakinta, da kyar ta chanza kaya zuwa kayan bacci ta kwanta sai bacci.

Washe gari sai after one suka fita ita da Ya Ahmad, kwalliya sosai taci tasaka blue lace mai dutse din gold, tayafa gold gyale tasaka gold takalmi da karamin mini gold hand bag, tai wani irin shegen kyau dako ya Ahmad saida ya yaba.

Parking yayi awurin paka motocin a park din suka fiffito, atare suka jera har zuwa wani wurin hutawa haka cafe ne da akai bukka ga kujeru da table a hadaddu aciki, order yafara musu na mock tails da chicken wings sanan sukai ciki suka zauna ya ciro waya kiran deejay tace "sun kusa karaso wa" ko 10min ba'a karaba ta kiranshi hakan yasa ya kalli Nadeera datai nisa a chatting da Fauzy yace "ke am coming" murguda mai baki tayi tace "nine ke?" amma harya juya yay gaba abin shi basu wani jimaba yadawo tareda wata kyakywar mace taci bakin hadadden doguwar riga suka shigo wajen tashi Nadeera tayi ta rungumeta tana murmushi tace "Anty barka da zuwa, please zauna nabarki a tsaye" tai maganan tana nuna mata kujera zama Deejay tayi suna hira abinsu suka ma manta da Ya Ahmad daya gama shaka yana hararan Nadeera, nan aka kawo mock tail da chicken wings din daya musu order daukan mock tail dinta tayi ta saka straw aciki tadan zuka sanan ta cire baki ta kalli Deejay tace "natafi nima nazagaye wajen Yayan mu nata hararana to nabaku gurin, asoye amma kar akone" tai maganan tana ma ya Ahmad fari da ido itadai Deejay dariya taketa musu, ficewa tayi daga wurin tana tafiya ahankali abinta tana sipping mock tail dinta tana zagaye gun, ahaka harta fito ta baki bakin hanya inda motoci ke wucewa, ajikin motarsu ta jingina tana facing hanya, hanunta daya rike da mocktail din dayan hanun kuma rike da waya tana daddannawa.

"p..park d car." yacema Omari dake tuki, gabaki daya hankalin shi nakanta, yanda take tsaye jikin mota tana danna waya dayan hanunta kuma rike da mocktail yasa yaji zuciyar shi na bugu, gangarawa gefen hanya Omari yayi yay parking yajuyo danya kalli wannashi ya tambayay maisa akai parking anan saiyaga hankalin na waje ma, ahankali ya juya danyaga maiyake kallo suda sukeda important work zasuje karbo wasu supplies na operation din gobe dazasuyi, wata kyakywar yarinya yagani tsaye jingine da mota bama yaganin face dinta sosai dan kanta aduke yake tana danna waya yake kallo, juyowa yayi ya kalleshi yace "Ya Marwan zamuyi latti fa, wats up with dat gurl why are you looking at her?" ahankali batare daya juyo ya kalli Omari dakemai magana ba yace "shiiii" hakan yasa Omari bai sake magana ba ya koma kujera ya ciro wayarshi yana dannawa.

Wani irin sanyi ne taji yana shiganta hakan yasa ta dago kai da sauri tana yatsine fuska tareda tura wayartata ajaka, takai hannun tana gyara gyalen jikinta tanadan kankame jikinta sabida sanyin, ahankali Marwan ya mika hanunshi dake cikin safan hannu ya daura akan glass din motar daidai ta saitin inda take ya daura dayan hanunshi kuma akan kirjinshi dake wani irin bugawa. Yatsine fuska tasake yi ganin hakanan she's not comfortable, kara gyara gyalen tayi daya rufe mata hannu sosai sanan ta juya ahankali ta koma ciki, wani irin kallo yake binta dashi yanajin wani iri dabaisan na menene ba harsaida ta bacema ganinshi, ajiyar zuciya ya sauke mai kara dahar saida yasa Omari juyowa yace "kodai jikin ne Ya Marwan" dan gabaki daya jiya da daddare ma basu gane kanshi ba, sosai yadinga zazzabi bayan sun koma gida, dan kome yakeyi ita kawai yake gani ko kadan baida sukuni yarasa gane kanshi, yarinya kaman aljana taki fita daga kanshi, girgixa kai yayi kafin yakarayin wani hucin yace "let's go" kunna motar Omari yayi suka hau titi.

Sai wuraren magrib suka baro park din, saida suka ajiye Deejay akofar gidansu sanan suka taho bayan ya tsaya ahanya yay magrib kafin sukai gidama ankira isha, yana parking yawuce masallaci itakuma tai cikin gida wanka tafara yowa ta shirya cikin simple gown tai salla kafin tacire tasaka kayan bacci tafada gado sai bacci da asuba ma Abba ne ya tadata taje tai salla tai karatu tafito ta hada musu breakfast.

Sai wuraren 12 narana Ya Muhsin ya shigo yace "ki shirya will drop u off kafin na wuce" gyadamai kai tayi ta wuce daki wanka tasake yowa ta shirya cikin doguwar bakar riga mai hade da baby pink color da Mum tasiyo mata daga 🇴🇲 Oman, bakaramin kyau doguwar rigan yamata ba gashi anbishi da stones, gaban madubi taje ta shafa hoda ta shafa man baki akan pink lips dinta sanan tai rolling gyalen rigan baki tadau small mini bag dinta baby pink tasaka baby pink flat shoe sanan tadau wayarta tafito, amota tasami Ya Muhsin hakan yasai tai motan ta bude ta shiga ta rufo, tace "gani Yaya" tada motar yayi batare daya kalleta ba yay horn mai gadi yabude musu suka fita, tafiyar kusan 20 minutes yakaisu anguwan su Fauzy, agaban gidansu yay parking baice mata komiba, hakan yasa ta juyo ta kalleshi kaman zatai kuka tace "Allah kiyaye hanya Yayan mu, please kadawo gobe kaji, byeee" gyada mata kai yayi sanan ya juyo ya kalleta yace "6 Adamu zaizo ya dauke ki so get ready kafin yazo karkisa yay ta jiranki" murmushi tamai tace "to, bye" tamai waving hannu tana murmushi, shima dan murmushi yamata yace "bye" bude kofa tayi ta sauka daga motan tai knocking gate din aka bude mata ta shiga tana ma Ya Muhsin bye, murmushi yayi yatada motar yay reverse yabar anguwan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull