Buzu book 1 complete - Chapter 10
Buzu book 1 complete Chapter 10: Buzu book 1 complete Chapter 10. Ya kalli yaron, da fatarsa duk ta yamutse ya ce "Ke ya aka yi ki ka bari mayya ta kama…
4,480 words
Ya kalli yaron, da fatarsa duk ta yamutse ya ce "Ke ya aka yi ki ka bari mayya ta kama miki ɗa? Tun yana ciki matar da ta aiko miki da kunu, ki ka sha ta kama miki ɗa"
Cikin damuwa matar ta ce "Innalillahi wa innalillahi raziƙuna, wallahi sarki ka ga ba ya gaba yaron nan, kullum cikin kuka ba ruwan nono na rasa yacca zan yi ohh ni Sakina, amma Allah ya isa wallahi"
Daga yadda matar ta faɗi Innalillahi, Nana ta ƙara tabattar da jahilci a gurin matar, yadda suke ba wa maganganun sarkin baka ammana ba tare da musu ba har mamaki yake bata. Ya faɗi maganin da za a bata suka yi gaba.
Wani guri suka shiga, shi kuma masu ciwon suga ne, ya yi musu ya jiki suka amsa. Bayan sun gama gaisawa ya kalli masu kula da su, ya ce "Yauwwa, kar a kuskura a karya dokokin da na saka, da sassafe kafin su ci komai a ba su magani, a basu zuma cokali biyu da garin habbatussauda, sai su karya kumallo da ruwan dahuwar yaɗiya mai ɗumi, sannan su ci ganyenta. Da rana a basu faten dankalin turawa da alayyahu, a sake basu zuma da habbatussauda, sai da daddare a ba su gurji da kwaɗon rama, sai a sake ba su magani. Yau maganin cikin ɓawon gyaɗa bibbiyu za a zuba musu a ruwa su sha. Shi ne jadawalin abincin da za a ba su yau" ma'aikatan suka amsa masa da to. Nana kuwa rasa bakin magana ta yi, sai kallon ikon Allah, tamkar likita a asibiti da marasa lafiyar sa.
Sun zagaya sosai da sosai a cikin gidan, sannan suka koma wancan ɗakin da suka tarar da shi da farko.
Bayan sun shiga, ya zura hannu a cikin zabirarsa ya din ga zaro gashin jariran nan, da belin da ya din ga cire musu, yana tarawa a cikin wata tasa, sai da ya cikata taf. Ya dubi Salamatu ya ce "Salameme zuba wa Fulani a randarta" Salmatu ta karɓa, ta je ta buɗe randar da bafulatanar nan ta ɗqzu sha wannan baƙin abun ta juye a ciki.
Ya kalli Nana ya ce "Za ki iya tuna daga wani lokaci, ki ka fara ganin uban duƙusa a bacci?"
"Waye hakan?" Nana ta tambaya cikin rashin fahimta.
"Aljanin da yake zuwar miki"
"Wai ƙaisar?"
Ya yi murmushi ya ce "Shi"
"Ba zan iya tunawa ba" ta bashi amsa.
"Ina kallonsa a tare da ke ɗazu, shi ya yi wannan tsawar mahaukatan nan suka yi shiru, so nake ya bayyana a jikinki mu yi magana da shi, amma yaƙi. Masu ihun nan da ki ka gani, duk masu baƙaƙen aljanu ne masu taurin kai, wanda ko an ba su magani, suke lafawa su dawo daga baya. Nan gurin ɗaure su na yi, nake hukunta su da azaba kala-kala, a matsayin gargaɗi da kashedi. Akwai hayaƙin da ake yi musu safe da yamma an gama hayaƙin muka je, amma ƙaisar ya ƙi bayyana. A duniya aljanun da suke irin sa ba su da yawa". Nana ta yi tsuru tana kallonsa da saurarensa, tare da kallon maganganun sa a matsayin soki burutsu.
"Amma ke me yasa ba zaki yadda ki karɓi abin da yake gadonku ba, ki ka gwammace ya yi ta azabtar da ke?"
Take Nana ta tsuke fuska, ta tsani ta ji an danganta ta harkar bori da gadonsu, kamar wani abin arziki.
"Ni ba zan yi shirka ba"
Sarkin baka ya ce "Ba shirka ba ce ba, bayar da magani, idan bayar da magani shurka ne, Asibiti ma shirka suke yi. Ki amince sai mu haɗu mu ci gaba da gudanar da taimakon al'umma"
Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan yi ba ba na so"
"Anya? Ki yi tunani kar ki zo nan gana kina nema ido rufe fa" tayi shiru ba ta yi magana ba.
"Salamatu mayar da ita ɗakinta, a bata abinci, idan tana buƙatar wani abin a bata"
Salamatu ta jinjina kai, daga nan ta jagoranci Nana suka bar ɗakin.
****
Zaune take a katafaren falonta, ta hakimce a kan kujera tana amsa waya "Hajiya Sa'a, ya mu ka ji da iftila'in nan da ya tinkaro mu, coustom sun riƙe mana kaya a Abuja?"
"Aikam, mu na nan muna ta up and down, Allah ya sa su sakar mana a kan lokaci"
"Amin ya rabb, wallahi hankalina duk a tashe yake, na haɗa kuɗin mutane da jarina duk na zuba na sayo kayan nan, ni dai fatana Allah ya sa kar su yi condeming ɗin kayan nan wallahi ban san in da zan saka raina ba, ga mutane sun fara ƙorafi"
Hajiya Sa'a ta ce "Ahha haba Sadiya, babu abin da zai faru fa, ki kwantar da hankalinki ki yi addu'a"
"To shikkenan Hajiya, na gode sosai da sosai" bayan sun yi sallama, Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta kalli maman khairat ta ce "Safiyya mutuniyarki ce fa, Sadiya"
"Ohh Allah sarki"
"Duk hankalinta a tashe yake, batun kayan da coustom suka riƙe, ni ba ta son ko kaɗan kayan nan ba a gabana suke ba"
Safiyya ta yi dariya ta ce "Haryanzu ita kanta a tukunya yake kenan, ba ta san dawar garin ba?"
"Ina fa ta sani, a zatonta business yake tara mini kuɗi, duk wannan abin shige mini take son yi, ta ji sirrina".
"To hajjaju a shigo da ita sabgar mana"
Cikin sauri ta ce "A'a tana da surutu, ga ƙaryar riƙon addini, kin san kuma ƙa'idarmu, muddin aka samu mushikila akwai matsala. Ai zatonta business ɗin nan na riƙe, har take neman yin takar da ni a wasu abubuwan. Ba ta san kare yawa ne kawai ba, da kawar da hankalin mutane".
"Gaskiya ne, sabgar tana buƙatar sirri sosai"
"Safiyya kin ga an sake samun matsala, yarinyar ba ta yi amfani da turaren nan ba, wanda ya yi amfani da shi daban, ya ce wani aljani ne a kan yarinyar hatsabibin gaske ba zai bari komai ya yi tasiri ba. Kuma wallahi ya tabbatar mini idan aka yi amfani da jininta, za a samu alkhairi sosai taurarinta masu haske ne. Kuma idan aka yi wannan aikin ba za a ƙara bamu wani aikin mai wahala ba. Mun riga mun wuce gurin mun samu sa'a, sai da na ce anya ba sato ta zan saka ayi ba?"
"Na shige su ni Safiyya, kuma Jamila ta tabattar mini da ta ba ta turaren har ta na murna"
"Wallahi ba ita ta yi amfani da shi ba, an yi amfani da turaren amma ba ita ba ce ba"
"Kai wannan wace irin jaraba ce? Ga shi kuma wai ba ta nan an kaita gidan mai magani an barota a can" da sauri Hajiya Sa'a ta ce "Haba dai? A ina ne na ji ko da yadda za mu yi mu samu gurin?"
Maman khairat ta ce "Wallahi ban sani ba, sai dai idan ta zo na tambayeta"
"To ki yi mata cikin hikima dan Allah, ki nuna mata wata 'yar uwakki za a kai, kar mu bar wani trace da za a gane wani abu"
"To shikenan hajjaju bari ta zo, it ma ina daf da jawota cikin ƙungiya, za ta yi mana amfani saboda tana da mugun kwaɗayi daga ita har iyayenta"
"Aikuwa nima na gani, yanzu dai a far wannan ɗin"
**** Ɓangaren Nana, ta ga abubuwan al'ajabi kala-kala a gidan sarkin baka. A kwana uku da ta yi, tana iya fita da kanta ta zagaya tana ganin marasa lafiya har ma ta yi magana da su, ta basu shawarar su din ga zuwa asibiti. Tana yawan zuwa ganin Kubra, sai dai yanayin da take tarar da ita a ciki, ba ya yi mata daɗi, saboda wataran da sauƙi wataran kuma hauka take yi tuburan.
Kullum idan Sarkin baka zai zagayen ganin marasa lafiya, da waɗanda ake kawo masa su ganshi, tare yake yi da ita. Aka kawo wata mata da tsohon ciki tana tafiya da ƙyar, cikinta har rinjayarta yake yi, wai shekarar cikin goma a jikinta, wasu lokutan ya tashi, wasu lokutan ya kwanta a neme shi a rasa.
Su na gama yi wa sarkin baka bayani, Nana tayi farat ta ce "Ba ku je asibiti ba?"
"Mun je, duk gwajin da aka yi sai ace babu ciki" babar matar ta ba wa Nana amsa. Sarkin baka ya bushe da dariya ya ce "Asma'u ma'u, su Asibiti duk abin da suka zo muku da shi, za ku karɓa ku ce technology ne, mu kuma namu da muke yi, shi ne shirka a gurinki. Shi maganin baturen kin san da me da me ake haɗawa? Kin tabattar da ingancin halaccin sa a addinance? Shi fa ilmi siffa ce ta Ubangiji, kuma yana bayar da ita ga wanda ya so, bai keɓantar da baiwarsa ga farar fata ba kawai, ku baƙaƙen fata ne ku ka raina abin da Allah ya baku na ilmi, ku ka yi amanna da bature ne kawai ya iya"
Ya mayar da hankalinsa kan mara lafiyar ya ce "Hajiya a da idan ki na al'ada ba ruwanki, duk gurin da ki ka samu yarda ƙunzugun jinin ki ke yi. Da ƙunzugun jinin hailarki aka yi miki sihiri, saboda a raba ki da mijinki, idan ba ki manta ba, kin yi ta zubar da jini tun yana taya ki neman magani har ya gaji ya yi aure ya rabu da ke. Da ki ka ce ki na da ciki ma rigima ku ka yi ta yi ya ce ba nasa bane ba" cike da amanna ɗari bisa ɗari suka gazgata sarki.
Nana ta ce "To kai ya aka yi ka sani, bayan baka nan aka yi?"
Ya kalli Nana bai ce mata komai ba ya tashi ya nufi kan matar. Ya saka Salamatu ta ɗebo ruwan magani, aka bawa matar ta sha. Ya dunƙule hannunsa ya buɗe tafukansa aska ta fito, ya saka aka buɗe cikin matar, ya din ga yi mata ƙananan tsagu da askar. Wannan karon sanho ne a jikinsa, (jakar magunguna) zabira (Jakar wanzamai ta kayan aski)
A wannan ƙaramar jakar, ya ciro garwashi jawur, ya ɗora a kasko ya zuba wani magani a kai.
Take matar ta hau tari, ya kama cikin ya lailaya ya tattara shi guri guda, sai ga wani jini baƙi ƙirin guda-guda yana fitowa daga cikin. Sai da jinin ya gama fita, ya tattare guri guda ya zama wani baƙin muzuru. A take cikin ya baje, Sarkin baka ya danƙi muzurun ya jefa a cikin sanhonsa ya ce "Aljani ne yake ta yi mata wannan siddabarun. Salamatu a kaita gurin su 'yar ƙashi ɗaya, a tsumata zuwa jibi a sallame ta" Sai da Nana ta razana da abin da ta gani.
Bayan fitarsu ya kalli Nana ya ce "Idan ki ka kuma ƙaryata ni a gaban mutane, sai na je na ɗaure ki a cikin mahaukatan nan kema"
Nana ta ce "Amma ka ce ƙaisar ba zai kamu ba"
Ya ce "Zai kamu, ban yi niyyar kama shi bane"
Ta sake cewa "Amma ya ake ka ke wannan abubuwan haka? Ta ya ya ka ke sanin abin da baka nan aka yi?"
"'yan aike ne suke gaya mini "
"Aljnu kenan ko? Haramun ne fa hakan shirka kenan" "Ba shirka ba ne, taimakon al'umma muke yi"
"Wallahi shirka ce, har fa tsafi ka ke yi "
Dariya ya yi ya ce "A ina na yi tsafin?"
"Ga shi nan ina gani kana yi, ya aka yi mage ya fito daga cikin mutum, kuma ya ake yi ka ke tura abubuwa da yawa a cikin 'yar ƙarama jakar nan?"
Sarki ya ce "Aljihuna ne da yawa a cikin jakar"
"To buɗe in gani" ya yi murmushi ya miƙa mata jakar ya ce "Buɗe da kanki" cike da ƙwarin gwiwa ta karɓi jakar, babu fargabar komai ta fara dubawa. Ya zuba mata ido yana dariya.
Sai dai ta zazzage jakar babu komai a ciki.
Ta kalle shi ta ce "Wallahi tsafi ne ina magen da ka saka a ciki ya tafi?" Ita kanta Nana tana mamakin yadda ta daina kewar gida gaba ɗaya, take jin kamar ta daɗe da sanin sarkin baka.
"Idan kin yadda ki bayar da magani, zan nuna miki yadda nake komai, ki koma gida ki taimaki mutane"
Ta girgiza kai ta ajiye masa jakarsa.
"Ki je ki huta, anjima tare za mu fita farauta da ke, ki je ki yi bacci yanzu"
Ta waro ido ta ce "Da wa za ayi farautar? Amma dai ba ni ba ko?"
"Eh ba ke ba" ya bata amsa
Ta juya da baya da baya, ta fita. Tana zuwa ɗakin da take, ta ga hayaƙi da wani irin ƙauri mara daɗi, cikin abin da bai fi mintuna uku ba, bacci ya kwashe ta.
Da Ƙaisar ta fara tozali, zaune a kan wani dutse a cikin wani rafi, ya miƙe ƙafafuwansa a cikin ruwan masu azabar tsayi kamar itacen dogon yaro. Duk da ta riga ta saba da ganinsa, ba ta fiye razana dan ta gan shi ba, amma biyo bayan tuna mafarkin da ta yi da shi, a cikin sahara ya sanya ta zura da gudu tana neman hanyar guduwa.
Ta yi gudu mai nisan gaske, ta ga wani gida, kawai ta faɗa gidan, tana addu'a a zuciyarta amma ta kasa furta ta, a bakinta. Sai dai bayan shigarta gidan, ta nemi hanyar fita ta rasa, kofofi kashi kashi a gidan, duk ƙofar da ta bi babu hanya sai dai ta sake dawowa guri ɗaya.
Ta dinga buɗe ƙofofin amma ta rasa hanya.
"Ina za ki ne?" Ya tambayeta bayan ya ajiye wata kwalba, jikinsa sanye da fararen kaya yana ɗigar da ruwa.
"Yau kuma tsoro na baki? Ko ba ki yi zaton ganina yanzu ba?"
Kuka Nana ta saka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, kar ka ƙona ni yau ma, dan Allah"
"Yaushe na ƙona ki?"
Nana ta ce"Ranar da ka zama tsoho ka koma raƙumi, ka yi haƙuri dan Allah"
Ya girgiza kai ya ce "Ba ni bane"
"Wallahi kai ne"
"Ni ban yi wannan tsufan ba ai, ba ni bane"
Cikin kuka ta ce "Kai na gani a sahara, ka zama raƙumi kana feso mini wuta"
Ya sake cewa "Ba ni bane ba, tawagar buzayen da ki ka gani ne lokacin da ku ka shiga gidan. Ni ban yi wannan tsufan ba dudu sheruna nawa ban fi ɗari biyar da goma ba, yaro ne ni"
Galala Nana ta saki baki tana kallonsa, shekara ɗari biyar da goman ne yaro. Tambayoyi ne fal a cikinta amma tana tsoron ta tambaye shi ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.
Ya ce "Kalli can" ta kalli gurin da ya nuna mata.
Suwaiba ta gani tana ta ihu ana danneta, mama na kuka tana tofa mata addu'a, sai fizge-fizge take yi tana kiran sunan Nana.
Cikin damuwa Nana ta ce "wai me ya sa take kiran sunana, ba fa ni ba ce ba, ni me na yi mata?"
Ya watsa wani abu daga hannunsa a gurin da take ganin su Suwaiba, sai ga wannan bararojin, tana ta zuƙar jinin Suwaiba, sannan jikin Suwaiba na ci gaba da zubar da jini ta huda-hudar nan da jikinta ya yi da ta fesa turare.
Ɗif ta daina ganinsu, ta juyo gurin ƙaisar cikin damuwa, sai dai ba ta yi magana ba.
"Kin san dalilin da ya sa na ƙyale mutumin nan, da ki ke gidansa? Wasu dalilai ne, ki gaya masa har yanzu bai san ni ba, duk hatsabibancinsa akwai sararin da bai isa ya jefe ƙafarsa ba. Na zuba masa ido ne na ga iya gudun ruwansa, amma dole sai na nuna masa iyakarsa, kuma zan gani tsakanin ni da shi waye zai yi maganin wani, kuma wannan abubuwan da yake yi miki akwai wani abu a ransa za ki ce na gaya miki "
"Mene ne a ran nasa?"
"Za ki gani, ya ce yau zai tafi da ke farauta, zai ci gaba da nuna miki magunguna. Zan ga iya ƙarshen hatsabibancinsa"
Nana ta yi sororo tana kallonsa, duk da tana son tambayarsa, amma tana tsoron ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.
Ya ce "Wuce ki tafi"
"Ai na rasa ƙofar fita"
"Bi waccan" ya yi maganar yana nuna mata hanya. Tana fita ta ganta a tsaye a ƙofar ɗakin da take tare da sarkin baka. Yana sanye da shigar hargi(irin shigar da maharba suke yi) Bayansa rataye da kwari da baka.
Ba ta iya musa masa ba, ko jin tsoro ko makamancin haka ba, kawai ta saka kai ta bi shi. Daga shi sai ita yana gaba tana bin sa a baya hannunsa da fitila. Wata ƙofa suka je, ya ɗaga asabarin ya shiga, Nana ma ta bi bayansa. Suna shiga ƙofar ta gansu a dokar daji.
Sai a lokacin jikin Nana ya hau rawa, tsoro ya kama ta, ta ja da baya ta domin koma amma ta ga babu ƙofar da suka shigo. Ya kalle ta ya ce "Kar ki tsorata, babu abin da zan yi miki, bari na ɗaure dajin"
"Ina ne nan?" Tayi maganar cikin tsoro.
"Dajin igbele ne, na jihar delta"
Ta waro ido cikin kiɗima ta ce "Delta kuma? Daga Kanon mu ka zo delta?"
Sarki ya ce "Eh, wata kububuwa nake son kamawa zan yi magani da dafinta. Daji ne mai haɗari ana tsafi iri iri a dajin, amma da na kama Kububuwar za mu tafi" ya yi maganar yana haɗa wuta a gurin, ya zuba wani turare yana kewaye wutar. Ita dai Nana ta yi shiru tana kallonsa.
Sai da ya gama sannan ya yi gaba, ta bi bayansa.
Gurin wani dutse suka nufa, daidai jikin dutsen akwai wani kogo, ya ajiye fitilarsa ya watsa wani abu a bakin kogon. Ya ciro wata raga a cikin sanhonsa ya kafa a gurin. Nana tana tsaye tana kallon ikon Allah.
Ya gama ya ce "Mu je wani dajin na nuna miki wasu abubuwan"
Al'ajabi ya hana Nana magana, suna tafe yana nuna mata wasu tsirran yana gaya mata amfaninsu.
"Kin ga idan ki ka samu kashin giwa, da hauren toronta, wato namijin giwa, da kashin ungulu, ki ka haɗa su da kaucin kuka, da tazargade da garin ganyen kuka, da ganyen magarya arba'in ki haɗa jan miski, a haɗe su guri guda. Idan aka yi hayaƙin su, duk wani ƙaramin shaiɗani sai ya gudu, ke babban ma sai ya sha wahala wallahi, kuma aljani sai dai ya ganki ya bar ki"
Nana ta dube shi ta ce "To ta yaya mutum zai samu wannan abun, duk sai mutum ya yi wannan wahalar? Najasar dabbobi ce za ta hana aljanu shafarsa? Bayan ga azkar da Alqur'ani"
Sarkin baka ya yi murmushi, yana son ƙi faɗin Nana ƙwarin gwiwar ta na burge shi ya ce "Hala ke da Ƙaisar yake tare da ke, ba kya azkar da karatun Alqur'ani"
Cikin damuwa ta ce "Ina yi mana, amma wasu lokutan idan ban yi ba na fi zama lafiya ma, na fara tsorata kar hakan ya sanya imanina ya yi rauni".
Ya yi murmushi ya ce "Magani fa ba ƙarya ba ne ba, kin yarda bature ya baki maganin ciwon kai ki sha ki warke, wannan ba shirka ba ce ko, wannan technology ku ke wa ko?" Sai kuma ta ɗan yi shiru.
Ja ya yi ya tsaya, ita ma ta tsaya, hasken wuta ta hango daga nesa, a hankali suka ƙarasa daf da gurin, suka tsaya, amma su na iya hango komai.
Mutane ne tsirara sai ɗaurin ƙyalle ja a ƙugunsu, maza da mata su na kewaye wuta kowa da ɗan ƙoƙo a hannunsa. Wani mutum a tsakiya yana ta karanta wasu abubuwa, gefe wata mata a kwance ba ta ko motsi da tsohon ciki a jikinta. Ta ga mutumin nan ya nufi kan matar da wata wuƙa a hannunsa yana karanto wasu abubuwan.
Razana ta yi, za ta ƙwala ihu sai kuma ta daina ganinsu, ta ga sun koma dajin da sarkin baka ya yi wa kububuwa tarko.
"Idan muka tsaya, ki ka ci gaba da gani, za ki iya rasa hankalinki"
Jikin Nana na tsuma ta ce "Su suka kashe matar?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh, jaririn cikinta za su cire, jininsa za su sha, ƴan ƙungiyar asiri ne. Nan da ki ka gansu manyan mutane ne, da suka sadaukar da lahirar su domin duniya. Akwai 'yan kasuwa a cikin su, da 'yan siyasa"
Jikin Nana sai tsuma yake yi, ba ta taɓa tunanin da gaske akwai ƙungiyar asiri ba, ta zata shaci faɗi ne kawai ake faɗa.
"Bari mu koma ki kwanta, da asuba zan dawo na kama macijiyar nan, naga duk a tsorace ki ke . Sai dai ina son mu yi wata magana da ke".
Jiki a sanyaye ta ce "Wace irin magana ce?"
"Ina son ki sadaukar mini da uban duƙusa wato ƙaisar, na din ga aiki da shi!"
Littafin nan 1k ne a telegram ta wannan account ɗin 0069685771 Aisha Adam Stanbic ibtc
Sai shaidar biya ta Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOTA/002
P14
Cikin hanzari Nana ta ce "Na yarda na amince, na bar maka shi"
"Ai ba da baki kawai za ki faɗa ba, akwai buƙatar yin wani aiki, idan kin amince za ki sadaukar mini da shi, za ku rabu har abada"
"Eh na amince"
Sarkin baka ya ce "Za mu ƙarasa maganar da safe"
Kawai ta gansu a ƙofar ɗakinta, suka yi sallama ta shiga ta kwanta. Sai dai jikinta na ta tsuma da tunanin wace matar aka kashe, kuma ake ƙoƙarin cin zarafin gawarta haka.
"Hmmm za ki sadaukar wa wani ni ko? Har kin yi sabo da shi haka kin yarda shi?" Ta ji maganar ƙaisar a tsakanin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta.
"Eh zan sadaukar da kai, muddin hakan zai sama mini lafiya da nutsuwa" ta yi maganar a fili. Dariyarsa kawai ta din ga ji, gidan baki ɗaya yana amsa kuwwa.
Bayan ta yi sallar asuba, ta zauna tana azkar bayan ta idar, ta yi shiru tana tunani, addu'a ta din ga yi Allah ya rabata da ƙaisar, muddin abin da sarkin baka zai sakata bai saɓa wa Allah ba, za ta yi domin ta rabu da ƙaisar.
Da kanta take zuwa gurin Sarkin baka yanzu, duk ta san hanyoyi a gidan. Kuma ganin ta samu sassauci daga takurar ƙaisar, da sanya mata cututtuka da sauran damuwowi ga abinci tana samu babu mai takura mata da damuwa, ga kuma sukulle da kyautatawar da sarkin baka yake yi mata, sai ta fara sakin jiki da mantawa da damuwar da take ciki.
Abin mamaki, yau da Alqur'ani ta tarar da sarkin baka, bugun warshi yana karantawa, sai da ya idar sannan suka gaisa suka fita.
Sai da suka fara zuwa gurin da ake harhaɗa masa magunguna, har da injin niƙa a gurin, shi ma ma'aikatan gurin daban, ga tarin saiwoyi da tsirrai.
Gaggaisawa ya yi da masu aikin gurin, ya ce "An kawo saiwoyin nan kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Salamatu.
Salamatu ta ce "A'a sarki, ta rafi ake jira, ba ta kawo ba"
"Aljanar nan akwai sheɗainiya, idan ta bari na nemo wani ya ɗebo mini, wallahi sai ta ɗanɗan kuɗarta" Nana ta kalle shi ta ce "Aljana kuma?"
"Eh, wasu saiwoyin ai sai dai aljani ya ɗebo, ba dai mutum ba. Akwai abubuwan da a cikin ruwa muke ɗebo su, kuma akwai dai-dai lokacin da muke ɗibar su, idan ba aljani ba sai dai ka nemi masunta, su kuma idan ba su ga dama ba, ba za su baka ainihin abin mai kyau ba" Yana gama yi wa Nana bayani, ya ci gaba da maganar sa.
"Akwai masu shanyewar ɓarin jiki, mutum biyu Salamatu a je a duba, idan na aljanu ne, a jira ni ki ba su taimakon gaggawa. Idan kuma na larura ne maza a haɗa musu magani, a ɗauki ɓawon kwakwa, da sassaƙen zogale, da zoɓo da ɓawon abarba, a dafa su sosai, a ƙara ruwa, a din ga basu kofi ɗaya sau uku rana. Ba cin man gyaɗa, ba cin gishiri ba cin kanwa, uzairu ya yi musu ƙaho zan zo na ga jikin nasu" cikin girmamawa ta ce "To sarki"
Tun Nana tana mamakin al'amuran sarkin baka, har ta zuba wa sarautar Allah ido kawai
Amma duk da haka, Nana ta kan kasa jurewa sai ta tambayi wasu abubuwan, yanzun ma ɗan gyaran murya ta yi ta ce "Sarki, su wannan magungunan da ka ke bayarwa haka da ka, ba ka tunanin ya yi wa mara lafiya illa, a asibiti akwai maganin da idan mutum yana da wani ciwon fa ba a ba shi, ku kuma nan ba tantancewa ku ke yi ba, kuma ba auna maganin ku ke yi ba"
Ya gyara zaman sanhonsa ya ce "Ban da sharri irin naki, da kuma abu irin naku na 'yan boko aƙida, da ku ke cewa maganin hausa ba shi da awo, ba yanzu a kunnen ki na faɗi gwargwadon abin da za a ba su ba? Wanda ya sani fa ya sani Asma'u, wanda bai sani ba bai sani ba, galibi gurin masu neman na Abinci kawai ake zuwa, wani koya ya yi amma ba a koya masa maganin yadda yake ba, dan ba kowa ne yake yarda ya bayar da sirrin sa ba. Ni na gada kuma na koya. Bature ya yi nasa ban raina masa ba, kuma nima na yi nawa ba wanda ya isa ya raina mini. Ke shaida ce duk abin da ba ni da maganinsa ina gaya wa mutane. Kuma ni ba dan neman kuɗi nake bayar da magani ba. Ki din ga tambayata abin da ba ki gane ba zan yi miki bayani, amma muddin na ji kushen abin da nake yi, ba zan ba ki amsa ba, kuma kin yi wa kanki, dan ba ki san a ina abubuwan da ki ka koya a gurina, za su iya amfanar ki ba, ko su amfani wani ba" jin sa kawai Nana take yi, tana ganin me za ta amfani wani da wannan abubuwan da babu scientific proof ko research a kan su.
Bayan sun gama da nan suka tafi ɓangaren da ba ta taɓa zuwa ba a gidan.
Shi kuma garke garke ne na dabbobin dawa da na gida, wani abin ma ba ta taɓa ganinsa ba.
Ya din ga nuna mata dabbobin, da magungunan da ake yi da wasu sassa na jikinsu.
Yana cikin yi mata bayani, ta ga ya yi shiru ya daina magana, ta leƙa fuskarsa za ta yi magana kawai ta ga ƙwayar idonsa ta koma baƙa gaba ɗaya, jikinsa ya hau tsuma.
Cikin sanhonsa ya zira hannu, sai ga shi ya fito da wani shirgegen zaka, ya gaji da riƙa cerarsa jawur da ita.
Jiki na tsuma Sarkin baka ya saka hannu ya raba kan zakaran da gangar jikinsa. Ya ɗaga gangar jikin, ya tsiyaye jinin a bakinsa, ya gama ya hau cin gangar jikin zakaran a ɗanyensa da gashinsa da komai yana zazzaro ido.