Buzu book 1 complete - Chapter 23
Buzu book 1 complete Chapter 23: Buzu book 1 complete Chapter 23. "Da farko dai ina mai ba ki haƙuri a kan abin da ya faru, kin san komai Allah ne yake…
4,469 words
"Da farko dai ina mai ba ki haƙuri a kan abin da ya faru, kin san komai Allah ne yake ƙ'addarawa. Jikina ya yi matuƙar sanyi da abin da ya faru. Na gane dalilin wannan auren ne ya sanya muka baro gida. Ki yi haƙuri bawa ba ya tsallake ƙaddararsa. Ina yi muku fatan alkhairi da fatan Allah ya baku zaman lafiya. Na san abubuwan da mu ka ba ki na aure, be kai abin da ake kashe muku na aure ba, amma ki yi haƙuri a hankali za mu duba a yi miki, kin san masu ƙaramin ƙarfi ne mu. Dama ɗan kuɗin gadin tarawa muke yi, za mu tura gida wannan abu ya bijiro, kuma kuɗin hannunmu duk ya ƙare. Dan Allah ki yi haƙuri da abin da Allah ya ƙaddara miki."
Nana dai ba ta ce komai ba, ya sake nuna mata kayan da suka zo da su ya ce "Ga sayayya nan, abin wanka ne da kayan wanke baki, da ɗan abin da ba a rasa ba na kayan tsafta. Yanzu mu na sauri mu koma, ba wanda zai kula da ƙofa dole mu koma da wuri, amma zamu dawo da yardar Allah" su ka ƙara yi musu fatan alkhairi. Shi kuwa tun da ya zauna, ƙwaƙwƙwaran motsi ma bai yi ba, balle ya tofa wani abu ba.
Sai da Nana ta ga sun miƙe baki ɗaya shi yana zaune, sannan ta fara zazzaro ido.
Gaba ɗaya sai suka juya yare, su na yi masa magana, har suka gama maganar, shi dai bai ce uffan ba.
Ɗaya bayan ɗaya suka fice, hakan ya ƙara tabattar mata da shi ne mijin nata. A take ta tuna Sule ya taɓa gaya mata ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa. 'kenan mahaukaci Baba ya aura mini?' ta tambayi kanta. Ƙoƙarin tuna wasu abubuwan take yi a kansa, amma abu ya gagara, ta ji gaba ɗaya kanta ya toshe.
Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta yi sallar isha'i. Sai dai bayan ta yi alwala da ƙyar ta baro banɗakin, saboda duk taku sai ta ji tamkar zuciyarta za ta fashe. Ƙafafuwan ta su ka gaza ɗaukar ta, a dole ta zauna ta kalli gabas, ta tayar da salla. A zaunen ma jiri take yi, da haka ta yi salla.
Shi dai bai kula ta ba, bai kuma tashi daga gurin da yake a zaune ba, kamar gunkin budda.
Ta idar da sallar, ta koma jikin bango ta matse jikinta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ji take kamar ta kurma ihu, ga sanyin nan da take ji ƙaruwa yake yi, tsigar jikinta sai tashi take yi.
"Allah ka dube ni, dan Allah ƙaisar kar mu yi haka da kai, ni hauka shi hauka ta ya ya za a yi wannan zaman" ta furta hakan a hankali. Sun shafe dogon lokaci, kamar babu halitta mai motsi da ta wanzu a gurin, Nana tana ta tufka da warwara a zuciyarta, kawai ta ga ya tashi tsaye. Zuciyarta ta ƙara tsinkewa da tsoro da razani, tare da hakaito mata miyagun abubuwa, yanzu idan ya yankata a gurin nan ya gudu fa? Mussaman wannan takobin da take gani. A hankali yake tafiya, ya tafi gefen wardrobe ɗin ɗakin, da aka kafe abin rataye kaya. Ya cire takobin ya rataye ta. Ba tare da ya waiwayo ba, ya fara kwance rawaninsa. Kasancewar ya juya mata baya, ya sanya ta zuba masa ido ko ƙiftawa ba ta yi. Ya kwance rawanin gaba ɗaya, ya ninke Nana ta zuba wa sarautar Allah ido, ganin kansa ɗauke da gashi baƙi wuluk, ya tufke shi tamkar an yi wa kan bahauhishiya saloon. Ya saka hannu ya zare rigar jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana kallon gefe, kamar mara gaskiya.
A hankali ta ƙara ɗagowa, ta ganshi da dogon wando, da shirt, ya ninke rigar da rawaninsa, ya buɗe wardrobe ɗin ya saka kayan a ciki.
Ba ta san ya aka yi ba, kawai sai gani ta yi sun haɗa ido. A take ta tuno ganin da ta yi masa, har ta suma a ɗakin su.
Da wata irin azama ta tashi, duk da bugun zuciyar da take ji da kuma jiri, ta ja da baya ta tsaya cikin tsoro da razani.
Ya ci gaba da kallonta, ba tare da ko ƙifta ido ba. Kawai Nana ta fashe da kuka, ba tare da sanin dalilin da ya sanya ta kukan ba.
Gani ta yi ɗakin yana juya mata, ya kawar da kansa daga kallonta, ya fice daga ɗakin. Fitarsa ke da wuya ta silale a gurin ta faɗi.
A hankali ta fara juyi tana tari, a cikin kunnuwanta take jin bugun zuciyarta, ta ja jikinta ta tashi da ƙyar. Ta karkaɗe hannunta saboda ƙura, ƙaisar ta gano sanye baƙar riga tana jan ƙasa, yana shirya litattafan sa, yana goge su.
Da ƙyar tarin ya ɗan lafa mata ta ce "Ƙaisar"
"Ya aka yi?" Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.
"Tsoro nake ji, ji nake yi kamar zan mutu. Ba ka ji yadda zuciyata take bugawa ba"
"Ina jin yadda take bugawa mana, ai mutuwar ma za ki yi idan ba ki yi wasa ba, tun da ke dai kin ƙware a taurin kai. Wannan mutumin ƙila shi zai yi ajalin ki. Ki kan ji bugun zuciya da sanyi ne, idan ina guri to me yasa ba na gurin daga ke sai shi ki ke jin bugun zuciyar?" Ya jefo mata tambayar.
Nana ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ware ido, amma ta kasa magana. Ya ce "Eh, ai na gaya miki ba ki da tabbacin abin da ki ka aura, mutum ne ko kuma jinsinmu" yana gama maganar ya yi gaba. A rikice Nana ta bi shi tana faɗin "Dan Allah ka tsaya ka saurare ni, yanzu ya zan yi dan Allah?"
Ya waiwayo ya kalle ta ya ce "Au tambayata ma ki ke yi ya ya za ki yi? Shirka fa ki ke ƙoƙarin ko kin manta?"
Nana cikin kuka ta ce "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi tsoro nake ji idan na ci gaba da rayuwa da shi, zan iya mutuwa"
Ƙaisar ya ce "Ai da da na gaya miki ba ki yadda ba" ya juya zai tafi, ta riƙo rigarsa"
"Zan watsa ki ta waje, idan ki ka kuma bi na" Za ta yi magana ya ce "Sai kuma ki yi" kawai ya ɓacewa ganinta.
Kawai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da kuka.
Yana zaune a gefen ɗakin nasu, ya na shan hantsi, sai ga Sule ya zo da kwandon kayan abinci.
"Ango har ka tashi? Ya mariée ɗin ?"
Ya nuna masa ɗakin, alamar tana ciki. Gaba gaɗi Sule ya nufi ɗakin da kwandon Abincin cikin hanzari Buzu ya miƙe ya tsaya a ƙofar ɗakin. Sule ya ce "Au yi haƙuri, bari na zauna daga nan" ya nemi guri ya zauna a gefensa.
Nana kuma ta buɗe idonta, ta ganta kwance a kan katifar, jikinta babu naɗin lafayar da aka kawo ta da shi, sai riga da skirt ɗin ta na ciki, kanta ko ɗan kwali babu. A razane ta dubi jikinta tana tambayar kanta, ko ya yi mata wani abin ne?. Ta kalli gefen katifar ta ga lafayar a ninke a ajiye. Da azama ta yinƙura ta faɗa banɗaki, amma ba ta ga alamar an yi mata wani abu ba. Ta yi tsarki, ta yi alwala tana ta istigfari ta yi sallar asuba, cike da jin kunyar Ubangiji, yadda lokaci ya ja gari ya yi haske ba ta yi salla ba.
Bayan ta idar tana jiyo Sule yana ta zuba da yaren su, shi dai ba ta ji maganar sa ba. Ta yi mamakin abin da ya sanya Sule kasa yin zuciya ya ci gaba da surutu ba tare da ana kula shi ba.
Babu tsammani ya shigo ɗakin, ba tare da ko sallama ba. Aikuwa ta zabura ta ja da baya tana kallonsa. Kai tsaye ya nufo ta, ya ajiye mata kwandon Abincin a gabanta. Ya nemi guri ya zauna ya zuba mata ido, da kwandon kayan abincin a tsakiyar su.
Nana ta sunkuyar da kanta, sanyi na ratsa ta.
"Zan ci abinci" ta ji muryarsa kamar daga sama, ɗaga kai ta yi ta kalle shi, ji ta yi kamar ta ce masa to ya ci mana, sai kuma ta tuna ashe fa wai yanzu mijinta ne. Mamaki ne ma ya kamata, dan har a lokacin tana mamakin idan ba kurma ba ne ba.
Ta janyo kwandon ta sassuke abincin, ta fara ƙoƙarin zuba masa, kawai ta ga ya tashi ya fita. Sai ga shi ya dawo da abin da suke hura wutar dafa shayi, har da butar shayin ma, da alama abin da suke yi a wajen tun ɗazu kenan, shan shayin.
Ya buɗe cikin kayansa, ya ɗaukko turaren wuta, ya zuba a kan sauran garwashin. Take ɗakin ya karaɗe da ƙamshi mai daɗin gaske. Ya samu guri ya zauna, ya karɓi abincin, ya koma gefe ya sauke takunkumin rawaninsa ya hau ci.
Nana kuwa kasa cin abincin ta yi, ta yi tsuru sai satar kallonsa da take yi, ya gama ci ya ɗauki kwanukan da ya ci, ya fita waje ya wanke ya dawo ya ajiye mata. Ya tsiyayi sauran shayinsa na butar, ya shanye abin sa.
Ya kewaye ta, ya ɗauki pillow ya koma can gefe ya ajiye ya kwanta. An shafe tsawon lokaci, na zaune ba tare da sanin abin yi ba. Jin yunwa ta uzzura mata ya sanya ta ɗan zuba abincin ta fara ci. Tun tana cakala har ta saki jiki, ta ci gaba da zurawa kawai suka yi ido huɗu, tana ta loma. Sai kuma ta yi sak, ta ci gaba da ci ta kasa kamar wadda ta aikata rashin gaskiya, kuma ya ƙi daina kallonta. Ƙarshe sai haƙura ta yi da cin abincin, kallon da yake yi mata duk ya sanya ta damu.
***** Gidan su Nana tun a ranar kowa ya watse, dan baba faɗa ya yi ta yi, yana cewa duk wanda ya kwana sai dai ya nemi abin da zai ci, shi ba shi da abin da zai sake bayarwa a bawa mutane.
Suwaiba ta ƙarewa ɗakin su kallo ta ce "Ohhh abin tsiya, ko tsinke ba ta bari ba, duk ta kwashe komai balle mu gada."
Mama ta ce "Au ke har wata tsiyar ki ke saka ran gada a gurinta? Me za ki gada banda gayyar masifa, ai gara da tarkata komai ta tafi, ma sake mu miƙe ƙafa mu huta mu ma"
Jamila da ta shirya tsaf za ta fita ta ce "Aikuwa dai"
"To kafin hankali ya dawo kan ku, Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari 'yan uban uban su, wanda kowa sai ya koka a tashi kan munafukan unguwa da na family"
Suwaiba har da tsalle ta ce Amin Mamanmu maganin kukanmu.
Jamila ta yi murmushi ta ce "Ni dai sai anjiman ku"
Mama ta ce "To a sauka lafiya"
*****
A tsanake take kallon yadda mai gidan nata, yake ɗan yamutsa fuska bayan ya kammala cin abinci.
A hankali ta ce "Daddy"
"Na'am baby"
"Ya dai? Jikin ne ko garin? Na ganka so silent"
Ya ɗan yi miƙa ya ce "Pressure ce ta ɗan yi mini yawa wallahi, ina shirin tafka asara ne, kwana biyun da ban je kasuwa ba, har an yi mini ɓarna wallahi. Ga kaya sun iso Nigeria na gama clearance amma coustom sun ƙi sakar mini kayan"
"Subhnallah, in sha Allah ba za ka yi asarar ko naira biyar ba. Allah zai warware komai, bari mu duƙufa da addu'a in sha Allah ba wani abu"
Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, ɗan duba mini paracetamol idan ki na da shi, kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau"
Cikin damuwa ta ce "In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na buƙar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ƙaddara"
Ya girgiza kai ya ce "A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daɗi"
Ta tashi ta ce "Bari na ɗaukko maka" ta nufi bedroom ɗin ta.
*****
Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ƙarya.
"Na rasa gane abin da ya faru gaba ɗaya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura ɗin, na ba shi kuɗi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi ɗin a zahiri, ban kira shi ba na kasa tunawa, ni dai kawai na ganshi a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an shaƙe ni, da ƙyar nake numfashi"
Malam Gambo ya yi shiru ya ce "Kuma ka tabattar ba ka yi maganar da shi a zahiri ba?"
"Wallahi na kasa tunawa"
"Hakan na nufin da akwai matsala kenan, ka ɗan bani lokaci zan yi bincike"
Cikin damuwa ya ce "Zuwa yaushe kenan? Ni fa duk abin da za ayi sai dai a yi, fatana kawai burina ya cika"
"Kar ka manta burin naka ba ɗaya bane ba, kar ka manta bayan burinka na son haska taurarinka, na mallakar dukiya mai tarin yawa da kujerar siyasa, akwai burinka na son kawar da babban amininka, idan ka yi wasa za mu yi jifar gafiyan ɓaidu, dole ka tattara hankalinka a kowane ɓangare, muddin ba ka durƙusar da shi ba, taurarinka ko sun haska ba za ka taɓa shan gabansa ba, dan haka ka kula da kyau"
Ya yi ajiyar zuciya ya ce"Na fahimta, shi ma ba mantawa na yi da nasa ɓangaren ba, shi ma na shirya komai, amma ina sauraren ka abin da binciken naka ya baka sai ka sanar da ni. Dan ko ya kama na zubar da jininsa ne zan yi domin na samu cikar muradina"
"Ka dai dakata, zuwa lokacin da zaka ji daga gare ni tukuna"
Da ƙyar ya lallaɓa Alhaji Zailani ya kwantar masa da hankali.
*****
Cikin tsananin tsoro da razani Jamila take kallon hajiya Sa'a, jikinta na wata irin tsuma cikin faragaba da tashin hankali. Yawun da za ta haɗiye ma ya gagare ta, saboda tsoron da ya mamaye ta.
"Jamila, na gaya miki sirrinmu, idan kin ga dama ki yi shiru da bakin ki, ki tara arziki ki bar shi, idan kuma kin so ki fallasa, ba ki da hujjar kare kanki, kuma sai na ƙarar da zuriyar ku, ta hanyar bayar da jinin ku ɗaya bayan ɗaya. Abin farko da nake buƙata ki taimaka mini, shi ne mu na buƙatar jinin yayar ki Nana, a baya na sha baki abu ki bata, ba tare da kin san dalilin hakan ba, to yanzu na gaya miki abin da nake so. Dan haka za ki taimake mu muma"
Jamila na jan numfashi da kyar cikin rauni ta ce "Amma ba za ta mutu ba?"
Safiyya ta ce "Ke ina ruwan ki da zata mutu ko ta rayu, idan aka so har babanki za a iya nema ki bayar, to dan dai wannan da ba uwarku ɗaya ba"
Hajiya sa'a ta ɗaga mata hannu ta ce "ƙyale ta, dole za ta ji banbarakwai abin, ina ga sai dai mu sanya ta a wani ɓangaren, tana da tsoro sosai da sosai. Yanzu dai ki fara yi mana wannan aikin tukuna"
Jamila cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Hajiya a canza mini wani, tausayinta nake ji" har maman khairat ta hasala za ta yi kan Jamila da masifa, hajiya Sa'a ta ɗaga mata hannu. Ta dubi Jamila ta ce "Ba fa kashe ta za a yi ba, ɗan kaɗan muke son jinin nata"
"To ai ta yi aure, babanmu ya aura mata wani buzu" ta yi maganar hawaye na cika mata idanu.
"Eh na san ta yi auren, na ga duk kin tsorata kin damu, bari na kawo miki lemo ki sha" ta tashi ta ƙiftawa maman khairat ido, ta fice daga ɗakin.
Ba a jima ba ta dawo da lemo a cikin glass cup, ta miƙa wa Jamila. Jin sa da sanyi, ya sanya ta karɓa kai tsaye ta fara sha. Sai dai tun kafin ta gama shan lemon, jiri ya fara ɗibar ta.
Maman khairat ta karɓe kofin lemon, Jamila kuma ta silale, cikin fita hayyaci.
Suka sassaki labulaye, suka kashe fitila, duhu ya mamaye ɗakin, ta kunna kyandira, ta bawa maman khairat ta riƙe mata, ta ɗaukko wata jakar fata ta zazzageta.
Wani irin tarkace ya zubo daga ciki, tare da layoyi, ta cire wa Jamila kayan jikinta, ta din ga sha mata wani irin mai jawur da shi. Bayan ta gama ta ɗaukko wata allura a cikin wata laya, ta sokawa Jamila a wuyanta. Aikuwa ta zabura jikinta ya yi wata irin girgiza. Ta juya bayanta ta kuma soka mata a ƙeyar ta. Nan ma jikin nata ya sake girgiza. Ta sake saita ƙahon zuciyar ta, ta sake soka mata. Jikinta ya din ga tsuma ba tare da ta tsaya ba. Hajiya sa'a ta din ga karanto wasu abubuwa cikin wani irin yare, jikin Jamila na ci gaba da rawa tamkar ana girgiza ta. Ta kama hannunta, ta saka mata wasu awarwaraye, sannan ta kawo wani bargo ta rufe ta da shi.
****
Tamkar mujiya haka Nana take zaune a ɗakin nan, duk abin duniya ya ishe ta, yamma tana yi ya ɗauki radiyo ya fice ya bar ta a ɗakin ita kaɗai.
Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su. Ɗan kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daɗi sosai da sosai. Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata wannan abin. Ta haɗa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe.
Ta janyo jakar kayanta, ta buɗe wardrobe ɗin, ta ga ɓangare ɗaya shaƙe da kayansa, sai da abin ya bawa Nana mamaki. Ɓangare ɗaya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ta daɗe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ƙarewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ƙarshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a kai ga ɗinkawa ba. Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe ɗin. Drower ƙasan wardrobe ɗin kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad ɗin ta. Ta gyara kan katifar ta ɗame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ƙatuwar katifa.
Wani murmushin ne ya sake suɓuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta.
Ba ta san lokacin da ta ƙwala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba. Kuma kasancewar ta ƙure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faɗa kan katifar.
Taku ɗaya ya ƙara, ya tsaya a kanta yana kallonta.
Ayshercool 08081012143
29
Ƙara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa.
Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi zaune tana kallon wayar, gaba ɗaya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta.
Ta bi wayar da kallo, ta kasa taɓa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta ɗan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta ɗauki wayar ta duba ta ga a kashe take, sai ƙamshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya.
Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke.
Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ƙofar ɗakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta yi mata maraba, ta shimfiɗa mata sallaya ta zauna.
Bayan sun gaisa Nana ta ce "Ban gane ki ba"
"Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa"
Nana ta ce "Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo"
Matar ta ce "Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ai ban san da mutane a gidan ba"
Haula ta ce "Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo."
Zuwan Haulat sai ya ɗebe wa Nana kewa, su ka yi ta hira.
Sun daɗe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ƙofar ɗakin ta ce "Idan na fara fita, nima zan kawo miki ziyara"
"To shikenan, ai a nan baya muke"
Nana ta ce "Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?"
Haula ta ce "Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin"
"Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida"
Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin ɗan ƙaramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ƙoshi ba. Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa. Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai ɗaga kai ya kalle ta ba, ta fita.
Sai da Nana ta ji babu daɗi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi magana ba kurma bane ba, tsagwaron wulaƙanci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru.
Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne.
Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake ɗaukar kwanon da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai. Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun zuciyar, sai dai sanyi da take ji.
Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take ɗan dannawa, sai da ta saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa. Ya rage kayan jikinsa, ya ɗauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga ɗakin. Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banɗaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta shirya ta kwanta.
A iya saninta, wayarta take ɗan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta.
"Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?"
"Meye haka wai?"
"A ina?"
"Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?"
Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?"
A ƙule Nana ta ce "Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum ɗin ne ko akasin haka"
Ƙaisar ya ce "Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata ki tsaya kar allura ta tono garma"
"Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa"
Kawai ƙaisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce "Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa ba, ni ba jinnil ashiƙ bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne ba su yi mini ba, duk da wannan ma da na farga da wuri sai na ruguza shi, sai dai idan na matsa za ki iya rasa rayuwar ki baki ɗaya, shi yasa na ƙyale"
Nana ta ce "Saboda me?"
"Kawai" ya bata amsa.
"Amma wai da gaske aljani yana auren mutum?"
"Eh"
"To ku ina naku matan ku ke auren na mutum?"
Ya ce "To ai ni ba aljanin soyayya ba ne ba da za ki tambaye ni."
Nana ta ce "Amma ka hana ni aure? Me yasa ka saka Saleh ciwon ciki?"
"Ke ko duk matan bil'adama sun ƙare zan auri masifaffiya ne mai azabar taurin kai kamar ke ne?"
"Eh abin nan ne, da ake cewa makaho ga ido, ya ce wari yake, na fi ƙarfin ka ne kawai"
Ya ce "Ko?"
"Eh mana, dan Allah ka gaya mini ya ake yi ku ke auren bil adama"
"Ni ma ban sani ba, sai dai zan baki wani littafi ki karanta, soyayyar Aljani Ridwan, da bil adama" Nana ta zabura ta ce "Dan Allah, ya sarkin baka, a wane hali yake yanzu? Kuma ni ba littafin soyayya nake so ba, wannan littafin na Jaddul jinn nake so ka bani na ƙarasa karantawa"
"Ba zan bayar ba, kuma ba wannan ne ya sanya na kira ki ba, duba jikin mudubi, ki zo ki gaya mini abin da ki ka gani"
Nana ta ce "Wallahi ba zan kalla ba, masifa da bala'i kawai ka ke nuna mini a cikin mudubin nan, Allah ya sa ya tarwatse...
"Wallahi sai kin kalla, wataƙila zuciyar ki ta saduda, ki yi abin da ya dace"