Kenza eBookz

Buzu book 1 complete - Chapter 25

Buzu book 1 complete - Chapter 25

Buzu book 1 complete Chapter 25: Buzu book 1 complete Chapter 25. "Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka ɗazu ma ka jefa…

4,484 words

"Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka ɗazu ma ka jefa mini bedsheet a kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ƙarfi ta suma a gurin.

*****

Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana gefen gado tana shan abu a cikin kofi.

Da sallama ya shigo ɗakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce "Ya yi baccin?"

Ya ce "Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?"

Ta kwaɓe baki ta ce "Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu"

Ya ce "Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?"

Shukura ta ce "Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan"

"Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun shaƙu, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?" Ya yi magana yana karɓar kofin.

Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce "Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?"

Shukura ta ɓata fuska ta ce "Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi"

"Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya ɓaci" ya tashi ya fice ya bar mata ɗakin.

Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta.

Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya. Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, miƙa masa hannu take yi, tana faɗin "Dan Allah ka taimake ni"

Lokaci ɗaya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dunƙulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da durƙusawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi.

Mutumin da yake bin ta ya ƙaraso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi.

Cikin tashin hankali ta ce "Daddy"

"Ki yi haƙuri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki"

Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar naƙuda take faɗin "A'a Daddy, dan Allah ka bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah"

Ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake buƙata"

Mutumin nan mai farar riga, ya buɗe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa "Dan Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi haƙuri".

Bai saurare ta ba, ya durƙusa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faɗo.

Ya ɗauke shi har mabiyiyar, ya miƙa wa Alhaji Zailani.

Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wuƙa, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwan sa a sama.

Ihu take iya ƙarfin ta, tana yi masa magiya, amma ya ɗaga wuƙar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana ɗaga kai ta ga Nana. Nana ta jefa mata wata sharɓeɓiyar wuƙa, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa wuƙar da Nana ta jefo mata.

"Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?" Ta buɗe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta da ke ɗauke da matsananciyar damuwa.

"Meya faru?" Ya sake tambayarta.

Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali. Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba.

*****

Da safe Nana na ta karkaɗe ɗaki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki ɗaya. Sai dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin Ƙaisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi.

"Zan yi wanka" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara ɗakin.

Ta kalle shi ta ce "To banɗakin zan biyo ka ko ya za a yi?" Ta yi maganar cikin tsiwa.

Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba, kawai ya wuce banɗakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata.

"Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba"

Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet ɗin da ta gama shimfiɗawa ya rufa yana rawar sanyi.

A hanzarce ta ɗago a ƙule ta ce "Lafiya, meye haka wai?" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda a lokacin ta gama sanya zanin gadon.

Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya ɗauki bedsheet ya sanya ya miƙe, ya watsar mata da shi a gurin.

Ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata ɗakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna ya takure jikinsa, ɗumin ranar yana taɓa shi.

Nana ta ci gaba da mita tana ƙara gyarawa.

Muryar Habu ta jiyo, ta leƙa ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ƙasa-ƙasa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji.

Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ƙofar ɗakin. Ta amsa masa. Ya ce "Na shigo?"

"Eh bismillah" sai ta ga ya shigo shikaɗai.

Nana ta ce "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Ya rayuwar?"

Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce "Lafiya ƙalau"

"Ga wannan" ya yi maganar yana ba ta leda.

Jiki a sanyaye ta ce "Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ƙaddara, wannan ɗawainiyar ta isa haka, kullum sai kun kawo mana Abinci, ga ɗawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah"

Ya yi murmushi ya ce "Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni" Nana ta jinjina masa kai.

Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce "Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ƙarar ki, ya ce ki na yi masa rashin kunya, ki na ɗaga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi haƙuri da shi dan Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki yi haƙuri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare"

Nana ta haɗiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce "Hmm ƙara ta ma ya kawo ko? To shikenan na daina"

"Ki yi haƙuri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa"

Nana ta ce "Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma dawowa"

Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya miƙe. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai.

Ya zo ya wuce ya buɗe wardrobe, ya ɗebo kayansa masu datti, da ya nannaɗe ya bawa Habu.

Habu ya karɓa, ya yi musu sallama, ya tafi.

Nana ta din ga kallonsa, bakinta fal magana, amma ya ƙi kallonta.

"Shi ne ka ce ina yi maka rashin kunya ko? To me na yi maka na rashin kunya? Dama ashe ka na magana ni ce ba ka kulawa ko?" Ya lumshe idanunsa yana kaɗa ƙafar sa.

"Idan ba ka yi mini magana, ba zan san na yi maka laifi ba, ko na san abin da ka ke so ba, da wanda ba ka so" ta gama surutunta, ganin ba shi da niyyar tanka mata ya sanya ta kama wani abin.

Kayan miyar da Habu ya kawo, ta zauna ta gyara tsaf, ta yi greating ɗin su. Ta ɗora a kan gas. Tana jin yadda yake tari, saboda zafin attaruhu. Ta dafa taliya da miya.

Ya din ga bin ta da ido, har ta gama.

Ta zuba masa ta ajiye masa komai, ta tashi ta je ta yi alwala, ta dawo ta tayar da sallar azahar.

Ta idar ta yi azkar, ta ninke dadduma, ta gan shi ya haɗa gumi, yana cakalar abincin, fuskarsa ta yi jawur, sai gumi ne yake tsatstsafo masa.

"Lafiya ya na ga ka na gumi, abincin babu daɗi ne?" Ya ja numfashi ya kalle ta, hannunsa riƙe da cokali mai yatsu. Babu irin tambayar da ba ta yi masa ba, amma bai ba ta amsa ba, har ta gaji ta rabu da shi. A haka ya cinye abincin.

Nana ta rasa abin da ya sanya shi haɗa wannan uban gumin. Idonta ne ya sauka a kan wayarta. A take tunanin mahaifiyarta ya ƙara faɗo mata. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin.

Jiki a sanyaye ta buɗe wayar, ta shiga gurin kira, ta shigar da lambobin kamar yadda ta haddace su, cike da fatan Allah ya sa wayar ta shiga.

Babu zato babu tsammani, ta ji wayar ta shiga. Gyara zamanta ta yi tana fatan Allah ya sa ta ji abin da take tsammanni. Sai dai akasin haka ta ji muryar namiji, muryar mutumin da ta tsana a rayuwarta.

Cikin dakiya ta ce "Baba ina wuni?"

"Lafiya kalau wace ce?"

Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah me wayar nake nema"

Ya ce "To wace ce ke ɗin?"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baba Nana ce, mamana nake nema" ta yi maganar cikin rawar murya, idanunta na cika da hawaye.

"Ai dama na sani, wallahi na sani, na san ba ta fasa bibiyar tsohon mijinta ba, wallahi zan gauraya da ita"

A ruɗe Nana ta ce "Dan Allah Baba ka tsaya ka ji, wallahi ba sa waya da Babanmu, lamba ta ce, dan Allah ka haɗa ni da ita ko muryarta na ji, dan Allah.. ƙit ya kashe wayar ba tare da ta gama faɗar abin da za ta faɗa ba.

Wata irin tafasa zuciyarta ta din ga yi, cike da ɓacin rai da tashin hankali. Wasu irin hawaye masu raɗaɗi suka fara biyo fuskar ta.

Ta ɗauki wayar ta yi jifa da ita, caraf ya cafke wayar.

Ya kalli yadda hawaye yake fita daga idanunta.

Kawai ya ga ta taso za ta fita daga ɗakin, jikinta yana rawa.

Har za ta gota shi, ya danƙo hannunta ya yo baya da ita, yana ƙarewa Ƙaisar kallo da ya bayyana a gefenta yana huci!.

Ayshercool 08081012143

31

Bai kula Ƙaisar ba, ya ja Nana zuwa kan katifa, ya zaunar da ita, idanunta a lumshe, har a lokacin kuma fitar da hawaye suke yi, babu ƙaƙƙautawa. Ya taɓa tafukan hannayenta, ya ji sanyi ƙalau kamar an ciro ta daga ƙanƙara.

Ya ƙura mata ido yana nazarin ta, a take ya tuno ranar da ta shiga ɗakinsu, tana kiran Haidar, su na haɗa ido ta ja da baya ta ƙwala ihu ta faɗi. Haka jikinta ya ƙandare, ta din ga karkarwa, ya ga wani narkeken baƙin muzuru ya bayyana a ɗakin, yana ta zagaye ta.

Ya sauke numfashi, ya sanya yatsunsa biyu, ya danna bayan kunnenta. Ya miƙe ya bar kusa da ita. A hankali jikinta ya daina rawar, ta buɗe idonta, sai dai tun da ta buɗe idon, ba ta tashi daga gurin ba balle ta ci abinci. Ya din ga satar kallonta, amma ba ta tashi daga in da take ba, balle ta ci abinci. Yana son ya yi magana amma ya rasa me zai ce mata. Ta tashi zaune da ƙyar, ta haɗa kai da gwiwa, ta yi kuka mai isar ta. Sai da aka kira la'asar sannan ta tashi ta yi alwala, ta tayar da salla.

Bayan ta idar tana zaune ta yi shiru, ya dawo ɗakin, ya duba gurin da ta gama girkin, babu alamar ta ci abinci.

"Ba za a ci abinci ba?" Ta ji maganar sa babu tsammani.

Ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar mai jiran ƙiris, kawai ta sake fashewa da kuka. Ya yi zuru da ido yana bin ta da kallo, bai ce ta yi shiru ba, har ta yi mai isar ta yi shiru.

Duk ya damu ganin ba ta ci abinci ba, ya rasa me zai ce mata, ga shi yanayinta ya fahimci rigimammiya ce.

Jin motsi a waje ana taɓa gate, ya sanya ya tashi ya rufe fuskar sa, ya fita ya duba waye. Tsayawa ya yi yana kallon su, mata ne su uku, da ƙanan yara sai wani ɗan matashin saurayi.

"Sannu malam, ko kai ne mijin Nanan?" Ya tsaya tsuru yana kallon su.

"Gurin Nana mu ka zo tana nan?" ya nuna musu ɗakin su.

Suka wuce, Ummi tana cewa "Na yi ƙoƙari fa da na iya kawo mu gidan nan"

Bayan Jamila ya bi da kallo, jikinsa na ba shi wani abu a game da ita.

Wata irin zabura Nana ta yi ta rungume Ummi, ba ta taɓa tsammanin ganin su ba. Ta rungume Jamila cikin farin ciki ta ce "Dama za ku zo ba ku gaya mini ba?"

Ummi ta ce "Mu ki bamu guri mu zauna"

Nasiru ya ce "Hajiya Anty Nana amarya" daƙuwa ta yi masa ta ce "Gidanku"

Ya yi dariya ya ce "Na yi missing ɗin ki sosai"

Take ta manta da damuwar da take ciki, ta ware suka hau hira. Ta juye musu sauran abincin da ba ta ci ba, ta ce za ta ɗora musu wani.

Ummi ta ce "Ke a ƙoshe muke, ga shi wannan miya ce na ɗan yi miki, tun bayan kawo ki da kwana biyu, na so yi miki, bana jin daɗi ne. Ga ɗan cin-cin da dubulan na yi miki. Ga kuma turarukan wuta da wata maƙwanciyar ku, ta bayar a kawo miki ga humra ma. Sai kuma kaya da na ɗan ƙara sayo miki"

Nana ta ce "Allah sarki, na gode sosai da sosai Anty Ummi, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Jamcy ya garin ne?"

Jamila ta ce "Uhumm mamaki nake yi, kamar ba ke ce ki ka gama uban kuka ba, an aura miki buzu, amma kalli yadda ki ka ware yanzu"

Nana ta yi murmushi ta ce "To ba dole na ware ba, lafiyayyen ɗaki, ga wardrobe, ga katifata ga banɗakina nikaɗai ba takura ga wuta 2hrs ba yankewa"

Suwaiba ta ce "Katifa ko abin da ake yi a kan katifar?"

Nana ta ce "Duka ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Jamila, tun da dan haka ake auren"

Ummi ta ce "Dan uban ku da yara a gurin ku ke yi mana batsa"

Nana ta yi murmushi ta ce "Ya Baba, ina mama su ba za su zo ba?"

Ummi ta ce "Za su zo ne, Baba babu lafiya ƙafarsa ce take ciwo"

Nana ta ce "Ciwon ƙafa kuma?"

"Wallahi kuwa, ba za ki kira mijin naki mu gaisa ba"

Nana ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Ba kula ku zai yi ba, Nasiru ya makaranta" ta karkatar da zancen ga Nasiru. "Makaranta lafiya ƙalau Alhamdilillah"

A ƙofar ɗakin ya yi gyaran murya ya tsaya, Nana ta yinƙura ta tashi, ta ɗaga labulen. Babu hijjabi a jikinta, sai doguwar rigar atamfa.

Ya miƙo mata leda, ta saka hannu biyu ta karɓa, bai ce mata komai ba, ya juya ya koma bakin gate.

Fura da Nono ne kaya guda, abin sai da ya bawa Nana mamaki, ba ta san a ina ya samo su ba. Ta ajiye musu suka dama, suka sha.

Jamila ta miƙa wa Nana ɗan ƙaramin flask ta ce "Nana ga mutuniyar ki na yi miki wainar fulawa" Nana ta haɗiyi yawu cikin murna ta din ga yi wa Jamila godiya. Ta ce "Wannan sai dare zan dafa shayi na ci da ita"

Suwaiba ta ce "Ashe fa buzu ki ke aure, ba za a gaya miki shayi ba yanzu"

Nana ta ce "Kamar kin sani, ni yanzu shayi ai sai dai na koya wasu, kwana muke mu wuni shan shayi babu ƙaƙƙautawa" suka yi dariya. Har magariba su na gidan, sai da suka yi sallar magariba, Nana ta fito har bakin gate ta rako su, sai dai baya nan.

Ummi ta ce "Kin ga har zamu tafi, bamu haɗu mun gaisa ba"

Nana ta ce "Ina ga yana masallaci"

Suka yi sallama, suka tafi Nana ta koma ɗaki. Har cikin ranta ta ji daɗin zuwan su.

Ta yi wanke-wanke ta gyara ɗakin fes. Ta ɗaukko flask ɗin wainar fulawar, ta saka a gaba ta fara ci. Ba ta ci da yawa ba, Haula ta yi sallama.

Nana ta amsa cikin sakin fuska, duk da ta yi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin.

"Anty Haula ba ki yi fushi ba? Haryanzu ban fara fita ba, shi yasa ban shigo miki ba"

Haula ta ce "Allah sarki, kar ki damu wallahi, ashe baƙi ki ka yi?"

Ba tare da Nana ta yi tunanin komai ba, ta ce "Eh, 'yan gidanmu ne su ka zo, bismillah matso mu ci abinci" Aikuwa Haula ta gyara zama ta zura hannu a kwano, ta fara cin abincin. Kafin Nana ta yi loma ɗaya ta yi huɗu da rabi, kafin wani lokaci Nana sai filin kwanon ta gani, Haula na ta suɗar baki saboda yajin wainar.

Sai da ran Nana ya sosu, dan kuwa ta so cin wainar nan ta ƙoshi.

Labulen ɗakin kawai ya ɗaga ya shigo, Haula ta tashi zumbur. Ta kalli Nana ta ce "Na gode sosai sai anjima" sai da Haula ta fice sannan ya shigo ɗakin.

Ya zauna a gurin da ya saba zama, Nana ta ɗaukko ta sa furar da ta ajiye masa, da cin-cin da dubulan a plate, ta nufe shi.

"Sannu da zuwa" ya jinjina mata kai.

" 'yan gidanmu ne fa suka zo" ta yi maganar fuskarta na bayyanar da annashuwa. Ya gyaɗa mata kai.

"Na gode sosai da sosai, da karamcin da ka yi mini, ga taka furar ga kuma wannan" ta yi magana tana tura masa plate ɗin dubulan.

Ya saka hannu biyu ya karɓi kofin furar, Nana ta zauna a gefensa, a tsanake yake sha, ya ɗauki cin-cin ya saka a bakinsa, maimakon ya tauna yadda yakamata, amma ya din ga tauna shi a hankali kamar mai tsoron tauna dutse.

"Da daɗi?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Nana ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce "Dan Allah ka din ga yi mini magana mana. Haryanzu ban san sunanka ba" ya kalle ta yana ci gaba da tauna cin-cin ɗin sa.

"Ka gaya mini sunan ka" ya ajiye kofin hannunsa yana hamma, ya jingina da jikin bango yana lumshe idanunsa.

Ta gaji ta ƙyale shi, ta fara shirin kwanciya, ta shiga banɗaki domin kama ruwa ta yi alwalar kwanciya bacci.

A sukwane ya miƙe, duk da bacci ya fara ɗaukarsa, kwanon da Nana ta ci wainar nan ya ɗauka, ya jujjuya kwanon ya ga babu komai a ciki.

Ya ajiye kwanon, ya koma gurin da yake kwanciya, ya zauna ya yi shiru.

Nana kuwa tana saka ƙafarta a banɗakin, ta ganta a cikin wani gida, mai dogon gini, mai ɗauke da ƙofofi daban-daban. Ɗaya daga cikin kofofin ta bi, tana neman hanyar fita, amma da ta shiga sai ta ga ta koma ainihin gurin da take da farko.

Tana cikin laluben ƙofar, kawai ta ci karo da Baba, ƙafarsa ɗaya an nannaɗe ta da sarƙa, an ɗaure ta tamau. Da sauri Nana ta nufe shi, cikin tashin hankali ta ce "Baba lafiya kuwa? Me ya same ka haka?"

"Ni ma ban sani ba Nana, dan Allah ki kwance mini sarƙar nan, ina jin ƙafata kamar za ta cire, ba na iya bacci"

Cikin damuwa ta ce "Ka kwantar da hankalinka, bari na gani idan zan iya kwance maka" Ta durƙusa ta fara ƙoƙarin kwance masa sarƙar, sai dai ta rasa ina ne ainihin gurin da aka ƙulle ƙafar.

"Idan ki ka kuskura ki ka kwance masa, ba zai sake taka ƙafarsa ba har abada" Nana ta ɗago tana kallon Ƙaisar.

"Dan me za ka ce kar na kwance masa? Ba ka ga halin da yake ciki ba, ko iya taka ƙafar baya yi ba?"

Ƙaisar ya ce "Ban gaya miki sai na hukunta shi ba? Har yanzu ba ki yadda mu na cikin mummunan haɗari daga ni har ke ba, a dalilin wannan auren. Dan haka dole shi ma ya ɗanɗana kuɗarsa"

Cikin ɗaga murya ta ce "Ƙaisar baban nawa? Ka kwance masa ƙafarsa" kawai tana waiwayewa ta daina ganin Baba.

"Idan duniya za ta taru, babu wanda ya isa ya kwance masa ƙafar nan, idan bai yi wasa ba sai ta yi ajalinsa" yayi maganar cikin ɗaga murya.

Tamkar mai shirin haukacewa ta ce "Ba zai yiwu ba, wallahi sai ka kwance shi, wai kai wane irin halitta ne da babu ɗigon imani, a zuciyar ka?"

Ƙaisar ya ce "Ko ma dai mene ne, abu ɗaya za ki yi ki kwance masa ƙafar nan, wanda kin san mene ne, ba sai na gaya miki ba. Mu ajiye wannan a gefe tukuna, ban san iya adadin lokacin da za a ɗauka kafin ki san ciwon kanki ba, ki daina wasa da rayuwar ki ba. A wannan karon ma an baki abu kin ci, za kuwa ki ɗanɗana kuɗar ki, a nan na nuna miki an tsaface ƙanwar ki, amma ta kawo abu ta baki ki ka ci"

Nana ta ce "Idan ma ka nuna mini, da na tashi nake manta komai, kuma ba zan taɓa yarda da maganganun ka ba, yaudarata kawai ka ke so ka yi, domin na amince da mugun nufin ka, kuma har abada ba zan amince ba, ko da ba ma jituwa da su, na san ba za su cutar da ni ba"

Ya ce "Shikenan, zamu gani"

A hankali ta yi kokarin yin juyi a kan katifar, amma ta ji wani irin azababben fitsari, tamkar mararta za ta yi bindiga, ga wata irin ƙullewa da mararta ta yi har cikin bayanta da ƙafafuwanta. Da ƙyar da dabara, ta tashi ta tafi banɗaki. A zaton ta da ta yi fitsarin shikenan, za ta ji marar ta saki, amma babu abin da ya canza.

Da bin bango ta fito ,ta dawo kan katifar ta kwanta. Bacci ne a kanta, amma wani irin azababben ciwon mara ya turnuƙe ta. Yana kwance yana jin nishinta sama-sama, tun farkawar ta da shigarta Banɗaki, duk a kan idanunsa. Murƙususu ta din ga yi a kan katifar, tana numfarfashi. Rabonta da ciwon mara mai irin wannan azabar, tun farko-farkon fara period ɗin ta. Da idan ta fara sai an kai ta chemist an yi mata allurai. Daga baya abin ya ragu sosai, amma na yau kam, ba ta taɓa makamancin irin sa ba, ji take tamkar ba za ta wayi gari ba.

Ko na minti ɗaya ciwon baya lafawa, ga shi ya haɗe mata da ciwon ciki, da na ƙirji kamar za ta bar duniya. A duƙe ta sake komawa banɗaki ta saka pad.

A haka ta wayi gari, cikin mawuyacin hali, ta yi kukan ta gaji. Ta saukko daga kan katifar ta kwanta a ƙasa amma babu afuwa. Ko sau ɗaya bai ce mata sannu ba, da gari ya yi haske ma bar mata ɗakin ya yi, saboda yadda kukanta ya cika masa kunne.

Tamkar za ta haihu, haka ta fita daga hayyacinta, gaba ɗaya ta manta da batun ba itakaɗai ce a ɗakin ba, ta cire kayan jikinta, ta bar vest da underwear. Rashin tanka matan da ya yi ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba.

Can amai ya din ga taso mata, ga wata irin gudawa ta azaba da fitar ta kawai, yake ƙara gigita ta saboda sai cikin ya haɗu ya ƙule da marar sannan take yin ta. Ga fitarta tamkar tana zawon wuta haka take ji, ta ga duniyar tana juya mata, ta din ga salati tana ambaton Allah. Tun tana iya zuwa banɗakin a duƙe, ta koma rarrafe.

Ta din ga wani irin amai, mai wari da ƙarni. Idanunta suka yi zuru-zuru, kamar ta yi wata da watanni tana rashin lafiya.

Ta kwanta ta yi rub da ciki, ta lumshe idonta. Ta ji an ɗagota. Sosai ya ɗago ta ya haɗa ta da ƙirjinsa. Babu rawani a kansa, ya kwance gashin kansa, ya sauka a kan kafaɗarsa. Suna haɗa ido, ta sake fashewa da kuka, saboda ta ji zafin rashin kula ta da ya yi balle ya yi mata sannu.

Ya kai dogwayen yatsunsa ya share hawayen da yake fitowa daga idonta. Ta saka hannu ta ture hannunsa, da yake share mata hawayen.

Ya kama bayan hannunta ya kai bakinsa ya sumbuta, ya ɗago ya ƙura mata ido, yana matsa hannunta a hankali. Zuba masa ido Nana ta yi, sai ta ga kamar ba shi ba. Ya sake kai bakinsa goshinta ya sumbaci goshin nata. Ta sake fashewa da kuka, ya haɗa goshinsa da nata ya ce "Shhhhh" Gabanta ya faɗi, sai da ta razana jin ya ɗora hannunsa a kan marar ta.

A hankali ta fara jin releif, daga wannan matsanancin ciwon da take ji. Bai ɗauke goshinsa daga nata ba, numfashin sa da yake shiga nata, jikinta ne ya saki ya mutu murus, ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. A hankali ta fara jin bacci yana ɗaukar ta.

*****

Su Jamila kuwa bayan sun dawo daga gidan Nana, Baba ya tambaye su ya suka baro ta.

Suwaiba ta ce "Tana nan lafiya kalau, ta ce a gaishe ka"

"Ina amsawa, ya gidan nata akwai abinci kuwa?"

Nasiru ya yi farat ya ce "Baba ɗaki dai, a ɗaki ɗaya take da banɗaki, amma akwai abinci a ɗakin. Har mijinta ya kawo mana fura da Nono".

Baba ya ce "Ko ma dai a rami suke ba ɗaki ɗaya ba, ai ita ta jiyo, tun da Allah ya nufi ya rufa mata asiri, ya bata miji na gari na rufin asiri ta zaɓi ta tonawa kanta asiri, yanzu ta ƙare a tantalbatete"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull