Buzu book 1 complete - Chapter 28
Buzu book 1 complete Chapter 28: Buzu book 1 complete Chapter 28. Habu ya numfasa ya ce "Kin yi gaskiya Amarya, shi yasa na yi ta ce miki ki yi haƙuri, ki…
4,487 words
Habu ya numfasa ya ce "Kin yi gaskiya Amarya, shi yasa na yi ta ce miki ki yi haƙuri, ki karɓi ƙaddara, sai a yanzu na ƙara tabattar da wannan ƙaddarar ce ta haɗo mu baki ɗaya. Magana ta gaskiya, ban san waye Buzu ba, a sahara na tsince shi cikin mawuyacin hali, mai kama da gushewar hankali da ɗimuwa. Yanayin kamaninsa ya sanya na san ɗan uwa ne buzu, kuma buzyen ma kala-kala ne, na ji yana iya hausa ya kuma iya French, shi yasa na tabattar da Buzun Nijar ne. Na yi yinƙurin tafiya da shi Nijar, saboda idan na bar shi a saharar nan, zai iya rasa ransa, ban kuma san da wa zai haɗu ba, dan haka na yi nufin tafiya da shi Nijar, domin neman ahalinsa. Sai dai da na yi yinƙurin nufin komawa Nijar da shi, sai guguwar sahara ta taso, ta rufe hanyar baki ɗaya. Dole na canza hanya na nufo Nigeria, jikina ya bani akwai wani abu, domin duk wata hanya da zan bi mu koma Nijar na kasa samun ta. Ina da wasu abokai a Nigeria, su na kira suka karɓe ni, da niyyar a taimaka mini, a samo masa magani. Saboda duk abin da na tambaye shi game da shi bai sani ba, sunansa, waye shi, daga ina yake, ina za shi duk bai sani ba. Wasu lokutan zai yi miki abu lafiya kalau na cikakken mai hankali, sai dai ba zai taɓa iya ce miki waye shi ba. Wasu sai ya burkice, ba magana yana ma iya daina gane mutane gaba ɗaya. Ba ya son magana ko da yana normal, sannan wasu lokutan ya kan burkice ya din ga jijjiga. Duk gurin mai maganin da muka je a Nigeria sai a ce ba za a iya ba shi magani ba. Shi yasa tun da aka yi auren nan, za ki ga kusan kullum ina zuwa, ina kawo muku abin amfani, wallahi ina matuƙar tausayinsa ne. Ba shikaɗai ba har da ke ma"
Jikin Nana ya mutu murus, ta ce "Yanzu shikenan ba ku san kowa na shi ba? Me na aura kenan?"
Cikin kwantar da hankali Habu ya ce "Akwai dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ku, da babu wanda ya sani sai shi. Ni kaina na fuskanci ƙalubale baro ahalina na taho Nigeria nema wa wanda ban sani ba magani. Idan ki ka saka hannu ki ka dafa mini a kan wannan jihadin, Allah ne kawai zai biya mu. Idan ba ki amince ba kuma shikenan babu dole, sai na wuce gaba a raba auren, dama mahaifinki ne ya matsa ya sanya aka yi auren dole".
Ba su ankara ba kawai su ka gan shi a cikin ɗakin, ya ajiye abin dafa shayinsa, da kayan dafa shayin, ya juya zai bar ɗakin.
Habu ya tashi da sauri yana faɗin "Tun ɗazu na zo ai, ba ka nan ga kayan dahuwar shayin nan na kawo maka"
Banza ya yi masa ya nufi hanyar fita, Habu ya bi shi da sauri, ya riƙo hannunsa amma ya fizge yana yi masa wani irin mugun kallo.
Ayshercool 08081012143 Habu bai yi zuciya ba, ya sake bin bayan Buzu, ya juya yare, ya tsaya yana yi masa magana, ya din ga zuba babu ƙaƙƙautawa.
Nana kuma mamaki ne ya ishe ta, ganin Yadda Habu ha rikice gaba ɗaya, kuma ita ba ta ga abin da ya yi na ba daidai ba, da zai yi wannan rikicewar kamar mara gaskiya ba. Ita wasu lokutan har mamaki yake bata, kamar tsoron buzun yake ji, shi da yake taimakonsa amma ba ya ƙaunar ya ga ɓacin ransa ko kaɗan.
Nana ko a jikinta, ba ta ma san yadda suka ƙarke ba. Sai dai ta yi ta jujjuya maganganun da Habu ya gaya mata. Yanzu shikenan haka za ta ci gaba da rayuwa da mutumin da ba a ma san suwaye danginsa ba? Ko a daɗe ko a jima dole tana buƙatar sanin waye shi, kuma suwaye ahalinsa. Ba ta taɓa jin lallai tana son ganin Ƙaisar ba sai a wannan lokacin. Ba shiri ta kwanta ta hau bacci, ko za ta gan shi, amma ba ta ga komai ba, har ta gama baccin ta tashi.
Bayan farkawarta ta ga wayarta a gefenta, a lokacin yamma ta yi sosai da sosai. Da sauri ta ɗauki wayar, ta kira lambar Ummi, dan tun da suka zo, ba ta ji ya suka je gida ba.
Sai da ta kusa katsewa, sannan Ummi ta ɗaga.
Nana ta yi sallama, Ummi ta amsa ta ce "Kai, Nana a ina ki ka samu waya?"
Nana ta ce "Dama ina da ita, kin san lambar ki na haddceta, saboda ke ce line 911 ɗi na"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Eh lallai kam, ya ki ke ya mai gidan?"
"Alhamdilillah, ya ku ka je gida, ban samu na kira ku ba, bayan tafiyar ku na ɗan yi rashin lafiya ne"
Ummi ta ce "Alhamdilillah, mun je gida ƙalau. Kai Nana daga zuwa sai rashin lafiya, a dai ciki ba ne ko?"
Nana ta kwashe da dariya ta ce "Dan azaba auren kwanaki sai ciki?"
"Eh mana, tun da ina jin fitsarar da ki ke yi, ranar da mu ka zo"
Nana ta ce "Wallahi kawai cika baki ne, ji na yi za su raina mini hankali ne. Kuma ba na fatan ko alama, a ga ɓaraka a tattare da aurena"
Ummi ta ce "Allah sarki Nana, in sha Allah auren nan, sai ya baki kwanciyar hankalin da ba ki taɓa tsammani ba. Ke Jamila fa babu lafiya fa"
Nana ta dafe ƙirjinta ta ce "Babu lafiya kuma? Me ya same ta?"
"Oho, ni mun yi waya da maman, ban gama gane kan zancen ba. Wai tun da mu ka baro gurin ki, washegari ta tashi ba ta iya tsayuwa, wani abu duk ya feso mata a jikinta".
Nana ta girgiza kai ta ce "Hmm na san cewa aka yi ni ce ko?"
"A'a wai sun je gurin wani mai magani, aljani ne yake hawa kansa ya bayar da magani, ya ce musu wai wani aljani suka yi wa laifi" Kan Nana ya sara, ta yi shiru tana son tuna wani abu, amma ta gagara tuna komai.
Ummi ta ci gaba da cewa "Shi ne ya basu magani, wai ya sha sannan a yi sadakar ƙosai mai zafi da la'asar"
Nana ta ce "Ita sadakar ƙosan ta mece ce, sharaɗin mene ne? Kin ga Mama ba za ta din ga kiyaye irin wannan yawace-yawacen ba ko? Wane irin sadakar ƙosai mai zafi da la'asar?"
"A'a ni ina zan sani, tun da ba ni na ba su maganin ba, ina gefe labari aka bani"
Nana ta numfasa ta ce "Sadaka mahaɗin Addu'a ce, amma wannan sharuɗɗan da ake sakawa ne, ni ba na gane kansu"
"To ni ya za ni tsitsiye ni, labari kawai na ji, ban ma je na duba ta ba"
Jikin Nana a sanyaye ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya sauwwaƙe ya jikin Baban?"
"To da sauƙi, ni rabona da gidan tun biki, amma sun ce yana jin jiki, ƙafar nan tana yi masa ciwo sosai"
Nana ta ce "To shikkenan, zan samu na je na duba su baki ɗaya, in sha Allah, amma jikina ya yi sanyi, na san ciwon Jamila cewa za a yi nice"
"Ke rabu da su dan Allah, ni wallahi na jiye miki daɗin auren nan, Allah ya sanya shi ne mafi alkhairi, amma da zaman wannan gidan namu, ba gara auren ba, kullum cikin bala'i. Ko banza ɗakin ki a cike yake da kayan abinci"
Nana ta ɗan yi shiru, kamar ta gaya wa Ummi halin da ake ciki, na rashin sanin dangin mijinta, amma ta basar. Ta ce "To Allah ya sa mu dace"
na gode sosai ki gaida yaran"
Suka yi sallama, Nana ta tashi ta ɗan yi gyare-gyaren ta, ta ɗauki magic coal ɗin sa da yake haɗawa da gawayi, ya kunna wutar dafa shayi, ta kunna turaren wuta. Ta ɗauki wayarta ta kunna karatun Alqur'ani.
Fafur ya ƙi shigowa ɗakin, sai bayan isha'i.
Ya shigo da 'yar ledarsa, ya ɗauki kwano ya zazzage fruit, ya je ya wanko abin sa, ya dawo ya zauna a gurin zamansa, ya fara ci a hankali. Nana ta na kallon sa, zuciyarta ɗauke da tunani daban-daban.
Ta dake zuciyarta, ta tashi ta tafi kusa da shi ta zauna. Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya nuna ya san tana zaune a gurin.
"Ba za ka ci abincina ba ne, ka je ka sayo fruit ka ke ci?" Sannu a hankali yake tauna apple ɗin bakinsa, bai kula ta ba.
"Ni mamaki ma nake yi, idan ka je da yaya ka ke sayayyar, magana ka ke yi musu, ko kuma ni ce kawai ba ka kulawa?"
Ya ɓare ayaba zai kai bakinsa, ta riƙe hannun, ta sauke shi ƙasa a hankali. Ya ɗago idanunsa yana kallon ta. Ta yi saurin sauke nata ta yi murmushi ta ce "Na san na yi maka laifi, bai kamata abubuwan da na gaya maka ba, ka yi haƙuri ina cikin damuwa ne, amma ka yi mini afuwa ba zan sake ba" ya sunkuyar da kansa ya yi shiru.
"Ka yi magana mana" ta yi maganar a raunane.
Ture ta ya yi daga kusa da shi, ya tashi ya bar mata ɗakin. Abin ya yi wa Nana ciwo, sai dai ta tuna bayanin Habu daki-daki, tabbas wasu abubuwan da yake za ka san ba normal yake ba.
Ta tashi zuciyar ta cike da damuwa, sai dai a zuciyarta ta ƙuduri aniyar jure kowane irin ƙalubale, tun da ba duka yake ba, ba kuma zagi yake yi ba, gara zamanta a nan da shi sau dubu, a kan ta koma gidan su.
Ta kunna gas ta ɗora ruwa, domin ta yi wanka kafin ta kwanta, garin akwai yanayin hadari, dan haka akwai sanyi. Tana ɗan dube-dube, da goge kan mududinta, ta ga ɗan littafin da yake yawo da shi, ko ta ga yana karantawa, da biro a cikin drower mudubi.
Ta ɗauka ta buɗe, ta ga kyakyawan rubutunsa, wani da French, wani da hausa.
"A ba ni kankana, da ayaba na dubu biyu. A bani buredi mai kyau babba guda ɗaya. Ina son wannan jan abin, na kuɗin da na bayar" sai da Nana ta yi dariya, wato duk a rubuce yake sayen abin da yake zuwa da shi. Tana shirin buɗe wani shafin, ta ji wutar gas ɗin na fita da yawan gaske, tukunyar kai na wata irin tafasa kamar ta diro daga kan gas ɗin. A gigice ta nufi gas ɗin ta sauke, abin ya ba ta mamaki, dan ko mintuna biyar a yi da ɗora ruwan ba, yake wannan tafasar. Ta juye ruwan a flask, ta sake ɗora wani.
Yana tafasowa ta haɗa ruwan ta shiga wanka, sai dai bayan ta shiga banɗakin, ta ji ruwan ya yi mata zafi sosai, maimakon ta kunna famfo, ta ƙara sirkawa, sai ta jingina da bango tana jiran ya huce. Shiru ta yi tana ta tunani daban-daban a zuciyarta.
Ɓangaren buzu bayan ya dawo ɗakin, ye nemi Nana ya rasa, ya ga littafin sa a kan mudubi. Ya ɗan yi jimm ko zai ji motsinta amma shiru. Kusan mintuna goma bai ji ko zubar ruwan famfo ba, balle ya yi tunanin tana banɗaki.
Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi, kamar yadda ya tashi ɗazu, da ya dawo ya tarar ba ta nan ashe tana cikin gidan nan ba ta gaya masa ba.
Kasa jurewa ya yi ya nufi banɗakin kawai ya buɗe ƙofar.
Zabura Nana ta yi, ta saki ƙara, domin ƙoƙarin cire zanin jikinta take yi ta yi wanka.
Cak ya tsaya yana kallonta, ta saka hannu ta riƙe zanin da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta kare ƙirjinta da shi.
Sannu a hankali take jin sanyi, ƙirjinta kuma ya fara bugawa.
Ta sake ɗaga ido, suka haɗa ido, ko a jikinsa ya ci gaba da tsare ta da ido. Ta yinƙura da niyyar magana, amma ta ji ta kasa furta komai, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.
A hankali ta ji ya rufe ƙofar toilet ɗin, wata irin ajiyar zuciya ta yi, jiki a sanyaye ta yi wanka, sai dai ta kasa fitowa saboda kunya. Da kyar ta iya fitowa, amma ta ga baya ɗakin, cikin hanzari take shiri, domin kwanta, kafin ya sake shigowa.
Gari sai walƙiya ake yi, da wata irin tsawa hadari yana tasowa.
Tana gama zura rigar ta ya shigo, bai ce komai ba, ya rufe taga sai dai yana juyowa gaba ɗaya kamaninsa sun sauya, ya koma wannan tsohon.
Kallon kallo suka yi da ita, ta tsaya tana yi masa wani irin kallo, mai cike da tsoro da razani, a take fitilar ɗakin ta ɗauke, ɗakin ya gauraye da wani irin matsanancin duhu, ƙofa da tagar ɗakin su ka din ga bugawa da ƙarfin gaske. Wata irin walƙiyya ta haska ɗakin, ta ganshi sanye cikin wannan fararen kayan da take ganinsa da su, hannunsa riƙe da sandar sa, idanunsa baƙi ƙirin wani baƙin hayaƙi na fitowa daga cikin su.
Ya hangame bakinsa, ya fara fito da wuta.
"Allahumma ajirni fil musibati, wa aklifni kharin min ha" ta yi maganar tana sanya hannunta, ta ɗora a kanta.
"Meyafaru?" Ta ji muryarsa. Ta buɗe idonta ta kalle shi a hankali. Fuskarsa ɗauke da damuwa yake tambayarta. Da sauri ta ja da baya tana girgiza masa kai.
"Kar ka sake zuwa kusa da ni, ka yi mini duk abin da za ka yi mini, na gaji me na yi maka ne?" Ta yi maganar cikin kuka.
Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan kururwar.
Ya taka ya ƙara matsawa kusa da ita, amma ta din ga ja da baya, tana maimaita "kar ka matso kusa da ni, ba na buƙatar ka, kar ka zo inda nake".
"Kalli ni mutum ne ba abin tsoro ba, babu abin da na yi miki, le regard kalli" ya yi maganar yana nuna mata hannunsa domin ta taɓa ta tabattar.
Cikin fita hayyaci Nana ta ce "Ka fita ba na son ganinka, ba za ka haukata ni a banza ba, ka fita ba na son ganin ka" ta yi maganar jikinta na tsuma da karkarwa. Cikin sauri ya nufi ƙofar fita yana waiwayen ta.
Yana fita ta silale ta faɗi a gurin.
Fitar sa ke da wuya, ruwan sama mai ƙarfin gaske ya sauka.
****
Dare ya tsala, Fadila na zaune bacci ya gagari idonta, ta kalli kusa da ita, mijinta Sagir yana ta baccinsa hankali a kwance, ita kuwa duk dare fargabar kwanciya bacci take yi, saboda miyagun mafarke-mafarken da take yi. Tun Sagir na damuwa har ya gaji ya rabu da ita. Ta yi niyyar yin alwala ta yi nafila ko raka'a biyu ce, amma kasala ta danne ta, ga wani irin tsoro da take ji. Dama ko normal sallar farilla a zaune take yin ta, saboda yadda cikin ya tsufa sosai da sosai ga shi da girma. Ga exams tana facing, ba ta iya karatun sam. Ta dafe goshinta tana wani irin gumi, duk da sanyin A.C da ya sanyaya ɗakin.
Tana jiyo surutan Haidar a cikin bacci, yana ta kiran sunan Nana.
Kawai ta zuba uban tagumi hannu bibbiyu ba tare da sanin abin yi ba.
****
Ko da Nana ta buɗe idanunta, da hasken fitilar ƙwan ɗakin, ta fara karo.
Ta juyo da kanta, da ya yi mata nauyi tamkar zai tarwatse, kawai ta hange shi a bakin ƙofar banɗaki, yana ta sanɗa yana cire kayan jikinsa a hankali, da suke ta ɗigar da ruwa, jikinsa yana ta wata irin karkarwa. Aka yi walƙiya ta hangi yadda ruwa yake zuba ta taga. A take ta tuna abin da ya faru, da azama ta tashi zaune, ta yinƙura ta tashi, ta nufe shi. Sai a lokacin ya farga da ta tashi. Sai da ya tsorata ya tsaya cak, yana tsoron kar ta sake rikicewa ta ce ba ta son ganinsa.
"Me yasa ka fita ruwa ya dake ka har haka? Subhanallah" ta yi maganar tana karɓar rigar hannunsa. Babban abin da ya tsorata ta, bai wuce yadda jikinsa yake karkarwa ba, haƙoransa suke haɗuwa da juna, su na bayar da wani irin sauti. Ta buɗe wardrobe ta ɗaukko zaninta, ta fara goge masa ruwan jikinsa. Cikin damuwa ta ce "Me yasa ka tsaya ruwa ya dake ka haka?" Kawai ya kalle ta.
Ta ajiye zanin, ta ɗaukko flask ɗin da ta zuba ruwan zafi, ta shiga banɗakin ta zuba a bokiti, ta haɗa masa ruwa mai zafi.
"Ka shiga ka yi wanka da shi, za ka rage jin sanyin" bai musa ba ya shiga banɗakin, ta ɗauko wando ta rataye masa a jikin ƙofar, ta rufe masa ƙofar.
Ta ɗaukko bargonta, ta ajiye a kan katifar, ta duba kayanta, ta samo man zafi ta ajiye. Ta tsaya tana jiransa. Ba a jima ba ya fito, sai dai jikinsa na ta ci gaba da tsuma, yana karkarwa.
Mamaki take yi, yadda dukan ruwa ya saka shi haka, ita ba ta san adadin dukan da ruwa ya yi mata ba, ko ciwon kai bai taɓa saka ta ba.
Ta ɗaukko riga, ta miƙa masa, amma ya ture ta, ya nufi gurin da yake kwanciya.
Ta riƙo hannunsa ta ce "Zauna a nan" ta nuna masa gefen katifar. Ya zauna a hankali yana rintse idanunsa.
Ta ɗauki man zafi tana shafa masa a jikinsa, sai dai jikinsa ya ɗauki zafi rauuu.
"In baka rigar ka saka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Ta gyara masa fulo ta ce "To kwanta" ya ja jikinsa a hankali ya kwanta, ta lulluɓe shi da bargo.
Ta yi shiru cikin matsananciyar damuwa, ita kanta ba ta san ya aka yi yau ta gigice har haka ba. Ba ta san yadda aka yi ta rasa nutsuwar ta har hankalinta ya gushe ba, duk da abubuwa irin haka na faruwa da ita, wasu lokutan kuma ta na iya sarrafa kanta.
Ji ta yi yana wani irin nishi, jikinsa tamkar ana girgiza shi. Ta ɗaga bargon cikin damuwa, ta ga yana jijjiga.
Ta rikice ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, tsoro ka ke bani ne, ba ina nufin ka fita ruwa ya dake ba ne ba."
Tana kuka ta ɗaukko ɗan kwalinta, ta jiƙo shi da ruwa, ta ci gaba shafa masa. Amma ta ga leɓensa har ya fashe saboda karkarwa. Ta kalli gari yadda ake ta lafta ruwa, balle ta ce a taimaka mata a kai shi asibiti.
Ya yi mata alama da hannunsa ta matsa kusa da shi, ta matsa sosai a hankali ya ce "Zafi, ana ƙona ni, ƙonewa nake yi"
Cikin kuka ta ce "A'a babu wanda yake ƙona ka, zazzaɓi ne ka yi haƙuri"
"A'a, ƙona ni ake yi, sanyi nake so"
Cikin rashin fahimta ta ce "Sanyi kuma?"
"Eh, saboda ƙonewa nake yi yanzu" yayi maganar haƙoransa na ƙara karo da juna.
Cikin damuwa ta ce "To mu koma bakin ƙofar ɗakin?"
Ya girgiza kai ya ce "Sanyin da ki ke ji nake so"
"Sanyin da nake ji kuma? Ai ba na jin sanyi"
"A'a ki na ji, ki taimaka mini dan Allah, sanyin da ki ke ji nake so"
"To ta yaya zan baka?"
"Jikinki za ki bani, shi nake buƙata ko zan daina jin zafin wutar nan" duk da jikinsa yana rawa, amma tana fahimtar abin da yake faɗa.
"To ai ni ban san ta yaya zan baka ba" Ta yi maganar a sanyaye dan ba ta san ya yake nufi ba.
"Kin yarda za ki bani?" Ya yi maganar yana buɗe idonsa da suka kaɗa su ka yi jawur ya kalle ta.
Ta jinjina masa kai alamar eh, cikin tsoro dan ba ta san ya yake nufi ba.
Ya buɗe mata cikin bargon, ya saka hannunsa ɗaya ya janyo ta, ya mayar da bargon ya rufe., ya mirgina ta gefensa ya saka hannayensa ya ƙanƙame ta.
"Wash Allah! Zafi zan ƙone" ta yi maganar a gigice, saboda wani irin zafi da yake fitowa daga jikinsa, yana ratsa fatarta, duk da akwai rigar bacci a jikinta.
Ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta kasa, saboda ya danne ta, ta kowane ɓangare.
"Yi hakuri, ba za ki ƙone ba, za ki daina ji"
Nana ta fashe da kuka tana girgiza kanta, shi da zafin yake fitowa daga jikinsa ya yake ji kenan?.
A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa bayanta, yana sauke numfashi a wahale. Cike da ƙarfin hali yake cewa "Yi haƙuri, na san ba zaki ƙone ba, nikaɗai nake ƙonewa" ya din ga hura mata iska a kunnenta. A hankali ta daina jin zafin, temperature jikinsa, ta fara komawa normal, ta ji ya daina wannan tsumar, numfashin ma da yake ta saukewa ya daina. Sai ta ɗan zabura a rikice ta ɗago, ta kai hannu hancinsa. Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ban mutu ba, ina numfashi" ajiyar zuciya ta sauke tare da gode wa Allah ganin yana raye ya kuma dawo daidai.
"Sannu ka daina jin zafi?" Ya jinjina kai alamar eh.
"Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, tsorata ni ka ke yi ne, ba ina sane na yi maka ba"
"Ni ma ki na tsorata ni wasu lokutan"
Cikin mamaki ta ce "Ta yaya?"
"An gama ruwan ko?" Ya yi maganar yana basar da wadda ya yi.
"Eh an daina, amma dama ka na doguwar magana haka sosai?"
"Eh"
"Amma na yi ta magana ɗazu ka ƙyale ni" ta yi maganar da shagwaɓar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba.
Dariya ta ji yana yi, ya ƙara riƙe ta gam.
"Yanzu wai da gaske ba ka iya tuna komai game da kan ka?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Haka ne, ina iya tuna abubuwa na yau da kullum, wasu lokutan kuma ba na iya tuna komai ma. Tun da farka a cikin wannan duniyar da nake jin ta tamkar mafarki, nake iya ƙoƙarina na tuna waye ni, saboda na fuskanci babu wanda yake rayuwa shikaɗai kowa yana da ahali. Amma a duk lokacin da na yi ƙoƙarin hakan, na takura ƙwaƙwalwata, sai na ji wani duhu ya ƙara ninkuwa a cikin kaina, na ji kamar kan zai tarwatse. Kuma a ƙarshe sai na yi rashin lafiya, ko dai na ji wannan zafin tamkar ana babbaka mini wuta, ko kuma na sake manta wasu muhimman abubuwan. Amma yanzu ke ce ahalina"
"Kenan ba dalilin dukan ruwan nan ne ya saka jijjiga ba?"
"Ba zan iya ganewa ba, abubuwan suke saka ni hakan da yawa"
Nana ta ce "To ni dai ka yi haƙuri dan Allah, ka yafe mini na gaya maka ba ni da cikakkiyar lafiya ba da son raina ba" ta yi maganar cike da jin daɗin, yadda suke hira yau sosai har haka.
Ya yi shiru, yana ƙoƙarin karkata ga wani abin daban.
"To bari na tashi, tun da ka koma daidai"
"A'a ban koma ba"
Ƙirjinta ne ya fara bugawa cikin matsanancin tsoro, za ta yi magana muryarta ta din ga rawa.
"Dan Allah" shi ne kawai abin da ya iya fitowa daga bakinta.
"Shhhhhh"
Wutar ɗakin ta ɗauke gaba ɗaya, duhu ya mamaye ko ina, sai ƙamshin turaren da ta ji a wancan ɗakin da ta yi mafarki da shi, ya ziyarci hancinta. Gaba ɗaya sai ƙwaƙwalwarta ta juye, ta rikice. Yau ma mafarkin ne? Ko kuma zahiri ne? Nan ta shiga dambarwa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tantance, sai dai haƙar ta, ba ta cimma ruwa ba.
Ayshercool 08081012143.
35
Nana ta motsa, ta ji taushin katifar da suke kai, ta fi ta ɗakinsu. Ga ƙamshin turaren da ya sauya, ya sanya Nana sakankancewa a kan a wannan karon ma, irin wancan mafarkin ne. Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, a wannan karon ma ta kasa sarrafa kanta da nutsuwar ta.
Sai dai a wannan karon al'amarin ya banbanta da na farko.
"Kai ka rabu da ni" Ta faɗa da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture shi.
"A'a" ya faɗa ƙasa-ƙasa.
Tabbas ba mafarki ba ne ba, bayan Buzun mijin nata ya dangana da ita, wani bugire mai girman gaske, bugiren da ba ta taɓa kawo faruwar sa a tsakanin su ba. Ita a tunaninta tun da ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa ba ya jin komai, hakan ne ya sanya take yawonta ma babu hijjabi a ɗakin, sai ta ga ya dame ta da kallo, ta rufe jikinta.
Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka ƙyale ni"
"je suis désolé (ki yi haƙuri)" ya yi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa.
Bayan wani lokaci da Nana ba ta iya tantance adadinsa ba, domin ta daɗe da daina gane komai.
"Ma femme. (Matata)" Ya yi maganar yana ɗan murza ya tsunta. Ta buɗe idonta da ya yi jawur, da ƙyar tana kallon sa.
A wannan karon fitilar ɗakin a kunne take. Sai dai fatarsa ta yi jawur.
Ta sunkuyar da kanta daga kallonsa.
Ya saka hannu ya share hawayen da ke fuskarta, sai dai kuma ya kasa magana.
Ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta, ya kamo hannunta ma ya sumbata. Ta lumshe idanunta tana numfashi a hankali.
"Merci (Na gode)" shiru ta yi tana ƙara sunkuyar da kanta.
Ya saka hannunsa ya ɗago fuskarta, amma ta lumshe idanunta, ta ƙi buɗewa.
"Kalle ni mana"
Kwaɓe baki ta yi, ta ci gaba da kuka. Ya saki murmushi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce "A yi haƙuri"
Ya ci gaba da wasa da yatsun hannunta, daga baya ya tashi a hankali yana kallonta, sai dai ya rasa abin gaba ɗaya.
Nana ta yinƙura da ƙyar, ta tashi zaune, ta ja bargon ta rufe jikinta.
Su na haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa, fuskarta a haɗe, hawaye na biyo fuskarta.
"Yi haƙuri" ya yi maganar yana kallon ta.
Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshsheƙa.
Shafa bayanta ya ci gaba da yi, cikin sigar rarrashi, amma ta maze ta din ga kuka.
Ya ce "Ki yi shiru"
Ba ta kula shi ba, ta janyo rigarta, ta saka ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta nufi gas ɗin ta.
Ta dafa ruwa ta shiga banɗaki, ta jima sannan ta fito, a ƙofar banɗakin ta tarar da shi a tsaye.
Sai da ta ɗan tsorata, ta na ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, ya ce "Ni fa?" Ta kalle shi.
Ya ce "Zan yi wanka"
Ta ba shi hanyar shiga banɗakin, ya kalli hanyar ya ce "Ruwan sanyi? A a ina jin sanyi"
"Bari na dafa" ya koma gefe ya zauna, ta ɗora masa ruwan, ta kalli agogon ɗakin, huɗu da rabi, ta san idan ta kwanta yanzu ba bu lallai ta samu sallar asuba.
Ta shimfiɗa sallaya, ta ajiye wayarta a kai, ta ajiye hijjabinta.
Yana gefenta, sai bin ta yake yi da ido.
Ta kai ruwan banɗaki, ta na haɗa masa, sai a yanzu ta tuna lokacin da ya ce mata zai yi wanka, ashe ruwan sanyi ne ba ya so.