Buzu book 1 complete - Chapter 30
Buzu book 1 complete Chapter 30: Buzu book 1 complete Chapter 30. A banɗaki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin littafin da take karantawa na Ƙaisar, ta san…
4,486 words
A banɗaki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin littafin da take karantawa na Ƙaisar, ta san yanzu kafin ta sake samun littafin sai an daɗe. Kenan da gaske dai shi ne uban duƙusa? Ya aka yi sunansa ya canza zuwa Ƙaisar?
Ta wanke fuskarta ta yi brush ta fito. Har ya karkaɗe mata shimfiɗa.
Ta zauna, ya ɗaukko kofi da murfi ya miƙo mata. Ta saka hannu ta karɓa, ta buɗe ta ga abu a kofin kamar madara, da ɗan wani gari gari a kai.
Ta kalle shi ya ce "Sha" ta kai bakinta, ta ji babu ƙarni, ta yi bismillah ta fara sha.
Babu zaƙi, sai dai akwai garɗi da maiƙo a baki, ga ɗumi kuma babu ƙarni mai damu. Sai da ya saka ta shanye tas, ta kalle shi ta ce "Wai mene ne wannan?"
Ya yi murmushi ya ce "Nonon raƙumi ne"
"Raƙumi kuma? A ina ka samu Nonon Raƙumi?"
Ya ce "Habu na saka ya kawo miki, jikinki zai yi ƙwari, ga abinci ma sun haɗo da shi, na ce ba ki da lafiya"
"Gaya musu ka yi?"
Ya ce "Me?"
"Abin da ya faru jiya?"
"A'a ban ce musu, kin kore ni waje ruwa ya jiƙa ni saboda ki na tsoro na ba"
Ta ce "Ba wannan ba"
"To me?"
"Ba komai" tayi maganar cikin basarwa. Ya yi dariya ya ce "Ban faɗa ba, daga ni sai ke kawai wannan" ta yi shiru wata irin kunya tana mamaye ta.
Babu babban abin da yake ƙara sanya Nana farin ciki, sama da samun abinci sau uku a rana da take yi a wadace, babu geji kuma babu hantara.
Ƙaton buredi ne lafiyayye, aka soya ƙwai fal, shayin ma shi ya zuba mata. Tana ci yana ƙare mata kallo.
"Ka daina kallona, ko na tashi"
"A'a"
Ta ce "A'a me?"
"Ba zan daina ba"
Ta juya gefen sa, yadda sai dai ya kalli side ɗin fuskarta, ta gama ci ta koma gefe.
Shi ya yi mata komai, da ta motsa sai ya ce ta zauna. Sai dai ya lura gaba ɗaya ta zama so silent yau, ba karaɗi da surutu. Duk sai ya ji hakan babu daɗi. Ita kuwa ta yi matuƙar mamaki, ganin yau bai fice ya bar ta ita kaɗai ba.
Ya dawo kusa da ita ya zauna, har gashin sa yana taɓa wuyanta, kasancewar bai tufke shi ba, sakin sa ya yi.
"Me ya faru?" Yayi maganar yana ɗora hannunsa a nata.
Ta girgiza masa kai, alamar babu komai.
"Ko ana fushi ne?" Ta ɗaga kai alamar eh.
"Me yasa?" Ya tambaye ta, yana shafa jikinta.
A ranta ta ce "Ikon Allah, ji mutumin nan da samun guri"
"Ba ki ce mini ya jiki ba, kin kore ni ruwa ya jiƙa ni, ba ni da lafiya"
Nana ta tura baki ta ce "Ba ga shi ka warke ba, kuma ba ina sane bane ba"
"To ke kin warke?" Yayi maganar ƙasa-ƙasa. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa, hakan ya ba shi damar haɗe bakinsa da nata. Gaba ɗaya Nana sai ta rasa bakin magana, sai rarraba ido.
Yana sane yake wannan shirun, yana sunkuyar da kai, ko kuwa ya abin yake? Ta tambayi kanta.
Tana jin yadda ya ƙanƙame ta a jikinsa, sai yawo yake da hannunsa a jikinta, yana neman ya sanya lissafi ya ƙwace mata. Domin har mamakin kanta take yi, yanayin da take shiga, idan su na tare ko da kuwa a cikin bacci ne.
"Ammm ya aka yi yau ka ke magana sosai? Maganar ba ta ɗauke ba?"
Ya ce "Mmmm, tun jiya ma na ji ina iya yi, haryanzu ban ji kaman an shaƙe ni ba ta daina fitowa. Wataran ina son na yi nake kasawa"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To yanzu baka san sunan ka ba, wane sunan zan din ga gaya maka kenan?"
"Ko wanne"
"In ce Buzu nima?"
"Nima in ce buzuwa?" Ya tambaye ta.
Ta ɗago ta kalle shi ta ce "Buzuwa kuma?"
"Eh, macen buzu shi ne buzuwa ba? Idan ki na kallona zan kuma sumbutar ki ne a baki"
Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta, ya sake gyara riƙon da ya yi mata da hannayen sa.
"To yanzu me zan din ga ce maka ne?"
"Ki saka mini ko mene, nima zan ji daɗi, kowa yana da suna ni ba ni da shi"
"To da yaya aka ɗaura mana aure ba ka da suna?"
Ya ce "Habu za ki tambaya"
"To ni yanzu ina na ga Habun?"
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "Ka ga kai mijina ne, to in ce maka Sayyid ka na so?" Ta yi maganar tana ɗagowa ta kalle shi.
Sake haɗe bakinsa da na ta ya yi, na wani ɗan lokaci, sannan ya cire bakinsa ya kalli idanunta ya ce "Sayyid, j'aime ça (I like it) ma vie"
"Ni ka daina yi mini wannan yaren ba na ganewa" ta yi maganar da sigar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba.
Murmushi ya cigaba da yi, yana lumshe idanunsa.
"Yau ba za ka fita ba ne? Kar su zo su na neman ka, kana nan a zaune"
"Ba na son fita"
Ta ce "Saboda me?"
"Saboda ke"
"Ni har yanzu mamaki ka ke bani, kamar an canza ka, ka yi magana ta fi guda goma sha biyar"
Wannan karon sosai ya buɗe haƙoransa ya yi dariya, ya ce "Kin ƙirga ne?" Ta ɗaga masa gira ɗaya tana murmushi.
"Me yasa nake ba ki tsoro? Me na yi yake ba ki tsoro?" Shiru ta yi ta rasa abin da za ta ce masa, kenan shi ma bai san abin da take gani ba.
Horn aka yi da mota, Nana ta fara ƙoƙarin zame jikinta ta ce "Ana horn, shi yasa na ce maka ka shirya ka fita, kar a zo ana buƙatar ka".
A matuƙar kasalance, ya tashi ya je gaban mudubin ya tsaya.
Nana ta tashi ta ɗaukko masa yin rawaninsa. Sai dai mai horn ɗin ya ci gaba da yi babu ƙaƙƙautawa.
"Sayyid ko za ka buɗe musu, sai ka dawo ka saka rawanin?"
Hankalinsa a kwance ya ce "Za ki iya fita ba riga?" Sororo ta yi tana kallon sa.
"Idan ba za ki iya fita ba riga ba, ba zan iya fita babu rawani ba, gashina a buɗe. Yadda ki ke jin abin da ki ke ɓoyewa haka buzu yake ji, idan ya fita bai suturta gashin sa ba".
"To ni dai ka bar wannan falsafar, ka yi sauri" a nutse ya naɗa rawanins, Nana na ta azalzalarsa, saboda horn ɗin ya wuce hankali.
Ya gama naɗawa ya fita, ya buɗe gate ɗin.
Ko ƙarasa shigo da motar ba a yi ba, ta fito daga cikin motar a matuƙar hasale cikin matsananciyar fusata ta ce "Malam bagidajen ina ne kai? Kurma ne kai ko ba ka ji ne? Wannan ai tsagwaron wulaƙanci ne?"
Bagidajen da ta faɗa ya sauka a ƙirjin Nana. Kallo ɗaya ya yi wa matashiyar budurwar, ya sake gyara zaman takunkumin fuskar sa, ya nemi guri ya zauna a kan bencin da yake zama.
"Ba magana nake yi maka ba? Ba za ka iya ba ni haƙuri ba?"
Cikin azama Nana ta sako hijjabinta ta fito, ta nufi inda Siyama take ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yana uzuri ne shi yasa bai fito da wuri ba"
"Ni kun san meye nawa uzurin da zan ta horn over 10 minutes, amma bai buɗe ba, kuma ina magana ya yi mini shiru dan wulaƙanci?"
Nana ta sake kwantar da murya ta ce "Ai ni na baki haƙuri a madadinsa, dan Allah ki yi haƙuri, ba zai sake ba"
"Wawa kawai" ta furta tana juyawa t nufi gurin da motarta take.
Nana ta haɗiye wani abu mai matuƙar ɗaci, ta ji zafin maganganun da aka gaya wa mijin nata. Duk da ta san ya yi laifi amma kalmomin sun yi tsauri. Ta kalli idonsa ta ga ya yi jawur, hannayen sa na rawa, launin fatarsa ya canza zuwa ja.
Ta zauna a kusa da shi a kan bencin, ta ɗora hannunta a bayansa ta ce "Sayyid. Ka yi haƙuri na fika jin zafin abin da ta gaya maka, amma ka yi haƙuri ka ji?" Kawai ya jinjina mata kai.
Ta sake kallon idanunsa, yadda suke ƙara rinewa zuwa launin ja, hakan ya ƙara bayyanar da matsanancin ɓacin ran da yake ciki.
"Taso mu koma ciki to, tun da ka buɗe mata" ya girgiza mata kai alamar a'a.
Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ƙyale shi, dan ya fara ba ta tsoro.
Duk da yanayin da take ciki, ta ji daɗin hirar da suka ɗan yi da shi.
Ta kama aikace-aikacen ta a cikin ɗakin.
*****
Jamila ce take gaya wa Mama batun unguwar da Hajiya Sa'a ta ce za ta raka ta.
Mama ta ce "To mene ne a ciki? Ai babu komai yadda take nuna miki ƙauna, ni ko bangon duniya ta ce za ku je, ai ba zan hana ba"
"To Mama Baba fa? Ni ba na son masifar nan tasa"
"Dalla rabu da shi, uwar me yake bamu a gidan, Ubangiji Allah ya haɗa ki da iyayen ɗaki masu ƙaunar ki, mu na samun alkhairi ta hannunsu, za ki din ga kawo zancen sa, ki yi tafiyar ki, ni na san abin da zan gaya masa"
Jamila ta yi murmushi ta ce "To shikenan, ni dama ba na jin ki, na san za ki bar ni"
Can Asibiti kuwa, likitoci sun yi deciding, tiyata za a yi wa Shukura a cire jaririn cikinta, saboda a tseratar da rayuwarta da ta abin da yake cikinta. Sai dai da Jininta ya sauka sai ya sake hawa, saboda gaba ɗaya a tsorace take, ta yanke tsammani da rayuwar duniya ba ki ɗaya. Duk da irin rarrashi da ƙoƙarin kwantar da hankalinkin da ake yi mata.
Bayan Nana ta ɗora girki, ta kira Hajiya Amina su gaisa, a nan take gaya mata halin da ake ciki, cewar su na Asibiti an kwantar da Shukura. Hankalin Nana ya tashi sosai da sosai, tana son zuwa duba Baba da Jamila ma, ga kuma wannan maganar ta rashin lafiyar Shukura. Sai dai yadda ransa yake a ɓace ta san ba ta da damar yi masa magana.
Tun da abin nan ya faru, bai sake shigowa ɗakin ba, ta je ta same shi a kan ta gama girki ya yi mata shiru. 'yar walwalar da ya fara yi ta gushe baki ɗaya. Gaba ɗaya abin ya dame ta sosai da sosai, ko abincin kirki ta kasa ci.
Sai bayan sallar isha'i ya shigo ɗakin ya nemi guri ya zauna, ba tare da ya furta komai ba.
"Sayyid ba ka ci abinci ba fa tun na safe ba ka kuma cin komai ba, dan Allah ka yi haƙuri ka ci abinci".
Bai ko kalle ta ba, balle ta saka ran zai ci, ƙarshe sai haƙura ta yi ta zura masa ido.
Ta gama shirinta, ta nemi guri ta kwanta, amma yana zaune. Nana ta jinjinawa girman zuciyar sa. Ya jima a zaune sannan ya tashi ya canza kayan jikinsa.
Bacci har ya fara ɗaukar Nana, ta ji yana shigowa cikin bargonta, gabanta ya faɗi tuna abin da ya faru jiya, sai dai ba ta motsa ba, sai addu'a da take yi a karkashin zuciyarta. Ya matsa sosai ya rungume ta, yana yi mata numfashi a wuya.
"Idan ina fushi, ki daina kula ni" ya faɗa kamar mai raɗa.
Ba ta iya tanka masa ba, bai kuma sake ce mata komai ba, sai da ta ga babu alamar zai yi mata wani abu, sannan nannauyan bacci ya ɗauke ta.
Tamkar wani zai ƙwace ta, ya ƙara ƙanƙame ta a jikinsa. Sai ƙamshin turaren sa take yi.
A cikin baccin ta ji muryar Ƙaisar "Ba kin shige cikin bargo ba, idan ki ka kuma ɗaukar littafin nan ki ka karanta, sai na baki mamaki, sai na yi miki abin da ba ki taɓa tsammani ba"
"To ina ruwanka da bargon da na shiga, ya naga kamar ka na kishi da mijin nan nawa ne?"
Tsaki ya ja ya ce "Da me zan yi kishin? Haryanzu ba ki san a hatsarin da ki ke ba, wauta da shirme ne kawai yake ɗawainiya da ke. Kin ƙi ki buɗe ido ki kalli gaskiya. Gaba ɗaya kin ma manta da batun tantance waye shi, duk da irin abubuwan da ki ke gani da ya saɓa da ɗabi'ar bil adama"
"A'a ba kyau zurfafa bincike, tun da Allah ya sa ina samun shinkafar da zan ci, ba ya saka ni kuka, babu tashin hankali ai gara na haƙura na lallaɓa haka. Duk wani abu da yake yi da ya saɓawa ɗabi'ar Adam wannan kuma na san kai ne, kai ka ke ƙulla komai. Na san so ka ke ka kashe mini aure, saboda kai duk yadda za ka yi hana ni jin daɗin rayuwata, shi ka ke yi"
Galala yake bin Nana da kallo baki buɗe cikin mamaki. Ya ce "Gaskiya ne, idan ya gama baki jin daɗin za kuma ki ɗanɗana kuɗar ki, banda ina duba wani abu da da kaina zan bayar da jininki ga matsafan nan ki mutu uban kowa ma ya huta!"
Ayshercool 08081012143 37
Nana ta saci kallon ƙaisar, jikinsa har fitar da hayaƙi yake yi saboda fusata.
Ko a jikinta ta ce "Amm dan Allah ka gaya mini ya aka yi da Lanti a gurin yin girka? Ya aka yi ka hau kanta, tun da na ga ba da kai a ka fara yi mata girka ba, kuma ya aka yi ka canza sunanka? Ya aka ƙarke da sarkin aska kuma a garin? Ta yaya duk nake da alaƙa da wannan abubuwan?"
Wani irin takaici ya turnuƙe Ƙaisar, ya tashi a fusace da niyyar ya yi jifa da ita, ko ya samu ya huce, sai kuma ya fasa kawai ya fice ya bar ta a gurin.
Ta ce "Wallahi sai na kai ƙarshen littafin nan, ko da kuwa za ka kashe ni ne, sai na ga ƙwal uwar daka, sai na karanta har ƙarshe ko me za ka yi sai dai ka yi"
Sannu a hankali yake shafa fuskarta, yana kallonta, kamar wata jaririya haka ta yi miƙa sannu a hankali, sai da ta banƙare gaba ɗaya. Ita gaba ɗaya ta manta da shi a kan katifar, a zatonta ita kaɗai ce a kan katifar, sai da ta ji ta a jikin mutum. Ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai kuma ta ɗan tsorata, ta yinƙura da sauri. Amma ya riƙe ta yana kallon ta.
"Amm lokacin salla ya yi ko?" Ya ɗaga mata kai alamar eh.
"To bari na je na yi alwala"
Ya cika ta tashi, ta je ta yi alwala, sai da ta fito sannan ya ce "Zan yi wanka"
Ta ce "Wanka kuma? Yanzu?"
Ya ɗaga mata gira daga kwance. "Ka yi da safe mana, gari da sanyi yanzu" Ya lumshe idanunsa ya buɗe, ya ce "Tare mu ka kwana a shimfiɗa, kuma ya dai kamata na yi wanka" Ba ta ce komai ba, ta yi shiru, Allah ya taimake ta, tana da ruwan zafi a tea flask ta haɗa masa. Ya yi wanka ya yi alwala ya fita Masallaci.
Nana kuwa bayan ta idar da sallar asuba, ta zauna a inda take ta fara karatun Alqur'ani. Ya dawo ya tarar da ita, ya tsallake ta, ya nemi guri ya kwanta.
Wajen ƙarfe takwas ya farka, tuni Nana ta gyara ɗakin yana ta ƙamshi, tana zaune a kusa da socket, tana caji tana danna waya.
Ya ɗora hannunsa a kan cinyarta, ya rufe fuskar wayar, ta waiwayo ta kalle shi ya ce "Ina kwana?"
Murguɗa masa baki ta yi ta ture hannunsa. Ya tashi zaune, ya matsa kusa da ita ya ce "Na yi laifi ne?"
"Ai ka san me ka yi mini"
Ya ce "A'a abun tun shekaranjiya ba ya wuce ba?"
"Ni ba wannan ba, jiya na yi ta baka haƙuri amma ka haɗe rai ka ƙi kula ni, ka ƙi cin abinci ma" ta ƙarasa maganar tana hararsa
Ya ɗan yi murmushi ya sake matsawa, tamkar zai shige cikinta ya ce "Na ce idan ina fushi ki daina kula ni"
Ta noƙe kafaɗa ta ce "Ni ba zan iya ba"
Murmushin fuskarsa ne ya faɗaɗa cikin matsanancin farin ciki ya kama hannunta ya ce "Ki yi haƙuri, idan raina ya ɓaci, ko bani da lafiya, bana iya magana. Wasu lokutan ina kasa magana haka kawai, amma ya fi idan raina ya ɓaci."
"To ni da ba ni na yi laifin ba, sai ka daina yi mini magana? Na fi ka jin haushin abin da aka yi maka fa"
"Na sani, ban san ya aka yi nake iya magana sosai ba idan ina tare da ke, ina iya yin sati ban iya yin magana ba, kuma ina son na yi amma ba ta fitowa. Amma ke yanzu ina yin magana da ke sosai, ina jin daɗi"
Nana ta kwashe da dariya ta ce "Bagware idan ka yi magana dole sai mutum ya gane kai ba bahaushe ba ne ba"
Yayi dariya ya ce "Na fiki iya Hausa sosai, buzuwata saka kaya muje sayo abun karyawa1"
Cikin murna Nana ta ce "Yauwwa, dama ina son na fita na ga waje, tun da aka kawo ni ban taɓa fita ba".
Dama ta yi wanka, ta saka hijjabi a kan kayanta, shi ma ya saka kaya, suka rufe ɗakin su ka fita.
Sosai unguwar ta yi wa Nana kyau, duk da ruwan da ake yi, babu alama a unguwar saboda akwai wadatattun magudanan ruwa, ba kamar unguwarsu ba, da ruwa ɗaya sai unguwar ta shafe kwana uku maƙil da ruwa da azababben sauro.
Ya saka hannunsa ya riƙo na Nana, ta ɗaga kai ta kalle shi, ya kashe mata ido. Sosai abin ya ƙayatar da ita.
"Sayyid"
Ya kalle ta, yana jiran jin abin da za ta ce.
"Dan Allah ina son ka bani dama, na je gida na duba Baba, yana ciwon ƙafa tun bayan biki ƙanwata ma da suka zo, ba ta da lafiya. Kuma ka ga a al'adarmu yakamata mu je mu yi wa mutane bangajiya"
"Mene hakan?"
Ta yi murmushi ta ce "Mu yi musu sannu, saboda hidimar biki da suka yi, ka ga Shukura ma babu lafiya tana asibiti, maman yaron da nake raino"
"Tom"
Nana ta ce "To yaushe za mu je?"
"Zan gaya miki"
"To na gode sosai mai rawani"
Gurin da yake zuwa sayen ƙosai suka je, Nana ta yi mamaki ganin har a manyan motoci ake zuwa gurin sayen ƙosai, da kunu gurin matar.
Nana ce ta yi wa mai ƙosan magana ta gaishe ta.
Matar ta ce "Laa kece matarsa ko 'yar uwassa?"
Nana ta yi murmushi ba ta ce komai ba.
"Allah sarki, yana zuwa sayen ƙosai ai, na nawa za a baku? Ki ce masa na ce kwana biyu bai zo sayen ƙosai ba, ban iya maganar su ba"
Nana ta ce "Ai yana jin ki"
Matar ta ce "Haba dai? Ba kurma ba ne?"
Nana ta kwashe da dariya ta ce "Yana magana"
"To ai kullum ya zo kuɗi yake bayarwa kawai, ko ya rubuta"
Ya yi mirsisi kamar ba a kan shi ake magana ba, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya bawa Nana.
Kamar Nana ta san matar, suka din ga hira, ta sallame su, suka nufi gida.
"Sayyid dan Allah ka din ga yi wa mutane magana, ko dan saboda yanayin rayuwa. Ka ga da yawa ana ɗauka ko kai kurma ne" shiru ya yi mata, haryanzu ba ta gama fahimtar sa ba.
Ba ta damu da rashin bata amsar waccan maganar ba ta sake cewa "Yauwwa, dan Allah akwai gidaje a bayan gidan nan ne? Ina son sanin gidan Anty Haula, ina son na kai mata ziyara nima"
"Babu gidaje a baya"
"Amma ta ce mini gidanta a bayan inda muke yake"
Ya ce "Mu duba tare" ya biyo da ita ta bayan layin, wasu irin manyan gidaje ake yi, sai dai duk kangwaye ne, babu ma alamar wani gida da yake da mutane a gurin.
"Ina ga ban gane kwatancen ba, idan ta sake zuwa na tambaye ta. Amma sai na din ga jin hayaniya a bayan ɗakin, kamar akwai mutane a gidan" kawai ya kalli Nana ba tare da ya ce mata uffan ba.
Ko da suka gama karyawa, roƙonsa ta yi tana son shiga cikin gidan, ta gaida Hajiyar. Ya ce "A dawo lafiya, idan kuma da maza ki dawo" ta jinjina masa kai tana murmushi.
Yau ma a falon saman benen, ta iske Hajiyar gidan, tana waya a matuƙar fusace.
"Ni wallahi na gaji, idan ka dawo ka san yadda za ka yi da ita. Ni me ake yi wa Yusra a gidan nan, balle a ce depression ya kama ta? Ga anti depressants ɗin nan, mun je mun ga Likita an bata, amma ta ƙi sha. Sai kuka, ba damar na yi mata magana ko nasiha ce sai ta hau kuka ta ƙule ta wuni a ɗaki"
Nana ba ta iya jin abin da ake faɗa a cikin wayar, ta gama bambaminta, ta kashe wayar.
Nana ta gaisheta ta amsa, ta ɗora da cewa "Yi haƙuri kin same ni ina waya ne"
Nana ta ce "Babu wani abu, bari na gyara falon"
Matar ta ce "Yauwwa dan Allah da kitchen ma"
Nana ta ce "To" ta fara gyara ɗakin, tana cikin mopping ta fara jiyo wani sauti, da ta rasa sautin mene ne, kamar ana buga wani abu. Ta basar ta ci gaba da aikinta amma sautin ya ci gaba da fitowa daga wata siriryar hanya.
"Ƙaisar" ta furta a hankali. Kwana biyu hankalinta ya ɗan fara kwanciya, amma ta fuskanci matsalolinta na ƙoƙarin sake dawowa.
Ta gama mopping ɗin falon, ta tafi kitchen ɗin, nan ma ta fara tattarewa kamar ba kitchen ɗin mata ba. Kaca-kaca ga tarkacen kwanuka wasu abinci duk ya bushe.
Ta haɗa kwanukan a sink, ta fara wankewa. A hankali ta ji sautin nan ya biyo ta har kitchen ɗin, ya ci gaba da nufo inda take, ba ta waiwaya ba, ta fara karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakin ta. Aka jefo mata kofi a cikin sink ɗin, mai jefowar ta nufi hanyar barin kitchen ɗin. Tamkar an dasa Nana ta kasa motsi, sai da ƙyar ta kalli ƙasan rigar matar har ta fice.
A hankali Nana ta fara jin sanyi, gabanta ya fara faɗuwa, hakan ya tabattar mata da akwai matsala. Kawai ta ɗauraye hannunta ta bi bayan matar.
Tamkar ana hankaɗata ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ɗakin. Wata farar mace ta gani a ɗakin, a zaune fuskarta ta yi ja alamar ta yi kuka. Ta zubo wa Nana ido.
Nana ta taka a hankali ta nufi gadon da matar take, ta zauna a kusa da ita.
"Sannu"
"Yauwa" ta amsawa Nana.
"Shigowata ta uku kenan, ban taɓa ganin ki ba" matar ta yi ƙurii da ido tana kallon Nana.
Nana ta miƙa mata hannu, da nufin su gaisa.
Tamkar doluwa, matar ta bawa Nana hannu da nufin su yi musabaha.
Su na gaisawa jikin Nana ya hau rawa, ita kuma launin fatar matar, ya ƙara yin jawur, idanunta ya fara zubar da hawaye.
Nana ta ce "Wace ce ke?"
Bakinta yana rawa ta ce "Ha...ha..Haulat"
"Me yasa ki ka yi mini ƙarya? Ki ka zo mini a matsayin mutum? Kuma me ki ke yi a jikin bil'adama?"
"Fansa na ɗauka, nan gidan a nan mune rayuwa da 'yan uwana, kawai su ka gina gida, hankalinsu kwance su ka yi zaman su, ba su yi tunanin akwai wata halittar a gurin ba. Da sun gabatar da karatun Alkur'ani ne ma, da mun haƙura mun tashi, amma kawai suka yi gini suka zauna"
Nana ta numfasa ta ce "Kuma sai ki shiga jikin wanda bai ji ba bai gani ba ki zauna? Kun san ba ma ganin ku, me yasa za ku din ga zaluntar mu, ba za ku yi mana uzuri ba? Yanzu kin kyauta an ce matar nan ba ta ci ba ta sha, sai kuka kin yi adalci kenan?"
"Nima ba a yi mana adalci ba, ramawa muke yi"
Buzu yana zaune a kan benci, ya saka hanyar fitowa daga gidan, yana jiran ya ga ta ina Nana za ta fito, dan tana fita ya ji zaman ɗakin ya dame shi.
Kawai ya hango ta, ta fito idanunta a rufe, ta nufo shi. Sai da ta kusa ƙarasowa, sannan ya nufe ta yana son tambayarta ko lafiya. Kawai ta tafi za ta faɗi ƙasa. Riƙe ta ya yi yana mamakin me ya same ta haka?
Ɗakinsu ya shigar da ita, ya kwantar da ita, yana mamakin yadda jikinta ya yi sanyi ƙalau.
Mamaki ne ya cika Nana bayan da ta ganta a tsakiyar daji, da ita da Haula.
"Wace ce ke? Kuma me yasa ki ka yaudare ni ki ka zo mini a matsayin mutum?"
Haula ta yi dariya ta ce "Kamar dai yadda na gaya miki, laifi aka yi mini nake ramawa. Kwatsam kuma ke ma sai na haɗu da ke. Yanzu a duniya babu abin da nake ƙauna sama da hadimin ki, shi ya sanya ma har na yi yinƙurin taimakon ki, dan na samu shiga a gurin ki"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Waye Hadimin nawa?"
"Ƙaisar, tun da na buɗi ido a duniya ban taɓa ganin kyakyawan matashin Aljani mai kyau da cikar zati kamar sa ba"
Galala Nana ta kalle ta, ta ce "Ƙaisar ɗin? Wannan zanƙalelen abin?"
"Ƙwarai shi, saboda na burge shi na zo na cinye gubar da aka kawo miki a wainar fulawa, sai dai kash! Haƙa ta ba ta cimma ruwa ba. Ina roƙon ki, ki taimaka mini na samu Ƙaisar, ni kuma na yi miki alƙawarin barin jikin matar can, da taimaka miki da duk abin da ki ke so"
"Tirrr Allah ya yi mini tsari da sake ja wa kaina wata jarabar, ta hanyar haɗa kaina da ku, shi ma maraba nake nema da shi, ido rufe, balle na sake rakito ki, ki je can Allah ya daidaita ku. A'uzu bi kalimattilahi tammat" Nana ta furta a zahiri tana hamma. Ta tashi zaune ta ga an rurrufe ko ina na ɗakin, an kuna garwashi a ɗan kaskon dafa shayinsa.
"Sayyid" ta kira sunansa da ɗan ƙarfi, amma ta ji shiru.
Ta yi mamakin dalilin da yasa ya rufe ko ina haka. Ta shiga banɗaki ta yi alwala, saboda an idar da sallar azahar ma.
Da ya shigo ɗakin ya tarar da ita ta idar da salla, bai ce mata komai ba, ta ɗora girki tana yi masa hira, saboda ba ta iya tuna komai ba. Jin ya yi shiru ba ya tanka mata, ya sanya ta yin shiru.
*****
Yaya Atine ce ta zo gida duba Baba, ta ga yadda yake tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa.
Ta jinjina kai ta ce "Wai Isa wannan ƙafar taka, ka je asibiti kuwa?"