Buzu book 1 complete - Chapter 32
Buzu book 1 complete Chapter 32: Buzu book 1 complete Chapter 32. "Shi ba shi da nasa buƙatun zai din ga kashe mana kuɗi har haka?"
4,497 words
"Shi ba shi da nasa buƙatun zai din ga kashe mana kuɗi har haka?"
Ya yi shiru bai amsa mata ba.
A hankali Nana ta ce "Sayyid"
"Husnahh"
"Dan Allah ya ake yi ka ke yin wasu abubuwan, ka san na ce maka, ba ni da cikakkiyar lafiya wasu lokutan gaba ɗaya a rikice nake ba na tantance ainihin zahiri da mafarki, amma sai na ga kana abubuwan da mutane normal ba sa iya yi"
"Kamar me?"
Ta ce "Ammm ka na shigowa cikin mafarkina"
Kawai ta ji ya yi dariya "Dama wani na shiga cikin mafarkin wani ne? Ba mafarkinki nake shiga ba, ruhina ne yake rayuwa a cikin naki, kuma naki yake rayuwa a nawa. Na fuskanci hakan a ranar da na fara ganin ki, zuwa ranar da aka ɗaura mana aure"
"Ban gane ba, ka yi mini bayani sosai"
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ƙirjina ya fara nauyi"
"Saboda me?"
Ya yi mata shiru.
"Amma Sayyid.... "Shhhh zan yi bacci"
Ta ce "Tambaya ɗaya zan yi maka dan Allah"
"A'a"
"Allah fa na ce"
"Na ce A'a"
Ta ɗan ja numfashi ta ce "To amm... Tsit ta yi dalilin bakinsa da ta ji a nata.
Ya riƙe hannunta a nasa yana matsa nata a hankali.
"Dan Allah ka bari yau mu samu isasshen bacci, ni dan Allah ka ƙyale ni"
Ya ce "Idan ma kin yi baccin, zan biyo ki har cikin baccin naki. Na gaya miki ruhinki a cikin nawa yake rayuwa, ko fushi ki ke yi a cikin jikina nake ji".
Haka ya yi ta tsaro maganganun, da suka ci gaba da dagulawa Nana lissafi, da birkita mata ƙwaƙwalwa, wanda ba ta gama warwarar su ba, har ya nufi inda yake son zuwa.
*****
Tun bayar tafiyar Nana, da Shukura ta ga mahaifinta ta ji gabanta ya faɗi, ta kalle shi cike da tsoro da razani.
Cikin kulawa ya ce "Sannu Auta, haka ki ka koma? Ya jikin naki?"
A tsorace ta ce "Daddy dama yau zaka dawo, Mummy ba ta gaya mini ba"
Cikin damuwa ya ce "Ina can hankalina ya ƙi kwanciya, na ce bari na zo na ganki, na kira Sharif ya ce mini jikinki da saura, shi yasa na ce gara na zo na gan ki"
Ta dai yi shiru, gabanta na ci gaba da faɗuwa, ya gama yi mata sannu ya tashi suka fita tare da doctor Sharif.
"Sharif "
"Na'am ranka ya daɗe"
"Muddin yaron nan zai rayu, ka yi duk mai yiwuwa a cire shi kawai, a matsa nake"
"Zan yi iya ƙoƙarina, amma ka san wannan sabga ce mai haɗarin gaske, sai an yi taka tsantsan yadda ba za a bar duk wani trace da za a gane wani abu ba, zan yi setting date da komai da yadda abin zai kasance"
"Better" Alhaji Zailani ya furta yana yin gaba.
Gidansu Nana har ƙarfe goma na dare Jamila ba ta dawo ba, Baba yana tsakar gida yana yi wa Mama bala'i.
"Yanzu Rabi sakarcin naki har ya kai Jamila ta kai bayan goma a waje? Gidan uwar wa ta tafi haka?"
"Wai dan Allah Jamila za ta gudu ne? Na ga dai ba yarinya ce ƙarama ba, na ce maka za ta dawo"
"Za ta dawi gidan uban ta je? Goma na dare ta riga ta wuce, me take yi a waje a wannan lokacin?"
"Dan Allah ni kar ka ɗaga mini hankali, na ga dai yarinyar nan ba sauke hakkin da Allah ya ɗora maka ka ke yi ba, abinci ma ba bamu ka ke yi ba, sai ma dai ta samo ka ci"
"Da ba na sana'a sai na zuba ido su lalace? Sana'ar uwar me take fita?"
"Ni fa 'ya ta ba lalacewa ta yi ba, na ga dai nan Nana take nata yawo, ba ka yi magana ba"
"Ai Nana na san me take fita yi, Jamila fa, na san dai tana yawon maƙota, bayan wannan uwar me take yi?" Sosai su ka ci gaba da jayayya tsakanin Mama da Baba, sai sha ɗaya da rabi na dare, sai ga Jamila ta yi sallama, hannunta niƙi-niƙi da ledoji.
Duk da ledojin hannunta, sun ɗauki hankalin Baba, amma ya dake ya fara tuhumar ta daga ina take. Mama ta kankane, ta hana Jamila magana, ta din ga karewa.
Ƙarshe sai haƙura ya yi, ya rabu da su.
Ita kanta Suwaiba jiki a sanyaye take kallon kayan da Jamila ta zo da su, tana fargabar Allah ya sa ba kauce hanya 'yar uwarta ta fara yi ba. Sai dai Mama ko a jikinta, musamman da Jamila ta ce mata, Hajiya Sa'a ce ta saya mata, wai gidan 'yar uwatta ta raka ta.
Wajen Sha biyu na dare, Jamila na ta bawa Suwaiba, labarin abin duniyar da ta gani. Suwaiba ta yi tsuru da ido tana kallon Jamila, daga bisani ta ce "Ni dai Jamila na fara jin tsoron matar nan, anya haka kurum take yi miki wannan ɗawainiyar. Jamila kar ki kai kan ki ga halaka, idan rayuwar ki ta lalace ba ki da wata makoma wallahi"
Jamila ba ta yi magana ba, Gaddafi ya faɗo ɗakin ya kalli Suwaiba ya ce "Bar ɗakin nan" Jamila ta miƙe ita ma a tsorace tana kallon sa"
"Fita na ce" ya yi wa Suwaiba tsawa.
Jamila na ƙoƙarin fita, ya danna ƙofar ɗakin ya saka sakata, ya fito da wani irin danƙo na injin markaɗe, ya kalle ta ya ce "Gidan uban wa ki ka je, ki kai yanzu ba ki dawo ba?"
Jamila ta rikice jikinta yana tsuma, amma ta kasa magana.
"Ba magana nake yi miki ba?"
"Babu inda na je?"
"Ƙarya ki ke yi, uban waye ya sauke ki a mota?"
"Hajiya Sa'a ce"
"Babar ki ce ita? Meye tsakanin ki da ita?" Jin ta tsaya inda inda, ya sanya ya fara zuba mata danƙon nan a jikinta.
Cikin kururuwa Mama take dukan kofar ɗakin, tana neman agajin mutane, kar Gaddafi ya kashe mata 'ya.
Ya zuba wa Jamila danƙon nan, ya fi sau sha biyar, sai da ya zamana daga ita sai underwear.
Sai da aka taru aka yi ta yi masa magiya, sannan ya buɗe ƙofar ɗakin ya yo ball da ita waje.
Mama hankali a tashe ta nufi Jamila tana salati, saboda wahala ko kukan ba ta iya yi, sai wani yawu da yake fita daga bakinta.
Baba ya ce 'Haba Gaddafi, ba kowane lokaci duka da zuciya yake aiki ba, yanzu idan ka illata ta fa, mace ce fa"
Gaddafi bai saurari Baba ya ce "Wallahi ta sake sai na karairayata, ba za ta ɓata mana suna a banza ba"
Cikin ƙaraji Mama ke faɗin "Wallahi ba zan yarda ba, sai na kai ka gurin hukuma"
Nasiru da yake gefe ya ce "Allah sarki, Nana na can, da yanzu an ce ta hana mutane bacci" babu wanda ya saurari abin da Nasiru yake faɗa, suka ci gaba da hayaniyar su.
**** Ko da Nana ta fito daga wanka, yana tsaye a ƙofar banɗaki yana jiran ta, ta murguɗa masa baki, za ta wuce ya riƙe ta yana murmushi ya ce "Meya faru?"
"Ni rabu da ni, ka hana ni bacci, ga jiƙa kai sai na yi ciwon kai"
"Ba dai fi na gashi ki ka yi ba" ya yi maganar yana taɓa gashin nata.
Nana ta kalle shi ta ce "To yi mini gori" bakinta ya sake sumbata yana murmushi.
Ta gyara shimfiɗa ta hau, shi ma ya haye yana buɗe bargo.
"Ni gaskiya katifar nan ta yi mana kaɗan"
Ya ce "Ya za ayi?"
"Ka saukar mini daga kan katifa, ai na ga ma ba a ɗakin nan ka ke kwana ba"
"Na gama yi miki amfani dole ki kore ni, ba inda zan je" ya yi maganar yana kwanciya"
Nana ta ce "Na shige su, idan muka futa sai ka yi gumm, sai na yi ta yi wa mutane bayanin ka na magana, ba kurma ba ne ba, amma daga ni sai kai ka yi ta wasu maganganu"
Tana jin sautin dariyar sa, cikin nutsuwar sa, da ta fi kama da Iyayi ya ce "Asma'u ke duniyata ce, tun da na farka a cikin wannan duniyar, nake jin tamkar nikaɗai ne baƙo, Habu yana iya ƙoƙarin sa a kaina, amma ba ya wadatar da ni. Fatana da burina na yi na gama mafarkin nan na tashi, na koma ainihin rayuwata. Ba na jin daɗin komai a wannan rayuwar, sai ranar da na fara ganin ki, tare da yayar ki da suka zo kun je gidan mai magani, har ki ka faɗi. Ina ganin ki na ji kamar ina da wata alaƙa mai ƙarfi da ke."
"Ni ɗin? Yanzu dama kai na gani ranar da muka je?"
"Mun haɗu a gidan sarkin baka ma."
A zabure ta ce "Sayyid ka san sarkin baka?"
Ya ce "Na sani, Habu sun kai ni, ko zan iya tuna ni waye. Ban taɓa maganar awanni biyu cikakkiya a rana ba, ban taɓa shafe sati guda ina iya magana ba. Duk sai bayan zamanmu a guri guda. Ni na ce Habu ya biya mini sadakin auren ki, tun ranar da na ganki kullum sai na yi mafarki da ke. Shi yasa da mai gidan da muke yi wa gadi ya ce na sake ki, zai biya ni na ji kamar na kashe shi. Na san ni mahaukaci ne, amma mahaukaci bai kyautu a kyautata rayuwar sa ba. Ke Duniyata ce, a tare da ke nake iya doguwar magana, na ci abinci, na daɗe hankalina bai gushe ba. Ba na son kowa ya raɓe ki, ko ya kula ki, saboda ina jin tsoron kar na buɗe ido na ga ba kya kusa da ni."
Ya kwantar da kansa a ƙirjinta ya ce "Ke ce Ahalina, kuma Duniyata. Ke Duniyata ce"
Haka ya din ga maimaitawa har muryarsa ta fara rawa, tamkar zai fashe da kuka.
Nana ta saka hannu ta zagaye bayansa, ta rintse idanunta, sai dai ta kasa magana a dalilin sanyi da ta fara ji.
Sauti ta fara ji na tasowar guguwa, ta buɗe idonta, ta gansu a cikin sahara tsakiyar dare, sai hasken farin wata da ya gauraye ko ina.
Tsohon nan ta gani a tsaye a kan su, hannunsa riƙe da sandarsa.
Ayshercool 08081012143 "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" Haka Nana ta rintse idanunta tana maimaitawa. Tana jin yadda yake sauke numfashi a jejjere, yana ƙara ƙanƙame ta.
Ta sake buɗe idanunta a hankali, ta gansu still a cikin saharar.
Tamkar wani zai ƙwace shi, haka ita ma ya rirriƙe shi, tana ci gaba da karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Zuwa jimawa ta daina jin sanyin, ta buɗe idanunta ta gansu a cikin ɗaki, jikinta ya gaji saboda yadda ya sakar mata nauyin shi.
"Sayyid" ta kira shi a hankali. Amma shiru, sai dai tana jin yadda cikin sa yake ɗagawa yana sauka a hankali alamar bacci yake yi. Ta motsa a hankali ta gyara kwanciyarta ta ci gaba da shafa kansa, tana tofa masa addu'a.
Wani irin nishi ta ji ya yi, ya yinƙura a gigice cikin ɗaga murya ya ce "Imam"
Cikin azama Nana ta tare shi, duk da ya fi ƙarfinta, ta riƙe shi gam. Haki yake yi tamkar wanda aka biyo ya ƙwace da ƙyar.
Ta yinƙura ta kunna fitilar ɗakin, ta dawo ta zauna a kusa da shi. Cikin sanyin murya ta ce "Sayyid. Me ya faru? Waye Imam ɗin?"
Hannunta ya kamo, ya ɗora a saitin zuciyarsa, ya riƙe hannun nata yana sauke numfashi.
"Sannu" ya jinjina kai.
Ya sunkuyar da kansa ya yi shiru, fuskar sa na bayyanar da matsananciyar damuwa. Ta sanya ɗaya hannun nata ta dafa shi ta ce "Sayyid mene ne?" Ya ɗago da ƙyar ya kalle ta, ya buɗe baki zai yi magana amma sai ya kasa.
Can tamkar an jefo maganar bakinsa ya ce "Wani abu ne yake damun zuciyata, ban san mene ne ba, amma ya yi mini nauyi, kamar zan bar duniya"
"Ya isa, ya isa haka ka yi shiru, in sha Allah babu wani abu, ka yi haƙuri" ta yi maganar tana shafa gadon bayansa. Ga mamakin ta kawai ta ga hawaye na gangarowa daga idanunsa. Rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta ce "Sayyid mene ne? Meye ya saka ka kuka?"
Ya girgiza mata kai alamar bai sani ba. Tun yana yi a hankali, kukan nasa ya din ga ƙaruwa, har da jijjiga. Ganin ta rasa abin yi kawai ta fashe da kukan ita ma, ta hau taya shi.
Ya janye ta daga jikinsa, ya kwantar da ita a kan pillow, shi ma ya kwanta a gefen ta, yana son ya yi mata magana amma tilas ya haƙura ya kasa ce mata uffan.
*****
Hajiya Amina na kwance tana bacci, a kan carfet, a ɗakin da take jinyar Shukura, ita kuma tana kan gadon marasa lafiya tana bacci, ta ji an kama hannunta. Ta yinƙura za ta yi magana amma wani irin jiri ya ɗebe ta daga kwancen da take, duk yadda ta so ta yi wani yinƙuri ko ta yi magana, ta kasa sannu a hankali jikinta ya yi sanyi, ya mutu murus, daga nan hankalinta ya gushe baki ɗaya.
*****
Fuska ɗauke da damuwa, Nana take kallon inda Ƙaisar yake ta haɗe-haɗen maganunansa, ba tare da ya dubi inda ma Nanan take ba.
"Ƙaisar"
"Na'am"
"Karo na farko zan roƙi alfarmarka"
"Ina jin ki" ya amsa ba tare da ya kalli inda take ba.
"Abu na farko ina roƙon ka, dan Allah ka yi haƙuri, ka saki ƙafar mahaifina, abu na biyu dan Allah ka bar ni mu zauna lafiya da mijina, ka daina wahalar da mu har haka dan Allah ka yi haƙuri."
Ya ajiye abin da yake yi, ya dawo gaban Nana ya zauna, ya kalle ta ya ce "Na riga na rantse sai na hukunta mahaifinki, mijinki ya shiga gona ta, ya kwance ƙullin da na yi wa mahaifinki a ƙafa, zai ɗanɗana kuɗarsa zan nuna masa gaba ma akwai gabanta"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Ta yaya ya kwance ƙullin da yake ƙafar Baba?"
"Oho ya dai kwance, kuma zai ga abin da zan yi a kai, sannan ki daina yi mini magiya a kan wani da yake faruwa, wannan wani abu ne da ki ka amince da shi da kan ki, dan haka dole ki jure duk abin da za ki gani. Sauran tambayoyin da ki ke son yi mini kuma ki adana abin ki, dan amsa miki su, dai-dai yake da amincewa da sharuɗana"
Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah Ƙaisar kar ka cutar da shi, shi kansa bai san wasu abubuwan na faruwa ba"
Ƙaisar ya miƙe tare da cewa "Allah ko?"
"Da gaske, bai san su na faruwa ba, dan Allah ka bar mu, mu ji da ƙalubalen rashin lafiyarsa, da rashin sanin waye shi"
Wata irin guguwa ce, ta gauraye cikin Libraryn, da sauri Ƙaisar ya buɗe rigarsa, ya kare Nana.
Tsohon nan ne ya bayyana a cikin libraryn, ya tsaya yana kallon Nana.
Ƙaisar ya tsaya a gaban Nana ya ce "Me ya kawo ka inda nake? Da izinin wa ka shigo gurin nan?"
"Ba na buƙatar izini, kafin zuwa inda farauta ta yake"
"Kar ka ƙetare layin da ka iya kawo, gagarumin tashin hankali da rashin jituwa tsakaninmu"
"Hannun agogo za ka mayar baya, ka gyaro ɓarnar da ka tafka, idan kuwa ba zai gyaru ba, to ba zaka hana ni, aikata abin da na yi niyya ba".
"Ka aikata duk abin da ka so, amma ka taɓa uwar gijiyata a wannan karon ƙarshen rayuwarka zan kawo a doron Duniya"
Jin tarin da Nana ta yi ne, ya sanya ta farkawa.
A ƙasa ta hango shi, maimakon kan katifa, yana wannan jijjigar da ya yi.
A rikice ta tashi ta nufe shi, tana ambaton Allah.
"Sayyid jikin ne dai?"
Wayarta ta ɗaukko, ta kunna karatun Alqur'ani, sannan ta ɗakko bargo ta lulluɓe shi da shi, ta zauna ta saka shi a gaba, ta zura masa ido cike da damuwa.
Har gefin Asuba, sannan Allah ya sanya ya daina wannan rawar sanyin.
*****
An kai ruwa rana da Mama sosai da sosai, kafin ta amince ta haƙura, amma da rantsuwa ta yi a kanz sai ta kai Gaddafi gurin 'yan sanda. Ana bata haƙuri shi kuma ya ce "Idan ba ta kai shi gurin 'yan sanda ba, ba Hudu mai ice ne ya haife ta ba" wato mahaifinta.
Duk da Baba yana cikin wannan tashin hankali, amma ya lura da sauƙin da ya samu, game da ciwon da ƙafarsa take yi masa tun jiya. Sai dai damuwa da tashin hankali ya sanya, bai mayar da hankali a hakan ba, ya karkata ga son kashe wutar da ta taso a gidansa.
****
Hajiya Amina na tsaye cikin matuƙar damuwa, Doctor Sharif ya ce "Hajiya ki yi haƙuri, amma a daren nan, za mu yi mata tiyata domin a ceto ta, da abin da yake cikinta.
"Kuma Doctor babu wata matsala, babanta ba ya kusa, haka ma mijinta"
"To Hajiya ai ba zamu bar ta haka a cikin ciwo ba, ki na kallo ba ta hayyacinta dole mu ceto ta da abin da za ta haifa".
Jiki a sanyaye Hajiya Amina ta karɓi consent form, ta saka hannu, tana mamakin yadda suka kwanta lafiya ƙalau da Shukura, har likitan da ya ganta da yamma, yana faɗin za a sallame ta washegari, a ce lokaci ɗaya ta rikice, duk da ba a tara sani da Allah, kuma babu kusa babu nesa a gare shi.
Haka tana tsaye aka turo Shukura a kan gado, aka shiga da ita tiyata. Ta koma gefe jikinta a sanyaye tana ta adduo'i daban-daban, tana fatan Allah ya sa ba abin da Shukuran take faɗa ne, zai faru ba, da take cewa tana ji a jikinta kamar mutuwa za ta yi, ba za ta rayu ba.
Shukura a hankali ta buɗe idonta, tana kallon likitoci a kanta, ba ta san me suke yi mata ba, ita dai tana jin ana girgiza ta.
Anesthetic ɗin ya ce "Kin farka?" Ta lumshe idanunta ta buɗe alamar eh.
"Ɗaga ƙafarki sama mu gani"
"Ba zan iya ba" ta faɗa a hankali.
Ya ce "To yauwwa, suma ki ka yi ne, shi yasa saboda kar a rasa ki, a rasa babyn, ake yi miki tiyata ba zai yiwu mu ci gaba da barin ki da shi ba, sai mu rasa ku, kuma ba mu sani ba sarkinmu ne na gobe ko shugaban ƙasa" ya yi maganar da sigar wasa.
Ta kasa dauke idanunta daga kan Doctor Sharif, da ya haɗa gumi suke ta ƙoƙarin ciro jaririn.
****
Ƙarfe bakwai da rabi, Nana ta dafa ruwa, ta kai masa banɗaki.
Ta zo kansa ta ce "Sayyid taso ka watsa ruwa, za ka ji daɗin jikinka sosai da sosai"
Ya tashi ya zauna, ya ɗan jima a zaune, sannan ya yinƙura, ta bi bayansa ta raka shi ƙofar banɗakin, ta miƙa masa zanin hannunta ta ce "Idan ka gama ka lulluɓa sai ka fito" bai karɓi zanin ba, ya kalle ta, sannan ya kalli banɗakin.
A take ta gane Abin da yake nufi, amma wani irin nauyin sa take ji, saboda ba su yi sabon da za a ce ta sake ta saba da shi haka ba. Amma ganin ya ja ya tsaya, ya ƙi gaba ya ƙi baya, ya sanya ta wuce shi, ta shiga banɗakin.
Bayan ta ya biyo, yana bin bango, saboda jirin da yake ji, Nana ta din ga sinne kai, tamkar ta gudu saboda tsananin kunyar da ta lulluɓe ta.
Kafin a gama wankan, ita ma sai da ya jiƙa ta jalaf da ruwan, tamkar ɗan ƙaramin yaron goye. Tana zuba masa ruwa a jiki yake zabura, kamar zai shiɗe, sai ya rirriƙe ta. Da dabara a hankali ta ci gaba da zuba ruwan a jikinsa. Ta gama ta goge masa jikinsa su ka fito.
Da ta kalle shi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, amma ta din ga dakewa, tana mazewa.
Ta soya dankalin Hausa da suke da shi, ta dafa shayi, ta zuba masa ta ajiye masa a gabansa.
"Ko na baka a baki?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
Ta yi murmushi, ta saka hannu tana ba shi.
Ya ƙura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi, ya ɗage girarsa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa.
Nana ta ce "Ai na san maganar ta ɗauke, ba sai ka yi mini magana ba, na fahimta" ya sake kallon ta da mamaki.
Ta ce "Ka manta ka ce mini ruhinka yana rayuwa a cikin nawa? Shi yasa nake fuskantar yinƙurinka ko ba ka furta ba"
Murmushi ya yi yana jinjina kai, ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya ɗago su daidai ƙirjinsa, 🙏 ya risunar da kansa alamar ya gode sosai.
Nana ta sauke hannun ta ce "Babu godiya tsakanina da kai, duk da ban san wace irin rayuwa ka baro a baya ba, amma kula da kai dolena ne Sayyid"
Idanunsa suka cika da hawaye, ya kamo hannayenta, ya din ga sumbata, ciki da waje. Tausayinsa ya ƙara mamaye ilahirin jikinta, cikin dakiya ita ma ta sumbaci hannunsa, ta ci gaba da bashi abinci. Sai da ya ƙoshi, sannan ta saka hau kan katifar ya jingina, ta rife masa ƙafafuwan sa da bargo. Ta tashi tana gyara ɗakin, horn ɗin mota ta ji, ya ɗago ya kalli Nana. Ta ce "Ka zauna kar ka tashi" ta saka Hijjabinta ta fita waje.
Matashin saurayin nan da take gani a gidan, mai tara samari su na kallon Ball ta gani a cikin mota. Ta ƙarasa inda motar take ya sauke gilashin motar ta ce "Sannu da fitowa"
Ya ce "Yauwwa sannu"
"Ka ga ba ya jin daɗi ne, ba shi da lafiya, bari na buɗe maka"
Ya dubi Nana ya ce "Subhnallah me ya same shi?"
"Zazzaɓi ne yake damun sa"
"Allah sarki, wataƙila malaria ce, unguwar akwai sauro sosai. Kin ga wani magani da likita ya bani ɗaya na sha, na ji daɗin sa sosai da sosai, nake yawo da shi a mota. Ki ba shi ga paracetamol ma, zai ji daɗin sa. Je ki kawai zan buɗe ƙofar Allah ya sauwwaƙe"
Nana ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai"
"Ahh ba damuwa" Nana ta ji dadin mutuntawar da ya yi mata, duk da za su yi sa'anni da shi, amma ya yi mata karamci saɓanin 'yar uwassa da ta wulaƙanta mata miji"
Ya sauka ya buɗe gate ɗin ya fita, ya dawo ya rufe.
Nana na shiga ɗakin, ta tarar da shi a tsakiyar ɗakin a tsaye, yana muzurai.
"Ya na ganka a tsaye kuma? Ka kwnata ka huta, ga magani ma ya bayar ya ce a baka, sai ka samu ka sha"
Ya koma kan katifar, ya kwanta, ba tare da ya tanka mata ba.
AREWABOOKS
***** Shukura ba ta san adadin lokacin da ta shafe ba ta hayyacinta ba.
A hankali ta buɗe idonta, amma sai dai dishi-dishi take gani, tana jin maganganu, amma sama-sama, ba ta gane me ake cewa. Sai sannu a hankali idanunta suka washe ta gane komai.
Mummy ta taso tana faɗin "Sannu Shukura ya jikin"
A wahale ta ce "Mummy"
"Na'am Shukura"
"Ina abin da na haifa?"
"Ki kwantar da hankalinki, an kai shi nursery ne, an saka shi kwalba"
Kawai Shukura ta fashe da kuka tana faɗin "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba mafarkina ne zai tabatta ba, dan Allah Mummy ni a karɓo mini ɗa na, a ciro shi daga kwalbar ba na so a dawo mini da jaririna ba na son wata kwalba"
Cikin damuwa Mummy ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Shukura yanka ki aka yi fa, ko awa uku ba a yi ba, sai kin yi wa kan ki illa? Mene ne dan an kai shi nursery?"
"Ni dai ba na so, ki ce su dawo mini da ɗa na, wallahi zan tashi na je na karɓo ɗa na, idan ba za ki karɓo mini ɗa na ba"
"Shukura ina za ki tashi ki je, jikinki da ciwo meye haka ne?"
Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi da gaske, sai ta tashi sai dai ƙafafuwanta suka ƙi motsawa. Hargowar Shukura da kukanta, ya janyo hankalin ma'aikatan gurin. Suka haɗu a kanta ana ba ta haƙuri, amma fafur ta ƙi yin shiru. A dole aka yi mata allurai ta koma bacci.
Sosai yake tsala gudu a kan titin, yana fatan ya isa gari ya waye.
Yana yi yana kallon inda ya kwantar da jaririn a gefensa, jikinsa kaca-kaca da ƙazantar haihuwa da sauran jini, ga mahaifarsa a gefe ita ma kaca-kaca da jini a jiki.
Yaron baya iya kuka, sai kaɗan-kaɗan, bakinsa sai rawa yake yi, saboda azabar sanyin da yake ji.
Alhaji Zailani yana yi yana kallon yaron, sai dai ƙirjinsa ya yi masa nauyi, ya rasa dalilin hakan. Yana matuƙar ƙaunar Shukura, haka kurum ya din ga jin kamar bai kyauta mata ba. Amma da ya tuna girman buƙatar sa, na mamaye duniyar sa da samun duk abin da ya sanya a gaba, sai ya ƙara azama da ƙara gudun giyar motar.
Daji ne sosai da sosai, ya yi parking ya ɗaukko jaririn, ya fita ya nausa cikin duhun duƙununun dajin. Yana tafe ya hango wuta tana ci, ya ƙarasa gurin da wutar take ci. Malam Gambo ne sanye da jajayen kaya, ya nufo shi yana faɗin "Ka kusa makara fa"
"A yi mini afuwa, amma ina fatan wannan aikin zai zama daidai da sadaukarwata ta shekara".
"Ƙwarai kuwa, ba za a sake neman jini daga gare ka ba a wannan shekarar"
Ya miƙa wa Malam Gambo jaririn, ya saka hannu ya karɓi yaron, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwansa a sama, ya danna tafin ƙafar jaririn, a take ya tsanyara ihu, ihun jaririn ya cika dajin.
Malam Gambo ya haska fitila, ya ɗaukko wani abu a cikin wata jaka, ya saka shi a wuta, ya yi ja ya juya bayan yaron, ya zana wani hatimi a jiki, ya sanya sunan Fatuhu Magaji a cikin hatimin. Yaron ya din ga tsala ihu tamkar ana zare masa rai.
Suka haɗu da shi da Malam Gambo, suka tona rami, suka binne jaririn da ransa.
Duk da ba yau Alhaji Zailani ya saba irin wannan abubuwan ba, amma na wannan karon shi kansa ya girgiza zuciyarsa.
Malam Gambo ya ɗauki mahaifar, ya ce "Wannan na 'yan aike ne, su za su cinye ta, kai za ka iya tafiya, bayan kwana talatin za mu zo a cire ƙwarangwal ɗin, za a yi wani aikin da shi. Ka huta ka yi yadda ka ke so Alhajin Allah, in dai Duniya ce ka same ta yadda ka ke so".
Suka yi sallama Alhaji Zailani, ya hau motarsa ya nufi gida.
A wani irin mugun razane Nana ta tashi daga nannauyan baccin da take yi, ta tashi zaune. Tsaf abin da ta gani ya dawo mata kai fes ba ta manta komai ba.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ka duba lamarin nan, Allah ya sa shirmen mafarki ne"